Instagram zai ba da damar dora bidiyo mai tsawon sa’a daya


Hakkin mallakar hoto
Instagram

Image caption

Daya daga cikin mutanen da suka kirkiro Instagram Kevin Systrom

Shafin Instagram ya fitar da wani tsari da ya bai wa masu amfani da shafin damar wallafa bidiyo masu tsawo.

Tsarin na IGTV zai sa masu amfani da shafin su dinga dora bidiyo mai tsawo sosai sabanin da da ake iya dora bidiyon da bai wuce minti guda ba kawai.

Sai dai babu cikakken bayani a kan ko bidiyo mai tsawo zai ba masu amfani da shafin damar tallata hajjarsu, ko kuma biyan wadanda suka sa bidiyonsu kamar yadda ake yi a shafin YouTube.

A hirar da ya yi da BBC Newsbeat, mutumin da ya kirkiro Instagram Kevin Systrom, ya ce kamfanin ba ya cikin “hanzari wajen gano yadda haka zai yiwu.”

IGTV zai rika nuna bidiyo kamar yadda mutane suke yi idan za su dauki hoto in ji Instagram.

Kevin ya ce: “Ya kamata a yi bidiyo mai kyau a waya.”

Alex Brinnand kwarare ne kan harkar fasaha daga mujallar TenEighty Magazine, ya ce watakila tsarin IGTV ya sa shafin Instagram ya kasance mai tasiri sosai a shafukan sada zumunta.

Ya ce: “Kawo yanzu ba mu san irin karfin da Instagram ya ke da shi ba.”

Na san akwai muhawara a kan abubuwan da ke faruwa a sauran shafukan sada zumunta da kuma yadda hakan zai kawo barazana, kuma wannan abu ne mai muhimanci.”

An dai shirya liyafar cin abinci iri- iri a taron kaddammar da tsarin na IGTV a birnin San Francisco na Amurka.

Bidiyon mai tsawo na da muhimanci sosai ga uwar kamfanin Instagram wato Facebook.

Matasa da kuma masu shekaru fiye 20 su na yin kaura daga amfani da Facebook zuwa Instagram, saboda a ganinsu shafin facebook ya fi dacewa da iyayensu ko ma kakanninsu.

Don haka matasan sun fi amfani da shafin Snapchat da kuma YouTube .

Kamar yadda ya yi a baya, Instgaram zai yi amfani da tsarin IGTV, wajen kwaikwaiyon sauran takwarorinsa.

Yana ganin idan ya kashe makudan kudi kuma ya inganta kayansa to hakan zai sa kayansa su samu karbuwa ko da ya kasance cewa ya fitar da nasa a makare.

Tuni manhajar ta soma amfani da wani bidiyo irin na Snapchat inda masu amfani da shafin suke wallafa labarin da ya ke bacewa bayan kwana daya, ta hanyar sanya hoto ko bidiyo.

Kudi mai yawa

IGTV ba zai tallata hajja ba sai dai shugaban Instagram Kevin Systrom ya amince da cewa wannan kan iya sauyawa nan ba da jimawa ba.

Kuma zai iya zama kuskure idan ba su yi hakan ba.

A kan bukaci kudi mai yawa idan za a tallata kaya a bidiyo fiye da sauran tallace-tallacen da ake yi a shafin intanet.

Cibiyar bincike ta eMarketer ta yi hasashen cewa za a kashe dala biliyan 18 wajen tallata hajja ta hanyar amfani da bidiyo a shafin intanet a bana – abin da ke nuni da cewa an samu karuwa da kashi 22 cikin 100 kan na shekarar 2017.

Sabuwar manhajar za ta ba da damar samun karin kudi.

“Shafin Facebook ya gano cewa tallar da kan fito a shafin intanet ba tare da mai shafin ya latsa ba, ba ya tsairi sosai a bidiyo mara tsawo saboda mutane ba su cika mayar da hankali a kansu ba,” in ji Joseph Evans, daga kamfanin Enders.

“A kan haka idan kana son ka saka tallace-tallace a bidiyo to za ka bukaci bidiyo mai tsawo.”

Shafin Facebook na bayan YouTube a tsakanin bibiyar da matasa masu shekaru 18-24 suke amfani da shafukan sada zumunta, kuma sune rukunin shekarun da ma su tallace-tallace suke so, a cewar wani bincike da wata cibiya a Amurka ta yi.

Kuma muhimmin abu a nan shi ne masu amfani da shafin YouTube na shafe tsawon lokaci a cikin shafin, inda suke kallon tallace-tallace daban-daban.

Me ya hana alkali halartar shari’ar Zakzaky a Kaduna?


Hakkin mallakar hoto
IMN

Image caption

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya dade yana saka kafar-wando daya daga gwamnati a Najeriya

An dage shari’ar da ake yi wa shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a Sheik Ibrahim Zakzaky a birnin Kaduna saboda rashin halartar alkalin kotun.

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare jagoran na ‘yan Shi’a ya shaida wa BBC cewa an gaya musu cewa alkali bai halacci zaman kotun ba a don haka aka dage shari’ar.

Duka bangarorin biyu sun amince su sake bayyana a gaban kotu a ranar 11 ga watan Yuli.

A watan Afrilu ne gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi malamin tare da wasu mutum uku da laifuka takwas ciki har da kisan wani soja a shekarra 2015, lamarin da suka sha musantawa.

Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai lokacin da suka yi arrangama da ‘yan shia a garin Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2015.

Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran ‘yan Shi’a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.

Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan aka yi awangaba da wasu da dama.

Amma lauyan na ‘yan Shi’a bai yi wani karin haske ba a kan dalilin da ya sa alkalin bai je kotun ba.

An rufe manyan hanyoyi a birnin na Kaduna da ke kusa da kotun gabanin shari’ar, in ji wakilin BBC a birnin, Nura Mohammed Ringim.

Hakkin mallakar hoto
WhatsApp

Image caption

‘Yan Shi’a na ci gaba da zanga-zangar neman a sako jagoransu

Rahotannin sun ce jami’an tsaro sun kuma hana ‘yan jarida da suka hallara shiga cikin kotun.

An samu arangama tsakanin ‘yan Shi’a da jami’an ‘yan sanda lokacin da su ka yi zanga- zanga a kan hanyar Ahmadu Bello a ranar Laraba inda suka nemi a sako mu su jagoran nasu.

A farkon watan da ya gabata ne magoya bayan Sheikh Zakzaky suka fara zanga-zanga cikin lumana a kowace rana a birnin Abuja inda suka nemi a sako mu su jagoran nasu.

Sai dai sun sha ruwan hayaki mai sa hawaye daga jami’an tsaro wadanda suka zarge su da ta tada fitina, zargin da suka musanta.

An ‘kashe jami’an tsaro 84’ a Kamaru


Hakkin mallakar hoto
AFP

Gwamnatin kasar Kamaru ta ce ‘yan awaren kasar sun kashe sojoji da ‘yan sanda 84.

Firai ministan kasar, Yang Philemon, ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana wadansu laifuka da gwamnatin kasar take zargin ‘yan awaren da aikatawa.

Mista Philémon ya kara da cewa masu fafitukar sun kashe wadansu jami’an gwamnati tare da yin garkuwa da su.

Kawo yanzu dai ‘yan awaren ba su yi tsokaci ba game da zargin da gwamnatin ta yi musu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Har ila yau firai ministan ya ce masu fafitikar ballewar yankin renon Ingila na kasar suna amfani da shafukan sada zumunta wajen saka kyashi da tsoro cikin zukatan mutane tare da yin kira kan a bijire wa gwamnati.

An dade dai ana kai ruwa rana tsakanin gwamatin kasar da masu fafitukar neman ‘yancin yankin renon Ingila wadanda suka ce ana nuna musu wariya.

Buhari na ziyara a Bauchi don jajanta bala’in iska da gobara


Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi domin jajantawa wadanda gobarar da aka yi a kasuwar garin Azare ta shafa da kuma bala’in guguwa a jihar.

Shugaban ya isa jihar da ke arewa maso gabashin kasar ne a ranar Alhamis da safe, inda Gwamna Muhammed Abubakar da kakakin majalisar dokokin jihar Kawuwa Damina suka tarbe shi.

A ranar Asabar ne aka yi wata mummunar guguwa a jihar wacce ta yi sanadin mutuwar mutum tare da jikkata wasu da dama, ta kuma lalata dukiyoyi.

An shafe sa’a guda ana iskar wacce ta jawo duhu a garuruwa da dama na jihar, al’amarin da ya sa gidaje da dama suka rushe.

Bayan wannan iftila’i ne kuma wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Azare na karamar hukumar Katagum a ranar Lahadi da daddare, inda ta shafe tsawon daren har zuwa wayewar garin Litinin ta na ci.

Gobarar ta jawo asarar dumbin dukiya da kawo yanzu ba a tantance adadinta ba.

Gabanin zuwan nasa na ranar Alhamis dai, shugaban ya aike da tawaga zuwa jihar don yin ta’aziyya da jajantawa al’ummar jihar, karkashin jagorancin ministan ilimi Malam Adamu Adamu.

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Image caption

Mutane sun taru sosai don yi wa shugaban kasar maraba da zuwa Azare

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Image caption

Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da Shugaba Buhari ke da goyon baya sosai

Shugabar kasar New Zealand Jacinda Ardern ta haifi ‘ya mace


Hakkin mallakar hoto
@jacindaardern

Image caption

Firai ministar New Zealand Jacinda Ardern ta wallafa hotonta da jaririyarta a shafin Instagram

Firai ministar New Zealand Jacinda Ardern ta haifi ‘ya mace ta farko mai nauyin kilogram 3.31.

Hakan ya sa ta kasance shugabar kasa ta biyu a zamanin nan da ta haihu a lokacin da take kan karagar mulki.

An kai Misis Ardern wani asibiti da ke garin Auckland da safiyar ranar Alhamis, kwana hudu kafin lokacin haihuwarta.

Firai ministar mai shekara 37 ta dauki hutun makoni shidda domin kula da jaririyarta kuma ta mika ragamar mulki ga mataimakin firai ministan kasar Winston Peters.

Sai dai ta ce za ta ci gaba da sa ido a kan yadda za a tafiyar da harkokin gwamnati.

Da misalin karfe 04:45 na agogon GMT shugabar kasar ta haihu.

Daga bisani Misis Ardern ta sanar da labarin haihuwarta a shafukan sada zumanta tana mai cewa tana ji kamar ta tsinci dami a dala kuma ta yi wa ma’aikatan asibitin godiya.

A cikin sanarwar da ta fitar ta ce : “Tabbas na san muna jin yadda sabbin iyaye suke ji a lokacin da suka samu karuwa amma kuma ina son na nuna godiya ga mutanen da suka kula da ni da kuma wadanda suka yi mata fatan alheri. Na gode .”

‘Yan siyasa sun rika tura mata sakonnin taya murna, ciki har da sakon da tsohuwar firai ministar New Zealand Helen Clark ta tura mata a shafin Twitter da kuma firai ministan Ostriliya Malcolm Turnbull.

A watan Oktoban da ya gabata ne aka zabi Misis Ardern, kuma a watan Janairun da ya gabata ne ta yi shellar cewa ita da saurayinta Clarke Gayford za su samu karuwa nan ba da jimawa ba.

“Ba ni ce mace ta farko da take abubuwa na komai da ruwanka ba”.

“Ba ni ce mace ta farko da ke aiki kuma ta haihu ba; akwai mata da dama da suka yi haka a baya,” Ta bayyanna hakan ne a wata hira da ta yi da wani gidan rediyon New Zealand a farkon bana.

Mai jegon ita ce firai minista mafi kankantar shekaru da aka samu a kasar tun bayan shekarar 1856.

A shekarar 1990, Benazir Bhutto ta haifi ‘ya mace tana rike da mukamin firai ministar Pakistan, kuma ita ce haihuwar farko da wata zababbiyar shugabar kasa za ta yi a lokacin.

Madam Ardern ta kuma haifi jaririyarta ne a ranar da aka haifi marigayiya Benazir Bhutto.

Mu ba ‘yan amshin shatan Buhari ba ne – Majalisa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Majalisar dokokin Najeriya ta mayar da martani game da korafin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi a kan cewa bangaren ya yi masa cushe a cikin kasafin kudin da ya mika masa.

Shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar, Abdulrazak Namdas, ya ce daya daga cikin dalilan da suka sa majalisar ta rage kudaden da za a saka a wasu ayyuka shi ne ganin cewa ba lallai ba ne a iya amfani da kudaden da aka fitar wa ayyukan cikin shekara daya ba.

Shugaba Buhari ya ce bai ji dadin yadda ‘yan majalisar suka ki neman izinin bangaren zartarwa kafin su kara wasu kudade a kasafin kudin na naira triliyan 1.9 ba, wanda ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Namdas ya ce, “Duk lokacin da aka ce majalisa ta amince da kasafin kudi, wata ranar za a ce wannan ma’aikatar an ba ta kudi kamar biliyan hudu, za ka tarar a cikin kasafin kudi.

Majalisa ba ‘yan amshin shatan bangaren zartarwa ba ne, a don haka bai kamata su yi tunanin duk abin da suka turo zai wuce kamar yadda suke so ba, a cewar sanarwar.

“Amma fannin zartaswa ba zai fitar da kudin nan ba. Za ka tarar cewa har shekara ta kare bliyan daya kawai fannin zartarwa ya bayar. Za ka ga biliyan uku na zaune ba aiki.

“Mu kuma muna zaune a wannan majalisar shekara da shekaru. Ba kasafin kudin shekara daya muka gani ba, ba biyu muka gani ba, mun gan su da yawa.

“Don haka maimakon ka dauki kudi ka ajiye a wata ma’aikata wanda za a zo, a cikin biliyan 10, a sake biliyan uku ko hudu, gara ka dauki wasu kudaden da ba za a yi amfani da su ba ka kai ma’aikatar da za ta amfani jama’a,” a cewar Namdas.

Game da kudin da ‘yan majalisar suka kara wa kansu kuma ba tare da neman izinin bangaren zartarwa ba, dan majalisar ya ce tun shekarar 2015 ne dai ake rage wa majalisar kasafin, kuma ya ce yadda wasu ma’aikata ke neman kari haka shi ma bangaren dokoki ke namen kari.

Hakkin mallakar hoto
Bashir Ahmed/Twitter

Image caption

Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin naira tiriliyon 9.1 ne a Abuja a ranar Laraba

Namdas ya kuma ce ba gaskiya ba ce cewar ‘yan majalisar na yi wa gwamnatin Buhari zagon kasa domin dambarwar siyasar da ake yi tsakanin bangarorin zartarwa da na dokoki, yana mai cewa wasunsu sun samu cin zabe ne da sunan shugaban na Najeriya.

Korafin Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa game da wadansu sauye-sauye da majalisa ta yi a kasafin kudin bana, bayan ya sanya hannu kansa a ranar Laraba.

Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin na naira tiriliyon 9.1, bayan majalisar dokokin kasar ta amince da shi a tsakiyar watan Mayu.

Sai dai shugaban ya ce bai ji dadin yadda majalisar ta rage biliyoyin naira da aka ware don yin wadansu manyan ayyuka ba, a kasafin, wanda ya gabatar a watan Nuwambar bara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A farko-farkon hawan shugabannin mulki dai akwai jituwa a tsakaninsu kafin daga bisani a dinga samun sa-in-sa

Ayyukan sun hada da aikin tashar wutar lantarki ta Mambila da gada ta biyu ta kogin kwara da gina wadansu tituna da layin dogo da shirin gina gidaje na gwamnatin tarayya da wadansu ayyuka a bangaren kiwon lafiya da samar da tsaro da sauransu.

Sai dai ‘yan majalisar sun ce sun yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da adalci a tsakanin yankunan kasar kamar yadda tsarin mulki ya ba su dama.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, ba tare da tuntubar bangaren zartarwa ba, majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14, wanda a ya sa a yanzu take da kasafin sama da naira biliyan 139 maimaikon naira biliyan 125 da aka ware mata tun da fari.

Shugaban kasar dai ya ce yana da aniyar gyara wasu muhimman sauye-sauyen da aka yi ta hanyar gabatar da wani kwarya-kwaryan kasafi ga majalisar ko kuma yin gyara ga wannan kasafin.

Sharhi, Muhammad Kabir Muhammad, BBC Abuja

Alkaluma na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta Najeriya (wato National Bureau of Statistics ko NBS a takaice) ta fitar sun nuna cewa a watan Maris, kimar hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a Najeriya idan aka kwatanta da watan Fabrairu, daga kashi 14.33 cikin 100 zuwa kashi 13.34 cikin 100.

Wannan ne kuma wata na 14 a jere da kimar hauhawar ke raguwa.

“Wannan raguwar, a karo na 14 a jere tun daga watan Janairun 2017, ta nuna hauhawar ta ragu da kashi 0.99 cikin dari idan aka kwatanta da watan Fabrairun bana”, in ji NBS.

Daga watan Fabrairun 2016 ne dai kimar hauhawar ta fara tashin gwauron zabi (lokacin da ta tashi daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu zuwa kashi 11.38 cikin dari) har ta kai matakin da aka yi shekara shida ba a kai makamancinsa ba a watan Janairun 2017, lokacin da ta kai kashi 18.72 cikin 100 (duba hoton da ke kasa).

Tattalin arzikin Najeriya a shekara uku da suka wuce

 • Mayu 2015: Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki
 • Fabrairu 2016: Farashin danyen man fetur ya fadi warwas zuwa kasa da $35 daga $115 a watan Yunin 2014
 • Fabrairu 2016: Kimar hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 11.38 cikin dari daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu
 • Afrilu 2016: A rubu’i na farko na 2016 kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi asarar sama da tiriliyan daya na Naira. Zuwa karshen shekarar kuma jimillar abin da ta yi asara ya tashi naira biliyan 604.
 • Yuni 2016: CBN ya karyar da darajar Naira
 • Agusta 2016: Tattalin Arzikin Najeriya ya durkushe a hukumance
 • Satumba 2017: Tattalin arzikin Najeriya ya farfado

Najeriya dai ita ce kasar da ta fi ko wacce arzikin danyen mai a Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen da suka fi arzikin man a duniya. Kuma tattalin arzikinta ya dogara ne matuka a kan man, ko da yake gwamnati mai ci na ikirarin fadada hanyoyin samun kudaden shigar.

A bara ne kasar ta farfado daga matsin tattalin arziki, wanda aka kwashe kimanin shekaru 25 ba ta shiga irinsa, a sanadiyyar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Danyen mai na Bonny Light wanda Najeriya ke samarwa na daga cikin mai mafi tsada a kasuwannin duniya.

Ko Messi da Argentina za su kai labari?


Hakkin mallakar hoto
EPA

Daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya na fuskantar kalubalen ficewa daga gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha.

Lionel Messi na Argentina, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyar, zai jagoranci kasarsa a wasa na biyu na rukunin D da za su kara da Croatia.

Za su shiga wannan wasa ne da matsin lamba ganin cewa sun tashi canjaras ne kawai a wasansu na farko da Iceland.

Hakan ya sa Argentina samun maki daya, yayin da Croatia ta doke Najeriya da ci 2-0, abin da ya bata maki uku, kuma ta kasance jagora a rukunin.

Idan har Argentina ta sha kaye a hannun Croatia, kuma Iceland ta samu nasara a kan Najeriya ranar Juma’a, to babu shakka makomarta a gasar za ta kara shiga cikin rashin tabbas.

Messi, wanda ya lashe gasar cin kofin Zarakun Turai sau hudu da Barcelona, da kofunan La Liga da sauran kofuna da dama a matakin kulob, bai taba cin wani muhimmin kofi da tawagar kasarsa ba.

Kuma wasu na ganin wannan ce gasar kofin duniya ta karshe da gwarzon dan kwallon zai taka.

Musamman ganin cewa ya taba sanar da yin ritaya daga bugawa Argentina kwallo a baya, kafin daga bisani ya sauya shawara.

Messi zai so ya nuna kansa kuma ya fitar da kasarsa kunya, musamman ganin yadda ya zubar da fanareti a wasansu da Iceland.

Bugu da kari ganin yadda babban abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ya ke haskakawa a gasar, inda kawo yanzu ya ci kwallo hudu a wasa biyu.

Wasu dai na ganin Messi zai yi kukan-kura a wasan na Croatia domin ceto Argentina daga barazanar da ta ke fuskanta na ficewa daga gasar.

Sai dai a gefe guda wasu na ganin cewa zai yi wuya, kuma ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, musamman ganin yadda ita ma Crotia ba kanwar lasa ba ce.

Wasannin da za a buga a ranar Alhamis

13:00 BST DENMARK v AUSTRALIA

16:00 BST FRANCE v PERU

19:00 BST ARGENTINA v CROATIA

Jifan kwallon da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Rasha


Hakkin mallakar hoto
The sun

Wani jifan kwallon da dan wasan baya na kasar Iran Milad Mohammadi, ya so ya yi ya shafe duk wani abin bajinta da aka yi a wasannin da aka buga na cin kofin kwallon duniya a ranar Larabar data wuce.

Wannan jifa da dan wasan ya yi a cikin mintin karshe na wasan da Spain ta doke Iran, ya haifar da muhawara da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da kuma bakunan masu sharhi kan wasan kwallon kafa.

Abin ya faru ne a dai-dai lokacin da ake gab da tashi a wasan, sa’ilin da Iran ke matukar bukatar jefa kwallo guda daya domin yin canjaras da Spaniya

Milad Mohammadi, ya dauki kwallon bayan da ta tsallake layi domin yin jifan turoyin.

Ya ja da baya sosai, ya sumbaci kwallon da ke hannunsa, sannan ya rugo da gudu ba tare da ya jefa kwallon ba.

Daga nan ne ya sake ja da baya, a yayin da ya rage saura dakika talatin a tashi wasa, ya sake sumbatar kwallon ya taho da gudu ya yi alkafura a kasa sannan ya mike tsaye a dai-dai bakin farin layi da niyyar jefa kwallon zuwa cikin fili, inda sauran ‘yan wasa ke jira.

Sai dai alkalin wasa ya katse masa hanzari ta hanyar hura usur, sannan ya bukace shi da ya jefa kwallon kamar yadda aka saba yi.

Wannan al’amari dai ya bai wa masharhanta da kuma masu kallo mamaki, abin da ya sanya hakan ya zama babban labari jim kadan bayan kammala wasan.

Hotunan yadda mata ke koyon tukin mota a Saudiyya


A daidai lokacin da Saudiyya ke shirin fara barin mata su yi tuki a ranar 24 ga watan yuni, kamfanin mai na kasar watau Aramco na koya wa ma’aikatanta mata tuki

Mai daukar hoton kamfanin dillancin labaran Reuters, Ahmed Jadallah da kuma ‘yar jaridar kamfanin Rania El Gamal, sun kasance tare da mata ma’aikata 200 da ake koya wa tuki a sansanin koyon tuki da ke Dhahran mallakar kamfanin Saudi Aramco.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Daya daga cikin daliban ita ce Maria al-Faraj (wadda aka saka hotonta a kasa), wadda take daukar darasin tuki daga Ahlam al-Somali.

Student Maria al-Faraj with driving instructor Ahlam al-SomaliHakkin mallakar hoto
Reuters

Baya ga koyon tuki, tana kuma koyon yadda za ta iya auna gejin mai da sauya taya da kuma muhimmancin amfani da madaurin kujerar mota.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

Dage dokar da ta hana tukin matan wani muhimmin lokaci ne ga mata a Saudiyya. A baya a kan kama su ko a ci su tara idan an gansu suna tuki kuma sun dogara a kan maza ‘yan uwansu wadanda za su tuka su idan za su fita ko yin hayar direba.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

Amira Abdulgader wadda kwararriya ce wajen zanen gine-gine (ga hotonta a kasa) ta ce ranar 24 ga watan Yuni ta na shirin jan mahaifiyarta a mota.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

“Zama a rike sitiyarin [na nufin ] ke kike jan ragaramar tafiyar,” in ji Amira Abdulgader.

“Ni ce zan yanke shawarar lokacin da ya kamata a yi tafiya, abin da za a yi, da kuma lokacin da zan dawo.

“Muna bukatar mota domin mu yi ayyukanmu na yau da kullum. Mu na aiki, mu iyaye ne, muna sada zumunta ta kafafen sadarwa na zamani, muna bukatar fita – saboda haka muna bukatar sufiri. Zai sauya rayuwata.”

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

Kashi biyar cikin 100 na ma’aikatan kamfanin Aramco su 66,000 mata ne, kuma abin da haka ke nufi shi ne cewa watakila mata dubu uku za su shiga makarantar koyon tuki a cewar, Reuters.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in DhahranHakkin mallakar hoto
Reuters

Duk da cewa an yaba wa Saudiyya game da soke dokar hana mata tuki, sai dai an samu ce-ce-ku-ce game da lamarin.

Masu fafituka da suka kasance suna neman a soke dokar sun samu sakonnin barazanar kisa, kuma an kama wasu daga cikinsu a watan Mayu kan cewar maciya amana ne kuma suna cewa suna aiki wa kasashen waje.

Hotuna daga Ahmed Jadallah.

Maganin rage radadi ya kashe mutum 456


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani rahoto ya gano cewa fiye da marassa lafiya 450 sun mutu bayan an ba su maganin rage radadi wato painkillers masu karfi a wani asibiti da ke Birtaniya.

Wani kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar wannan lamari, ya ce idan aka yi la’akari da wasu bayanan da suka bata, to za a iya samun wasu marassa lafiyar 200 da suma irin wannan iftila’i ya shafa.

Wannan lamari dai ya faru ne a asibitin Gosport War Memorial Hospital,da ke Birtaniya.

Rahoton ya gano cewa, ba a damuwa da rayuwar marassa lafiya a kasar tun daga shekarar 1989 zuwa 2000.

Rahoton ya ce, Dr Jane Barton ce ta lura da yadda ake rubutawa marassa lafiya magani ba bisa ka’ida ba.

Ana dai rubuta magani ga marassa lafiya barka tai ba tare da la’akari da irin illar da shan sa zai haifar ba asibitin.

Firaministan kasar, Theresa May, ta bayyana wannan lamari da ya faru a asibitin a Gosport da cewa abin damuwa ne matuka gaya, sannan kuma ta nemi afuwa daga iyalan da lamarin ya shafa.

Babban sakatare a ma’aikatar kula da lafiya a kasar, Jeremy Hunt, ya shaida wa jami’an ‘yan sanda da kuma masu shigar da kara na kasar cewa, zai yi nazari a kan rahoton, sannan ya duba matakin da za a dauka na gaba a kan wannan badakala.

Yawancin iyalan wadanda lamarin ya shafa, sun yi allawadai da asibitin, tare da neman da a shigar da asibitin kara a kotun hukunta manyan laifuka, saboda a cewarsu, wannan lamari na tare da sakaci a wajen aiki.

Karanta wasu karin labaran

Kasafin kudi: Ban ji dadin cushen da majalisa ta yi ba – Buhari


Hakkin mallakar hoto
Bashir Ahmed/Twitter

Image caption

Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin naira tiriliyon 9.1 ne a Abuja a ranar Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa game da wadansu sauye-sauye da majalisa ta yi a kasafin kudin bana, bayan ya sanya hannu kansa a ranar Laraba.

Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin na naira tiriliyon 9.1, bayan majalisar dokokin kasar ta amince da shi a tsakiyar watan Mayu.

Sai dai shugaban ya ce bai ji dadin yadda majalisar ta rage biliyoyin naira da aka ware don yin wadansu manyan ayyuka ba, a kasafin, wanda ya gabatar a watan Nuwambar bara.

Ayyukan sun hada da aikin tashar wutar lantarki ta Mambila da gada ta biyu ta kogin kwara da gina wadansu tituna da layin dogo da shirin gina gidaje na gwamnatin tarayya da wadansu ayyuka a bangaren kiwon lafiya da samar da tsaro da sauransu.

Sai ‘yan majalisar sun ce sun yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da adalci a tsakanin yankunan kasar kamar yadda tsarin mulki ya basu dama.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, ba tare da tuntubar bangaren zartarwa ba, majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14, wanda a ya sa a yanzu take da kasafin sama da naira biliyan 139 maimaikon naira biliyan 125 da aka ware mata tun da fari.

Shugaban kasar dai ya ce yana da aniyar gyara wasu muhimman sauye-sauyen da aka yi ta hanyar gabatar da wani kwarya-kwaryan kasafi ga majalisar ko kuma yin gyara ga wannan kasafin.

Martanin Majalisa

A nata bangaren, majalisar dai ta ce ta kara kasafin ne daga sama da naira tiriliyan 8 zuwa sama da tiriliyan 9 saboda hasashen cewa farashin danyen mai zai iya kai wa dalar Amurka 51 a kowacce ganga, ba dala 45 da shugaban ya sanya ba.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Abdulrazak Namdas ya ce dokar kasar ta ba su damar su yi ragi ko kuma kari a kasafin kudi a wuraren da suka kamata.

Game da ayyukan da aka ce ‘yan majalisar sun kara, ya ce su ma wakilai ne “na jama’a kuma suna da damar sanya ayyukan da za su yi tasiri a rayuwar talaka,” kamar yadda wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ta ce.

Hakazalika ya ce game da batun cewa majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14 a kasafin kudin, ya ce kafin shekarar 2015 ana ware majalisar naira biliyan 150 a kasafin kudin.

“Amma sai aka rage zuwa naira biliyan 120 a shekarar 2015, aka kuma kara rage shi zuwa naira biliyan 155 a shekarar 2016, sai a shekarar 2017 da aka ware mana naira biliyan 125, bana kuma naira biliyan 139.”

Ya ce: “ka ga ke nan har yanzu bai koma yadda aka saba yinsa ba kafin shekarar 2015, wato yadda ake ware mana naira biliyan 150,” in ji shi.

Sharhi, Muhammad Kabir Muhammad, BBC Abuja

Alkaluma na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta Najeriya (wato National Bureau of Statistics ko NBS a takaice) ta fitar sun nuna cewa a watan Maris, kimar hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a Najeriya idan aka kwatanta da watan Fabrairu, daga kashi 14.33 cikin 100 zuwa kashi 13.34 cikin 100.

Wannan ne kuma wata na 14 a jere da kimar hauhawar ke raguwa.

“Wannan raguwar, a karo na 14 a jere tun daga watan Janairun 2017, ta nuna hauhawar ta ragu da kashi 0.99 cikin dari idan aka kwatanta da watan Fabrairun bana”, in ji NBS.

Daga watan Fabrairun 2016 ne dai kimar hauhawar ta fara tashin gwauron zabi (lokacin da ta tashi daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu zuwa kashi 11.38 cikin dari) har ta kai matakin da aka yi shekara shida ba a kai makamancinsa ba a watan Janairun 2017, lokacin da ta kai kashi 18.72 cikin 100 (duba hoton da ke kasa).

Tattalin arzikin Najeriya a shekara uku da suka wuce

 • Mayu 2015: Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki
 • Fabrairu 2016: Farashin danyen man fetur ya fadi warwas zuwa kasa da $35 daga $115 a watan Yunin 2014
 • Fabrairu 2016: Kimar hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 11.38 cikin dari daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu
 • Afrilu 2016: A rubu’i na farko na 2016 kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi asarar sama da tiriliyan daya na Naira. Zuwa karshen shekarar kuma jimillar abin da ta yi asara ya tashi naira biliyan 604.
 • Yuni 2016: CBN ya karyar da darajar Naira
 • Agusta 2016: Tattalin Arzikin Najeriya ya durkushe a hukumance
 • Satumba 2017: Tattalin arzikin Najeriya ya farfado

Najeriya dai ita ce kasar da ta fi ko wacce arzikin danyen mai a Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen da suka fi arzikin man a duniya. Kuma tattalin arzikinta ya dogara ne matuka a kan man, ko da yake gwamnati mai ci na ikirarin fadada hanyoyin samun kudaden shigar.

A bara ne kasar ta farfado daga matsin tattalin arziki, wanda aka kwashe kimanin shekaru 25 ba ta shiga irinsa, a sanadiyyar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Danyen mai na Bonny Light wanda Najeriya ke samarwa na daga cikin mai mafi tsada a kasuwannin duniya.

Jami’ar OAU ta kori farfesan da ya nemi yin lalata da dalibarsa


Hakkin mallakar hoto
OAU

Image caption

Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

Hukumomi a Jami’ar Obafemi Awolowo sun kori wani babban malami bayan samunsa da laifin neman yin lalata da wata daliba domin ba ta damar cin jarrabawa.

Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya ce an kori Farfesa Richard Akindele ne bayan da ya amsa laifin kulla alaka da daya daga cikin dalibansa ta hanyar ba ta dace ba.

“Farfesa Akindele ya nemi yin lalata da Monica Osagie domin sauya maki kashi 33 da ta ci zuwa adadin da zai ba ta damar tsallakewa,” a cewar Ogunbodede.

A watan Afrilu ne aka dakatar da Mr Akindele domin gudanar da bincike bayan da aka nadi muryarsa yana neman yin lalata da wata daliba domin ba ta sakamakon jarabawa.

Muryar ta Farfesa Akindele, wanda ke koyarwa a sashin harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi na jami’ar, ta bazu a shafukan sada zumunta.

Lamarin dai ya janwo ce-ce-ku-ce a kasar tare da nuna damuwa kan halayyar wadansu malamai game da dalibansu.

Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba bayan taron hukumar makarantar, Farfesa Eyitope Ogunbodede ya ce an tabbatar da muryar da aka rinka yada wa a watan Afrilu, kuma babban malamin bai musanta cewa tasa ba ce.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

A lokacin da aka fara bincike kan lamarin, mai magana da yawun jami’ar ya shaida wa BBC cewa Monica ba ta halarci gayyatar da kwamitin ya yi mata ba, sannan ba ta tura da wakilci ko wani uzuri ba.

Babu tabbas ko daga baya ta halarci zaman kwamitin ko kuma ta aika wakili.

Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami’o’in Najeriya.

Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin dan adam ta MDD


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Jakadar Amurka a MDD Nikki Haley da sakataren harkokin wajan Amurka Mike Pompeo suka sanar da matakin

Amurka ta janye daga hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, tana mai cewa “mattatara ce ta nuna son kai ta fuskar siyasa.”

Jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta ce hukuma ce da ke cike da “munafinci”, “wadda ta ke yi wa harkokin kare hakkin bil adama zagon kasa.”

Hukumar da aka kafa a shekarar 2006, wadda ofishinta ya ke Geneva ta rika fuskantar suka a baya saboda ta amince da wasu mambobi masu alamar tambaya wajen kare hakkin bil’adam.

Sai dai masu fafituka sun ce matakin da Amurka ta dauka kan iya yin nakasu ga kokarin da ake yi wajen sa ido da kuma kawo karshen cin zarafin bil adama a duniya baki daya.

A lokacin da ta yi shelar ficewar Amurka daga hukumar, Ms Haley ta bayyana hukumar a matsayin “munafika wadda ta ke nuna son kai” wadda kuma ta ke “nuna wa Israila kiyaya.”

Ta bayyana hakan ne tare da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, wanda ya yi Allah-wadai da hukumar, yana mai cewa tana kare kasashe masu “tauye hakkin bil’adama.”

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Niki Harley ce Jakadiyar Amurka a MDD

Sukar da jami’an Amurkan suka yi ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da aka rika yi a kan matakin da Shugaba Trump ya dauka na jinjina wa shugaban kasar Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un, a taron da suka yi a baya-baya nan inda bai tabo batun cin zarafin bil adama ba.

MDD ta sanya Koriya ta Arewa a cikin jerin kasashen duniya da ake cin zarafin bil adama kuma ta tattara bayanan cin zarafin bil dama a cikin kasar da ke gudanar da harkokinta cikin sirri.

Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da manufar gwamnatin Shugaba Trump ta kara zafafa, inda ake raba yara da iyayensu ‘yan ci-rani a iyakar Mexico da Amurka.

Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam, Zeid Ra’ad Al Hussein, ya kira matakin a matsayin “kuskure.”

Sakatare janar na MDD António Guterres ya mayar da martani kan matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga hukumar, yana mai cewa a ra’ayinsa yana son Amurka ta ci gaba da kasancewa mamba a cikin hukumar.

Mr Hussein ya kira ficewar Amurka a matsayin “abin takaicin, da ya zo da ba-zata”. Sai dai Israila ta yi maraba da matakin.

Sharhin Nada Tawfik, wakiliyar BBC a New York

Wannan shi ne matakin kin amincewa da hadewar kasashen duniya a matsayin tsintsiya madaurinki daya da gwamnatin Trump ta dauka, kuma watakila hakan zai sa wasu kasashen duniya da suka dogara a kan Amurka wajen samun kariya da daukaka hakkin bil dama a duniya su nuna rashin jin dadinsu.

Tun farko babu jituwa a dangatakar da ke tsakanin Amurka da hukumar kare hakkin dan Adam.

Tsohuwar gwamnatin Shugaba Bush ta yanke shawarar kaurace wa hukumar a lokacin da aka kafa ta a shekarar 2006, saboda wasu dalilai irin wanda gwamntin Trump ta bayar.

A wancan lokacin John Bolton shi ne jakadan Amurka a MDD wanda a yanzu shi ne mai bai Shugaba Trump shawara kan tsaron kasa, kuma mai kakkausar sukar MDD ne.

A shekarar 2009 ne Amurka ta sake komawa cikin hukumar karkashin gwamnatin Barack Obama.

Akwai kawayen Amurka da dama da suka yi kokarin shawo kan Amurka a kan ta cigaba da kasancewa cikin hukumar.

Akwai kasashe da dama da suka amince da matsayin Amurka na sukar hukumar, wadanda suke ganin cewa ya kamata kasar ta ci gaba da taka rawa a cikin hukumar ta hanyar kawo sauye-sauye a maimakon ficewa daga ciki.

Bayyani kan hukumar kare hakkin biladama

A shekarar 2006 ne MDD ta kafa hukumar domin ta maye gurbin ofishin kare hakkin dan adam wanda ya rika fuskantar suka a wurare da dama saboda ya amincewa kasashen da ba sa mutunta hakkin dan Adam shiga cikin kungiyar.

Kasashe 47 ne suka taru suka kafa hukumar, kuma sai bayan wa’adin shekara uku na shugaban hukumar ya zo karshe suke zabe domin samun wanda zai maye gurbinsa.

Hukumar ta UNHRC na taro sau uku a ko wacce shekara tare da yin nazari a kan ayyukan kare hakkin bil adama na mambobinta kuma ta bai wa ko wacce kasa damar yin bayani a kan abubuwan da suka yi domin inganta hakkin bil adama a kasashensu.

Hukumar kan tura kwararu masu zaman kansu zuwa kasashe domin su yi bincike, kuma tana kafa kwamitin bincike kan rahoton cin zarafin bil adam a kasashe irinsu Syria da Koriya Ta Arewa da Burundi da Myanmar da kuma Sudan Ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Hukumar na taro sau uku a ko wacce shekara kuma tana nazari kan mambobinta kan baututuwan kare hakkin bil adam

Shin me yasa Amurka ta fice?

Matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga cikin hukumar ya biyo bayan sukar da ta rika yi mata a shekarun da suka gabata.

Kasar ta ki shiga cikin hukumar da aka kafa a shekarar 2006, tana mai cewa babu banbanci tsakanin sabuwar hukumar da kuma tsohuwar, saboda sabuwar hukumar ta sake amincewa kasashe masu alamar tambaya kan hakkin dan adam shiga cikin hukumar.

A shekarar 2009 ne ta koma cikin hukumar karskashin Shugaba Barack Obama, kuma an sake zabarta a cikin hukumar a shekarar 2012.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun rika yin korafi a kan hukumar a shekarar 2013, bayan da aka zabi China da Rasha da Saudiyya da Algeriya da Vietnam a matsayin mambobin hukumar.

Yadda ‘ya’yan ‘yan ci-ranin Amurka ke kukan an raba su da iyayensu


Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An saki wasu muryoyin yaran ‘yan ci-ranin Amurka da aka nada suna kuka sakamakon raba su da iyayensu, yayin da Shugaba Donald Trump ke ci gaba da bujirewa sauya dokokin ‘yan ci-rani.

Kusan ‘ya’yan ‘yan ci-rani 2,000 ne aka raba da iyayensu a watannin da suka gabata, bayan da iyayensu su ka yi kokarin shiga Amurka ta kan iyaka ba tare da izini ba.

Mista Trump ya ce ba zai bari Amurka ta zama sansanin “‘yan ci-rani ba.”

Russia 2018: Ronaldo ya kora Maroko gida


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Cristiano Ronaldo ya ci gaba da cin kwallo a gasar kofin duniya, inda ya ci kwallo daya tilo da ta bai wa kasarsa damar cire Maroko daga gasar kofin duniya.

Hankali ya koma kan dan wasan na kungiyar Real Madrid a filin wasa na Luzhniki Stadium tun da aka fara wasan, bayan kwallo ukun da ya ci a wasan kasarsa na farko da Spain.

Kuma dan wasan ya ba marada kunya.

Kyaftin din na Portugal ya ci kwallon ne a minti na hudu da fara wasan.

Kwallon ta Ronaldo ta saka zakarun na nahiyar Turai a saman rukunin B, kafin Spain ta kara da Iran ranar Laraba.

Maroko wadda ta rasa samun karbar bakuncin gasar kofin duniya wadda za a yi a shekarar 2026 a makon jiya, ta zama kasa ta biyu da aka cire daga gasar ta kofin duniya bayan kasar Masar.

Jiragen yakin Isra’ila sun kai harin ‘ramuwa’ Gaza


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Rundunar sojin Isra’ila ta ce jiragen yakin sun kai harin ne kan sansanoni 25 da ke da alaka da Kungiyar Hamas

Rundunar sojin Isra’ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari sansanonin mayakan sa kai da ke Gaza bayan da Falasdinawa suka harba rokoki cikin yankin Isra’ila.

Wata sanarwa ta ce jiragen yakin sun kai harin ne kan sansanoni 25 da ke da alaka da Kungiyar Hamas domin mayar da martani kan lugudan wutar rokoki 45 da suka yi wa Isra’ilan.

An yi amannar cewa wasu jami’an tsaron Hamas biyu sun ji rauni kadan. Amma babu rahoton da ke nuna cewa an samu asarar rai ko jin ciwo daga bangaren Isra’ila.

Hare-haren dai na zuwa ne bayan da aka shafe makonni ana fito-na-fito a kan iyakar Zirin Gaza.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce dakarun Isra’ila sun kashe Falasdinawa fiye da 120 tare da raunata dubbai tun lokacin da aka fara zanga-zangar a watan Maris.

Dubban Falasdinawa sun fito zanga-zangar a kan iyaka don nuna goyon bayan ganin ‘yan gudun hijirar Falasdinu sun samu ‘yancin komawa matsugunansu na asali inda ya kasance Isra’ila a yau.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi dakarun Isra’ila da amfani da karfi fiye da kima.

Sai dai Isra’ila ta ce su na bude wuta ne kawai a kokarin kare kansu ko a kan mutanen da suke son su shiga yankinsu da karfin tuwo da sunan zanga-zanga.

Sojin Isra’ila ta ce ta kai hari da jiragen yaki sau uku cikin dare a wasu wuraren Hamas – ciki har da wasu sansanonin soji – bayan an harba rokoki a kan kauyuka da garuruwan Isra’ilan da ke kan iyakar Gaza.

Isra’ila ta kakkabo rokoki bakwai da mayaka suka harba, in ji rundunar sojin kasar.

An kuma aika jiragen leda dauke da wuta da mai zuwa cikin Isra’ila.

Hukumar yankin Eshkol Regional da ke kudancin Isra’ila ta ce rokoki biyu sun fadi kusa da wata cibiyar al’umma, kuma roka ta uku ta lalata gine-gine da motoci.

Kamfanin dillancin labaran Faladisnawa na Wafa, ya bayar da rahoton cewar a kalla mutum uku sun jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai kudancin Gaza – biyu sun mutu a Rafah, kuma daya ya mutu a Khan Younis.

Mazauna garin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar biyu daga cikinsu jami’an tsaron Hamas ne.

Wani mazaunin wurin ya shaida wa jairidar Haaretz ta Isra’ila cewar: “Kara da kuma fashe-fashen abubuwan sun tuna mana wani daren lokacin zafi na shekarar 2014,” yayin da yake nuna ishara ga muhimmin fito-na-fito na baya-bayan nan da aka yi tsakanin Isra’ila da mayakan Falasdinawa a Gaza.

Rundunar sojin Isra’ila sun gargadi Hamas da cewar tana kokarin shigar da zirin Gaza da farar-hularta cikin wani tafarki mai tabarbarewa.

Ta kara da cewa: “Hamas ce ke da alhakin dukkan abin da ya faru a zirin Gaza kuma za ta samu sakamakon hakon farar-hular Isra’ila da gan-gan.”

Kamfanin dillancin labaran AP ya bayar da rahoton cewar mai magana da yawun Hamas, Fawzi Barhoum, ya yaba wa hare-haren, amma bai ce kungiyar ce ta kai su ba.

An harbe wani dan majalisa har lahira


Hakkin mallakar hoto
Mpumalanga News

‘Yan bindigsa sun harbe wani dan majalisa na jam’iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu har lahira.

Sibusiso Radebe ya rasa ransa ne a wani lamari da ake yi wa kallon aikin ‘yan fashi da makami ne.

An harbe shi ne a ka da kuma kafa bayan da maharan suka bukaci wayar salularsa, kamar yadda wani dan uwansa Lungile Dube ya shaida wa kafar watsa labarai ta Mpumalanga News.

Lamarin ya faru ne a birnin Roodepoort a cibiyar kasuwanci ta kasar da ke Gauteng.

Wani dan jarida da ke yankin ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter kamar haka:

“An harbe dan majalisar ANC Sibusiso Radebe har lahira a Roodepoort”.

Hotunan yadda mota dauke da katako ta rufta kan motoci a Lagos


A ranar Talata da yamma ne wata babbar mota dauke da katako ta mirgino da katako mai tarin yawa daga kan gadar da take tafiya a kai, inda suka fada kan motocin da ke bi ta kasan gadar.

Image caption

Al’amarin ya faru ne a unguwar Ojuelegba da ke birnin Legas na kudu maso yammacin Najeriya.

Image caption

Motoci da dama ne suka lalace sakamakon ruftowar katakon kansu. Ana fargabar cewar mutane da dama sun rasa rayukansu a hatsarin.

Image caption

Wani karan mota ya tsira yayin da direban nasa ya mutu a hatsarin.

Image caption

Kawo yanzu dai ma’aikatan agaji na kai wa wadanda lamarin ya rutsa da su dauki.

Image caption

Ma’aikatan tsaftace birnin na ta kokarin share baraguzan katakon da ya zube a kan hanya.

Image caption

Afkuwar hatsarin ya jawo tsananin cunkoson motoci a yankin. Da ma kuma birnin Legas daya ne daga cikin biranen da aka fi samun cinkoson mutane da ababen hawa a Afirka.

Image caption

Kawo yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba a hatsarin.

Rushewar kofar Mata na haifar da dimuwa a Kano


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A cikin watan Mayun da ya gabata, wata babbar mota ta auka kan ginin tarihi da ake kira Kofar Mata, lamarin da ya sa a yanzu sai kufenta.

A shekarun 1400 ne, Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, ya gina wannan kofa lokacin da ya fadada birnin Kano amma an sake gina kofar cikin 1985, kafin rushewarta a baya-bayan nan.

Al’umma dai a birnin Kano na ci gaba da bayyana jimami kan rushewar wannan kofa, mai dadadden tarihi.

Lokacin da BBC ta tuntubi wasu daga cikin mazauna birnin na Kano, sun ce ba su ji dadin faduwar kofar ba, musamman ganin tasirin da take da shi ga al’adun al’umma, kamar a lokacin hawan sallah, inda sarki kan fita da kuma dawowa ta kofar sa’ilin gudanar da hawan Nassarawa.

Sun kuma ce, rashin kofar na haifar da rudani ga baki wadanda ake wa kwatance da kofar a lokacin da za su shigo birnin na Kano domin harkokin kasuwanci da sauran sabgogi.

Masana sun ce kofar ta zamewa mutanen Kano garkuwa lokacin da Damagarawa suka kawo musu yaki a zamanin sarkin Kano Alu.

Yadda Donald Trump ke raba ‘ya’yan ‘yan ci-rani da iyayensu


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda ‘ya’yan ‘yan ci-ranin Amurka ke kukan an raba su da iyayensu

An saki wasu muryoyin yaran ‘yan ci-ranin Amurka da aka nada suna kuka sakamakon raba su da iyayensu, yayin da Shugaba Donald Trump ke ci gaba da bujirewa sauya dokokin ‘yan ci-rani.

Kusan ‘ya’yan ‘yan ci-rani 2,000 ne aka raba da iyayensu a watannin da suka gabata, bayan da iyayensu su ka yi kokarin shiga Amurka ta kan iyaka ba tare da izini ba.

Mista Trump ya ce ba zai bari Amurka ta zama sansanin “‘yan ci-rani ba.”

Babban jami’in hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ya ce ba za a amince da dokar ba.

Wata kafar watsa labarai mai binciken kwaf a Amurka ProPublica ce ta saki muryoyin a ranar Litinin, kuma an ce an nadi kukan ne a wani sansani na hukumar kwastam da tsaron iyaka ta Amurka.

A ciki, an ji muryoyin yara da dama ‘yan yankin Tsakiyar Amurka da aka raba da iyayensu da ake tsammanin ‘yan tsakanin shekara hudu zuwa goma ne, suna kuka da shessheka tare da kiran sunan iyayensu.

A ciki an ji muryar wani jami’i mai kula da kan iyaka ya na cewa: “Mun samu kayan kida a nan. Abun da babu kawai shi ne wanda zai buga.”

Babban jami’in UNHCR Filippo Grandi, ya shaida wa BBC cewa ba za a amince da dokar Trump ta korar ‘yan ci-rani ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matsayin Donald Trump kan ‘yan ci-rani na haifar da ce-ce-ku-ce a kasar

Ya ce: “Ba daidai ba ne a raba yara da iyayensu a ko wanne irin yanayi musamman a lokacin da mutane ke cikin tsanani kamar gujewa rikici ko cin zarafi, kamar yadda yake faruwa a Tsakiyar Amurka.

“Don haka mu na shawartar gwamnatin Amurka cewa ba wannan ce hanyar da ya kamata ta bi wajen daukar mataki ba,” in ji Musa Grandi.

A ranar Litinin ne Mista Trump ya ce Amurka ba za ta zama sansanin ‘yan ci-rani ba.

“Idan aka kalli abun da ke faruwa a Turai da sauran wurare, ba za mu bar hakan ya faru a Amurka ba. Ba zan bari ba.”

Shugaban dan jam’iyyar Republican ya zargi ‘yan jam’iyyar Democrat da cewa sun ki zuwa teburin sasantawa kan dokar ci-rani.

Mece ce dokar?

Hakkin mallakar hoto
Administration for Children and Families at HHS

Image caption

Hoton farko da aka saki a hukumance da ke nuna birnin da ake kafa tantuna don ajiye ‘ya’yan ‘yan ci rani a Texas

Kusan yara 2,000 aka raba da iyayensu a kan iyaka daga tsakanin tsakiyar watan Afrilu zuwa karshen watan Mayu.

Daga cikin dokar Shugaba Trump din akwai kama da kuma tuhumar wadanda aka kama su na shiga Amurka ba bisa ka’ida ba da laifi, har da masu neman mafaka.

Al’amarin ya jawo an raba yara da iyayensu, da ba su da laifin komai.

A sakamakon haka, an ajiye daruruwan yara a cibiyoyin tsare mutane da dama.

Wasu hotunan sansanonin sun nuna yadda aka kange yara a cikin keji.

A yanzu haka dai babu isasshen wajen da za a ajiye yaran.

Jami’ai sun kuma sanar da shirin gina birnin da za a kafa tantuna da za su iya daukar daruruwan yara a dajin Texas inda yanayin zafin wajen ke kai wa digiri 40 a ma’aunin salshiyas.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jama’a da dama ne ke kokarin shiga Amurka ba bisa ka’ida ba musamman daga yankin Tsakiyar Amurka

Wa ke sukar dokar?

Jam’iyyar Democrat da wasu ‘yan jam’iyyar Republican ta Mista Trump sun yi Allah-wadai da mulkinsa.

Al’amarin ya jawo suka mai tsanani daga matarsa Melania Trump, wacce a karshen makon da ya gabata ma ta ce ta “tsani ganin an raba yara da iyayensu.”

Ita ma tsohuwar ‘yar takarar shugabar kasa ta Democrat Hillary Clinton ta ce abun da Mista Trump ke ikirari cewa raba iyaka na cikin doka, “karya ce tsagwaronta.”

Sai dai da dama daga cikin ‘yan majalisar dokoki na Republican ba su soki Trump kan dokar ba.

Karanta karin wasu labarai kan Mexico


Beraye sun daddatsa makudan kudi a ATM


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu masu gyaran injin ATM da suka je gyara a jihar Assam ta kasar Indiya, sun ga abin mamaki bayan da suka bude injin za su fara aiki.

Masu gyaran dai sunga an daddatsa takardun kudi da yawansu ya kai fiye da dala 17 a cikin injin ATM din bayan da suka bude shi.

Masu gyaran sun ce suna zargin beraye ne suka shiga cikin ATM din ta wata ‘yar karamar huda suka daddatsa kudin.

‘Yan sanda a jihar sun ce berayen sun shiga ta wata karamar kofa ne da aka jona ta da waya a injin.

Rahotanni sun ce injin ATM din ya shafe kwana 12 baya aiki, saboda targardar da ya samu, don haka ne berayen suka samu dama suka shiga ciki suka daddatsa takardun kudin.

An dai ta yada hotunan kudaden da berayen suka daddatsa ta kafafan sada zumunta a kasar, inda mutane ke ta mayar da martani a kan lamarin.

Masu gyaran sun kwashe kudin da berayen suka lalata inda suka ajiye a gefe, sannan suka ware wadanda ba a taba ba suka ajiye su a a gefe guda suma.

Wannan lamari dai ya bawa kowa mamaki, saboda yadda berayen suka shiga cikin injin ATM din, sannan suka lalata makudan kudi.


Karanta wasu karin labaran

An hana jami’an tsaro amfani da shafukan sada zumunta a Kamaru


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Haka kuma an hana jami’an yin amfani da wayoyin hannu na Android

Gwamnatin Kamaru ta haramtawa jami’an tsaro na Jandarma amfani da shafukan sada zumunta irin su WhatsApp da Facebook da Twitter.

Karamin ministan tsaro na kasar wanda ya sanya dokar, ya kuma nemi da jami’an tsaron su soke zaurukan mahawarori da na kulla zumunta da suka bude a dukkanin shafukan sada zumunta.

Haka kuma an hana jami’an yin amfani da wayoyin hannu na Android.

Wannan hukuncin ya biyo bayan abin da kakakin Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya kira bata wa jami’an tsaro suna ba tare da hujja ba.

Kazalika an kuma bukaci daidaikun jami’an tsaron da suka bude shafukan karan-kansu a Facebook da Twitter da WhatsApp da hakan ke tantance su a matsayinsu na jami’an tsaro da su rufe su.

Karamin ministan ya dauki wannan matakin ne domin takaita bayyana wasiku, da kuma wasu tsare-tsare na sirri da Gwamnati take yi daga fadar Shugaban kasa zuwa ma’aikatar tsaro.

Baya ga haka kuma da akwai yunkurin wanke jami’an tsaron ga zarge-zargensu da ake yi na cin zarafi da gallazawa da tauye hakkin fararen hula da suke yi, a tarin faya-fayan bidiyo da jama’a suke yin musaya a tsakaninsu.

Japan ta kafa tarihi a Rasha 2018 bayan doke Colombia


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan ce kwallo ta uku da Yuya Osako ya ci wa Japan

Yuya Osako ne ya ci wa Japan kwallonta ta biyu da ka domin samun nasara kan Colombia, wacce ta kammala wasan na rukunin G da mutum 10.

Shinji Kagawa ne ya fara zuwa kwallo ta bugun fanareti bayan da Carlos Sanchez ya taba kwallo da hannu, abin da ya sa aka ba shi jan kati.

Colombia ta rama kwallon ta hannun Juan Quintero kafin a tafi hutun rabin lokaci, wanda ya ci kwallon daga bugun tazara.

Sai da aka yi amfani da na’urar tantance kwallo kafin a tabbatar da ita.

Sai dai kwallon da Osako ya ci da ka minti 17 kafin a tashi ta raba-gari tsakanin kasashen biyu a filin wasa na Mordovia Arena.

Wannan nasara ta sa Japan ta zamo kasa ta farko daga nahiyar Asiya da ta doke wata kasa daga Latin Amurka a tarihin gasar cin kofin duniya.

Najeriya za ta rufe iyaka saboda shigo da ‘shinkafa mai guba’


Hakkin mallakar hoto
NDUDU BY FAFA

Image caption

Sinadarin Arsenic na jawo cutar sankara

Hukomomi a Najeriya sun ce za su rufe iyakokinsu da wata kasa makwbciya da ba a bayyana sunanta ba nan da kwanaki kadan masu zuwa domin hana shigo da shinkafa daga kasashen waje ta bayan fage.

Ministan ma’aikatar noma na Najeriya Audu Ogbeh, ya ce: “Akwai abubuwa masu guba da ake sakawa a cikin shinkafar” kuma akwai sinadarin “arsenic”, ya kuma yi ikirarin cewa daga China da kuma kudu maso gabashin Asiya ne ake shigowa da shinkafar cikin Afirka.

Ministan ya ce yana da kwarewa sosai kan maudu’in saboda “shi ne manomi na farko da ya sassake shinkafa ba tare da tsakuwa ba.”

Ya kara da cewa: “A nahiyar kudu maso gabashin Asiya inda ake suke shinkafa, idan ka yi shekara hudu zuwa shida kana shuka shinkafa a wuri guda babu kakautawa yawan sinadarin arsenic zai ci gaba da karuwa.

“Sinadarin Arsenic na kawo cutar sankara kuma wannan shi ne abin da suke jibge mana. Wasu mutane sun ce sun fi son shinkafar kasar Thailand saboda tana da tsafta . Amma fa tana da guba!”

Ko da yake hukumomin Najeriya ba su bayyana sunan kasar da ake shigo da shinkafar ta kan iyakarta ba, amma kafofin watsa labarai na cikin gida sun dora alhaki kan Jamhuriyar Benin.

Najeriya na cikin kasashen Afirka da su ke son su kara yawan shinkafar da suke samarwa a cikin gida.

A cikin kasashe 39 masu samar da shinkafa a Afirka, 21 daga cikinsu na shigo da kashi 50 da kashi 99 na shinkafar da suke bukata a cikin gida, a cewar hukumar abinci da aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2017 ne ministan noman ya yi ikikarin cewa Najeriya za ta samar da shinkafar da za ta iya ciyar da kanta, sai dai wasu masana sun bayyana matakin a matsayn “mafarki”.

Arsenal ta amince ta dauki Bernd Leno na Leverkusen


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bernd Leno ya kasance a Bayer Leverkusen tun 2011

Rahotanni sun bayyana cewa Arsenal ta amince ta biya fam miliyan 19 domin sayen golan Bayer Leverkusen kuma dan kasar Jamus Bernd Leno.

Dan wasan mai shekara 26 wanda ya kasance a Leverkusen tun 2011, ba a kai ga gwada lafiyarsa ba tukunna.

Petr Cech da David Ospina su ne masu tsaron gidan Gunners amma kawo yanzu ba a san ko wane ne daga cikinsu zai kauce domin bai wa Leno dama ba.

Arsenal na da kwarin gwiwar cimma yarjejeniya domin daukar dan kwallon Sampdoria mai shekara 22 Lucas Torreira, wanda yanzu haka ke cikin tawagar Uruguay a gasar cin kofin duniya.

Tuni sabon kocin kulub din Unai Emery ya sayi dan wasan baya Stephan Lichtsteiner daga zakarun Italiya Juventus a kyauta bayan da yarjejeniyarsa ta kare.

Zaben 2019: Atiku ya daura damarar doke Buhari


Hakkin mallakar hoto
NurPhoto

Image caption

Atiku ya goyi bayan Buhari a zaben 2015 amma sun babe daga baya

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma mai neman jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da shi takara a zaben 2019, ya fara rangadin wasu jihohin kasar a yankurinsa na doke Shugaba Muhammadu Buhari.

Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Ekiti, inda ya gana da Gwamna Ayo Fayose da sauran jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar a jihar.

Duka Mista Fayose da Atiku sun bayyana aniyyarsu ta neman yi wa PDP takara domin kawar da gwamnatin APC, wacce suka ce ta gaza wurin ciyar da kasar gaba.

Sanarwar da jagoran yakin neman zaben Atiku Abubakar, Gbenga Daniel, ya fitar ta ce tawagar za ta ziyarci birnin Yenagoa na jihar Bayelsa ranar Talata domin ci gaba da rangadin.

Ta kara da cewa Atiku zai sake kai ziyara jihar Rivers, inda zai shafe kwana biyu yana tattaunawa da jami’an gwamnati da na jam’iyya, sannan ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Nyesom Wike ya aiwatar.

A lokacin da yake Ekiti, Atiku ya nemi jama’ar jihar da su goyi bayan dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna da za a yi a ranar 14 ga watan Yuli wato Kolapo Olusola.

“Daga nan kuma tawagar za ta garzaya jihohin Legas da Delta a ranakun 24 da kuma 26 ga watan Yuni,” a cewar sanarwar.

A baya ma dai Atiku ya ziyarci Ekiti da Rivers, da Akwa Ibom da kuma Cross River inda ya gana da gwamnonin jihohin kafin fara azumin watan Ramadan.

A nan gaba kuma ana sa ran zai ziyarci jihohin Abia, Enugu, Ebonyi, Gombe da Taraba.

Masu sharhi na ganin jam’iyyar PDP na da kalubale a gabanta a wurin karbar mulki duk da cewa jam’iyyar APC mai mulki na fama da dimbin matsaloli.


Masu neman takara a PDP

 • Alhaji Atiku Abubakar
 • Ayo Fayose
 • Malam Ibrahim Shekarau
 • Sule Lamido
 • Ahmed Makarfi
 • Ibrahim Hassan Dan Kwambo (bai bayyana ba kawo yanzu)

Najeriya: An tura jirgin yaki mai saukar ungulu Zamfara


Hakkin mallakar hoto
NAF

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta tura jirgin yaki mai saukar ungulu jihar Zamfara ga rundunarta ta 207 Quick Response Group da ke Gusau.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ya aike wa BBC a ranar Talata.

Sanarwar ta ce an tura wannan jirgi ne samfurin EC-135 domin taimakawa wajen yaki da barayin shanu a jihar Zamfara da kewaye.

Jirgin dai zai dinga aiki ne daga wani sansani da aka tanadar masa a Gusau, domin yin aikin da ya kamata.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar sojin saman ta kuma kara samun kwarin gwiwa ta yadda za ta gudanar da ayyukanta a jihar, tare da kai dauki a duk lokacin da ya kamata don samar da tsaro.

Haka kuma an samar da dukkan wasu kayan aiki da rundunar ke bukata a jihar kuma dakarun rundunar na cikin shirin ko-ta-kwana.

Hakkin mallakar hoto
NAF

Majalisar Canada ta amince da amfani da tabar wiwi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Majalisar wakilai a Canada ta jefa kuri’ar amincewa da dokar bai wa mutane daman amfani da tabar wiwi don nishadi.

Daftarin dokar da gwamnatin kasar mai sassauci ra’ayi ta gabatar ya samu kuri’u 205 sama da 82 da suka nuna adawa.

Kudirin dokar amincewa da amfani da tabbar wiwi na cikin alkawarukan gangamin yakin neman zaben Firai minista Justin Trudeau, wanda ya kunshi sarrafawa, sayarwa da shan tabar hankali kwance.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana sayar da tabar wiwi a wadansu kasashe ‘domin magani’

Amincewar majalisar wakilai na kuma nuna cewa daftarin zai tsallake karatun majalisar dattawa, kafin sa hannu shugabar kasa a madadin fada.

A watan Satumba ake sa ran tabbatuwar haka a kasar, da zata kasance ta farko a cikin kungiyar kasashen masu karfin tattalin arziki ta G7 da zata bai wa balagaggu daman shan wiwi cikin nishadi.

A baya dai Mista Trudeau ya fito fili yana cewa ya taba shan tabar wiwi tare da abokansa sau ‘biyar ko sau shida’.

Isra’ila: Tsohon ministanta Gonen Segev dan leken asiri ne


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana tuhumar Gonen Segev da alifukan “taimakawa abokan gaba a lokacin yaki”

Isra’ila na tuhumar wani tsohon ministan kasar da laifin yi ma kasar Iran leken asiri, inji ma’aikatar tsaro ta cikin gida, Shin Bet.

Isra’ila ta ce jami’an leken asiri na Iran sun dauke shi aiki a yayin da yake zaune a Najeriya.

Mutumin mai shekara 62, wanda kuma likita ne, ya taba rike mukamin ministan makamashi a shekarun 1990.

An kama shi ne a kasar Equatorial Guinea lokacin da ya kai wata ziyara a watan Mayu, kuma daga bisani aka maida shi gida Isra’ila.

An taba daure mutumin na tsawon shekara biyar a shekara ta 2005 saboda laifukan fasa-kwaurin magunguna da kuma amfani da fason diflomasiyya na jabu.

An kuma soke lasisinsa na aikin likita, amma bayan da aka sake shi daga kurkuku sai ya koma Najeriya da zama, inda aka kyale shi ya cigaba da aikin likita a shekarar 2007.

Sweden ta fara gasar kofin duniya ta hanyar doke Koriya ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Andreas Granqvist shi ne dan Sweden na farko da zai fara cin bugun fenareti da aka bayar a gasar cin kofin duniya tun lokacin da Henrik Larsson ya ci Najeriya ta bugun fenareti a shekarar 2002

Sweden ta doke Koriya ta kudu a wasanta na farko da ta yi a gasar kofin duniya tun shekara 12 da suka wuce ta kafar keftin dinta, Andreas Granqvist, wanda aka bai wa fenareti ta hanyar bidiyo.

An samu wani dan jinkiri kadan kafin a tabbatar da ketar da Kim Min-woo ya yi wa Viktor Claesson ta hanyar bidiyo, kuma lafiri ya ayyana fenareti, kana Granqvist ya yasar da mai tsaron gida Cho Hyun-woo.

Sweden, wadda ita ma tana saman teburin rukuni na F da maki uku kamar Mexico, ta samu damarmaki masu kyau a Nizhny Novgorod.

Da Marcus Berg ya ci kwallo a tsakiyar wasa kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma Cho ya doke kwalon da ya buga, yayin da Koriya ta Kudu ta kasa auna mai tsaron gidan Sweden ko sau daya.

A wani wasa cike da hayaniya, Cho ya kuma doke wani kwalon da Ola Toivonen bugo da kai.

Koriya ta Kudu a gasar kofin duniyarta ta tara a jere ta kasa katabus kuma damar da ta samu kawai ita ce lokacin da Koo Ja-cheol buga kwallo da kai zuwa gefen raga.

Wannan sakamakon na nufin Mexico, wadda ta yi nasara kan Jamus da ci daya mai ban haushi ranar Lahadi, da kasar Sweden suna da maki uku-uku bayan bayan wasannin farko a rukunin F.

‘Da gaske akwai wariyar launin fata’ – ‘Yar Afrika mai tallan kayan kayan kawa


Olivia Sang ‘yar Afrika ce mai tallan kayan kawa kuma tana kalubantar yadda ake kallon wariyar launin fata cikin al’umma.

Ta ce an yi mata dariya game da kasancewa baka sosai a lokacin da take karama, amma a yanzu ta yi suna ta hanyar tallan kayan kawa, kuma ba za ta sauya launin fatarta da komai ba a duniya.

Jarumi dan ci-rani zai gana da shugaban kasarsa ta asali


Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Dan ci-rani daga Mali

Dan ci-rani dan asalin kasar Mali, wanda ya nuna jarumta wajen ceto wani jaririn da ya makale a saman wani bene a birnin Faris, zai gana da shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta, a ranar Litinin.

Mamadou Gassama, wanda aka yi wa lakani da “mai yanar gizo” domin jarumtakar da ya nuna, ya koma Mali inda aka masa tabar gwarzo kamar yadda wannan sakon Twitter din ya nuna:

Ana sa ran zai koma Faransa domin rattaba hannu kan takardar aiki da hukumar ‘yan kwana-kwana ranar 28 ga watan Yuni.

Mista Gassama, wanda ya kasance bakon haure, ya samu izinin zama dan kasar Faransa tare da aikin dan kwana-kwana bayan ya samu yabo domin hawa bene hudun da ya yi a watan jiya domin ceto wani yaro dan shekara hudu.

Mista Gassama ya ja hankalin duniya ne bayan an yi ta yayata bidiyon ceton ban mamakin da ya yi.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Lokacin da dan ci-ranin ya ceto yaro a wani bene

An samu tashin gobara a kasuwar Azare


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gobarar ta fi shafar bangaren kayayyakin abinci, tufafi da sauran kayayyakin masarufi.

Rahotanni daga garin Azare da ke jihar Bauchi a Najeriya na cewa an samu tashin gobara a babbar kasuwar garin.

Gobarar dai kawo yanzu ta yi sanadiyar hasarar dukiya mai dimbin yawa kamar yadda mazauna garin suka shaida wa BBC.

Wakilin BBC, Ishaq Khalid ya ce har yanzu ba a gano musababin gobarar ba, sai dai ma’aikatan kwana-kwana na kokarin gani yadda za su kashe gobarar da ke ci tun daran jiya Litinin.

Gobarar ta fi shafar bangaren kayayyakin abinci, tufafi da sauran kayayyakin masarufi.

Kuma kawo yanzu babu rahotanni asarar rayuka.

Tashin Gobarar na zuwa ne adai-dai lokacin da al’ummar jihar ke jimamin aukuwar iftila’in ruwan sama mai karfin gaske da ya haifar da asarar dimbim dukiya da gidaje.

Melania Trump ta soki mijinta kan bakin haure


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hotunan yadda ake raba iyaye da kananan yaransu a kan iyakokin Amurka sun janyo wa gwamnatin kasar bakin jini

Matar shugaban Amurka Melania Trump ta fito fili ta soki shirin gwamnatin Amurka na raba iyaye da ‘ya’yansu idan an kama su da laifin shiga kasar ba bisa ka’ida ba.

Melania Trump ta ce “na ki jinin yadda ake raba yara da iyayensu”, kuma ta na son ganin an samar da wata sahihiyar hanya ta tunkarar matsalar.

Kalamanta sun biyo bayan karuwar damuwa da Amurkawa ke nunawa kan yadda shugaba Donald Trump ke aiwatar da shirin nasa mai suna “zero tolerance” wajen yaki da bakin haure.

Laura Bush, matar tsohon shugaban Amurka George W Bush ma ta soki lamirin shirin, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ke cike da keta.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Melania Trump ta yi kira ga ‘yan siyasar kasar da su hada kai domin kawo karshen matsalar

A ‘yan makonnin da suka gabata, an raba iyalai kimanin 2,000 da ‘ya’yansu bayan da gwamnatin kasar ta tashi tsaye wajen yaki da masu tsallaka iyakokin Amurka ta barauniyar hanya.

A kan tsare dukkan balagaggen da aka kama na kokarin shiga kasar ko da yana da dalilin yin haka, kuma zai fuskanci matakin shari’a.

Iyalan gida daya da direba sun mutu a hatsari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Saboda cunkoso da rashin kyawun hanyoyi akan sami aukuwar hadurra masu yawa

A ranar Lahadi wani mutum da iyalansa suka gamu da ajalinsu a wani hadari mai sosa rai.

Mutumin mai suna Kamalu, na tare da matarsa Surayya da ‘ya’yansu biyu ‘yan mata, daya mai shekara biyu daya kuma mai wata takwas.

Sun fito daga Maidile za su unguwa Uku gidan iyayen matar a birnin Kano cikin wata keken a daidaita sahu a lokacin da iftila’in ya auku.

Sun isa daidai gadar Lado da ke Western Bypass sai wata babbar mota trela ta bi ta kan keken da suke ciki.

A sandiyyar hadarin dukkan iyalan gida dayan suka mutu nan take har da direban keken.

Jamus ta sha kashi a hannun Mexico 0-1


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Lozano ne ya ci wa Mexico kwallo a ragar Jamus

Jamus ta fara gasar cin kofin duniya da kafar hagu bayan ta sha kashi a karawarta da Mexico.

Mexico ta samu sa’ar Jamus da ke rike da kofin duniya 0-1.

Ana minti 35 da wasa Lozano ya zura wa Mexico kwallo a ragar Jamus.

Yanzu Mexico da ke rukuni guda da Koriya ta kudu da Sweden da kuma Jamus ta dare teburin rukuninsu na F da maki uku.

A gobe ne Sweden za ta fafata da Koriya ta kudu.

Sakamakon wasan ya nuna akwai kalubale a gaban Jamus musamman idan daya daga cikin Sweden ko Koriya ta kudu ta samu nasara a kan daya.

Wasu na dai na ganin doke Jamus a wasan rukuni na farko kamar Mexico ta tsallake ne zuwa zagaye na gaba.

A ranar 23 ga wata ne Jamus za ta buga wasanta na biyu tsakaninta da Sweden, yayin da Mexico za ta kara da Koriya ta Kudu.

Barar da fanareti ba dadi – Messi


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda Lionel Messi ya barar da fanareti a wasan Argentina da Iceland

Lionel Messi says it “hurts” after his penalty was saved during Argentina’s draw with Iceland.

Lionel Messi ya ce ya ji zafin fanaritin da ya barar wa Argentina a wasansu da Iceland a gasar cin kofin duniya.

Golan Iceland ne Hannes Halldorsson ya kabe fanaretin da Messi ya buga wanda ya haramtawa Argentina samun narasa a kan Iceland.

Iceland ta rike Argentina ne 1-1 a wasan farko da suka buga a rukuninsu na D wanda ya kunshi Croatia da Najeriya.

Croatia ce ke jagorantar rukunin da maki uku bayan ta doke Najeriya 2-0.

Messi ya yi kokarin nuna bajintar Ronaldo wanda ya a wasan farko da ya jagoranci Portugal ya ci kwallo uku shi kadai.

“Da abubuwa sun sauya domin ma ce muka samu,” in ji Messi.

Ya ce ba ya jin dadi idan ya barar da fanareti. “Mun ji zafin rashin samun maki uku domin farawa da nasara yana da matukar amfani, yanzu muna tunanin haduwarmu da Croatia.”

Messi yanzu ya barar da fanareti hudu daga cikin guda bakwai na baya-bayan nan da ya buga wa kulub din sa da kuma kasarsa Argentina.

A ranar Alhamis Argentina za ta hadu da Croatia, yayin da Najeriya kuma za ta fafata da Iceland, karawar da za ta tantance makomar Najeriya a gasar a bana.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Goland Iceland Halldorsson ya haramtawa Messi cin faneri

‘Harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 31 a Borno’


Akalla mutane 31 aka ruwaito sun mutu a harin kunar bakin wake guda biyu da ake kyautata zaton mayakan Boko haram ne suka kai a jihar Borno.

An kai hare-haren ne a garin Damboa a ranar Asabar washegarin Sallah da dare, amma hukumar agajin gaggawa NEMA ta ce akalla mutum 20 suka mutu.

Wasu rahotanni sun ce kimanin mutane 31 suka mutu, yayin da gwammai suka jikkata.

Rahotannin sun ce bayan harin kunar bakin wake, mayakan kuma sun bude wuta ga taron jama’a a Damboa da ke bikin Sallah tare da harba gurneti.

Biyu daga cikin ‘yan kunar bakin waken sun kai harin ne a Shuwari kusa da Abashari, inda suka kashe mutum shida, kamar yadda Kamfanin dillacin labaran AFP ya ambato Babakura Kolo shugaban ‘yan kato da gora a Borno yana cewa.

“Yanzu mutane 31 suka mutu, kuma adadin na iya karuwa saboda wadanda suka ji mummunan rauni suna yanayi na rai-kwakwai-mutu-kwakwai.” in ji shi.

Ya ce mutane da dama sun samu rauni ne daga gurnetin da aka harba a taron jama’a a wajen garin Damboa.

Hukumar NEMA ta ce an tura jirage masu saukar Angula na Majalisar Dinkin Duniya domin kwaso wadanda al’amarin ya shafa zuwa Maiduguri.

Harin ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan kuma na zuwa a yayin babban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai ya yin kira ga ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da su koma gidajensu saboda an tabbatar da tsaro a yankin.

Direban Taxi ya bi ta kan mutane a Moscow


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Motar Taxi din ta buge turakar wutar lantarki kafin ta haye inda mutane ke tafiya da kafa

‘Yan sanda a Moscow na bincikar wani mutum da ya kutsa kan motarsa ta taxi kan hanyar mutane da ke tafiya da kafa, tare da jikkata mutum 8.

Cikin wadanda suka samu raunin hadda magoya bayan kungiyar kwallon kafar kasar Mexico da suka je Rasha saboda wasan cin kofin duniya.

Hotunan bidiyon jami’an tsaro sun nuna yadda direban taxi din ya bar titi ya haye inda mutane ke tafiya da kafa kafin daga bisani ya tsere.

‘Yan sandan sun ce mutumin dan tsakiyar jamhuriyar Kyrgystan ne, kuma da taimakon masu wucewa aka cafke shi.

Matukin motar ya bayyana cewa yana cikin yanayi ne na gajiya bayan shafe sa’o’i 24 yana aiki, dalilin da ya sa ya bai wa motar wuta kenan a kokarin taka birki.

Sai dai wasu rahotanni na cewa za a gabatar da shi a gaban kotu.

Shugaba Donald Trump ‘sakarai ne’ – Xinhua


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shugaba Xi Jinping na China

Kafofin watsa labaran China sun soki shugaban Amurka Donald Trump saboda shawarar da ya yanke ta saka harajin kashi 25 cikin 100 akan kayayyakin da China ke shigarwa Amurka.

Kafofin watsa labarai na karkashin kulawar gwamnati ne, kuma ba kasafai suke raba gari da gwamnatin kasar ba.

Saboda haka babu mamaki da kamfanin dillacin labarai na China, Xinhua ya soki Mista Trump kai tsaye.

A wani sharhi da ta fitar, kamfanin dillancin labaran ya ce, “Shugaba mai basira gina gadoji yake yi, amma sakarai kuwa gina katanga yake yi”.

Ita kuma jaridar Global Times cewa ta yi shugaban na Amurka na lalata tsarin zamantakewa tsakanin kasa da kasa ne domin ya dadadawa masu goyon bayansa na cikin gida, wadanda – a cewar jaridar – suna ganin kamar yana kare muradunsu ne.

Jaridar People’s Daily ma ba ta kyale shugaba Trump ba, domin ta bayyana matakan da ya dauka a matsayin abin kunya. Amma jaridar China Daily ta ce tangal-tangal din da ya ke yi akan muhimman abubuwa na nufin cewa bai san inda ya nufa ba, saboda haka ta shwarci China ta jinkirta mayar da martani.

Saboda matakan na maka wa China harajin kashi 25 cikin dari, hukumomin kasar sun ce nan ba da jimawa ba suma za su saka wa wasu kayayyakin Amurka da take shigarwa China haraji mai yawa.

Afghanistan ta tsawaita tsaigata wuta da Taliban


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Daya daga cikin Mayakan Afghanista lokacin da ya rugumi Jami’in tsaro a Kunduz

Gwamnatin Afghanistan ta bukaci kungiyar Taliban ta bi sahunta wajen tsawaita tsaigata bude wuta tsakanin dakarunsu.

A wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin kasar, Shugaba Ashraf Ghani ya ce babu alfannu ko hujjar ci gaba da yaki.

Ya ce ”tsaigata wutar da muka yi ta zowa duniya da mamaki, kuma mun yi haka ne domin samar da zaman lafiya, babu hujjar cigaba da yaki, mu hada kai wajen kawo karshen matsalolinmu.”

Yarjejeniyar tsaigata wutar da aka cimma domin bukukuwan sallah ta samu karbuwa a kusan fadin Afghanistan.

Sai dai Taliban bata ce uffan ba, wanda a daren yau Lahadi wa’adin tsaigata wutarta ke cika.

Mayakan IS kuma sun yi ikirarin cewa su suka kai harin a gabashin kasar wanda ya yi sanadin rasa rayuka 25.

An hana ‘yan Najeriya shiga filin wasa da kaji


Hakkin mallakar hoto
Universal Images Group

An hana ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar Super Eagles zuwa da kaji cikin filayen wasan kwallon kafa a Rasha.

An ruwaito ministan al’adu da yawo bude ido na Rasha Andrei Ermak na cewa:

“Cibiyar watsa labarai da muka samar na samun tambayoyi da dama: inda wasu ‘yan Najeriya masu goyon bayan kungiyar Super Eagles suka nemi izinin shiga cikin filayen wasanni da kaji masu rai, domin wanna alama ce tasu, kuma su kan je da kaji wajen dukkan wasanninsu. Amma mun sanar da su cewa shiga wurin da kaza mai rai ba abu ne mai yiwuwa ba.”

Amma ya ce ba za ahana ‘yan Najeriya masu kallon wasannin a wajen filayen wasan su tafi can da kajin nasu:

“Babu damuwa, za mu iya sanar da su inda ake sayar da kaji idan suna bukatar su.”

Habasha da Somaliya na son farfado da dangantakarsu


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Firai ministan Habasha Abiy Ahmed

Firai ministan Habasha, Abiy Ahmed na ziyara a birnin Mogadishu na Somaliya, inda zai tattauna da shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo.

Ana kallon wannan ziyarar a matsayin wani matakin sake gina dangantaka tsakanin makwabtan biyu da suka dade suna zaman doya da manja.

Firai minista Abiy Ahmed na kokarin inganta dangantaka da Masar da Eritriya, kuma ya saki fursunonin da ake tsare da su saboda dalilan siyasa domin domin kawo zamna lumana a kasar.

Babban batun da firai minista Abiy Ahmed zai tattauna da shugaban Somaliya a Mogadishu shi ne na tsaro.

Sojojin Habasha na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da kungiyar masu tayar da kayar baya na al Shabab, amma duk da haka kasashen biyu sun dade suna zaman zulumi.

Wannan ne ma dalilin da yasa yawancin ‘yan Somaliya ke kallon sojojin Habashan a matsayin dakarun kasashen waje masu kokarin mamaye kasarsu.

Saboda haka firai minista Abiy zai yi kokarin mika sakon zaman lafiya da hadin kai ga dukkan ‘yan Somaliya, matakin da yake fatan zai bunkasa yanayin da ake ciki a kasarsa.

Ban da karfin ba jami’an tsaro umurni – Gwamnan Zamfara


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar

Latsa hoton da ke sama domin sauraren hirar gwamnan Zamfara da Awwal Janyau

Gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar ya ce mukamin babban jami’in tsaron jiha ga gwamna batu ne da ya kamata majalisar dokokin Najeriya ta diba.

Gwamnan wanda jiharsa ke fama da matsalar tsaro ya shaidawa BBC cewa zai kai kudirin gaban majalisa, “ko dai a cire mukamin ko kuma a kara wa gwamna karfi.”

“Zaloya ce a kira gwamna da mukamin babban jami’in tsaro domin bai iya hukuntawa ko dauka da korar karamin jami’in tsaro” in ji shi.

Ya ce doka ba ta gwamna dama ba, sai dai ya kara da nashi kokari ga wanda gwamnatin Tarayya ke yi.

Zamfara ta shafe shekaru kusan takwas tana fama da matsalar ‘yan fashi da barayin shanu da sace-sacen mutane.

Gwamnan jihar ya ce yana jagorantar wani sabon shiri na tunkarar matsalar tsakanin al’ummar jihar ta hanyar tattaunawa da masarautun gargajiya domin gano bakin zaren.

Daruruwan mutane ne aka kashe a hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara.

Yawaitar kashe-kashen da ake samu kusan a kullum ya tursasawa daruruwan mutanen Zamfara yin kaura zuwa makwabtan jihohi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hotunan Atisayen Super Eagles kafin fafatawa da Croatia


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Super Eagles na Najeriya suna shirin fafatawa da Croatia a wasan rukuninsu na D a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Najeriya za ta yi fatan samun maki uku a wasan farko kafin wasanninta na gaba da Iceland da kuma Argentina a rukunin D.

Ana ganin rukunin D wanda ya kunshi Najeriya da Argentina da Croatia da Iceland ya fi sauran zafi, wanda ake kira rukunin mutuwa.

Lashe wasan farko na da matukar muhimmaci ga Super Eagles, domin kamar zakaran gwajin dafi ne ga sauran wasanninta.

Ga wasu hotunan atisayen Super Eagles na Najeriya kafin fafatawarsu da Croatia:

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Fazlullah: An kashe shugaban Taliban a Afghanistan


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban kungiyar Taliban reshen Pakistan Mullah Faizullah

Rahotanni daga Afghanistan na cewa an kashe shugaban kungiyar Taliban ta Pakistan a wani harin da Amurka ta kai da jirgin sama mai sarrafa kansa.

Ana tuhumar Mullah Faizullah da hannu kan harin da aka kai wa Malala Yusufzai da wasu hare-hare kan manyan mutane a Pakistan.

Kakakin ma’aikatar tsaron Afghanistan ya fada ma BBC cewa an kashe Faizullah ne a yankin Kunar a kusa da iyakar kasar da Pakistan.

Fazlullah yayi kaurin suna, inda har ake masa kirari da sunan Rediyon Mullah, saboda salon wa’azinsa da yake watsawa ta wata tashar rediyo a yankin Swat Valley na Pakistan.

Ya zama Amirun kungiyar Taliban reshen Pakistan a 2013, kuma a karkashin mulkinsa ne kungiyar ta kai wani mummunar hari akan wata makaranta a birnin Peshawar.

Harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 150, yawancinsu yara kanana, kuma tun bayan wannan harin ikon kungiyar yayi ta raguwa.

Dakarun Pakistan sun yi nasarar fatattakar kungiyar, dalilin da yasa sauran ‘ya’yanta suka tsere zuwa makwabciyar kasar Afghanistan ta kan iyakokin kasar, amma sun cigaba da kai hare-hare zuwa cikin Pakistan.

Afirka ta Kudu: An sake kai hari a masallaci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu

Mazauna birnin Cape Town na cikin tashin hankali bayan wani harin da wani ya kai kan masu ibada a wani masallaci.

Harin yayi sanadin mutuwar mutum uku har da shi maharin.

Wannan harin ya auku ne a daidai lokacin da masu ibadah ke shirin gudanar da sallar asuba da misalin karfe 3 na asuba a birnin Cape Town.

Ana ganin maharin ya shiga masallacin ne, inda ya tambayi wasu su nuna masa hanyar zuwa wani wuri, amma kuma babu sanannen ciki sai ya daba ma wasu masallata su biyu hari da wata wuka, kana ya bar wasu mutum uku da raunuka.

Da jami’an tsaro suka isa wurin, sun ce maharin yana da shekara 30 da wani abu, kuma ya ki yarda ya mika makamin da yake rike da shi.

Ya kai ma dan sanda hari, amma ya harbe shi. Wadanda suka gane ma idansu lamarin sun ce wukar babba ce irin wadda aka yi amfani da ita a fim din Rambo ce.

Hukumar da ke kula da al’amuran Musulmai a kasar ta yi tir da harin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce ta kadu kwarai da jin yadda aka kai wannan harin na rashin imani.

Wannan harin dai ya auku ne kasa da wata daya da aka kai wani hari a wani masallacin da ke garin Durban a yankin KwaZulu-Natal.

A wancan harin, wasu mahara uku ne suka kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya, kuma mutum biyu sun sami rauni.

Kofin Duniya: An doke Masar da Morocco


Hakkin mallakar hoto
FIFA

Image caption

An ajiye Salah a benci

Masar da Morocco sun sha kashi a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Rasha.

Uruguay da Iran ne suka doke Masar da Morocco da ke wakiltar Afirka a a Rasha.

Uruguay ta doke Masar ne ci 1-0. Ana dab da hure wasa Jose Gimenez ya jefa kwallo a ragar Masar.

Iran ma ta samu sa’ar Morocco ci 1-0. Dan wasan Morocco Bouhaddouz ne ya ci ragarsu bayan karin lokaci, wanda ya ba Iran nasara.

Masar ta fara wasanta a Rasha ba tare da gwarzon dan wasan kasar ba Mohamed Salah.

Duk da an tabbatar da dan wasan n Liverpool ya murmure amma an ajiye shi a benci har aka kammala wasan.

Yanzu Uruguay da Rasha na da maki uku a rukunin A. Rasha ta doke Saudiyya 5-0 a ranar bude gasar a Moscow.

Iran ma ta samu maki uku a rukunin B.

Bana ban sha azumi ko daya ba – Buhari


Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Rashin lafiyar Buhari ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an kammala azumin Ramadan na bana ba tare da ya sha ko daya ba.

Shugaban ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da al’ummar Abuja da suka kai ma sa ziyarar barka da Sallah a fadarsa karkashin jagorancin ministan birnin Tarayya.

A sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar, shugaban ya ce: “Ban yi azumin bara ba saboda rashin lafiya, amma a bana na samu cikakkiyar damar yin azumin.”

Shugaba Buhari ya shafe watanni yana jinya a Birtaniya a bara, jinyar rashin lafiyar da har ya dawo ba a bayyana ainihin cutar da ke damunsa ba.

Ko a watan Mayun bana, shugaban ya sake komawa Landan domin ganin likitansa bayan ya dawo daga Amurka.

Shugaban wanda ya bayyana aniyar sake neman wa’adin shugabanci na biyu a zaben 2019 ya ce, “ajiye azumi bai wajaba ga musulmin da ke cikin koshin lafiya ba.”

Wannan na nufin shugaban ya samu lafiya daga cutar da ya yi fama da ita wacce a baya ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya inda har wasu suke ganin shugaban ba zai iya shugabancin kasar ba.

A cikin jawabinsa, Buhari ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su yi aiki don gyara kasar daga matsalolin da ta fada a baya.

“Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya. Za mu iya hada kai mu ceto ta gaba daya” in ji shi.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

Hakkin mallakar hoto
@NSAdhama

Image caption

Buhari zai sake tsayawa takara a zaben 2019.

 • 19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
 • 5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
 • 28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
 • 3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a Landan
 • 23 ga watan Yuli – Ya gana da wasu gwamnoni
 • 26 ga watan Yuli – Ya sake ganawa da wasu karin gwamnoni
 • A watan Mayu 2018 Buhari ya sake komawa ganin likita

Ana samun karuwar mata masu shan tabar wiwi


Hakkin mallakar hoto
Image copyrightDIEGO_CERVO

Wani bincike da aka yi a jami’ar York, ya gano cewa ana samun karuwar shan tabar wiwi a tsakanin matan da suka haura shekara 40.

A shekara 10 da ta wuce, yawan matan da ke bayyana damuwarsu a kan ta’ammali da tabar a cibiyoyin lafiya ya rubanya daga 471 zuwa 1008.

Masu bincike sun dora alhakin karuwar da ake samun a kan wadatar kwayar wiwin, inda kuma suke kira da a samar da maganin da zai sa a daina shan tabar wiwin.

To sai dai kuma har yanzu, an fi samun matasa maza da suke ta’ammali da tabat wiwi.

Tabar wiwi dai na da araha da kuma saukin samu, hakan ya bayar da dama ga mutane ke samun ta har ma su yi amfani da ita.

Hakkin mallakar hoto
MARLO74

Mutane da dama dai na ganin cewa tabar wiwi ba ta zama jiki ga masu ta’ammali da ita.

Wasu matan dai na shan tabar wiwin ne a mastayin magani, yayin da wasu kuma suka mayar da ita wata kwaya da idan ba su sha ba ba sa jin dadi.

Karanta wasu karin labaran

Rikici ya barke gabanin zabuka a Turkiyya


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

Wata fastar shugaban Turkiyya a wani ganagamin yakin neman zabe a Istanbul

A kalla mutum uku ne su ka mutu yayin da takwas kuma su ka yi raunuka a wani ba takashi da makamai a garin Suruc da ke kudancin Turkiyya, kusa da iyakar Syria.

Suruc gari ne da ke da rinjayen Kurdawa. Rikicin ya barke ne a lokacin da wani dan majalisa Ibrahim Halil Tildiz dan jam’iyyar AK mai mulki kekamfe din sa na zabukan da za a gudanar kwanan nan.

Kafofin watsa labarai masu goyon bayan gwamnati sun ce wasu Kurdawa masu tsaron shaguna sun kai wa tawagarsa farmaki, amma majiyoyin bangaren adawa sun ce masu tsaron dan majalisar sun bude wuta.

A baya bayan nan ne wani hoton bidiyo ya bayyana, inda a ka nuna Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya na zuga jami’an jam’iyya da su tsorata Kurdawa domin samun kuri’u.

Ina goyon bayan tawagar ‘yan wasan Jamus a Rasha 2018 — John Abraham


Hakkin mallakar hoto
Mid-Day

Shahararren jarumin fina-finan kasar Indiya, John Abraham, ya ce shi fa tawagar ‘yan wasan kasar Jamus ya ke goyon baya a gasar cin kofin duniya ta 2018 da ake a Rasha.

John Abraham, wanda mai sha’awar wasan kwallon kafa ne, ya ce zai iya kashe ko nawa ne wajen nuna goyon bayansa ga kasar Jamus.

Jarumin dai ya kan taba wasan kwallon kafa a kasarsa, saboda gwani ne.

A wasu lokuta, John kan buga wasanni sada zumunta da takwarorinsa jarumai a kasar.

John Abraham dai, ya fito a fitattun fina-finai kamar ,Dhoom da Jism da Race 2 da kuma Dostana.

Karanta wasu karin labaran

An tabbatar da ganin watan Shawwal a Najeriya


Hakkin mallakar hoto
AFP

Mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya bayyyana Jumu’a, 15 ga watan Yuli a matsayin ranar sallah a Najeriya, bayan ganin watan Shawwal.

Wannan shi ya kawo karshen azumin watan Ramadan.

Sarkin musulmin na Najeriya ya ce an ga sabon watan na Shawwal a warare da dama na kasar da suka hada da Sakkwato da Kano da Zaria da Maiduguri da Jos da sauransu.

Hakan na nufin musulmi a Najeriya za su yi bukukuwan Sallah tare da takwarorinsu na Saudiyya da wasu kasashen musulmi da aka sanar da Juma’a a matsayin ranar Sallah.

Tun a ranar Alhamis al’ummar musulmi a jamhuriyyar Nijar suka yi sallah bayan sun riga Najeriya fara daukar azumin Ramadan

Tuni dai gwamnatin Nigeria ta ayyana Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu ga ma’aikatan kasar.

Bukukuwan Sallah sun kunshi zuwa Sallar Idi, da saka sabbin tufafi da kuma ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Hotunan yadda Musulmai ke shirin bikin Sallah a fadin duniya


APC ta zargi Okorocha da bata wa shugabanninta suna


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zargi gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda shi ma dan jam’iyyar ne, da bata wa shugabanninta suna.

Zargin na jam’iyar na cikin wata sanarwar da kakakin jam’iyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.

Jam’iyyar ta shawarci gwamnan ya yi aiki tare da sabbin shugabannin jam’iyyar da aka zaba a jiharsa tare bin hanyar sulhu.

Mista Okorocha dai ya zargi jam’iyyarsa ta APC da kin bin umarnin kotu wajen rantsar da sabon shugaban jam’iyyar na jihar Imo bayan ce-ce-ku-ce da aka yi akan zabensa.

Sai dai kuma jam’iyyar ta ce ba ta samu wani umarnin kotu ba game da taron jam’iyyar da ya samar da sabon shugaban.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sanarwar ta ce: “Cikin ‘yan makwannin nan, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, yana bata wa jam’iyyarmu da shugabanninta suna a ko wace rana.”

Sanarwar ta kara da cewa, kusan babu wata ranar da gwamnan ba zai caccaki shugaban jam’iyyar APC na kasa, Chief John Odigie-Oyegun ba, da sauran shugabannin jam’iyyar kan zaben shugabanni da aka yi a jihar Imo.

“A cikin wata talla da aka wallafa a jaridar Daily Trust, ranar 11 ga watan Yunin 2018 mai taken: ‘A bar gaskiya ta yi magana da kanta’ wadda sanannen makusancin gwamna Okorocha, Ireagwu Obioma, mai kiran kansa sakataren riko na jam’iyyar APC a Imo, an yi ikirarin wasu abubuwan da ba gaskiya ba game da jam’iyyar.”

Sanarwar ta ce jam’iyyar ta gudanar da taronta na jihar duk da cewar ta sami takardar umarnin da ta hana ta yin hakan daga kotu.

Sai dai kuma jam’iyyar ta ce ba haka ba ne, tana mai cewar hukuncin kotun da gwamnan yake yayatawa bai mara wa abun da yake ikirari baya ba.

Zaben shugabannin APC a mazabu da kananan hukumomi da aka gudanar a jihohin da jam’iyyar ke mulki ya bar baya da kura.

Rikicin cikin gida na jam’iyyar ya yi tasiri sosai a zabukan inda a wasu jihohi wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka ware suka gudanar da nasu zaben na daban.

Duk da cewa APC ta ce ta yaba da yadda aka gudanar da zaben na shugabanninta a sassan kasar, amma masharhanta na ganin sabanin da ya biyo baya babban kalubale ne ga jam’iyyar.

Ana ganin idan har jam’iyyar ba ta sasanta tsakanin ‘ya’yanta ba, to wasu daga cikinsu da suke ganin an saba ma su na iya ficewa zuwa wata jam’iyyar adawa.

‘An kashe mutum 31 a Zamfara’


Wasu ‘Yan bindiga sun kashe mutum 31 a hare-haren da suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamafara.

Hare-haren sun shafi kauyuka hudu da ke cikin yankin Kiyawa da Gora a karamar hukumar Birnin Magaji.

Alhaji Ibrahim Birnin Magaji Dan madami ya shaidawa BBC cewa an kai kai hare-haren ne kauyukan Illojiya da Madambaji da Sabon Garin Madambaji da Oho da kuma Dutsen wake.

“Kauyen Dutsen Wake kawai an kashe mutum 18, a kauyen Oho mutum 8, a kauyen Illojiya mutum biyu, a Madambaji mutum biyu, yayin da Sabon garin Madambaji aka kashe mutum daya,” in ji shi.

Sai dai kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara DSP Muhammad Shehu ya shaidawa BBC cewa mutum 10 ne aka kashe a hare haren da aka kai a Dutsen Wake da kuma Oho.

Ya ce rundunar ‘yan sanda ta samu labarin harin amma ko da jami’anta suka isa yankin har maharan sun gudu.

Wannan al’amari na zuwa bayan kisan mutane sama da 50 a cikin mako daya a Zamfara, inda aka kashe mutum 23 a kauyen Zaloka a karamar hukumar Anka da kuma mutum 27 da aka kashe a yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar mulki ta Maradun.

Daruruwan mutane aka kashe a Zamfara a tsawon shekaru shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.

Yawaitar kashe-kashen da ake samu kusan a kullum ya tursasawa daruruwan mutanen Zamfara yin kaura zuwa makwabtan jihohi.

Ko kun san kasashen da mata ke da asusun banki fiye da maza?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Kasashen shidda ne kawai a duniya, inda mata su ka fi maza asusun banki.

Kasashen sun hadar da Ajentina da Jojiya da Indonesiya da Lawos da Mongoliya da kuma Philliphines.

Wani rahoto da Babban bankin duniya ya fitar ya nuna yadda mutane a sama da kasashe 140 ke da damar bude asusun banki ta hanyoyi daban daban.

Sama da mutane miliyan 500 ne ko kuma kashi 69 cikin 100 na manyan mutane ne ke da asusun banki a duniya, wanda adadin ya karu daga kashi 51 cikin 100.

A Indiya misali, kashi 83 cikin 100 na maza na da asusun banki inda kashi 77 cikin 100 na mata kuma ke da asusun banki.

Hakan ya nuna cewa a Indiyar maza ne ke kan gana wajen mallakar asusun banki.

A duka kasashen shidda, in ban da Laos, akwai yi wuwar cewa a na biyan mata ta hanyar aika kudi ta banki a wani tsari na gwamnati.

A Mongolia, kashi 43 cikin 100 na mata sun bayyana cewa ana biyansu kudi ta wannan hanyar fiye da kashi 24 cikin 100 na maza.

Sai dai kuma, matan na daina amfani da asusun da zarar gwamnati ta daina biyansu kudin bisa wasu dalilai.

Me ya sa ba za a dagewa Koriya ta Arewa takunkumi ba?


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Sakataren harkokin wajen Amurka Mr Pompeo tare da takwarorinsa na Koriya ta Kudu da Japan

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce ba za a dagewa Koriya ta Arewa duk wani takunkumi ba, har sai ta soke shirinta na nukiliya kwata-kwata. Mr Pompeo ya yi wannan bayani ne a wajen wani taron manema labarai da aka yi a Seoul tare da takwarorinsa na Koriya ta Kudu da kuma Japan. Sakataren harkokin wajen ya ce Pyongyang a shirye ta ke ta soke shirinta na nukiliyar.

Taron da suka yi yazo ne kwanaki bayan ganawa mai dumbin tarihi da Shugaba Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jung-un suka yi a Singapore. Shugabannin sun sanya hannu a kan wata takarda inda suka yi alkawarin kulla sabuwar dangantaka a tsakaninsu.

Koriya ta Arewa dai ta kara tabbatar da cewa za ta cika alkawurran da ta dauka na soke shirinta na nukiliya kwata-kwata a yankin Koriya. Masu nazari dai sun nuna shakku akan wannan yarjejeniya da aka cimma, inda suka ce akwai lauje cikin nadi wajen yadda Koriya ta Arewar za ta soke shirin nata domin ba ta yi cikakken bayani a kan hanyoyin da zata bi ba wajen sokewar da kuma yadda za a gane ta soke din.

Dama dai tunda farko shugaba Trump ya ce Koriya ta Arewar zata kasance cikin takunkumin, har sai ta soke shirinta na nukiliya. Mr Pompeo dai ya je Koriya ta Kudu ne domin sanar da kawayenta na yankin Koriya yarjejeniyar da aka cimman, da kuma sanarwar ba zata da shugaba Trump ya yi na cewa zai tsayar da duk wani aiki na rundunar hadin gwiwa tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu lamarin da ke matukar ciwa Koriya ta Arewa tuwo a kwarya.

Yau ake bikin sallah a Nijar


A Jamhuriyar Nijar, an kammala azumin watan Ramadan, bayan shaida ganin jaririn watan Shawwal cikin garuruwa da dama a kasar.

Da maraicen ranar Laraba ne al’ummar kasar suka kai azumi na 29, kuma a yau sun wayi gari ranar karamar sallah inda za a fara bukukuwan sallar.

Rahotanni sun ambato fira ministan kasar, Birji Rafini, na bayyana sanarwar ganin watan a ranar Larabar.

Wasu daga cikin al’ummar kasar da BBC ta tattauna da su sun bayyana farin cikinsu a kan kammala azumin lafiya.

Yayin da wasu kuma suka ce, sallar ta zo musu da ba dadi, saboda matsin tattalin arziki, da kuma ranar da aka kwalla a cikin watan azumin.

‘Yan kasar ta Nijar sun ce, da dama daga cikin al’ummar kasar ba su dinka kayan sallah ba, sai dai za su wanke tsoffin kayansu ne su je sallar idi.

Suma wasu teloli a kasar da BBCn ta tattauna da su, sun ce gashi sun an kawo musu dinkuna har ma sun dinka, amma masu su ba suzo sun dauka ba, saboda rashin kudin dinkin da za su biya.

Telolin suka ce, hasali ma, wasu daga cikin wadanda suka kai musu dinkin, kance musu su taimaka su sayar da kayan, za suzo su karbi kudin.

Al’ummar kasar ta Nijar dai sun ce anjima ba a shiga matsi na tattalin arziki ba a kasar, kamar wannan lokaci.

A ranar 16 ga watan Mayun 2018 ne, al’ummar kasar ta Nijar suka fara azumin watan Ramadan, lamarin da ya sha bam-ban da na makwabciyarta wato Najeriya, inda aka fara azumin a washegarin ranar da Nijar din ta fara.

Karin bayani

Batun fara azumi da ajiye shi yana yawan jawo ce-ce-ku-ce a kasashen duniya musamman a Najeriya.

Ramadan dai wata ne da Musulmi suke kauracewa ci da sha da kuma jima’i daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, inda suke matsa kaimi wurin ibada da addu’o’i.

Karanta wasu karin labaran

Abubuwan da ake so Musulmi ya yi kafin sallar Idi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana son a sanya sabbin tufafi a ranar Sallah

Mutumin da ya yi azumin watan Ramadan, an so ya cika azumin da sallar Idi.

Sallar Idi Ibada ce da Allah ya shar’anta a matsayin kammala Ibadah ta Azumin watan Ramadan.

Ba ana yin Sallar Idi ba ne don tunawa da wata ranar haihuwa ko wata nasara da aka samu. Idi Ibadah ce ta yin godiya ga Allah.

BBC ta tattauna da Dakta Bashir Aliyu babban Malamin addinin Islama a Najeriya wanda ya bayyana wasu abubuwa da ake son musulmi ya yi a ranar Sallar Idi kamar haka:

Bayar da zakkar fidda-kai ga mabukata

Zakatur fitr wajiba ce kamar yadda SAW ya farlanta ta. Ta fi falala a fitar da ita kafin a tafi masallacin Idi.

Amma an sawwaka a fitar da ita a daren Idi ko kwana biyu ko uku kafin ranar Idi, wato tun a ranar 27 na watan Ramadan musamman ga kungiyoyi ko wakilai da ke tattara zakkar domin raba wa mabukata.

Fitarwa da wuri zai taimaka zakkar ta isa ga mabukata da wuri kafin lokacinta ya wuce.

Annabi SAW ya ce: “Wanda ya fitar kafin Sallar Idi, to ya samu zakkar fidda kai. Wanda kuma ya fitar bayan idar da Sallar Idi to tana matsayin sadaka ne daga cikin ayyukan sadaka amma bai samu zakkar fidda kai ba.”

Wankan zuwa Idi

Wankan zuwan Idi Sunnah ne. Ana son mutum ya yi wanka a ranar Idi kamar yadda yake wankan zuwa Juma’a.

Cin abinci kafin tafiya masallaci

Cin abinci kafin Idi Sunnah ce. Ana so mutum ya ci abinci kafin zuwa Idi domin koyi da Manzo SAW.

Ba a so mutum ya jinkirta cin abinci domin ka da ya nuna kamar ana azumi, domin rana ce da ba a yin azumi.

Malam ya ce Annabi SAW yana cin dabino kamar uku ko biyar ko bakwai ko tara kafin ya tafi sallar Idi.

Sanya tufafi masu kyau

Wannan al’ada ce da musulunci ya tabbatar da ita. Kuma sunnah ce ga musulmi ya saka tufafi sabo mai kyau.Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi farare.

Idi ranar bayyana farin ciki ne da godiya ga Allah a kan ni’imar da ya yi wa bayinsa da dacewa da yin Azumi da ibadun da aka gudanar da kuma kyautar da ya samu na daren Lailatul Kadri.

Zikiri yayin tafiya zuwa masallacin Idi

Ana son a yi ta yin kabbara a yayin tafiya Idi har idan an zauna a filin Idi zuwa sai liman ya zo.

Mai tafiya idi zai dinga cewa: “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar,” ko kuma ya ce ” Allahu Akbar, Allahu Akbar, Lailaha illahahu Wallahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil Hamd.

Ana kuma cewa: “Allahu Akbar Kabira Walhamdu lillahi kasira, Walhamdulillahi bukratan wa asila.”

Za a daina kabbara idan Liman ya tayar da sallah.

Ba a sallar nafila a filin idi

Sallar Idi ba ta da Nafila domin ita ma Nafila ce. Amma idan a cikin masallaci ne za a yi Idi watakila saboda ruwan sama, to mutum yana iya nafilar gaisuwa ga Masallaci.

Amma a filin Idi ba a nafila. Mutum yana zuwa zai zauna kuma ya ci gaba da kabbara har isowar liman.

Sauraron huduba bayan sallar idi

Ana hudubar Idi bayan sallame Sallah. Ana son a zauna a saurari hudubar Liman, ba a son daga sallame sallah a fice.

Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malam ya ce yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu’ar musulmi da ake yi a cikin huduba.

Sauya hanyar tafiya da dawowa

Wannan Sunnah ce ta Manzo SAW ba a son a tsayar da hanya daya. Ana son mutum ya csauya hanya idan zai dawo daga Idi domin zai yi wa wasu mutane na daban sallama sabanin wadanda ya yi wa sallama a lokacin tafiyarsa.

Yara da mata da tsoffi duka na zuwa sallar idi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana son Mata su je Idi

Ana son dukkan al’umma su tafi idi, maza da mata da yara da tsoffi. Mata masu haila za su iya zuwa amma ba za su shiga sahu ba, za su tsaya a gefen masallaci.

Ana son mata idan za su tafi idi su suturta jikinsu, ka da su tafi Ibadah suna bayyana jiki kuma suna bayyana adonsu. Sannan ba a son mata su jera sahu daya da maza a filin idi. An fi son maza suna gaba mata na baya.

Za a iya hasashen wanda zai lashe gasar kofin duniya a Rasha?


Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Kasashe 32 za su fafata a gasar cin kofin duniya

Kasashe 32 ne za su fafata, amma a karshe kasa daya ce za ta yi nasara.

Amma ta yaya za ka yi hasashen tawagar da za ta dauki kofin duniya a birnin Moscow ranar 15 ga watan Yuli?

Ta hanyar nazari kan salo da alkaluma da kuma tarihi na gasar da aka gudanar a baya, sashen wasanni na BBC ya zubar da kasashe 31 inda ya zabi kasa daya da ya yi hasashen za ta lashe kofin gasar.

Ga abubuwan da suka wajaba kasasashe da suka lashe gasar cin kofin duniya su yi…

Matsayin kasashe

Tun da aka kara yawan kasashen da ke buga gasar kofin duniya zuwa 32 a shekarar 1998, kusan dukkan kasashen da suka ci gasar sun kasance kasashe ne da aka ware.

Bugu da kari kasa ta karshe wadda ta ci gasar ba tare da an ware ta ba ta yi hakan ne a shekarar 1986, a lokacin da Ajantina ta dauki kofin ta hanyar kwallon da Diego Maradona ya ci da hannu.

Ta wannan hanyar mun cire tawagogi 24 daga cikin gasar, lamarin da ya bar mu da tawagogi takwas.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Kasashen Turai za su fi taka rawar gwani – Hasashe

Rashin kasancewa mai masaukin baki

Rasha ta ci arzikin al’adar gasar ta tsawon shekara 44 inda ake ware kasa mai masaukin baki.

Kasancewa kasa ta 66 a cikin jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, ba za ta kasance daya daga cikin kasashe takwas da ke kan gaba idan ba a kasarta ake gasar ba.

Karbar bakuncin gasar kofin duniya ba ya cikin hanyoyin da ake ganin za su kai ga kasa ga nasara kamar yadda tarihi ya nuna.

Gasa sha daya na farko da aka gudanar, daga shekarar 1930 zuwa shekarar 1978, kasashen da suka karbi bakunci gasar biyar ne suka yi nasara.

Tun wancan lokacin, a gasar tara da aka yi a baya sau daya kasar da ke karbar bakunci ta yi nasara – wato gasar da Faransa ta karbi bakunci a shekarar 1998.

Ya kasance abu mai wuya ga Amurka da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Afrika ta Kudu su ci gasar, a gasar Italiya 1990 da Jamus 2006 da kuma kasar Brazil a shekara hudun da suka wuce dukkacinsu karbar bakuncin gasar bai ba su damar lashe gasar ba.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Za a fitar da Rasha a wasan dab da kusa da karshe

Iya tsare gida da kyau

A lokacin da ake buga gasar tsakanin kasashe 32, babu daya daga cikin zakaru biyar na wannan lokacin da aka ci fiye da kwallaye biyar cikin wasanninsu biyar.

Idan aka kwatanta kasashe bakwai da suka rage, Poland ce ta fi samun koma baya a tsaron gida.

Ma’aunin yawan kwallayen da aka ci Jamus da Portugal ya kai 0.4 a ko wane wasa, ma’aunin Belgium da Faransa kuma shi ne 0.6 a ko wane wasa, Brazil kuma 0.61 a ko wane wasa na Ajantina 0.88 a ko wane wasa.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Faransa da Belgium da Jamus da Portugal da Brazil da Argentina za su kai zagayen dab da na kusa da karshe. Hasashe

Kasancewa daga Nahiyar Turai

Masu cin gasar kofin duniya daga nahiyar Turai da kuma kasashen kudancin Amurka suke fitowa.

Sai a baya-bayan nan ne kasashen Turai suka zaburo, amma nasarar Spain a Afrika ta Kudu da kuma Jamus a Brazil ya sauya wannan salon.

Akasari wadanda suke karbar bakunci gasar da ake yi a Turai su suke samun nasara.

A gasa cin kofin duniya 10 da kasashen Turai suka karbi bakunci, gasa daya ce kawai wata kasa daga wajen nahiyar ta Turai ta ci, kuma sai an koma shekarar 1958 inda Brazil ta ci gasar a Sweden.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Faransa da Belgium da Jamus da Portugal za su buga wasan dab da karshe – Hasashe

Sai idan kana da kwararren gola

Za ka iya tunanin cewa masu cin kwallo ne ke cin gasar cin kofin duniya, amma sau biyu ne kawai aka samu wanda ya ci kyautar zura kwallo ta takalmin zinari a tawagar kasar da ta dauki kofin tun shekarar 1982- Ronaldon Brazil a shekarar 2002 da kuma David Villa na Spain a shekarar 2010.

Masu cin kofin duniya sun fi siffantuwa da mai tsaron gidansu, inda ake samu hudu daga cikin wadanda suka ci kyautar gwarzon mai tsaron gida biyar suka kasance ‘yan tawagar da suka dauki kofin.

Daga cikin kasashe hudun nan da suka rage ba zaka yi mamakin idan daya daga cikin su Manuel Neuer (Jamus) da Hugo Lloris (Faransa) ko kuma Thibaut Courtois (Belgium) ya kasance an fitar da sunansa a matsayin gwarzon mai tsaron gida a wannan lokacin.

Abu ne mai wuya a ce mai tsaron gidan Portugal, Rui Patricio, zai ci kyautar gwarzon mai tsaron gida.

Faransa da Belgium da Jamus da Portugal za su buga wasan dab da karshe – Hasashe

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Faransa za ta doke Portugal a matsayin na uku – Hasashe

Kasance kwararre

Kasashen da suke cin gasar kofin duniya suna ci gaba da zama kwararru, wani salon da ya fara a lokacin da aka fadada yawan kasashen da ke shiga gasar zuwa 32 a shekarar 1998.

A wancan lokacin, kasar Faransa da ta dauki kofin ko wane dan wasanta ya taka mata leda kimanin sau 22.77.

A shekaru hudun da suka gabata, ko wane dan wasan Jamus ya yi mata wasa sau 42.21. A tsakiyarsu an samu kari a hankali -taka ledar ko wane dan wasan Brazil ya kai 28.04 a shekarar 2002.

‘Yan italiya sun taka leda 32.91 gasar a shekarar 2006, Spain kuma sau 38.30 a shekarar 2010.

A lokacin da sauran tawagogin ukun suka fitar da sunayen ‘yan wasansu, yawan wasannin da ko wane dan wasan Faransa ya haska ya kai 24.56, yayin da na Jamus ya kai 43.26, na Belgium ya kai 45.13.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Belgium da Jamus za su buga wasan karshe – Hasashe

Kasar da ba ta rike da kofi

Yana da wahala kasar da ta ke rike da kofin duniya ta iya kare kofin.

Wannan ya kasance haka ne tun lokacin da Brazil ta ci gasar sau biyu a jere tsakanin shekarar 1958 da shekarar 1962.

Kuma tun da Brazil ta dauki kofin sau biyu a wancan lokacin, sau biyu ne kawai aka samu mai rike da kofi da ta wuce matakin kusa da dab da na karshe cikin kasashe 13 da suka taba cin kofin.

Ajantina a shekarar 1990 da Brazil a shekarar 1998, duk da cewa Brazil ta zama ta hudu a shekarar 1974 a lokacin da matakin rukuni na gasar ya kasance guda biyu kafin wasan karshe.

A gasar cin kofin duniya hudu da suka gabata, sau uku aka fitar da kasar da ke rike da kofin a matakin rukuni.

Jamus tana da tarihi mai kyau game da kofin duniya a baya bayan nan. A cikin gasa tara da suka wuce – ciki har da ukun da suka yi a matsayin yammacin Jamus- sun ci gasar sau biyu, sun kai ga wasan karshe sau uku kuma sun kasance na uku a gasar sau biyu.

Sai dai kuma, idan ana maganar sake cin kofin ne a Rasha, tarihi ba ya tare da su.

Saboda haka, bayanin ke nan. Belgium za ta ci kofin duniya. Sai idan wani ya ci kofin wanda kuma abu ne mai yiyuwa.

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Belgium za ta lashe kofin duniya a Rasha – Hasashen BBC

Tasiwrar hoto: Katie Moses da Andrew Park na sashen wasanni na BBC

Amurka na son Koriya Ta Arewa ta rabu da makaman nukiliyarta a 2020


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mista Pompeo ya ce, har yanzu akwai sauran babbar yarjejeniyar aiki da ake bukatar cimma da Koriya Ta Arewa”

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce kasarsa na fatan ganin Koriya Ta Arewa ta rabu da makaman nukiliyarta dungurungum a karshen shekarar 2020.

Kalamansa na zuwa ne kwana guda bayan da aka yi wata ganawar da ba a taba yin irin ta ba tsakanin Shugaba Donald Trump da takwaransa Kim Jong-un a Singapore.

Sun cimma gajeriyar yarjejeniya domin “yin aiki don kawo raba yankin Koriya da makaman nukiliya dungurungum.”

Amma ana ta sukar yarjejeniyar da rashin gabatar da kwararan bayanai kan yadda da kuma lokacin da Koriya Ta Arewar za ta rabu da makaman nata.

Da yake magana a Koriya Ta Kudu inda yake tattauna sakamakon taron, Mista Pompeo ya ce, har yanzu akwai sauran babbar yarjejeniyar aiki da ake bukatar cimma da Koriya Ta Arewa.”

Amma ya kara da cewa: “Batun raba Koriyar da makaman dungurungum…. Muna fatan mu cimma wannan nan da shekara biyu da rabi.”

Ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Koriya Ta Arewa ta fahimci bukatar da ake da ita ta gudanar da cikakken bincike na rusa shirin makaman nukiliyar.

Hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Trump ya ayyana cewa a yanzu Koriya Ta Arewa ba barazana ba ce ta bangaren makaman nukiliya, inda ya hakikance cewa “kowa ya saki jiki.”

Sai dai akwai shakku a tabbacin ikirarin nasa, saboda a karkashin yarjejeniyar, Koriya za ta ci gaba da mallakar makaman nata, da rokokin kaddamar da su, kuma ba ta amince da duk wata hanya ta yin watsi da su ba.

Koriya Ta Arewa dai ta yi bikin murnar wannan taro a matsayin wata gagaruwamr nasara ga kasar.

Hakkin mallakar hoto
KCNA

Image caption

Kafar yada labaran Koriya Ta Arewa ta saki wasu hotuna da ke nuna tashar makaman nukiliyarta

Kwastam ta kama manyan motoci makare da shinkafa


Image caption

Bincike ya nuna ana hada baki da direbobin kamfanonin sarrafa barasa domin fasa kwaurin shinkafa ‘yar waje.

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kwastam, da ke kula da shiyyar kudu ma so yammacin kasar ta ce a baya-bayan nan ana kara kama manyan motoci mallakar manyan kamfanonin cikin gida makare da shinkafa ‘yar waje.

Wannan dai ya zo ne bayan da hukumar kwastam din ta kama manyan motocin kamfanonin Dangote da kuma kamfanin da ke sarrafa barasa na Nigerian Breweries makare da shinkafa ‘yar waje da aka shigo da ita daga bakin iyakar kasar ta Jamhuriyar Benin.

Kontirola na kwastom mai kula da shiyyar kudu ma so yammacin kasar ya ce: “Mu na kyautata zato wadannan kamfanoni ba su kafa kamfanoninsu domin yin fasa kwaurin shinkafa ba. Mun kama shinkafa wacce direbobi suka boye.

“Mu na kyautata zato kamfanonin ba su da hannu, sai dai mun gano yadda bara-gurbin dirobobi ke amfani da motocin kamfanonin Dangote da kamfanin sarrafa barasa domin fasa kwaurin shinkafar.”

Image caption

An kama manyan motocin `kamfanonin Naijeriya biyu da fasa kwaurin shinkafa ‘yar waje.

A yanzu haka dai hukumar kwastam da ke a kudu maso yammacin kasar a karkarkashin Kontirola Muhammad Uba Garba na tsare da wasu direbobi, kuma nan gaba za a gurfanar da su a gaban shari’a.

Me kamfanonin ke yi akan wadannan direbobi?

Kamfanonin dai sun sha tsame hannunsu daga abin kunya kamar wannan.

Sa’annan sun sha jan kunnen direbobin cewa kar su kuskura su yi amfani da dukiyar ko motocin kamfanoninsu domin aikata wasu abubuwa da su ka yi hannun riga da fadar dokar kasa.

Kamfanonin sun kuma sha hukunta direbobi da ake kamawa da hada baki da ‘yan fasa kwauri domin shigo da shinkafa Najeriya.

Yanzu haka dai hukumar kwastam ta kama direbobi biyu kuma suna ci gaba da yin karin haske tun bayan haduwa da fushin hukuma.

Gwamnatin tarayya ta haramta shigo da shinkafa ‘yar kasashen waje a wani yunkuri na bunkasa noman shinkafa a cikin gida.

To amma duk da haka ana samun wasu da ke cin gajiyar shigo da shinkafar ta hanyar yin fasa kwaurinta cikin kasuwannin Najeriya.

A wannan shekara kadai an kama shinkafa ta biliyoyin nairori duk kuwa da a cikin gida ana noma ta har ma ana ketarawa da ita domin sayar wa ga kasashen duniya.

A baya dai kafin shigowar gwamnatin Muhammadu Buhari, Najeriya ta dogara da ciyar da al’ummar ta abinci daga shinkafar da aka shigo da ita. Sai dai a yanzu gwamnati ta haramta shigo da shinkafa ta kan tudu, sai dai ta gabar teku.

Amma rahotanni sun nuna akwai yiwuwar kafin karshen shekarar 2019 gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da shinkafar ‘yar waje daga sassan da ke a gabar teku da kuma ta tudu.

Masar ta fi Birtaniya da Amurka zaman lafiya – Bincike


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dakarun tsaron Masar na fafatwa da ‘yan kungiyar IS a yankin Sinai da wasu wuraren

Wani sabon bincike na duniya da aka gudanar ya gano cewa Masar ce kasar da ta fi tsaro da zaman lafiya a Afirka, inda har ta fi Amurka da Birtaniya.

Binciken na shekara-shekara na Gallup Global Law and Order ya tambayi mutane kan ko su na samun tsaro idan su na tafiya da daddare, ko kuma sun taba fuskantar wata barazanar tsaro.

Binciken ya sanya Masar ta zamo ta 16 cikin kasashe 135, yayin da Birtaniya ta zama ta 21 Amurka kuma ta 35.

Singapore ce kasar da ta fi ko wacce zaman lafiya, inda Venezuela kuwa ta kasance ta karshe a kasashen da ke da karancin zaman lafiya a duniya.

Masar ta samu maki 88 cikin 100 na binciken, abun da ya sanya ta a mataki daya da kasashe irin su Denmark da Slovenia da China. An samu ci gaba kan makin da ta samu a 2016 inda ta samu 82.

Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ne ke jagorantar kasar tun 2013 bayan da aka hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi.

Gwamnatinsa ta yi ta fama da masu tsattsauran ra’ayi, wadanda a bara suka kashe fiye da mutum 70 da suka hada da kai hare-haren kunar bakin wake coci-coci a babban birnin kasar Al-Kahira, da kuma biranen Tanta da Alexandria.

Mayakan sa kai masu alaka da kungiyar IS ma sun kaddamar da hare-hare da dama a Yankin Sinai inda suke hakon dakarun Masar da ke aiki a wajen.

Africa Live: For more on this and other stories from around the continent

Binciken Gallup ya ce ya yi hira da mutum 148,000 a kasashe 142 da yankuna a yayin binciken.

Tambayoyin da aka yi sun hada da gamsuwar da mutane ke da ita kan ‘yan sanda da tsaro cikin dare da sata ko cin zarafi cikin wata 12 da suka gabata.

Kashi 46% a Afghanistan da kashi 49% a Uganda da kashi 50% a Sudan Ta Kudu dukkansu sun fi samun zaman lafiya fiye da Venezuela, wacce ita ce kasar da mutanenta suka fi fuskantar matsalar sata a shekarar da ta gabata.


Manyan kasashe biyar da suka fi zaman lafiya a duniya:

 • Singapore
 • Norway
 • Iceland
 • Finland
 • Uzbekistan

Kasashe biyar din da babu isasshen zaman lafiya a duniya:

 • Venezuela
 • Afghanistan
 • Sudan Ta Kudu
 • Gabon
 • Liberiya

An sanya Sudan Ta Kudu a matsayin kasar da ta fi ko wacce rashin zaman lafiya a Afirka.

Kasashen da ke bin bayan Sudan Ta Kudu wajen rashin zaman lafiya a Afirka su ne Gabon da Laberiya da Afirka Ta Kudu, wadda ita ce kasar da masu yawon bude ido suka fi zuwa a nahiyar.

A yankin Kudu da Hamdar Saharar Afirka kuwa, kashi 60% na ‘yan yankin ne kawai suka shaida wa bincinken Gallup cewa sun gamsu da aikin ‘yan sanda, yayin da kashi 68% na mazauna yankin Afirka Ta Kudu da Gabas Ta Tsakiya suka ce sun gamsu da aikin ‘yan sanda.

Rwanda ce kasar da ta fi ko ina a nahiyar idan ana maganar samun tsaro da daddare, inda kashi 88% suka ce ba sa fargabar fita da daddare.

FBI ta kama wasu ‘yan Najeriya da laifin zamba a intanet


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar tsaro ta Amurka, FBI ta ce ta kama wasu mutane fiye da 70 ciki har da ‘yan Najeriya, wadanda ake zargi da zambar miliyoyin daloli ta hanyar intanet.

Hakan ya biyo bayan wani hadin guiwa da FBI din ta yi da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFFC a Najeriya.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, inda tace ta samu karbo kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka kusan miliyan 2.5.

Sannan ta samu katse wasu sakonni na kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 14 da ake shirin turawa.

Ana zargin mutanen da aika wasiku ta hanyar intanet inda suke angulu da kan zabo suka kuma damfari wasu Amurkawa.

Aikata manyan laifuka ta hanyar intanet dai babbar matsala ce a Najeriya, lamarin da ya jima yana bata sunan kasar a kasashen ketare.

Cikin mutanen 74 da hukumar ta FBI ta kama sun hada da ‘yan Najeriya 29 da wasu ‘yan kasashen China da Mauritius da kuma Poland.

Mr. Wilson Owujaren shi ne kakakin hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati ta EFCC ta Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa: “Mun yi aikin hadin guiwa tare da FBI a Lagos tsakanin ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata zuwa ranar 7 da watan Yunin da muke ciki.

“Ba zan ce ga adadin mutanen da abin ya shafa ba. Amma zan iya tabbatar muku da cewa mun damke wasu mutane kuma muna ci gaba da bincikensu.”

Yaya suke wannan lamari?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mista Uwajaren ya kara da cewa: “Damuwarmu ta shafi abin da ake kira wasikun email na kasuwanci. Wata hanyar zamba ce inda masu yin ta ke fakon mutanen da ke tura sakonnin kudi ta hanayar intanet.

“Sai su datse bayanan da ake yi tsakanin mai aika sakon da wanda za a aikawa. Kuma da zarar sun samu bayanka sai su sauya bayanan asusun ajiyar kudadenka daga nan kuma sai su kwashe kudaden.

“Yawanci sun fi zambatar ‘yan kasashen waje, shi yasa ma hukumar FBI ta shiga cikin binciken. Kuma kungiya ce babba wadda ke ayyukanta ba kawai a Najeriya ba har ma da wasu kasashen duniya.”

Hukmar FBI ta ce ta kwashe tsawon wata shida tana bin diddigin ayyukan masu zambar kafin ta kai ga kama mutanen wadanda wasunsu ‘yan Najeriya ne mazauna Amurka.

Tuni dai har an gurfanar da wasu mazauna jihohin Dallas da Texas, inda ake tuhumar wasu daga cikinsu da zambatar wani lauyan kamfanin dillancin gidaje na fiye dala dubu 240, kuma suka halatta kudaden haram da yawansu ya kai sama da 600,000.

Matsalar aikata miyagun laifuka ta hanyar intanet, matsala ce da ke ci gaba da ci wa hukumomi tuwo a kwarya, a yayin da ake samun ci gaba ta fuskar fasaha a duniya.

2026: Canada da Amurka da Mexico sun doke Morocco


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kada kuri’ar ne a birnin Moscow na kasar Rasha

Kasashen Amurka da Canada da Mexico sun yi nasara a bukatar hadin gwiwa ta neman karbar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya a 2026.

Hadin guiwar kasashen ya doke bukatar Morocco da ke neman karbar bakuncin gasar.

Kasashen sun samu rinjayen kuri’u 136 na mambobin hukumar Fifa, fiye da Morocco wadda ta samu kuri’a 65.

Gasar da za a gudanar a 2026 za ta kasance mafi girma da aka taba gudanarwa, inda kasashe 48 za su fafata a wasanni 80 cikin kwanaki 34.

“Kwallon kafa ta hada kan mu” in ji shugaban hukumar kwallon Amurka Carlos Cordeiro.

“Muna godiya sosai a kan wannan karramawar” a cewarsa bayan tabbatar da nasarar bukatar hadin gwiwar Amurka da Canada da Mexico.

Mambobin Fifa 200 ne suka kada kuri’a daga cikin 211 a taron hukumar karo na 68 da aka gudanar a Moscow a ranar Laraba.

Ana bukatar samun kuri’a 104 ga wadanda suka shigar da bukatar neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

An kebe Amurka da Canada da Mexico da Morocco daga cikin mambobin kasashen da suka kada kuri’a.

Ghana ta kauracewa zaman bayan ta dakatar da hukumar kwallon kafarta saboda badakalar rashawa da ta mamaye kwallon kafa a kasar.

Mexico ta taba karbar bakuncin gasar cin kofin duniya sau biyu a 1970 da 1986.

Haka ma an taba gudanar da gasar cin kofin duniya a Amurka a 1994.

Canada ce ba ta taba karbar bakuncin gasar ba, ko da yake ta karbi bakuncin ta mata da aka gudanar a 2015.

Spain ta kori kocinta Julen Lopetegui kwana biyu kafin Rasha


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An nada Lopetegui kocin Spaniya ne a shekarar 2016 kuma bai taba shan kaye ba a lokacin da yake jan ragamar ‘yan wasan kasar

Spain ta kori kocinta Julen Lopetegui bayan sanar da cewar shi ne sabon kocin Real Madrid.

Spain ta kore shi duka kwana biyu kafin wasanta na farko a gasar cin kofin duniya inda za sa kara da kasar Portugal a ranar 15 ga watan Yuni.

A ranar Talata Real Madrid ta bayar da sanarwar cewar Lopetegui ne kocin da zai gaji Zinedine Zidane a Bernabeu.

Hukumar kwallon kafa ta Spain ta ce ta kori Lopetegui mai shekara 51 saboda ya kulla yarjejeniya da Real Madrid ba tare da sanar da ita ba.

Za fara gasar cin kofin duniya ne ranar Alhamis a Rasha.

Kun san me Buhari ya tattauna da gwamnonin APC?


Hakkin mallakar hoto
Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam’iyarsa ta APC a fadarsa da ke Abuja.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha bayan ganawar, ya shaida wa manema labarai cewar sun tattauna batutuwan da suka shafi APC, musamman batun babban taron jam’iyyar da ke tafe.

Sai dai bai yi cikakken bayani game da abin da ganawar ta kunsa ba.

Amma gwamnan na Imo ya kuma ce sun zo ne domin yaba wa Shugaba Buhari kan matakinsa na amincewa da ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimukradiya da kuma karrama Moshood Abiola.

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar a Abuja, a ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da aka soke.

Gwamnonin da suka halarci ganawar sun hada da na Zamfara da Kaduna da Kebbi da Kano da Jigawa da Kogi da Katsina.

Sauran sun hada da gwamnonin Imo da Kwara da Adamawa da Ogun da kuma Benue.

An yi ganawar ne a ranar Talata da dare a dakin taro na uwar gidan shugaban a Villa.

Ana ganin dai ganawar ba ta rasa nasaba da tattauna yadda za a magance rikicin cikin gida da jam’iyyar APC ke fama da shi a wasu jihohi a yayin da zaben 2019 ke karatowa.

Rikicin cikin gida a wasu jihohi da dama na APC ya yi tasiri a zabukan shugabannin jam’iyyar a mataki na kananan hukumomi da mazabu da aka gudanar a kwanakin baya.

Wasu bangarori na APC a jihohin da dama da suka hada da Kano da Adamawa da Bauchi da Zamfara sun gudanar da nasu zaben ne na daban na shugabanin jam’iyyar a kananan hukumomi.

Masharhanta siyasa na ganin rigingimun da jam’iyyar da ta ke fama da su a jihohi na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2019.

Kada a saki jiki wajen shawo kan Ebola a DRC- WHO


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ma’aikatan lafiyar kasar dubu biyu ne a ka yi wa riga kafin cutar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya yi gargadi kan kada a saki jiki bisa barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. Lokacin da ya kai ziyara kasar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, duk da dai akwai alamomin da ke nuna cewa an fara shawo kan annobar, har yanzu ba ta gushe ba.

Cutar ta kashe mutane saba’in da biyu a lardin Equator tun farkon bullarta a watan jiya, amma ba a sake samun wani da ya kamu da cutar ba tun ranar shidda ga watan Yuni.

Ma’aikatan lafiyar kasar dubu biyu ne a ka yi wa riga kafin cutar, wacce kuma gwaje-gwaje su ka nuna alfanunta.

Cutar Ebola dai ta kashe fiye da mutum dubu 11 a yammacin Afrika a shekarar 2014.

Wannan dai shi ne karo na 9 da ake samu bullar Ebola a Congo tun shekara ta 1967.

Me ya sa yara ke yawan fadawa masai a Afirka Ta Kudu?


Hakkin mallakar hoto
Gallo

Image caption

Abokan Micheal da iyalinsa sun halarci jana’izar Micheal Komape

A makonsa na farko a makaranta, Michael Komape mai shekara biyar ya fada cikin masai a arewacin kasar Afirka ta kudu.

Al’amarin ya faru ne a watan Janairu na shekarar 2014 kuma ya kasance ranar da mahaifinsa James Komape ba zai taba mantawa da ita ba.

Ya kai wakiliyar BBC makarantar da ke kauyen Chebeng kuma har yanzu yana cikin wani mawuyacin hali.

“A lokacin da na je bakin shaddar, na hango karamin hannunsa,” in ji shi.

“Wasu mutane sun tsaya suna kallon shaddar, babu wanda ya yi tunanin ciro shi. Na ji takaici sosai game da abin da na gani.

“Ba dai dai ba ne a samu wani da ya rasa ransa ta wannan hanyar.”

Ya yi shuru na wasu dakikoki kafin ya ci gaba.

“Ya rika kokarin ganin cewa an kai masa dauki ko kuma ya kubatar kansa. Har yanzu ina jin wani iri idan na tuna cewa dana ya mutu shi kadai kuma watakila ya rika jin tsoro.”

Image caption

Iyayen Michael Komape za su daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke, wadda ta yi watsi da bukatarsu ta diyya

Mr Komape ya sunkuyar da kansa.

Ya zira ido kan wani jan bulo da aka saka a kan masai.

Bakin masan ya rufta ne lokacin da Micheal ya zauna akai a cewar hukumomi.

Sai dai wannan matsala ce da ake fuskanta a wasu makarantu da ke kasar.

Duk da cewa kowa na da hakkin a samar musu da muhali mai tsafta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, amma dalibai ba su da wani zabi illa su yi amfani da masai.

Makaratun masu masai a kasar Afirka ta kudu

Image caption

Taswirar kasar Afrika ta kudu wadda ta nuna lardunan Limpopo da KwaZulu Natal da Eastern Cape

 • Makaratu fiye da 4,500 ne suke da masai a cikin makarantu 25,000 da ke kasar baki daya
 • Akasarinsu an kafa su ne da wani karfe mai arha sosai kuma babu inganci a kan yadda aka gina su, kuma a bude ake barinsu
 • Matsalar ta fi kamari a lardunan Eastern Cape da KwaZulu-Natal da Limpopo in ji ministar ilimi Angie Motshekga
 • Makaratu 61 ake da su a lardin Eastern Cape kuma babu ba haya a cikinsu kuma makarantu 1,585 kadai ne suke da masai
 • Makwabciyar KwaZulu-Natal na da masai 1,379 da ake amfani da su
 • Lardin Limpopo, inda a nan ne Michael Komape ya rika zuwa makaranta na da wurin baya haya 932 marasa inganci.

Shin ya aka yi lamura suka tababbare?

Wasu masu sharhi sun dora alhakin hakan kan wariyar launin fata, saboda a karkashin mulkin farar fata marasa rinjaye babu wani kason da aka ware domin inganta makarantun da aka kafa domin marasa galihu, wadanda galibi yaran bakar fata ne.

Sun kuma dora alhaki kan gazawar gwamnati wajen kula da makarantun yadda ya kamata.

Hakkin mallakar hoto
Gallo

Image caption

A cikin wannan shaddar ne ta makarantar Mahlodumela Michal Komape ya rasu

A gidansu da ke wajen garin Polokwane, a lardin Limpopo, iyalin Komapes sun shaida wa BBC cewa suna son a yi mu su adalci dangane da mutuwar Michael.

Tare da taimakon wani kamfanin lauyoyi masu kare hakkin bil’dama mai suna Section 27, iyayen Micheal na shirin daukaka kara a kan hukuncin da wata kotu ta yanke, wadda ta yi watsi da bukatarsu ta neman diyya kan abun da ya faru.

Suna tuhumar ma’aikatar ilimi ta lardin Limpopo da sakaci.

Hakkin mallakar hoto
Kirsten Whitefield

Image caption

Kamfanin Section27 na taimakawa iyalin Komapes daukaka kara gaban kotu

“Abin da ya faru da iyalin Komape abin takaici ne kuma ya fito fili ya nuna karara halin da makarantun suke ciki a kasar,” kamar yadda Zukiswa Pikoli jami’a a kamfanin Section27′ ta shaida wa BBC.

“Mun kadu lokacin da muka ji labarin abin da ya faru da Micheal. Babu yadda zamu yi mu ce ba za mu taimaka musu ba.”

Ms Pikoli ta ce kamfaninsu na da niyyar daukaka kara a kotun kundin tsarin mulkin kasar wadda ita ce kotun koli a Afirka Ta Kudu.

Image caption

Wasu dalibai na kusa da wurin da Micheal Komape ya mutu kuma a yanzu suna yi wa junansu rakiya

Sai dai iyalin Komapes ba su kadai ba ne suka rasa yaronsu a cikin wannan yanayi.

A farkon shekarar da mu ke ciki wata yarinya ‘yar shekara biyar ta fada a cikin masai a lardin Eastern Cape.

Lumka Mkhethwa ta bata a makarantar frimare ta Luna a watan Maris da ya gabata.

An sanar da kauyen kuma an shafe daren ranar ana nemanta amma ba a ganta ba.

Bayan kwana daya da faruwar lamarin ne ‘yan sanda suka koma makarantar, inda nan aka yi mata gani na karshe.

Wasu karnuka ne suka yi musu jagora inda ka gano gawarta a cikin masai.

Bayan muturwarta ne sabon shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya nemi a kawar da amfani da masai kafin shekarar da mu ke ciki ta kare.

Sai dai shiri ne da zai bukaci makudan kudi.

Shekaru da ka shafe babu kula’

Rahoton gwamnatin hadin gwiwa ya yi hasashen cewa za a bukaci kudi fiye da rand biliyan 11 kwatankwacin dala miliyan 876, kuma kudin da take son ta tara tare da taimakon kamfanoni masu zaman kansu.

“Mun dauki mataki ne kan shekarun da ake yi ba a kula da makaruntu ba sai dai za a samu sauyi, ko da yake a hankali ne za a kawo sauyin,” in ji Elijah Mhlanga, jami’i a ma’aikatar ilimi.

Hakkin mallakar hoto
Supplied by Komape family

Image caption

Mutuwar Michael Komape ta sa mutanen yankinsa sun farga

“Lamuran nan biyu da suka faru abin takaici ne, amma muna fatan wannan ya nuna wa kowa yadda girman matsalar ta ke,” in ji shi.

“Akwai wasu da suka nuna aniyyar taimaka mana da tallafi.

“Aniyyarmu ita ce mu ga an kiyaye tsaron lafiyar yara a makaruntunmu.”

Malamai masu sintiri

A wani kauye da ke lardin Limpopo, labarin rasuwar Micheal ta sauya yadda ake tafiyar da al’amura a cikin makarantu.

An tsafttace muhalli a makarantar firame ta Sebushi.

A bayan wani wuri mai ciyawa da aka yanka ne aka gina masai masu inganci.

Akwai wurin da aka ware domin malamai su rika sa ido kan daliban da za su yi amfani da su.

“Karfe shida na ko wacce safiya akwai malamin da ke sintiri domin ya ga wanda ya shiga da kuma wanda ya fito,” in ji Joseph Mashishi, ahugaban makarantar.

Image caption

Salgar da aka gina bayan mutuwar Michael

“Ba ma son abin da ya faru da iyalin Komape ya auku a makarantarmu. Ba daidai ba ne yaro ya rasa ransa a cikin masai, babu tausayi a ciki.”

Mutane da dama a kauyen Michael sun farga.

Sun fara fafutukar ganin cewa an samar mu su da sabbin ba-haya a dukkanin makarantun da ke yankin domin tunawa da marigayin.

‘Yar Najeriya ta shiga ajin manyan marubuta a duniya


Fitacciyar marubuciyar nan ‘yar Nijeriya, Chimamanda Ngozi Adichie, ta lashe wata kyautar karrama marubutan da suka yi fice a Burtaniya da kuma kasashe renon Ingila karo na goma.

Ana ba da wannan kyauta mai suna PEN pinter award ce don tunawa da ayyukan wani marubuci Harold Pinter, ga marubutan da suka yi fice wajen fito da gaskiya a zamantakewar duniya.

Chimamanda Adichie, wadda ta rubuta fitaccen littafin nan mai suna Half A Yellow Sun, da Purple Hibiscus, ta ce tana kaunar tsayin dakan Harold Pinter wajen fadar gaskiya, kuma karramawa ce babba a gare ta samun wannan kyauta da sunan marubucin.

Ita ce bakar fata ta farko da ta samu nasarar cin wannan gasa.

Abdul’aziz Ahmed Abdul’aziz, dan jarida kuma marubuci ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, dole ne a taya wanann marubuciya murna saboda ita kanta wannan kyauta ta na da matukar tarihi.

Marubucin ya ce, ko shakka ba bu wannan kyauta za ta karfafi gwiwar marubuta musamman bakar fata a duniya, saboda yadda ta kasance bakar fata ta farko da ta samu wannan kyauta.

Karanta wasu karin labaran

Shugaba Buhari ya nemi afuwa kan Abiola


Hakkin mallakar hoto
Facebook/Nigeria Presidency

Image caption

Shugaba Buhari ya mika wa dan marigayin Kola Abiola lambar GCFR a madadin mahaifinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi afuwar iyalan marigayi Moshood Abiola a madadin gwamnatin kasar bisa soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Yunin 1993.

An dai kyautata zaton cewa Mr Abiola ne ya lashe zaben, wanda gwamnatin Ibrahim Babangida ta soke, tun kafin a kai ga bayyana sakamakonsa.

Ya ce: “A madadin gwamnatin tarayya, ina nema wa kasar nan afuwa daga iyalan marigayi MKO Abiola wanda ya samu kuri’u mafiya yawa da kuma wadanda suka rasa ‘yan uwansu a fafutukar 12 ga watan Yuni”.

Ya kara da cewa ba an shirya taron ba ne domin fama ciwon da lamarin ya haifar ba, sai dai kawai domin kawar da mummmunan tasiri, da bakin cikin da ke tattare da abin da ya faru.

A don haka ya yi kira ga ‘yan kasar da su karbi abin da ya faru na soke zaben da zuciya daya.

Wakilin BBC Ishaq Khalid ya ce wurin ya kaure da tafi a lokacin da shugaban ya bayyana neman afuwar.

Ya kara da cewa wasu da dama daga cikin mahalarta taron sun kadu da kalaman nasa.

Image caption

Har ila yau Farfesa Wole Soyinka da kuma Ministan Ayyuka da Lantarki da kuma Gidaje Babatunde Fashola sun halarci taron

Shugaba Buhari ya mika wa dan marigayin Kola Abiola lambar GCFR a madadin mahaifinsa.

Har ila yau an girmama Babagana Kingibe wanda ya tsaya a matsayin mataimakin Abiola.

Hakazalika an bai wa marigayi Gani Fawehinmi wato wani babban lauya wanda ya yi ta fadi tashi game da ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin.

Hakkin mallakar hoto
Facebook/Nigeria Presidency

Image caption

Baba Gana Kingibe da marigayi Gani Fawehinmi sun samu lambar GCON ne

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da kuma masu fafutukar ganin an girmama wannan rana ciki har da fitaccen marubucin nan Wole Soyinka.

Sai dai babu wani daga cikin tsaffin shugabannin kasar da ya halarta.

Janar Ibrahim Babangida ya aika sakon uzurin rashin lafiya yayin da Olusegun Obasanjo ya ce yana wajen kasar domin halartar wani taro.

Hakazalika shugabannin majalisun dokokin kasar ba su halacci taron ba.

An daure tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 16


Hakkin mallakar hoto
EFCC

Image caption

Joshua Dariye ya mulki jihar Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017

Wata kotu a Najeriya ta daure Tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye shekara 16 a gidan yari bayan ta same shi da laifin cin amana da almubazzaranci.

Mai shari’a Adebukola Banjoko ta samu Mr Dariye, wanda sanata ne da ke wakiltar Filato ta tsakiya, da laifi a kan tuhumce-tuhumce 17 daga cikin 23 da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.

Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017.

Sanata Dariye ya kasance cikin damuwa da dimuwa a lokacin da ake karanta hukuncin, ya nemi lauyan EFCC ya nuna tausayi da afuwa a matsayinsa na mai bin addinin Kirista.

Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da mai Shari’a Banjoko ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.

An yanke masa shekara 14 saboda cin amanar duniyar jama’a, sannan shekara biyu saboda almubazzaranci.

Za a hade hukuncin wuri guda, wanda hakan ke nufin zai yi zaman jarum na shekara 14.

Mr Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke unguwar Gudu.

Mai shari’a Bamijoko ta ce Sanata Dariye ya barnatar da sama da naira biliyan daya da aka bai wa jihar domin shawo kan matsalar zaizayar kasa.

Lauyansa Kanu Agabi ya soki sahihancin shaidun da aka yi amfani da su wurin samunsa da laifi, amma mai shari’ar ta ce shaidun sun tabbatar da almundahanar da aka tuhume shi da aikatawa.

Maitland-Niles ya sabunta yarjejeniyarsa a Arsenal


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ainsley Maitland-Niles yana cikin tawagar Ingila da ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya na U20

Dan wasan Arsenal Ainsley Maitland-Niles ya sanya hannu a sabuwar yarjejeniya da kungiyar.

Maitland-Niles ya fara taka leada a Arsenal ne a shekarar 2014, lokacin ya na da shekara 17, kuma ya buga mata wasanni 28.

Dan wasan, mai shekara 20, ya buga wa kungiyar Ipswich Town wasanni 30 a kakar 2015-16, lokacin da yake zaman aro a kungiyar wadda take wasa a Gasar Championship.

Dan kwallon yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka lashe Gasar Cin Kofin Duniya na ‘yan kasa da shekara 20 (U20) a watan Yunin shekarar 2017.

Karanta wadansu karin labarai

Julen Lopetegui ne sabon kocin Real Madrid


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lopetegui ya zama kocin tawagar kasar Spain a shekarar 2016

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nada Julen Lopetegui a matsayin sabon kocinta.

Kungiyar ta fara neman sabon koci ne tun bayan da Zinedine Zidane ya bar kulob din a watan da ya gabata.

Sabon kocin, mai shekara 51, ya kulla yarjejeniyar shekara uku ne a kungiyar wadda za ta fara aiki bayan kammala Gasar Cin Kofin Duniya.

Lopetegui ne zai jagoranci Spain a gasar.

Lopetegui wanda tsohon kocin kungiyar Porto ne ya taba kasancewa da karamar kungiyar Real Madrid kuma sau daya ya taba yi wa babbar kungiyar wasa.

A karshen watan Mayu ne Zinedine Zidane ya ajiye aikin horar da Real Madrid, kwana biyar bayan ya lashe Kofin Zakarun Turai a karo na uku a jere.

Kotu ta samu Joshua Dariye ta laifin almundahana


Wata babbar kotu a Najeriya ta samu Tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye da laifin almundahana da halatta kudaden haram.

Mai shari’a Adebukola Banjoko ta samu Mr Dariye, wanda sanata ne da ke wakiltar Filato ta tsakiya, da laifi a kan tuhumce-tuhumce 17 da cikin 23 da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.

Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017.

Nan gaba kadan ne za a yanke masa hukunci.

Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da wata kotu ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.

Mr Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke unguwar Gudu.

Mai shari’a Bamijoko ta ce Sanata Dariye ya barnatar da sama da naira biliyan daya da aka bai wa jihar domin shawo kan matsalar zaizayar kasa.

Lauyansa Kanu Agabi ya yi soki sahihancin shaidun da aka yi amfani da su wurin samunsa da laifi, amma mai shari’ar ta ce shaidun sun tabbatar da almundahanar da aka tuhume shi da aikatawa.

Kalli hotunan isar ‘yan wasan Super Eagles kasar Rasha


Kalli hotunan isar ‘yan wasan Super Eagles kasar Rasha – BBC News Hausa

Hakkin mallakar hoto
Super Eagles/Twitter

Image caption

‘Yan wasan Najeriya sun isa kasar Rasha domin fafatawa a gasar cin kofin duniya ta bana

Hakkin mallakar hoto
Super Eagles/Twitter

Image caption

Da tsakar dare ‘yan wasan na Super Eagles suka isa kasar

Hakkin mallakar hoto
Shehu Abdullahi/Twitter

Image caption

Za a fara gasar ne a ranar 14 ga watan Yuni inda mai masaukin baki Rasha za ta bude filin da Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Super Eagles/Twitter

Image caption

A ranar 16 ga wata ne Najeriya za ta fara kece raini da kasar Croatia a rukunin D, wanda ya kunshi Iceland da kuma Argentina

Hakkin mallakar hoto
Super Eagles/Twitter

Image caption

‘Yan wasan sun isa Rasha ne bayan sun kammala atisaye a kasar Austria

Hakkin mallakar hoto
Twitter

Image caption

‘Yan kasar da dama na fatan cewa za su taka rawar gani amma kashin da suka a wasannin sada zumunci na baya-bayan nan ya fara sanyayawa wasu gwiwa.

Musabahar Trump da Kim ta kafa tarihi


Hakkin mallakar hoto
AFP

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jung-un, sun sa hannu a kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa bayan wata tattaunawa da ba a taba yin irinta ba a Singapore.

Mr Trump ya ce, ya na alfahari da abubuwan da su ka cimma a tattaunawar, kuma alakar da ke tsakanin Amurka da yankin Koriya zai sauya idan a ka kwatanta da yadda ya ke a da.

Shugaban na Amurka, ya kuma ce bangarorin biyu sun kulla wata alaka ta musamman.

A nasa bangaren, Mr Kim ya ce tattaunawar za ta kafa tarihi kuma duniya za ta ga babban sauyi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Za a dai a rabawa manema labarai kwafin yarjejejniyar.

Sai da shugabanni biyu suka fara ganawa su biyu in banda masu fassara, kafin daga bisani su gana da manyan ba su shawara da sauran jami’ai.

Karin bayani a kan wannan labari

Amurka dai ta dade ta na dagewa a kan dakatar da da kuma kera makamin nukiliyar da Koriya ta Arewa ke yi.

Kazalika Amurka, ta yi alkawarin tabbacin tsaro da habaka tattalin arzikin Koriya ta Arewar idan ta amince da kwance d’amara.

Masharhanta dai na ganin Shugaba Trump, ya dauko wata babbar kasassab’ar diflomasiyya, inda zai kasance shugaban Amurka na farko da zai gana da takwaransa na Koriyar Arewa.

Karanta wasu karin labaran

Za a kama ‘yan aware da sojojin da suka ci zarafin mutane a Cameroon


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tun a shekarar da ta gabata rashin zaman lafiya ya tsananta a yankin arewacin Kamaru

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin kamaru da ta tabbatar ta kama sojoji da mayakan ‘yan aware da alhakin laifukan da su ka aikata a yankunan rainon Ingilishi na kasar.

Tashin hankali a yankunan rainon Ingilishi a arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar ya yi kamari shekaru biyun da su ka gabata bayan zanga-zanga da mazauna yankunan su ka yi kan nuna bambanci da hukumomi ke yi musu.

Kungiyar Amnesty ta ce ta na da shaidar cewa sojoji sun hallaka kauyuka kuma sun azabtar da wadanda a ka tsare, ta kuma yi zargin ‘yan aware da kashe sojoji da kokarin kai wa malamai da dalibai hari.

Tun a shekarar da ta gabata, rashin zaman lafiya ya tsananta a yankin arewaci, da masu turancin Ingilishi ke da rinjaye a Kamaru, bayan da ‘yan tawaye suka dau doka a hannu su.

Akwai mutane da dama da suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma sun yi gudun hijira.

Wai me Obasanjo ke tsoro da gwamnatin Buhari ne?


Image caption

Dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin Cif Obasanjo da Muhammadu Buhari

Kusan za a iya cewa a yanzu Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na kan gaba a sahun mutanen da ke adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma suke kokarin ganin bayanta. Sai dai wasu na sanya almar tambaya kan ainahin manufar tsohon shugaban.

A ‘yan makonnin da suka wuce ne Obasanjo ya kai ziyara ga shugabannin kungiyar Yarbawa ta Afenifere domin duba yadda “za a sauya gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ya ce tana neman jefa kasar cikin wani hali na tsaka mai wuya”.

Sai dai ganin yadda ziyarar ta zo a lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin tsohon shugaban da kuma gwamnatin APC, wasu na ganin akwai lauje a cikin nadi.

Amma Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya nuna ba shi da abin da za a zarge shi da shi, illa dai ziyarar ta neman ceton kasar ce.

Kalaman da Buhari ya yi na shagube a kan yadda aka kashe makudan kudade kan wutar lantarki a lokacin mulkin Obasanjo “ba tare da an gani a kasa ba” sun sa wasu na hasashen cewa shugaban na da niyyar daukar mataki kan lamarin.

Kwatsam kuma ana cikin haka, sai Obasanjo ya fitar da sanarwa yana zargin cewa gwamnati na shirin amfani da shaidun boge domin kama shi da shafa masa laifi ta karfi da yaji.

Sai dai gwamnatin ta hannun ministan sadarwa Lai Mohammed, ta ce mai kashi a gindi ne kawai zai tsorata, kuma shi mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi.

Tsohon shugaban ya dade yana takun saka da kungiyar ta Afenifere, kuma daga dukkan alamu akwai babban kalubale a gabansa na ganin ya shawo kanta domin cimma manufarsa.

Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa kuma mamba a kngiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida min cewa ba za su saki jiki da Mr Obasanjo ba.

“Duk da cewa muna da matsalolinmu da gwamnatin Buhari, ba mu san manufar Obasanjo ba kuma ba za mu saki jiki da shi ba tukunna,” a cewarsa.

Me Obasanjo ke tsoro?

Wasu majiyoyi kuma sun yi zargin cewa Obasanjo na kamun kafa ne ga kungiyar domin ta mara masa baya idan har Shugaba Buhari ya yanke shawarar bincikar gwamnatinsa kamar yadda wasu kungiyoyi ke kiran da aka yi.

Kuma ba za a iya watsi da masu wannan ra’ayi ba ganin kalaman Obasanjo na baya-bayan nan ka cewa ana shirin kama shi, duk da cewa babu wata hujja mai kwari da ya bayar.

Image caption

Obasanjo na sukar gwamnatin Buhari a kan rashin iya mulki duk da cewa ya goyi bayansa a 2015

Wannan ne ya sa wasu ke zargin cewa Obasanjo na tsoron matakin da Buhari ka iya dauka a kansa ko kuma kan wasu matakai da gwamnatin ta dauka a baya, shi ya sa yake kokarin ganin bayan gwamnatin.

Sai dai shi mutum ne da ya yi kaurin suna wurin juyawa gwamnatoci baya kamar yadda ya yi wa marigayi Umaru ‘Yar’adua da kuma Goodluck Jonathan.

Kuma ya nace cewa yana gwagwarmaya ne domin ganin an ceto kasar, saboda a cewarsa Buhari ya gaza ta fannoni da dama.

Sai dai gwamantin ta ce badakalar da Obasanjo da sauran gwamnatocin PDP suka yi ne suke kokarin gyarawa, kuma kawo yanzu an fara samun ci gaba.

Kawo yanzu dai ‘yan kasar na zuba ido su ga yadda wannan lamari zai kaya.

Ko Obasanjo zai yi nasara wurin ganin karshen gwamnatin Buhari, ko kuma jam’iyyar APC za ta yi galaba wurin karya tasirin tsohon shugaban a siyasance.

Kuma ko abin da Obasanjo ke tsoro zai faru ganin yadda Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa, duk da cewa wasu na ganin binciken Obasanjo kamar wani abu ne da shugaban ba zai so ya yi ba?

Sabanin Obasanjo da Buhari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Obasanjo ya mulki Najeriya a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007

 • Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015
 • A watan Janairun 2018 ne Obasanjo ya bukaci Buhari kada ya nemi wa’adin shugabanci na biyu
 • Obasanjo ya ce Buhari ya gaza inda ya bukaci ya sauka cikin mutunci bayan wa’adinsa na farko
 • A martaninta, gwamnatin Buhari ta ce ba za ta iya muhawara da Obasanjo ba
 • Ministan watsa labaria Lai Mohammed ya ce idon Obasanjo ya rufe ga nasarorin gwamnatin Buhari
 • Buhari da Obasanjo sun hadu a taron Tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Habasha a ranar 28 ga Janairu
 • A watan Afrilu Obasanjo ya jaddada cewa Buhari ya gaza wajen ciyar da Najeriya gaba.
 • Obasanjo ya ce bai kamata a sake zaben Buhari ba saboda gazawarsa.
 • Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa bayan ya caccaki gwamnatin Buhari
 • A ranar 22 ga Mayu Buhari ya soki gwamnatin Obasanjo kan lantarki
 • Buhari ya ce wani tsohon shugaban kasa ya kashe dala biliyan 16, kuma har yanzu ba lantarki
 • Obasanjo ya mayar wa Buhari da martani a ranar 22 ga Mayu
 • Obasanjo ya ce gwamnatin Marigayi Umaru ‘Yar’adu ta kafa kwamitin bincike, kuma kwamitin ya wanke shi.

A wacce kasa fetur ya fi arha da kuma tsada a duniya?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hoton wani gidan man fetur

Tsayawa domin sayen man fetur ba sabon abu ba ne ga mutane. Ko da yake wannan ya danganta ne da kasar da mutum ya ke zaune, a kan haka akwai bambanci game da yawan kudin da za a kashe.

Duk da cewa ana samun fetur da man disel a ko wanne sako-sako na duniya, kuma dukkanin kasashen duniya na sayen man fetur a kasuwanin duniya, amma ko wacce kasa na da farashinta.

Haraji da tallafin da gwamnatin ta ke bayarwa da farashi mai da hauhawar farashin kayayyaki duk suna cikin abubuwan da ke shafar farashin mai.

Idan kasa ce da ke fitar da mai ko kuma shigo da mai shi ma farashin fetur zai bambanta.

A bayanne take cewa kudin da mutum zai biya zai ninka sau 200 a kan lita daya ta mai, ko da yake wannan ya danganta ne a wurin da ka yi siyayya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Farashin mai ya ta’alaka a kan harajin gwamnatin ta sa da kuma tallafin da take bayarwa

Farashin fetur mai rahusa

Venezuela: Ita ce kasar da ake sayar da man fetur da arha a duniya a cewar wani rahoto na cibiyar kayyade farashin mai ta duniya, watau Global Petrol Prices, da aka wallafa a ranar 28 ga watan Mayu 2018.

Cibiyar, wadda ta ke nazari kan alkaluman da ake fitarwa daga kasashe 167 da kuma yankuna ta ce ana sayar da lita daya ta fetur a Venezuela kan dala 0.01, duk da cewa tattalin arzikinta na fuskantar koma baya kuma tana fama da hauhauwar farashin kayayyaki.

Dalilin da yasa mai ba shi da tsada a kasar?

Venezuela ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a kasa duk da cewa tana fuskantar koma baya a tattalin arzikinta, amma har yanzu gwamnati na bayar da tallafi kan akasarin albarkatun man fetur din kasar.

A dayan bangaren kuma akwai kasar Saudiyya wadda ita ce kasa ta biyu mai arzikin mai, amma ita ce ta 14 wajen sayar da fetur da arha a duniya, inda ake sayar da lita daya ta man fetur a kan dala $0.54.

Hakkin mallakar hoto
BBC/Getty

Fetur na da arha a Iran inda ake sayar da lita daya ta man fetur da arha kan dala $0.28 da kuma Sudan in da ake sayar da lita guda a kan $0.34, kuma dukanninsu kasashe ne masu arzikin man fetur.

A kasar Kuwait dala $0.35 ake sayar da lita guda ta mai, yayin da a Algeriya dala $0.36 ake sayar da lita daya na man fetur.

Gwamnatocin wadannan kasashe sun amince a rika sayar wa al’umominsu man fetur a farashi mai rahusa, sai dai wannan ya sa ba sa samun riba sosai.

Sai dai man fetur da suke fitar wa zuwa kasashen waje da suke sayar wa a kasuwannin duniya zai sa su samu gagarumar riba.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Petrol is still cheap in Venezuela

Farashin man fetur ya tashi a cikin watanni 12 da suka gabata – kuma idan lamura suka ci gaba a haka (kamar yadda masana suka yi hasashe), to zai yi wuya wadannan gwamnatoci su cigaba da sayar da man fetur a farashi mai arha ga al’ummominsu.

Kasashen da ake sayar da man fetur da tsada

Iceland: Ita ce kasar da ta fi sayar da man fetur da tsada a duniya inda ake sayar da lita guda ta man kan dala 2.17, a cewar kungiyar kayyade farashin man fetur ta duniya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu ababen hawa na cikin a Iceland sun fi jin jiki a duniya

Yankin Hong Kong na China shi ne na biyu inda ake sayar da lita guda ta man fetur a kan dala 2.14 – watau ta fi ta Venezuela tsada sau 194.

Sai dai kasar da ta ba da mamaki ita ce Norway, wadda ita ce kasa ta uku da ke sayar da man fetur da tsada inda mutane ke sayen lita guda a kan dala 2.05, duk da cewa tana cikin masu arzikin man fetur.

Gwamnatin Norway ta sanya haraji kan man fetur domin ta rage yawan amfani da motoci daga wurin mutane, kuma domin ta karfafa mu su gwiwar amfani da sufurin gwamnati.

Ribar da kasar ta ke samu daga man da ta fitar zuwa kasashen waje tana adana su ne a cikin asusun kauce wa bacin rana, watau Sovereign Wealth Fund, da ake kira Oljefondet, kuma an yi kiyasin cewa shi ne asusu ma fi girma a duniya.

Manufar asusun ita ce tattalin arzikin kasar ba zai dogara a kan man fetur kadai ba, kuma kasar ba za ta shiga cikin matsala ba ko da man fetur dinta ya kare.

Hakkin mallakar hoto
BBC/Getty

Netherlandsna sayar da lita guda ta mai a kan dala 1.97. Sai kuma Monaco da Girka da kuma Denmarkinda ake sayar da lita guda a kan dala 1.92

Sai dai matsalar durkushewar tattalin arziki ce ta sa Girka ta kara farshin mai kamar yadda kasashen duniya masu ba da bashi suka bukace ta karkashin ka’idojin ceto tattalin arzikin kasar da suka cimma.

Israila:Ita ma wata kasa ce da ke sayar da man fetur da tsada sakamakon yawan harajin da ake biya.

Ana sayar da lita guda ta mai kan dala 1.88 kuma ita ce ta tara a cikin jerin kasashen duniya masu sayar da mai da tsada a cewar cibiyar kayyade farashin man fetur ta duniya.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Petrol is still cheap in Venezuela

Is’raila na sayar da man fetur da tsada ne saboda tana shigo da galibin man da ta ke amfani da shi daga ketare, kuma kasashen da ba kawayenta ba ne ke sayar mata da man a cewar majiyoyin gwamanati.

Yadda ake tsara farashin man fetur

Kamfanin mai na Brazil watau Petrobras ya ce idan ya zo kan batun farashi mai, to wannan ya ta’alaka ne a kan wasu abubuwa uku kan farashin da kasashen da suke fitar da mai da kuma wadanda a kai wa man suka kayadde, da yawan harajin da ko wace gwamnati ta amince ta sa, da kuma ribar da mutum ko kamfanin da ya sayar da man zai samu.

Ko wanne bangare na da rawar da ya ke takawa, haraji da kuma tallafin da ko wacce kasa ta ke bayar wa za su sa a samu bambanci a farasahin man fetur a kasashe daban-daban.

Karfin sayan man fetur

Wannan wani abu ne da ya kamata a duba, wato karfin sayen man fetur tsakanin al’umma.

Alal misali watakila an sayar da mai da tsada a Netherlands fiye da Bolivia, sai dai wannan ba wai yana nufin cewa man ya fi karfin ‘yan kasar Netherlands ko kuma’ yan Bolivia suna da karfin sayen man fetur din.

Wannan ya danganta ne a kan kudin da ka ke da shi a hannunka.

Abiola mai tsoron Allah ne kuma bashi da mugunta — Zainab Abiola


Tsohuwar matar marigayi Cif Moshood Abiola, mutumin da ake jin shi ne ya lashe zaben 12 ga watan Yunin 1993 a Najeriya, wato Zainab Duke Abiola ta shaida wa BBC irin halayensa da kuma irin abubuwan sa da ya yi a rayuwarsa wadanda za a iya tunawa da shi.

Zainab Abiola, ta yabi maigidan nata, tare da kuma da nuna farin cikinta da ma na sauran iyalansa a kan ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiyya a Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ne ya ayyana ranar 12 ga watan Yunin a matsayin ranar dimokradiyya, mai makon ranar 29 ga watan Mayu da aka saba gudanar da bikin zagayowar ranar dimokradiyyar.

Ko da yake, gwamnatin kasar ta ce bikin ranar dimokradiyyar zai fara ne daga 12 ga watan Yunin shekarar 2019.

Duk da wasu jihohi a yankin Kudu maso yammacin Najeriyar sun ayyana ranar 12 ga watan Yunin na shekarar 2018, a matsayin ranar hutu, kuma ana sa ran bikin zai zo da wani irin sauyi don kuwa masu rajin tabbatar da ganin 12 ga watan Yuni ta kasance ranar dimokradiyya, za su fita ne don yin bukukuwa maimakon zanga-zanga da kiraye-kirayen da suka saba yi shekara da shekaru.

Patrick Vieira ne sabon kocin kungiyar Nice


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Patrick Vieira yana cikin ‘yan wasan Arsenalk din da suka ci gasa biyu a kaka daya tare da kasancewa daya daga cikin ‘yan wasan da suka yi wasa a gasar 2003-04 ba tare da shan kaye ba

Tsohon dan wasan wanda ya taba yin wasa a kungiyoyin Manchester City da Inter Milan da Juventus yana cikin kakarsa ta uku ne a matsayin kocin kungiyar New York City a kasar Amurka, kafin samun wannan sabon mukamin.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Patrick Vieira ya zama kocin New York City ne a watan Janairun shekarar 2016

Sai dai gabanin nadin nasa, wadansu suna ganin Vieira, mai shekara 41, yana daya daga cikin mutanen da za su iya maye gurbin Arsene Wenger a Arsenal.

“Yanke shawarar barin kungiyar New York City abu ne mai matukar wahala gare ni da kuma iyalina,” in ji Vieira.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Patrick Vieira, kamar Arsene Wenger, ya koma Arsenal ne a shekarar 1996 daga AC Milan. Ya buga wa kungiyar wasannin gasar Firimiya 279

Kungiyar Nice kare kakar Gasar Ligue 1a matsayi na takwas ne, wato maki daya tsakaninta da samun tikitin zuwa Gasar Europa.

Vieira zai maye gurbin kocin kungiyar Lucien Favre wanda aka nada kocin Borussia Dortmund a watan Mayu.

Tsohon dan wasan kasar Faransa, Vieira yana daya daga cikin ‘yan wasan kasar da suka lashe Kofin Duniya a shekarar 1998.

Ana alhinin wani mawakin Najeriya da yamutu


Mawakin reggae Ras Kimono ya mutu a Legas yana mai shekara 60 a duniya.

Wakokinsa kamar galibin wakakokin reggae sun fi karkata ne wajen wayar da kan al`uma a kan `yanci da hakokinsu.

Ibrahim Isa ya tattauna a kan marigayi Ras da gudummuwar da bayar wajen raya wakar reggae da wani shahararren mai gabatar da shiri a kan mawaka a gidan talabajin na Arewa24,Aminu Abba Umar, shirin da aka fi sani da Zafafa-goma!

Umar ya ce Kimono ma ya kasance yana amfani nau’in harshen Ingilishi da aka fi sani da Patois kamar sauran masu irin wannan wakar.

Ya ce ko da yake shi tun shekarun 1989 ya san Kimono, sai dai a shekarun 1993 zuwa 1994 ne wakokinsa suka yi tashe.

Umar ya dan rera wa Ibrahim Isa kadan daga cikin wakar mawakin da ta fi karbuwa.

Latsa alamar lafika domin saurar hirar.

Garba Lawal: yadda ya kamata Super Eagles ta tunkari Rasha 2018


Yayin da ake tunkarar gasar cin kofin dunikya da za a fara a kasar Rasha nan da kwana uku, tshon dan wasan tawagar Super Eagles, Garba Lawal, ya yi tsokaci game da yadda ya kamata ‘yan wasan Najeriyar na yanzu su tunkari gasar.

A wata hirar da ya yi da BBC, Lawal, wanda yake cikin wadanda suka wakilci Najeriya a gasar a shekarar 1998, ya nuna cewa kada ‘yan wasa su damu da tsoron jin ciwo in suna son taka rawara ganai.

Lawal ya ce dabarar wasa a hankali a cikin fili ba zai taimaki dan wasa ba wajen kauce wa rauni domin tsautsayi na iya zuwa ko ta wace hanya.

Tsohon dan wasan Roda JC na kasar Holland din ya ce duk wanda ya je gasar na son ya ci gasar.

Sai dai kuma dan wasan ya ce ko wane dan wasa ya san lokacin da ya kamata ya huta bayan ya dawo daga atisaye domin samun isasshiyar lafiya da hutun da jikinsa ke bukata.

Ku latsa alamar lafikar da ke sama domin jin hirarsa da Awwal Janyau.

Spain za ta ‘karbi ‘yan ci-ranin’ da Italiya ta ki karba


Hakkin mallakar hoto
SOS MEDITERRANEE

Image caption

Kungiyar agaji ta SOS Méditerranée ta wallafa hotunan ‘yan ci-ranin da aka ceto

Firai ministan Spaniya ya ce kasarsa za ta karbi jirgin ruwan da ya ceto ‘yan ci-ranin da suka makale a tekun Mediterranean, domin ganin ba su fada cikin mummunan bala’i ba.

Pedro Sánchez ya ce zai bayar da “matsuguni” ga Aquarius da kuma mutum 629 da ke cikinsa, bayan da Italiya da Malta suka ki su bai wa jirgin izinin shiga kasarsu.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da kuma Tarayyar Turai sun yi kiran da aka kawo karshen takaddamar da kasashe biyun ke yi cikin gaggawa.

Mr Sánchez, wanda ya hau mulki a makon da ya gabata, ya ce jirgin zai sauka a birnin Valencia.

An debo ‘yan ci-ranin ne daga wasu kananan jiragen ruwa a gabar ruwan Libya a karshen mako, a wani aikin ceto guda shida, kamar yadda kungiyar agaji ta Jamus SOS Méditerranée ta bayyana.

“Hakkinmu ne mu ga an kaucewa aukuwar bala’i sannan mu samar da wuri ga wadannan mutane, kamar yadda dokokin kare hakkin bil’adama suka nemi mu yi,” a cewar Mr Sanchez.

Ko a ranar Asabar baki sama da 100 aka ceto daga teku bayan jirgin da ke dauke da su ya samu matsala.

Su wa ye a cikin jirgin?

Wadanda suak tsira sun hada da matasan da ke tafiya su kadai 123, kananan yara 11 da kuma mata masu juna biyu su bakwai, a cewar SOS Méditerranée.

Shekarun matasan sun kama daga 13 zuwa 17 kuma sun fito ne daga Eritrea, Ghana, Najeriya da Sudan, kamar yadda wani dan jarida da ke cikin jirgin, Anelise Borges, ya ce.

Ya shaida wa BBC cewa “Kusan dukkansu sun gaji matuka, sun samu kansu a wani mawuyacin hali saboda sun shafe sa’a 20 zuwa 30 a teku kafin a tserar da su”.

Najeriya ta ceto yara 10 daga masu safarar mutane zuwa Rasha


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An haramta safarar mutane zuwa wasu kasashe a Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun ce sun dakile wasu masu safarar mutane tare da ceto yara 10 wadanda ake son kai wa Moscow da sunan zuwa kallon gasar kofin duniya.

Gwamnatin Najeriyar ta yi gargadin cewar masu laifi suna amfani da gasar cin kofin duniya domin samun takardar shiga ga yara kanana wadanda masu safarar mutane za su yi amfani da su ta hnayar da bai dace ba.

Yara mata tara da kuma yaro namiji daya suna dab da shiga jirgin sama na kamfanin jiragen sama na Turkiyya ne daga Legas zuwa Moscow, a lokacin da jami’an hukumar da ke yaki da fataucin mutane (NAPTIP) su ka ceto su.

An kama mutum biyar da ake zargi, ciki har da dan sanda daya da kuma wani jami’in wajen fitar da yaran.

An bai wa yaran fasfo da kuma takardar shaida na masu goyon bayan ‘yan kwallo a filin jirgin, domin a dauke su tamkar masoya kwallon kafa ne masu son tafiya Rasha kallon gasar kwallon kafar ta duniya.

Mai yiwuwa ne bayan sun kai isa kasar, za a kai su wasu kasashen daban inda masu safarar mutanen ke da abokai wadanda za su tilasta musu yin aiki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Trump da Kim na dab da kafa tarihi a Singapore


Hakkin mallakar hoto
Reuters/Getty Images

Image caption

Shugabannin sun isa Singapore, kuma tsakaninsu awoyi kadan ne

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya isa Singapore domin halartar taron koli tsakaninsa da Shugaba Trump na Amurka.

Shugabanni biyu za su tattauna kan batun makaman nukiliyar Koriya ta Arewa, da samar da dauwamammen zaman lafiya a yankin Koriya.

Shi ma shugaba Trump ya isa Singapore daga baya, kuma shugabannin biyu na son kafa tarihi a lokacin da suka hadu a karon farko ranar Talata,

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya isa Singapore a wani jirgin saman China, inda ministan harkokin waje na Singapore ya tarbe shi, kafin ya gana da Firayiministan kasar.

Wannan babbar dama ce ga shugaban na Koriya ta Arewa, domin yana da yekinin sauyawa daga yadda duniya ke kallonsa a matsayin mai mulkin kama karya da kuma mai son tada rikici.

Yana son ya zama mai fada aji a siyasar duniya da diflomasiyya.

Hakkin mallakar hoto
Singapore/MOCI

Image caption

Kim Jong-un ya riga Donald Trump zuwa, kuma ya isa can ne a wani jirgin kasar Sin

Yana kuma fatan wannan ne lokacin da kasarsa za ta sami karbuwa a cikin kasashen duniya.

Babban batun da za a tattauna a kai shi ne na mallakar makan nukiliyar kasar – ko zai yarda ya mika su domin a dage ma kasarsa jerin takunkuman karya tattalin arziki.

Shi ma shugaba Trump na Amurka na fatan wannan taron zai ba shi damar cimma yarjejeniyar da za ta ama irinta ta farko a duniya.

Amma duk da haka, Mista Trump yayi kasa-kasa da fatan da yake yi na cimma wata kwakkwarar yarjejeniya a haduwarsu ta farko.

Bakin-haure dubu 6 sun makale a kan teku


Hakkin mallakar hoto
SOS MEDITERRANEE

Image caption

Bakin-hauren na cikin bukatar ceton gaggawa

Kasar Malta ta hana jirgin ceto da ke dauke da bakin-haure sama da dubu 6 izinin sauke su a tashar ruwa ta Maltese.

Matakin da ke zuwa bayan, sabon ministan cikin gida Italiya, Mattaeo Salvini–wanda ke jagoranci jam’iyyar League ta masu ra’ayin rikau–ya bukaci Malta ta karbi jirgin bakin bayan haramta musu tsayawa a Italiya.

A wata sanarwa, mahukuntan birnin Maltese na Valetta sun ce babu wata doka da ta bukaci lallai sai sun karbi jirgin–saboda an gudanar da aikin ceton ne a mashigin ruwa da ke karkashin ikon Italiya.

Kakakin gwamnatin kasar, kurt Farrujia ya ce lokacin da aka gudanar da aikin ceton da jirgin wata kungiyar agaji SOS a mediterranean, ‘The Aquarius’ ba a yankinsu ba ne, kuma babu wani aikin kwarewa ko hadin-gwiwa a ciki don haka babu ruwan kasar.

Ko a ranar Asabar Baki sama da 100 aka ceto daga teku bayan jirgin da ke dauke dasu ya samu matsala.

Yanzu dai jirgin da ke dauke da bakin na makale tsakanin Malta da Sicily.

Zamfara: Mutane na yin kaura saboda ‘yan bindiga


Daruruwan mutane na yin kaura zuwa makwabtan jihohi kamar Katsina sakamakon karuwar ayyukan ‘yan bindiga.

Banda ‘yan bindiga akwai kuma matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa.

Al’amarin, a cewar wasu mazauna garuruwan jihar ya kai har da rana tsaka ‘yan bindiga na iya zuwa su sungumi mutum zuwa daji har sai an biya kudin fansa.

Wani mazaunin karamar hukumar Shinkafi, Sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya shaida wa BBC cewa matsalar ta na neman fin karfinsu.

“Tura ta kai bango, matsala ta taso mana, wanda tun ana yi kauyuka har an kai yau sai a shiga Shinkafi da bindigogi, da manyan makamai a dauki mutum a tafi da shi.”

Sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya kuma koka da cewa, “Mutane na kallo ba abin da za su iya yi saboda da manyan makamai suke zuwa.”

Rahotanni sun ce da misalin karfe daya da rabi na dare mahara suka shiga garin na Shinkafi suna harbe-harbe.

“Sun dauki wani dan uwanmu da karfin tsiya tare da sakataren karamar hukumar Shinkafi, kuma sun tafi da su daji. Sun kuma sake daukar wani kaninmu.”

Najeriya da Ghana ne inda aka fi zub da ciki a duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Yadda ake bincike game da kwayoyin zubar da ciki a Google ya nunka a shekaru 10 da suka gabata, kamar yadda wani binciken da BBC ta gudanar ya nuna.

Sakamakon binciken kuma ya gano cewa an fi yin binciken kwayoyin a intanet a kasashen da aka haramta zubar da cikin.

Mata sun koma bin hanyoyi na fasaha domin zubar da ciki ta hanyar sayen kwayoyin a intanet da yada bayanan likita ta kafar Whatsapp.

Yanzu wannan ake kira hanyar zubar da ciki ta zamani.

Kasashen da aka tsaurara dokoki, inda sai don a ceto rayuwar mace ake zubar da ciki ko kuma inda aka haramta baki daya, an fi binciken kwayoyin zubar da cikin a intanet fiye da kasashen da babu wata doka.

Hanyoyi biyu ne ake a bi wajen zubar da ciki: Tiyata da magani.

Zubar da ciki ta hanyar shan magani ya shafi shan nau’o’in magungunan Misoprostol da Mifeprostone, wadanda idan an sha zai sa ciki ya zube.

Kamar a Birtaniya, likitoci ne ke rubuta magungunan, yayin da kuma matan da ke bincike a intanet a kasashen da aka takaita zubar da ciki, suke keta doka, inda za su iya fuskantar hukunci.

Ghana da Najeriya ne kasashe biyu da aka fi binciken kwayar Misoprostol, kamar yadda alkaluman Google suka nuna.

A Ghana ana bayar da damar zubar da ciki ne idan an yi wa wata fyade ko kuma don kokarin ceto rayuwar wata.

Haka ma a Najeriya, dokar kasar ta bayar da damar zubar da ciki ne kawai idan an ga rayuwar mace na cikin hatsari.

Daga cikin kasashe 25 da aka fi binciken maganin zubar da ciki na Misoprostol, kasashe 11 daga Afirka ne yayin da 14 kuma daga Latin Amurka.

Dukkanin kasashen sun haramta zubar da ciki ko kuma sun yarda ne kawai a zubar da ciki a lokacin da rayuwar mace ke cikin hatsari.

Zambiya da Mozambique ne kawai daga cikin kasashen da ba su haramta zubar da ciki ba.

A Ireland, hukuncin shekaru 14 a gidan yari ake yanke wa duk wadda ta zubar da ciki ta hanyar shan kwayoyi, ko da yake sakamakon kuri’ar raba gardama da aka gudanar a watan Mayu ya nuna ‘yan kasar na son a soke dokar.

Alkaluman Google ba wai kawai sun nuna kasashen da aka fi binciken magungunan zubar da ciki ba. Sun kuma nuna kalmomin da ake yawan amfani da su a kan maudu’i daya.

“Kwayoyin zubar da ciki” ne aka fi amfani da su wajen bincike a mafi yawancin kasashen da BBC ta gudanar da bincike akai.

“Yadda za a zubar da ciki” wannan ce tambayar da aka fi yawan tambaya a kasashen.

“Yadda za a yi amfani da Misoprostol, Farashin Misoprostol, sayen Misoprostol da yadda za a sha Misoprostol, su ne kalmomin da aka fi amfani da su a wajen binciken batun zubar da ciki.

Ana kuma yawan binciken magungunan gargajiya na zubar da ciki a intanet.

A yayin da kuma ake binciken kwayoyin zubar da ciki, mata kuma na amfani da Google domin binciken hanyoyin da mutum zai bi da kansa don zubar da ciki.

“Yadda za a zubar da ciki a gida” ne aka fi bincike a Google.

Wani bincike wanda ya yi nazari game da yadda ake yawan amfani da itatuwan gargajiya domin zubar da ciki ya gano cewa wasunsu na yin lahani ga mahaifa.

Yadda babu cikakkun bayanai da suka shafi kare lafiya, binciken ya nuna cewa abu ne mai wahala a iya kiyaye adadin maganin da ya kamata a sha da kuma illolinsa.

Babu daya daga cikin hanyoyin zubar da ciki na gida a jerin hanyoyin zubar da cikin da suka dace na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yana da wahala matan su tafi asibiti a duba lafiyarsu idan har sun zubar da ciki a hanyar da ba ta dace ba

A duniya, ana zubar da ciki sau miliyan 25 a hanyoyin da ba su dace ba duk shekara, a cewar WHO.

Duk da cewa amfani da Misoprostol ana daukarsa hanyar zubar da ciki da ta dace idan kwararre ne ya bayar da umurnin amfani da maganin, amma akwai barazana idan ba a bi tsarin da ya kamata ba.

“Ko da a ce maganin yana da kyau kuma an bi umurnin likita, ana iya samun matsala,” in ji Dhammika Perera, darakta a Marie Stopes International.

Idan mace ta sayi maganin a intanet, ko kuma daga likitan da ba kwararre ba, yana kara damar zubar da ciki a hanyar da ba ta dace ba, in ji shi.

Yana da wahala wadannan matan su tafi asibiti a duba lafiyarsu idan har sun zubar da ciki a hanyar da ba ta dace ba.

Kunya da tsada da rashin wadatuwar wuraren shan magani ne matsalolin da matan ke fuskanta, a cewar Mista Perera.

A kwanan nan BBC ta saurari labarin Arezoo, dalibar nazarin ilimin shari’a da ke Iran, lokacin da ta gano tana dauke da juna biyu na saurayinta da suke rayuwa shekaru biyar.

Sun dade suna amfani da kwayoyin hana daukar ciki.

“Duk wani ofishi na likitan mata da na gani sai na shiga” in ji ta.

“Duk lokacin da likitoci suka duba ni kuma suka fahimci cewa ba ni da aure zan zubar da ciki, nan take suke watsi da ni.”

Ta yi takardun karya cewa ita bazawara ce domin samun amincewar likita ya taimake ta.

Arezoo ta shiga intanet inda ta ci karo da wata kungiya da ke bayar da maganin zubar da ciki ga mata a kasashen da aka haramta zubar da ciki. A nan ne ta samu taimako da shawarwari.

Maganin da ta karba daga hannun likita ya sa ta yi ta zubar da jini, lamarin da ya sa aka ruga da ita zuwa wani asibiti mai zaman kansa tare da rakiyar ‘yar uwarta.

“Na yi ma su karya cewa mijina yana Faransa kuma na manta inda na ajiye takardu a wani wuri kuma ina son na zubar da ciki ta hanyar da ta dace.”

Jami’an asibitin dai ba su gamsu ba kuma sun ki ba ta gado.

Arezoo ta ce kamar wani abin al’ajabi, daga baya sun amince da ita.

“Duk da labarin karyar da na shirya, an kwantar da ni a asibiti, kuma cikin minti 30 aka kammala aikin. Wannan shi ne lokaci mafi muni a rayuwata,” a cewarta.

Kusan kashi 14 na zubar da cikin da ake yi, ana bin matakan da ba su dace ba, wanda ke nufin ana bin matakai ne masu hatsarin gaske.

Wasu matsaloli na cututtuka kan biyo baya da kuma matsalar zubar da cikin da ba a kammala ba a irin wannan tsarin.

Idan har ba a yi sa’ar zubar da ciki da kyau ba, kwararren likita kan bayar da shawarwari na wasu magunguna ko kuma tiyata, ya dai danganta da yanayin matsalar.

A kalla mata 22,800 ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin sa’ar zubar da ciki da kyau, kamar cibiyar Guttmacher ta ruwaito.

Wadanda suka tsara rahoton: Amelia Butterly da Clara Guibourg da Dina Demrdas da, Nathalia Passarinho da kuma Ferenak Amidi.

Mene ne shirin mata 100?

A ko wacce shekara shirin BBC na mata 100 yana fitar da mata 100 wadanda suka yi fice ta hanyar tasiri da kwarjini a sassan duniya.

A shekarar 2017, mun kalubalance su da su warware matsaloli hudu da suka fi addabar mata a yau a sassan duniya – matsalar da ke hana ci gaban mata da rashin karatun mata da muzguna wa mata a wuraren taron jama’a da kuma nuna wa mata bambanci a harkar wasanni.

Da taimakonku, za su samar da hanyoyin magance matsalolin, kuma muna son ku ba da naku hanyoyin magance matsallolin ta shafukan Facebook da Instagram da kuma Twitter. Ku yi amfani da maudu’in #100Women.