Hukumomin Kamaru sun kama wasu sojoji kan zargin kisan mata da yara


Image caption

An ta watsa wanna bidiyon a kafofin sada zumunta ana nuwa wasu da kayan sojoji suna harbe mata da yara.

Gwamnatin Kamaru ta ce ta kama wasu sojoji shida bayan bincike kan wani bidiyon da aka watsa makwannin da suka gabata, da ya nuna yadda wasu sojoji suka ci zarafin fararen hula.

Wata kafar yada labarai ta Kamaru ce ta ruwaito wannan labarin a shafinta na Internet.

Hakan na nuna cewa gwamnatin ta sauya matsayar da ta dauka tun da farko na musanta cewa an kama sojojin.

Ana zargin sojojin shida da hada baki wajen kisan gilla ga mata da kananan yara a yankin Arewa Mai Nisa.

A cikin wani hoton bidiyo da aka ringa watsa wa a kafofin sada zumunta, an gano wasu mutane sanye da kayan sojoji sun harbe mata biyu daya da goyo a bayanta, da kuma wata yarinya.

An jiyo suna zargin matan da dangataka da kungiyar Boko Haram.

Hukumomin Kamaru sun tura sojoji yankin Arewa Mai Nisa da ke makwabtaka da Najeriya, domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi sojojin kamaru da laifukan yaki, a yunkurin murkushe Boko Haram.

Osinbajo ya ba da umarnin a yi wa SARS garambawul


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayar da umarnin yin garam bawul wa hukumar gudanarwa da kuma ayyukan rundunar ‘yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami (SARS).

Mukaddashin shugaban Najeriyar ya ba da umarnin ne bayan korafe-korafen take hakkin bila Adama da aka yi wa rundunar yaki da fashi da makami (SARS) din.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai matasa a Najeriya sun yi ta neman a soke rundunar a shafukan sada zumunta, musamman ma Twitter ta hanyar amfani da maudu’in #EndSARS .

Wata sanarwa da babban mai taimakawa na musamman na mukaddashin shugaban kasar kan harkar watsa labarai, Laoulu Akande ya fitar, ta ce duk wata rundunar da za ta fito bayan garam bawul din za ta mayar da hankali ne kawai kan aiki da bayanan sirri da hanawa tare da gano fashi da makami da satar mutane, gami da kama wadanda da suka yi irin wadannan laifukan.

Hakazalika Osinbajo ya umarci sufeto janar na ‘yan sanda ya tabbatar da cewar dukkan jami’an da za su kasance cikin sabuwar rundunar su zama masu gudanar da ayyukansu ta hanyar mutunta dokakin kasa da kuma kiyaye hakkin bil Adama na wadanda ake zargi da aikata laifi.

Mukaddashin shugaban kasar ya kuma ce dole ne jami’an rundunar su ringa tafiya da alamar rundunar a duk lokacin da suke bakin aiki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Har wa yau, Osinbajo ya umarci shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya da ya samar da wani kwamiti na musamman wanda zai yi bincike game da zargin da ake yi wa rundanr SARS na yin wasu ayyuka ba bisa doka ba, domin mutane su samu damar gabatar da koke-kokensu.

Mece ce makomar Eriksen da Pogba da Nzonzi da Loftus-Cheek da kuma Darmian?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Christian Eriksen

Paris St-Germain tana shirin ataya dan wasan Tottenham mai shekara 26 wanda shi ne madugun kasar Denmark Christian Eriksen, kan kudi fan miliyan 100, in ji (Express).

PSG tana kuma son wani dan wasan Tottenham kuma – dan wasan bayan Ingila Danny Rose. Spurs ta yarda ta sayar da dan wasan mai shkeara 28 a wannan watan, in ji (Mirror).

Schalke na son daukar dan wasa tsakiyar Ingila mai shekara 22 Ruben Loftus-Cheek domin ya buga mata wasan aro , amma da alama Chelsea ba za ta yarda da tafiyarsa ba, in ji (Telegraph).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ruben Loftus-Cheek

Loftus-Cheek ya shirya domin jajircewa wajen samun gurbin wasa a cikin ‘yan wasa 11 na farko na Chelsea, in ji(Guardian).

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu bai yanke kaunar neman dan wasan tsakiyar Manchester United dan kasar Faransa Paul Pogba ba, mai shekara 25, kuma ya ce “kawo yanzu dai muna da lokacin ciniki” a kasuwar musayar ‘yan wasa ta lokacin bazara, in ji (Sun).

Marseille na tunanin taya dan wasa tsakiyar Arsenal dan kasar Masar mai shekara 26 Mohamed Elneny, wanda ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta shekara hudu a watan Marais, in ji (Mirror).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mario Balotelli

Kocin Nice Patrick Vieira ya ce tsohon dan wasan gaban Manchester City da Liverpool ami shekara 28 Mario Balotelli – dan kasar Italiya – na son barin kulob din, in ji Canal+ .

Dan wasan bayan Manchester United Matteo Darmian yana son tafiya, kuma Juventus da Napoli da kuma Inter Milan na son dan wasan bayan Italiya din mai shekara 28, in ji (Manchester Evening News).

KocinManchester United Jose Mourinho ya shiga rudu game da maganar da Paul Pogba ya yi ta nuna cewar akwai matsala tsakaninsu, in ji (Telegraph).

Liverpool za ta saurari tayi akan dan wasan bayan kasar Estoniya, mai shekara 32, Ragnar Klavan, in ji (Liverpool Echo).

Dan wasan gaban Ivory Coast, Wilfried Zaha, mai shekara 25, ya ce har yanzu yana tattaunawa da Crystal Palace game da tsawaita kwantiraginsa ,in ji (Mail).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Steven Nzonzi

Paris St-Germain da Monaco suna son dan wasan Sevilla dan kasar Faransa mai shekara 29, Steven Nzonzi, in ji (France Football).

Kocin Real Madrid Julen Lopetegui yana son sayen dan wasan baya da kuma dan wasan gaba kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa, in ji(AS).

An kai harin ‘ta’addacin majalisar dokokin Birtaniya


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

An hango lokacin da Motar ta daki shinge binciken ‘yan sanda da gudu

Ana cafke wani mutum da ake zargi da ta’addanci bayan ya bi ta kan mutane da mota a wajen ginin majalisar dokokin Birtaniya.

Motar ta bi ta kan mutanen da ke tafiya a gefen hanya da misalin karfe 7:30 na safiya, inda ya jikkata mutum 3.

Babu wasu bayanai da ke nuna cewa mutum mai shekara 20 yana cikin mutane da hukumar leken asiri ta Birtaniya MI5 ko ‘yan sanda da ke yaki da’addanci ke sa ido a kansa.

Akwai wata mace guda cikin mutanen da suka jikkata da ake bai wa kulawar gaggawa sai dai raunin da ta samu ba wanda yake barazana ga rayuwarta ba ne.

Shugaban ‘yan sandan da ke yaki da ta’addanci a London, Neil Basu ya ce babu wata sauran barazanar tsaro da ake fuskanta a yanzu a birnin Landan, dama Birtaniya baki daya.

Image caption

‘Yadda ‘yan sanda suka tusa keyar mutum da ake zargi da kai harin.

Shaidu da dama sun ce da gangan matukin motar kirar Ford ya saki hannusa tare da buge mutane da ke kan kekuna da masu tafiya a kafa.

Hotunan BBC sun nuna lokacin da direban ya haye inda masu tafiya da kafa ke bi, kafin daga bisani ya tunkuyi shingayen binciken jami’an tsaro. An kuma hango lokacin da wani jami’in dan sanda ya arce daga kan hanya, gudun kar ya bi ta kan sa.

Yau dai ba a bude Majalisar ba. Kuma an rufe hanyar jirgin karkashin kasa a Westminister da wasu manyan tittuna da ke kewayen birnin.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka cafke wanda ake zargi tare da sa masa ankwa bayan faruwar al’amarin.

Image caption

Yadda Motar ta daki shinge binciken ‘yan sanda a Westminister

Wakiliyar BBC kan harkokin da suka shafi cikin gida June Kelly ta bayyana kamen a matsayin babban ci gaba.

”Yan sanda za su binciki mutumin da kuma asalinsa, watakila su gano haka ko suna kan hanyar gano hakan,” a cewar Kelly. ”Za su binciki abinda ya yi imani da shi, da mutanen da ya ke alaka da su, da lafiyar kwakwalwarsa.

Firaminista Theresa May ta ce: ”Hankalina na tare da wadanda suka jikkata a harin Westminister, kuma ina godewa sashin kai daukin gaggawa da bai yi kasa a gwiwa ba.”

Magajin garin London Sadiq Khan ya yi alla-wadai da faruwar lamarin da ya bayyana da halayen ‘yan ta’adda.


‘Shaidu na bayyana yadda suka tsere da ran su’

Barry Williams, wani ma’aikacin BBC da ke zaune a Millbank, ya ce: “na ji ihun ya yi yawa shi ne na juya.

“Motar ta saki hanya, ta koma hannun da ba nata ba, inda masu keke ke jiran a basu hannu, ta bi ta kan su.

“Direbar ya sake komawa kan titi ya karawa motar wuta da gudu ya tunkuyi shinge da ke kan hanya’

“Yar karamar motar ce ruwan azurfa, amma tsabar gudun da ya ke yi sai da motar ta yi sama sannan ta dawo kasa.


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An dakatar da hada-hadar motoci a Millbank

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jami’an tsaro na ci gaba da shawagi a inda aka samu hatsarin

Sama da motar ‘yansanda 10 da motar bada agajin gaggawa akalla 3 aka girke a wajen ginin Majalisa bayan faruwar lamarin.

Jami’ai dauke da makamai da karnuka na cigaba da bincike a yankin.

‘Yan sandan Birtaniya da ke kula da sufuri sun ce za su karfafa matakan tsaro a Ingila da Scotland da Wales, kuma jami’ansu za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a tashohin jirage da Motoci

Image caption

Taswirar kewayen da lamarin ya faru a birnin Landan

‘Legas na cikin biranen da suka fi wuyar sha’ani’


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Legas ta zo ta 138 cikin birane 140 da aka yi kuri’ar jin ra’ayin jama’a

Binciken shekara-shekara na Mujallar The Economist da ke Burtaniya, ya ce birane 7 cikin 10 na duniya da ba su da dadin zama a nahiyar Afirka su ke.

Binciken da ya wallafa jerin kasashe 140 inda aka aiwatar da bincike a kai, ya yi nazari akan daidaiton siyasa da walwala da miyagun ayyuka da ilimi da wadatuwar kiwon lafiya.

Birnin lagos da ke Najeriya, shi ne na 138-inda mataki 2 ya raba shi da babban birnin Syria wato Damascus da yaki ya daidaita kuma yake mataki na 140 a rukunin kasashen da mujallar ya wallafa.

Birnin Harare na Zimbabwe shi ne ke mataki na 135, yayin da birnin Tripoli a Libya ke mataki na 134, sai Douala a Kamaru da ke mataki na 133.

Sauran sun hada da Algiers na Algeriya da ke mataki na 132, Dakar na Senegal na mataki na 131.

Sai dai birnnin Johannesburg na Afirka ta Kudu da ke mataki na 86 a duniya, ya kasance birnin da yi fi kowanne birni dadin rayuwa a Afirka.

Rahotan da mujallar ke wallafa kowacce shekara ya ce birane a yankunan gabas ta tsakiya da Afirka da Asiya su ne 10 karshe cikin 140 da ke fuskantar karancin kwanciyar hankali, hade da rigingimu da ta’addanci da kuma yaki.

Birnin Melbourne na Australia shi ya fi kowanne dadin rayuwa a duniya a cewar The Economist, yayin da Vienne a Austria ke mataki na Biyu sai Vancouver na Canada da ke na 3.

Kamar yadda rahotan ya nuna kasashen Australiya da Canada kowanne na da birane 3 da rayuwa ke da dadin zama a cikin birane 10 da ke kan gaba a duniya.

Kuma wadanan kasashe biyu ke kan gaba wajen samun farin ciki a duniya kamar yadda rahotan Majalisar dinkin duniya ya bayyana a baya.

Babu birnin Amurka ko guda da ke cikin rukunin 10 farko, sakamakon matsalolin da suka shafi rashin kwanciyar hankali da ke da alaka da mutuwar bakaken fata a hannu jami’an tsaro.

Suma biranen masu alfarma da arziki irin su London da Paris da Tokyo ba sa cikin jerin farko na biranen da ake rayuwa mai dadi a yanzu, saboda karuwar matsalolin tsaro da cunkoson mutane da matsalolin sufuri da ke tasiri ga walwalar al’ummarsu.

Karyewar babbar gada ta zub da mutane a ruwa


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani bangaren rusasshiyar gadar ya fada ne cikin wani tafki.

Wata babbar gada ta karye a kusa da birnin Genoana na Italiya, abinda ya janyo motoci da dama suka fada cikin ruwa.

Ministan sufurin kasar, Danilo Toninelli, ya ce alamu na nuna cewa hadarin ya yi muni.

Kamfanin dillacin labarai na Adnkronos ya ambato wani jami’in lafiya yana cewa mutane da dama sun mutu.

Hukummomi sun shaida wa AFP cewa mafi yawan wajen da ya karye ya fada ne kan layin dogo na jirgin kasa, inda suka kara da cewa motoci manya da kanana sun fado daga karyayyiyar gadar.

An gina gadar ne a shekarun 1960, kuma akwai dimbin jama’a a garin da da lamarin ya faru.

Gadar dai ta fadi ne lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Dole Bukola Saraki ya bar majalisa —Akpabio


Hakkin mallakar hoto
Facebook/ Godswill Akpabio

Tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom, Sanata Godswill Akpabio, ya ce dole shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya bar majalisar idan ana son a kore shi daga majalisar.

Sanata Akpabio, wanda ya bar mukaminsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar a lokacin da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, ya fadi wannan maganar ce a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Saraki ya bi sawun wasu sanatoci da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP mara rinjaye lamarin da ya sa jam’iyyar APC mai rinjaye ke cewa ya kamata ya sauka daga shugabancin majalisar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato Akpabio yana cewar idan wasu suna neman a ayyana cewar babu kowa kujerar mazabarsa a majalisar saboda ya koma APC, dole Saraki da wadanda suka bar APC su ma su bar kujerunsu a majalisar.

Akpabio ya ce “duk wanda ya bar APC zuwa PDP, za mu ayyana kujerarsa a matsayin kujerar da babu kowa.”

Cikin ‘yan kwanakin nan dai an yi guguwar sauya sheka a siyasar Najeriya kamar yadda a aka yi gabannin zabukan 2015.

Hakkin mallakar hoto
Facebook/Bukola Saraki

Yayin da wasu ke ganin guguwar sauya shekar za ta iya tasiri kan yunkurin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na sake komawa kan karagar mulki a shekarar 2019, wasu gani suke sauye-sauyen shekar ba za ta hana Buhari komawa wa’adi na biyu ba.

Yawan muninka yawan farin jininka


An sabunta wannan labari bayan da aka wallafa shi a karon farko a watan Maris, 2016.

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Wannan biri wanda ake kira orangutan a Ingilishi yana da wata halitta ce mai kama da faifai a gefen kumatunsa, wadda mata ke sha’awa, amma kuma sai namiji ya kai shekara 20 take fito masa.

Melissa Hogenboom ta yi nazari.

Duk balagaggen nau’in wannan biri na orangutan, wanda ake samun irinsa asali a kasashen Indonesia and Malaysia yana da wannan abu mai kama da faifai, kuma matan birin sun fi kaunar wanda yake da shi kan wanda ba shi da abin.

Cikakken balagaggen birin ya kai tamata biyu a girma kuma yana da babban makoko (a makogaro) wanda dukkanin wadannan alama ce ta iko da kuma karfi.

Sai dai wadannan abubuwa sukan dauki lokaci kafin su fito wa namijin.

Wani yakan kai shekara 20 kafin wannan abu mai kamar kunne ko mahuci ya fito masa a gefen kumatu.

Mazan da wannan abu bai fito musu ba, sukan yi kama da mata kuma ba su kai wadanda na su ya fito ba girma.

Wani sabon bincike ya yi kokarin bayyana dalilin da ya sa abin ya kan dauki lokaci kafin ya fito wa mazajen.

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Image caption

Mata sun fi son mazan da suka fi fadin fuska

Domin gudanar da wannan bincike masana kimiyyar, sun tattara kashin mazajen wannan nau’in biri guda 17.

Goma daga ciki wadanda wannan abu ya fito musu ne, shida kuwa ba su da shi, yayin da sauran dayan ya fara fito masa.

Dukkanninsu suna gandun daji ne na Mawas da ke Kalimantan a Indonesia.

Masanan sun duba yawan kwayoyin halitta a cikin kashin birran, inda suka gano wadanda suke da wannan halitta ta gefen kumatun suna da yawan kwayoyin halitta na jima’i na namiji (testosterone) a cikin kashin nasu.

Jagoran masi binciken Pascal Marty na jami’ar Zurich a Switzerland, ya ce, ” mazan da wannan abu mai kama da mahuci bai fito musu ba ba su da yawan kwayoyin jima’i na namiji a cikin kashin nasu”.

An wallafa wannan bincike ne a mujallar, ”American Journal of Primatology”.

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Image caption

Baligan maza sun fi mata girma

Da zaran mazajen sun fara fitar da wannan halitta ta gefen kumatun mai girma sai yawan kwayoyin halittarsu na jima’i ya karu.

”Yawan wannan kwayoyin halitta a jikin irin wadannan mazaje da ake wannan nazari a kansu ya dan bayar da mamaki, amma ya nuna bukatar samun karin kwayoyin halittar jima’in domin bayyanar sauran alamu na balaga (kamar wannan abu na gefen kumatu),” in ji Marty

Idan namijin birin ya samu cikakkiyar wannan halitta sai kuma yawan kwayoyin halittarsa na jima’i su sake karuwa.

Wani nazari da aka yi na baya a kan irin wadannan birrai da ke gidan namun daji ya nuna cewa gasa tsakanin mazaje na iya sa wannan halitta kara girma.

Haka kuma wani nazarin na baya ya nuna cewa gasa tsakanin mazaje na iya haddasa gajiya a tsakaninsu wadda kuma ka iya dakushe girman wannan halitta a mazan da ba su da karfi sosai.

Sai dai binciken Marty bai samu shedar da ke tabbatar da hakan ba.

”A wurin da muke gudanar da bincikenmu ba mu taba ganin lokacin da wasu mazaje baligai masu wannan halitta ta gefen kumatu suke fada ba.

Saboda haka ba mu da shedar da ta nuna gogayya tsakanin mazajen na da nasaba da ya karin yawan kwayoyin halitta,” in ji masanan.

”Sakamakon wannan binciken ya sa mu yi watsi da maganar cewa damuwa ko hamayya ita ce babbar abar da ke sa dakushewar girman wannan halitta ta gefen kumatun birran.”

Hakkin mallakar hoto
SUWI

Image caption

Wasu mazajen ba su da sa’ar samun wannan halitta ta fuska

Bayan farin jini a wurin mata, bincike ya nuna cewa wadanda suke da wannan halitta babba a kumatun nasu sun fi koshin lafiya.

Wadanda suka tsufa da kuma masu rauni ana ganin wannan halitta ta motse a jikinsu.

Girman wannan halitta na nunawa karara cewa abu ne da ya dogara ga sauyin kwayoyin halitta.

Amma ”abin da ke haddasa wannan sauyi shi ne har yanzu ba a gano ba,” in ji Marty.

Yana ganin wadanda suka yi bi diddigin rayuwar wannan nau’i na biri (orangutan) gaba dayanta watakila su iya gano amsar.

Idan ana son karanta wannan a harshen Ingilishi a latsa nan Why male orangutans have such weird faces

‘Yan sanda na bincike kan Salah


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon da aka nuna Mo Salah yana taba waya kuma yana tuki

Kungiyar Liverpool ta sanar da ‘yan sanda game da wani hoton bidiyo da aka dauka na Mohammed Salah yana dannar wayar salula yayin da yake tukin mota.

Rundunar ‘Yan sandan yankin Merseyside ta tabbatar a wata sanarwa da ta wallafa a Twitter cewa an gabatar da bidiyon a sashen da ya dace domin bincike.

Liverpool ta ce ta sanar da ‘yan sanda ne bayan ta tattauna da dan wasanta.

Ta kara da cewa duk wani mataki da za ta dauka kan dan wasan na Masar za ta dauke shi ne a cikin gida.

Bidiyon wanda ya mamaye shafukan sada zumunta ya nuna Mo Salah wanda ya jefa wa Liverpool kwallaye 44 a raga a kakar da ta gabata yana dannar waya a gaban motar da magoya bayansa suka mamaye kuma yana tuki.

Liverpool ta ce ba za ta sake cewa komi ba game da batun haka ma dan wasanta Salah.

Matashi ya kirkiri na’urar rage barnar abinci a Afirka


Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Barnar abinci matsala ce da ake fama da ita a duniya baki daya.

A Afirka kadai, abincin da ake barnatarwa duk shekara zai iya ciyar da mutum miliyan 300.

Amma wani dalibi a Uganda ya kirkiri wata fasaha wacce za ta magance wannan matsala a kasarsa.

Wannan labari na daga cikin shirin BBC na masu Fasahar Kirkira wato BBC Innovators, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta dauki nauyi.

Facebook zai fara nuna La Liga kai-taye kyauta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kamfanin Facebook ya sanar da matakin fara nuna wasannin gasar La Liga ta Spain kai-tsaye kuma kyauta a wasu kasashen kudancin Asiya.

Za a fara kallon wasannin na kwallon kafa kai-tsaye a kafar Facebook a kyauta bayan kamfanin na sada zumunta ya sanar da kulla yarjejeniya da hukumar gasar La Liga ta Spain.

Wata sanarwa da kumar La Liga ta fitar ta ce Facebook zai nuna dukkanin wasannin gasar 380 na kakar bana da za a soma a ranar Juma’a.

Masu amfani da Facebook da ke sha’awar kwallon kafa za su kalli wasannin a kasashen India da Afghanistan da Bangladesh da Nepal da Maldives da Sri Lanka da kuma Pakistan.

Facebook zai ci gaba da nuna wasannin kai-tsaye daga wannan kakar har zuwa kakar wasanni biyu masu zuwa, a karkashin yarjejeniyar.

Facebook ya ce zai fara nuna wasannin ne ba tare da saka wata talla ba.

Sai dai kuma gasar ta La liga da kuma kamfanin na facebook ba su bayyana kudin da suka amince ba na yarjejeniyar.

Ana ganin wannan babban mataki ne ga Facebook na nuna wasannin gasar kwallon kafa. Kuma duk da cewa kasashen yankin sun fi sha’war kwallon kuriket da kuma wasannin kwallon kafa na Firimiyar ingila amma kuma sha’war kwallon kafa na ci gaba da karuwa a yankin musamman a India.

Ana dai ganin nuna wasannin kyauta da Facebook zai yi zai kashe wa wasu kafofin da ke nuna wasanni, musamman kamfanin Sony da aka ruwaito ya biya dala militan 32 don ‘yancin nuna wasannin gasar La Ligar Spaniya a yankin tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018.

Facebook na da mabiya mliyan 348 a India da kudancin Asiya.

Kuma fara nuna wasannin kwallon kafa a shafukan sada zmunta na intanet kai tsaye kuma kyauta, wasu na ganin babbar barazana ce ga masu ‘yancin nuna wasannin kwallon kafa a kafofin talabijin.

An cire tallafin mai a Venezuela


Image caption

Cire tallafin man wani yunkuri ne na samawa gwamnati kudaden shiga

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya ce za a kara farashin man fetur da kasarsa ke samarwa dan su yi kai daya da sauran kasashe, hakan shi ya karshen shirin tallafin mai na gwamnatinsa.

Mista Maduro ya ce ya dauki matakin ne saboda masu fasa kwauri na cutar kasar na miliyoyin daloli da ya kamata su zama kudaden shigar gwamnati.

Ita ma Venezuela ta na bai wa ‘yan kasar wani kaso a matsayin tallafi, kamar yadda wasu kasashe masu arzikin man fetur ta hanyar saukakawa ‘yan kasa farashinsa.

Amma ba su taba kara farashin mai ba, duk kuwa da cewa tattalin arzikin kasar ya dade ya na fuskantar koma baya.

Wakilin BBC a Venezuela ya ce matakin da gwamnati ta dauka katsahan, kokari ne na kara samar da hanyoyin kudaden shiga ga gwamnati dan ceton tattalin arzikin da ya fada halin ni ‘ya su.

Likitar Najeriya ta yi nasarar samun damar ci-gaba da aiki a Ingila


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

An sami likita Hadiza Bawa-Garba da laifin kisan kai bisa kuskure ta hnayar tsantsan sakaci a shekarar 2015

Wata likita wadda aka fitar da sunanta daga jerin sunayen likitoci saboda mutuwar wani yaro mai shekara shida ta yi nasara a daukaka karar da ta yi ta neman damar ci-gaba da aikin likita.

An cire sunanta ne a watan Janairun shekarar 2018.

Daukaka kararta ta sami tallafin ma’aikatan kiwon lafiya domin sun ce hukuncin zai rage wa ma’aikatan kiwon lafiya kwarin gwiwar bayyana gaskiya a lokacin da ake bincike kan kurakurai.

Hukuncin ya biyo bayan Jack Adcock mai shekara shida wanda ya mutu a asibitin Leicester Royal Infirmary a shekarar 2011 a lokacin da wata cuta mai suna sepsis wadda ba a gano ba ta janyo masa bugun zuciya.

Kare alumma

An dakatar da likita Bawa-Garba daga jerijn sunayen likitoci masu aiki na shekara daya a watan Yunin shekarar 2017.

Duk da haka, hukumar kula da aikin kiwon lafiya a Ingila (GMC) ta daukaka kara kan hukuncin tana mai ikirarin cewar bai “kai ya kare dukkan mutane ba” kuma an cire sunanta daga sunayen likitoci a watan Janairun 2018.

Dubban likitoci sun rattaba hannu kan wata budaddiyar wasikar goyon bayan likita Bawa-Garba, suna masu cewar shari’ar za ta “rage damammakinmu na hana aukuwar irin mutuwar”.

Daga farko dai, manyan alkalai uku sun soke hukuncin babbar kotun kuma suka tabbatar da karamar ladabtarwar dakatarwar shekara daya.

Alkalin kotun daukaka kara, Sir Terence Etherton, wanda ya bayyana hukuncin, ya ce “ba a taba nuna wata fargaba” ba “game da kwarewar Dr Bawa-Garba a aikin likita, fiye da mutuwar Jack”.

Hakkin mallakar hoto
Adcock family

Image caption

Jack died at Leicester Royal Infirmary in 2011 when undiagnosed sepsis led to cardiac arrest

Ya ce “Hujjara da ke gaban kotu ta nuna cewa tana kashi daya cikin uku na awadanda suka fi hazaka cikin wadanda suke karatun kwarewa tare.”

Ababen damuwa’

Charlie Massey, shugaban hukumar GMC, ya yarda da hukuncin kotun daukaka karar.

Ya ce: “A matsayinmu na hukumar dake kare marasa lafiya ana yawan kiranmu mu dauki matakai masu wuya, kuma ba ma wasa da wannan aikin.”

Mista Massey ya kara da cewa lamarin ya “fitar da ababen damuwa” dangane da hurumin dokokin laifuka a harkar kiwon lafiya kuma hukumar GMC ta bayar da aikin bincike mai zaman kansa sakamakon wannan lamarin.

“Likitoci sun kalubalance mu mu fito domin kare wadanda ke aiki a cikin yanayi mai wuya, kuma wannan ne muke kara matsa kaimi wajen yi,” in ji shi.

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

An cire sunan Dr Hadiza Bawa-Garba (dake dama) bayan hukumar dake sa ido akan aikin likitoci ta daukaka kara

Tunisia: Za a daidaita rabon gado tsakanin maza da mata


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaba Essebsi ya ce Tunisia kasa ce mai sassaucin ra’ayi.

Shugaban Tunisia zai bayyana wata sabuwar doka da za ta daidaita rabon gado tsakanin maza da mata.

Shugaba Beji Caid Essebsi ya ce zai gabatar da kudurin dokar ga Majalisar dokokin kasar.

A adinin musulunci maza sun fi mata samun kaso mai yawa , sai dai shugaba Essebsi ya nanata cewa Tunisia kasa ce mai sassaucin ra’ayi.

Ana sa ran zai sanar da kudurin daidaita rabon gado tsakanin maza da mata a ranar mata ta duniya .

Haka kuma ana ganin shugaban zai sanar da kudurin kare hakkin yan luwadi da madugo, sai dai ya ce zai kafa wani kwamiti da zai yi nazari kan shirin nasa kafin ya wallafa shi domin kaucewa fushin yan kasar, ko kuma a bayyana shi a matsayin wanda ya yi ridda.

Mece ce makomar Pogba da Karius da Rabiot da Mario da Norwood da kuma Bakayoko?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tiemoue Bakayoko

AC Milan tana hakon dan wasan Chelseadan kasar Faransa mai shekara 23, Tiemoue Bakayoko, domin ya buga wasan aro, wanda zai zama kwantiragi na din-din-din, in ji (Sun).

Barcelona za ta nemi Paul Pogba bayan an rufe kasuwar musyaar ‘yan wasa ta Turai ranar 31 ga watan Agusta, bayan ta “amince a asirce” cewar Manchester United ba za ta sayar da dan wasan Faransan mai shekara 25 ba a cikin wannan watan, in ji (Telegraph).

Golan Liverpool Loris Karius, mai shekara 25, dan wasa ne da Besiktas ke hako. Kungiyar ta Turkiyya tana son dan kasar Jamus din ya buga mata wasan aro a tsawon kaka daya, in ji (Sun).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Raheem Sterling

Kawo yanzu dai dan wasan Ingila, Raheem Sterling, bai yarda ya tsawaita kwantiraginsa ba da Manchester City ba, yayin da kocin kungiyar Raheem Sterling ya ce kungiyar “tana jin dadinsa kuma za ta so Raheem ya tsaya”, in ji (Telegraph).

KocinChelsea Maurizio Sarri ya ce dan wasan baya David Luiz yana da “babbar makoma” a kulob din , duk da cewa dan kasar Barazil din mai shekara 31 ba ya samun gurbin wasa sosai karkashin tsohon kocin kulob din Antonio Conte, in ji (Mirror).

Sarri ya ce ya yi nadamar rashin saya wa Chelsea Gonzalo Higuain, amma dan kasar Argentina din mai shekara 30 ya ce ya koma AC Milan ne daga Juventus domin Sarri “kadai ne yake so na a Chelsea” amma kuma “a Milan kowa na so na”, in ji Star

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jason Denayer

Dan wasan tsakiyar Tottenham dan kasar Ingila Dele Alli ya ce ababen da ke tafiya a kulob din ba su yi tasiri kan ‘yan wasan ba bayan Spurs ba ta sayi ko dan wasa daya ba a kasuwar musayar ‘yan wasan lokacin bazara da aka rufe kwanan nan, in ji (Mail).

Dan wasan bayan Manchester City mai shekara 23 Jason Denayer ya ki ya je ya buga wasan aro domin dan wasan bayan Belgium din yana son ya koma kungiyar kwallon kafar Turkiyya, Galatasaray, in ji(Star).

Keftin din Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bukaci Juventus ta nemi dan wasan tsakiyar Lazio Sergej Milinkovic-Savic. An alakanta dan wasan mai shekara 23 dan kasar Serbiya da komawa Manchester United da Chelsea, in ji (Star).

Dan wasan tsakiyar Paris St-Germain Adrien Rabiot, mai shekara 23, ya ki tayin tsawaita kwatiraginsa da zakarun gasar Ligue 1. Kwantiragin dan wasan Faransan zai kare a karshen wannan kakar ,in ji (L’Equipe – in French).

Dan wasan bayan Schalke dan kasar Jamus Thilo Kehrer, mai shekara 21, ya shirya domin komawa Paris St-Germain bayan an cimma yarjejeniyar fan miliyan 33, in ji (Guardian).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Joao Mario

Real Betis za ta iya tayin sayen dan wasan kungiyar Inter Milan, Joao Mario. Dan wasa tsakiyar Portugal din, mai shekara 25 ya buga wasanni 14 a lokacin da ya je buga wasan aro a West Ham United a kakar da ta gabata da gasar kofin duniya, in ji (Mundo Deportivo).

Dan wasan tsakiyar Watford dan kasar Faransa Abdoulaye Doucoure, mai shekara 25, ya nuna cewar zai bar kulob din a gaba, in ji (Watford Observer).

Rahotanni sun ce Manchester United na tattaunawa da Fenerbahce kan dan wasan bayan Argentina mai shekara 28, Marcos Rojo, in ji (Mirror).

‘An shawo kan sojojin da suka yi bore a Maiduguri’


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Rundunar tsaro ta ce kura talafa bayan boren da wasu sojoji suka yi

Rundunar da ke yaki da Boko Haram da aka yi wa lakabi Operation lafiya dole ta ce kura ta lafa bayan bore da wasu sojoji suka yi a filin jirgin saman Maiduguri, ranar Lahadi.

Ta ce shugaban rundunar Janaral Abba Dikko ya shiga tsakani kuma ya yi wa sojojin bayani.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar, Kanal Onyema Nwachukwu ta ce za a dauki mataki, domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.

Bayyanai sun ce sojojin da ke fada da kungiyar Boko Haram sun shafe kusan sa’o’i hudu suna harbi sama tare da yin barazana ga kwamandojinsu.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu daga cikin sojojin na cewa fushi ne shi ya sa suke harbi, suna cewa basu ga dalilin da zai sa a dauke su zuwa wani wuri ba bayan sun yi shekaru hudu a Maiduguri.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce wasu tsiraru ne suka yi boren saboda matakin da aka dauka na turasu fagen daga.

Ta ce an dauki matakin ne bayan nazarin da rundunar ta yi kan yanayiin tsaro a yankin .

“An dauki matakin ne bayan nazari na baya-baya nan da aka yi kan yanayin tsaro a yankin. Sai dai abin takaici wasu sojoji tsiraru basu fahimci dalilin da yasa aka dauki wannan matakin ba , sun dauka zai shafi yawan shekaru da za su yi suna aiki , shi yasa suka fusata suka rika harbi sama”. in ji sanarwar.

Sai dai akwai rahotanin da ke cewa ana ci gaba da samun karuwa a yawan sojojin da suke da damuwa a kan yadda ake tafiyar da shirin yaki da Boko Haram, duk da cewa gwamnatin kasar ta yi ikirarin karya lagwon mayakan kungiyar tun daga shekarar 2015.

Amma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

PDP za ta kalubalanci sakamakon zaben Katsina —PDP


Hakkin mallakar hoto
Twitter/@PDPNigeria

Babbar jam`iyyar adawar Najeriya, PDP, ta ce za ta kalubalanci sakamakon zaben cike-gurbi na kujerar dan majalisar dattawa ta mazabar Katsina ta Arewa, inda ta sha kaye a hannun jam`iyyar APC mai mulkin kasar.

Jam’iyyar APC dai ta yi nasara ne a zaben da wa da kani suka yi takara inda APC ta samu kuri’u 224,607, ita kuwa PDP ta samu 59,724.

Duk da irin tazarar da sakamakon zaben ya nuna cewar APC ta bai wa PDP, jam’iyyar PDP ta ce ba ta yarda ba domin tana ganin an yi magudi.

Sai dai kuma, jam’iyyar APC ta musanta zargin, tana mai cewa shure-shure PDP din ke yi kawai.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Majigiri kuma ya shaida wa wakilin BBC Ibrahim isa cewa ba su amince da sakamakon zaben ba.

“Gaba daya mun yi watsi da sakamakon wannan zabe. Ba mu taba samun lokacin da ake sayen kuri’a da kudi ba irin wannan lokacin. Tamkar sakamakon nan a rubuce yake, karanta shi ake yi. Yaya za a yi a ce cikin mazabu 128 a yankin Daura in banda mazabata babu inda PDP ta ci zabe?” Inji Alhaji Salisu

Ya kara da cewa “A shirye muke za mu wuce kotu da yardar Allah.”

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta ce mazabar Katsina ta arewa mazaba ce da APC ta yi kaka-gida kasancewarta mazabar Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Kakakin jam’iyyar APC na jihar, Abubakar Gambo Danmusa, ya shaida wa BBC cewa tun daga shekarar 2003 da Buhari ya shiga siyasa, jam’iyyarsa ce ke cin zabe a yankin.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@APCNigeria

Image caption

Dan takarar jam’iyyar APC Ahmad Babba-Kaita ya doke dan uwansa Kabir Babba-Kaita na PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar dattawa da aka gudanar a Katsina ta arewa a ranar Asabar

Zabukan cike-gurbi na kujerun `yan majalisar dattawa biyu da dan majalisar wakilai daya da kuma dan majalisar dokokin jiha daya aka yi a Najeriyar a ranar Asabar din da ta gabata, amma kujera dan majalisar jiha kadai jam`iyyar PDP ta tsira da ita, wadda aka yi a jihar Cross-River da ke kudu-maso kudancin kasar. Sauran kuwa duka APC ce ta lashe su.

Yadda rashin sanin asali ke taba rayuwar yara


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda rashin sanin asali ke taba rayuwar yara

Gidan marayu nan ne wajen da ke zamewa yaran da aka tsinta, ko wadanda iyayensu suka mutu sanadiyar hatsari kuma aka kasa gane danginsu gidan zama na dindindin.

Zubar da yaran da aka haifa ba bisa aure ba, ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a Najeriya, musamman a arewacin kasar.

Hakan na faruwa ne sakamakon irin abun kunyar da ke tattare da haifar yara ba ta hanyar aure ba, inda iyayen ke ganin gara su jefar a kwata, ko kududdufi ko bola ko su ajiye a wajen wucewar mutane maimakon sun rike a wajensu.

Wasu ko ba a jefar da su ba, to su kan taso cikin rayuwa ta kunci, don yadda ake nuna musu kyama kan nasabarsu, wato haihuwarsu ba tare da aure ba.

Kamar dai yadda wata mata da ta bukaci na sakaya sunanta ta shaida min, “Babu abun da ke tunzura zuciyata ya sa ni bakin ciki da kuka irin idan na tuna cewa ban san waye mahaifina ba.”

Duk da cewa shekarunta a yanzu 35, wannan mata ta ce ba za ta taba daina kuka ba a rayuwarta in har ba ta gano waye mahaifinta ba.

“Duk da cewa na san mahaifiyata, amma rashin sanin mahaifina da sanin hanyar da na fito ba karamin saka ni kuka take ba duk da tarin shekarun, kuma abun bacin ran shi ne yadda mahaifiyar tawa take kin amsa tambaya ta son sanin mahaifina,” in ji ta.

Image caption

Mace

Yawanci idan aka tsinci irin wadannan yara, waje na farko da ake fara kai su misali a jihar Kano, shi ne ofishin hukumar Hisbah, ko wajen masu unguwanni ko dagatai. Su kuma daga nan sai su mika su ga Sashen Walwala da Jin Dadi na jiha wato Social Welfare.

Daktra Zahra’u Umar, ita ce mataimakiyar shugaban hukumar Hisba a jihar Kano, ta kuma shaida min cewa: “A kalla mu kan samu jariri daya a wata, wani lokaci kuma idan abun ya birkito ma sai mu samu har zuwa jarirai hudu a wata.”

Ta ce mafi munin irin wannan lamari shi ne yadda mafi yawan yaran da ake tsintowa jarirai ne, “Kuma an fi jefar da su a kwata ko a bola ko kududdufi, amma cikin ikon Allah a hakan a mafi yawancin lokuta da ransu ake kawo mana su.”

Alhaji Mai-Fada Ali, shi ne mai unguwar Gama B da ke Brigade a Kano, kuma majalisarsa na daga cikin wuraren da “in dai ana neman yaran da suka bata, aka zo nan ba a samu ba, to yawanci sai a fidda tsammani”, kamar yadda ya shaida wa BBC.

“Ana kawo mana yara ‘yan tsintuwa daga jarirai har zuwa wadanda suka dan tasa. Wasu ma za ku ga tamkar dama iyayen sun shirya tsaf ne kafin su kawo su, don har da kayansu ake hadawa a ajiye su.”

“Duk da cewa ba ma ajiye yawan yaran da ake kawowa, amma a kalla a wata wani lokacin sai a kawo mana yara kamar 40. Wani sa’in kuma sai a kwana biyu ma ba a kawo ba,” in ji Mai Unguwa Mai-Fada.

Ina ake kai su?

Dukkan bayanan da hukumar Hisba da Mai-Unguwa suka yi sun nuna cewa a kan kai yaran ne ga hukuma, wato Sashen Walwala da Jin Dadi da ke karkashin ma’aikatar mata ta jiha don daukar bayanansu, daga can kuma sai a kai su Gidan Marayu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rashin sanin nasabar mutum babban tashin hankali ce kamar yadda mafi yawan wadanda ke cikin irin wannan hali suka shaida wa BBC

Amma kafin nan sai an kai su asibiti don duba halin lafiyarsu sun yi kamar mako biyar a can.

“Wani lokaci kuma sai na tafi da su gidana sun kwana biyu ma kafin a kammala cike takardun daukar bayanansu,’ in ji Malama Zahara’u.

Wasu mutanen daga cikin al’umma kan bukaci a ba su irin wadannan yara don su dauki nauyin kula da su tare da zame musu iyaye.

Mai Unguwa Mai-Fada ya ce: “Akwai yarinyar da aka kawo mana nan sai wata mata ta bukaci a ba ta, amma bayan an kwana biyu sai ake ta yi mata gori kan cewa ta dauko ‘yar da ba ta sunna ba, sai ta dawo da ita.

“Sai mai dakina ta ce ba sai mun mayarwa hukuma an kai gidan marayu ba, mu rike ta kawai.”

A yanzu dai Mai Unguwa yana rike da irin wadannan yara har biyu.

Me ke faruwa a Gidan Marayun?

Gidan Marayu na Nassarawa na daya daga cikin gidajen da ake kai wadannan yara don rayuwa ta dindindin, har zuwa lokacin da za su yi aure ko kuma idan aka yi sa’a iyayensu suka bullo don nemansu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a iya cewa yaran da ke gidan marayu na Nasarawa sun yi sa’a da samun ingantaccen wajen zama idan aka kwatanta da wasu a nahiyar Afirka, kamar wannan hoton da ke nuna wani gidan marayu a Nairobi na kasar Kenya

A ziyarar da tawagar BBC ta kai, ta fahimci cewa gida ne mai girman gaske da yake da bangarori daban-daban da dakuna da makarantar Islamiyya da filin wasa da dakunan girki da dakunan zama don hutawa masu kayan kallo da dai sauran su.

Hajiya Lauriya Sagir Garba ta ce “Yanzu ‘ya’yanmu guda 65 a gidan nan, maza 44 sai mata 21. Shekarunsu sun fara daga wata biyu zuwa shekara 31.

“Yaran suna zuwa makarantun boko a cikin gari wadanda suka hada da na gwamnati da na kudi, sannan suna islamiyya a nan cikin gida.

“Akwai masu kula da su dare da rana, kuma muna mu’amala da su irin ta ‘ya’ya da iyaye don ganin mun debe musu kewa,” in ji Hajiya Lauriya.

Cikin yaran da muka tattauna da su a wannan gida, sun shida mana cewa suna matukar jin dadin rayuwarsu don ana wadata su da duk abun da yara ke bukata.

“Muna cin abinci sau uku, wani lokaci ma sau hudu a rana. Muna wanka sau biyu, sannan muna da suturu da dama, don gaskiya mutane na waje ma na iya kokarinsu wajen kawo mana ziyara da wadata mu da kayan bukatu,” in ji wata matashiya mai shekara 18 da muka boye sunanta.

Kewa

Sai dai duk da irin wannan daula da yaran ke ciki, hakan bai hana masu wayo daga cikinsu kewar mahaifansu da ba su ma san su waye ba.

Hajiya Lauriya ta ce duk kokarin da suke na ganin sun cike wa yaran nan gurbin iyaye da suka rasa, “to wani lokacin sai an ga alamar damuwa a tare da masu wayo daga cikinsu, kuma damuwar ba ta komai ba ce sai ta rashin sanin asalinsu.”

Habu (Ba sunansa na gaskiya ba) matashi ne mai shekara 18 da shi ma yake gidan, ya kuma shaida min cewa ba shi da wani buri da ya wuce Allah ya sa yana da rabon ganin iyayensa ko wani jininsa a duniya.

“Duk da cewa ba abun da nema na rasa a gidan nan, amma duk dare idan na kwanta sai na yi ta fatan ina ma wata rana na hadu da mahaifana ko wasu dangina. Ban dai fidda tsammani ba,’ in ji Habu, kamar dai yadda da dama daga cikin yaran ma suka shaida min irin wannan magana.

Aure

A gidan marayu Hajiya Lauriya ta shaida min yadda suke aurar da ‘ya’yan nasu, bayan sun kammala karatu.

Ko a loakcin da muka kai ziyara ma mun iske ana shirye-shiryen bikin daya daga cikin yaran maza, don har mun ga lefensa.

“Duk lokacin da suka kai aure in dai sun samu masu son su to biki muke shirya musu na bajinta a nan gidan. Sannan mu kan kai wasu hidimomin kamar Kamu ko liyafa gidajen manyan jami’an gwamnati ko gidajenmu tamkar yadda ake kai biki sauran ‘ya’ya gidajen ‘yan uwansu,” a cewar Hajiya Lauriya.

Sai dai a wasu lokutan samun abokan rayuwa na iya yi wa wadannan yaran wahala, don ganin yadda al’umma take jinjina batun asali a wajen neman aure.

Na hadu da wata matashiya da akai wa aure a gidan amma auren ya mutu bayan shekara daya, kuma ta ce min har da gorin da ake mata a dangin mijin cikin sanadin mutuwar auren.

“A kan yi min gori wasu lokutan cewa ba ni da iyaye ko asali, abun dai ba dadi,” in ji ta.

Image caption

Sau da yawa, wadanda suka taso a cikin irin wannan yanayi na rashin sanin uba ko ma uwa da uba kan fuskanci tsangwama da kyara daga al’umma

Matsayar musulunci kan nasabarsu

Sau da yawa, wadanda suka taso a cikin irin wannan yanayi na rashin sanin uba ko ma uwa da uba kan fuskanci tsangwama da kyara daga al’umma, har ma akan kira su da wasu sunaye da ke muzanta su.

Sai dai, a cewar Dakta Zahra’u wannan bai dace ba, kuma ba shi da asali a musulunci.

Image caption

Dakta Zahra’u ta ce bai dace a dinga tsangwamarsu ba don musulunci bai yarda da hakan ba

“Wallahi ba su da wani laifi don ba su ne suka yi zinar ba, iyayensu ne suka yi. Kuma ko su iyayen idan suka nemi gafara Ubangiji Mai Gafara ne da Jin Kai, zai dube su ya yafe musu. Don haka bai kamata al’umma su dinga kyamarsu tare da gudunsu ba,” kamar yadda ta ce.

Fatan yawancin wadannan yara dai shi ne al’umma ta gane hakan, a kuma daina tsangwamarsu, a kuma dauke su kamar sauran mutane.

Darajar kudin Turkiyya na kara faduwa


Image caption

Shugaba Erdogan ya shaidawa ‘yan kasar faduwar darajar Lira tamkar wani abu ne ya fada cikin kofin shayi, ba duka ba ne ya zube

Darajar kudin Turkiyya Lira na ci gaba da faduwa cikin sauri idan aka kwatanta da kudaden kasashen waje, duk da cewa ministan kudin kasar Berat Albayrak ya sanar da daukar matakan ceto tattalin arzikin Turkiyya da ke fuskantar barazana.

Shugaba Racep Tayyep Erdogan ya shaidawa dandazon magoya bayansa a birnin Trabzon cewa Amurka ce ta janyowa kasarsa halin da suke ciki yanzu.

Ya sanar da cewa za a mai dawa wadanda suke yakin kasuwanci da kasashen duniya ciki har da Turkiyya martanin cewa ba za’a dawwama a haka ba.

Mista Erdogan ya kara da cewa”Za mu warware ta hanyar sabbin abokan huldar kasuwanci, idan kun lura sun kara haraji kan Tama da Karafa, ba za mu karaya ba dan mu ma mambobin kungiyar kasuwanci ta duniya ne”.

A ranar asabar da ta gabata shugaba Erdogan ya yi kira ga ‘yan kasar musamman mata da suke ajiyar kadarar gwala-gwalai, da su dauko su dan sauyawa zuwa kudin Lira da zuba kudin a bankuna dan ceton tattalin arzikin kasarsu.

Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa tuni hannayen jarin wasu kamfanonin kasar suka fara fuskantar koma baya, ya yin da masu zuba jari kuma su ka dan janye saboda rashin sanin halin da kasar za ta iya fadawa a ciki.

Masana tattalin arziki sun ce idan aka kara daukar makwanni ba tare da Lira ta fara farfadowa ba, farashin kayan amfanin yau da kullum musamman na abinci za su kara tashi abin da hakan ke nufin ‘yan kasar za su dandana kudarsu.

Cutar Kwalara ta barke a jamhuriyar Nijar


Image caption

Cikin wadanda suka kamu da cutar amai da gudawar kananan yara sun fi shan wahala

A jumhuriyar Nijar cutar amai da gudawa ce ta barke tare da hallaka kusan mutane 19.

Mutane dubu 1,168 ne suka kamu da cutar a gundumar Madarunfa ta jahar Maradi da ke yankin kudancin kasar.

Sama da wata daya dai kenan da aka samu barkewar wannan cuta a wannan yanki, kuma cikin wadanda lamarin cutar ya shafayara kanana sun fi yawa.

Dr Alhaji Ibrahim Tasiu shi ne darakatan kiwon lafiya a gundumarta Madarunfa kuma ya shaidawa BBC cewa daga ranar Juma’ar da ta gabata zuwa yanzu dai ana iya cewa kusan mutane 19 ne.

Mutanen da suka kamu da wannan cuta ta amai da gudawa na kwance a babban asibitin birnin Maradi ne, kamar yadda hukumar jin kai ta Majalasar Dinkin Duniya wato OCHA ta sanar.

Rahotanni sun bayyana cewa a garin N’Yelwa ne aka fara samun mutum na farko da ya kamu da cutar ta Cholera tun a farkon watan Yuli da ya wuce.

To sai ministan ma’aikatar lafiya Nijar Illiassou Mai Nassara ya shaidawa manema labarai cewa , tuni gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar zuwa wasu sassan kasar musamman yankunan karkara.

Kungiyar likitocin kasa da kasa Medecin sans frontiere, da Asusun kula da yara na Majalasar Dinkin Duniya sun isa yankin da cutar ta bulla dan taimakawa wadanda suka kamu da cutar.

Da wayar da kan al’uma muhimmancin tsafar muhalli da wanke hannu kafin ci da bayan kammala cin abinci da tsaftar kayan abincin musamman kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa.

Sojojin Najeriya sun yi bore a Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An shiga wani tashin hankali a filin jigin saman birnin Maiduguri inda rahotanni suka ce Sojoji sun ta yin harbi sama domin nuna rashin amincewa da matakin dauke su daga Maiduguri a jihar Borno.

Sojojin sun ki shiga jirgin da zai kwashe su daga Maiduguri zuwa karamar hukumar Marte da ke kan iyaka da Nijar.

Bayanai sun ce sojojin da ke fada da kungiyar Boko Haram sun shafe kusan sa’o’I hudu suna harbi sama tare da yin barazana ga kwamandojinsu.

Lamarin ya faru ne da yammacin lahadi kuma rahotanni sun ce kura ta lafa sai kuma babu tabbacin ko sojojin sun tafi Marte inda aka bukaci su koma.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu daga cikin sojojin na cewa fushi ne dalilin da ya sa suke harbi, suna cewa ga dalilin da zai sa a dauke su zuwa wani wuri ba bayan sun yi shekaru hudu a Maiduguri.

Babu dai wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya ko kuma rundanar da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar game da boren na jami’an sojin.

Ranar Talata za a yi babbar sallah a Najeriya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Babban kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ranar Talata 21 ga wannan watan ne ranar babbar Sallah a Najeriya.

Kwamitin ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana dalilinsa na yin haka:

“A kan batun cewa Saudiyya ta bayyana ranar Dhl Hijjah da ta bambanta da wanda muka riga muka bayyana, kwamitin ganin wata ya tuntubi babban kwamitin Fatawa na kasa a shekarun baya, kuma an fitar da wata Fatawa mai cewa ya kamata mu rika bin hukuncin ganin watan da kasar Saudiyya ta yanke na Dhul Hijjah saboda muhimmancin hawan Arafat.”

Wannan sanarwar ta ci karo da sanarwar farko da kwamitin ya fitar.

Sanarwar kwamitin ta cigaba da cewa, “A kan haka ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, bayan ya tuntubi kwamitin Fatawa da kwamitin ganin wata da sauran malaman addini har da sarakunan gargajiya, ya bayyana Lahadi 12 ga watan Agusta 2018 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah 1439H.”

A sanadiyyar wannan sauyin, mutane da dama sun fito suna maganganu na nuna rashin gamsuwa da matakin da kwamitin ya dauka.

A shafin kwamitin na Twitter, wasu sun soki wanann mataki:

Hamma @HAHayatu ya bayyana rashin jin dadinsa, “Kamata yayi ku amince cewa bamu fara azumin bana a kan lokaci ba, kuma kwanaki tsakanin Eid el Fitir da Eid al Adha ba sa wuce 70, kuma ba sa kasa 67. Mutane da dama sun ga watan a wurare masu yawa, amma kuka ki amincewa da haka.”

Shi ma Osama Ibraheem @GmIBRAHEEM cewa yayi, “Dama mun san haka za kuyi tun bayan ganin wata Zhul Qada, watan Shawwal bai cika kwana 30 ba, kuma kun yi ta gardama da mu a cikn wannan zauren. Ku koma ku duba, zaku tabbatar da abin da nake cewa.”

Amma wani mutumin mai suna Simwal @Simwal ya bayyana cewa ba Najeriya ce kawai ta sauya ranar babbar sallah ba.

Ya saka wata sanarwa daga mahukuntan Oman da ke bayyana haka:

“Daular Oman ta sauya ranar 29 ga watan Dhul Qadah ta koma 1 ga watan Dhul Hijjah a hukumance saboda sanarwar da Saudiyya ta fitar.”

A nasu bangaren kwamitin ganin watan ya kare kansa daga dukkan zargin da ake ke yi masa.

“Allah zai tambayemu dukkan abubuwan da muka aikata. Masu cewa an ga wata amma mun ki amincewa da bayanansu, kamata yayi su gabatar mana da hujjojinsu – a shirye muke da mu duba. Idan aka hada kwana 30 na Shawwal da 28 na Dhul Qadah da kuma kwana 10 na Dhul Hijjah sun kasance kwana 68 kenan.”

PDP ta lashe zaben Kuros Riba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan takarar jam’iyyar PDP ya lashe zaben maye gurbi na mazabar Obudu, inda ya doke sauran ‘yan takara daga jam’iyyu hudu.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Abbey Awara Ukpukpen ya lashe zaben da kuri’u 12, 712.

Ya doke sauran ‘yan takarar da suka fafata da shi, ciki har da na jam’iyyar APC wanda ya sami kuri’u 4,345.

An dai gudanar da zabuka guda hudu na maye gurbi a wasu mazabu dake ciki tarayyar Najeriya a jiya Asabar.

Mazabun sune na sanatoci a Arewacin Katsina da Kudancin Bauchi da na dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe na jihar Kogi.

Akwai kuma zaben maye gurbin dan majalisar jiha a mazabar Obudu ta jihar Kuros Riba.

APC ta lashe zaben dan majalisa a Kogi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin wanda ya lashe zaben na majalisar wakilai na mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe.

Farfesa Rotimi Ajayi na sashin nazarin kimiyyar siyasa na Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Lokoja ne ya bayyana sakamakon.

Ya bayyana Haruna Isa na dan jam’iyyar APC, wanda ya sami kuri’u 26,860 a matsayin wanda ya lashe zaben:

“Haruna Isa ya cika dukkan sharuddan zabe, kuma hi ne ya sami kuri’u mafi yawa, saboda haka shi ne ya lashe zaben dan majalisar da ya gudana.”

An gudanar da zaben ne don maye gurbin dan majalisar wakilai na mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe wanda wata babbar kotu ta sauke daga mukamin.

Dan takarar APCn ya fafata ne da wasu ‘yan takara su takwas daga jam’iyyu daban-daban.

Mai bi masa shi ne Abubakar B. Muhammad na jam’iyyar PDP wanda ya sami kuri’u 14,845.

Sai kuma Muhammad Kazeem na jam’iyyar ADC wanda shi kuma ya sami kuri’u 2,984.

An dai gudanar da zabuka guda hudu na maye gurbi a wasu mazabu dake ciki tarayyar Najeriya a jiya Asabar.

Mazabun sune na sanatoci a Arewacin Katsina da Kudancin Bauchi da na dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe na jihar Kogi.

Akwai kuma zaben maye gurbin dan majalisar jiha a mazabar Obudu ta jihar Kuros Riba.

Abin da ya faru a Afirka makon jiya


Zababbun hotuna masu kayatarwa daga sassa daban-daban na Afirka da aka dauka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan matar na daya daga cikin Kristoci 10 na Ethopia da suke murnar dawowar Bishof Merkorios da aka kora daga birnin Addis Ababa a ranar Juma’a.

Dubban 'yan addinin Ethopia sun taru a Millenium hall a Addis Ababa ranar asabar.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yaran da ba a haifa ba a lokacin da bishof din ya gudu Amurka shekara 27 da ta wuce suma sun shiga jerin wadanda ke wakokin addini a babban dakin Millenium.

Ranar Talata: Dakaru na musamman na Ivory Coast sun shafa ma fuskokinsu launin tutar kasarsu.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ranar Talata: Dakaru na musamman na Ivory Coast sun shafa ma fuskokinsu launin tutar kasarsu, a lokacin wani fareti na murnar cika shekara 58 da samun ‘yancin kai daga kasar Faransa.

A man in traditional Khoi San regalia waits before a land expropriation hearing being held in a church in Cape Town - Friday 4 August 2018Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani mutum ya halarci wani taron jin ra’ayin jama’a kan shirin da gwamnatin ke yi na karbe filayen fararen fata ba tare da biyan diyya ba a yankin Cape Town na Afirka ta Kudu.

A ranar Asabar mutane sun fito da motoci masu kama da wadanda 'yan sanda suka yi amfani da su a wurin kama Nelson Mandela shekaru 56 da suka gabata.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Asabar mutane sun fito da motoci masu kama da wadanda ‘yan sanda suka yi amfani da su a wurin kama Nelson Mandela shekaru 56 da suka gabata.

Ranar Asabar wani dalibi mai karanta Engineering akan motarsa mai amfani da iska da ya kirkiro domin taimakawa a wurin tsaftata iska a babban birnin Masar, Cairo.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ranar Asabar wani dalibi mai karantun kimiyya da fasaha na tuka motarsa mai amfani da iskar gas da ya kirkiro domin tsaftace iska a babban birnin Masar, al Kahira

A ranar Litinin wani mutum a birnin al Kahira ya wuce ta gaban wani allo da aka rubuta "Masar na zukatanmu."Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Litinin wani mutum a birnin al Kahira ya wuce ta gaban wani allo da aka rubuta “Masar na zukatanmu.”

A ranar Litinin din dai, wata yarinya a Zimbabwe ta tsaya kusa da wani hoton shugaban kasar Emmerson Mnangagwa da aka lalata a Harare babban birnin kasar.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Litinin din dai, wata yarinya a Zimbabwe ta tsaya kusa da wani hoton shugaban kasar Emmerson Mnangagwa da aka lalata a Harare babban birnin kasar.

Su kuma wadannan 'yan matan sun je makarantar Lahadi-Lahadi ce ta cocin Katolika na birnin Harare ranar Lahadin da ta gabata.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Su kuma wadannan ‘yan matan sun je makarantar Lahadi-Lahadi ce ta cocin Katolika na birnin Harare ranar Lahadin da ta gabata.

Wata mata da ta rasa dangi a wani harin bom da kungiyar al-Qaeda ta kai a babban birnin kasar Kenya shekaru 20 da suka gabata. Fiye da mutane 200 ne suka mutu a harin.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wata mata da ta rasa dangi a wani harin bom da kungiyar al-Qaeda ta kai a babban birnin kasar Kenya shekaru 20 da suka gabata. Fiye da mutane 200 ne suka mutu a harin.

A ranar Alhamis kuwa a kasar Masar, wasu maza ne suka dauko tunkiya a kan babur a wajen garin Giza wanda ke cikin shirye-shiryen sallah babba.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Alhamis kuwa a kasar Masar, wasu maza ne suka dauko tunkiya a kan babur a wajen garin Giza wanda ke cikin shirye-shiryen sallah babba.

A wannan hoton kuma mai sayar da dabbobi ne ke a jan wata tunkiya domin ya kai ta mota, ya saye ta ne domin bikin sallah babba.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A wannan hoton kuma mai sayar da dabbobi ne ke a jan wata tunkiya domin ya kai ta mota, ya saye ta ne domin bikin sallah babba.

A ranar Talata wani mahayin doki ya nuna kwarewarsa ta sukuwar doki a wani taro na shekara-shekara da aka fi sani da the "Knights of Libya Festival".Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Talata wani mahayin doki ya nuna kwarewarsa ta sukuwar doki a wani taro na shekara-shekara da aka fi sani da the “Knights of Libya Festival”.

Wadannan hotunan an samo su ne daga AFP, EPA, Getty Images da Reuters

An jinkirta bikin rantsar da zababben shugaban kasa a Zimbabwe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hukumar zabe a Zimbabwe ta ayyana shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda yayi nasara a zaben na 30 ga watan Yuli

An dage bikin da aka shirya gudanarwa a yau Lahadi na rantsar da shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban Zimbabwe.

Wannan matakin na bangaren ‘yan adawa ya biyo bayan rashin amincewa da sakamakon zaben da suka yi ne, inda suka shigar da kara a gaban kotu.

Jagoran jam’iyyar adawa ta MDC, Nelson Chamisa, ya ce suna da hujjoji da ke cewa an kwace masa nasara ne a zaben shugaban kasa na 30 ga watan Yuli.

Jam’iyyarsa ta kuma ce “an tafka gagarumar satan kuri’u da magudi”, amma hukumar zaben kasar ta kafe cewa ba a aikata irin wannan laifi ba.

Mista Mnangagwa ya lashe zaben da kashi 50.8 cikin 100 na kuri’un da aka kada, shi kuma Mista Chamisa ya sami kashi 44.3 cikin 100.

Ministan shari’a Ziyambi Ziyambi ya bayyana cewa “an dakatar da bikin rantsar da shugaban kasa kamar yadda aka shirya”, bayan da jam’iyyar MDC ta kalubalanci sakamakon zaben a kotu a ranar Jumma’a.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Jagoran jam’iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa ya ce an sace zaben da yayi nasara ne

Al’ummar Zimbabwe ta yi ta fatan wannan karon za a sami kwanciyar hankali da sauyi mai dorewa bayan shekaru 37 na mulkin hambararren shugaba Robert Mugabe.

Ana zabe cikin matakan tsaro a Mali


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Al’ummar Mali na zabe cikin fargabar tsaro

Al’ummar Mali na zaben shugaban kasa zagaye na biyu mai cike da kalubalen tsaro wanda za a fafata tsakanin shugaba mai ci Ibrahim Boubakar Keita da ke neman wa’adi na biyu da kuma shugaban adawa Soumaila Cisse.

Shugaba Keita ne ya zo na farko a zagayen farko da kashi 42 na yawan kuri’u fiye da Cisse tsohon ministan kudin kasar wanda ya samu kashi 18 na kuri’u.

Ana zagaye na biyu na zaben ne cikin yanayi na barazanar tsaro bayan rikici ya mamaye zagayen farko.

Da misalin karsfe takwas na safe agogon GMT ake sa ran bude runfunan zabe yayin da kuma ake sa ran rufe wa da misalin karfe shida na yamma.

An dai samu karancin fitowar masu kada kuri’a a zagayen farko inda kashi 40 ne kawai suka fito daga cikin kashi dari na yawan adadin masu kada kuri’a.

Rikicin da aka samu a zaben zagayen farko na shugaban kasa da aka gudanar watan jiya ya sa gwamnatin Mali kara yawan dakaru domin wanzar da tsaro a runfunan zabe.

Sojoji kimanin 36,000 gwamnatin Mali ta ce za ta girke domin zaben, inda aka kara yawan dakaru 6,000 fiye da adadin wadanda aka girke a zagayen farko.

Kusan kashi uku na masu kada kuri’a ne rikicin ya hana wa kada kuri’a a zagayen farko bayan rikicin ya hana bude runfunan zabe kusan 900.

Mali na fuskantar barazanar hare-hare ne daga arewaci da kuma tsakiyar kasar.

Ministan tsaron kasar Salif Traore ya shaidawa BBC cewa za su tsaurara tsaro a yankin tsakiyar kasar da aka samu matsaloli a zagayen farko.

Saboda matsalar tsaron ne dai ya sa ‘yan takarar zaben na shugaban kasa suka takaita yakin neman zabensu a Bamako babban birnin kasar.

Ana dai ganin shugaba Bubakar Keita ne zai yi nasara a zaben bayan samun yawan kuri’u a zagayen farko duk da suka da yake fuskanta daga abokin takararsa Cisse kan gazawa wajen shawo kan matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

‘Yan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko da aka gudanar sun ki marawa Cisse tsohon ministan kudin kasar baya, wani babban kalubale gare shi akan shugaba Keita a zaben.

Tun kafin zaben na zagaye na biyu Kotun kundin tsarin mulki ta yi watsi da zargin da ‘yan adawa suka shigar kan an yi magudi a zagayen farko.

Barazanar mayakan jihadi a Mali dai ta bazu daga yankin arewaci zuwa tsakiya da kudancin kasar har zuwa kasashe makwabta, wanda wannan ne babban kalubalen da ke gaban sabon shugaban da za a zaba, Musamman wajen tabbatar da yarjejeniyar 2015 da aka kulla tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye.

Yadda ake cinikin ragunan Sallah a Intanet a Algeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana sayen miliyoyan raguna da tumaki domin Sallar layya

Matsalar satar ragunan Sallah ya sa masu sayar ragunan Sallah da tumaki a Algeria sun koma suna amfani da shafin Facebook da wasu shafukan intanet domin tallar dabbobinsu.

Suna fatan cinikayya ta hanyar Intanet zai kare su daga hatsarin da ke tattare da daukar dabbobinsu zuwa birane don sayar wa a lokuttan sallar layya, saboda an dade ana yi wa ‘yan kasuwa duka a kwace dabbobinsu, kamar yadda shafin labarai na Echouurouk ya ruwaito.

Shafin Facebook da Ouedkniss.com a Algeria, ya ba ‘yan kasuwa damar saka hutunan dabbobinsu daga gida domin talla.

Sannan akwai wani shafi kuma da ke tallar dakon dabbobin ga ‘yan kasuwa zuwa ga wadanda suka saya a Intanet.

‘Yan kasuwar yanzu na amfani da shafin Facebook domin tallar ragunan sallah a sassan Algeria don gujewa hatsarin da ke tattare wajen kwasar ragunan zuwa birane domin sayar wa ga masu bukatar yin layya.

Hakkin mallakar hoto
Ouedkniss.com

Image caption

‘Yadda ake tallar Raguna da Tumaki a Intanet.

Ana sa ran za a yi layya da dabbobi kusan miliyan shida a Algeria a bana, sabanin miliyan hudu da aka yanka a shekarun baya.

Kungiyar manoma ta Algeria ta ce tana son sawwake wa mutane dabbobin layya inda za su iya saya cikin sauki.

A ranar 21 ga watan Agusta ake sa ran gudanar da sallar layya, biki na biyu mafi muhimmaci ga musulmi bayan bikin Sallar Azumi wato Eid el-fitr.

Ka san ma’anar launin lakataye?


An sabunta wannan labari bayan da aka wallafa shi a karon farko a watan Mayun 2016.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Lokacin da Joshua Blue mataimakin shugaban makarantar Kennedy School a Hong Kong ya shirya wa ɗalibansa wani taro, ya sanya lakataye mai launin shanshanbale (shudi-shudi), domin ya fita daban a cikin ɗaliban ta yadda ba za su ƙosa da maganganunsa ba idan yana jawabi.

Malamin ya ce lakataye din yana da launi mai kyau amma kuma duk da haka ba ya fitowa sosai, abin da shugaban ya ke gani zai hana daliban gajiya idan suna sauraron jawabinsa.

A daya hannun Mista Blue mai shekara 35, ba ya son sanya lakataye me launin da yake da haske idan zai yi wa dalibai jawabi domin kada launin ya rika dauke musu hankali a lokacin jawabin.

Za ka ga kamar shirme ne kawai, amma kwararru sun ce kowane irin taron muta ne ne za ka yi wa jawabi, ma’aikata ko dalibai ko wani rukuni na jama’a na daban, idan ka sanya lakataye mai launin da ya dace hakan zai taimaka ma wajen isar da sakonka.

David Zyla marubucin littafin Color Your Style, wanda yake a New York ya ce, ”launi yana bayar da wani sako na musamman, za ka iya amfani da kwat (riga) daya amma da lakataye launi daban-daban, kowanne da irin sakon da zai bayar da kuma tasiri.”

Yanzu ka fara tunanin launin lakatayen da za ka sa zuwa taro na gaba? To ga yadda za ka zabi launin lakatayen da zai dace da kowane taro:

Launin ja me karfin mulki da iko

Ba wai katari ba ne ya sa kake ganin yawancin ‘yan siyasa suke sanya jan lakataye da riga ‘yar ciki (shat) mai haske da kuma kwat mai launi mai duhu ba.

Mark Woodman, mai fashin baki, wanda ya yi karatu a kan launi a birnin Laurel da ke Maryland a Amurka, ya ce ”launin ja lakataye ne na mulki, akwai wani abu da ke tattare da ja wanda ke nuna karfi da ado.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Yanayin jan naka ma yana da tasiri. Ja jazur na sa mutane su yarda da kai, yayin da jan da ba jazur ba da kuma launin ruwan hoda zai iya nuna irin tsarin sha’awar adonka da kuma kirkira.

Woodman ya kara da cewa, ”a shekara goma da ta wuce, lakataye mai ruwan hoda na nuna alamun goyon baya ga mata ne.” Idan kuma kana son nuna cewa kana kan gaba a wani aiki ko ka nuna kai mai wani buri ne to sai ka sa lakataye mai launin ja mai sheki.

Lakataye mai ruwan Algashi

Ross Znavor, babban jami’i a kan harkokin kudi a New York, yana sanya lakataye jaja-jaja mai ruwan algashi (purple), maimakon cikakken ja idan za shi taron harkokin kasuwanci saboda launin yana ba mutum kwarin gwiwa kuma yana burge mutane a haduwarsu ta farko ma.

Ya ce, ”sanya lakataye mai launin da ba kasafai aka saba da shi ba, yana nuna wa mutane ko ‘yan kasuwa cewa mutumin yana da kwqanciyar hankali da kwarin gwiwa, wanda kuma za ka so kulla alaka da shi.”

Lindsay ta ce, lakataye mai launin algashi wanda ake dangantawa bisa ala’da da sarauta da kuma dukiya, yanzu ya fara karbuwa a wuraren aiki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ta ce, ”maza na sanya riga ‘yar cikin kwat mai launin algashi maras duhu sannan su daura lakataye mai launin algashi mai duhu, idan suna son su fita daban, a cikin taro, ba tare da sun rika daukar hankalin mutane ba.

Bakin lakataye

Zyla ta ce, ”duk da cewa ba lalle ka sanya bakin lakataye zuwa taron manyan jami’ai ba akai akai, amma sanya shi zuwa liyafa yana fito da mutum. Woodman kuwa cewa ya yi, sanya lakataye mai launin fatsa-fatsa zai iya fito da kai fes, ba tare da ana maka kallon wani wanda kamar ba a san gabansa ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ya ce, ”launin fatsa-fatsa lakataye ne da zai sa a dauke ka wani dan zamani, idan kana son ya kara fito da kai sai ka hada shi da rigar shat mai launi maras duhu ko wanda bai turu ba sosai.

Koren lakataye

Launin kore na iya nuna abubuwa da dama kama daga alamar sabuwar rayuwa zuwa launin kudi a wasu kasashe, amma kuma abin mamaki, bai dace ba da wurin aiki domin za a iya daukar kamar ya yi bau ko kara da yawa.

Woodman ya ce, ”kana son a rika tuna ka saboda lakatayen da kake sanya wa ko kuma saboda kai kanka yadda kake?.” Zabar koren lakatayen da ya dace abu ne mai wuya. Koren da ya yi haske sosai yawanci yana daukar hankalin mutane da yawa, kuma wani lokaci ma zai yi maka wuya ka iya samun kwat ko shat din da za ta dace da shi, in ji masanin.

Hakkin mallakar hoto
Thinkstock

Duk da haka koren lakataye wanda bai turu ba sosai zai iya dacewa da shat mai launi tsaka-tsakiya.

A kasashe da dama ciki har da Ingila an dauki launin dorawa ko rawaya a matsayin launin lakataye na ainahi ko na al’ada, wanda zai nuna alamar dattaku da ado da kuma kuzari, kamar yadda Woodman ya bayyana.

Idan ka sanya lakataye mai ruwan dorawa, abokan aikinka za su iya zuwa wurinka ba tare da wata fargaba ko wani shakku ba, saboda launi ne na kwazo da ke alamta rana.

A wurin mutane da yawa, sanya lakataye mai ruwan dorawa, ”na iya nuna kwarin gwiwa da rashin shakku da kuma kyakkyawan fata a rayuwa,” kamar yadda Eve Roth Lindsay, kwararriya kan siffa a Hong Kong, ta kara da cewa.

Sai dai ka yi hankali kada ka je ka yi kwaba idan za ka zabi launin lakataye ko kayan da za ka sanya. Misali a kasar Indiya farin lakataye na iya nufin mutum dan kasuwa ne, in ji Zayla. A China kuwa farin lakataye na nufin lokacin makoki.

Launin Shudi daban-daban

kana jin tsoron aikewa da sakon da ba shi ka yi niyya ba da launin lakataye dinka? To ka sanya shudin lakataye, wanda zai iya dacewa da komai. Shudin lakataye yana da amfani sosai saboda launin yana tuna wa mutane sama da kuma teku, wadanda ke kwantar da hankali, kamar yadda Lindsay ta ce.

”Shudi launi ne da ya fi kwanciyar hankali ka sanya,” ta ce.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Lakataye shudi mai dan ado-ado a jiki yana sa mutum ya yi ruwan wani kwararren ma’aikaci kuma za a iya sanya shi a wurin wata harka ta kasuwancin duniya.

Shudin da bai nuna ba sosai yana nuna saukin kai da tunani, yayin da shudi sosai zai iya sa ka fito daban a cikin mutane, ta ce.

Shudi mai duhu yawanci yana tuna wa mutane kayan matukin jirgin sama ne shi kuwa shudi sosai launi ne da ka amince da shi wanda kuma ke bayar da karfin gwiwa, in ji Lindsay.

Ka zama daidai da duniya

”Lakataye masu launukan da ke nuna alamar zumunta kamar mai duhun kasa-kasa, da nau’in ruwan kasa daban-daban da launin hadakar ruwan hoda da na lemo da kuma ruwan dorawa suna dacewa da mutanen da suke mu’amulla da jma’a, kamar talla ko sayar da kaya da malamai da kuma ma’aikatun ayyukan jin dadin jama’a,” in ji Lindsay.

Ka tabbatar lakatayen ba launin ruwan kasa ba ne wanda ba shi da wani zane-zane ko wani dan ado-ado a jikinsa, saboda za a iya daukar mutum kamar wani dakiki idan ya sanya shi.

Lakataye mai launin kasa-kasa mai kyalli na nuna alama ta kwanciyar hankali, masaniyar ta ce. Amma ka guji hada lakataye mai ruwan kasa da riga mai irin launin, domin idan ka damu da samun karin girma a wurin aikinka, to ka kaucewa wadannan launukan ma gaba daya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What the colour of your tie says about you

Ana jiran sakamakon zabe a jihohin Najeriya hudu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana dakon sakamakon zabukan da hukumar zaben Najeriya ta gudanar a wasu mazabu da ke cikin jihohi hudu na kasar.

Da safiyar yau aka fara gudanar da zabukan kamar haka:

 1. Zaben sanata a gundumar arewacin jihar Katsina
 2. Zaben sanata a gundumar kudancin jihar Bauchi
 3. Zaben sanata a gundumar gabashin jihar Kogi
 4. Zaben dan majalisar jiha na mazabar Obudu a jihar Kuros Riba

A jihar Katsina, wani yaya da kaninsa ne ke takarar kujerar sanata ta arewacin Katsina wato yankin Daura a dalilin rasuwar tsohon sanata Mustapha Bukar.

A jihar Bauchi kuwa, ‘yan takara tara ne ke neman darewa kujerar sanatan gundumar kudancin jihar.

Sun hada da Lawal Yahaya Gumau (APC), sai Isah Yuguda (GPN), sai Haruna Ayuba (ADC), da Aminu Tukur (APP) da kuma Usman Hassan (Kowa Party).

Sauran sun hada da Maryam Bargel (SDP) da Husseini Umar (NNPP) da Usman Chaledi (PDC) da kuma Ladan Salihu (PDP).

Kamar jihar Katsina, duk wanda yayi nasara zai maye gurbin tsohon sanatan yankin ne, Sanata Ali Wakili wanda ya rasu a watan Maris na bana.

A jihar Kogi an gudanar da zabe ne domin maye gurbin tsohon sanatan yankin wanda wata babbar kotu ta sauke daga mukaminsa.

Sanata Atai Aidoko ya rasa mukaminsa ne saboda kotu ta gano cewa ya tafka kura’kurai wajen samun tikitin tsayawa takara a karkashin jam’iyyarsa ta PDP.

A jihar Kuros Riba da ke kudu maso gabashin Najeriya kuwa, an gudanar da zaben dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Obudu ne.

Mazabar ba ta da wakili tun bayan mutuwar wakilinsu Mista Stephen Ukpukpen a karshen watan Mayun bana.

Tuni dai aka gudanar da zabubbukan kuma a halin yanzu ana dakon sakamako ne a wadannan mazabu hudu da ke cikin jihohi uku na arewacin Najeriya da daya da ke udu maso gabashin kasar.

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa wadanda suka kada kuri’unsu sun zarce mutum miliyan biyu a cikin kanana hukumomi 22 na jihohi hudun.

Yaya rayuwa take kafin zuwan Google?


Me ke maganin ciwon sanyi? Wacce kasa ce tafi yawan jama’a a duniya? Me ake nufi da so? Wa ya kirkiri jirgin sama?

Tun kafa shi shekaru 20 da suka gabata, Google ya kasance kundin bincike da ke amsa tambayoyi kai-tsaye a intanet cikin sauki. Ya zama aikatau inda a ranar Laraba aka ci shi tarar dala biliyan biyar kan gwagwarmayarsa da abokan hamayya.

An rasa ayyuka da dama da suka shafi bincike bayan kirkiro da Google, har ya kasance yanzu an manta da yadda ake gudanar da ayyukan bincike.

Dan jarida

Gareth Hughes tsohon dan jarida ne da ya yi aiki da jaridar Daily Post a arewacin Wales tsakanin 1974 zuwa 2006 (shi ne mahaifin wanda ya rubuta wannan makala).

Hakkin mallakar hoto
Gareth Hughes

Image caption

Gareth Hughes ya fara amfani da tafraita kafin kwamfuta

“Na kan yi rubutu game da irin abubuwan da babu wanda zai yi tunanin nasan komai,” in ji shi. “Ina da kundin litattafai da dakin karatu, amma abu mafi muhimmi shi ne tabbatar da gaskiya.”

Muna da kuma dakin karatu a ofishinmu da ke Liverpool inda muke ajiye dukkanin jaridu da duk wani labari.

“Idan kana neman wani abu kan wani batu, jami’an da ke kula da dakin karatu za su bincika kuma su gabatar da shi a gareka. Aikinsu yana da ban sha’awa.”

“Ni ma na rika ajiye komai – na tuna da labarin wata jaririya da aka haifa can wani waje mai nisa kuma a tsakiyar hunturu, kuma nauyinta bai wuce kullin suga ba. An lullube ta da auduga a cikin wata motar daukar marar lafiya a yayin da sannu a hankali ake tafe da ita zuwa asibiti, kuma ta rayu cikin yanayi na zubar dusar kankara, a cikin wani lamarin da ba a taba tunanin za ta yi rai ba.

Na rubuta labarin watanni shida bayan ta bar asibiti, daga baya kuma ina cikin binciken abubuwan da suka faru sai na ci karo da labarinta. Sai na lura cewa ta kusa cika shekar 21 da haihuwa, saboda haka sai na fara neman inda take. kuma sai na gane cewa tana zaune a kusa da ofishina ne.”

“Zuwan Google ya taimaka kwarai, amma babu abin da yafi yin bincike da kanka dadi”.

Na kiyaye duk abin da ya faru – ina tunawa da labarin game da jaririn da aka haife mil daga ko’ina cikin tsakiyar hunturu, nauyin jakar sukari. An saka shi a cikin gashi na auduga a cikin motar motar asibiti ta hanyar tafiya ta hankali da dusar ƙanƙara da kankara a fadin mahaifa, kuma ba a sa ran ta tsira.

The barrister

Hilary Heilbron QC ta fara aiki a matsayin karamin lauya a shekarar 1972. Yanzu ta zama mambar wani babban ofishin lauyoyi a Landan, kuma ta dade tana aikin shari’a.

“A matsayina na karamar lauya, akan ba ni umarni kuma dole ne in yi cikakken bincike akai – kamar kundin shari’a. da litattafai – har zuwa dakin karatu. Domin yin sauran bincike kuwa, dole nake zuwa bababn dakin karatun lauya na Middle Temple domin samun bayanin wata shari’ar da ke da alaka da wata shari’ar.”

“A yanzu kuwa dukkan bayanan shari’a na cikin intanet – kaga ina da jerin littatafan shari’a a kantar ofishina, amma basu da wani amfani a greni sai dai na ado.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hilary Heilbron (Dama) tare da mahaifinta da mahaifiyarta Rose Heilbron, a lokacin da ake rantsar da mahaifiyarta a matsayin mai shari’a a babbar kotu a 1974

“Kuma babu damar yin tallace-tallace a wancan lokacin, saboda haka dukkan maganar kasuwanci da ake yi a yanzu bai ma taso ba. Kana yin aikinka ne yadda ya kamata, kuma sai kayi fatan wadanda kayi ma aikin za su ji dadi su kuma dawo.”

Mai lura da dakin karatu

A shekarun baya, ma’aikata a bababn dakin karatu na birnin New York sun zama tamkar manhajar Google mai jini, domin sun rika karbar tambayoyi daga mutane kuma su kan ba su amsoshin tambayoyin.

Amma a ‘yan shekarun nan, ma’aikatan sun gano wani tsohon akwati cike da irin tambayoyin da jama’a suka yi masu a da. Sai suka saka su a shafinsu na Instagram.

Wani ya tambayesu a 1948: “Ina zan iya samun ciakakkun bayanai akan dukkan ciniki da kudaden da su kayi musayar hannu a kasuwancin gawawwaki?”

A 2018 Google ya yi nuni kan wannan binciken da Reuters suka yi kan cinikin gawa a Amurka.

Wani kuma ya tambayesu a 1949, “Shin beraye na yin amai?”

An amsa masa cewa lallai beraye na yin amai.

“Idan maciji mai guba ya sari kansa, gubar za ta kashe shi?”

Da alama mutane na da tambayoyi masu sarkakiya a 1949. Amma har zuwa 2018 Google ya ce: babu wanda ya sani har yanzu.

“Wane lokaci ne tsakar rana?”

Amsar ita ce Karfe goma sha biyun rana.

The academic

Janice Yellin ta kammala karatun digirinta na uku wato PhD a fagen nazarin tarihin al’ummar Nubiya a kwalejin Brandeis da ke birnin Bostaon a farkon shekarar 1970. A yanzu ta zama farfesa a bangaren tarihi a kwalejein Babson da ke Massachusetts.

Hakkin mallakar hoto
Janice Yellin

Image caption

Janice Yellin kenan a cikin wani tsohon ginin dala na Nubiya da ya kai akalla shekaru 2,400 kafin zuwan Google

Ta ce “Google ya sauya komai. A yanzu ba sai na tafi wani dakin karatu ba domin neman wani bayani. Ina samin saukin bincike na kimanin kashi 80 cikin 100.

An rufe filin jirgin saman Seattle bayan da wani ya sace jirgin sama


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana iya ganin jiragen yaki na bin jirgin

Wani ma’aikacin kamfanin jirgin sama ya sace wani jirgin fasinja daga filin jirgin sama na birnin Seattle a Amurka, kuma jirgin ya fadi a wani tsibiri dake kusa.

Jami’ai a filin jirgin saman sun ce mutumin da ya sace jirgin a jiya Jumma’a, ya tashi da shi ne ba tare da izini ba.

A sanadiyyar aukuwar wannan lamarin an rufe filin jirgin sama na Seattle-Tacoma International.

Wasu jiragen yaki biyu samfurin F-15 sun bi jirgin wanda daga baya ya fado a Puget Sound. Jami’ai sun ce da alama matukin jirgin ya mutu nan take.

Ofishin ‘yan sandan garin ya ce lamarin “ba aikin ta’addanci ba ne”, kuma sun ce mutumin mai shekara 29 da haihuwa sananne ne a garesu.

Jirgin samfurin Bombardier Q400 mai injuna biyu mallakin kamfanin Horizon Air ne.

An tura wasu jiragen yaki biyu nan take, kuma bidiyon da wasu ‘yan kallo suka nada na nuna jiragen yakin na bin jirgin da aka sace.

Shin me yasa ya saci jirgin?

Ana ganin mutumin da ya saci jirgin yayi haka ne saboda ya burge kawai.

Sautin da jami’ai suka nada a lokacin da suke magana da mutumin ya tabbatar da haka.

An kuma ji mutumin na nuna damuwarsa saboda rashin isasshen mai a cikin jirgin.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan hoton jirgin ne yana tafiya kasa-kasa kusa da ruwa

Ya kuma ce zai iya sauka da jirgin da kansa saboda ya iya “tuka jiragen sama na cikin wasannin komfuta”.

A cikin sautin an kuma ji mutumin na cewa:

 • Ya na sha’awar zuwa dutsen Olympic Mountain da ke jihar Washington domin ya sha kallo
 • Ko zai iya yin wasa da jujjuya jigin kamar mazari kafin ya sauka
 • Yana fatan kamfanin da suka mallaki jirgin za su dauke shi aiki a matsayin direban jirgi idan har ya koma da jirgin ba tare da wata matsala ba

Hakkin mallakar hoto
CBS

Image caption

Hoton inda jirgin ya fadi kuma ya kama da wuta

‘Dodo’ Pogba ya taimaki Man Utd doke Leicester 2 -1


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Paul Pogba ya zura kwallo a wasansa na baya-bayan nan a gasar Rasha 2018

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya yaba ma “dodo” Paul Pogba bayan da dan wasan ya jagoranci kungiyarsa ga nasara akan Leicerster City a ranar farko ta gasar firimiyar Ingila na bana, inda ya jefa kwallon farko.

Dan wasan da a kwanan nan ake rade-radin zai koma Barcelona ya bayar da mamaki, kwanaki hudu bayan da ya soma atisaye tun daworsa daga gasar cin kofin duniya da kasarsa Faransa ta lashe.

Man Utd ta fara wasan da kafar dama a filinsu na OLd Trafford, inda suka sami bugun daga kai sai gola bayan da Daniel Amartey ha taba kwallon da Alexis Sanchez ya buga da hannunsa.

Nan take Pogba ya aika da ita cikin ragar Leicester bayan wani bugu da yayi mai ban sha’awa, kuma gola Kasper Scmeichel bai iya tare ta ba.

Daga baya dan wasan baya na United, Luke Shaw ya jefa tasa kwallon bayan da ya yi nasarar gyara kuros din da Juan Mata ya aika cikin gidan Leicester.

Amma Leicester ma ta zura kwallo daya ta hannun Jamie Vardy wanda aka saka daga baya.

Pogba ya buga wasa na tsawon minti 84 kafin Marouane Fellaini ya maye gurbinsa.

Mourinho ya ce bai yi tsammanin Pogba zai iya dadewa a wasansa na farko ba:

“Pogba dodo ne. Mun yi tsammanin ba zai iya wuce minti 60 ba, amma sai ga shi ya wuce minti 80 ma.”

“The decision belonged to Paul. I asked him and he made himself available and he was very good.”

Mourinho ya kara da cewa, “Zabin cigaba da buga wasan na Pogba ne. Na tambaye shi ko zai huta, amma sai ya ce gara ya cigaba da buga wasan”.

Isa Ali Pantami: ‘Ya halatta matar aure ta yi Facebook’


Hakkin mallakar hoto
Twitter/Pantami

Image caption

Dr Isa Ali Pantami

Shugaban hukumar kula da ci gaban fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Dokta Isa Ali Pantami ya ce ya halatta miji ya bar matarsa ta shiga shafukan sada zumunta, idan ba za ta saba wa dokokin addini ba.

Ya shaida wa BBC haka ne a wata tattaunawa ta musamman ranar Talata, inda ya ce miji na iya hana matarsa shiga shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter da Instagram da Whatsapp da makamantansu “idan har ba za ta saba wasu hakkokin addini ba.”

Hakazalika ya kuma ce idan har a ka bi hanyoyin da suka dace, amfani da shafukan sada zumunta na iya shigar da mutum aljanna.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Sadar da zumunta wajibi ne a addinin Musulunci’
 • Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar.

“Idan dai a manufofi na alheri ne, bai dace miji ya hana matarsa shiga shafukan sada zumunta ba,” in ji shi.

Har ila yau ya ce bai kamata matar aure ta rika abokanta da mutanen da ba su dace ba a shafukan sada zumunta.

“Ta rika abokanta da kawayenta da suka yi karatu tare, ta tarbi abokanta da yayyanta da kannenta da kuma sauran ‘yan uwanta na jini,” kamar yadda ya ce.

Rushe masallacin China ya jawo takaddama a Ningxia


Hakkin mallakar hoto
Weibo

Image caption

Masallacin na Weizhou wani kataferen gini ne mai kubbobi da hasumiyoyi, kuma an gina shi ne a salon gine-ginen gabas ta tsakiya

Daruruwan musulmi a yammacin China na takaddama da hukumomi domin hana rusa masallacinsu.

Jami’ai sun ce masallacin da a ka gama gininsa kwanan nan ba shi da takardun izinin gini a Ningxia.

Sai dai musulman sun ki amincewa, inda daya daga cikin mazauna garin ya ce ba za su “yarda gwamnati ta taba masallacin ba.”

China na da musulmi miliyan 23, kuma musulunci ya karbu a yankin Ningxia tsawon karni da dama da suka wuce.

Amma masu fafutikar kare hakki sun ce akwai karuwar nuna kiyayya ga Musulmi a China daga hukumomi.

An gina masallacin ne a wani salo na gabas ta tsakiya, inda ya ke da hasumiyoyi da kubbobi masu tsayi da dama.

Ya a ka fara boren?

Ranar 3 ga watan Agusta, jami’ai su ka buga wata sanarwa da ke cewa za a rushe masallacin da karfi da yaji saboda ba a bayar da izinin tsarawa da gina shi yadda ya kamata ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan kabilar Hui na daya daga cikin manyan kabilu musulmai a China

An rarraba sanarwar a shafukan intanet tsakanin ‘yan kabilar Hui, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta Reuters ta ruwaito.

Mutane da yawa sun bukaci sanin dalilin da ya sa hukumomi ba su hana gina masallacin ba, wanda a ka gama shekaru biyu da su ka wuce, in dai har ba a bayar da takardun izinin gina shi ba, kamar yadda wata jaridar kasar Hong-Kong ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa an yi zanga-zanga a wajen masallacin ranar Alhamis kuma a ka ci gaba a ranar Juma’a. Hotunan da su ka bazu a shafukan sada zumuntan China sun nuna taron mutane mai dimbin yawa a wajen masallacin.

Har yanzu dai ba a tabbatar ba idan za a fara rushe masallacin ranar Juma’a kamar yadda a ka tsara, ko kuma idan an cimma matsaya.

Kafar watsa labaran kasar China ba ta ce komai ba har yanzu.

‘Yan gida daya na takarar kujerar sanatan yankin Daura


Hakkin mallakar hoto
Kabir Babba Campaign

Image caption

Ahmad Babba Kaita (dama) da dan uwansa Kabir Babba Kaita

Wasu ‘yan uwa biyu wa da kaninsa za su fafata a zaben neman kujerar sanatan yankin Daura da ke jihar Katsina a Najeriya da za a yi ranar Asabar.

Ahmad Babba Kaita na jam’iyyar APC da dan uwansa Kabir Babba Kaita na jam’iyyar PDP ne ‘yan takarar da suke fafatawa a wannan zaben a mazabar sanata ta arewacin Katsina wanda aka fi sani da yankin Daura.

Kabir wan Ahmad ne domin mahaifinsu daya ne daga garin Kankiya na jihar Katsina.

Ahmad shi ne dan majalisar mai wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada a majalisar wakilan Najeriya.

Shi kuwa Kabir tsohon ma’aikacin hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ne wato kwastam.

‘Yan uwan biyu na neman cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.

Wani abin sha’awa shi ne duk wanda ya yi nasara a zaben na gobe zai kasance wakilin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin garin Daura na cikin yankin Katsina ta arewa ne.

BBC ta tambayi wasu ‘yan uwan wadannan ‘yan takarar yadda suka fuskanci wannan lamarin ganin cewa siyasa kan zama wani dalilin samun baraka tsakanin ‘yan uwa.

Hajiya Rabi Babba Kaita da Ali Babba Kaita sun bayyana cewa suna da karfin gwuiwa cewa wannan zaben ba zai kawo rabuwar kawuna a tsakaninsu ba.

Ga yadda hirarsu da Sani Aliyu na BBC ta kasance:

BBC Hausa: Ko yaya dangantaka take tsakanin wadannan ‘yan uwa su biyu a da?

Rabi Babba Kaita: Mu dai mun taso da girmama na gaba da mu. Saboda haka Ahmadu da Baba Kabir su ma haka suka taso.

A yanzu, Baba Ahmadu ya dauki Baba Kabir wanda muka fi sani da Baba Daddy kamar uba kuma yana girmama shi.

Shi kuma Baba Ahmadu, biyayyar nan da aka koya mamu ta sa yana bin Kabir shi sau da kafa. Har gobe idan ka je za ka tadda su tare.

BBC Hausa:Shin siyasa ba ta kawo baraka tsakaninsu ba?

Rabi Babba Kaita: To gaskiya muna ta bibiyar yadda suke tafiyar da al’amarinsu tun da aka fara wannan siyasa. Kuma har yanzu Baba Ahmadu na biyayya ga Baba Daddy, suna zaunawa su yi hira, babu abin da ya sauya tsakaninsu. Kuma mu ma tsakaninmu da su babu abin da ya sauya.

BBC Hausa: To mutanen gari fa, yaya suke kallon wannan lamarin?

Rabi Babba Kaita: Na taba karanta wani abu a Facebook da wani dan Kankia ya rubuta game da wannan siyasar. Ya ce ya lura da yanayin gidan da suka fito.

Sabili da haka ya rubuta cewa ya kamata mutane su yi kamfen dinsu cikin hankali da natsuwa. Saboda duk abin da aka fada wanda ya soki Kabir, to Ahmadu ba zai ji dadi ba, kuma duk abin da aka fada ya soki Ahmadu, shi ma Baba Kabir ba zai ji dadinsa ba.

BBC Hausa: Kina nufin babu wata matsala tsakanin Ahmad Babba da Kabir Babba?

Rabi Babba Kaita: Ana ma yin kamfe kansu na hade, ballantana an gama? Kuma ba yau aka fara irin wannan salon siyasar a nan gidan ba.

BBC Hausa: Ko za kiyi mana karin bayani?

Rabi Babba Kaita: Dama an taba samun ‘yan gidan nan su biyu da suka yi takarar mukamai a jam’iyyun siyasa mabambanta. Da Bishir Babba wanda yayi shugaban karamar hukumar Kankia a jam’iyyar PDP da kuma shi Ahmadu Babba wanda ya tsaya takarar kujerar dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC.

A karshe dukkansu sun sami nasara a kan mukaman da suka nema.

To BBC ta kuma nemi Aliyu Babba Kaita wanda shi ma dan uwan ‘yan takarar ne yadda iyalan gidan Babba Kankia za su tunkari wannan kalubalen a gobe?

BBC Hausa: Wa za ku zaba cikin ‘yan takarar biyu tun da dukkansu ‘yan gida daya ne?

Ali Babba: Ni yaya ne ga Ahmad Babba dan takarar sanata a karkashin jam’iyyar APC. Sannan ni kani ne na shida ko na bakwai ga Kabir Babba, shi ma dan takarar sanata a jam’iyyar PDP.

Kasancewa wadannan ‘yan uwan na takarar kujerar sanata daya daga mazabar arewacin jihar Katsina ya sa mu ‘yan uwansu muka duba lamarin da basira sosai.

Muna da sabanin ra’ayoyi da sabanin tunani kamar kowa, amma wannan bai taba shafar dangantakarmu da juna ba.

BBC Hausa: Ko za ka bayar da wani misalin irin wannan hadin kan?

Akwai wata ‘yar uwarmu da ta yi wa motocin kamfe na wadannan ‘yan takarar kwalliya da sitika. Ta yi wa motar Ahmadu kwalliya da alamar jam’iyyar APC, kana tayi wa motar Kabiru kwalliya da alamar PDP. Duk yawan moocinsu daya, kuma kowa ta ce a je a zabe shi.

BBC Hausa: To idan kun je runfunan zabe, wa za ku zaba a cikinsu?

To mu iyalan gidan mun zauna mun duba yadda za mu tunkari zaben. Kuma a matsayinmu na manyan gidan, mun bayar da shawara cewa gobe kowa ya yi zamansa a gida.

Babu wanda cikinmu zai fita ya yi zabe saboda muna son Baba Kabir kamar yadda muke son Ahmadu Babba.

Marar lafiya ya lakada wa Likita duka a Jihar Ondo


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Marar lafiyan ya far wa likitocin da ma’aikatan jinya har daya daga cikinsu ya suma

Wani marar lafiya ya far wa tare da raunata wasu likitoci biyu da kuma ma’aikatan jinya uku a Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce mara lafiyar mai fama da tabin hankali ya fusata ne lokacin da ma’aikatan jinyar suka zo su ba shi magani.

Ya far wa likitoci biyu da kuma ma’aikatan jinya uku inda ya raunata biyu daga cikinsu kuma ya lakadawa daya daga cikin likitocin duka har sai da ya suma.

Rahotannin sun ce wani da yake jinya a asibitin ne ya kubatar da likitocin biyu daga hannun maralafiyan.

Lamarin ya sa ma’aikatan jinyar dakatar da aikinsu har sai gwamnati ta dauki matakin tabbatar da tsaron lafiyarsu, inda suka yi zanga-zanga rike da kwalaye domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda rayuwarsu ke cikin hadari da kuma rashin matakan tabbatar da tsaron lafiyarsu, abinda ya sa ayyuka suka tsaya cak har na wasu yan sa’o’i.

Shugaban kwamitin sulhu na gwamnatin jihar Ondo Opeyemi Oloniyo ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin kuma ya ce al’amura sun daidaita kuma ma’aikatan jinyar sun koma bakin aiki.

BBC ta tambayi Mr Opeyemi a kan matakin da gwamnat ta dauka game da korafe-korafen ma’aikatan sai ya ce “ba a fafe gora ranar tafiya, a hankali a hankali ake abubuwa.

Ma’aikatan jinya a Najeriya dai sun dade suna korafi game da yanayin da suke aiki, inda a wasu lokutan su kan shiga yajin aiki domin matsawa gwamnati lamba.

Ko kun san an bude kantin mutuwa a Najeriya?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kantin hirar mutuwa an yi shi ne a matsayin wurin da mutane za su je don rage radidin rashin da suka yi

An bude kantin hirar mutuwa na farko a birnin Legas da ke kudancin Najeriya.

Kantin, wani taro ne na wata-wata da mutane ke zama su ci kek, su sha shayi kuma su yi hirar mutuwa.

Mai kantin, Hope Ogbologugo ta ce yana taimaka wa mutane su kara kimar rayuwa.

A cewar Hope “Mutane na matukar tsoron yin maganar mutuwa, kamar idan suka yi maganar mutuwa to tabbas za su mutu. Amma ko mun tattauna batun mutuwa ko ba mu tattauna ba, ai za mu mutu.”

Ta ce kafin ta bude kantin mutuwar, wanda irinsa ne na farko a Afirka ta yamma ba ta iya magana a kan rasuwar mahaifiyarta. Ta ce, duk da dai har yanzu tana kukan mutuwar mahaifiyar, amma tana iya yin hirar mutuwar da mutane.

Kantin hirar mutuwa an yi shi ne a matsayin wurin da mutane za su je don rage radidin rashin da suka yi.

Wani ma’aikacin cibiyar raya al’adun Birtaniya, Jon Underwood ne ya kafa kantin hirar mutuwa na farko a 2011, amma sai dai an bude kantin ne a bara a Najeriya

An yi musayar ‘yan wasa da yawa ranar rufe kasuwar musaya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Everton da Fulham da kuma Leicester sun kashe makudan kudade wajen sayen ‘yan wasa yayin da aka rufe kasuwar musayar ‘yan wasan gasar firimiya da wuri kamar yadda ba a taba yi ba a tarihi.

Duk da haka, kudin da aka kashe a kasuwar musayar ‘yan wasan ya ragu a karon farko cikin shekara takwas zuwa fan biliyan 1.2.

Tottenham – wadda ba ta sayi ko wane dan wasa ba a wannan lokacin bazarar – da kuma Manchester United ba su sayi ko wane dan wasa ba ranar 9 ga watan Agusta, wato ranar karshe.

An matsar da ranar rufe kasuwar ne daga ranar 31 ga watan Agusta zuwa ranar jajiberin fara gasar Firimiya bayan kungiyoyin gasar sun kada kuri’a a kan batun.

Komawar Yerry Mina zuwa Everton kan kudi fan miliyan 27 daga Barcelona ita yarjejeniyar da ta kudi a ranar.

Wa’adin rufe kasuwar ya shafi kungigyoyin rukunin kasa da gasar Firimiya ta Ingila – duk da cewa wadannan kungiyoyin na da damar sayen ‘yan wasan da ba su da wata yarjejeniya da kuma damar daukar aron ‘yan wasa zuwa ranar 31 ga watan Agusta.

Kungiyoyin gasar Firimiya da wadanda ke rukunin kasa da su – duk da cewa ba gaba kidayansu ba ne – sun yarda cewa a rufe kasuwar ‘yan wasa da wuri don guje wa dagula lissafi a a makonnin farko na wannan kakar.

Sai dai, an samu wannan sauyin ne kawai a Ingila, inda kungiyoyin Spain da Jamus da kuma Scotland za su iya ci gaba da sayen ‘yan wasa zuwa karshen wannan watan.

Ranar karshe a Italiya ita ce ranar Juma’a, 17 ga watan Agusta – ranar jajibirin fara gasar Serie A.

‘Yan wasa za su iya barin gasar firimiya- inda rahotanni ke cewa Real Madrid tana hakon dan wasan Chelsea, Eden Hazard, duk da cewa idan aka sayar da shi the Blues ba za ta iya sayen wanda zai maye gurbinsa ba.

Yadda ake karkare ranakun rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a tarihi

Baya ga rufe kasuwar kwanaki kafin yadda aka saba rufe ta ba, an rufe ta ne karfe biyar na yamma (agogon Najeriya) maimakon karfe 11 (agogon Najeriya) da aka saba rufe ta.

Bisa ga dukka alamu an yi tunanin cewa wannan za ta kasance ranar rufe kasuwar mafi karancin harka tun da aka bude ta a shekarar 2003 – inda kungiyoyin gasar Firimiya suka tabbatar da yarjejeniyoyi takwas kafin karfe biyar.

A wancan lokacin dai yarjejeniya mafi kudi ita ce ta dan wasan tsakiya Mateo Kovacic wanda ya koma buga wasan aro a Chelsea daga Real Madrid – yayin da mai tsaron gida Thibaut Courtois ya koma Madrid bisa yarjejeniyar din-din-din.

Amma kungiyoyi sun samu karin sa’o’i biyu domin kammala rattaba hannu kan yarjejeniyo, a lokacin ne Everton ta sayi dan wasan bayan Colombia Mina da kuma dan wasan tsakiya Andre Gomes don buga wasa aro daga Barcelona – bayan ta sayi Bernard wanda ba shi da wani kwantiragi a kansa.

Fulham ta yi shelar ‘yan wasa biyar bayan an rufe kasuwar – sun hada da dan wasan tsakiyar Marseille Andre-Frank Anguissa a wata yarjejeniyar kudi fan miliyan 22.3 da dan wasan bayan Bristol City, Joe Bryan kan kudi fan miliyan 6 da Sergio Rico da Luciano Vietto da kuma Timothy Fosu-Mensah don buga wasan aro.

Wannan ya sa a zama kungiyar da ta kashe sama da fan miliyan 100 a lokacin bazara a kakar da ta samu shiga gasar Firimiya daga rukuni na kasa.

Kuma Leicester City ta tabbatar da sayen dan wasan bayan Freiburg da Turkiyya Caglar Soyuncu, a wata yarjejeniya wadda ta kai kudi fan miliyan 19.

Kafin wannan lokacin ta sayi dan wasan baya Filip Benkovic daga Dinamo Zagreb kan kudin da rahotanni suka ce ya kai fan miliyan 13.

Image caption

Sayayya 10 mafi girma da kungiyoyi suka yi a kasuwar musayar ‘yan wasan (bisa kudaden yarjejeniyoyin ta farko)

Wasu yarjejeniyoyin sun hada da komawar Danny Ings Southampton daga Liverpool don buga wasan aro wadda za ta zama ta din-din-din a lokacin bazara mai zuwa da komawar Jordan Ayew Crystal Palace daga Swansea.

Domin buga wasan kaka daya da kuma sayen da West Ham ta yi wa dan wasan Arsenal Lucas Perez da kuma dan wasan tsakiyar Fiorentina Carlos Sanchez.

Su wa suka yi asara a ranar karshe na kasuwar?

Wasu kungiyoyi shida ba su sayi ko dan wasa daya ba ranar Alhamis.

An baya da rahoton cewa Tottenham ce kungiyar gasar Firimiya ta farko wadda ta kasa sayen ko dan wasa daya a kasuwar lokacin bazara, duk da cewa koci Mauricio Pochettino ya ce shi bai karaya ba domin kananan ‘yan wasa biyu ne kawai suka bar kulob din.

Ya ce “Zai yi wahala mutane su gane abin da ya sa Tottenham ba ta sayi dan wasa ko daya ba, amma a wasu lokuta a wasan kwallon kafa kana bukatar ka fita daban, kuma mun gamsu da ‘yan wasan da muke da su.”

Manchester United ta sayi ‘yan wasa uku ne kawai a lokacin bazarar – da farkon watan Yuli.

Amma ta yi kokarin sayen dan wasan baya kuma ranar Lahadi Jose Mourinho ya ce suna fuskantar “kaka mai tsanani” idan ba za su iya sayen wani karin dan wasa ba.

An kuma alakanta kulob din da dan wasan Tottenham, Toby Alderweireld, da dan wasan Leicester, Harry Maguire, da kuma dan wasan Bayern Munich, Jerome Boateng, a lokacin bazara.

Kuma Red Devils sun nemi sayen dan wasan bayan Atletico Madrid, Diego Godin – amma ana tsammanin ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Spain.

Spurs ta kasance daya daga cikin kungiyoyi 14 da suka kada kuri’ar kan rufe kasuwar musayar ‘yan wasa da wuri a watan Satumbar bara, ita kuma United ta kuri’ar na ki ta kada.

Arsenal da Liverpool na daga cikin kungiyoyin da ba su saye ko dan wasa daya ba – amma ba a yi tsammanin su sayi ko dan wasa daya ba, bayan sun sayi wasu ‘yan wasa tun daga farkon lokacin bazarar.

Yaushe majalisar dokokin Najeriya za ta dawo zama?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An dai yi ta matsa lamba ga shugabancin majalisar dokokin Najeriya da su sake bude zauren majalisar domin yin nazari game da wasu muhimman batutuwa na ci gaban kasa.

Wani muhimmin abu da ake ganin ya kamata a duba cikin hanzari shi ne kasafin kudin zaben kasar na shekara ta 2019, wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar kafin ta tafi hutu.

A ranar Talatar da ta gabata ne majalisar dokokin Najeriya ta ce ta so ta zauna domin duba batun na kasafin kudin hukumar zaben kasar INEC.

Sai dai zaman bai yiwu ba, bayan da jami’an hukumar farin kaya DSS suka datse kofar shiga majalisar na wani lokaci.

Amma a ranar Alhamis, majalisar ta ce akwai yiwuwar za ta katse hutunta a mako mai zuwa domin yin nazari game da kasafin kudin zabukan na 2019, wanda aka kasa yi a ranar Talata.

Hakan kuwa ya zo ne bayan wata ganawa tsakanin shugabannin majalisar da shugaban hukumar zaben kasar INEC, farfesa Mahmood Yakubu.

Sanata Isah Hamma Misau, daya ne daga cikin wakilan kwamitin da ke kula da hukumar zabe a majalisar dattijai, kuma su ne za su duba kasafin kudin kafin majalisar ta amince da shi.

Ya ce akwai yiwuwar majalisar ta dawo daga hutu a mako mai zuwa, amma ba a tsayar da takamaimiyar ranar da hakan zai faru ba.

An kashe yara 29 a wani hari ta sama a Yemen


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan tawayen Houthisun ce mutum 43 ne suka mutu, sai dai kawancen na Saudiyya ya ce ba su taba kai hari kan fararen hula ba

Akalla yara 29 ne suka mutu wasu kuma 30 suka ji raunuka bayan wani hari ta sama da kawancen da Saudiyya ya kai Yemen, kamar yadda kungiyar agaji ta Red Cross ta bayyana.

Yaran da abin ya rutsa da su suna tafiya ne a wata motar bas a wata kasuwa da ke garin Dahyan, a arewacin lardin Saada.

Sai dai ma’aikatar lafiya wadda ‘yan tawayen Houthi ke tafiyar da shi, ta ce mutum 43 ne suka mutu, yayin da mutum 61 suka ji raunuka.

Kawancen, wanda Saudiyya ke jagoranta na da goyon bayan gwamnatin Yemen wadda ke yaki da ‘yan tawayen Houthi.

Sai dai kawancen sun ce suna da “hujjar kai harin.”

Sun ce ba su taba kai hari kan fararen hula ba, amma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi zargin cewa kawancen ya kai hare-hare a kasuwa da makarantu da gidaje.

Hukumar EFCC za ta ‘binciki’ Lawal Daura


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati za ta binciki tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Lawan Daura, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Batutuwan da za a masa tambayoyi a kai sun shafi yadda hukumar da ya jagoranta ta kashe naira biliyan 17 da ya gada daga tsohon shugaban hukumar Mista Ita Ekpeyong, a cewar rahotannin.

Ana kuma zargin Mista Ekpeyong da ya karbi Naira biliyan 20 daga babban bankin Najeriya a karshen mulkin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.

Rahotannin suna cewa Mista Ekpeyong ya canza Naira biliyan 17 zuwa dalar Amurka wanda ya bari a baitumalin hukumar lokacin da ya mika ragamar shugabanci ga Lawal Daura.

Har ila yau rahotannin sun ce jami’an hukumar EFFC sun bankado batun kudin ne bayan makudan kudin da suka kai dala miliyan 43 da aka gano a wani gida da ke Legas wanda ke da alaka da hukumar tattara bayanan sirri ta kasa, NIA.

Jami’an hukumar ta EFFC sun rika kokarin gudanar da bincike kan yadda hukumar DSS ta kashe kudin, sai dai sun yi zargin cewa tsohon shugaban hukumar da mukaddashin shugaban kasa ya sallama ya rika kawo cikas.

Jami’an hukumar EFFC sun yi zargin cewa Lawal Daura ya hana jami’an nasu kama tsohon shugaban hukumar DSS Ita Ekpeyong da kuma tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasa Ayo Oke a samamen da suka kai a ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2017.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar EFCC Wilson Uwajeren a kan lamarin, sai dai hakan bai cimma ruwa ba, domin an ce ba ya ofis.

Sai dai ya zuwa lokacin aka hada wannan rahoton, hukumar EFCCn ba ta musunta rahotannin ba.

A hukumance dai ba a bayyana wurin da ake tsare da tsohon shugaban hukumar ta DSS ba.

Kodayake rahotannin sun ce ana tsare da shi ne a sashin yaki da miyagun laifuka na hukumar ‘yan sanda.

Sai dai kakakin hukumar ‘yan sanda Jimoh Moshood ya shaida wa BBC cewa ba shi da masaniya game da wurin da ake tsare da shi.

A ranar Litinin ne mukadashin shugban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kori Malam Lawal Daura daga aiki sakamakon jami’an tsaron farin kaya da aka tura zuwa Majalisar Dokokin kasar ba tare da sannin fadar shugaban kasa ba.

Za a binciki Boris Johnson kan shaguben da ya yi wa hijabi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jam’iyyar Conservative ta fara binciken tsohon sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Boris Johnson saboda wasu kalaman batanci da ya yi.

Jam’iyyar ta karbi gomman koke-koke game da kalaman na tsohon sakataren harkokin wajen kasar game da mata masu sanya nikabi ko burka.

Wani kwamiti na musamman ne zai duba koken, wanda ka iya mika maganar zuwa ga babban kwamitin jam’iyyar, wanda ke da ikon korarsa daga jam’iyyar gaba daya.

Amma kawo yanzu jam’iyyar ba ta ce uffan ba game da binciken.

Wani kakakin jam’iyyar Conservative ya ce: “Ba a bayyana yadda binciken ke gudana sai bayan an kammala shi.”

Wani na kusa da Mista Johnson ya ki amincewa ya yi wani bayani kan batun.

Mista Johnson ya ki yarda ya bayar da hakuri ga mata Musulmi masu sanya burka, bayan da ya ce suna kama da “akwatin aika wasika” ko “‘yan fashi a banki.”

Ya kuma yi kira da a fitar da wata doka da za ta hana irin wadannan matan sa burka a Birtaniya.

Kun san wanda ya rasa ransa wajen ceto mutane a kogi a Fatakwal?


Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/JOE BLANKSON

Image caption

Joe Blankson and im wife Mercy plus dia son Owen wen im be two years old.

Mercy, matar marigayi Joe Blankson wanda ya rasa ransa bayan da ya ceto mutum 13 daga kogi, ta ce har yanzu tana ganin mutuwar mijin nata tamkar mafarki, kwana tara bayan jana’izarsa.

Mr Blankson ya samu yabo ta ko ina inda aka mayar da shi gwarzo sakamakon rasa ransa da ya yi a garin ceto mutane bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a kogi a jihar Fatakwal.

Mista Blankson ne kadai wanda ya rasa ransa a hatsarin jirgin ruwan da ya faru ranar Asabar 28 ga watan Yulin.

Matarsa Mercy ta shaida wa sashen Turancin Buroka na BBC cewa abin da mijinta ya yi bai ba ta mamaki ba, saboda ta san shi wajen son taimakon mutane.

“Mijina yana da kirki sosai… ya fi damuwa da taimakon wasu kafin kansa. Idan da zai ji ihun wani da karfe biyar na asuba, to zai iya fita shi kadai don ganin me yake faruwa,” in ji ta.

Ta ce ko a hanya Mista Blankson ya ga ana fada to yana iya tsayar da motarsa don ya je ya raba.

Blankson, mai shekara 38, ya auri Mercy shekara biyar da ta gabata, kuma suna da ‘ya’ya uku, amma babbar ‘yarsu ta rasu a watan Disambar 2016.

Hakkin mallakar hoto
Mercy Blankson/Facebook

Image caption

Mercy ta ce ta ga wasu alamu kafin mutuwar tasa

Mercy ta ce har yanzu ta kasa yarda cewa mijinta ya mutu saboda a wasu lokutan, sai ta ga kamar zai koma gida.

“Gidan babu dadi sam da baya nan,” in ji ta.

“Rannan ma haka dana Owen ya dauki jakarsa ya ce zai tafi Bakana neman babansa.”

Yadda mummunan labarin ya iske ta

A wannan bakar rana ta Asabar 28 ga watan Yulin 2018, yayin da Joe ya tafi aiki, ya shaida mata cewa daga wajen aiki zai wuce Bakan don halartar wata jana’iza.

Amma yayin da ta ga dare yana kara yi kuma Joe bai kirata ba kamar yadda ya saba, sai ta yi ta kiran wayarsa, amma sai ta ji ta a kashe.

Sai Mercy ta yi ta kiran abokan Joe amma dukkansu ba wanda ya iya gaya mata komai. Daga nan sai ta shiga damuwa.

Daga baya ne sai mahaifiyar Joe ta kirata ta shaida mata cewa kwale-kwale ya kife a Bakana kuma mijinta na ciki don haka sun tafi nemansa.

Sai ta ce mata tana fatan su same shi a raye. Sai ta tafi gidan surukarta inda ta iske dafifin mutane suna ta kuka, kuma suka ce mata ai ba a gan shi ba.

Hakkin mallakar hoto
Mercy Blankson/Facebook

Sai washegari ranar Litinin 30 ga watan Yuli ne sai matar wan mijinta ta shaida mata cewa ai Joe ya mutu bayan da wani masunci ya gano gawarsa na yawo a saman kogi.

Daga nan fa sai ta fara kuka.

Sai ta ruga zuwa bakin kogin Abonnema amma sai aka hana ta ganin gawarsa saboda tana shayarwa, kuma a bisa al’ada duk mutumin da ya mutu a cikin ruwa, to a ruwa ake binne shi.

Don haka ba ta san inda suka binne mijinta ba.

Mercy ta ce ta ga wasu alamu kafin mutuwar tasa.

Ta ce mako guda kafin mutuwar Joe, sun je wani waje don halartar liyafar murnar zagayowar ranar haihuwar makwabtansu.

Sai ta ce masa karo na karshe da ta zo wannan waje, washe gari aka yi wata gobara da ta yi sanadin mutuwar ‘yarsu ta fari, don haka jikinta na ba ta wani mummunan abu zai faru nan ba da jimawa ba.

Amma sai mijinta ya ce ta kwantar da hankalinta ba abin da zai faru. A wannan Asabar din kuwa sai Joe ya mutu.

Rayuwa bayan mutuwar Joe

Mercy ta ce tana fatan mutuwar Joe za ta sa gwamnati ta yi wani abu don kawo gyara a kogin Abonnema, don samar da kwararrun masu iyo da rigunan ruwa ga dukkan fasinjojin da ke hawa kwale-kwale.

Ta ce ya kamata a samu ‘yan sandan bakin ruwa da za su dinga lura da al’amuran zirga-zirga a kogin da kuma tsaftace kogin, ta yadda datti ba zai dinga makalewa a injinan kwale-kwalen ba da har zai jawo hatsari.

A yadda al’amura suke tafiya yanzu, Mercy ta ce gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya yi alkawarin tallafa wa karatun yaranta da kuma ba ta aikin gwamnati a jihar.

Ta ce yana da kyau a gina wani abu a Bakana don tunawa da mijinta wanda ya mutu saboda nan gaba idan yaranta suka tambaye ta inda aka binne babansu, sai ta nuna musu wannan gini a matsayin nan ne kushewar mahaifinsu.

Isra’ila na yi wa Falasdinawa luguden wuta a Zirin Gaza


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wata ta tashi lokacin da Israi’la ta kai wani harin sama

Rahotanni sun ce Falasdinawa uku sun mutu a wasu jerin hare-haren sama da Isra’ila ta kai Zirin Gaza, bayan da mayakan sa kai suka harba gomman rokoki kudancin Isra’ila.

Jam’ian ma’aikatar lafiya ta Gaza sun ce an kashe wata mai ciki da ‘yarta mai shekara daya a yankin Jafarawi.

Jami’an sun kuma ce wani mayakin sa kai na Hamas ya mutu.

Kafofin watsa labarai na Isra’ila sun ce fararen hula da dama sun mutu a harin rokar da aka harba Sderot da wasu garuruwan kusa da kan iyakar Gaza.

Rikicin na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya da Masar suka yi kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon lokaci tsakanin Isra’ila da Hamasa, wato kungiyar mayakan sa kai da ta mamaye Gaza.

Wakilin MDD a Gabas Ta Tsakiya Nickolay Mladenov ya ce “hankalinsa ya tashi sosai kan abun da ke faruwa.”

“Kokarin da muke yi shi ne ya sa lamarin bai munana fiye da haka ba har yanzu. Idan kuma har ba a samu damar shawo kan lamarin ba da gaggawa, to abun na iya munana ta hanyar mayar da martani daga bangarorin,” kamar yadda ya yi gargadi.

Bayan da Isra’ila ta mayar da martani tankar yaki, an harba gomman rokoki yankin Israi’a a ranar Laraba da daddare.

Kungiyar Hamas ta dauki alhakin kai hare-haren rokokin. A farkon makon nan ne aka kashe mayakan kungiyar biyu bayan da Isra’ila ta kai hari kan iyakar arewacin Gaza.

Rundunar Tsaron Isra’ila ta bayyana a shafinta na Twitter cewa jiragen yakinta sun kai hari wasu muhimman wurare 140, da suka hada da wajen kera makamanta.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An dauki hotunan rokokin da Hamas ta harba Birnin Sderot na Isra’ila

Wuraren ban sha’awa da za ku iya ziyarta a Najeriya


A yayin da ake hutun makarantu a Najeriya, a lokacin ne mutane da dama ke neman wajen zuwa domin shakatawa da iyalansu.

Abu daya da za ku saka a ranku shi ne kuna bukatar kashe kudi domin tafiya hutu.

Akwai wurare masu kyau a Najeriya inda za ku iya zuwa ku ga al’adu da yanayi kala-kala.

Wadannan wasu wuraren shakatawa ne da za ku iya zuwa tare da iyalanku a lokacin wannan hutun.

1. Gandun namun daji na Lekki da ke Lagos

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wannan gurin shakatawar yana Lekki ne a Legas kuma gurin ya kai shekaru 21 yana tashe.

Wurin ya kuma kunshi birai da masu neman tsokana. Za kuma ku ga dawisu – in har kun ci sa’a – zai iya bude maku gashinsa. AbIn da ya fi burge mutane a wurin shi ne wani rufin bishiyoyi da ya kasance mafi dadewa a Afirka.

2. Kajuru Castle a Kaduna

Hakkin mallakar hoto
Google

Kajuru Castle wani kasaitaccen gida ne da aka gina mai tsari irin na Turawa a garin Kaduna da ke Najeriya.

An gina kasaitaccen gidan tun shekaru 30 da suka wuce.

Dakunan gidan sun yi kama da kurkuku irin na zamanin da, kuma akwai wani rami da aka ajiye kada. Gidan na dauke da wurin ninkaya da na wankan sauna.

3. Gidan ajiye kayan tarihi na yaki da ke Umuahia

Hakkin mallakar hoto
Google

Idan kuna son sanin wani abu kan yakin basasa a Najeriya, wannan ne wurin da ya kamata ku je. Wannan gidan adana kayan tarihin na garin Abia, kuma yana da dakuna 3 da ake baza hotunan tarihi. Akwai kuma dakin adana hotunan yakin basasa, da na hotunan sojoji, da kuma na hotunan kayan tarihin yaki.

4. Gidan namun daji na Jos

Hakkin mallakar hoto
Google

Wannan gidan ajiye namun daji ne a garin Jos. Garin na daya daga cikin manyan garuruwa a Najeriya da ake ajiye namun daji daban-daban kamar giwaye, da zakuna, da birai, da kadduna, da kuma wasu namun dajin. Jos Wildlife Park na budewa ne daga ranar Litinin zuwa Asabar a kowane mako, daga karfe 9 na safe zuwa 5 din yamma.

5. Wajen shakatawa da wasan yara na Wonderland Amusement da ke Abuja

Hakkin mallakar hoto
Google

An bude wurin wasan yara na Wonderland a shekarar 2007.

Wannan shi ne babban wurin wasan yara a Najeriya kuma yana nan a daura da babban filin wasa na kasa a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Kuna bukatar ku cika cikinku kafin kuje wurin domin ku samu karfin iya hawan duka abubuwan wasan yaran da ke wurin.

6. Tafkin Oguta da ke Imo

Hakkin mallakar hoto
Google

A jihar Imo za a sami tafkin Oguta. Wanan wurin shakatawa ne da za ka iya zuwa ka yi hutu, kuma ba ka ma bukatar kudi da yawa domin aji dadi a wanan wurin.

Wurin shakatawar yana da abubuwan yi da dama na jin dadi da za ka iya yi da iyalanka kamar ninkaya, da yawo cikin kwale-kwale, da kuma buga wasan golf.

7. Gandun namun daji na Yankari a Bauchi

Hakkin mallakar hoto
Google

Wannan gandun namun daji ne a jihar Bauchi, kuma shi ne wurin da aka fi zuwa domin shakatawa a Najeriya.

Ba namun dawa ne kadai a wurin ba har da koramar ruwan dumi ta Wikki. Ku da iyalanku ko abokanku na iya kama daki domin kwana a wurin.

‘An kora mu cikin daji kamar shanu’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani da ‘yan fashi suka sace a Najeriya ya zanta da BBC, inda ya bayyana yadda aka tare su a kan hanya sannan aka kora su cikin daji bayan an yi masu fashi.

Mutumin wanda aka tare shi yayin da yake ka hanyarsa ta zuwa Gusau ya ce ‘yan fashin na amfani da wasu sautuka domin sadarwa a tsakanin su.

“Zan je Gusau, ina kan hanya kafin na kai Giwa, sai na ga mutane da kayan sojoji.”

“Sai muka ji an bude wuta ana ta harbi.”

“Suna cewa tsaya ko in harbe ka.”

A cewar mutumin, an tare motoci da dama a lokacin fashin, sannan an kwace masu kudade da wayoyinsu na hannu.

“Bayan an gama fashin sai suka kora mu cikin daji suna dukan mu.”

Ya tabbatar da cewa an kwashe kimanin minti talatin ana fashin ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.

Abin da ‘yan Najeriya ke fada game korar Daura


Hakkin mallakar hoto
.

‘Yan Najeriya suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da abin matakin da Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya dauka na korar shugaban hukumar DSS, Lawal Daura.

Da safiyar Talata ne dai wasu jami’an tsaro suka hana wasu sanatoci shiga majalisa, kodayake sun bari sun shiga daga bisani.

Al’amarin ya ba ta wa wasu sanatoci rai, abin da ya sa suka yi Allah-wadai da matakin.

Ana cikin wannan halin ne mukaddashin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya gana da Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, da kuma shugaban hukumar jami’an tsaron farin kaya (DSS), Lawal Daura.

Bayan wannan ganawar ne dai mukaddashin shugaban ya kori Daura daga aiki tare da yin tir da abin da jami’an tsaron suka yi a harabar majalisar dokokin kasar.

Da yammacin ranar Talatan ne dai aka bayar da sanarwar cewa mutumin da ya fi girman mukami a hukumr DSS bayan Daura, Matthew B. Seiyefa, shi ne sabon shugaban hukumar ta DSS.

Ga abubuwan da ‘yan Najeriya ke fada game da matakin da mukaddashin shugaban kasa ya dauka a shafin Twitter bayan an tambaye su kan ko ya dace Osinbajo ya tuntubi Buhari kafin ya kori Lawal Daura:

Da sanin Buhari aka kori Lawal Daura – Fadar shugaban Najeriya


Hakkin mallakar hoto
FEMI ADESINA

Image caption

A ranar Juma’a ne Shugaba Buhari ya fara hutun kwana 10 a Birtaniya

Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya ce kan Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a hade yake.

Femi Adesina ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake gana wa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta kasar wanda aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja ranar Laraba.

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya shugabanci taron.

Shugaba Buhari ya fara hutun kwana 10 ne a birnin Landan ranar Juma’a.

Bayan an kammala taron, manema labarai sun tambayi Mista Adesina ya fayyace musu ko Shugaba Buhari na da masaniya a kan korar da mukaddashin shugaban kasar ya yi wa shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Lawal Daura.

Mista Osinbajo ya sallami Lawal Daura ne bayan da wadansu jami’an hukumar DSS wadanda suke rufe fuskokinsu sun hana wadansu ‘yan majalisar kasar shiga zauren majalisar a ranar Talata.

Mista Adesina ya ce kawunan shugabannin hade yake kuma babu wata baraka tsakaninsu.

Ya bayyana cewa dukkan lokacin da shugaban kasa zai tafi hutu, ya kan mika ragamar mulki ga mataimakinsa.

Kuma daga lokacin mataimakin ya zama mukaddashin shugaban kasa mai cikakken ikon da shugaban kasa ke da shi.

Har ila yau, ya ce a wannan karon ma Sshugaba Buhari ya dauki wannan matakin na mika masa ragamar kasar.

A karshe ya ce akwai kyakkyawar fahimta tsakanin shugabannin biyu, kuma daukan wannan mataki da aka yi ba abu ne da za a iya tattauna shi a gaban manema labarai ba.

Saudiyya ta kirkiro manhajar kimanta wa’azi


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hukumomin Saudiyya na ciyar da Musulunci mai sassauci gaba

Hukumomi a Saudiyya na kirkirar wata manhajar wayar hannu wacce za ta sa ido kan wa’azuzzuka da addu’o’i a masallatai domin bai wa masu ibada damar sani idan mai wa’azi zai dade yana wa’azin.

Jaridar Al-Watan ta kasar Saudiyya ta ruwaito cewa Ministan harkokin musulunci na kasar Abdul Latif Al-Sheikh, ya bayyana cewa manhajar za ta bayar da damar sa ido a masallatai, kan tsawon lokaci da kuma ingancin wa’azuzzukan duk minti kuma duk dakika.

Ba a bayyana wanda zai rika sa idon ba, amma a na tunanin masu zuwa masallaci ko da yaushe za su iya kimanta mai wa’azin a wasu bangarori a harkar aikinsu.

A halin da a ke ciki, Saudiyya na duba batun kawo sauyi a koyarwar addini, kuma a na ci gaba da muhawara kan daidaita abubuwan da a ke wa’azi a kan su domin karakatar da mutane daga ra’ayin kasashen waje, ko na bangaranci ko kuma na kungiyar ‘yan uwa musulmi.

Ministan ya ce addini “ba fagen da za a rikita zukatan mutane ba ne, ko kuma a yi sagegeduwa da tsaro da zaman lafiyar kasar nan mai albarka ba”.

A shekarar 2014 ne hukumomin Saudiyya suka ayyana Kungiyar ‘yan uwa musulmi a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Yanzu ‘yan Saudiyya na iya kimanta ayyukan gwamnati a wayoyinsu na hannu

Don gina al’umma mai sassaucin ra’ayi

Jaridar intanet ta Sabq ta ruwaito cewar manhajar kimanta wa’azin ta zo ne ‘yan kwanaki bayan kaddamar da wata manhajar wayar hannu inda ‘yan kasar Saudiyya za su iya kimanta ko wani irin aikin gwamnati, daga kiwon lafiya zuwa wasanni da walwala.

An yi wa manhajar ta Watani lakabi da “manhajar wayar hannu da zata bai wa ‘yan kasar da mazauna kasar da baki damar kimanta ayyukan gwamnati, sannan su kimanta gamsuwarsu kuma su bayar da gudummawa ga kokarin da a ke yi na inganta ayyukan gwamnati”.

Da alama yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ke jagorantar sauye-sauyen da a ke yi a Saudiyya yanzu, wanda shirinsa na kawo sauyi a masarautar ya hada da dawo da “sassauci a addinin musulunci” da kuma al’umma.

Sai dai kuma, a wannan makon Saudiyyar ta ce za ta kori Jakadan Kanada kuma za ta dakatar da kawancen kasuwanci bayan da Kanadar ta bukaci a saki masu fafutukar kare hakkin dan adam a masarautar.

Abdirahim Saeed da Alistair Coleman su ka hada wannan rahoton.

Ba zan sauka daga mukamina ba —Saraki


Hakkin mallakar hoto
.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba.

A jawabin da ya yi wa manema labarai ranar Laraba bayan hatsaniyar da aka samu a majalisar dokokin Najeriya ranar Talata, Saraki ya ce zaben shi aka yi kafin ya samu kujerar, ba nada shi aka yi ba.

Saraki ya kara da cewa shi ba ya mutuwar son mulki kamar yadda mutane ke fada, yana mai karawa da cewar da zarar kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisarsa sun kada kuri’ar tsige shi zai sauka daga kujerarsa.

Ya ce babu kashin gaskiya a zargin da ake yi cewar ya hada baki da tsohon shugaban rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) wajen kitsa hatsaniyar da aka yi a majalisar dokokin kasar.

Mece ce makomar Pogba da Boateng da Kepa da kuma Courtois?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Paul Pogba

Dan wasan tsakiyar Manchester United dan Faransa Paul Pogba, mai shekara 25, ya shaida wa ‘yan wasan kungiyarsa cewar yana son ya bar Old Trafford zuwa Barcelona, in ji(Mail).

Pogba ya shaida wa United cewar yana son a kara masa albashi fan 200,000 a ko wane mako idan har ana son ya tsaya a kungiyar, in ji (Sun).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jerome Boateng

United tana fushi da ejen din Pogba, Mino Raiola, kan kokarinsa na yi wa dan wasan hanyar komawa Barcelona, in ji (Star).

United ta kasa sayen dan wasan bayan Bayern Munich Jerome Boateng. Dan kasar Jamus din mai shekara 29 ya kira kocin United, Jose Mourinho, kuma ya nuna godiyarsa game da sha’awarsa, amma ya sanar da shi cewar ba zai koma Manchester ba, in ji (Bild).

Sai dai kuma, Leicester City ta bai wa United sabon kwarin gwiwa na sayen dan wasan bayan Ingila Harry Maguire, mai shekara 25, ta hanyar sayen sabbin ‘yan wasa baya biyu. Dan wasan Croatia Filip Benkovic, mai shekara 21, ya yi gwaje-gwaje kafin ya koma kulob din daga Dinamo Zagreb kan kudi fan miliyan 13.5. Kuma yarjejeniyar fan miliyan 22.5 na dan wasan Freiburg dan kasar Turkiyya, Caglar Soyuncu, mai shekara 22, ta kusa nuna, in ji (Mirror).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kepa

Golan Athletic Bilbao Kepa, wanda ke gab da komawa Chelsea kan kudi fan miliyan 71.5, saura kiris ya koma Real Madrid watan Janairu kan kudi fan miliyan 17.9. Dan kasar Sfaniya din mai shekara 23 zai kasance mai tsaron gida da ya fi kwarewa a lokacin da ya koma Stamford Bridge, in ji (Guardian).

Kepa zai tafi Landan domin kammala yarjejeniyar komawarsa Chelsea lamarin da zai sa albashinsa na shekara ya karu wanda a halin yanzu ya kai fan miliyan 3.58, in ji AS

Kepa zai maye gurbin dan wasan Belgium Thibaut Courtois, wanda yake da kwarin gwiwar cewar kin komawarsa Chelsea domin atisaye zai sa ya samu ladar komawa Real Madrid. Kungiyar ta Sfaniya ta shirya domin barin dan wasan tsakiyar Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 24, ya koma Stamford Bridge buga wasan aro a matsayin wani bangare na yarjejeniyar, in ji Telegraph.

Real Madrid za ta maye gurbin Kovacic da Thiago Alcantara ko kuma Miralem Pjanic. Dan wasan tsakiyar Bayern Munich dan kasar Sfaniya Alcantara zai kai fan miliyan 54, yayin da dan wasan tsakiyar Juventus dan kasar Bosniya Pjanic zai kai fan miliyan 72, in ji (AS – in Spanish).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tiemoue Bakayoko

Courtois, mai shekara 26, yana fuskantar tara ta fan 200,000 daga Chelsea domin kauracewa atisaye, in ji Mail.

AC Milan na kan tattaunawar sayen dan wasan tsakiyar Chelsea dan kasar Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 23, domin buga wasan aro, in ji (Sky Sports).

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kurt Zouma

Tottenham ta taya tsohon dan wasan tawagar ‘yan kasa da shekara 21 ta Ingila Jack Grealish, mai shekara 22 kan kudi fan miliyan 25 ranar Talata, kuma suna jiran sakamako daga Aston Villa, in ji(Telegraph).

Everton tana da kwarin gwiwar sayen dan wasan Chelsea dan kasar Faransa Kurt Zouma, mai shekara 23, domin buga wasan aro, in ji (Mirror).

Yadda ‘yan mata ke zama ‘yan kwallo don gujewa auren wuri a Kenya


Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon.

Wasan kwallon kafa a arewacin kenya na tainakon daruruwan ‘yan mata kaucewa auren wuri da samun ciki da wuri da kuma kaciyar mata.

Wannan labari na daga cikin labaran shirin Kirkira na BBC, wato BBC Innovators wanda Gidanuiyar Bill and Melinda Gates ta dauki nauyin kawowa.

APC ta goyi bayan hana sanatoci shiga majalisa


Jam’iiyyar APC mai mulkin Najeriya ta goyi bayan matakin da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka dauka ranar Talata na hana sanatoci shiga majalisar dattawan kasar.

Hakkin mallakar hoto
@lorghenkwange

Wata sanarwar da mukaddashin kakakin jam’iyyar, Yekini Nabena, ya fitar ta ce binciken da jam’iyyar ta gudanar ya gano cewar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya shirya tayar da hankali domin hana yunkurin tsige shi.

Ta kuma ce da ba don jami’an tsaro ba, da an yi tashin hankali da ka iya haddasa salwantar rayuka a majalisar.

Sai dai kuma Saraki ya ce babu hujjar kai jami’an tsaro majalisar dokokin kasar domin su musguna wa ‘yan majalisa.

Da safiyar Talata ne dai wasu jami’an tsaro suka hana wasu sanatoci shiga majalisa, kuma suka kyale su shiga daga baya.

Wannan lamarin dai ya bata wa sanatocin rai, lamarin da ya sa suka yi Allah-wadaran matakin.

Ana cikin wannan halin ne mukaddashin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya gana da Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, da kuma shugaban hukumar jami’an tsaron farin kaya (DSS), Lawal Daura.

Bayan wannan ganawar ne dai mukaddashin shugaban ya kori Daura daga aiki tare da yin tir da aikin da jami’an tsaron suka yi a majalisar dokokin kasar.

Da yammacin ranar Talatan ne dai aka bayar da sanarwar cewar mutumin da ya fi girman mukami a hukumr DSS bayan Daura, Matthew B. Seiyefa, shi ne sabon shugaban hukumar ta DSS.

Hakkin mallakar hoto
Bukola Saraki/Facebook

Image caption

Rahotanni sun ce cikin ‘yan kwanakinnan an yi ta matsa wa Bukola Saraki ya kira zaman majalisar na gaggawa

A sanarwar da APC din ta fitar ranar Laraba, ta yi zargin cewar Saraki ya kai ‘yan bangar siyasa majalisar kuma saura kiris ‘yan bangar su kashe dan majalisar wakilai na APC daya tilo da ya je majalisar, E.J. Agbonayinma, da ba don taimakon jami’an tsaro ba.

Jam’iyyar ta kuma nemi sanin dalilin da ya sa shugaban majalisar dattawa ya kira taron ‘yan majalisa domin dakile yunkurin wasu ‘yan majalisa na tsige shi.

Ta kuma ce abin mamaki ne cewar ‘yan majalisar jam’iyyar PDP ne kawai suka je majalisar tun karfe bakwai na safe, yayin da ‘yan majalisar APC ke zama game da halin da kasa ke ciki a wani wuri daban.

Jam’iyyar ta nemi hukumomi su yi bincike kan abubuwan da ta gano tare da kira ga Saraki ya sauka daga kujerar shugaban majalisar dattawan nan take.

An jima ranar Laraba ne dai Saraki din zai gabatar da jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin kasar.

‘Buhari bai ce a tsige Saraki ba’


Fadar gwamnatin Najeriya ta nesanta kanta daga matakin da jami’an tsaron farin kaya wato DSS suka yi na datse babbar kofar shiga majalisar dokokin kasar.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan ayyukan Majalisar wakilai, Abdurrahman Kawu Sumaila ya musanta cewa bangaren zartarwa na da hannu a wani yunkuri da ake ta yadawa na kokarin tsige shugaban Majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki daga kan mukamin sa.

Ya ce matakin da mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya dauka na korar shugaban DSS Lawal Daura, na nuna cewa matakin da jami’an tsaron suka dauka na hana sanatoci shiga majalisar, gaban kansu suka yi.

Jami’ai sun ce gobarar daji a California ta Amurka za ta ci gaba da ci har karshen wata


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jami’ai a ranar Talata sun ce ana sa rai gobarar daji mafi muni da ke addabar jihar California da ke kasar Amurka za ta ci gaba da ci har zuwa karshen watan Agusta.

Tuni dai gobarar ta lakume filin da ya kai girman eka 290,692.

Sashin kula da dazuka da kariya daga wuta ya ce yanzu haka akwai wuraren da aka kange wutar daga bazuwa.

‘Yan kwana-kwana na kokarin kashe bakunan wuta 18 da ke ci, yayin da ake fama da iska mai karfi.

A ranar Litini aka ayyana wutar a matsayin mafi muni a tarihin jihar ta California.

A baya dai masu aikin kashe gobara sun yi hasashen cewa za su iya kawo karshen wutar dajin zuwa tsakiyan watan Agusta, amma yanzu sun ce abin zai kai su har farkon watan Satunba.

Akalla ‘yan kwana-kwana 14,000 suke aikin kashe wutar dajin.

Har yanzu dai ba a san sanadiyyar tashin wutar ba.

Amma wani kaulin na cewa sacewar tayar wata mota ce ya haifar da wutar.

Bayanin ya nuna cewa gare-garen tayar wata mota da ya rinka gurzar kwalta a ranar 23 ga watan Yuli ne sanadiyyar tashin wutar.

An nada sabon shugaban hukumar DSS


Hakkin mallakar hoto
Facebook/Nigeria Presidency

Image caption

Seiyefa wanda dan jihar Bayelsa ce, ya gana da mukaddashin shugaban a fadar shugaban kasa da ke Abuja

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya umarci mutumin da ya fi mukami a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Matthew B. Seiyefa ya maye gurbin Lawal Daura, wanda aka sallama daga aiki ranar Talata.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta shafinta na Twitter.

Hakazalika rahotanni a kasar suna cewa mukaddashin shugaban yana ganawa da sabon shugaban hukumar.

Rahotanni sun ce, Mista Seiyefa, mutumin da ya fito daga jihar Bayelsa, ya isa fadar shugaban kasar ne da misalin karfe 4 yamma rike da wasu takardu a hannunsa.

A ranar Juma’ar da ta ne Shugaba Muhammadu Buhari ya fara hutun kwana 10 a kasar Birtaniya.

Abin da ya sa mataimakinsa yake jan ragamar kasar a matsayin mukaddashin shugaba.

Burnley ta sayi golan Manchester City a kan fam miliyan 3.5


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ingila ba ta je da golan gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha ba

Burnley ta sayi golan Manchester City Joe Hart a kwantaragin shekara biyu a kan fam miliyan 3.5.

Shugaban kungiyar Sean Dyche ya sayi golan ne tare da saurarn gololi biyu wato Nick Pope da Tom Heaton.

Hart, wanda ya yi wa kasar Ingila wasanni 75, ya kuma yi wa City wasanni 350, inda suka lashe kofin Firimiya biyu da kuma Kofin FA daya.

Golan ya fara nuna sha’awar barin City ne tun bayan da Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya rika ajiye shi a benci.

Sau daya Hart ya kama wa City gola tun bayan da Guardiola ya zama kocin kungiyar a shekarar 2016.

Ya kuma kwashe kaka biyu a matsayin aro a kungiyar Torino da kuma West Ham.

Hakazalika kasar Ingila ba ta je da shi gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha a shekarar 2018.

Yadda girgizar kasa ta riske mutane a masallaci a Indonesiya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu masallacin da ke da koriyar kubba a arewacin Lombok ya zama baraguzai

Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane a buraguzan masallacin da ya rushe a tsibirin Lombok da ke kasar Indonesiya, bisa fargabar da ake yi cewa akwai wasu mutane da suka makale a ranar Lahadi bayan da akai girgizar kasa.

Girgizar kasa da ta kai maki 6.7 ta kashe kusan mutum 100 kuma ta sa mutane 20,000 sun rasa matsugunansu.

Masallacin na daya daga cikin dubban gine-ginen da suka ruguje a arewacin Lombok.

Hukumar ceto ta Indonesiya ta ce an ceto mutum biyu daga cikin baraguzan ginin.

Girgizar kasar ta faru ne ranar Lahadi lokacin da ake sallar Isha.

Wani ganau ya sahida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa a lokacin akwai kusan mutum 50 a cikin masallacin Jabal Nur da ke nan kauyen Lading-Lading.

Kelana dan shekara 53 ya ce Limaminsu ya gudu ana sallah sai sauran mamu ma suka bi shi.

An samo gawarwaki guda uku da suka rudiddige a cikin baraguzan masallacin.

Mai magana da yawun hukumar ceto Sutopo Purwo Nugroho, ya ce an tsinci takalma da yawa a kofar masallacin, hakan ya sa ake tsoron ko za a samu wasu gawarwakin.

Ya yada hoton bidiyon wani mutum ana ciro shi daga karkashin ‘baraguzan gine-gine.

Tsibirin Lombok ya kai kimanin murabba’in kilomita 4,500 wanda yake gabashin Tsibirin Bali.

Tasirin girgizar kasar da aka yi wannan Lahadin ya fi wanda akai a Lombok makon da ya gabata inda mutane 16 suka rasa rayukansu.

Hukumomi sun ce wadanda suka mutu sun kai 98 amma jami’ai sun yi amanna cewa adadin na iya karuwa. Galibin mutanen sun rasa rayukansu ne bayan da baraguzan gini ya fado musu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu ceto na leken karkashin ‘baraguzan masallacin

Masu ceto sun ce yanzu abin da ya fi masu muhimmanci shi ne su samar wa marasa matsuguni wurin zama, saboda har yanzu fargaba ba ta saki mutanen da ke wajen ba.

A babban birnin Lombok Mataram, ma’aikatan asibiti na kokarin ganin sun kula da wadanda suka ji rauni a asibitocin da suka rushe. Sun koma kula da mutane a waje.

Amma kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akwai wani abun al’ajabi da ya faru a lokacin ibtila’in.

Ma’aikatan kungiyar sun tainakawa wata mata mai shekara 38 ta haihu a wata cibiyar kula da marasa lafiya ta wucin gadi a ranar Litinin.

Daya daga cikin sunayen da matar ta sanyawa ‘yar tata shi ne “Gempa” wanda yake nufin girgizar kasa a yaren Indonesiya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan hoton na nuna yadda ake mayar da marasa lafiya a Mataram waje karkashin tanti da aka kafa

A lokacin da girgizar kasar ta auku Philipa Hodge na Otal din Katamaran da ke nan arewacin Mataram. Ta fadawa BBC cewa wuta ta dauke sai kuma aka shiga rudani a wajen.

“Mutane na ta turereniya don su samu su fita a wurin, kuma gilasai suka farfashe. Sai muka ji baraguzai na fado mana.

Ban ga saurayina ba amma ina ta kiran sunansa. Daga baya dai sai muka ga juna kuma akwai jini a fuskarsa da rigarsa.

Man Utd za ta sake taya Alderweireld, Arsenal na zawarcin Welbeck


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Toby Alderweireld

Manchester United ta sake taya dan wasan bayan Tottenham,mai shekara 29, Toby Alderweireld, in ji (Mirror).

Chelsea za ta biya fam miliyan 89 kan Jan Oblak na Atletico Madrid domin sayen golan Sloveniyar, mai shekara 25, inda zai maye gurbin mai tsaron gidan Belgium, mai shkeara 26, Thibaut Courtois, wanda ya shirya domin koma wa Real Madrid, kamar yaddaMundo Deportivo. ta bayyana.

A maimakon haka kuma, Chelsea za ta yi kokarin sayen golan Stoke, mai shekara 25, Jack Butland, idan Courtois ya tafi, a cewar (Sky Sports).

Chelsea tana nazari kan sayen Butland kan kudi fam miliyan 25, kamar yadda jaridar (Star)ta ruwaito.

Image caption

Victor Wanyama

Roma tana zawarcin dan wasan tsakiyarTottenham dan kasar Kenya, Victor Wanyama, mai shekara 27, kamar yadda jaridar La Repubblica, ta bayyana.

Fulham ta son sayen dan wasan bayan Belgium, Dedryk Boyata, amma Celtic ba ta son sayar da shi, in ji jaridar (Mail).

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan Ingila, mai shekara 27, Danny Welbeck, kamar yadda jaridar (Evening Standard) ta ruwaito.

Dan wasan tsakiyar Croatia, Luka Modric, mai shekara 32, yana tunanin barin Real Madrid domin kwadayin yarjejeniya mai maiko daga Inter Milan, in ji(La Sexta – in Spanish).

Shugaban kungiyar Lyon Jean-Michel Aulas ya ce dan wasan bayan Barcelona,mai shekara 23, Yerry Mina yana son koma wa kulob din na Faransa, duk da cewa rahotanni na cewa dan wasan na kasar Colombia ya shirya domin komawa Everton, kamar yadda(Liverpool Echo) ta ce.

Manchester United na shirin zawarcin dan wasan Lazio Sergej Milinkovic-Savic, a cewar (Calciomercato).

Dan wasan Real Madrid Mateo Kovacic ya ki zuwa atisaye a wani yunkuri na take-takensa don barin kungiyar, in ji (Marca).

Burnleyta shirya sayen dan wasan Stoke Peter Crouch, kamar yadda jaridar (Sun) ta ruwaito.

Jami’an tsaro sun hana sanatoci shiga majalisa


Hakkin mallakar hoto
@lorghenkwange

Image caption

‘Yan majalisar dattawan Najeriyar dai suna son gudanar da wani taron gaggawa ne

Jami’an tsaron Najeriya na farin kaya (DSS) sun hana wasu ‘yan majalisar dattawan kasar shiga zauren majalisar da safiyar Talata.

Jami’ian, da suka ce sun tare hanyar shiiga zauren ne bisa umarnin da aka ba su ‘daga sama’, sun kyale ‘yan majalisar sun shiga zauren majalisar daga baya.

Rahotanni dai suna zargin cewar hana ‘yan majalisar shiga na da alaka da yunkurin tsige shugaban majalisar, Bukola Saraki.

Wasu ‘yan majalisar dake jam’iyyar APC suna ganin ya kamata Saraki ya yi murabus daga mukaminsa tun da dai ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai kuma wasu ‘yan jam’iyyar PDP suna ganin bai kamata Saraki ya sauka daga mukaminsa ba.

Hakkin mallakar hoto
Bukola Saraki/Facebook

Image caption

Rahotanni sun ce cikin ‘yan kwanakinnan an yi ta matsa wa Bukola Saraki ya kira zaman majalisar na gaggawa

Daliban arewacin Najeriya sun yi bajinta a Afirka


Hakkin mallakar hoto
Muhammad Ibrahim Jega

Image caption

Daliban uku dai sun fito ne daga Jihar Kaduna ta arewacin Najeriya

Daya na karatu ne a Jami’ar Abuja; biyu kuma a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Amma daliban uku – Fatima Auwal Aliyu, da Peter Balarabe, da Salisu Yusuf Bako – sun yi tarayya a wasu abubuwa: dukkansu ‘yan arewacin Najeriya ne, kuma Kimiyyar Kwamfiyuta (Computer Sceince a Turance) suke karantawa a jami’a, kuma dukkansu suka hadu suka kirkiri wata manhajar wayar salula.

“Mutum zai iya amfani da wanna manhaja a wayarsa ta salula ya kunna abubuwan da ke cikin gidansa, kamar su fanka, kamar su talabijin, kamar su soket haka.”

Mutum daga wayarshi a hannunsa zai iya kunna wadannan abubuwa”, in ji Fatima.

Wannan manhaja dai za ta yi aiki ne a kan waya komai-da-ruwanka mai amfani da tsarin Android ko iOS.

A cewar Salisu, “Idan muka sa maka ita a wayar salularka, sannan akwai na’ura da muka hada wadda za mu saka maka a gida. To da wannan manhajar da na’urar ne za ka rika kunnawa da kashe duk kayan da kake so.”

Image caption

Za a iya amfani da manhajar a wayar salula a kashe ko a kunna fitilun lantarki ko fanka ko talabijin

Hikimar kirkirar wannan manhaja dai, inji Peter, “Mun yi tunani ne na yadda za mu saukaka wa ‘yan Afirka – musamman ‘yan Najeriya – rayuwa.”

Sai dai kuma su biyu ne suka fara wannan tunani, kafin Fatima ta shigo cikinsu a yi tafiyar da ita, tun da a cewarta, “in dai har ra’ayoyin mutane suka zo daya, haduwa a yi irin wadannan abubuwa ba ta wahala”.

Kafin zuwan Fatima dai, jami’an kungiyar Startup Arewa mai karfafa wa matasan arewa gwiwa sun rungumi harkar fasahar kirkire-kirkire ne suka fara tuntubar su.

Ko da yake shida daga cikin kasashe 10 da aka yi amannar tattalin arzikinsu na bunkasa cikin hanzari a duniya a Afirka suke, nahiyar ce koma-baya ta fuskar bunkasa harkar kula da lafiya da kula da bukatun nakasassu.

Don haka ne wata gasa da aka saba gudanarwa duk shekara a kan kirkirar butunbutumi (wato robot a Turance), Pan African Robotics Competition, ta kalubalanci daliban nahiyar su kirkiri fasahohin da za su taimaka wajen inganta harkar kula da lafiya da rayuwar nakasassu.

Ko da jami’an Startup Arewa suka rungumo wannan kalubale suka ce wa Salisu da Peter “kule!”, daliban ba su bata lokaci ba suka ce “cas!”

“Da labarin wannan gasa ya zo mana, sai suka ce suna so ne mu kirkiri wata na’ura da za ta saukake rayuwar mutanen da ke fama da matsalar gani ko wadanda ba sa iya tafiya. Da ma muna tunnain yin wani abu irin haka, to sai muka ga ga dama ta samu”, inji Salisu.

Hakkin mallakar hoto
Muhammad Ibrahim Jega

Image caption

Daliban na aiki da kungiyar Startup Arewa don ganin wannan manhaja tasu ta yadu

Sai dai wani hanzari ba gudu ba: a cewar shugaban kungiyar ta Startup Arewa, Muhammad Ibrahim Jega, akwai bukatar a samu mutum na uku da zai shigo a yi tafiyar da shi, kuma kamata ya yi a samu mace.

Don haka aka tuntubi Fatima, wadda da ma tana sha’awar irin wadannan abubuwa, ta kuma amsa.

Daga karshe dai daliban sun shiga jerin wasu kungiyoyin dalibai biyu wadanda suka hadu suka wakilci Najeriya a gasar wadda aka gudanar a Senegal a karshen watan Yuli.

Wannan manhaja da wadannan dalibai suka kirkiro ce dai ta zo ta hudu a karshen gasar – kuma yanzu haka suna aiki tare da kungiyar Startup Arewa don ganin an samu masu zuba jari an yawaita na’urar da manhajar saboda mutane su amfana.

Ebola ta zama alakakai a Congo


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukomomin lafiya a jamhuriyyar demokuradiyyar Congo sun fara shirin tunkarar yaki da cutar Ebola wacce ta sake bulla a kasar kuma yanzu ke ci gaba da barazana ga rayukan jama’a.

Mutune sama da 43 aka ruwaito sun kamu da cutar yayin da alkalumman farko na ma’aikatar lafiya a kasar suka ce mutane 30 sun mutu.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce za ta tura tawagar likitoci zuwa yankin arewa maso gabashi kusa da iyaka da Uganda inda cutar ta sake bulla.

Jami’an lafiya sun fara sanya allurar riga-kafin cutar a cikin firji domin sanyaya maganin.

Ma’aikatar lafiyar ta ce a ranar laraba take fatan jami’anta za su fara aikin yaki da cutar.

An dai yi nasarar gwajin rigakafin maganin wanda wani kamfanin hada magunguna na Macrk ya samar.

Kuma gwamnatin kasar ta ce tana da sama da 3000 na rigakafin maganin da ta ajiye a Kinshasa, wanda ke bukatar a jiye shi wuri mai sanyi da kankaara

Babbar matsalar da jami’an lafiya ke kokawa shi ne makwanni kalilan allurar ke yi a ajiye ba tare da an yi amfani da ita ba.

Ghana ta sallami ministan makamashi daga bakin aiki


Image caption

Tun a lokacin yakin neman zabe, jam’iyya mai mulki ta sha alwashin kawo karshen Ameri deal

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Adoo ya sallami ministan makamashin kasar daga bakin aiki.

Wani bayani daga fadar shugaban kasa ya kara da cewa an umarce shi da ya mika mukamin sa hannun ministan filaye da ma`adinan kasa wanda zai yi rikon kwarya kafin a nada sabon ministan.

Sallamar ministan makamashin Mista Boakye Agyarko ta fara aiki nan take ne bayan fitowar ta a Cikin wata gajeriyar sanarwa, dauke da rattaba hannun daraktan sadarwa na fadar shugaaban kasa Mr Eugene Arhin.

Shugaba Nana Akufo Adoo ya bukaci ministan ya mika ofishin sa ga ministan filaye da ma`dinai Mr Peter Amewu wanda zai yi rikon kwarya kafin a nada wani sabon ministan makamashin.

Duk da yake babu wani dalili da aka bayar na sallamar ministan daga aiki, amma masu sharhi na zargin hakan baya rasa nasaba da yarjejeniyar makamashi ta Ameri Deal, wadda aka shiga tun lokacin tsohowar gwamnatin NDC, wadda kuma jam`iyya mai mulki ta NPP ta yi ta suka tare da cin alwashin soke ta da zarar ta hau mulki.

Ministan makamashin ya fara shan matsin lamba ne tun bayan da yayi ikirarin yunkurin sake sabunta yarjejeniyar ta AmeriI deal hujjar cewa tafi wacce aka kulla a baya.

Sai dai wasu manyan jami`an hukumar samar da makamashi Volta River Authority tayi gardamar cewa,ikirarin da ministam yayi na kebewa Ghana dala miliyan hudu saboda sabunta yarjejeniyar bashi da tushe bare makama.

A cewar su, idan majalisar dokoki ta amince da yarjejeniyar zata iya janyowa kasa asarar kudi dala milyan 472

Yayin da wata wasikar da ake zargin ta fito ne daga kamfanin Ameri ta mamaye shafukan sada zaumunta, da ta musanta cewa kamfanin yasan da maganar sake sabunta yarjejeniyar Ameri da aka rattabawa hannu 2015 lokacin tsohuwar gwamnatin NDC.

Hanyoyi biyar na yaki da shan miyagun kwayoyi


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli bidiyon yadda matasa ke rububin shan Codeine

Wani bincike da BBC ta gudanar kan sayar da magungunan rage radadin ciwo ba a bisa ka’ida ba ya janyo sauye-sauye a Najeriya da makwabtan kasashe.

Cikin sa’o’i 24 da yada binciken sashen musamman na Africa Eye, wanda ya bankado yadda mutane a wasu manyan kamfanonin sarrafa magunguna a Najeriya ke siyar da magungunan tari masu dauke da sinadarin Codeine daga kamfanonin zuwa masu sayar da magunguna, aka haramta sayar da maganin.

Ga wasu abubuwan da suka faru tun bayan yada shirin talabijin na musamman mai suna Sweet Sweet Codeine a watan Mayu.

1. An mayar da miliyoyin kwalabe kamfani

Fiye da kwalaben maganin tari mai dauke da sinadarin Codeine miliyan 2.4 ne gwamnatin kasar ta mayar kamfani daga kasuwa.

Image caption

Jami’an yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya na duba wani maganin tarin mai dauke da Codeine da aka kwace a Kano

Wannan babbar nasara ce ga masu yaki da shan miyagun kwayoyi kuma babbar asarar kudi ga kamfanonin sarrafa magunguna, wadanda a da suke siyar da kwalbar magani guda har naira dubu uku wato dala takwas ko kuma fan shida.

A baya gwamnati ta yi kiyasin cewa a na shanye sama da kwalaben maganin tari mai dauke da Codeine miliyan uku, wanda kuma ke haifar da lalacewar kayan ciki idan aka fiye amfani da shi, kulli yaumin a jihohi biyu.

Da zarar an kammala mayar da kwalaben, gwamnatin Najeriya za ta tattara tarin miyagun kwayoyin da kudinsu zai kai miliyoyin fama-famai.

Har yanzu dai ba a san yadda za su zubar da shi ba, duk da dai an kona maganin da yawa da aka kwato daga kasuwar bayan fage.

2. Kamamasu tserewa

An kama gwamman mutane tun bayan da gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da maganin tari mai dauke da Codeine da yawansu masu sarrafa magunguna ne da kuma kananan ‘yan kasuwa.

A wani farmaki da a ka kai a jihar Kwara, wanda babban jigo ne binciken na BBC, mutane 17 aka kama suna kokarin fasa kwaurin kwalaben maganin a Kaduna. A wasu jerin farmaki da aka kai a Katsina, daliban jami’a 21 ne aka kama da kwalabe 128 na Codein.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta karkatar da kayan aiki zuwa iyakar Kamaru domin hana mutane fasa kwaurin kodin zuwa kasashen waje.

Image caption

Chukwunonye Madubuike, tsohon ma’aikacin kamfanin sarrafa magunguna na Emzor ya tsere

An bayar da odar kama Chukwunonye Madubuike, tsohon mai kula da ci gaban kasuwanci a kamfanin sarrafa magunguna na Emzor wanda aka tona wa asiri a binciken BBC amma har yanzu ba a san inda ya ke ba. Amma kamfanin Emzor ya kore shi daga aiki.

3. Haramtawa a Ghana

Shirirn na musamman na yin tasiri a sauran kasashen Afirka.

Jim kadan bayan da BBC ta bankado kasuwar bayan fagen siyar da magungunan Codeine da kamfanonin sarrafa magunguna a Najeriya, hukumar sarrafa magunguna ta Ghana ta kaddamar da wani bincike kan amfani da Codeine ba a bisa ka’ida ba, har ma da wani maganin kashe radadin ciwon, Tramadol.

Image caption

An kai farmaki otel-otel a Najeriya inda aka kwace kwalaben magungunan tari

Binciken ya yi bitar shagon saida magunguna 35 kuma ya gano cewa ana shan magungunan a birnin Kumasi.

A watan Yunin shekarar 2018, cikin wani shiri da kasar ta shirya na bitar manufofin magunguna, Ministn Lafiya Kwaku Agyeman-Manu ya sanar da cewa za a haramta samarwa da shigar da kodin daga Ghana.

4.Nunawa a bainar jama’a

Jama’ar gari da kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da nuna bidiyon Sweet Sweet Codeine a fadin Najeriya, inda yake janyo hankulan jama’a.

Wani rahoto na majalisar dattawan Najeriya ya ce ana shan miyagun kwayoyi ya fi shafar mata matasa.

A arewacin Najeriya inda mafi rinjaye Musulmi ne, an haramta shan giya kuma maganin tari ya zamo abin mayen da ake tu’ammali da shi.

Fiye da mata 2,000 sun halarci taron nuna shirin na musamman a Keffi, arewacin Najeriya a watan Yuni.

A lokacin wani taron nuna shirin a Kaduna a ranar 29 ga watan Yuli, sama da daliban jami’a 4,000 ne suka taru domin kallon shirin kuma suka tafka muhawara kan yadda za a magance matsalar shaye-shayen kwayoyi.

Mairo Mandara, tsohuwar wakiliyar gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, ta shirya irin wadannan tarukan a lokuta da dama kuma tana jagorantar yaki da kawo karshen shan Codeine a kasar.

Image caption

Masu fafautuka na so su zaburar da mata matasa ga hadarin maganin tari

Ta ce binciken Africa Eye ya taka muhimmiyar rawa wajen zaburar da kasar kan yaki da magungunan rage radadin ciwo.

“Sweet Sweet Codeine ya kasance kololuwa a kamfe din mu na haramta shan maganin tari mai Codeine a Najeriya,” kamar yadda ta ce.

“Tun da aka haramta shan maganin, akalla mata da yara mata da maza sun kira ni su a neman taimako.

“Har yanzu mu na nuna shirin a fadin kasar a makarantu da masallatai da coci-coci da sansanin masu yi wa kasa hidima.”

5. Hukunci

Lokacin da gwamnatin Najeriya ta fara haramta shan maganin Codeine a watan Mayu, an yi shi ne ta hanyar umarnin ma’aikatar lafiya.

Zuwa karshen watan Mayu, majalisar wakilai ta yi daftarin tsauraran dokoki da su ka shafi nacewa Codeine da Tramadol.

A baya, wadanda aka kama da Codeine ko Tramadol ba sa fuskantar hukunci.

Yanzu, ana iya kai mutum kurkuku tsawon shekaru biyu kuma a ci tarra shi fiye da naira miliyan daya idan aka kama shi da kwayoyin ko kuma abin da ya danganci haka.

Image caption

Mayakan Boko Haram sun yi kaurin suna wajen safarar Tramadol

Ba kamar maganin tari mai dauke da kodin ba, wanda ake sarrafa shi a kasar, Tramadol shigo da shi a ke yi kuma akwai tsoron cewa magungunan rage radadin ciwo na rura wutar Boko Haram a Arewa maso gabashin kasar.

A cewar hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya, kashi 20 cikin 100 na Tramadol da ake safarar shi ba a bisa ka’ida ba a duniya an kwace shi ne a Najeriya a bara.

A wani bincike da aka gudanar a filin jirgin sama na Legas a watan Mayu, fiye da kilogram 4,000 na Tramadol aka kwace.

Yarinyar da ta kuduri aniyyar kare hakkin Fulani


Ba kasafai ake samun ‘yayan Fulani makiyaya da sha’awar karatun boko mai zurfi ba, to amma da alama Maryam Sa’idu Baso ta fita daban.

Mairo, kamar yadda ake kiranta a rugarsu ta Nyama da ke garin Akwuke a jihar Enugu, daya ce daga cikin ‘ya’yan Ardo Sa’didu Baso, sarkin Fulanin kudu maso gabashin Najeriya da kudu maso kudanci.

Mahaifinsu yana da sha’awar ‘ya’yansa da ma sauran ‘yayan Fulani su yi karatun zamani, sai dai ba duka ne suke yi ba, don haka yake karfafawa Maryam gwiwar karatun, da kuma daukar dawainiyar karatunta, saboda sha’awar da take nunawa.

A yanzu haka Maryam ta kammala karamar sakandare, tana kuma shirin tafiya babbar sakandare.

Image caption

Maryam ta yi karatu ne a wannan aji, kuma a yanzu tana taimakawa kannenta wajen koyar da su karatu da rubutu a rugar Nyama

Babban burinta shi ne ta yi karatu mai zurfi har zuwa jami’a. Tana fatan zama lauya.

“Abin da ya sa na ke son zama lauya shi ne mutanenmu suna samun matsala, saboda babu wanda ya yi karatu ya yi ilimi yake da wani abu. Saboda haka, in na yi lauya zan iya taimakawa mutanenmu a bangaren shari’a.”

Ba Maryam ce kadai ke da wannan buri ba, akwai ‘yan uwanta a rugar Nyama da ke da irin wannan fata.

Maryam tana rayuwarta ne gaba daya a jihar Enugu da e kudu maso gabashin Najeriya tun daga haihuwa har kawo yanzu.

Hakan ya ba ta damar iya harshen Igbo da ake magana da shi a shiyyar.

Ba ma magana kawai ba, Maryam da ‘yan uwanta suna wakokin gada da harshen Igbo, kasancewa suna haduwa wajen wasannin, musamman a makaranta.

To sai dai duk da kasancewa Maryam tana zaune tana kuma karatu a kasar Igbo, ba ta manta yarenta na asali ba wato Fulatanci.

Tana magana da Fulatanci sosai, har ma da rera wakokin harshen.

Watakila hakan dai ba ya rasa nasaba da yadda suke kebe a rugarsu su kadai, da kuma yadda iyayensu suke musu magana da harshen Fulatanci zalla.

Rayuwar Fulani a rugar Nyama dai kusan irinta ake yi a sauran rugage da dama.

An shafe shekaru da dama ana yunkurin kafa makarantun ‘ya’yan Fulani domin bunkasa karatunsu.

To sai dai har yanzu makarantun ba su bunkasa ba kamar yadda aka yi fata.

Akwai dalilai da dama da suka hana makarantun bunkasa, abin da kuma ya sa da dama daga ‘ya’yan Fulani makiyaya ba su yi karatun zamani ba.

Rashin zaman Fulanin waje guda na daga manyan dalilan da ke kawowa karatun ‘ya’yansu koma baya.

Fulani makiyaya na yawan yawo ne suna neman wuraren danyar ciyawa da dabbobinsu za su ci, da kuma inda ruwa yake.

Wani dalilin kuma shi ne rashin malamai a makarantun.

Alal misali a rugar Nyama malami daya ne yake karantar da duka daliban makarantar rugar shekaru da dama.

Akwai kuma karancin kayan aiki, da rashin ajujuwan karatu.

To amma da yake a yanzu Fulanin makiyaya na fuskantar wasu matsaloli fiye da baya, wasunsu sun fara tunanin cewa ya kamata su tsaya su yi ilimin zamani.

Wasunsu na fatan cewa hakan zai saukaka musu wahalhalun da suke ciki da tsangwama da suke fuskanta.

Sai dai duk da haka akwai matasan Fulani da dama da babu abin da suke sha’awa a rayuwa kamar kiwo da suka taso suka ga ana yi.

Image caption

A wannan ruga Maryam take rayuwa da iyayenta da ‘yan uwanta

Saraki zai yi zaman gaggawa da shugabannin majalisa


Hakkin mallakar hoto
Twitter/The Senate

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki zai yi zaman gaggawa da sauran shugabannin majalisar dokokin kasar a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata.

Wani na kusa da shugaban majalisar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ne ya shaida wa BBC hakan.

Ya ce za a yi zaman ne tsakanin shugabannin majalisar dattawan da na wakilai kuma za su kwashe tsawon sa’a guda suna tattaunawar.

Ya ce cikin batutuwan da za su tattauna har da batun zaben shekarar 2019, da batun sauya shekar wasu ‘yan majalisar kasar.

Sai dai sabanin yadda wasu rahotanni suka bayyana, zaman ba zai duba batun tsige Sanata Saraki daga shugabancin majalisar ba.

“Wannan ba ya daga cikin batutuwan da za su tattauna,” a cewarsa majiyar BBC.

A karshen watan jiya ne majalisar ta tafi dogon hutu bayan sauya shekar wasu ‘yan majalisa fiye da 50 daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.

Akwai wasu rahotanni wadanda ba a tabbatar ba da ke cewa akwai wani shirin tsige Sanata Saraki daga kujerarsa, bayan da shi ma ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a makon jiya.

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka daga APC zuwa yanzu

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Wadannan na cikin ‘yan majalisar dattawan da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal

Kakakin jam’iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed

Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

‘Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su

Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa’i

Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 – wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam’iyyar

Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam’iyyar ADC

Hakeem Baba Ahmed – shugaban ma’aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Usman Bawa – mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

An kama wani jigo a kungiyar Boko Haram


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta cafke Maje Lawan ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Banki a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Hakan yana kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun daraktar yada labaranta, Birgediya Janar Texas Chuku, inda ta kara da cewa an kama mutumin da ake zargin ne a ranar Asabar.

Mutumin shi ne mutum na 96 a cikin jerin sunayen ‘yan Boko Haram 100 da rundunar sojin kasar take nema ruwa a jallo.

Kawo yanzu dai yana ci gaba da kasancewa a hannun sojoji zuwa lokacin da za a kammala bincike a kan lamarin.

Sai dai rundunar ba ta ya yi wani karin bayani ba kan yadda aka yi dan Boko Haram din da ake zargi ya kasance a sansanin da kuma tsawon lokacin da ya kwashe a can, duk da matakan tantance mutane da hukumomi ke cewa suna dauka don tabbatar da cewa hakan bai faru ba.

Kodayake a baya rundunar ta sanar da kama kalilan daga cikin ‘yan kungiyar ta da ta ce tana nema ruwa a jallo, amma kama Maje Lawal ya kara sanya alamar tambaya a kan matakan tattara bayanan sirri da hukumomin tsaron kasar ke cewa suna amfani da shi.

A baya dai an sha kai hare-haren kunar bakin wake a wasu sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke yankin na arewa maso gabashin kasar.

Kun san yadda za ku tsira daga hadarin jirgin sama?


Hakkin mallakar hoto
EPA/Handout

Image caption

Rahotanni sun ce jirgin da ya fadi a jihar Durango na Mexico ya rasa injunansa biyu

Labarin da ke cewa dukkanin fasinjoji 103 sun tsira a wani hadarin jirgin saman da aka samu a jihar Durango na Mexico ranar Talata ka iya kama da wani abin al’ajabi, musamman idan aka yi la’akari da hotunan baraguzan jirgin da ke (konewa da) hayaki.

Kusan dukkanin wadanda suke cikin jirgin sun ji ciwo, sai dai kuma yawancinsu sun bar wurin da hadarin ya auku ne da ciwo.

Wane irin abin alajabi ne wannan? Abun mamaki, aukuwarsa ba zai yi wuyar da za ka yi tunani ba.

Wace irin dama muke da ita na tsira daga hadari?

A takaice, babu wata amsa kai tsaye – kamar yadda ba za mu iya bayyana yadda za a iya tsira daga hadarin mota ba, domin ya dogara ne bisa yanayin aukuwar hadarin.

Amma a lokacin da Hukumar Kiyaye Haddura a Harkar Sufuri ta Amurka, ta gano cewar sama da kashi 95 cikin 100 na mutane sun tsira daga hadduran, ciki har da kashi 55 cikin 100 na hadduran da suka fi muni.

Damarmakinmu sun dogara ne kan wasu dalilai kamar kamawa da wuta da nisan wurin da aka yi hadarin a sama da kuma wurin da aka yi hadarin.

A cikin wani bincike da Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayyar Turai ta gudanar a shekarar 1996, an gano cewar a na iya kare aukuwar kashi 90 cikin 100 na hadduran jirgin sama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A shekarar 2009, fasinjoji 150 sun tsira daga wani jirgin da bya lume a kogin Hudson na birnin New York’

A cikin shekaru 20 da suka zo bayan an yi wadannan binciken biyu, an samu ci-gaba a harkar sufurin jiragen sama inda aka samu raguwar hadduran jirage, kuma haddura masu muni suka ragu sosai.

Tafiya ta hanyar jiragen sama ta fi sauki kan tafiye-tafiye kan sauran hanyoyin sufuri kuma ta fi rashin hadari idan aka kwatanta da adadin hadduran da ake samu a sauran hanyoyin sufurin, amma wannan ba ya hana wasunmu fargaba.

Ta yiwu hakan ta faru ne domin muna yawan ganin haddura masu muni ne a cikin labarai ko kuma ta wasan kwaikwayon masana’antar fina-finan Hollywood.

Mene ne yake sa a gane in za a iya tsira daga hatsari?

Tom Farrier, tsohon darakta ne na kiyaye haddura a kungiyar kamfanonin jiragen sama na kasuwa (Air Transport Association), ya yi bayani a kan shafin Quora cewar wasu sharruda uku ne suke taimaka:

 • Ko abubuwan da mutanen dake cikin jirgi suka ci karo da su na cikin abubuwan da mutum zai iya jurewa
 • Idan jirgin da suka shiga bai lalace sosai ba
 • Idan yanayin wurin da suka fada bayan hadarin jirgin ya yi barazana nan take ga mutanen ko kuma masu ceto

A takaice: wane irin aibi ko wane bugu ya yi wa jiki da kuma mene ne matakin ta’adin da ya yi wa jirgin da kuma irin hatsarin da ke tattare da baraguzan jirgin da kuma wurin da abin ya faru.

A hadarin da aka yi a Mexico, jirgin ya fadi ne jim kadan bayan ya tashi kuma yawancin fasinjojin jirgin sun samu sun tsere kafin jirgin ya kama da wuta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Nuwambar 2016, mutum 71 sun mutu a cikin wani jirgin da ya dauko ‘yan wasan wata kungiyar kwallon kafa a Brazil, Chapecoense. Mutum shida ne kawai suka tsira – ciki har da Jakson Follmann (da yake cikin wannan hoton)

Da aka tambaye shi kan ko faduwa a kasa ko kuma akan ruwa ne ya fi muni, masani a kan sufurin jiragen sama Adrian Gjertsen ya ce tsira ya fi danganta ne kan kusancin masu aikin ceto fiye da kan wurin da jirgi ya fada.

Ya shaida wa BBC cewar: “Alal misali, a lokacin da aka samu hadari a kan kogin Hudson, an samu masu aikin ceto nan take. Amma idan kana tsakiyar teku, za a samu karin matsala ta samun kai wa ga kan tudu.”

“Idan aka samu hadari a Sahara ko kuma a tsakiyar tekun Atlantic – ba zan iya cewa akwai bambanci tsakaninsu ba, tunda dai babu wanda zai taimaka a wurin”

Ta yaya za mu kara damarmakinmu?

Intanet na cike da shawarwari kan wannan maudu’in: saka damarar kujerar da kin saka riga mai saurin kamawa da wuta da kuma kirga layin kujeru tun daga farko saboda yiwuwar mutuwar hasken wutar lantarki.

Mutane suna muhawara kan inda ya fi rashin hadari mutum ya zauna a cikin jirgi, kuma wasu bincike sun nuna cewar zama a baya ka iya kasancewa mafi karancin hadari.

Mr Gjertsen ya ce ba abu ne mai sauki ba. Ya danganta da irin jirgin da kuma irin hadarin.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Air Steward: “No one pays attention to the in-flight demonstration”.

Ya ce “Daya daga cikin lamuran da ke janyo matsaloli shi ne yadda matafiya ke son tsira tare da kayansu”.

“Wannan na iya shafar tsaron lafiya, ba ma tasu ba kadai, har da ta kowa”.

‘Yan kunar bakin wake biyar sun kashe kansu a Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
BOUREIMA HAMA

Image caption

Mahara biyar ne su ka kai harin a unguwar Kaleri

Wasu da a ke zargin ‘yan kunar waken kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Babban jami’in hukumar agaji ta gaggawa mai kula da Arewa maso Gabashin Najeriya, Bashir Garga ya shaida wa BBC cewar harin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren Lahadi a unguwar Kaleri da ke cikin birnin Maiduguri.

Mazauna yankin sun ce sun ji karar fashewar bama-baman cikin dare.

Mahara biyar ne su ka kai harin inda guda uku mata ne, guda biyu kuma maza – dattijo daya da matashi daya.

Gaba daya maharan sun mutu, yayin da wasu mutum uku su ka samu raunuka, inda a yanzu su ke asibiti inda a ke basu kulawa.

Har yanzu dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, amma kungiyar Boko Haram ce aka sani da yawan kai hare-hare wannan yankin.

Wannan ne dai hari na farko cikin kusan wata biyu a birnin na Maiduguri.

Har yanzu kungiyar Boko Haram na kai hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro, duk da ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi cewa ta “murkushe” su.

A mako biyu da suka gabata maharan da ake zargi ‘yan kungiyar ne sun kai wa sojoji hari, inda rahotanni suka ce an kashe sojoji da dama tare da kwace makamai, sakamakon kwanton baunar da suka yi wa dakarun tsaron.

Hukumomi sun cean kashe ‘yan Boko Haram da dama a wannan arangamar.

Rundunar sojin Najeriyar dai ta sauya kwamandan da ke jagorantar rundunar da ke yaki da kungiyar bayan wannan artabun.

Karin Labaran da za ku so ku karanta

Everton na neman Mina, Chelsea na zawarcin Zaha


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wilfried Zaha

Kungiyar Everton ta cimma yarjejeniya da Barcelona kan dan wasan Colombia Yerry Mina, mai shekara 23, a kan fam miliyan 28.5, in ji (Sport – in Spanish).

Everton ta sanar wa Manchester United cewa za ta karbi dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekaru 28, ko dan wasan bayan Sweden Victor Lindelof, mai shekara 24 ,idan kolub din biyu suka kasa cimma jarjejeniya game da dan kwallon Argentina, Marcos Rojo, a cewar (Teamtalk)

Manchester United na shirye-shirye don neman dan wasan Leicester, Harry Maguire, mai shekara 25, kuma sun san cewa za su biya makuddan kudi domin karbar dan wasan na Ingila, in ji (Sky Sports).

A halin yanzu, Manchester United ta tuntubi Bayern Munich don sayar da dan wasan Jamus, Jerome Boateng, mai shekara 29, wanda aka kimanta a kan fam miliyan 44, kamar yadda (Bild – in German) ta ruwaito.

Chelsea na da sha’awar sayen Wilfried Zaha, na Crystal Palace da dan Ivory Coast, mai shekara 25, bayan Tottenham ta fita daga zawarcinsa, in ji (Mirror).

Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya ba da shawara cewa Thibaut Courtois, mai shekara 26, wanda yake tare da Real Madrid za a sayar da shi idan ya so barin kungiyar, in ji (Times).

Saura shekara daya kwantaragin dan wasan Arsenal, Aaron Ramsey, ya kare a kungiyar, kuma wakilansa sun musanta cewa dan wasan mai shekara 27 ya nema a biya shi fam 300,000 a kowane mako a wata sabuwar yarjejeniya, in ji (Express).

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino yana sha’awar dan wasan tsakiya na Celta Vigo, Stanislav Lobotka, wanda ke da albashin fam miliyan 31 a kwangilarsa, kamar yadda jaridar (Mirror) ta ruwaito.

Kungiyar Leicester City tayi tayin dan wasan kungiyar Brentford, Chris Mepham, mai shekara 20, a kan fam miliyan 10 amma kungiyar ba ta amince ba, kuma Bournemouth su ma suna so su sayi dan wasan na Wales, a cewar (Mail).

Wolves suna son su biyan Middlesbrough fam miliyan 22 a kashi-kashi don siyan dan wasan Spain Adama Traore, mai shekara 22 a kan su biya su fam miliyan 18 a nan take, in ji (Sun).

Crystal Palace suna cikin tattaunawa a kan yarjejeniyar siyan dan wasan kasar Israel, Munas Dabbur, mai shekara 26, in ji (Mail).

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin ‘yan NYSC tara a Taraba


Hakkin mallakar hoto
NYSC Facebook

‘Yan sanda a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla masu yi wa kasa hidima (NYSC), tara, sakamokon tafiyar da ruwa ya yi da su ranar Asabar a kauyen Mayo Salbe da ke karamar hukumar Gashaka.

‘Yan sandan sun tabbatar wa da BBC cewa zuwa yanzu sun gano gawawwakin bakwai daga cikin matasan, yayin da ake ci gaba a neman sauran biyun.

Bayanai sun ce matasan su fiye da 20 ne suka je yawon shakatawa ne a wani kogi amma sai kogin da ya ciko, ya yi awon gaba da wasu a cikinsu.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jihar Taraba David Misal, ya ce, matasan ba su yi aune ba sai kogin ya ciko ya makare, har ya yi awon gaba da wasu daga cikin masu yi wa kasa hidimar.

Kogin Mayo-Selbe dai yana samun ruwansa ne daga babban Kogin Benue.

Mista Misal ya ce: “Matasan suna cikin walwala da nishadinsu ne a kogin, to da alama an yi ruwan sama a wani waje nesa kadan kuma ta wannan kogin yake ratsawa, sai ruwan ya taho da karfi ya tafi da tara daga cikinsu.”

Ya kara da cewa a yanzu dai suna ci gaba da tantance jinsin gawawwakin don gano sunayensu da garuruwan da suka fito.

Wata matashiya daga cikin ‘yan bautar kasar da take cikin tawagar da wadanda abin ya rutsa da su, ta ce: “Sun isa wajen da karfe biyun ranar Asabar, kuma sai abokan tafiyarsu suka ce su je sashen da ya fi kayatarwa.”

“A kan hanyarmu ta dawowa daga bangaren da ya fi kayatarwar ne sai muka ga kogin ya ciko har yana ambaliya, sai kuma ruwan ya tafi da mutum tara daga cikinmu,” a cewarta.

Rundunar ‘yan sandan jihar dai ta ce yawancin wadanda abin ya rutsa da su ‘yan kudancin Najeriyar ne.

Dalilan da suka sa mataimakin gwamnan Kano yin murabus


Hakkin mallakar hoto
Hafiz Abubakar

Image caption

Farfesa Hafiz Abubakar

Gwmnatin jihar Kano ta ce mataimakin gwamnan jihar ya yi gaggawar yin murabus ne yayin da ‘yan majalisa ke shirin tsige shi.

Mataimakin gwamnan na jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar wanda ya gabatar da takardar murabus din sa, ya zargi gwamnatin Ganduje da mayar da shi saniyar ware, tare da cewa wani lokaci da kudin aljihunsa yake amfani wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

A baya-bayan nan ne tsohon mataimakin gwamnan ya shaidawa BBC cewa tsawon fiye da shekara biyu, zaman doya da manja yake tsakaninsa da Ganduje saboda yana ra’ayin Kwankwasiya. Ya kuma ce har ta kai ana yi rayuwarsa barazana.

A martanin da ta mayar, gwamnatin Ganduje ta musanta dukkanin zarge-zargen inda ta ce babu wani sabani ko bi-ta-kulli da ake yi wa tsohon mataimakin gwamnan.

Wata sanarwar da kwamishin watsa labarai na jihar Kano ya fitar ta ce gwamnatin ya yi murabus ne a yayin da ‘yan majalisar jihar ke shirin tsige shi.

Sanarwar ta kuma musanta zargin da mataimakin gwamnan ya yi cewar ana tauye shi wajen fitar da kudaden alawus na tafiye-tafiye tare da yin barazana ga rayuwarsa.

Gwamnatin Kano ta ce ” a 2017 kadai, Naira miliyan 120 aka kashe wa ofishin mataimakin gwamnan na alawus din tafiye- tafiyensa. A 2018 kuma an kashe ma sa Naira miliyan 30.”

A cikin wasikar murabus din mataimakin gwamnan, ya ce ya so ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wa’adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar:

“Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.

A cikin wasikar, ya kara da cewa, “Idan ba ka manta ba mai girma gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba.”

Hakkin mallakar hoto
KANO STATE DG MEDIA

Image caption

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da tsohon mataimakinsa Hafiz Abubakar a kwanan baya

Gwamnatin Ganduje ta ce tana iya daukar matakin shari’a kan da zargin da tsohon mataimakin gwamnan ya yi cewar gwamnati za ta dauki nauyin shirya zanga-zanga domin nuna goyon baya ga bukatar tsige shi.

Salva Kiir da Riek Machar sun amince su raba madafan iko


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Riek Machar da Salva Kiir suna sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Shugabannin Sudan ta Kudu da ke gaba da juna sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar raba madafan iko tsakanin bangarorin da suke jagoranta.

Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, sun sanya hannun ne a wani biki da aka yi cikin Khartoum, babban birnin kasar Sudan mai makwabtaka.

Wannan wani al’amari ne da ake ganin zai iya kawo karshen mummunan rikicin da aka shafe shekara biyar ana gwabzawa a kasar.

Yanzu ana sa rai za su kafa wata gwamnati da za ta kunshi dukkanin bangarorinsu.

Murna dai ta barke a Juba, babban birnin kasar bayan sanar da kulla yarjejeniyar.

An dai dade ana kulla yarjejeniya kuma ana wargazawa tsakanin bangarorin biyu.

Amma ministan harakokin wajen Sudan Al-Dirdiri Mohamed, wanda ya jagoranci sasantawar ya bayar da tabbacin cewa a wannan karon yarjejeniyar za ta dore.

Rikici tsakanin dakarunsu ya janyo kashe-kashen kabilanci da hare-hare a kan fararen hula da aikata fyaden da ya zama ruwan dare da daukar kananan yara aikin soja.

Dubban mutane aka kashe a rikici, yayin da wasu kimanin miliyan biyu suka tsere wa gidajensu.

Saudiyya ta yanke huldar kasuwanci da kasar Canada


Image caption

Samar Badawi tare da matar tsohon shugaban Amurka Michelle Obama da Hillary Clinton a shekarar 2012 da aka bata lambar yabo ta karfafawa mata gwiwa

Kasar Saudiyya ta sanar da dakatar da duk wata huldar kasuwanci da zuba jari da Canada, tare kuma da korar jakadanta daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce shi ma jakadan Saudiyya a birnin Ottawa na Canada an bukaci ya koma gida.

Saudiya ta fusta ne sakamakon wata sanarwa da ma’aikatar harakokin wajen Canada ta fitar a makon da ya gabata inda take sukar gwamnatin Riyadh kan yadda take kame ‘yan rajin kare hakkin dan adam da suka kunshi har da wata ‘yar Amurka Samar Badawi.

A cikin sanarwar Canada ta bukaci saudiya ta saki Samar Badawi da sauran ‘yan rajin kare hakkin biladama da kasar ke tsare da su.

Wannan ne kuma ya Saudiya ta sanar da katse duk wata hulda ta kasuwanci da Canada tare da korar jekdan ksar daga Riyadj .

Saudiya kuma ta janye dukkanin jami’an diflomasiyasar daga Canada.

A makon jiya ne Saudiya ta kame Badawi, daya daga cikin masu gwagwarmayar ganin kasar ta kawo karshen tsarin dokokinta da suka shafi tauye hakkin mata.

Zuwa yanzu babu wani martini da ya fito daga gwamnatin Canada kan matakin na diflomasiya da Saudiya ta dauka.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya yi murabus


Hakkin mallakar hoto
Hafiz Abubakar

Image caption

Farfesa Hafiz Abubakar

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya yi murabus bayan an shafe watanni ana takun saka tsakaninsa da gwamnan.

Mataimakin gwamnan ya sanar da murbus din nasa ne a wata wasika da ya mika ma gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.

A cikin wasikar, ya ce ya so ya cigaba da rike mukamin mataimakin gwamna har zuwa karshen wa’adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar:

“Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.

Hakkin mallakar hoto
KANO STATE DG MEDIA

Image caption

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da tsohon mataimakinsa Hafiz Abubakar a kwanan baya

A cikin wasikar, ya kara da cewa, “Idan baka manta ba mai girma gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba.”

A baya bayan nan ne mataimakin gwamnan ya rubuta wata wasika ga hukumomin tsaron Najeriya, inda yake neman da su dauki mataki akan abin da ya kira wata barazana da jami’an gwamnatin jihar Kano ke yi ga lafiyarsa.

Gagarumar girgizar kasa ta auku a tsibirin Lombok na Indonisiya


Wata gagarumar girgizar kasa mai karfin lamba 7 a ma’unin Richter ta auku a tsibirin Lombok na Indonisiya.

Lamarin ya sa hukumomi sun sanar da yiwuwar aukuwar igiyar ruwan teku mai karfi ta tsunami a yankin.

Hukuma mai kula da girgizar kasa ta Amurka, US Geological Survey, ta ce girgizar ta auku ne arewa da tsibirin, kilomita 10 a karkashin kasa.

Tsibirin Lombok wata cibiya ce ta masu yawon bude idanu, kuma yana da nisan kilomita 40 ne gabas da Bali.

Kawo yanzu ba a sami bayanin wadanda suka jikkata ko suka rasa rayukansu ba, amma jami’ai sun yi gargadin aukuwar igiyar ruwa ta tsunami, kuma sun shawarci jama’a da suk janye daga yankunan da ke kusa da gabar teku.

Mazauna Bali sun ji wannan girgizar kasar na kusan minti guda, lamarin da yasa su ka yi ta ficewa daga cikin gidajensu.

‘Man Utd ko Liverpool ko Arsenal ne kawai za su raba Gerrard da Rangers’ – Miller


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Gerrard’s man-management crucial – Adam

Steven Gerrard ba zai bar kungiyar Rangers ba sai idan Liverpool ko Manchester United ko Arsenal ne suka bukaci ya zama kocinsu.

Wannan maganar ta fito ne daga bakin Alex Miller, wani tsohon mataimakin mai horas da kungiyar Liverpool a lokacin da Steven Gerrard ke taka leda a kungiyar.

Mista Miller ya taba buga ma kungiyar Rangers lokacin yana matashi.

Ya kuma ce yana da karfin gwuiwa cewa Rangers za ta sami daukaka a karkashin sabon koci Steven Gerrard.

Ya fada ma BBC Scotland cewa: “Rangers za su ja daga da kungiyar Celtic nan ba da jimawa ba”.

Ya kara da cewa, “Idan ka sami aikin horas da Rangers, me zai sa ka tafi? Sai dai idan kungiyoyi kamar Liverpool ko Manchester United ko kuma Arsenal ne suka bukaci ka zama kocinsu.”

Miller na ganin cewa ‘yan wasan da Gerrard ya saya a kakar wasa na bana zasu yi tasiri a gasar firimiyar Scotland.

Kawo yanzu, Rangers sun sai ‘yan wasa 10, kuma sun bambanta da irin ‘yan wasan da aka saba gani a kungiyar ta Ibrox.

Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Gerrard yayi wasa karkashin jagorancin Alex Miller da Rafa Benitez a kungiyar Liverpool

Miller ya taba zama mataimakin kocin Scotland a karkashin Craig Brown kafin daga baya ya rike irin wannan mukamin a karkashin Rafa Benitez a Liverpool, kuma ya horas da Steven Gerrard na wasu shekaru.

Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya


Zababbun hotuna mafi kyau daga kowane sako na Afirka da sauran sassan duniya a makon da ya wuce.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani yaro yana bacci a jirgin kasan da ya dosa wani gari mai suna Musina da ke kudancin Afirka a bakin iyakar Zimbabwea ranar Juma’a

Ranar Asabar matan Etopia sunyi murna yayin da firam ministan kasar Abiy Ahmed ya ziyarci Amurka.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ranar Asabar wadansu mata a Habasha sun yi wani bikin murna yayin da fira ministan kasar Abiy Ahmed ya ziyarci Amurka

Mutane na huce zafi a tekun Bahagum a ranar Lahadi a kasar Masar yayin da zafi ya karu sosai a garin Port Said.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mutane a tekun Bahar Rum a ranar Lahadi a kasar Masar yayin da zafi ya karu sosai a garin Port Said

A ranar kuma wani manomin vanilla yana kula da amfanin gona a cikin tarin tsibirin Comoros na gaba kafin a raba gardama a kan iyakokin shugaban kasa.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani manomin icen Vanilla yana kula da amfanin gona a tsibirin Comoros a ranar Lahadi

Wani dan adawa a zimbabwe a yayin da ake zanga-zanga a babban birnin kasar na Harare a ranar Laraba don an rike sakamakon zaben da akayi.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani dan adawa a Zimbabwe a yayin da ake zanga-zanga a babban birnin kasar Harare a ranar Laraba don hukumoki sun ki bayyana sakamakon zabe

Masu damben boksin a babban birnin Kenya wato Nairobi a wata gasar Kibera a ranar Lahadi.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Masu damben boksin a babban birnin Kenya wato Nairobi a wata gasar Kibera a ranar Lahadi

Wakilai a kasar Morocco suna murnar zagayowar ranar da aka nada Mohammed VI a ranar Talata.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wakilai a kasar Morocco suna murnar zagayowar ranar da aka nada Sarki Mohammed VI a ranar Talata

Lokacin da shugaban kafirai Orthodox patriarch Bishop Merkorios ya dawo daga neman mafaka ma shekara 27 a Addis Ababa inda aka tarbesa da kide-kide da wakokiHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Lokacin da shugaban wadansu Kiristoci Bishop Merkorios ya dawo daga gudun hijira inda aka tarbe shi da kide-kide da wakoki a Addis Ababa

Sauran masu tarbon sun tsaya a cikin gari inda suka busa kakakin bukukunaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sauran masu tarbarsa sun tsaya a cikin gari inda suka busa kakaki

A wani barin nahiya a babban birnin Mali Bamako wani mutumi ya na hutawa a gaban wurin zaben shugaban kasa a ranar Lahadi.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A wani barin nahiyar AfirkA a babban birnin Mali Bamako wani mutumi yana hutawa a gaban wurin zaben shugaban kasa a ranar Lahadi

Tsohon shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina a yayin da ya ke karkarin sake dawowa a wani taro da akayi a birnin Antananarivo.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina a yayin da yake kokarin dawowa fage a birnin Antananarivo

Mata a garin Cape na Afirka ta kudu a yayin da suke tafiya hanyar majalisa da zanga-zanga don a daina cin zarafin jinsi.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mata a garin Cape na Afirka ta Kudu a yayin da suke zanga-zanga don a daina cin zarafin mata

Hotuna daga AFP, EPA, Getty Images da kuma Reuters

Venezuela: Maduro ya tsallake rijiya da baya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumomin Venezuela sun ce jirage marasa matuka sun sako ababen fashewa a kusa da shugaba Nicolas Maduro a lokacin da yake gabatar da jawabi.

Lamarin ya faru ne lokacin da ake gudanar da bikin sojin kasar da gidan talabijin din kasar ke yadawa kai tsaye a Caracas fadar gwamnatin kasar.

An ga shugaba Maduro ya dakatar da jawabin da ya ke yi tare da kallon sama bayan ya fashewar ta razana shi.

Gwamnatin kasar ya ce jirage marasa matuka biyu ne suka saki ababen fashewa a kusa da shugaban.

Tun da farko an nuna sojojin da ke fareti suna gudu kafin a katse jawabin na shugaba Maduro wanda ake nuna wa kai tsaye a talabijin.

Daga baya shugaban ya fito ya shaida wa ‘yan kasar cewa yana raye kuma ba abin da ya same shi.

Sai dai ya zargi Colombia da kuma ‘yan adawa, yana mai cewa makiyansa na gida da waje ne suka yi yunkurin halaka shi, zargin da gwamnatin Colombia ta musanta.

Hukumomin kasar sun ce sojoji bakwai suka ji rauni, sannan an kame mutane da dama da ake zargi.

An yi gargadi ga ‘yan Nijar kan siyasar Najeriya


Kungiyar ‘yan Nijar mazauna Najeriya ta gudanar da wani taron fadakar da al’ummarta kan muhimmancin bin doka da oda a daidai lokacin da gangar siyasa ta fara kadawa a Najeriya.

Sai dai mahalarta taron sun koka kan yadda jami’an shige da fice na Najeriya ke gallaza masu kan iyakokin kasashen biyu, duk da tsarin kungiyar ECOWAS ya ba su damar shiga kasashen yammacin Afirka.

Amma Shugaban hukumar shige da ficen na Najeriya Mohamed Baban Deedee ya mayar da martani kan korafin na ‘yan Nijar.

Abdou Halilou wanda ya halarci taron ya aiko da rahoto.

‘Yanzu PDP ta fi APC karfi a majalisar dattawa’


Image caption

Dogara da Amaechi da Wamakko ba su fice daga jam’iyyar APC ba

Cikin ‘yan makwannin nan ne dai wasu daga cikin jigajigan ‘yan siyasa a Najeriya da ke kiran kansu ‘yan sabuwar jam’iyyar PDP suka fita daga jam’iyyar APC mai mulki.

Komawarsu jam’iyyar APC na cikin dalilan da suka bai wa jam’iyyar nasara a zaben 2015.

Yayin da wasu masharhanta ke ganin tarihi ne yake son maimaita kansa, ya kamata a san adadin ‘yan sabuwar PDP din da suka bar jam’iyya mai mulki din da kuma wadanda ba su bar jam’iyyar ba.

Tun karshen shekarar 2013 ne dai wasu ‘yan majalisar wakilai 37 suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Cikin wadannan ‘yan majalisu 37 na wancan lokacin, akwai Yakubu Dogara daga jihar Bauchi.

Kafin zaben 2015, guguwar sauya shekar ta fara ne da ficewar gwamnoni biyar daga bangaren sabuwar PDP zuwa APC, kafin ‘yan majalisar su sauya sheka.

Gwamnonin sabuwar PDP din da suka fice sun hada da gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano da Murtala Nyako na jihar Adamawa da Aliyu Magatakarda Wamakko na jihar Sokoto da Rotimi Chibuike Amaechi na jihar Ribas da kuma Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara.

Gwamnoni biyu daga cikin ‘yan sabuwar PDP ne kawai ba su fice daga jam’iyyar ba, wato Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu na jihar Neja da Sule Lamido na jihar Jigawa.

Kuma a watan Janairun 2014 ne dai ‘yan majalisar dattawa 11 suka sauya sheka daga sabuwar PDP din zuwa APC.

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/EFFC

Image caption

Attahiru Bafarawa na cikin wadanda suka kafa APC, amma ya fice daga jam’iyyar gabannin zaben shekarar 2015

‘Yan majalisar sun hada da Bukola Saraki da ke wakiltar jihar Kwara ta tsakiya da Umaru Dahiru da ke wakiltar jihar Sokoto ta kudu da dai sauransu.

Ba ‘yan sabuwar PDP ne kawai suka sauya sheka daga PDP ba a wancan lokacin.

Ministan kasuwanci a gwamnatin tsohon Shugaba Jonathan, Samuel Ortom ya fice daga PDP zuwa APC daf da zaben 2015.

A zaben na shekarar 2015 ya zama gwamnan jihar Benue.

Amma a wancan lokacin ne tsoffin gwamnonin jihar Sokoto da na Kano, Attahiru Bafarawa da Ibrahim Shekarau, suka sauya sheka daga APC din PDP.

Bayan kimanin shekara biyar da aka yi guguwar sauya sheka daga PDP, yanzu kuma guguwar ta sake kadawa inda wasunsu ke fita daga APC zuwa inda suka fito.

A cikin wadanda suka sauye shekar daga APC, akwai tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya sauya sheka daga APC zuwa jam’iyyar PDD tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin jam’iiyar APC, Bolaji Abdullahi.

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da dansa, Abdul-Azeez Nyako sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwe ma ya sauye sheka daga APC zuwa PDP.

Su wasuka rage a APC?

Shugaban majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara yana cikin wadanda suka shigo APC daga PDP, kuma wasu na ganin yana kan hanyar fita daga jam’iyyar duk da cewa bai fito ya nuna zai fita ba kawo yanzu.

Amma kusancin da ke tsakanin shi da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, wasu ke ganin yana tare da PDP, ko da kuwa har yanzu yana ci gaba da zama a APC bai fita ba.

Sannan akwai wasu tsoffin gwamnoni da ba su sauya sheka ba cikin gwamnonin da suka koma APC daga sabuwar PDP.

Tsoffin gwamnonin sun hada da ministan sufurin Najeriya, Rotimi Chibuike Amaechi wanda ya jagoranci yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben 2015. amma wasu na ganin don ana damawa da shi a gwamnatin APC da ke mulki, ba ya cikin lissafin ‘yan sabuwar PDP da ake ganin za su fice daga APC.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya ce yana nan daram dam a APC, duk da gwamnansa Aminu Waziri Tambuwal ya fita daga jam’iyyar da a karkashinta aka zabe shi.

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Jam’iyyar APC dai tana ganin ficewar ‘yan sabuwar PDP din ba za ta hana ta lashe zabukan da kasar ke fuskanta ba

Wa ya fi rinjaye a majalisa?

Image caption

Yanzu dai majalisar wakilai da ta dattawa na hutun makwanni

Batun jam’iyyar da ta fi rinjaye a majalisun dai wani abu ne da ake ganin shi ne ma fi muhimmanci a wannan al’amari.

A yanzu dai ‘yar manuniya ta nuna cewa jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a majalisar dattawan kasar inda ta fi PDP da mutum 1 bayan ficewar shugaban majalisar Bukola Saraki.

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka daga APC zuwa yanzu

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Wadannan na cikin ‘yan majalisar dattawan da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal

Kakakin jam’iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed

Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

‘Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su

Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa’i

Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 – wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam’iyyar

Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam’iyyar ADC

Hakeem Baba Ahmed – shugaban ma’aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Usman Bawa – mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

Wanne tasiri sauyin shekar zai yi?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Idayat Hassan, Darakta ce a Cibiyar Demukradiyya da Ci-gaba (CDD), kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa, ta ce a yanzu PDP ta kara samun tagomashi a majalisar dokokin kasar.

“Dama can jam’iyya mai mulki na fuskantar tarnaki wajen gabatar da sabbin dokoki: alal misali ana daukar lokaci kafin a fitar da kasafin kudi.

“Wannan abu da ya faru na nufin APC tana cikin tsananin rikici saboda a yanzu zai yi wa mutane wahala su hade waje daya.

“Sannan abubuwa kamar girke ‘yan sanda a kofar gidajen shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa abu ne da ka iya batawa gwamnati suna, saboda ya yi kama da bi-ta-da-kullin siyasa.A ganin Idayat Hassan, a yanzu tsige shugaban kasa abu ne mai yiwuwa, “Matakai ne masu sarkakiya, kuma da wuya hakan ta faru cikin wata shida kafin babban zabe, amma ‘yan adawa za su iya taso da maganar don aika wani sako,” in ji ta.

Shi ma Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce a yanzu ba za a iya sanin tasirin sauyin shekar ba, dalili shi ne a APC an san Buhari ne zai yi takara amma ba a san dan takarar PDP.

“Sai an san waye dan takarar PDP sannan za a san ko zai iya takara da Buhari ko ba zai iya ba.”

Ko za ku iya daina amfani da shafukan sada zumunta?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana karfafa wa ma su yawan amfani da shafukan sada zumunta da su yi amfani da wannan dama su daina ziyartar shafukan tsawon wata guda.

Kungiyar kula da ci gaban lafiyar al’umma a Birtaniya ta The Royal Public Health Society ce ta fito da tsarin Scroll Free September, wanda ke da nufin isa ga ma su mafani da shafukan Facebook da Instagram da Twitter da Snapchat.

Tsarin na ganin cewa fita daga shafukan sada zumuntan zai inganta bacci, da zamantakewa da lafiyar jiki.

Shirin lafiya na NHS a Ingila ya ce abu ne mai kyau a bayyana rawar da shafukan sada zumunta ke takawa a matsalolin lafiyar kwakwalwar matasa.

Kamfe din na kira ga masu jarabar amfani da wayar hannu da su daina ko kuma su rage amfani da shafukansu na sada zumunta.

Wani bincike ya nuna cewa rabin masu amfani da shafukan ma su shekara 18 zuwa 24 na ganin daina amfami da shafukan sada zumunta take-yanke tsawon wata guda, zai taimaka wajen inganta baccinsu da ma zamantakewarsu da mutanen duniya.

Kuma kusan rabinsu (kashi 47 cikin 100) na ganin ajiye wayoyinsu zai amfani lafiyar kwakwalwarsu gaba daya.

Abu ne da ba ya canzawa

Marianne Blandamer da Emma Jackson da Rianna Parry duka ma’abota shafukan Snapchat da Instagram ne.

“Abu ne da ba ya canzawa. da na farka daga bacci na ke shiga shafukan. Sai ka ji kamar dole ne ka saan abunda kowa ke cewa.” in ji Rianna.

“Wani lokaci sai in ji kamar ni baiwa ce ga wayata. Sai in ta duba ta haka kawai.”

Wannan Satumbar mai zuwa, matashiyar ‘yar Wigan za ta yi kokarin daina amfani da shafukan sada zumunta da yamma.

Hakkin mallakar hoto
RSPH

Image caption

(Daga dama zuwa hagu) Emma Jackson, Rianna Parry da Marianne Blandamer za su yi kokarin rage amfani da shafukan sada zumunta a watan Satumba.

Kawarta Emma, ita ma ‘yar Wigan ta ce kulli yaumin tana rike da wayarta. “Ina ganin ina amfani da ita da yawa, amma ya zamar min jiki. Tabbas, abun yana da dauke hankali,” kamar yadda ‘yar shekara 14 ta shaidawa BBC.

Emma ta ce ba ta ganin za ta iya daina wa gaba daya, amma za ta yi kokarin daina duba shafukan sada zumunta idan ta koma gida daga makaranta duk yammanci.

Marianne ta daina amfani da shafukan sada zumunta lokacin da ta ke rubuta jarabawar GCSE.

Daga farko na ji banbarakwai, amma da ya ke na kasance kullum cikin aiki, sai ya zo min a dai-dai,” inji ‘yar shekara 16 ‘yar asalin Trafford. “Ka na duba wayar ne idan ba ka da abun yi.”

Wannan Satumbar, Marianne za ta shiga aji shida inda za a bata damar rike waya, amma ta yanke hukuncin kin amfani da ita.

“Na san idan na fara amfani da ita, zan saba. Dole ne in ajiye ta daban.”

Ba ni da iko

Mai wasan barkwanci Russell Kane mai shekaru 42, ya bayyana cewa ya na karbar shawarwari saboda jarabar sa da intanet.

Lokacin da ya ke magana a manhajar podcast a shafinsa na Joe.co.uk, Russell Kane ya ce: “Zan fadi wani abu. Na karbi shawarwari sau shida saboda jaraba ta da intanet, saboda ya na shafar rayuwata.”

Hakkin mallakar hoto
PA

“Wata safiyar Lahadi na dawo gida daga wani taro, kuma iyalina sun iso domin gasa nama, sai na tafi in sauya kaya.

“Sai dai ba kayan na ke so in sauya ba, so nake in je in bude wayata in duba shafukan sada zumunta na ‘yan mintoci.

“Ba ni nake da ikon yadda nake amfani da wannan na’urar ba.”

Sai dai ga matasa da yawa, tasirin waya na da hadari a gare su.

Rahoton kungiyar RSPH din ya yi gargadin cewa shafukan sada zumunta na rura wutar rashin lafiyar kwakwalwa ga matasa, inda Snapchat da Instagram su ka zamo manyan masu yin tasirin.

Daraktar hukumar NHS, bangaren lafiyar kwakwalwa, Claire Murdoch ta ce kowa, har da ma manyan shafukan sada zumunta, na bukatar daukar nauyin yaki da annobar lafiyar kwakwalwar al’umma ta gaba”

Barin shafukan sada zumunta gaba daya na iya zama abun far gaba ga wasu. Amma kamfe din na da wasu shawrwarin da za su taimaka wajen daina al’adar:

 • Daukar hutu daga kowanne shafin sada zumunta a wajen taruka
 • Kar kai amfani da shafukan sada zumunta bayan karfe shida na yamma
 • Kar ka duba shafukanka na sada zumunta a makaranta ko a wajen aiki
 • Haramta wa kankaamfani da shafukan sada zumunta a dakin bacci

Yadda Tsoho ke fatan samar da kokumba mafi tsawo a duniya


Image caption

Masana sun ce Kokumbar ‘yar asalin Armenia ce tsohon ya shuka

Wani dattijo a Derby ya ce addu’ar da yake wa kokumbarsa ya taimaka ta yi girman da za ta kasance mafi girma a duniya.

Raghbir Singh Sanghera, wanda manomi ne a India kafin ya zo Birtaniya a 1991, ya shuka kokumbar ne a lambunsa.

Kuma tsawon kokumbar yanzu ya kai ma’aunin sentimita 129.54.

Mista Sanghera ya ce kokumbar da har yanzu ba a tantance asalinta ba, tana ci gaba da girma.

Kuma yanzu ta kere kokumbar da aka shuka a Wales a 2011 mafi tsawo a duniya a kundin tarihin kamfanin Guinness inda tsawonta ya kai ma’aunin sentimita 107.

Wani masanin shuka kayan lambu ya ce kokumar tsohon ‘yar asalin Armenia ce, wacce take da bambanci da yanayin nau’in kokumbar da aka saba gani.

“Mun taba ganin irin wannan doguwar kokumba a wani bikin nuna kayan lambu, amma ba a ba ta muhimmaci ba,” in ji Mista Glazebrook

Ya ce akwai nau’insu da ke yin tsawo kuma wadanda za su iya shiga kundin tarihi a duniya.

Kamfanin Guinness ya ba tsohon damar yin takara da kokumbar domin shiga kundin tarihi a duniya.

Kakakin kamfanin ya ce ba ya da wani bayani kan wani da ya taba shuka irin wannan doguwar kokumbar a Armenia

Image caption

Tsawon kokumbar ya sentimita 129.54cm, mafi tsawo a duniya

Mista Sangera ya ce zai dauki kokumbar idan ta nuna zuwa wuwin da mabiya addinin Singh ke ibada inda yake aiki a Nottingham domin raba wa mutane.

Ya ce bayan ya cire ta zai kuma ajiye irinta domin sake shuka wa a badi.

Image caption

Lambun Mista Sanghera

Neymar ya taimaki PSG doke Monaco a gasar Super Cup


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Neymar ya koma PSG a kakar wasan bara a kan fam miliyan 200

Neymar ya shiga wasan an kusa tashi, inda PSG ta doke Monaco 4 – 0 a gasar Super Cup.

Wasan na China shi ne karon farko da dan wasan dan asalin kasar Brazil ya buga ma PSG kwallo tun watan Fabrairu bayan ya sami rauni a kafarsa.

Neymar ya shiga wasan ne da misalin minti 75 a wasan da zakarun league 1 na Faransa suka kara da masu rike da kofin kasar na bara.

Angel Di Maria ne ya jefa kwallo biyu, shi kuma Christopher Nkunku da Timothy Weah suka jefa sauran kwallo biyun a ragar Monaco.

A gaban ‘yan kallo 41,237 da ke cikin filin wasa na Shenzhen, dan wasan Argentina Di Maria ya jefa kwallo ta farko a minti na 32, daga nan kuma Nkunku da Weah – dan tsohon dan wasan PSG da AC Milan kuma shugabn kasar Liberia George Weah suka aika da kwallayensu.

Sabon kocin PSG Thomas Tuchel ya saka Neymar daga baya kafin Di Maria ya sake jefa wata kwallon, kuma wannan ya ba kungiyar nasara a karo na takwas kenan a gasar Super Cup ta Faransa.

Arsenal na neman Domagoj Vida, Courtois na son komawa Madrid


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dan Barcelona Ousmane Dembele

Yadda ta ke kaya wa a fagen kasuwar ‘yan wasan kwallon kafa a Turai, inda ake saye da sayarwan ‘yan wasan kwallon kafa dab da bude kakar wasa ta bana.

Wakilin Thibaut Courtois ya nemi Chelsea ta kyale golan dan kasar Belgium mai shekara 26 ya koma Real Madrid inji jaridar Sun.

Liverpool na bukatar dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey, mai shekara 27 daga kungiyar Arsenal inji Express.

Da alama dan wasan gaba na Manchester United, Anthony Martial mai shekaru 22 zai yi zamansa a kulob din idan Jose Mourinho bai sami wanda zai maye gurbinsa ba, inji Mirror.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Golan kungiyar Chelsea Thibaut Courtois

An lura dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 21 na tare da ‘yan wasan Arsenal kwanan nan, kuma ana hasashen zai iya komawa Gunners, inji Goal.com.

Dan wasan gaba na Chelsea, kuma dan kasar Belgium Michy Batshuayi mai shekara 24 na kan hanyarsa ta komawa Atletico Madrid, inji L’Equipe – ta Faransanci.

Kocin Arsenal Unai Emery na shirya yadda dan wasa baya na Kuroshiya Domagoj Vida mai shekara 29 zaibar Besiktas akan fam miliyan 25 inji Sun.

Dan wasan Monaco kuma dan kasar Aljeriya Rachid Ghezzal mai shekara 26 ya shirya tsaf domin komawa kungiyar Leicester akan fam miliyan 12.5 inji L’Equipe – ta Farnsanci.

Kamaru ta nada Seedorf a matsayin koci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya Clarence Seedorf ya taba horas da AC Milan da Shenzen a China da kuma Deportivo La Coruna

Kamaru ta nada Clarence Seedorf a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar bayan da yarjejeniyar da kasar ta so kullawa da tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson bata samu ba.

Tsohon dan wasan tsakiya na Real Madrid, da AC Milan da kuma Netherlands, Seedorf zai kama aiki tare da mai taimaka masa kuma abokin wasansa dan Holland Patrick Kluivert.

Daga baya cikin wannan watan za a sanar da tsawon yarjejeniyar da kwantaragin da ya sa hannu za ta kasance.

A baya Clarence Seedorf mai shekara 42 ya horas da AC Milan da Shenzen a China da kuma Deportivo La Coruna.

Amma bai wuce wata shida ba a dukkan wadannan wurare uku da yayi aiki.

Seedorf zai gaji Hugo Broos, kuma zai yi aiki na shekara daya tare da kungiyar kwallon kafa ta Kamarun kafin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta 2019 ta fara.

Fafaroman Masar ya rufe shafinsa na Facebook


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fafaroma Tawadros na 2 shi ne shugaban darikar Kibdawa a Masar

Fafaroman Kibdawan Masar Tawadros na 2 ya sanar da cewa zi rufe shafinsa na Facebook domin mayar da hankalinsa ga batutuwan addinsa.

Kamfanin dilllancin labarai na Masar, MENA ya ruwaito fafaroman na cewa a shafin nasa na Facebook:

“Lokaci shi ne abu mafi muhimmanci da ubangiji ya bamu a kullum, kuma dole muyi amfani da shi yadda ya kamata. Kamata yayi kirista ya tsarkake lokacinsa, kuma dole ne mabiyi ya rabu da komai domin ya kusanci ubangijinsa.”

Kawo yanzu dai bai rufe shafin ba, kuma an bude shafin ne tun a shekarar 2009, kamar yadda bincike ya tabbatar.

Kamfanin dillancin labarai na MENA ya kuma ce cocin Kibdawan ya ba dukkan limaman cocin wata guda su rufe dukkan shafukansu na sada zumunta domin mayar da hankali kan ayyukan ibadarsu.

Wannan matakin ya biyo bayan wasu dokoki da cocin mai suna Coptic Orthodox Church ya fitar bayan wata mutuwa mai tayar da hankali da aka yi ma wani bishof da ke ibda a wani kebabben wurin a kusa da birnin Al Kahira a ranar Lahadi.

Wasu daga cikin hane-hanen da cocin ya fitar sun hada da:

 • Dakatar da karban sabbin masu sadaukar da kansu ga ibada a kebabbun wuraren ibada na shekara guda
 • Dakatar da nade-naden sabbin limaman cocin na shekara uku
 • An hana dukkan limaman cocin shiga dukkan shafukan sada zumunta
 • An kuma hana su fita daga wuraren ibadarsu zuwa wani wuri, sai dai idan cocin ne ya bukaci su yi haka.

Mutuwar wani bishof mai suna Bishof Epiphanius ya damu hukumomi. An gano gawarsa ce da aka sareta a ka, kuma jami’an tsaro na zaton kashe shi aka yi.

Mutum 18 sun mutu a hatsarin jirgi mai saukar angulu a Rasha


Hakkin mallakar hoto
EPA/HELI.UTAIR.RU

Image caption

Hoton irin jirgin mai saukar angulu samfurin MI-8 mallakin kamfanin Utair da ya fadi

Mutum 18 sun mutu a wani hatsarin jirgin mai saukar angulu a yankin arewa maso yammacin Saiberiya na kasar Rasha, kamar yadda jami’ai daga yankin suka bayyana.

Jami’ai masu bayar da taimakon gaggawa sun ce jirgin samfurin MI-8 ya fadi ne da karfe 10 da minti 20 agogon yankin (karfe 3:20 agogon GMT) kimanin kilomita 180 daga garin Igarka da ke yankin Krasnoyarsk.

Dukkan wadanda ke cikin jirgin sun mutu – akwai matuka jirgin su uku da fasinjoji 15.

Jirgin na kan hanyarsa ta jigilar ma’aikata masu aiki a wata tashar da ake hako man fetur ne, kuma jami’an ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike.

Bayanan farko sun ce farfelolin jirgin sun daki wasu kaya da wani jirgin mai saukar angulu ke dauke da su ne jim kadan bayan ya tashi, wanda yayi sanadin fadowarsa kasa inda nan take ya kama da wuta.

Amma daya jirgin ya sami sauka babu wata matsala.

Dukkan jiragen mallakin kamfanin Utair ne wanda kuma na gwamnatin Rasha ne.

Kamfanin dillacin labarai na Rasha TASS ya ruwaito cewa tuni aka dauko bakin akwatin jirgin domin gudanar da cikakken bincike akai.

Yadda awaki suka mamaye unguwanni a Amurka


Hakkin mallakar hoto
@joshscampbell

Image caption

An ta yada hutuna da bidiyon awakin a kafafen sada zumunta na Intanet.

Fiye da awaki 100 ne suka mamaye titunan yankin Boise a jihar Idaho da ke kasar Amurka, lamarin da ba a saba gani ba a kasar.

Awakin sun balle ne daga garkensu a ranar juma’a, inda suka shiga gari suna neman abinci.

Awakin sun ja hankalin mazauna Boise inda aka wayi gari da awakin suna kiwo a cikin gari.

An ta yada hutuna da bidiyon awakin a kafafen sada zumunta na Intanet.

Wani a shafin twitter ya ce bayan shekara 30 za su ba jikokinsu labarin yadda awaki suka tsere daga garkensu suka shigo gari.

Rahotanni sun ce awakin sun balle ne da misalin karfe bakwai na safe daga garkensu bayan wadanda ke kiyonsu sun tafi gyaran wani filin kiwo.

Yara da manya a unguwarsun fito suna ta wasa da awakin, abin da ba su taba gani ba a gidajensu.

Koriya ta Arewa ta ci gaba da shirinta na nukiliya


Image caption

Rahoton ya zargi Koriya ta Arewa da yin watsi da takunkumin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar ya kakaba ma ta kan hakan

Wani sabon rahoto da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar, ya nun Koriya ta Arewa ba ta daina shirinta na kera makaman nukiliya ba, ta kuma yi biris da takunkuman da aka kakaba mata tare da saidawa wasu kasashe makamai.

Rahoton wanda kwararru suka gudanar da bincike akai sun ce abinda Koriya ta Arewa ta yi ya tabbatar da sabon takunkumin MDD akan ta.

Harwayau rahoton ya ce Arewar na hada-hadar cinikin makamai ga masu fasakwairin sa da suke saidawa ga sojin Syria, da kananan makaman a Libya da Yemen da Sudan.

Sai dai jami’an Diplomasiyyar Koriya ta Arewar ba su ce uffan kan rahoton ba da zarge-zargen da akai musu.

‘Shekarun daukewar hailar mace ba maita ko surkulle ba ne’


Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron shirin:

Daukewar jinin haila na cikin abubuwan da mata masu shekarun da suka haura hamsin suke fuskanta.

Wannan ci gaban shirin da muka fara a makon jiya ne.

Wannan al’amari dai ba maita ba ce ko surkule kamar yadda wasu mutane suke tunani a cikin al’umma.

Abu ne da ke faruwa a rayuwar mata masu manyan shekaru.

Alamomin daukewar jinin sun hada da rashin ganin jinin al’ada a kan lokaci da yawan fushi da bushewar fata da rashin barci da kuma rashin son cin abinci.

A wannan makon za mu cigaba da tattauna ne a kan daukewar jinin ga mata masu manyan shekaru.

Za mu duba matakan da mata ya kamata su dauka idan wadannan alamomi sun fara bayanna a tare da su.

Wannan cigaban shirin da muka fara a makon jiya ne.

Denmark ta ci tarar wata mata kan saka nikabi


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da haramta saka nikabi a Denmark

A karon farko Denmark ta ci tarar wata mata bayan ta karya dokar haramta rufe fuska a bainar jama’a.

Matar mai shekara 28 da ke sanye da nikabi ta hadu ne da wata mata a wani kanti a arewacin Copenhagen wacce ta nemi ta yi amfani da karfi ta cire nikabin da ke fuskar matar, lamarin da ya janyo hankalin ‘yan sanda bayan rikici ya barke a wurin.

‘Yan sanda sun caji duka matan biyu da laifin kokarin yin barazana ga zaman lafiya tare da kuma dora tarar dala dari da hamsin kan matar da ke sanye da nikabin.

Sabuwar dokar ta haifar da zanga-zanga da suka, musamman daga kungiyoyin kare hakkin dan adam a Denmark.

Kuma ra’ayi ya banbanta tsakanin al’ummar kasar, yayin da wasu ke ganin dokar ta yi daidai wasu kuma sun kira ta da sunan “bakar doka.”

A ranar Laraba ne dai dokar ta fara aiki a Denmark bayan ta samu amincewar majalisa a shekarar nan.

Sai dai dokar ba ta ambaci burka ba ko nikabi ba amma ta ce za a hukunta duk wanda aka kama ya yi amfani da mayafin da ya rufe fuska a bainar jama’a.

Wasu al’ummar musulmi a kasar sun ce ba za su mutunta dokar ba duk da akwai tara mai tsauri ga wanda aka sake kamawa ya saba dokar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mutane daga addinai da dama sun yi zanga-zanga domin nuna goyon baya ga matan da ke saka nikabi

Kasashen turai da dama ne suka haramta sa nikabi ko burqa da rufe fuska a bainar jama’a wadanda suka hada da Faransa da Austria da Bulgeria da Jamus da Bavaria.