‘Yan kama wuri zauna na tsaka mai wuya a Ghana


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana tashin mutanen da ke zaune a kusa da gidan shugaban kasar Ghana

Gwamnatin kasar Ghana, ta sanar da cewar dalilan tsaro ne suka tilasta mata tashin wasu `yan kama wuri zauna da masu shagunan da ke makwabtaka da gidan shugaban kasar.

Wannan lamarin dai na ci gaba da janyo cece-kuce a kafofin watsa labaran kasar da dandalin sada zumunta.

Masu sharhi kan al’amuran tsaro a kasar, na ganin cewa tayar da ‘yan kama wuri zaunan da ke kusa da gidan shugaban kasar, ba shi ne zai tabbatar da tsaron shugaban ba.

Masu sharhin sun ce, ba ‘yan kama wuri zauna ne kadai ke zaune a kusa da gidan shugaban kasar ba, akwai wasu gidaje da kuma cibiyoyin kasuwanci da ke kusa da ma kewayen gidan.

A saboda haka, idan ana son tabbatar da tsaron shugaban kasar, to dole a tashi gidaje da kuma cibiyoyin kasuwancin da ke kusa da ma kewayen gidan shugaban kasar, inji masu sharhin.

Tuni dai ‘yan kasar ta Ghana suka fara bayyana mabambamtan ra’ayoyi a kan wannan mataki, inda wasu ke ganin tashin ‘yan kama wuri zaunan daga kusa da gidan shugaban kasar dai-dai ne, yayin da wasu kuma ke ganin bai dace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *