Nigeria: Yadda wata mace ke sana’ar fenti a Abuja


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Lariyat

Wata sana’a da aka fi sanin maza da yi ita ce sana’ar yin fenti, amma a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, an samu wata mace da take sana’ar hadawa da kuma yi wa gine-gine fenti.

Lariat ta ce ta fara wannan sana’a ce tun a shekarar 2009, inda a yanzu haka take da kamfanin hada fenti da kuma dumbin ma’aikata.

Ta shaida wa BBC cewa ta shiga sana’ar ce a lokacin da take neman kudin da za ta yi jari don fadada sana’arta ta sayar da kayan ciye-ciye.

“Na fara wannan sana’a ce jim kadan bayan da na daina sana’ar sayar da kayan kwalam. A lokacin ina neman kudin da zan fadada sana’ata ta sayar da kayan makulashe ne sai na ji wani babban kamfanin hada fenti na neman ma’aikata da za su tallata musu hajarsu.

“Sai na sa wa raina cewa zan nemi aiki da su na shekara biyu don na tara kudin da nake nema don fadada wancan kasuwancin nawa. A sakamakon haka ne na fara son sana’ar fenti sosai.”

Lariat ta ci gaba da cewa: “Duk lokacin da na ga masu yin fenti suna yi na kan ce musu su koya mun yadda ake yi, amma sai su ce aikin maza ne ba na mata ba na je kawai na ci gaba da tallata haja da aka sa ni.

Image caption

Lariyat tana aikin hada fenti

“Amma sai na nace, har dai rannan wani daga cikinsu ya ga da gaske nake sai ya ce zai koya min. Haka kuwa aka yi shi ya dinga koya mun sosai har na iya.

A hankali kuma na iya hada fentin kansa. Bayan shekara biyu sai na ga na hada isassun kudaden da zan iya fadada waccar sana’ar tawa ta farko, sai na sahawrci wata kawata, ita kuma sai ta ce me zai hana na koma sanaar fenti gaba daya, tun da dai har na iya yi wa wani wannan aikin ai ko zan iya yi wa kaina.”

Da farko Lariyat ba ta mincewa da shawarar ba saboda tunanin shi fenti sana’a ce da ke bukatar makudan kudade.

“Don sai na samu fili da injina, kuma kudin da na hada ba za su isa ba. Amma sai ta nace cewa zan iya, babanta yana da fili da ba ya amfani da shi don haka zai iya ba ni haya.

“Dan kudin da na dade ina tarawa kuma sai na sai injinan da zan fara aiki da su.”

A yanzu haka dai za a iya cewa sam barka don kuwa tuni Lariyat likafa ta yi gaba, duk da cewa dai akwai tarin matsaloli da har yanzu take fuskanta.

Matsalolin sun hada da rashin isasshen jari har yanzu, da rashin wutar lantarki da yawan harajin da hukumomin gwamnati daban-daban ke karba da kuma yadda ‘yan Najeriya ba sa son sayen kayan da aka yi a kasarsu sai na kasashen waje.

Amma a baya Lariyar ta taba samun tallafin kudi na gwamnati na YouWin, wanda ya taimaka mata sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *