Nigeria: Shugaba Buhari zai kai ziyara Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Gwamnan jihar Yobe tare da wasu mukarraban gwamnatin jihar ne suka tarbi Shugaba Buhari a Damaturu

Nan gaba a ranar Laraba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar, don ganawa da iyayen ‘yan matan sakandaren garin da aka sace.

Shugaban zai kai wannan ziyara ne a wani bangare na rangadin da yake yi a jihohin da ke fama da rikice-rikice a kasar.

Tun da safiyar Larabar ne Shugaba Buhari ya isa Damaturu, babban birnin jihar Yobe don inda yake ganawa da shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya.

Tuni dai iyaye a garin Dapchi suka yi dafifi a makarantar da aka sace ‘ya’yan nasu inda suke jiran isar Shugaba Buharin don ganawa da su.

Wani daga cikin iyayen yaran ya shaida wa BBC cewa: “Muna jira ne shugaban ya zo ya gamsar da mutanen gari kan kokarin da gwamnati ke yi na ceto ‘ya’yansu da kuma matakan da za a dauka don hana sake afkuwar irin hakan.”

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan mata sama da 100 daga makarantar sakandaren Dapchin kuma har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Shugaba Buhari ya gana da shugabannin al’umma a Damaturu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *