Ban yi nadamar fitar da United ba – Mourinho


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Mourinho ya ce ‘yan wasansa sun taka rawar gani

Manajan Manchester United Jose Mourinho ya ce fitar da kulub din daga gasar Zakarun Turai “ba sabon abu ne.”

Dan wasan Sevilla Wissam Ben Yedder ne ya ci kwallaye biyu a ragar Manchester United a Old Trafford inda aka tashi wasan ci 2-1.

Tun doke ta a wasan karshe a 2011, sau daya Manchester United ta tsallaka zuwa zagayen kwata fainal, lokacin da Bayern Munich ta doke ta a 2014.

Mourinho wanda karo na hudu ke nan yana shan kashi a zagayen kungiyoyi 16, ya ce ” Ba zan ce ba mu taka rawar gani ba.”

Sannan ya ce bai yi nadama ba. ” Na yi iya kokari na, ‘yan wasa ma sun iya nasu kokarin, mun yi kokari amma ba mu yi nasara ba, kuma dama kwallo ta gadi haka,” a cewar Mourinho.

Sau daya ne dai Manchester United ta samu nasara a wasanni tara da ta buga a baya a irin wannan zagayen, kuma sau biyu ke nan ana fitar da kulub din a karawa uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *