Trump ya kori Rex Tillerson


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shekara daya da ‘yan watanni Rex Tillerson ya yi a kan mukamin

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori Sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson daga kan mukaminsa, sannan ya maye gurbinsa da wani jami’in hukumar leken asirin kasar, CIA Mike Pompeo.

Mr Trump ya bayyana korar ce a shafinta na Twitter, yana mai gode masa bisa aikin da ya yi wa kasar.

Ya kara da cewa sabon sakataren wajen na Amurka zai yi “kyakkyawan aiki”.

An nada Mr Tillerson, wanda tsohon shugaban kamfanin ExxonMobil ne, kan mukamin shekara daya da ta wuce.

Shugaban na Amurka ya kuma nada Gina Haspel domin zama mace ta farko da za ta shugabanci CIA.

Rahotanni sun sha nuna yadda ake rashin jituwa tsakanin Mr Trump da Mr Tillerson, musamman kan yadda suka bayar da mabambantan manufofi kan manufofin harkokin wajen kasar – kama daga batu kan Korea ta Arewa zuwa Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *