MDD: Saudia ta saukaka wa mata tafiya da muharrami


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

MDD ta bukaci a bar mata su rinka tafiye-tafiye ba tare da muharrami ba a Saudia.

Kungiyar kare hakkin mata ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga hukumomin Saudiyya, da su cire haramcin barin mata gudanar da harkokin rayuwa ciki har da yin tafiye-tafiye ba tare da muharraminsu ba.

Wata doka da Majalisar ke ganin kungiyoyin kare hakkin matan na son bijirowa Saudiyyar a shekarar da ta wuce, ta ce zai fi wa matan kasar sauki idan suka samu amincewar gwamnati a kan wani abu da ya shafi rayuwarsu, maimakon sanya muharramansu, sai dai har yanzu ana ci gaba da amfani da tsohuwar dokar a kasar.

To sai dai kuma sauye-sauyen da yarima Muhammad bin Salman, ya fara a kasar, mata sun fara samun ‘yancin zuwa kallon wasanni a filin wasa da ke kasar, sannan an dage haramcin tuka mota a gare su.

Kazalika matakin daukar mata a aikin soja na cikin sauye-sauyen da kasar ke gudanarwa a watannin baya-bayan nan, domin inganta damar mata a kasar da ake yi mata kallon mai cike da ‘tsattsauran ra’ayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *