Man United za ta karbi bakuncin Sevilla


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United tana kofin zakarun Turai uku a tarihi

Manchester United za ta karbi bakuncin Sevilla a wasa na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

A wasan farko da suka fafata a ranar 21 ga watan Fabrairu a Spaniya, kungiyoyin biyu sun tashi ne babu ci.

United bata cin kallo fiye da daya a karawa 15 baya da ta yi da kungiyoyin Spaniya, inda jumulla ta ci bakwai.

Sevilla bata ta ba cin wasa ba a gasar cin kofin zakarun Turai a Ingila, inda ta yi rashin nasara a fafatawa uku ta yi canjaras a wasa daya.

Haka kuma Roma na karbar bakuncin Shakhtar Donetsk, bayan da Shathtar ta ci wasan farko 2-1.

Duk wadda ta samu nasara za ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar shekarar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *