Buhari bai san inda ya dosa ba – PDP


Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Buhari ya ce shi da Gwamna Ortom ba za su dawwama a mulki ba

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta ce kalaman da Muhammadu Buhari ya yi cewa bai san Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar ya ki bin umarnin da ya ba shi na tarewa a jihar Benue ba sun nuna cewa gwamnatinsa ba ta da alkibla.

PDP ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

A cewar sanarwar, wacce ke dauke da sa hannun kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan, “Wadannan kalamai da shugaban kasa ya yi sun nuna cewa ya mika jagorancin kasar ga wasu tsirarun mutane da ba su yi yakin neman zabe ba, sannan ba su ‘yan Najeriya suka zaba ba.”

A farkon watan Janairu ne Shugaba Buhari ya umarci Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Mr Ibrahim Idris da ya koma da zama a jihar Benue da ke tsakiyar kasar domin magance rikicin manoma da makiyaya.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jimoh Moshood ya fitar a wancan lokacin ta ce Shugaba Buhari ya bukaci Babban Sufeton na ‘yan sanda “ya gaggauta komawa Benue domin hana bazuwar rikicin.”

Sai dai masu ruwa da tsaki a jihar sun shaida wa shugaban kasar, wanda ya ziyarci jihar ranar Litinin, cewa Mr Ibrahim Idris bai zauna a jihar kamar yadda aka bukace shi ya yi ba.

Daga nan ne Shugaba Buhari ya ce bai san cewa Babban Sufeto Janar din ya bar jihar ba sai ranar ta Litinin.

An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue

‘Yan Kungiyar IS sun shigo Nigeria — Buhari

Sufeton ‘yan sandan Nigeria ya koma Benue

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK NPF

Hakan ya sa ‘yan siyasa musamman na jam’iyyar hamayya ta PDP suka dirar wa shugaban kasar inda suka ce bai iya mulki ba.

Jihar Benue dai na daga cikin jihohin da rikici tsakanin Manoma da Makiyaya ke kara kamari.

Kalaman Buhari a Benue

Yayin ziyarar tasa Shugaba Buhari ya ce, “Ba zan kasance shugaban kasa na har abada ba, kuma Gwamna Ortom na Benue ma ba zai tabbata yana mulkin jihar ba.

“Ko bayan mun gama mulki, makiyaya da manoma za su ci gaba da zam tare da juna a Benue ko a wasu wuraren a Najeriya, kuma dole su yi aiki tare da juna. Fatanmu ne mu ga cewa an samu zaman lafiya a wannan zamantakewar.”

Shugaban ya kuma sha alwashin ganin gwamnatinsa ta kawo karshen tashe-tahsen hankulan da ake fama da su a sassan kasar.

Ya ce: “Akwai kabilu fiye da 250 a Najeriya, masu mabanbantan yare da addini. Allah ya hada mu zama tare saboda wani dalili, don haka za mu iya zama da juna lafiya.

“A bangarenmu na gwamnati ina tabbatar muku da cewa, za mu jajirce wjen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *