Nigeria: Za’a tantance matasa 300,000 a shirin N-POWER


Image caption

Shugaba Buhari ya yi alkawarin rage matsalar rashin aikin yi

A ranar Litini ne gwamnatin Najeriya ke fara aikin tantance matasa dubu dari uku da ta ce ta bai wa ayyukan yi ta hanyar shirin nan na N-POWER.

Babban mai taimaka wa shugaban kasar kan shirin na Social Investment Program Barrister Isma’il Ahmad, ya ce shirin na daya daga cikin tsarin gwamnatin Buhari na tallafa wa matasa da mata da marasa karfi.

Sai dai wannan shiri na N-Power da ake kira social investment program ya samu suka daga ‘yan kasar musamman daga arewaci da ke cewa ana fifita ‘yan kudu a kan su duk da cewa su ne suka yi uwa da makarbiya wajen zaben shugaba Buhari.

A baya dai wasu matasan da suka samu aikin N-Power, karkashin gwamnatin tarayyar Najeriya, sun shaida wa BBC cewa gwamnati ba ta yi shirin fara aikinsu ba duk da cewa ya kamata su soma aikin.

Miliyoyin matasa ne dai a kasar ke fama da rashin aikin yi.

Kuma ‘yan kasar sun zura ido domin ganin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari za ta shawo kan wannan matsala.

Magance matsalar aikin yi dai na daya daga cikin batutuwan da shugaba Buharin ya yi alkawarin magancewa lokacin yakin neman zabensa.

Kididdiga ta nuna cewa akwai kimanin matasa miliyan 70 daga cikin mutanen Najeriya miliyan 167.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *