Darajar Salah ta karu a wata shida


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salah ya ci kwallo 25 a gasar Premier shekarar nan

Darajar dan wasan Liverpool Mohamed Salah ta karu a wata shida, inji rahoton wani bincike a kan kwazon ‘yan wasan kwallon kafa a duniya, wato CIES.

Kimar dan wasan na tawagar kwallon kafar Masar ta karu ne daga fam miliyan 66.4 zuwa 144.3, kuma shi ne kan gaba a tsakanin ‘yan kwallon da ke taka leda a Turai.

Salah mai shekara 25 ne ke kan gaba a yawan cin kwallo a gasar Premier, bayan da ya ci 24.

A watan Satumbar 2017, CIES ya tantance darajar Salah a kan kudi fam miliyan 78.3, bayan da dan kwallon ya koma Liverpool da murza-leda kan fam miliyan 34.

Ga jerin ‘yan wasa 10 da darajarsu ta karu a kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo in ji CIES:

  1. Mohamed SalahLiverpool £66.4 – £162.8
  2. EdersonMan City £66.1 – £87.5
  3. Leroy Sane Man City £56 – £134
  4. Kylian Mbappe PSG £48.6 – £167.1
  5. Gabriel Jesus Man City £47.2 – £93.9
  6. Joe Gomez Liverpool £42.9 – £50.8
  7. PaulinhoBarcelona £37.7 – £46.5
  8. Davinson Sanchez Tottenham £37.5 – £68.8
  9. Sergej Milinkovic-Savic Lazio £36.2 – 62.5
  10. Florian Thauvin Marseille £34.1 – £73

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *