Carrick zai yi ritaya a karshen kakar nan


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Carrick ya ci manyan kofi 12 a shekara 12 da ya yi a Manchester United

Dan wasan Manchester United, Michael Carrick ya sanar cewar zai yi ritaya daga buga tamaula a karshen kakar nan.

Carick mai shekara 36, ya buga wa United wasa 463 tun lokacin da ya koma Old Trafford daga Tottenham kan fam miliyan 18 a shekarar 2006.

Dan wasan wanda ya fara murza-leda a matashin dan kwallo a West Ham United ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila tamaula sau 34.

Carrick ya lashe kofin Premier biyar a United da na Zakarun Turai, ya kuma zama kyaftin din kungiyar bayan da Wayne Rooney ya koma Everton da murza-leda a bana.

Dan kwallon wanda ya lashe kofin Europa a bara, ya yi shekara 12 a United ya kuma ci kwallo 22.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *