Yobe Stars ta hada maki uku a kan Kano Pillars


Hakkin mallakar hoto
NPFL

Image caption

Kano Pillars tana ta biyu a kan teburi, ita kuwa Yobe tana ta uku da maki 19

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a gidan Yobe Stars da ci 2-0 a wasan mako na 12 da suka kara a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria a ranar Lahadi.

Wannan ne karo na biyu da aka doke Pillars a gasar bana, bayan ta ci wasa biyar ta yi canjaras biyar tana kuma ta biyu a kan teburi da makinta 20.

Ita kuwa Yobe mai kwantan wasa daya tana ta uku a kan teburi da maki 19.

Ga sakamakon wasannin mako na 12 da aka yi:

  • Lobi 1-0 Katsina United
  • Wikki 3-0 Rivers United
  • FCIU 1-1 Abia Warriors
  • Kwara United 1-1 El-Kanemi
  • Tornadoes 1-0 Plateau United
  • Go Round 1-0 Sunshine Stars
  • Rangers 1-0 Enyimba
  • MFM 3-0 Heartland

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *