Barcelona ta dauki Arthur na Gremio


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ta amince ta dauki dan wasan Brazil mai taka-leda a Brazil

Ana sa ran a watan Yuli dan wasan Gremio, Arthur Henrique Ramos de Oliveira Melo zai zama dan kwallon Barcelona.

Barcelona ta amince ta biya Yuro miliyan 30 da karin Yuro miliyan 9 kudin tsarabe-tsaraben daukar dan kwallon.

Sai dai har yanzu ba a fayyace ranar da Arthur zai koma Spaniya da murza-leda ba, amma wasu rahotanni na cewar zai fara atisaye da kungiyar a Janairun 2019.

Arthur dan kasar Brazil mai wasan tsakiya zai yi wasa shekara biyar a Camp Nou.

Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 72, bayan da aka yi fafatawar mako na 28.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *