‘Yan majalisar Ghana sun ki amincewa da dakarun Amurka


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Amurka dai tana so ta ci gaba da kai dakarunta yammacin Afirka

‘Yan majalisar jam’iyyun hamayyar Ghana sun ki amincewa da yarjejeniyar da kasar ta kulla domin Amurka ta aika da dakaru da kayan yaki kasar.

A zaman da majalisar ta yi ranar Juma’a, ta amince da bukatar bangaren zartawa domin a bar Amurka ta aika da dakarun kasar, yayin da ita kuma za ta ba da $20m sannan sojinta su samu horo.

Sai dai ‘yan majalisar jam’iyyun hamayyar sun yi fatali da bukatar inda suka fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewarsu.

Sun kara da cewa yarjejeniyar za ta cutar da kasar da kuma sarayar da ‘yancinta na kasancewa kasa mai cin gashin kanta.

Amurka dai tana so ta ci gaba da kai dakarunta yammacin Afirka a yayin da mayakan da ke ikirarin jihadi ke mamaye yankin.

Congo ta yi watsi da taron agaji


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 13 ‘yan kasar ne ke matukar bukatar agaji

Jamhuriyar Demukradiyyar Kongo ta sanar da cewa ba zata halarci taron neman agaji da aka shirya yi a Geneva a wata mai zuwa ba.

An dai shirya taron ne da nufi tattara gudummuwar kusan dala biliyan biyu da Majalisar Dinkin Duniya ta ce domin a tallafa wajen shawo kan babban bala’i mafi muni na jinkai.

Sai dai Firai ministan kasar Jose Makila ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin agaji da batawa kasar sa suna.

Ya ce duk da cewa kasar sa na cikin wani yanayi, ayyana bukatar neman agajin gaggawa na sanyaya guiwar masu son zuwa kasar don su zuba jari.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce fiye da mutum miliyan 13 ‘yan kasar ne ke matukar bukatar agaji, inda kusan mutum miliyan hudu da rabi suka fice daga kasar, adadin daya rubunya wadanda suka fice a bara.

Amurka ta tuhumi Iran da ‘satar bayanan jami’o’i 320’


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana tuhumar kamfanin Mabna da satar bayanai daga jami’o’i 320

Kasar Amurka ta saka wa wani kamfanin Iran da wasu mutane 10 takunkumi domin tuhumar da take yi musu na yin kutse a na’urorin komfuta da suka hada da daruruwan jami’o’i.

Kamfanin Mabna Institute na fuskantar tuhumar cewa ya saci terabyte 31 na bayanai “masu daraja mallakin jami’o’in”.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce kamfanin ya yi wa jami’o’i 320 kutse a sassa daban-daban na duniya da suka hada da gomman kamfanoni da wasu ma’aikatun gwamnatin Amurka.

Tara daga cikin wadanda ake tuhuma na fuskantar wasu tuhume-tuhumen da ke da alaka da aikata irin wadannan laifukan.

Kuma mutane biyu da suka kafa kamfanin na cikin wadanda ake tuhumar, kuma Amurka na iya kwace kaddarorinsu.

An dai kafa kamfanin Mabna Institute ne a 2013, kuma masu shigar da kara na ganin an yi haka ne domin taimakawa Iran yin bincike da satar bayanai.

Ana tuhumar kamfanin da kai hare-hare ta yanar gizo zuwa jami’o’i 144 a cikin Amurka da 176 a wasu kasashen daban.

Kasashen sun hada da Birtaniya da Jamus da Kanada da Isra’ila da kuma Japan.

Fursunoni sun kammala digiri a gidan yari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kimanin fursunoni dubu biyar ne a Uganda suka yi rijistar yin karatun a fannonin dabam dabam

A kasar Uganda wasu fursunoni uku sun samu shaidar digiri kammala karatun lauya daga wata jami’a dake London.

An dai ba fursunonin takardar shaidar kammala karatun su a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a gidan yari dake birnin Kampala.

Daya daga cikin fursunoni uku mace ce, wacce aka yankewa hukuncin daurin rai da rai amma daga bisani ta yi nasarar kalubalantar hukuncin da aka yanke mata.

An dai bayyana cewa matar ta kammala karatun ta na digiri ne ba tare da taje aji an koyar da ita ba, inda a mafi yawan lokuta ta rika yin karatun ta karkashin bishiya a gidan yarin.

Kimanin fursunoni dubu biyar ne a Uganda suka yi rijistar yin karatun a fannonin dabam dabam, kuma ana kallon bangaren kula da gidajen yari na kasar a matsayin mafi ci gaba a nahiyar Afrika.

Buhari ya yiwa ‘yan Boko Haram tayin afuwa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tayin afuwa ga mayakan Boko Haram idan suka amince za su ajiye makamansu.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Juma’a lokacin da ‘yan gana da ‘yan matan sakandaren Dapchi da mayakan na Boko Haram suka sako a fadarsa.

Shugaban kasar ya ce tashin hankalin da kasar ke ganin ya ishe ta haka.

Shugaba Buhari ya kuma gargadi hukumomin tsaron kasar da su tabbatar sun samar da cikakken tsaro a duk makarantun da ke fuskantar barazanar harin daga masu tayar da kayar baya.

A wata hira da BBC ministan harkokin cikin gida na Najeriyar Abdurrahman Bello Dambazau ya ce za’a dauki kwararan matakai na ganin an aiwatar da umarnin shugaban kasar.

Gidan yarin da ake tarairayar fursunoni


Mutanen da ake tsare da su za su iya yin kida, suna koyon kafintanci, sannan su suke girka abincin da suke son ci, wanda hakan tamkar basu horo ne na irin rayuwar da ya kamata su yi idan sun fita waje.

Duk da sukar da ake yi cewa jin dadin da ake yi a gidan yarin ya yi yawa, a duniya Norway ita ce kasar da ta fi samun nasarar raguwar mutanen da suke komawa aikata laifuka idan sun fita daga gidan kaso.

Buhari ya gana da dalibai 107 da aka sako


Hakkin mallakar hoto
ISAAC LINUS ABRAK

Image caption

Wani mahaifin ‘yar makarantar Dapchi na share hawayen murnar sakin matan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan matan makarantar sakandaren Dapchi da aka sako ranar Laraba.

Ya yi ganawar ce a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

A jawabinsa lokacin ganawar, Shugaba Buhari ya ce “Ina farin cikin sanar da ‘yan Najeriya da abokanmu na kasashen waje da kuma wadanda muke hada gwiwa da su cewa an saki ba tare da sharadi ba dalibai 107, 105 daga cikinsu ‘yan matan makarantar Dapchi da kuma mutum biyu da a baya aka sace.”

Ya kara da cewa sakin matan – bayan da ya umarci jami’an tsaron kasar su tabbatar babu abin da ya same su – abin farin ciki ne.

Shugaba Buhari ya sha alwashin ganin an sako daliba daya da ta rage a hannun mayakan Boko Haram da kuma ‘yan matan Chibok da aka sace tun 2014.

Ranar Laraba aka sako ‘yan matan, wadanda aka sace a watan jiya.

Mahaifin daya daga cikin ‘yan matan, Kundili Bukar, ya gaya wa BBC cewa wasu mutane da ake tsammani ‘yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci.

Abin da ya faru tun sace ‘yan Matan

Hakkin mallakar hoto
GGSS

 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace ‘yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace ‘yan matan
 • Da farko an ce ‘yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto ‘yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace ‘yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace ‘yan matan ba
 • Sace ‘yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da ‘yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

A cewarsa, sun ajiye su ne kawai suka tafi kuma ‘yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam’iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan domin cimma wata bukata ta siyasa.

Sai dai APC ta musanta zargin.

A watan jiya aka sace matan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami’an tsaron Najeriya.

A wancan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace ‘yan matan a matsayin wani bala’i da ya shafi kasar baki daya.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Bayanan da ku ke bukatar sani kan ‘yan matan Dapchi


‘Yan Najeriya sun yi ta murna da farin ciki sakamakon sako ‘yan matan makarantar sakandaren Dapchi da Boko Haram ta sace, ta kuma dawo da su ranar 21 ga watan Maris.

An mayar da yaran garinsu ne a ranar Laraba da misalin karfe 3 na tsakar dare.

Sai dai har yanzu akwai sauran yarinya daya mai suna Leah Sharibu, da mayakan kungiyar ba su mayar da ita ba, tana hannunsu.

Amma kuna da labarin duk abun da ya faru tun farkon lamarin?

Kuna iya duba wannan kalandar da ke kasa tare da ci gaba da latsa gaba don samun cikkkun labarai da rahotannin yadda abubuwa suka yi ta wakana.

 • Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai hari a makarantar sakandaren mata ta kwana a Dapchi jihar Yobe da ke arewa maso yammacin Najeriya.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe inda ta nemi afuwa kan sanarwar da ta bayar cewa sojoji sun ceto ‘yan matan Dapchi.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana sa ce ‘yan matan sakandaren Dapchi a matsayin wani bala’i da ya shafi kasa baki daya.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Rundunar Sojin sama ta sanar da tura jiragen yaki da karin dakaru domin bincike da kuma ceto ‘yan matan da aka sace.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • An samu sa’insa tsakanin Sojoji da ‘Yan sanda kan wadanda alhakin tsaron Dapchi ya rataya a kan wuyansu, inda ‘yan sanda suka ce ba da saninsu sojoji suka fice ba.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Majalisar wakilai ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike game da yadda aka sace ‘yan matan sakandaren garin Dapchi.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta zabi ta sasanta da Boko Haram maimakon yin amfani da karfin soja domin ceto ‘yan matan a raye.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Kafar yada labarai ta Amurka ta Wall Street Journal, WSJ, ta ce ta samu bayanan da suka tabbatar mata da cewa bangaren Abu Musab Abu Musab al-Barnawi ne suka sace ‘yan matan 110.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da yin biris da gargadin cewa ‘yan Boko Haram za su kai hari sa’o’i kalilan gabannin a sace ‘yan matan sakandaren Dapchi sama da 100, zargin da sojojin suka musanta.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta biya kudin fansa domin a saki ‘yan Matan makarantar sakandaren garin Dapchi da Boko Haram ta sace.

  Za ku iya karanta karin a nan.

Dan bindiga ya yi garkuwa da mutane a Faransa


Hakkin mallakar hoto
Google Maps

Wani dan bindiga ya yi garkuwa da mutane da dama a cikin wani babban kanti da ke Trèbes a kudancin Faransa.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce tun da farko sai da mutumin ya bude wuta kan wasu ‘yan sanda da ke motsa jiki, inda ya yi musu rauni, ko da yake ba shi da girma.

‘Yan sanda sun garzaya babban kantin mai suna Super U da ke Trèbes kusa da Carcassonne.

Wanimai daukaka kara ya ce dan bindigar ya yi ikirarin cewa shi dan kungiyar Islamic State ne. A watan Janairun 2015 wani dan bindiga ya kashe mutum hudu a wani babban kanti da ke Paris.

Fira Minista Édouard Philippe ya ce lamarin na da “girma”. Kafofin watsa labaran kasar sun ce dan bindigar ya kashe mutum daya amma hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.

An girke daruruwan ‘yan sanda a wurin sannan aka toshe hanyar da ke zuwa kantin.

An soma shirin tsige shugaban kasar Zambia


Hakkin mallakar hoto
AFP

Mambobin jam’iyyar hamayya ta Zambia sun gabatar da wani kudurin doka a zauren majalisar da zummar tsige shugaban kasar Edgar Lungu.

Kusan kashi uku cikin hudu na ‘yan majalisar karkashin jam’iyyar United Party for National Development ne suka sanya hannu kan kudurin dokar, wanda aka gabatar a gaban majalisar ranar Alhamis.

Wasu daga cikin mutanen da suka sanya hannu kan kudurin sun hada da tsofaffin ministoci Chishimba Kambwili da Harry Kalaba, wadanda mambobin jam’iyya mai mulki ne.

‘Yan majalisar sun ce sun dauki matakin ne saboda rashin iya aiki da kuma cin hanci da suke zargin shugaban kasar da aikatawa.

Sai dai kakakin shugaban ya yi watsi da zarge-zargen.

Tuni harkokin siyasar Zambia suka dauki dumi duk da yake ba za a yi zaben shugaban kasa ba sai 2021.

An takaita sadaki a Jamhuriyar Nijar


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kafa dokoki domin saukaka wa mutane aure a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, masarautar Damagaram ta bi sahun takwararta ta Azbin tare da amincewar al’ummar yankin ta kafa wasu dokoki domin saukaka aure, wadanda suka hada da kayyade kudin sadaki, da hana anko da takaita gara da kuma jerin gwanon ababan hawa ana wasan ganganci wajen kai amarya.

Haka kuma masarautar ta Damagaram, ta hana shan tabar nan ta ruwa wato shisha da matasa ke yi a fadin jihar.

Sarkin garin mai martaba Alh. Abubakar Sanda, ya sanar da hakan a yayin wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a jihar da ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyin mata, inda ya ce an dauki wannan mataki ne bayan jama’ar garin sun kai kukansu ga masarautar, a kan a nema musu sauki a al’amuran da suka shafi aure da suna da kuma wasu bidi’oi da ake yi a jihar.

Mai martaba sarkin na Damagaram, ya ce sun yi nazari a kan wannan koke, don haka yanzu aka sanya doka saboda la’akari da cewa dukkan wadannan abubuwa da jama’ar garin suka mayar bidi’a, abubuwane da addini ya hana su.

Kazalika mai martaba sarkin ya ce, irin wadannan bidi’ar, kan sa idan ta zo kan mutum, wani lokaci sai an ci bashi domin a yi abin da zai faranta wa jama’a.

Yanzu haka, masarautar ta Damagaram ta kayyade sadakin aure daga jaka 20 na CFA zuwa jaka 50, kuma an hana kai amarya a cikin jerin gwanon motoci, sannan an takaita gara da ma hana ankon biki kwata-kwata.

A bangaren lafiya kuma, masarautar ta Damagaram, ta hana shan tabar shisha kwata-kwata bisa shawarwarin likitoci, saboda a cewar masarautar, likitoci sun ce yawanci matasa na kamuwa da cutukan da suka danganci huhu ko tari sakamakon shan shishar.

Matasan garin dai sun bayyana jin dadinsu ga wadannan sabbin dokoki, musamman dokar takaita kashe kudade a yayin aure,inda suka ce da yawa daga cikinsu na son suyi aure, to amma idan suka tuna irin kudin da za su kashe, jikinsu kanyi sanyi.

Masarautar Azbin ma dai a Jamhuriyar ta Nijar, ta dauki irin wannan mataki na hana bidi’a ya yin biki ko suna.

Europol sun kama masu safarar mata dan yin karuwanci


Image caption

Tun a watan Nuwamba aka fara gudanar da binciken da tattara bayanai, ba a fitar da rahoto ba sai a yanzu saboda gudun kawo cikas a binciken da suke yi

Hukumar ‘yan sandan turai Europol, sun ce jami’an tsaron kasa da kasa sun gano wasu gungun masu aikata laifi a Nigeria.

Mutanen dai na wata kungiya ne mai suna The EIYE brotherhood da ke safarar mutane a ciki da wajen kasashen turai.

Europol ta ce aikin hadin gwiwa da kasashen Birtaniya da Sifaniya da kuma Nigeria, ka na da hukumomin da lamarin ya shafa ne ta kai ga yin wannan nasara.

Tuni kuma aka cafke mutane kusan 90, ya yin da aka kubutar da wasu mata da ‘yan mata 39 da aka tilastawa yin karuwanci a kasashe irin Italiya da Sifaniya.

Matan dai sun bayyana sai da aka yi musu sihirin Voodoo a Najeriya dan su bada hadin kai.

Kuma tun a watan Nuwambar bara aka yi wannan samame amma bayanai ba su fito ba sai a dan tsakanin, hakan ta faru ne sakamakon gujewa yin katsalandan a binciken.

Jirgin India ya wuce sararin Saudiyya zuwa Isra’ila


Image caption

Wannan shi ne karon farko da wani jirgi ya yi amfani da sararin Saudiyya zuwa kasar Isra’ila

A wani mataki da ba safai ake gani ba, kuma mai cike da tarihi a karon farko jirgin sama mallakar India ya sauka a kasar Isra’ila da hanyar keta sararin samaniyar Saudiyya.

Ministan sufirin Isra’ila Yisrael Katz ya ce Air India ya taso ne daga birnin Delhi zuwa Tel Aviv, kuma shi ne na farko a hukumance ya fara sufuri daga kasarsa da Saudiyya wadda sam ba ta amince da Isra’ila ba.

Jirgin El Al dai ba ya sauka ko keta sararin Saudiyyar, dan haka ake ganin jirgin India zai bude sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shi ma ministan yawon bude ido na kasar Yariv Levin ya ce amfani da sararin Saudiyya zai rage lokacin tafiya da sa’a biyu, da kuma rage kashe kudade.

Buhari ya lashi takobin kubutar da ‘yar Dapchin da ta rage


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin kubutar da ‘yar Dapchin da ta rage

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya lashi takobin cewa zai dukufa wajen ganin an ceto yarinya daya tilo da ta rage daga cikin yammatan makarantar Dapchi 110 da aka sace, kamar yadda ya yi a lokacin da suke hannun ‘yan Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na musamman a kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, gwamnatin shugaba Buhari, ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ganin ta ceto tare da dawo da Leah Sharibu, gida wajen iyayenta lami lafiya, kamar yadda aka ceto sauran yammatan, bayan da ‘yan ta’addar suka rike ta kamar yadda aka rawaito cewa saboda ta ki yar da ta musulunta ne.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari, na cike da sanin nauyin da ya rataya a wuyansa, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadi ya kare dukkannin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin addininsu ko kabilarsu ko kuma yankin da suka fito ba, kuma ba zai gajiya ba wajen sauke wannan nauyi.

Kazalika sanarwar ta ce, shugaban na sane da fadar cewa, dukkannin musulmai na gaskiya a fadin duniya, suna martaba ka’idar nan da ke cewa babu tilas a addini.

A dangane da haka, babu wani mutum ko wata kungiya da za ta tilasta addininta a kan wani.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugaban na Najeriya, na cike da alhini ga iyayen wannan yarinya, wadanda za su rinka kallon sauran takwarorinsu da aka sako ‘ya’yansu na murna, yayin da su kuma ‘yarsu har yanzu ba ta tare da su.

Daga karshe sanarwar ta ce, shugaba Buhari, ya jaddada cewa ba za a yi watsi da wannan yarinya da ta rage ba, kuma nan bada jimawa ba, iyayenta za su kasance cikin murna tare da ‘yarsu.

A watan jiya ne dai aka sace yammatan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami’an tsaron Najeriya.

A ranar Jumma’a ne ake kyautata zaton shugaba Buharin, zai karbi yammatan na Dapchi a fadarsa da ke Abuja.

‘Yan wasan da ke kan gaba a cin kwallo a Turai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salah ne kan gaba da kwallo 28 a gasar Premier Ingila

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware wannan makon a matsayin ranakun da kasashe za su buga wasannin sada zumunci a tsakanin su.

Hakan ne ya sa ake yin hutu a manyan gasar kasashen Turai, inda wasu ‘yan wasa ke kan gaba a cin kwallaye.

Mohammed Salah ne ke kan gaba a Premier da kwallo 28, bayan da aka yi wasa 31 a gasar, kuma shi ne na daya a Turai.

A spaniya kuwa, bayan da aka yi wasannin mako na 29, Lionel Messi na Barcelona ne da kwallo 25 ke kan gaba.

A kasar Italiya an kammala wasannin mako na 29 a gasar Serei A, inda Ciro Immobile na Lazio ne kan gaba da kwallo 24.

A jamus kuwa Robert Lewandowski ne na daya dan wasan Bayern Munich, bayan da ya ci 23, bayan da aka buga karawar mako na 27.

An buga wasannin mako na 31 a gasar cin kofin kasar Faransa, inda Edison Cavani ne ke kan gaba da kwallo 24 a raga.

APC ta mayar wa PDP da martani kan ‘yan matan Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Buhari na shan suka da yabo kan ‘yan matan Dapchi

Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya ta mayar wa da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da martani kan batun ‘yan matan Dapchi da aka sako bayan an sace su.

Jam’iyyar APC ta ce PDP ba za ta iya ganin duk wani abin kirkin da gwamnatinsu ke aikatawa ba saboda hamayya ta rufe mata ido.

Wannan dai martani ne ga furucin da PDP ta yi cewa APC ta shirya dodo-rido ne wajen sace `yan matan sakandaren Dapchi da kuma ceto su da nufin farfaganda, ganin babban zabe na karatowa.

Alhaji Maimala Buni sakataren jam`iyyar APC na kasa ya shaida wa BBC cewa wutar-ciki cce ke damun PDP, kasancewar APC ta yi abin da ya gagare su lokacin da suke mulki.

A ranar Laraba 21 ga watan Maris ne ‘yan Boko Haram suka shiga garin Dapchi suka mayar da ‘yan mata 105 da wani yaro daga cikin mutum 110 da suka sace a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Har yanzu ba a san makomar sauran ‘yan matan biyar ba da ba a gani ba bayan sakin sauran. Ko da yake wasu daga cikin wadanda aka sako sun ce sauran mutuwa suka yi.

Tun sace ‘yan matan ne dai gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari ta yi alkawalin za ta ceto ‘yan matan da ransu.

Bayan an sako ‘yan matan ne Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi zargin cewa jam’iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan Dapchi 110.

Wata sanarwa da kakakin PDP Kola Ologbondinyan ya aike wa manema labarai ta ce “APC da wasu jami’an fadar shugaban kasar ne suka shirya sace matan domin cimma wani buri na siyasa.”

Amma a lokacin da yake mayar da martani, sakataren jam’iyyar APC ya ce, “borin kunya ne PDP ta ke domin a lokacin mulkinta ne aka soma rikicin Boko Haram.”

Ya kuma ce: “wannan wani batu ne da ya kamata jami’an tsaro su nemi karin bayani daga jam’iyyar PDP a kan me suke nufi da shiri ne aka yi”.

Ra’ayin ‘yan Najeriya dai ya sha bam-ban kan rawar da gwamnatin kasar ta taka wurin dawo da ‘yan matan sama da 100 da Boko Haram ta sace a Dapchi.

A yayin da wasu da dama ke yabon gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jajircewa wajen cika alkawarin da ta dauka na ganin ta ceto yaran, wasu kuwa a kasar shakku suka nuna a kan wannan lamari.

Wannan batu dai zai ji gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya a ciki da wajen kasar har zuwa wani lokaci.

Iniesta bai yanke makomarsa a Barcelona ba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Iniesta ya buga wa Barcelona wasa 434 ya ci kwallo 35

Watakila kungiyoyin Premier suyi rububin daukar Andres Iniesta, bayan da ya sanar cewar bai yanke hukuncin barin Barcelona ko zama a kungiyar a karshen kakar shekarar nan.

Dan wasan mai shekara 33, wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar rai da rai a Nou Camp a watan Oktoba, ya ce ba shi da tabbaci idan zai iya saka kwazon da kungiyar ke bukata.

Ana alakanta Iniesta da cewar zai koma buga gasar kasar China, kuma watakila kungiyoyin Ingila za su so daukar kwararren dan wasan da ya gwanan ce wajen buga wasan tsakiya.

Iniesta zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Spaniya wasan sada zumunta da za ta yi da Jamus da kuma Argentina.

Dan wasan ya buga wa Barcelona wasa 33 a kakar shekarar nan.

Ibrahimovic zai bar Manchester United


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ibrahimovich ya ci wa United kwallo 29 a wasa 53 da ya yi mata

Dan wasan Manchester United, Zlatan Ibrahimovic na shirin barin kungiyar tun kafin yarjejeniyarsa ta kare a Old Trafford.

Babu wata sanarwa daga United, amma an ce Jose Mourinho ya amince Ibrahimovich ya bar kungiyar tun kafin kwantiragin da ya saka hannu da za ta kare a ranar 30 ga watan Yuni ta cika.

Har yanzu ba a fayyace inda Ibrahimovich zai koma da murza-leda ba, amma ana rade-radin cewar zai koma buga gasar Amurka a kungiyar LA Galaxy.

Ibrahimovich mai shekara 36, ya koma United daga Paris St-German a shekarar 2016.

Tshohon dan wasan tawagar kwallon kafar Sweden ya ci kwallo 29 a karawa 53 da ya yi wa United, amma har yanzu bai warke daga raunin da ya ji a wasa da Anderlecht a watan Afirilu ba.

Sanchez ya bukaci hutu daga Chile


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester United tana ta biyu a kan teburin Premier

Dan wasan Manchester United, Alexis Sanchez, ya ziyarci sansanin tawagar kwallo kafar Chile a shirin da take yi na buga wasan sada zumunta da Sweden.

Sanchez ya nemi a sawwake masa buga wasan, saboda rashin taka rawar gani tun komawarsa United da taka-leda a watan Janairu.

Dan wasan mai shekara 29, kwallo daya kacal ya ci a wasanni 10 da ya buga wa United tun komarsa Old Trafford daga Arsenal.

Sanchez ya ce, ”Tun zuwa na United ina shan wahala saboda sauyin yanayin da na tsinci kaina a ciki”.

Dan wasan ya yanke shawar bin tawagar Chile zuwa Sweden, bayan ya nemi shawarar abokin wasansa, mai tsaron ragar Manchester City Claudio Bravo.

Haka kuma Sanchez ba zai buga wa Chile wasan sada zumuntar da za ta yi da Denmark a ranar Talata ba.

Shugaba Buhari na ziyara a Zamfara


Hakkin mallakar hoto
BUHARI SALLAU

Image caption

Buhari ya aike da sojoji Zamfara

Shugaban Najeriya Muhammadu na ziyara a jihar Zamfara da ke aracin kasar ranar Alhamis.

Yana je jihar ne a ci gaba da ziyarar da yake kai wa jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro.

A makon jiya ne shugaban na Najeriya ya kai ziyara jihohin Taraba, Benue da Yobe wadanda ke fuskantar kabulaben tsaro.

Fadar shugaban kasar ta ce shugaban na ganawa da shugabannin yankuna daban-daban na jihar da kuma masu ruwa da tsaki.

Jihar Zamfara na fuskantar kalubalen rashin tsaro a baya bayan nan.

Ko da a watan jiya sai da Shugaba Buhari ya bayar da umurnin gaggauta tura sojoji zuwa jihar bayan wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.

Wani dan majalisar dattawan Najeriya da ke wakiltar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya yi zargin cewa gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya san ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar amma ya ki daukar mataki a kansu.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan zargi ba shi da kanshin gaskiya.

A farkon watan nan gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe Buharin Daji, mutumin da ake zargi da jagorantar barayin shanun da suka addabi jihar da hare-hare.

Biciken da ake yi min ya sanya ni cikin kuncin rayuwa — Sarkozy


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mr Sarkozy ya ce ana zarginsa ba tare da kwakkwarar hujja ba

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya ce zarge-zargen da ke yi masa cewa ya karbi tallafin kudi daga wurin tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi domin yin yakin neman zabe sun sa yana ji tamkar yana rayuwa a “jahannama”.

Mr Sarkozy ya shaida wa wata kotun majistiret cewa “Ana zargi na ba tare da wata kwakkwarar hujja ba”a lokacin da ake bincikensa, in ji jaridar Le Figaro.

Ana bincikensa ne kan karbar kudin da suka haramta domin yakin neman zaben 2007, da kashe kudin kasar Libya ba bisa ka’ida ba da kuma cin hanci.

Mr Sarkozy, mai shekara 63, ya musanta aikata laifi.

Dan siyasar, wanda aka sallama ranar Laraba bayan an kwashe kwana biyu ana yi masa tambayoyi, ya ce masu zarginsa daga Libya na yin hakan ne domin yin ramuwar gayya saboda matakin da ya dauka na aikawa da jiragen yakin Faransa lokacin boren da ya yi sanadin tumbuke Gaddafi daga kan mulki a 2011.

‘Yan sanda sun yi tambayoyi ga daya daga cikin tsofaffin ministoci kuma na hannun daman Mr Sarkozy, Brice Hortefeux, ranar Talata.

Ranar Alhamis, Le Figaro ta wallafa cikakken bayanin da ta ce Mr Sarkozy ya yi wa masu bincike na Faransa cikin harshen Faransanci.

A cikin bayanin, ya ce yana sane cewa zarge-zargen da ake yi masa “manya” ne, amma ana yi masa ne kawai domin a “bata” masa suna kuma hakan ya sa yana ji kamar yana rayuwa cikin jahannama tun 11 ga watan Maris din 2011, lokacin da Gaddafi ya yi zargin karon farko.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mr Sarkozy ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Libya da Faransa a 2007

I

Mutanen da suka kashe Musulmi za su sha daurin rai da rai a India


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akwai kungiyoyi da dama da ke sa ido kan masu safarar shanu a India

Wata kotun jihar Jharkhand da ke India ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan mutum 11 saboda samunsu da hannu kan kisan wani Musulmi mai tallan naman shanu a bara.

Mutanen sun lakadawa Alimuddin Ansari, mai shekara 55, dukan tsiya har sai da ya mutu saboda yana safarar naman shanu.

Wannan ne karon farko da kotun India ta daure mutanen da ke sanya ido kan masu cin naman shanu, duk da cewa an kwashe shekara da shekaru ana kai hari kan Musulmin da ke sayar da naman.

Mabiya addinin Hindu na kallon saniya a matsayin wata halitta mai tsarki kuma an haramta kisanta a jihohi da dama na kasar, ciki har da jihar Jharkhand.

Sau da dama masu sanya ido kan masu cin naman shanu suna kai hari kan maciya naman shanun da masu sayar da shi a India, kuma ko da ‘yan sadan sun yi bincike ba safai suke hukunta mutane ba.

Shekara guda da kai harin gadar London


Image caption

Maharin ya bi ta kan mutanen da ke tafiya akan gadar da mota, daga bisani ‘yan sanda suka harshe shi

A ranar Alhamis ne za a fara addu’ar cika shekara guda ga wadanda suka mutu ko jikkata a harin ta’addancin da aka kai gadar Westminsters da ke birnin London shekarar da ta wuce.

Mutane 5 ne suka rasu ciki har da dan sanda daya. ‘Yan majalisa za su yi shiru na minti guda, duk dai a wani bangare na tunawa da mamatan.

A shekarar da ta gabata ne matashi Khaled Masood (Mas’oud)ya afka kan mutanen da ke tafiya da kafa akan gada.

Daga bisani kuma ya sauka ya na sukar mutane da wukar da ke hannunsa yayin da ‘yan sanda suka bude masa wuta ya mutu nan ta ke.

A watan Yuli ma wasu mahara uku sun hallaka mutane 7 da jikkata wasu da dama a kusa da gadar birnin London.

Har wa yau a dai wannan watan, wani mahari da ya afkawa mutanen da ke salla a wajen wani masallaci kuma mutum guda ya rasu.

An daure ‘yar Palasdinu don ta mari sojan Isra’ila


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ahed Tamini ta isa kotun da aka yanke mata hukunci ne sanye da kayan fursunoni

An yanke wa wata matashiya ‘yar kasar Palasdinu mai kimanin shekara 17, hukuncin zaman gidan kaso na tsawon wata takwas, saboda ta mari wani sojan Isra’ila.

Wannan lamari dai ya ja hankalin mutane da dama a sassan duniya bayan da aka wallafa hoton lamarin a kafar intanet, inda aka nuna Ahed Tamini, ta tunkari sojojin a kofar gidanta a watan Disambar da ya gabata.

An sanya wa Ahed Tamini, ankwa a kafarta, inda kuma ta ke sanye da kayan da fursunoni ke sanyawa a lokacin da ake tafiya da ita zuwa wata kotun soji.

Bayan isar su kotun, ta daga wa ‘yan uwanta hannu tare da cewa ba bu adalci a wannan aiki na shari’a.

Yarinyar dai ta amince da wata yarjejeniyar amsa laifi, wadda a karkashinta za a zartar mata da daurin watanni takwas a gidan yari.

Kafofin yada labarai na Isra’ila sun ce, an rage tuhume-tuhumen da ake yi wa Ahed Tamimi, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da ke bukatar amincewar kotun soja.

Kazalika yarinyar, ta zama wata alama ta gwagwarmayar Palasdinawa, an kuma dauki hotonta ne a kofar gidansu ta na kalubalantar wasu sojojin Isra’ila biyu masu dauke da makamai.

Yawancin ‘yan kasar Isra’ila sun goyi bayan sojojin inda suke ganin laifin yarinyar, tare kuma da zargin iyayenta da goyon bayanta, suna masu cewa an sha kyaleta a lokuta da dama ta na tsigale sojojin Isra’ilan.

Hotunan bikin bude ofishin BBC na Afirka Ta Yamma a Lagos


Ga wasu zababbun hotuna na bikin kaddamar da sabon ofishin BBC a Afirka Ta Yamma da ke birnin Lagos a kudu maso yammacin Najeriya.

BBC ta kaddamar da sashen Afirka ta yamma a birnin Lagos na Najeriya, wanda ya kunshi manyan harsunan kasar guda hudu.

Hakkin mallakar hoto
Google

Mutane dada kabilun kasar daban-daban sun halarci kaddamar da katafaren ofishin da yake unguwar Ikoyi a babban birnin kasuwancin Najeriya.

Bikin kaddamar da sashen na zuwa bayan BBC ta bude sassa biyu na harsunan Igbo da Yoruba a ranar 19 ga Fabrairun da ya gabata.

A bara ne kuma BBC ta bude sashen Pidgin a Lagos, domin mutanen da ke magana da turancin buroka.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan al’amuran watsa Malam garba Shehu ya samu halartar bikin, tare da tsohon editan sashen Hausa na BBC Mansur Liman.

Yanzu sabon sashen na yammacin Afirka ya kunshi sashen Hausa da Yoruba da Igbo da kuma Pidgin, duka a Najeriya.

Image caption

Peter Okwoche da Bilkisu Labaran suna gabatar da tsare-tsaren bikin

Sabbin sassan da sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar, ya kasance shirinsa mafi girma tun shekarun 1940, sakamakon kudin da gwamnatin Birtaniya ta bai wa sashen a shekarar 2016.

An shirya gagarumin biki a Lagos domin kaddamar da reshen na Afirka ta yamma.

Daga kasa hoton tawagar ma’aikatan sashen Hausa na BBC ne da suka halarci kaddamar da ofishin.

Daga hagu Halima Umar Saleh ce, sai Aliyu Tanko da Jimeh Saleh editan BBC Hausa, da Isah Sunusi tsohon ma’aikacin BBC da NAziru Mika’ilu da Haruna Tanagaza, da Farima Othman da Ummulkhairi Saleh (masu bautar kasa), da Yusuf Ibrahim Yakasai da Abdussalam Ibrahim Ahmed da kuma wakilinmu na Lagos Umar Shehu Elleman.

Buhari na shan yabo da suka kan ‘yan matan Dapchii


Hakkin mallakar hoto
Sahara Reporters

Muhawara ta barke a shafukan sada zumunta na Najeriya sa’o’i kadan bayan da mayakan kungiyar Boko Haram suka sako mafi yawan ‘yan matan makarantar sakandaren Dapchi 110 da suka sace ranar 19 ga watan Fabrairu.

A yayin da wasu da dama ke yabon gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jajircewa wajen cika alkawarin da ta dauka na ganin ta ceto yaran, wasu kuwa nuna shakku suke a kan wannan lamari.

Da dama sun yi ta wallafa ra’ayinsu a shafukan Twitter da Facebook, inda suke cewa tun farko sace yaran ma ‘kitsa’ shi gwamnatin ta yi don neman farin jini wajen jama’a.

Wasu kuwa sun yi ta yaba wa kokarin gwamnatin ne amma a hannu guda kuma suna kira gare ta da ta dauki matakan magance faruwar irin haka a gaba.

JJ Omojuwa wani fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta ne a Najeriya, ya kuma wallafa a shafinsa na Twitter cewa: Ya kamata a ce an dauki lokaci kafin a dawo da yaran idan aka yi la’akari da matakan hanyoyin da za a yi hakan. Abu ne mai kyau a san me gwamnati ta bayar ko ta yi a wannan karon kafin a sako yaran nan.

”Mun ji dadin dawowarsu amma ka da mu manta da daukar mataki don gudun sake afkuwar hakan a gaba.”

Wasu kuwa da dama tababa suke kan yadda Boko Haram suka shiga garin Dapchi ido na ganin ido suka mayar da yaran nan, ba tare da jami’an tsaro sun tare su ba.

Kemi Ariyo @d_problemsolver ya rubuta cewar: “Boko Haram suka taho tun daga dajin Sambisa har garin Dapchi don mayar da yaran nan kuma a ce ba wanda ya gansu?

“Lallai ga alama batun Boko Haram da na rikicin Fulani da Makiyaya duk farfagandar siyasa ce. Abun takaici!”

Sai dai wani ma’abocin amfani da shafin Facebook Sheriff Almuhajir ya yi wani batu mai kamar martani ga maganar Mista Ariyo inda yake cewa: “Wai wasu sun dauka tunda Boko Haram sun kawo ‘yan mata kawai sai a kama harbe su.

“Hmmmm! Kun dauka su Boko Haram mahaukata ne za su kawo su haka kawai babu sharadi, shiri ko togaciya? Ina jin wasu mutanen ta hanci suke tunani.”

Dr Aliyu Tilde kuwa yabo da jinjinawa ya yi wa Shugaba Buhari kan ceto ‘yan matan.

Ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa: “Wannan lamari ne mai dadi ga iyayen yaran sannan abun a jinjinawa Shugaba Buhari ne, wanda ya yi barazanar gurfanar da kwamandojin sojin a gaban kotun sojoji.”

A ganin Dr Tilde ko da fansa aka biya aka karbo yaran, to hakan ya fi don su dawo gida da wuri maimakon a tsaya jiran shekaru.

Hakkin mallakar hoto
JIM WATSON

Ya kara da cewa a ganinsa ko da fansar aka biya, iyayen yaran za su zabi haka fiye da zama cikin zulumi.

A karshe ya bai wa gwamnati shawarar cewa ya kamata ta kara tsaurara tsaro a yankin arewa maso gabas ta yadda mayakan Boko Haram ba za su iya amfani da injin fidda kudi na ATM ba.

Wannan batu dai zai ji gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya a ciki da wajen kasar har zuwa wani lokaci.

Sai dai a yayin da aka samu damar ceto ‘yan matan na Dapchi, har yanzu akwai sauran ‘yan matan sakandaren Chibok da aka sace tun 2014 a hannun mayakan Boko Haram, duk da cewa fiye da rabinsu sun dawo.

Sharhi: Daga Tomi Oladipo, wakilin BBC kan sha’anin tsaro a Afirka

Dawowar ‘yan matan Dapchi da aka sace ya nuna cewa Boko Haram ta sauya salo karkashin jagorancin Abu Musab al-Barnawi.

Kungiyar masu tayar da kayar bayan dai ta kasu biyu, daya karkashin shugabancin Abubakar Shekau daya kuma karkashin al-Barnawi, wanda kungiyar IS ke marawa baya.

A baya, Shekau ya ki yarda ya sasanta da gwamnatin Najeriya, musamman kan batun sako ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sace a shekarar 2014.

A bayyane yake cewa a wannan karon bangaren al-Barnawi sun shirya sasantawa da gwamnati, kuma ‘suna da yakinin’ samun wani abu daga gwamnatin a matsayin fansa.

Matsalar ita ce ba abun da zai hana mayakan sake kai hari wata makaranta ko al’umma nan gaba, tare da sace wasu mutanen da nufin sake cika lalitarsu.

Wannan bahaguwar dabara ce ka karawa kungiyar da ka ke kokarin murkushewa karfi ta hanyar biyansu fansar kudi ko mayar musu da kwamandojinsu da ke hannun hukuma.

Amma gwamnatin Najeriya ta gwammace ta guji zubewar kimarta a idon duniya, kamar yadda ya faru da gwamnatin tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan, kan yadda ya ki daukar batun sace ‘yan matan Chibok da muhimmanci.

Karanta karin labarai masu alaka

Amma shi ma abun da ya faru na sace ‘yan matan Dapchi yana cike da “sakaci”.

Da farko hukumomi sun yi watsi da batun sace ‘yan matan, (har ma suka yi wa iyayen yaran da suka yi ikirarin hakan barazana) sai kuma daga baya suka ce an ceto yaran.

Wannan ya jawo bacin rayuka a al’ummar da abun ya shafa. Shugaba Buhari ya yi kokarin ziyartar yankin da kuma yin alkawarin cewa gwamnati za ta yi duk abun da ya dace don ceto yaran.

Ceto yaran Dapchi dai zai kwantar da hankalin ‘yan matan da iyayensu da masoyansu, amma kuma zai ja wa gwamnati farin jini ne dan kadan.

Ga alama dai wadannan masu tayar da kayar bayan ba su da wata asara a wannan lamarin, kuma Boko Haram za ta ci gaba da zamowa annoba ga Najeriya da makwabtanta na yankin Tafkin Chadi.

Amurka ta sanya dokar hakar mai a Sudan ta Kudu


Image caption

Kashi 93 cikin 100 na kasafin kudin Sudan ta Kudu ya dogara ne ga man fetur

Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanin mai a Sudan ta Kudu, a wani mataki na hana yadda kudaden da ake samu ke rura wutar yakin basasa a kasar ta Sudan ta Kudu.

Amurka ta ce daga yanzu Amurka da sauran kamfanoni za su bukaci lasisi na musamman gabanin samun fasaha ko kayan aiki ga wasu kwamfanonin mai sha biyar, da hukumomin gwamnati.

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta kasar tace gwamnatin Sylva Kiir wacce ta bayyana a matsayin gungun ‘yan cin hanci da rashawa.

Amurkar ta kara da cewa suna amfani da kudaden mai wajen sayar makamai, da bawa ‘yan bindiga dadi makamai, da kuma yin kafar ungulu ga zaman lafiya. A watan jiya Amurka ta sanyawa Sudan ta Kudu takunkumin sayen makamai.

Syria: Za a kwashe ‘yan tawaye daga Ghouta


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Yakin da ake tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwamnatin Syria, ya lalata garin Ghouta

Nan gaba kadan ne daruruwan mayakan ‘yan tawayen Syria tare da iyalansu, za su fara barin garin Ghouta da ke gabashin Syria wanda aka yi wa kawanya a karkashin wata yarjejeniya da Rasha ta shirya.

Rahotanni sun ce, mayakan ‘yan tawayen sun amince su ajiye makamansu domin a basu dama su koma lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar ta Syria, inda ‘yan tawayen ke rike dashi.

Idan hakan ta tabbata, to zai zama aikin kwashe ‘yan tawayen na farko daga Gabashin Ghouta, wanda ya fuskanci munanan hare-hare daga bangaren dakarun gwamnatin kasar tun a watan da ya gabata.

An yanke garin Harasta daga sauran sassan gabashin Ghouta.

Kungiyar ‘yan tawaye ta Ahrar al Sham, ce dai ke rike da shi, inda yanzu aka tabbatar da cewa ta amince ta dai na yaki, sannan kuma za su bar wajen.

Akwai irin wannan yarjejeniyar da ake tattaunawa da wasu manyan kungiyoyin ‘yan tawaye biyu a yankin, wato kungiyar ‘yan tawaye ta Jaish al Islam da Faylaq al Rahman, amma kuma har yanzu ba a cimma komai ba.

Dukkannin kungiyoyin biyu sun sha alwashin ci gaba da da yaki duk da cewa ana ta kora su.

Kazalika har yanzu ana harba makaman roka a Damascus, inda dakarun gwamnati ke rike da shi.

Wani hari da aka kai ranar Talatar da ta wuce, shi ne mafi muni a baya-bayan nan, inda aka hallaka mutum fiye da 40.

Dabarun da dakarun gwamnatin kasar keyi na yi wa waje kawanya da kuma ruwan bama-bamai, ta sa an samu muhimmiyar nasara, to sai dai kuma duk da haka, an yi asarar rayuka da yawa a cikin shekarun baya-bayan nan.

Irin wannan yanayi dai, shi ke faruwa a gabashin Ghouta, inda dubban fararen hula suka kasance ba su da wani zabi illa su bar gidajensu, sannan kuma ko su mika kansu ko kuma a hallaka su.

Gwamnatin Najeriya ta ce ‘Kyauta BH ta sako ‘yan matan Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani mahaifin ‘yar makarantar Dapchi na share hawayen murnar sakin matan

Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta biya kudin fansa domin a saki ‘yan Matan makarantar sakandaren garin Dapchi da Boko Haram ta sace.

Wata sanarwa da ofishin ministan watsa labaran kasar, Lai Mohammed, ya fitar ta ce babu wani musayar fursuna da aka yi domin sakin ‘yan matan.

Sanarwar ta kara da cewa yanzu jimillar mutane 106 aka sako wadanda aka sace a Dapchi da suka hada da dalibai ‘yan mata 104 da kuma wani yaro da yarinya daya.

“Rahotannin da suka ce an biya kudin fansa ba gaskiya ba ne,” a cewar Lai Mohammed.

Ya ce an mika ma su ‘yan matan da wani yaro daya, wato tawagar gwamnatin Tarayya ta mutane hudu da suka isa Maiduguri domin rako ‘yan matan zuwa Abuja.

Tawagar ta kunshi ministan cikin gida Janar Danbazau da Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ministan harakokin waje da kuma Hon. Goni Lawan Bukar, dan majalisa da ke wakiltar Dapchi.

An dauki ‘yan matan zuwa Abuja a cikin wani jirgin soji daga Maiduguri.

Yadda aka sace ‘yan matan

Daya daga cikin ‘yan matan ta shaida wa BBC yadda aka sace su:

“Muna zaune a cikin dakunanmu sai muka ji kara, da farko mun dauka cewa na’urar raba wutar lantarki ce ta fashe, sai muka ji karar ta ci gaba.

Sai suka shigo dakananmu, inda muka yi kokarin ficewa ta kofar baya amma sai suka sha kanmu suka zuba mu motoci.

A kan hanyar tafiya ne biyar daga cikinmu suka mutu.

Daga nan sai suka kaimu wani wuri inda muka kwana sannan suka sa muka dafa abinci muka ci.

Sai suka kara tafiya da mu wani wurin daban.

Sun rinka kula da mu suna ba mu abinci da ruwan sha, ba su yi mana komai ba”.

Da aka tambaye ta ko za ta koma makaranta sai ta ce:

“A’a. Sun shaida mana cewa ka da mu ci gaba da karatun boko”.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Jirgin Sojoji ya dauki ‘yan Matan zuwa Abuja daga Maiduguri

Abin da ya faru tun sace ‘yan Matan

 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace ‘yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace ‘yan matan
 • Da farko an ce ‘yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto ‘yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace ‘yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace ‘yan matan ba
 • Sace ‘yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da ‘yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam’iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan Dapchi 110 a watan jiya.

Wata sanarwa da kakakin PDP Kola Ologbondinyan ya aike wa manema labarai ta ce APC da wasu jami’an fadar shugaban kasar ne suka shirya sace matan “domin cimma wani buri na siyasa.”

Sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da wannan zargi na PDP.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Kasashe 44 sun sanya hannu kan kasuwancin bai-daya a Afrika


Hakkin mallakar hoto
AFP

Kasashen Afrika 44 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya wacce aka tsara da nufin cinikayya ba haraji tsakanin kasashen.

An bayyana cewa yarjejeniyar da ake kira ACFTA za ta samar da kasuwa ga mutanen Afrika sama da biliyan.

Sai dai kuma rahotanni daga Rwanda inda ake gudanar da taron sun ce kasashe 27 kawai ne suka amince a shigar da fitar da kaya ba tare da wani shamaki ba a iyakokin kasashen.

Bukatar kasashen da ke goyon bayan kulla yarjejeniyar shi ne shigar da kayayyyaki da ba mutane ‘yancin izinin shiga domin aiki a kasashen na Afrika.

A karkashin yarjejeniyar, dukkanin kasashen da suka sanya hannu za su rage harajin shigo da kayayyaki da nufin bunkasa kasuwanci tsakaninsu.

Tun kafin sanya hannu a yarjejeniyar ne dai ta fuskanci cikas inda Najeriya ta biyu a karfin tattalin arzikin Afrika ta janye.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta ce sai ta kara nazari kafin ta sanya hannu a yarjejeniyar.

Masana tattalin arziki na ganin kudirin kasuwancin na bai-daya a Afrika zai taimaka wajen magance matsalar rashin ayyukan yi tsakanin matasa a nahiyar.

Kuma suna ganin akwai kalubale da dama da za a fuskanta a gaba kafin fara cin moriyar yarjejeniyar.

Babban kalubalen shi ne yadda yawancin kasashen Afirka ke dogaro da huldar kasuwanci da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Misali kamar Najeriya da ke samar da manja, amma kuma yawancin kasashen Afrika sun fi gwammacewa su shigo da shi daga kasashen yankin Asiya da Turai.

​​’Yan kwallo 5 da ba a jin duriyarsu – ya kamata ku sansu​


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dan kasar Ingila ne amma yana murza-leda a Jamus ya kamata ku san shi

Shin kun gaji da jin labarin Messi ko Ronaldo da kuma Neymar?

BBC na gabatar muku da ‘yan wasa biyar da baku sansu ba, wadanda za su iya kafa tarihi a fagen tamaula a duniya.

1. Pietro Pellegri (Mai shekara 17, Italiy da Monaco)

Ana kiransa da sunan “sabon Messi”, yana da shekara 15 ya fara kafa tarihi a Genoa a Gasar Serie A: Matashin da ya fara buga gasar kuma ya ci kwallo biyu rigis a wasa.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Pietro Pellegri ya cika shekara 17, kuma yana koyon darasin tamaula

Wasu manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai sun yi kokarin sayen dan wasa, amma ya zabi Monaco wadda ta saye shi kan $24m a watan Janairu, a matsayin na biyu matashin da aka saya mafi tsada.

Har yanzu bai shiga cikin babbar kungiyar ba, amma tun da ya kai shekara 17 yana saka kaimi a wasannin da yake yi.

2. Justin Kluivert (Shekara 18, Netherlands da Ajax)

Idan ka ji sunan babu wanda za ka tuna illa mahaifinsa Kluivert – Justin dan gidan Patrick ne, tsohon dan wasan Holland da Barcelona wanda ya taka-leda a Newcastle.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Justin Kluivert zai buga wa Holland a karon farko wasan sada zumunta da za ta yi da Ingila da Portugal.

Kamar yadda mahaifinsa ya yi, Justin na cin kwallayen da ya haskaka shi a koda yaushe a jax. Ya kuma taba cin kwallo uku a wasa, abinda mahaifinsa bai yi a gasar Netherlands.

Manchester United da Barcelona na rige-rigen daukar dan wasa kuma tuni tawagar kwallon kafar Holland ta gayyace shi wasan sada zumunta da za ta yi da Ingila da kuma Portugal.

3. Jadon Sancho (Shekara 17, Ingila, Borussia Dortmund)

Wanda ake kira da sunan “Neymar Ingila”, Sancho ya yi atisaye a Watford da kuma Manchester City har zuwa bara – daga baya ya koma Borussia Dortmund kan dala miliyan 14.

Dan wasan bai amince ya zauna karkashin Pep Guardiola a Manchester City, inda ya koma Jamus domin ya dunga buga wasanni akai-akai.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jaridun Ingila sun ce duk da ba a gayyaci Jadon Sancho wasan sada zumunta ba, amma zai iya buga gasar Kofin duniya a Rasha a 2018

Yana cikin matasan Ingila da suka lashe kofin duniya na masu shekara 17, sai dai yarjejeniyar da aka yi da kungiyarsa shi ne ya buga wa tawagar kwallon kafar Ingila wasannin cikin rukuni.

Jaridun Ingila sun yi tsokaci kan rashin gayyatar sa wasannin sada zumunta da za ta buga a karshen mako, amma sun ce yana da kyau a kai shi gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.

4. Vinicius Júnior (Shekara 17, Brazil, Real Madrid yana wasa aro a Flamengo)

Kasa da minti 20 ya yi yana taka-leda Real Madrid ta tabbatar da cewar zai zama fitatcen dan kwallo a nan gaba, inda ta dauki dan wasan Brazil kan dala miliyan 54.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Vinicius Junior zai koma buga gasar Turai nan gaba

Saboda haka sai ya shekara 18 zai iya komawa Spaniya, saboda haka ya ci gaba da zama a kungiyarsa ta Flamengo.

A bara ya jagoranci tawagar kwallon kafar Brazil ta lashe kofin kudancin Amuka na matasa ‘yan shekara 17. kuma shi ne ya zama kan gaba a cin kwallaye a gasar kuma wanda ya fi yin fice a wasannin.

Idan ya cika shekara 18 a watan Yuni zai koma Real Madrid inda zai samu kwarewar da yake bukata.

5. Jan-Fiete Arp (Shekara 18, Hamburg, Jamus)

A bara yana da shekara 17, Arp ya zama na farko da aka haifa a shekarar 2000 ya fara buga gasar Bundesliga ya kuma ci kwallo.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dan kasar Ingila ne amma yana murza-leda a Jamus ya kamata ku san shi

Hukumar kwallon kafar Turai ta ce, “Daya ne daga matasan da za su haskaka a gasar kwallon Jamus”.

Dan wasan ya ci kwallo bakwai a gasar matasa ‘yan shekara 17 ta nahiyar Turaihe a bara, haka kuma ya zura kwallo biyar a gasar cin kofin duniya. dan kwallon yaki yadda ya koma Chelsea da murza-leda, amma yanzu ana cewa Bayern Munich ce ke zawarcin sa.

APC da fadar shugaban Nigeria ne suka kitsa sace matan Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam’iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan Dapchi 110 a watan jiya.

Wata sanarwa da kakakin PDP Kola Ologbondinyan ya aike wa manema labarai ta ce APC da wasu jami’an fadar shugaban kasar ne suka shirya sace matan “domin cimma wani buri na siyasa.”

A cewar sanarwar, “Jam’iyyarmu na ganin hakan a matsayin mugunta da rashin mutunci da kuma izgilanci inda aka yi amfani da ‘yan matan makarantar da ba su ji ba ba su gani ba domin shirya wasan kwaikwayon da aka yi na yaudarar ‘yan Najeriya, duk domin a sake zabensu a 2019.”

PDP ta ce wannan abu ne da ba za a taba yafewa ba.

Sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da wannan zargi na PDP.

“Mutanen Najeriya na sace cewa an aikata wannan mummunan aiki ne domin yaudarar jama’a… a kirkiro wani yanayi da zai nuna cewa gwamnatin APC ta yi rawar gani sannan Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da burinsa na sake tsayawa takara a zaben 2019, watakila cikin makonni masu zuwa,” in ji PDP.

A ranar Laraba ne wasu mutane da ake tsammani ‘yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci.

Mahaifin daya daga cikin ‘yan matan, Kundili Bukar, ya shaida wa BBC cewa ‘yan Boko Haram sun sauke matan ne kawai suka tafi kuma ‘yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Gwamnatin Najeriya ta ce ‘yan matan sakandaren Dapchi 101 kungiyar Boko Haram ta sako.

Wata sanarwa da ofishin ministan watsa labaran kasar, Lai Mohammed, ya fitar ta ce an sako matan ne tare da taimakon “wasu kasashe abokan Najeriya ba tare da an sanya wani sharadi ba.”

A cewar Lai Mohammed, gwamnati na ci gaba da kokarin ganin an sako sauran.

Image caption

Satar ‘yan matan ta jawo ce-ce-ku-ce

‘Yaran’ Buharin Daji sun kashe sojoji 11 a Kaduna


Hakkin mallakar hoto
IDRIS KPOTUN FACEBOOK

Image caption

Ana zaton harin na ramuwar gayya ne

Wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji 11 a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

BBC ta samu tabbacin faruwar lamarin na ranar Talata da dadare.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar, wadanda ake zargi yaran jagoran barayin shanun da aka kashe a jihar Zamfara Buharin Daji ne, sun yi kisan ne a matsayin ramuwar gayya.

Wata majiya ta shaida wa kafar yada labarai ta PRNigeria cewa mutanen, dauke da muggan makamai, sun abka wa sojojin da ke aiki a shingayen bincikensu wanda ke Doka, wadda ke tsakanin Funtua da Birnin Gwari sannan suka kashe sojojin nan take.

An jibge gawarwakin sojojin da aka yanka a wani dakin ajiye gawarwaki.

Rahotanni sun ce tun da fari maharan sun abka wa yankin Maganda inda suka kai harin ramuwar gayya saboda kisan Buhari Tsoho, inda suka raunata ‘yan kato da gora tara.

Bayan nan ne suka nufi Kampanin Doka da ke kan iyaka da hanyar da za ta kai ga kauyukan Gwaska da Dansadau inda suka sake kai hari wanda shi ne ya yi sanadin mutuwar sojojin.

A farkon watan Maris ne gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Buharin Daji, jagoran barayin shanu da suka addabi jihar da hare-hare.

Hakkin mallakar hoto
ZAMFARA GOVERNMENT

Image caption

Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris

BBC ta kaddamar da sashen Afrika ta yamma a Lagos


BBC ta kaddamar da sashen Afrika ta yamma a birnin Lagos na Najeriya, wanda ya kunshi manyan harsunan kasar guda hudu.

Bikin kaddamar da sashen na zuwa bayan BBC ta bude sassa biyu na harsunan Igbo da Yoruba a ranar 19 ga Fabrairun da ya gabata.

A bara ne kuma BBC ta bude sashen Pidgin a Lagos, domin mutanen da ke magana da turancin buroka.

Yanzu sabon sashen na yammacin Afrika ya kunshi sashen Hausa da Yoruba da Igbo da kuma Pidgin, duka a Najeriya.

Sabbin sassan da sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar, ya kasance shirinsa mafi girma tun shekarun 1940, sakamakon kudin da gwamnatin Birtaniya ta bai wa sashen a shekarar 2016.

Amma sabbin rassan Igbo da Yoruba da Pidgin za su watsa labaransu ne ta intanet.

An shirya gagarumin biki a Lagos domin kaddamar da reshen na Afrika ta yamma.

Bikin zai kunshi manyan masu ruwa da tsaki a BBC da suka hada da Jamie Angus daraktan watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC.

Sannan an gayyaci manyan mutane da fitattu a fannin kare harshe da kuma al’adu.

An kirkiri shafin #BBCWAfricalaunch a twitter ga wadanda ke son bibiyar lamurran shagalin bikin.

A shekarar 2015 ne gwamnatin Birtaniya ta sanar da ware wasu kudade don sake inganta ayyukan da BBC ke yi a duniya, wanda hakan ya sanya aka samu karin harasan da ya kamata a bude a Afirka da kuma yankin Asiya.

An ci zarafin ma’aikacin BBC a Lagos


Image caption

BBC ta ce ba za ta lamunci cin zarafin duk wani ma’aikacinta ba

BBC ta yi alawadai da wulakancin da wasu jami’an gwamnatin Lagos suka yi wa ma’aikacinta ta hanyar kwace masa kayan aikinsa ta karfin tsiya tare da goge dukkan hotunan da ya nada na wani aikin korar mutane daga wani waje a jihar.

An gudanar da aikin korar mutanen ne a wani wajen gyaran motoci wanda aka ajiye daruruwan motoci da sauran kayayyakin lantarki na miliyoyin dalloli.

Wajen dai na kusa da inda ake zubar da sharar data mamaye yankin Ojota a jihar ta Lagos..

Masu sana’a a wajen, sun nuna damuwa a kan shirin gwamnatin jihar ta Lagos na rufe wajen kafin a ba su inda za su ci gaba da gudanar da sana’arsu.

Gwamnatin jihar dai ta ce tulin sharar da ke kusa da wajen, na da matukar illa ga lafiya, shi ya sa ma ta ke bukatar wadanda suke gudanar da kasuwanci ko kuma ke zaune a wajen da su bari.

Ma’aikacin BBCn wanda ke aiki a shahen Yarabanci, Joshua Ajayi, ya ziyarci wajen ne domin tattaunawa da wadanda ke zaune a wajen, gabanin a rufe wajen kwata-kwata, lnda anan ne jami’an gwamnatin suka farmasa tare da kwace masa wayarsa ta salula.

Tawagar jami’an gwamnatin su shida wanda wani mataimakin darakta a ma’aikatar kula da muhalli ta jihar ke jagoranta, ta yi barazanar kama ma’aikacin BBCn, bayan da ya bukaci su bashi wayar salularsa.

Daga bisani dai an bashi wayarsa, amma kuma an goge wasu hotunan bidiyo da sauran muhimman abubuwan da ke cikin wayar.

Babban sakatare a ma’aikatar dai bai bayyana dalilin da ya sa aka kwace kayan aikin dan jaridar ba da kuma dalilin goge masa wasu muhimman abubuwa ba.

BBC ta ce, sam ba ta ji dadin abinda ya faru ba, kuma zata nemi karin bayani daga mahukuntan jihar a kan dalilin da ya sa aka yi wa ma’aikacinta haka.

Daga nan ta bukaci gwamnatin jihar ta Lagos, da ta rinka kyale ma’aikatanta na gudanar da aikinsu yadda yakamata ba tare da an yi mata katsalandan ba, saboda dukkan ma’aikatanta sun san ka’idar aikinsu da kuma abin da yakamata su yi da ma wanda bai dace suyi ba.

To sai dai kuma tuni kwamishinan ma’aikatar kare muhalli na jihar, Babatunde Durosimi–Etti, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce ya nemi afuwa a kan abinda ya faru, sannan ya ce, za su yi nazari a kan abinda ya faru”.

Kafin faruwar lamarin dai wakilin BBCn, ya zanta da wadanda ke zaune a wajen da za a rushen inda suka shaida masa cewa kafin a fara rusau din, sai da suka wakilta wasu a cikinsu domin su gana da jami’an ma’aikatar kula da muhallin, amma sa’oi kadan bayan dawowarsu, sai kawai ba zato ba tsammani suka ga an fara rufe musu shagunansu ba tare da an ce ga wajen da zasu koma ba.

Boko Haram ta sako ‘yan matan Dapchi


Image caption

Sama da makwanni hudu kenan da sace ‘yan matan a lokacin da suke makarantar kwana a garin Dapchi na jihar Yobe

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun sako ‘yan matan Dapchi da aka sace a watan jiya.

Daya daga cikin iyayen yaran ya shaida wa BBC cewa da sanyin safiyar ranar Laraba ne wasu mutane suka mayar da yaran garin a motoci.

Inda suka a jiye su suka tafi.

Ya kara da cewa iyaye na ta rububin zuwa domin dubawa da kuma dauko ‘ya’yansu.

Wasu rahotanni da BBC ba ta tabbatar ba na cewa wasu kadan daga cikin yaran sun mutu.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani.

Yau ce ranar rubutattun wakoki ta Duniya


Image caption

Ibrahim Sheme mutum ne mai sha’awar fina-finai da wakokin Hausa na da da na yanzu

A kowacce rana mai kamar ta yau 21 ga watan Mayu, Majalisar Dinkin Duniya na ware ta dan tunawa da rubutattun wakoki.

Manufar hakan dai ita ce, lalubo alfanun da tasirin da wakokin ke yi ga rayuwar al’uma ta fuskar zaman takewa, Ilimantarwa, Nishadi da sauransu.

Wake, ko rubutattun wakoki, wasu hanyoyi ne na fito da abin da ke kunshe a cikin zuciyar dan adam ya bayyana a fili.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, tun tale-tale, rubutattun wakoki kan nuna yadda bil-Adama sukai tarayya da juna.

Wannan ne ya sa Majalisar ta ware rana mai kamar ta yau, wato 21 ga watan Maris, don jaddada hakan.

A kasar Hausa ma rubutatun wakoki kan taka muhimmiyar rawa wajen ilmantarwa ko fadakarwa ko zaburar da al’umma.

Wasu ‘yan Najeriya da BBC ta zanta da su, sun shaida mata su na daukan darussan rayuwa daga cikin rubutattun wakokin fitattun mutane kamar Marigayi Sa’ad Zungur da sauransu.

Wadanda yawancin wakokinsu kamar fadakarwa ne, da nuni ga aikata halin kwarai da gujewa munanan dabi’u.

Masana sun bayya wata matsala da ake fuskanta a zamani ita ce, matasa ba su san muhimmancin rubutattun wakokin mashahuran mutanen da suka ci gajiyar halayyar kwarai da zamantakewa tsakaninsu da makofta da al’uma ba.

Hasali ma yawanci, ba su cika damuwa da saurare ko karanta wakokin da aka gada tun iyaye da kakanni ba.

Ana tilastawa ‘yan matan yin Rohingya karuwanci


Image caption

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mata da kananan yara da tsofaffi, su ne suka fi kowa shan wahala a lokutan tashin hankali irin wannan

Wani bincike da BBC ta gudanar, ya gano ana safarar yara mata ‘yan kabilar Rohingya da suka haura shekara 10 dan yi karuwanci a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bangladesh.

Baki ‘yan kasar waje da suke sha’awar yin jima’i da yara na samun damar daukar irin wadannan mata cikin sauki, wadanda suka baro jihar Rakhine ta Myanmar saboda tashin hankali.

Wata yarinya mai suna Awara yar shekara 14 da suka tsere daga Myanmar, aka kuma hallaka iyayenta a iyakar kasashen biyu ta dade ta na neman mai tallafa mata.

Ta ce halin da ta samu kanta a ciki, na gararanba a gefen titi, ya sanya da wasu mata a cikin mota suka bukaci taimaka ma ta ta bi su ba tare da tunanin wani abu makamancin hakan zai faru ba.

Anwara ta kara da cewa ”Bayan sun dauke ni, sai suka min alkawarin za su taimaka min na samu ingantacciyar rayuwa. Amma maimakon hakan sai suka kai ni birnin Cox’s Bazar”.

”Ba da jimawa ba sai suka kawo min wasu maza biyu. Tare da tsorata ni da wuka kan cewa idan ban amince da bin da suke bukata ba za su kashe ni. Daga nan sai suka mintsine ni da saman wukar a ciki na, suka kuma lakada min duka saboda na ki yadda su haike min,” inji Anwara.

A baya-bayan nan dai ana ta samun korafin safarar ‘yan mata daga sansanonin ‘yan gudun hijira da suke zaune a Bangladesh, kuma ana daukar su ne dan yin karuwanci.

Mata da ‘yan mata, da kuma tsofaffi na cike da fargabar halin da za su samu kansu a ciki a duk lokacin da aka samu matsala irin hakan a matsugunan da suke zaune.

Matsalar tsabtataccan ruwan sha ta karu a duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani rahoton Bankin Duniya ya ce yawan mutanen da ke rayuwa ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba sun karu.

Rahoton da Bankin Duniya ya fitar albarkacin ranar Ruwa ta duniya ya ce yawan mutanen da ba su da tsabtataccen ruwan sha a duniya sun kai miliyan dubu dari takwas da arba’in da hudu.

Rahoton ya ce mutum guda cikin tara a duniya na rayuwa ne ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba.

Binciken ya yi nazari ne kan yawan mutanen da suke samun tsabtataccen ruwan sha a gida ko kuma suke da halin samun ruwan a kasa da sa’a daya.

Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da aka ware domin bikin ranar ruwa ta duniya da nufin wayar da kan al’umma game da muhimmancin tsaftataccen ruwan sha.

Bankin Duniya ya yi kira ga ‘yan siyasa da su tashi tsaye domin tunkasar matsalar, kamar yadda rahoton ya ce: “Idan ba ruwa mai tsabta sauran bukatu na duniya da suka danganci kiwon lafiya da ilimi da kuma daidaiton jinsi ba za su samu ba.

Rahoton kuma ya ce matsalar ta fi muni a Afrika.

Kazalika rahoton ya yi gargadin ce cewa gwamnatoci da dama a nahiyar Afirka babu wani abin azo a gani da suke wajen samar da tsabtataccan ruwan sha, abinda ke jefa rayukan miliyoyin mutane cikin hadari.

Sai dai a India da China ne rahoton ya ce yawan mutanen suka fi yawa, amma idan aka yi la’akari da yawan jama’a, matsalar ta fi tsanani a Afrika, musamman a kasashen Eritrea da Uganda da Habasha da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo da kuma Somalia.

A Najeriya ma dai ana fuskantar matsalar rashin ruwa mai tsafta, kuma rashin ruwa da muhalli mai tsaftar na haddasa mutuwar yaran da ba su kai shekara biyar ba a kasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jama’ar yankunan karkara a Najeriya sukan dogara ne da gurbataccen ruwa daga tafkuna.

Rahoton na Bankin Duniya ya ce yara ‘yan kasa da shekaru biyar kimani dubu tamanin ke mutuwa duk rana a duniya sakamakon cututtuka da suka shafi matsalar tsabattaccen ruwan sha.

Masharhanta dai na ganin batun cimma burin samar da ruwan sha mai tsabta da kuma wadatarsa a kasashen duniya wani babban kalubale ne ga hukumomi.

India: Malami ya danganta maman daliba da kankana


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Daliban sun yi zanga-zangar ne rike da kankana a hannayensu

Daliban wata kwaleji a jihar Kerala da ke kudancin kasar India, sun gudanar da zanga-zanga, bayan wani malami a makarantar ya danganta maman wata daliba da kankana.

An watsa hoton bidiyon da aka dauka a lokacin da malamin ke fada wa dalibar wannan kalma a kafafan sada zumunta a cikin karshen makon daya gabata, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kai, inda mutane ke ta mayar da martani a fusace, musamman mata.

Wannan hoton bidiyo da aka sanya a kafafan sada zumuntar, shi ya har zuka wasu dalibai inda suka bi tituna, hannayensu kuma rike da kankanar da aka yayyanka suna zanga-zangar kin amincewa da irin wadannan kalamai ga mata.

Malamin dai farfesa ne, wanda ke koyarwa a kwaleji horarwa ta Farook da ke Kerala, ya kuma fada wa dalibar kalmar ne saboda yanayin shigar da ta yi inda ta bar kirjinta a waje, da kuma wasu sassa na jikinta.

Wannan shiga da dalibar ta yi ne ya fusata farfesan, saboda ya ga kamar ba ta yi shigar mutunci ba, shi ya sa ya ce mata, mamanta kamar kankana.

Wata kungiyar kare hakkin matasa a jihar, ta ce ba za ta lamunci cin zarafin mata ta hanyar fada musu duk maganar da aka ga dama ba.

Duk wani yunkuri da manema labarai suka yi don jin ta bakin hukumar gudanarwar kwalejin ko kuma malamin a kan wannan batu, ta ci tura.

Messi na atisaye a Manchester City


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Argentina za ta buga gasar cin kofin duniya a Rasha

Lionel Messi na yin atisaye a filin wasa na Manchester City tare da tawagar kwallon kafar Argentina.

Argentina ta zabi filin City domin yin atisayen tunkarar wasan sada zumunta da za ta yi da Italiya a Etihad a ranar Juma’a.

A ranar Talata Messi ya isa filin wasa na City, inda ya motsa jiki tare da sauran tawagar Argentina daga karshe aka bai wa ‘yan jarida damar yin magana da ‘yan wasa.

Sauran ‘yan kwallon Argentina da suke filin Manchester City har da Sergio Aguero wanda ke yin jinya da Nicolas Otamendi.

Haka kuma Gonzalo Higuain da Angel Di Maria da Javier Mascherano da kuma Marcos Rojo duk sun halarci motsa jikin.

An umurci ‘yan sanda su janye daga gadin masu kudi


Hakkin mallakar hoto
NPF

Image caption

An sha bayar da umurnin amma ana yin watsi da shi

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umurnin janye dukkanin jami’an ‘yan sanda da ke tsaron manyan mutane da kamfanoni.

Ya ce an dauki matakin ne saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kasar.

Jami’an ‘yan sanda kimanin 150,000 aka bayyana cewa suna gadin masu kudi da jami’an gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da babban sufeton ‘yan sandan na Najeriya ke bayar da umurnim janye jami’an ‘yan sandan daga aikin tsaron gidajen manyan mutane ba.

Sai dai sau da dama, ana yin watsi da umurnin.

A wani taron da ya gudanar tare da manyan jami’an ‘yan sanda, sufeto janar na ‘yan sandan Ibrahim Idris, ya ce wajibi ne kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Najeriya su mutunta umurnin cikin gaggawa.

Ya ce hakan ya zamo tilas saboda yadda rayuwar mutanen Najeriya miliyan 200 ke fuskantar barazanar kalubale na tsaro.

Har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashi.

Hakazalika, rikici tsakanin makiyaya da manoma na ci gaba da zama barazana a yankin tsakiya da arewa maso yammacin Najeriya.

Sannan ana fama da rikicin kabilanci da sace-sacen jama’a da fashi da makami a sassan kasar da kuma rikicin masu fafutikar kafa kasar Biafra a kudu masu gabashi.

Masana na ganin tura ‘yan sanda domin gadin wasu tsirarun mutane, a yayin da rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya ke cikin barazana ya nuna sakaci ga aikinsu na kare rayukan jama’a.

Pogba zai yi wasa da Neymar a kungiya guda


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pogba zai buga wa Faransa wasan sada zumunta a karshen mako

Dan wasan Manchester United, Paul Pogba ya ce yana fatan wata rana zai murza-leda kungiya daya da Neymar.

Neymar ya yabi kwazon Pogba a shekara biyu da suka wuce, inda ya ce salon wasan dan kwallon tawagar Faransa zai da ce da taka-leda a Barcelona.

Sai dai kuma yana yi ya sauya inda ba za su iya wasa tare a Nou Camp ba, bayan da Neymar ya koma Paris St-Germain a kakar shekarar nan.

Shi kuwa Pogba ya bar Juventus a watan Agustan 2016, inda ya sake komawa Manchester United da taka-leda.

Pogba na fatan wata rana zai buga tamaula da Neymar, ya kuma ce yana tuna abinda dan kwallon Brazil din ya fada a kanshi, zai so ya yi wasa tare da shi.

Ya kuma kara da cewar ”A Brazil kwallon kafa ita ce rayuwa, kowa yana buga tamaula, ina jin dadin kallon yadda yake murza-leda, yana da dabaru, ya lakanci kwallon kafa, sannan ya iya buga wasa, ina jin dadin kallon yadda yake buga kwallo”.

An kama tsohon shugaban Faransa saboda ‘karbar’ kudin Gaddafi


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ana zargin Sarkozy da karbar makudan kudade daga wajen Gaddafi don yakin neman zabe

‘Yan sanda sun kama tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy don yi masa tambayoyi kan zargin da ake masa na karbar makudan kudi don yakin neman zabensa, daga wajen tsohon Shugaban Libya Muammar Gaddafi.

‘Yan sanda suna bincike kan zargin rashin bin tsari kan samar da kudaden aiwatar da yakin neman zaben shugaban kasa da ya yi a shekarar 2007.

A baya ‘yan sanda sun yi masa tambayoyi kan wannan bincike. Sai dai Mista Sarkozy ya yi watsi da aikata ba daidai ba.

Tsohon shugaban kasar dai mai matsakaicin ra’ayi bai samu damar komawa kujerar mulki ba a 2012.

Majiyoyin shari’a sun ce ana yi masa tambayoyin ne a Nanterre, wani yanki da ke wajen yammacin birnin Paris.

A 2013 ne Faransa ta fara wani bincike kan zarge-zargen cewa ya karbi kudade sosai daga wajen Gaddafi don yakin neman zabe.

Majiyoyin sun ce ‘yan sanda sun kuma yi wa daya daga cikin tsoffin ministocin Mista Sarkozy kuma na hannun damansa Brice Hortefeux, tambayoyi a ranar Talata.

Ko za a gurfanar da Mr Sarkozy a gaban kuliya?

Har yanzu binciken bai kai wannan matakin ba.

Yana hannun ‘yan sanda don yi masa tambayoyi inda za a rike shi ne kawai na tsawon sa’a 48.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Nicolas Sarkozy ya musanta aikata ba daidai ba

Kafofin watsa labaran Faransa sun ce wannan ne karo na farko da ‘yan sanda suka tsare shi kan zargin karbar kudi daga Gaddafin.

Amma an taba tsare shi a 2014 a wani binciken na daban kan zargin yin bushasha da kudaden neman zabe.

Wadanne zarge-zarge ake yi kan wannan batun?

A watan Nuwambar 2016, Ziad Takieddine ya shaida wa kafar yada labaran Faransa ta intenet, mediapart cewa a tsakanin 2006-2007 ya bai wa Mista Sarkozy da shugaban ma’aikatansa Claude Guéant akwatuna uku cike da takardun kudin euro ‘yan 200 da ‘yan 500.

Mr Takieddine ya yi zargin cewa kudaden sun fito ne daga hannun Gaddafi kuma yawansu ya kai Yuro miliyan biyar, daidai da dala 6.2.

A wannan lokacin Mr Guéant ne ke tafiyar da harkokin yakin neman zaben Mr Sarkozy.

An taba bincikensa a farkon shekarar nan kan wani kudi da ya aike ta banki kimanin Yuro 500,000 a 2008. Ya yi watsi da aikata ba daidai ba, ya kuma ce ya samu kudin ne ta hanyar sayar da wasu zanensa guda biyu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ziad Takieddine ya ce ya bai wa mataimakan Sarkozy kudi lakadan da Gaddafi ya bayar

Jaridar Faransa Le Monde ta rawaito cewa Bashir Saleh, wanda shi ke kula da asusun tara kudade na musamman na Libya a wancan lokacin, ya tabbatar da cewa Gaddafi ne ya bai wa Sarkozy kudin domin yakin neman zabe.

Tuhume-tuhumen da ake sa ran za a yi musu kan wannan batu sun hada da amfani da tasirinsa da zamba da ajiye kadarorin sata da halatta kudin haram.

Wadanne bincike kuma a ke wa Sarkozy?

An umarci Mr Sarkozy ya fuskanci kuliya a wata shari’ar ta daban da ake zarginsa da amfani da kudade don yakin neman zabe ba bisa ka’ida ba.

Ana zarginsa da cewa ya yi zamba wajen kara yawan kudin yakin neman zabe a 2012, wanda yawansa ya kai Yuro miliyan 22.5.

Mr Sarkozy ya karyata cewa ya wuce gona da iri wajen kashe kudin.

An kwara wa wata daliba guba a Maiduguri


Wata dalibar jami’a ta hadu da ibtila’i inda ake zargin wasu sun yi watsa mata ruwan guba a garin Maiduguri na jihar Borno na arewa maso gabashin Najeriya.

Fatima Habu Usman, wacce daliba ce da ke karatu a sashen koyon aikin jinya a jami’ar Maiduguri, tana cikin mayuwacin hali yanzu haka.

Wasu mutum biyu ne ake zargi sun watsa ma ta ruwan guba na Acid bayan ta shiga Keke Napep ko a daidaita sahu a ranar Juma’a.

Wani malamin jami’ar ta Maiduguri ya tabbatar wa BBC ta faruwar lamarin, yayin rahotanni suka ce ‘yan sanda sun kaddamar da bincike.

Birnin ya sha fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, amma ba a sa ran cewa su ne suka aikata wannan aika-aikar.

Dangin dalibar sun shaida wa kafar yada labarai ta PRNigeria cewa, an sace ta ne a gaban wani banki da ta je domin cirar kudi.

Suka ce bayan ta shiga Keke Napep a hanyar Baga ne, ba ta sani ba, sai daya daga cikin mutanen da ke ciki ya fitar da wani kyalle fari ya shafa ma ta a fuska.

Daga nan ne ta fita hayyacinta, kuma sai ta tsinci kanta a kan kwangirin jirgin unguwar Bayan Quarters a Maiduguri misalin karfe daya na rana, kuma an yi ma ta lahani da ruwan guba a jikinta.

Dalibar dai tana shekarar karshe ne a jami’a.

Yanzu haka likitoci na gudanar da gwaje-gwaje a kan Fatima tare da duba yiyuwar ko za a yi mata tiyata a fuska.

PRNigeria ta ambato kwamishinan ‘yan sandan na jihar Borno, Damien Chukwu, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa suna gudanar da bincike domin gano wadanda aikata lamarin.

An nada dan shekara 16 kwamishina amma…


Hakkin mallakar hoto
Faysal Abdullahi Omar

Image caption

Omar ya ce ya shafe kwanaki ba ya zuwa makaranta tun bayan aika masa da takardar nada shi kan mukamin

Wani matashi dan shekara 16 ya yi watsi da tayin mukamin mataimakin kwamishinan wata jiha a kasar Somalia saboda rashin tsaro.

Ana sa ran Faysal Abdullahi Omar zai fara aiki a Jowhar, babban birnin Hirshabelle na Kudu maso Gabashin kasar.

Sai dai dan makarantar ya shaida wa BBC cewa yana tsoron karbar mukamin zai iya sa mayakan al-Shabab su far masa.

Kungiyar masu tayar da kayar bayan dai na da karfi a yankin.

Omar ya ce ba a tuntube shi ba kafin a sanar da sunansa, wanda shugabannin kabila ne ke yi a kasar, a don haka yana so ya mayar da hankali kan karatunsa.

“A yanzu ina karatu a babbar sakandare kuma nan ba da jimawa ba zan kammala, ina so na tafi jami’a domin gina rayuwata ta gaba,” kamar yadda ya shaida wa sashin Somaliya na BBC.

Ya kara da cewa ya shafe kwanaki ba ya zuwa makaranta tun bayan aika masa da takardar nada shi kan mukamin.

Iyayen Omar sun nuna damuwa kan nadin nasa. Sai dai ya ce wasu jama’a a yankin sun shaida masa cewa wata dama ce ta zamowa “abin koyi ga matasa”.

Ya ce “na hadu da mutane da dama da suka nemi na karbi wannan aiki”.

Birnin Jowhar yana arewacin Mogadishu, babban birnin kasar, kuma yana da karkashin ikon gwamnatin Somalia.

Kungiyar al-Shabab ce ke iko da yankunan da ke makwaftaka da yankin.

A ‘yan makonnin da suka wuce masu tayar da kayar baya sun kashe wani dan majalisa a yankin.

An tsayar da ranar karawa tsakanin Real da Atletico


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Atletico ta biyu, Real ta uku a kan teburin La Liga

Hukumar kwallon kafa ta Spaniya ta tsayar da ranar da za a buga wasan hamayya tsakanin Real Madrid da Atletico a Gasar Cin Kofin La Liga.

Hukumar ta amince Real Madrid ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasa na biyu na Cin Kofin La Liga karawar mako na 31 a ranar Lahadi 8 ga watan Afirilu.

Wasan farko da kungiyoyin suka buga a ranar 18 ga watan Nuwambar 2017, sun tashi babu ci ne wato 0-0.

Atletico tana mataki na biyu a kan teburi da maki 64, inda ta ci fafatawa 19 ta yi canjaras bakwai aka doke ta wasa uku.

Ita kuwa Real tana ta uku da maki 60, bayan da ta ci wasa 18 ta yi canjaras 6 sannan aka yi nasara a kanta sau biyar.

Barcelona ce ta daya wadda har yanzu ba a doke ta ba a wasannin shekarar nan, kuma tana da maki 75.

‘Yan Madrid 20 aka gayyata tawagar kasashensu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A karshen mako za a buga wasannin sada zumunta

Kimanin ‘yan wasan Real Madrid 20 ne aka gayyata tawagar kwallon kafar kasashensu, domin buga musu tamaula a karshen mako.

‘Yan wasan da za su buga wa kasashensu wasan sada zumunta a karshen mako sun hada da Sergio Ramos da Nacho da Isco da Asensio da Lucas Vazquez da Carvajal da Varane.

Sauran sun hada da Bale da Kroos da Casemiro da Marcelo da Modric da Kovacic da Keylor Navas da Cristiano Ronaldo da kuma Achraf.

Su kuwa Vallejo da Ceballos da kuma Mayoral za su buga wa Spaniya wasan neman shiga gasar cin kofin Turai da za a yi a shekarar 2019.

Shi kuwa Lucas zai halarci karawar da Spaniya za ta yi gida da waje da Amurka a wasan neman gurbin shiga gasar matasa ‘yan kasa da shekara 20 da za a yi a Faransa.

‘Yan majalisa sun girmama marigayi Sanata Ali Wakili


Hakkin mallakar hoto
House of Reps

Image caption

Shugabannin majalisa da sauran jama’a na zuwa ta’aziyya gidan marigayin

‘Yan majalisar wakilai da na dattawan Najeriya sun yi wani zama na musamman don girmama marigayi Sanata Ali Wakili.

Sanata Ali Wakili, wanda ke wakiltar Bauchi Ta Kudu a majalisar dattawan kasar, ya rasu ne a ranar Asabar a Abuja babban birnin kasar.

Babu wani bayani da aka samu dai kan musabbabin rasuwar marigayin, sai dai an yi ta yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa ko a ranar Juma’a ma ya halarci daurin auren diyar Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka, da aka yi a Kano.

Tun a ranar Asabar din aka yi jana’izar Sanata Wakili a babban masallacin kasa da ke Abuja kamar yadda musulunci ya tanada, inda daga bisani aka koma garin Bauchi don ci gaba da zaman makoki.

A zaman na ranar Talata, ‘yan majalisar sun yi addu’o’i na musamman ga marigayin, tare da bayyana irin kyawawan halayensa da ayyukan ci gaban da ya yi wa kasar.

Kakakin majalisar Yakubu Dogara ya bayyana rashin Sanata Wakili a matsayin wani abu da ya shafi kasa baki daya, ba al’ummar Bauchi Ta Kudu kawai ba.

Kalaman Dogara kan marigayin

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Senate

Image caption

Marigayi Sanata Ali Wakili ne shugaban kwamitin yaki da talauci na majalisar dattawan Najeriya

“Hakika rashin Sanata Wakili abu ne da zai shafi iyalansa da ‘yan uwansa da abokansa da masu kaunarsa a kafafen sada zumunta da al’ummar mazabarsa da kuma takwarorinsa na majalisa.

Kuma rashin nasa zai taba mutane sosai a karamar hukumar Tafawa Balewa da jihar Bauchi da Najeriya da ma duniya baki daya.

Mutum ne mara kumbiya-kumbiya, mai kokarin kwatowa talaka hakkinsa da girmama dimokradiyya.

Mutum ne mai yawan kare muradun al’ummarsa a majalisar dattawa.

Ya yi fafutika wajen ganin an samu shugabanci na gari musamman a jiharmu ta Bauchi da Najeriya baki daya.

Sanata Waliki bai taba kasa a gwiwa ba don kawo ci gaba duk da irin yadda wasu masu mummunar akida ke masa barazana”.

Wane ne Sanata Ali Wakili?

 • An haife shi a shekarar 1960, ya mutu yana da shekara 58
 • Dan asalin karamar hukumar Tafawa Balewa ne a jihar Bauchi
 • Ya kammala digirinsa a Jami’ar Bayero da ke Kano a 1982
 • Ya dade yana aiki a Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya tun daga 1984
 • Ya zama sanata mai wakiltar Bauchi Ta Kudu a 2015
 • Shi ne shugaban kwamitin Yaki da Talauci na majalisar dattawa
 • Ya rasu ranar 17 ga watan Maris na 2018
 • Ya bar mata biyu da ‘ya’ya 10.

Bayanai: Daga Majalisar Dattawa da iyalinsa

Hakkin mallakar hoto
Garba Shehu Twitter

Image caption

Mutane da dama ne suka yi ta zuwa mika ta’aziyyarsu a jihar Bauchi

A karshe ‘yan majalisar sun mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalansa da al’ummar mazabarsa da masarautar Bauchi da majalisar dattawa da al’ummar Bauchi da na Najeriya baki daya.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Obasanjo ya karbi takardar shaidar kammala digirin digirgir


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Obasanjo ya ce ya yi digirin digirgir ne saboda sha’awar da ya ke da ita ta neman ilimi

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya kasance daya daga cikin dalibai sama da dubu 14 da aka ya ye a budaddiyar jami’ar Najeriya, wato National Open University, a cikin watan Janairu.

Cif Olusegun Obasanjo, ya kammala digirin digirgir ne wato dokta a ilmin adinin Kirista.

Tsohon shugaban kasar ne dai ya farfado da jami’ar a shekarar 2001 a lokacin da ya ke mulki, bayan rufetan da aka yi a shekarar 1984, amma ba ta fara aiki ba sai a shekarar 2003/2004.

Dama dai Cif Obasanjo, ya dauki alkawarin kasancewa daya daga cikin daliban da za a yaye a jami’ar.

Tsohon shugaban Najeriyar, ya ce ya yi wannan karatu ne saboda sha’awar da ya ke da ita a bangaren ilimi.

Farfesa Abdullah Uba Adamu, shi ne shugaban jami’ar, ya kuma shaida wa BBC cewa, a lokacin da Cif Obasanjo, ke karatu a wannan jami’a, ya kiyaye duk wasu dokoki da ka’idojinta kamar yadda sauran dalibai ke yi.

Farfesan ya ce, idan an bayar da irin aikin nan da ake yi a gida wato ‘assignment’ a turance, Obasanjo, bai taba fashin kawo na sa ba.

Sannan kuma Obasanjo, ya bukaci malaman da suke koyar da shi da su rinka adalci a karatunsu, inda ya ce musu kada su yi la’akari da girmansa ko matsayinsa ace za a raga masa.

Ya ce, a rinka yi masa duk abin da ake yi wa sauran dalibai, domin shi ma a sahunsu ya ke.

Farfesa Abdallah, ya ce karatun da Obasanjo ya yi a wannan jami’a, darasi ne ga sauran jama’a, musamman matasa, inda ya nuna cewa tsufa ba ya hana karatu.

Jami’an Rasha na shirin ficewa daga Birtaniya


Image caption

An zargi Rasha da hannu a harin gubar Nerve da aka kaiwa tsohon jami’in hukumar leken asiri mai cin tudu biyu

Jami’an diplomasiyyar Rasha 23 sun gama tattara kayansu dan barin birnin London a yau talata, bayan gwamnatin Birtaniya ta dibar musu wa’adin ficewa daga kasar.

Hakan ya biyo bayan tsamin da dangantaka ta yi tsakanin kasashen biyu, kan zargin Rasha na da hannu a harin gubar Nerve da aka kai wa tsohon jami’in leken asirin Rasha da Birtaniya Sergei Skripal da ‘yarsa Yulia a birnin Salisbusry.

A ranar asabar ita ma rashar ta sanar da jami’an diplomasiyyar Birtaniya su fice mata daga kasa.

Firaiminista Theresa May za ta gana da manyan jami’an hukumar tsaron Birtaniya dan sake tattaunawa kan matakin da ya kamata su dauka nan gaba.

Rundunar ‘yan sandan Birtaniya masu yaki da ta’addanci ta ce an yi kokarin kashe wani tsohon dan leken asirin Rasha da ‘yarsa a birnin Salisbury da wata guba.

Sergei da Yulia Skripal na asibiti cikin matsanancin rashin lafiya tun bayan da a ka tsince su a sume a kan wani benci ranar Lahadi,

Rahotanni sun nuna cewa da alama an sa ma Sergei da Yulia Skripal gubar ne da gangan.

Na’urorin Amurka za su maye gurbin ma’aikatan Afirka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kirkiri fasaha domin gudanar da wasu ayyukan da ya kamata mutum ya yi

Wani sabon rahoto ya yi gargadin cewa cikin kasa da shekara 20 nan gaba zai fi sauki da arha a yi amfani da na’ura a masana’antun Amurka maimakon a yi hayar ma’aikatan da za su yi aiki a Afirka.

An kirkiri fasaha domin gudanar da wasu ayyukan da ya kamata mutum ya yi, kuma suna aiki ba tare da taimakon mutum ba.

An yi hasashen cewa faduwar farashin na’urorin za su jawo rashin ayyukan yi a yayin da masu kamfanoni za su koma kasashen da suka fi karfin tattalin arziki.

Wasu masu sharhi sun ce wannan zai fi shafar kananan kasashe, ko da yake cibiyar nazarin ci gaban kasashen waje (ODI) na ganin ba haka ba ne.

Rahoton da cibiyar ta fitar ya nuna cewa kasashen Afrika suna da damar da za su rungumi sabon sauyin.

“Kasashen Afrika ba za su yi wasa ba a harakar masana’antu, kuma maimakon haka za su inganta hanyar samun damar intanet da zuba jari ga fannin fasaha da kirkire-kirkire,” a cewar Karishma Banga, babban jami’in bincike a cibiyar ODI.

Ya kara da cewa: “Idan har aka yi da kyau, fasaha dama ce ga kasashen Afrika wajen samar da ayyukan yi a masana’antu.”

Ana ganin sauyin ba zai shafi kananan kasashe ba saboda ba su da kudin da za su saka jari a fannin ci gaban fasahar.

“Bincikenmu ya nuna cewa wannan ya wuce kima. A yanzu kudaden tafiyar da na’urorin ya fi tsada idan aka kwatanta da lebaranci, amma wannan ba zai kasance ba a cikin shekaru 15,” kamar yadda Dirk Willem te Velde daraktan ODI ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Rahoton ODI ya gano cewa sauya tsarin tafiyar da ayyukan sarrafa katako zuwa kujeru da sauransu a Afrika zuwa ta hanyar Intanet ya fi arha a Amurka fiye da kudaden da ake samu na lebaranci a Kenya daga shekarar 2034.

A Habasha kuma zai fi sauki tsakanin 2038 zuwa 2042.

Rahoton ya ce wannan dama ce ga Afrika ta fara gina tunaninta tsakanin shekaru 10 zuwa 20 a fannonin fasaha da suka shafi abinci da tufafi.

Rahoton ya kuma ba kasashen Afrika shawara su inganta wadatuwar intanet da bunkasa ayyukan hannu ta hanyar bayar da horo tare da mayar da hankali kan darussan ci gaban fasaha a makarantun Ilimi na Afrika.

Yaushe za a doke Barcelona a La Liga?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallo 13 kawai ta shiga ragar Barcelona a La Liga a bana

Akwai yiyuwar Barcelona na iya kafa tarihi a bana a gasar La Liga ta Spain, a matsayin kungiya ta farko da ta buga dukkanin wasannin gasar ba tare da an doke ta ba.

Barcelona ta ci gaba da kare matsayinta na daya a kakar bana bayan ta doke Athletic Bilbao da ci 2-0 karawar mako na 29 da suka yi a ranar Lahadi.

Kuma yanzu Barcelona ta buga wasa 29 ba tare da an doke ta ba a liga a kakar bana, wasa 36 idan aka hada da kakar ta gabata.

Rabon da a doke Barcelona a lig tun a watan Afrilun bara da ta sha kashi a gidan Malaga da ci 2-0.

Barca ta ci gaba da zama ta daya a kan tebur da maki 75, tazarar maki 11 tsakaninta da Atletico Madrid wacce ta sha kashi a hannun Villarreal da ci 2-1 a ranar Lahadi.

Sau daya aka samu galabar Barcelona a bana a dukkanin wasa 45 da ta buga.

Espanyol ce ta doke ta a karawar farko da suka fafata a gasar Copa del Ray zagayen daf da na kusa da karshe, amma Barcelona ce ta yi waje da ita a karawa ta biyu.

Babu dai wani Kulub a tarihi da ya buga wasanni 38 ba tare da an doke shi ba a La Liga.

Real Sociedad ce ta taba buga wasanni 32 ba tare da an doke ta ba a kakar 1979-80.

Yanzu wasa tara ne ya rage a kammala gasar lig, kuma Barcelona ta ci 23, ta yi canjaras shida a wasa.

Hakazalika kwallo 13 kawai aka zura musu a wasa 29 na lig, yayin da kuma suka ci kwallo 74.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Messi ya ci kwallo 25 a La Ligar bana

Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce ya fi kaunar ya kammala La liga ba tare da an doke shi ba, da ace ya lashe kofuna uku da Barcelona ke hari a bana.

“Za mu yi kokarin lashe sauran wasannin da suka rage,” a cewar kocin, wanda wannan ce kakarsa ta farko a kulob din.

Yanzu Barcelona na jiran buga wasan karshe ne tsakaninta da Sevilla a gasar Copa del Ray ranar 21 ga watan Afrilu, a yayin da ta ke harin lashe kofin La liga karo na 25.

Sannan ana ganin Barcelona na iya kai wa zagayen kusa da karshe bayan an hada ta da Roma a gasar zakarun Turai.

Sai dai duk da cewa wasa tara ne ya rage a kammala La liga, wasu na ganin akwai kalubale a gaban Barcelona.

Daga cikin manyan wasannin da za su kasance kalubale ga Barcelona sun hada hada karawar da za ta yi tattaki zuwa Sevilla a ranar Asabar din karshen mako mai zuwa.

Da karawa da Valencia a ranar 15 ga Afrilu da haduwar Barcelona da Celta Vigo a ranar 18 ga Afrilu.

Sannan akwai karawar hamayya ta Clasico da Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a Nou Camp a ranar shida ga watan Mayu.

A karawar farko da suka yi a watan Disamba, Barcelona ce ta doke Madrid da ci 3-0 a Santiago Bernabeu.

Nicaragua: ‘Ana zargin wani da yunkurin hallaka tsohuwar matarsa’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan sanda sun cafke mutumin, jim kadan bayan an garzaya da matar asibiti cikin mawuyacin hali

‘Yan sandan kasar Nicaragua sun cafke wani mutum, da ake zargi da yunkurin hallaka tsohuwar matarsa ta hanyar bata wata guba da ake amfani da ita dan kashe kwari a gona.

An dai tsare mutumin bayan an garzaya da matar asibiti, wadda ta shiga mawuyacin hali sakamakon gubar Alminium Phosphide da tsohon mijin na ta ya yi.

‘Yan uwan matar sun yi kirarin an dura mata gubar ne a lokacin da tsohon mjin na ta ke jima’i da ita ta hanyar yi mata fyade da dama can ya saba aikatawa a lokacin da suke da aure.

Lamarin ya fusata mata a Nicaragua, masu rajin kare hakkin mata sun yi kira ga gwamnati ta kara daukar tsauraran matakai kan cin zarafin mata.

Amnesty ta zargi sojin Nigeria kan sace matan Dapchi


Image caption

Makonni hudu kenan da sace ‘yan matan sama da 100, har yanzu babu amo ba bu labarinsu

Kungiyar kare hakkin bil’adam ta Amnesty International, ta ce sojojin Nigeria sun yi biris da gargadin ‘yan Boko Haram za su kai hari, sa’o’i kalilan gabannin a sace ‘yan matan sakandaren Dapchi sama da 100.

Wata guda kenan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan matan a lokacin da suke makaranta a garin Dapchi na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.

Amnesty ta kara da cewa yawancin shugabannin al’umar yankin, sun sanar da sojoji tun lokacin da suka samu labarin jerin gwanon motocin maharan na wani kauye mai nisan kilomita 30 daga garin na Dapchi, kwana guda gabannin sace ‘yan matan.

Sun yi ikirarin ko a lokacin da maharan suka iso an sanar da sojojin, amma ba su yi wani abu a kai ba.

Maimagana da yawun sojin Nigeriaya ce tuni gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai yi kwakkwaran bincike kan gazawar jami’an tsaro a yankin da ta kai ga sace matan.

Kawo yanzu iyayen ‘yan makarantar na zaman zullumi da tashin hankalin rashin sanin ainahin inda ‘ya’yansu suke.

Sama da shekara Hudu kenan da sace ‘yan matan sakandaren Chibok sama da 200 da Boko Haram ta yi, gwamnatin Najeriyar ta kubutar da wasu daga ciki ta hanyar amfani da tattaunawa tsakanin ta mayakan bisa jagorancin kungiyar agaji ta Red Cross, kuma kawo yanzu sama da 100 ba a kubutar da su ba.

Manufar Yarjejeniyar kasuwancin bai-daya a Afrika


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kasashen Afrika sun fi huldar kasuwanci da Turai da Asiya.

A yau Talata ne ake bude taron shugabannin Tarayyar Afrka inda ake sa ran za su sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya.

Sai dai za a gudanar da taron ne ba tare da Najeriya ba, ta biyu a karfin tattalin arziki a Afrika, bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar da kauracewa taron da za a gudanar a Rwanda.

Wasu na ganin kasancewar Najeriya a taron yana da matukar amfani, saboda matsayin tattalin arzikinta a Afrika, kamar yadda wasu ke ganin amincewa da yarjejeniyar zai bunkasa kasuwanci da samar da dubban ayyukan yi.

Wasu kuma na bayyana shakku ne game da sharudda da kuma yadda za a aiwatar da yarjejeniyar kasuwancin ta bai-daya tsakanin kasashen na Afrika.

An dade ana tattauna yadda za a kulla yarjejeniyar, kusan shekaru da dama.

A karkashin yarjejeniyar, dukkanin kasashen Afrika 54 za su amince su rage harajin shigo da kayayyaki da nufin bunkasa kasuwanci tsakaninsu.

Wannan dai shi ne matakin farko ga samar da hadin guiwar fadada tattalin arziki tsakanin kasashen.

Hakazalika, ana bukatar ko wace kasa ya kasance ta amince babu harajin shigo da kayayyaki ko kuma babu wani banbanci ga tsarin harajinta na shigo da kayayyaki da sauran kasashen.

Daga nan za a kulla kasuwanci na bai-daya, inda za a yi cinikin kayayyaki kyauta tsakanin kasashen tare da hada kai domin karfafa dangantakar kasuwanci da sauran kasashen duniya.

Karin hadin kan kuma ya kunshi na siyasa da samar da kudin bai-daya.

Wakilin BBC da ke aiko da rahotanni kan kasuwanci a Afrika Matthew Davies ya ce wadannan bukatun sun dauki kungiyar Tarayyar Turai fiye da shekaru 50 kafin a kafa bayan kammala yakin duniya na biyu.

Ko da yake an samu wanzuwar irin wannan hadin kan a Afrika, kamar kungiyar kasashen gabashin Afrika da kuma ta yammacin Afrika ECOWAS.

Amma ga dorewar kasuwancin bai-daya, dole sai ya kasance an gudanar da mafi yawancin kasuwancin tsakanin kasashen Afrika.

Wakilin BBC ya ce wannan shi ne babban kalubalen da za a fuskanta, domin yawancin kasashen Afrika sun fi hulda ne da kasashen waje maimakon makwabtansu na Afrika.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afrika bai wuce kashi 16 ba duka. A tsakaninsu da kasashen yankin Asiya kuma kashi 51, a Turai kuma adadin ya kai kashi 70.

Hakan ya nuna yana da wahala yarjejeniyar kasuwancin ta bai-daya karbu cikin lokaci kankani.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya sai ta yi nazari kan alfanu da ribar yarjejeniyar kafin ta shiga

Wani babban kalubalen shi ne girman Afrika, musamman yawan kasashen da za su sanya hannu a kan yarjejeniyar.

A lokacin da aka fara a Turai a 1950, kasashe shida ne kawai suka sanya hannu, sai bayan shekaru sama 60 kafin Tarayyar Turai ta samu mambobi 28. Afrika kuma yanzu tana da kasashe 54.

Ko da yake yanzu Najeriya ta fice.

Yanayin kasuwancin bai-daya a irin yanki na Afrika babban jan aiki ne. Amma idan matakan farko da aka bi na neman hadin kan tattalin arziki ne da bunkasa cinikayyya a Afrika, to ba mamaki mutanen nahiyar za su amfana.

Shin ko kun san garin da kusan kowa ke tallan da asuwaki?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mata da maza a kauyen Abokim, na sayar da asuwaki

Bisa tarihi dai, kowanne gari da sana’ar da ya shahara a kai wadda kuma galibi al’umarsa ke dogaro da ita.

A kauyen Abokim, da ke karamar hukumar Etung a jihar Cross-River ta kudancin Najeriya, baya ga noma wanda shi ne gadon al’ummomin Afirka da dama, jama’ar kauyen, maza da mata manya da yara, babu sana’ar da suke yi kamar sana’ar ferewa da kuma tallan asuwaki ko magogi.

A kwanakin baya, wakilin BBC, Is’haq Khalid, ya ziyarci kauyen, inda ya kuma tattauna da wasu masu wannan sana’a.

Wakilin BBC, ya ce wasu masu wannan sana’a sun shaida masa cewa, shaharar wannan sana’a ta kai ga har jama’a daga wasu kasashen Afirka musamman Jamhuriyar Benin na zuwa garin wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru domin sarin asuwakin buhu-buhu zuwa kasashensu.

To sai dai kuma rikicin ‘yan aware da ake yi a yankin Kamaru mai magana da harshen Ingilishi, inda ake sayo itacen da ake ferewa domin yin magogin, ya fara kawo cikas ga sana’ar a garin na Abokim da ke kan iyaka.

Fatan jama’ar wannan yanki dai shi ne, sana’ar tasu ta kara bunkasa domin su samu karin kudin shiga, sannan ita ma Najeriya, ta kasance mai alfahari da fitar da magogi kasashen duniya don bunkasa tattalin arzikinta.

United ta tsawaita zaman Yound a Old Traffiord


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Young yana cikin ‘yan wasan da Ingila ta bai wa goron gayyata a wasan sada zumunta da za ta yi

Kungiyar Manchester United ta tsawaita zaman Ashley Young zuwa shekara daya, domin ya ci gaba da murza-leda a Old Trafford.

Dan wasan mai shekara 32, ya koma United daga Aston Villa a shekarar 2011 a matakin dan wasan gaba na gefe, amma yanzu ya koma mai tsaron baya a kungiyar.

Young ya lashe Kofin Premier da na FA da League Cup da na Europa a zaman da yake yi a Old Trafford.

Dan kwallon ya buga karawa 29 a kakar shekarar nan, inda ya ci kwallo biyu, ya kuma koma buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila tamaula.

Zuckerberg na fuskantar matsin lamba kan saba ka’ida


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mark Zuckerberg da Facebook sun musanta aikata ba daidai ba

Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg yana fuskantar matsin lamba kan bukatar ya bayyana domin a bincike shi a kan abun da shafin nasa ke yi.

Ana zargin kamfaninsa da kin shaida wa masu amfani da shi cewar ana tattara bayanan da suka sanya a shafukansu da kuma ajiye su a wani kamfanin sadarwa na Cambridge, wanda da aka sani wajen taimakawa Donald Trump lashe zaben shugaban kasa a 2016.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Facebook ya ce ya toshe kamfanin Cambridge Analytica daga shafin, yayin da yake bincike kan korafin cewa kamfanin mai cibiya a Landan bai goge bayanan da ake zargi ya samu ta hanyar karya ka’idojin Facebook ba kamar yadda ya yi alkawari.

Dukkan kamfanonin biyu dai Cambridge Analytica da Facebook sun yi watsi da batun cewa sun aikata ba daidai ba.

Tuni hannayen jarin Facebook suka fara yin kasa sakamakon matsin lambar da ya ke fuskanta.

Duk da alwashin da ya sha a 2018 cewa zai gyara kamfanin nasa, Mark Zuckerberg ya yi kokarin kaucewa sukar da yake sha daga dumbin mutane – a maimakon haka sai yake ta aike lauyoyi zuwa kwamitoci domin sauraron korafe-korafe.

An wallafa kalaman Zuckerberg na baya-bayan nan a kan wasu ce-ce-ku-cen da ke faruwa kan Facebook a wani kebabben shafin intanet, sannan aka wallafa a shafinsa na Facebook din.

Yayin da ake kara nuna damuwa kan yadda bayanan da Facebook ke tatattarawa za su kara iza wutar farfagandar siyasa, wasu manyan masu fada a ji a karshen wannan makon sun ce lokaci ya yi da Mista Zuckerberg zai kara kaimi don fitowa fili ya kare kansa kan wannan batu.

Wasu ma sun yi kira da a yi bincike kan ko kamfanin Mista Zuckerberg ya karya wasu dokoki na tattara bayanai, da kuma dokokin rashin samun izinin masu amfani da shafin don tattara bayanan da suka shafe su.

‘Kungiyar IS ce ta sace ‘yan matan Dapchi’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne aka sace ‘yan mata 110 daga makarantar Dapchi

Bangaren kungiyar Boko Haram da ke mubaya’a da kungiyar masu fafutika ta IS ne ya sace ‘yan makarantar sakandare ta Dapchi a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kafar yada labarai ta Amurka ta Wall Street Journal, WSJ, ta ce ta samu bayanan da suka tabbatar mata da cewa bangaren Abu Musab Abu Musab al-Barnawine suka sace ‘yan matan 110 a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Da ma dai an dade ana rade-radin cewa mayakan Abu Musab al-Barnawi, wanda suke kiran kansu reshen IS na Afirka ta Yamma, su ne da alhakin lamarin.

Sace ‘yan matan na Dapchi na zuwa ne shekara hudu bayan da Boko Haram karkashin jagorancin Abubukar Shekau suka sace sama da ‘yan mata 200 daga garin Chibok.

Editan WSJ a Afirka ya yi ta wallafa jerin karin bayanai kan rahoton a shafinsa na Twitter:

Sakon yana cewa: “Sabon rahotonmu kan sace ‘yan matan Dapchi ya bayyana abubuwa da dama kan yakin basasar da ke kunshe cikin Boko Haram”. Ga bayanan da za ku karanta:

Ya kara da cewa: “Wani bangare na kuniyar IS karkashin jagorancin Abu Musab al-Barnawi ba bangaren Abubakar Shekau ba, su ne suka sace yaran Dapchi.

Rahoton ya bayyana cewa shugaban kungiya mai alaka da IS din Abu Musab al-Barnawi, shi ne dan marigayi Muhammad Yusuf, tsohon jagora, kuma mutumin da ya kafa kungiyar ta Boko Haram.

WSJ ta ce shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ya nesanta kansa da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, kuma yana fuskantar matsin lamba daga kungiyar da ta balle din.

Rahoton ya ce a watan Agustar 2016 kungiyoyin biyu sun yi arangama da juna, abun da ya jawo mutuwar mayakansu 400.

Rahoton dai ya kuma ce an fara tattaunawar sirri domin kubutar da ‘yan matan na Dapchi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai tattauna da wadanda suka sace ‘yan matan don ceto su.

Najeriya: Yadda aka kama shahararren mai safarar makamai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An shafe shekara 10 ana neman Mista Abbey ruwa a jallo

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta sanar da cewa ta kama wani shahararren mai safarar bindigogi a kasar, wanda ke cikin jerin sunayen mutanen da take nema ruwa a jallo.

Ana zargin Jonah Abbey wanda aka fi sani da Jonah IDI, da sayar da makamai ga kungiyoyin masu tayar da kayar baya a jihohi da dama na kasar.

A wata sanarwa da hukumar DSS ta aike wa manema labarai a ranar Lahadi, ta ce tawagoginta sun yi aiki tukuru cikin kwana 10 da suka gabata inda suka kama masu aikata manyan laifuka da dama.

Sanarwar ta ce an yi nasarar kama masu satar mutane don karbar kudin fansa da masu safarar bindigogi da masu satar shanu wadanda ke ayyukansu a jihohin Filato da Taraba da Benue.

Najeriya na fama da rikice-rikice da suka shafi addini da kabilanci, inda ake amfani da muggan makamai ba tare da sanin inda jama’a ke samunsu ba.

Jami’an tsaro sun ce an shafe shekara 10 ana neman Abbey ruwa a jallo.

A cewar sanarwar: “A ranar 13 ga watan Maris ne da misalin 12.20 na rana aka yi nasarar kama Mista Abbey a garin Wukari na jihar Taraba tare da direbansa Agyo Saviour wanda aka fi kira da Dan-Wase.

“Wasu bayanan sirri na baya-bayan nan sun nuna cewa Mista Abbey ya aiki direbansa Saviour da makamai da harsasai daga Konduga a jihar Borno zuwa jihar Taraba.”

‘Shigo da makamai ya karu’

Hukumar DSS ta ce Mista Abbey yana da abokan kasuwanci a jihohin Filato da Ebonyi da Cross River da Enugu da Bayelsa.

“Kuma alamu sun nuna cewa yana samun makaman ne daga Jamhuriyyar Kamaru da kuma wasu sassan Arewa Maso Gabashin Najeriya,” in ji DSS.

Hukumar ta kuma ce ta kama wani mai satar mutane don kudin fansa Lawal Ibrahim da aka fi sani da Alhaji Awalu a Angwan Rogo da ke kan titin Bauchi a birnin Jos.

“Shi ne wanda ake zargi da kashe wani ma’aikacin gwamnatin jihar Filato Daanan Balgnan, a ranar 30 ga watan Disambar bara, kuma yana da hannu a wasu sace-sacen mutane a jihohin Nasarawa da Kaduna da Bauchi,” in ji DSS.

Image caption

Hukumar kwastam ta sha kama bindigogi a tashar jiragen ruwa ta jihar Lagos

Kazalika kuma a ranar 7 ga watan Maris ne jami’an DSS suka kama wani babban kwamandan “gungun ‘yan ta’adda” na Terwase Akwaza da aka fi sani da Ghana, wato Sesugh Aondoseer, a kusa da babbar kasuwar Makurdi ta jihar Benue.

Ana zarginsa da kitsa sace mutane da dama da fashi a Katsina Ala-Ukum da Gboko-Makurdi da kuma Takum a jihar Taraba.

An samu kudi kimanin naira miliyan 1.5 a hannunsa, wanda wani bangare ne na kudin fansa da suka karba bayan sace iyalan jami’in wata hukumar gwamnati.

Ba ya ga rikicin addini da na kabilanci, da satar mutane don kudin fansa, akwai kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda shi ma ke kara bazuwa a fadin kasar.

Hakan dai ya jawo asarar dumbin rayuka a kasar da kuma dukiyoyi, duk kuwa da kokarin da gwamnati ke cewa tana yi don kawo karshen wadannan matsaloli.

A makon da ya gabata ne wani rahoto na masana’antar kera makamai ta duniya wanda Cibiyar Binciken zaman lafiya ta Stockholm ta fitar, ya ce an samu karin shigar da makamai da kashi 42 cikin 100 a Najeriya cikin shekara hudu da suka gabata.

A shekarar 2017 ma hukumar fasa kwauri ta kwastom ta sha kama daruruwan binbdigogi da aka shigo da su kasar ba bisa ka’ida ba ta jihar Lagos, inda ake zargin daga Turkiyya aka shigo da su.

Sai dai ba a sake jin komai kan batun ba tun bayan da Shugaba Buhari ya ziyarci kasar Turkiyya a watan Oktobar 2017.

Wutar Daji ta kona gidaje a Ostreliya


Hakkin mallakar hoto
SIMON WARD

Image caption

Wutar ta yi barna mai yawa a jihar Victoria mai makwaftaka da jihar New South Wales

Masu kashe gobara a jihar New South Wales da ke kasar Ostreliya, sun ce sama da gidaje saba’in ne su ka kone a wata wutar daji da ta tilastawa daruruwan jama’ar jihar tserewa.

Masu bayar da agajin gaggawa sun bayyana cewa wutar ta fara lafawa, amma za’a dauki tsawon kwanaki kafin a kashe ta gaba daya. Gidaje da dama da wata makaranta a garin Tathra sun kone, inda jama’ar garin su ka tsere domin kubucewa wutar.

Rahotanni sun nuna cewa wutar ta mamaye Tathra yayin da yanayin zafi ya kai maki 38 a ma’aunin yanayi na Celcius. Kuma iska mai karfi ta rika rura wutar. Masu kashe gobara dari da hamsin ne su ka raba dare wajen kokarin kashe wutar wacce a yanzu ta lafa.

A na dai zaton tsawa ce ta yi sanadiyyar wutar dajin. Wutar ta yi barna mai yawa a jihar Victoria mai makwaftaka da jihar New South Wales.

Puigdemont: Kataloniya za ta amince da kwarya-kwaryar ‘yanci


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mr Puigdemont ya tsere Belgium bayan da Catalonia ta ayyana ‘yancin kai a wata Oktobar bara

Shugaban awaren Catalonia, Carles Puigdemont ya ce Kataloniya za ta iya yadda da irin tsarin mulkin kasar Switzerland na kwarya-kwaryar ‘yanci a maimakon cikakken ‘yanci daga Spaniya.

Mr Puigdemont, wanda ya tsere Belgium bayan da Kataloniya ta ayyana ‘yancin kai a wata Oktobar bara ya ce ya na bakin ciki da cewar za a daure shi a gidan kaso idan ya fadi ra’ayinsa a Spaniya.

Dubban ‘yan Kataloniya sun yi wata zanga-zanga a birnin Barcelona domin nuna tsananin adawarsu ga neman ‘yancin kan.

Tsohon Firam ministan Faransa wanda kuma haifaffen Kataloniya ne, ya ce ba a yi nasara ba a shirin neman ‘yancin kan, a yayin da Turai da gwamnatin Spaniya da al’ummar Kataloniya ke nuna adawa ga shirin.

Tasmeniya : Jihar da mata suka fi maza yawa a majalisa


Hakkin mallakar hoto
TASMANIA LABOR

Image caption

Shugabar jam’iyyar adawa Rebecca White (hagu) tare da mataimakiyarta Michelle O’Byrne

Jihar Tasmeniya ta kafa tarihi a matsayin wadda ta zabi ‘yan majalisa mata fiye da maza a karon farko.

Jihar ce mfi kankanta a cikin jihohin Ostreliya, ta gudanar da zabuka a ranar 3 ga watan Maris, amma sai a wannan makon aka kammala kidayar kuri’u.

Amma yankin babban birnin Ostreliya ma ya taba zaban mata a majalisar yankin da suka zarce maza a 2016, sai dai yankin ba ba jiha ba ne.

An zabi mata 13 da maza 12 a majalisar wakilai ta Tasmeniya. ‘Yan siyasa daga jihar sun ce lamarin abin “alfahari ne kwarai”.

“Yana nuni ga mata masu tasowa cewa akwai haske ga mata domin cimma muradansu na siyasa,” inji Michelle O’Byrne, wadda ita ce mataimakiyar shugabar jam’iyyar Labor masu adawa ta fada wa BBC.

The Tasmania and ACT legislatures have a higher proportion of women than Australia’s federal parliament, where almost 70% of parliamentarians are men.

Amma a majalisar tarayyar Ostreliya, maza ne suke da rinjaye, inda kimanin kashi 70 cikin 100 na ‘yan majalisar maza ne.

Zaben Rasha: Vladimir Putin ya sami gagarumar nasara


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mista Putin ya shafe kusan shekara 20 yana mulkin Rasha

Vladimir Putin zai cigaba da mulkin Rasha na wasu shekaru shida baya da ya lashe zaben shugaban kasa a karo na hudu.

Bayan da aka kusan kammala kididigan kuri’un da aka kada, ya sami kashi 76 cikin dari, inji hukumar zabe ta kasar.

An hana babban mai adawa da Mista Putin, Alexei Navalny daga tsayawa takara a wannan zaben.

Bayan da aka bayyana wani bangare daga cikin sakamakon zaben, ya gaya wa magoya bayansa cewa masu kada kuri’a “sun fahimci tasirin cigaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan”.

Ya fada wa manema labarai cewa ba zai cigaba da neman shugabancin kaar ba har illa ma sha Allah:

“Wannan abin dariya ne. Kana ganin zan cigaba da zama a nan har sai na kai shakara 100 da haihuwa? Ina!” inji shi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Bayan da aka bayyana wani bangare na sakamakon zaben, Mista Putin ya gana da magoya bayansa

Real Madrid ta shararawa Girona kwallaye


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid ta koma ta uku a kan teburin La Liga

Real Madrid ta ci Girona 6-3 a Gasar Cin Kofin La Liga wasan mako na 29 da suka kara a ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Real ta ci kwallon farko ta hannun Cristiano Ronaldo minti 10 da fara wasa, yayin da minti 19 tsakani Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Cristiano Ronaldo ya kara na biyu, sannan Lucas Vazquez ya kara na uku, sai Cristiano Ronaldo y ci na hudu kuma na uku da ya ci a karawar.

Cristhian Stuani ne ya kara farkewa Girona kwallo na biyu, inda Real ta kara na biyar ta hannun Gareth Bale.

Girona ta ci kwallo na uku ta hannun Juanpe, sai dai kuma Real Madrid ta ci na shida ta hannun Cristiano Ronaldo kuma na hudu a wasan.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta uku a kan teburi da maki 60.

Man United za ta kara da Tottenham a FA


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United tana ta biyu a kan teburin Premier, yayin da Tottenham ke ta hudu

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta raba jadawalin Gasar Cin Kofin Kalubalen kasar a wasannin daf da karshe a ranar Lahadi.

Jadawalin ya nuna cewar Manchester United za ta kara da Tottenham, yayin da Chelsea za ta kece-raini da Southampton.

Wasannin na Cin Kofin Kalubalen ya koma tsakanin kungiyoyin da ke buga Premier, inda Manchester United ta kai wannan matakin bayan da ta ci Brighton 2-0 a ranar Asabar.

Tottenham kuwa Swansea ta ci 3-0 a ranar ta Asabar, ita kuwa Chelsea ta doke Leicester City 2-1, yayin da Southampton ta ci Wigan 2-0 a ranar Lahadi.

Za a yi wasannin ne a Wembley tsakanin 21 zuwa 22 ga watan Afirilun, 2018.

United wadda ke matsayi na biyu da kwantan wasa daya a teburin Premier tana da kofin FA 12, ita kuwa Tottenham mai kwantan wasan Premier ta hudu a kan teburi tana da FA takwas.

Chelsea ita ma mai kwantan wasa daya a Premier kuma ta biyar a teburi ta lashe kofin sau bakwai, inda Southampton ta 18 ta taba ci sau daya a 1976.

Najeriya: Me ya sa Buhari ya fasa zuwa Rwanda?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya za ta yi nazari kafin amincewa da yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fasa zuwa Rwanda domin halartar wani taron shugabannin Tarayyar Afrika kan yarjejeniyar kasuwanci.

Shugaban zai halarci taron ne kan batun yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya da za a gudanar ranar Talata kafin sanar da fasa zuwansa.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harakokin wajen Najeriya ta ce an soke tafiyar shugaban ne don samun isasshen lokacin da za a yi nazari mai zurfi game da yarjejeniyar da kasashen Afrika suka amince a kafa a watan Janairun 2012.

Yarjejeniyar ta shafi gudanar da kasuwanci kyauta ba haraji tsakanin kasashen da suka sanya hannu.

A ranar Larabar da ta gabata ne majalisar zartawa ta amince Najeriya ta shiga yarjejeniyar.

Wannan ne ya sa shugaba Buhari zai tafi Rwanda domin sanya hannu.

Wasu masu sharhi na ganin, an amince Najeriya ta shiga kawancen ba tare da diba ribar da kasar za ta samu ba idan har ta shiga.

Tuni dai wasu jami’an gwamnati suka isa Kigali, yayin da wasu rahotanni a Najeriya suka ce an bukaci su dawo bayan Buhari ya fasa tafiya taron.

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi gargadi game da amincewa da yarjejeniyar, inda ta ce matakin zai gurgunta masana’antu tare da haifar da rasa guraben ayyukan yi ga ‘yan kasa.

Yanzu dai ba a san matsayin Najeriya ba a yarjejeniyar.

Chelsea ta kai daf da karshe a FA


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chelsea tana ta biyar a kan teburin Premier da maki 56 da kwantan wasa daya

Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da karshe a Gasar Cin Kofin Kalubalen Ingila na bana, bayan da ta ci Leicester City 2-1 a ranar Lahadi.

Morata ne ya fara ci wa baki kwallo saura minti uku a tafi hutun rabin lokaci, bayan da aka dawo ne Jamie Vardy ya farke, inda karawar ta kai ga karin lokaci.

Pedro ne ya ci wa Chelsea kwallo na biyu a minti na 105, hakan ne ya kai Chelsea wasan daf da karshe a gasar shekarar nan.

Kungiyoyin da suka kai wannan matakin sun hada da Manchester United wadda ta ci Brighton 2-0 a ranar Asabar, ita kuwa Tottenham ta doke Swansea 3-0.

A ranar Lahadi ne sabon kofin Soutahmpton, Mark Hughes ya kai kungiyar wasan daf da karshe a kofin FA, bayan da ya yi nasarar cin Wigan 2-0.

Barca ta yi wasa 29 a jere a La Liga ba a doke ta ba


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, kuma har yanzu ba a doke ta ba

Barcelona ta yi nasarar cin Athletic Bilbao 2-0 a Gasar Cin Kofin La Liga wasan mako na 29 da suka fafata a Nou Camp a ranar Lahadi.

Barcelona ta fara cin kwallo ta hannun Paco Alcacer a minti na takwas da fara tamaula, sannan Lionel Messi ya kara na biyu saura minti 15 a tafi hutu.

Da wannan sakamakon Barcelona ta buga karawa 29 a Gasar Cin Kofin La Liga ta shekarar nan ba a doke ta ba, inda ta ci wasa 23 ta yi canjaras a karawa shida.

Barca ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 75, bayan da Atletico Madrid wadda ke da maki 64 ke ziyartar Villarreal.

‘Yan Real 18 da za su kara da Girona


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga, bayan da aka buga karawa 28

Real Madrid za ta karbi bakuncin Girona a wasan mako na 29 a Gasar Cin Kofin La Liga da za su kece-raini a Santiago Bernabeu a ranar Lahadi.

Tuni kocin Real, Zinedine Zidane ya bayyana ‘yan wasa 18 da su fafata da Gironar.

Wannan shi ne karo na biyu da kungoyin biyu za su kara a Gasar ta La Liga, bayan da Girona ta doke Real 2-1 a wasan farko da suka yi a ranar 29 ga watan Oktoban 2017.

Real tana mataki na hudu a kan teburi da maki 57, ita kuwa Girona tana da maki 43 a matsayi na bakwai a wasannin bana.

Yan wasan Real 18 da za su fuskanci Girona:

Masu tsaron raga: Navas da kuma Casilla.

Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Varane da Nacho da Marcelo da kuma Theo.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Asensio da Isco da kuma Kovacic.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo da Benzema da Bale da kuma Lucas Vazquez.

Damben Audu Argungu da Sojan Kyallu


Dambe sama da 13 aka fafata a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada wannan rahoton

Cikin karawar an yi kisa a wasa bakwai ciki har wasan da Audu Argungun daga Arewa ya buge Sojan Kyallu daga Guramada a turmin farko, sauran damban babu kisa wato canjaras aka tashi.

Wasannin da aka yi kisa:

 • Bahagon Dan Sama’ila daga Kudu ya buge Bahagon Dan Jibga daga Arewa.
 • Bahagon Dan Sama’ila daga Kudu ya doke Shagon Bahagon Maru daga Arewa.
 • Shagon Bahagon Gurgu daga Kudu ya doke Shagon Dan Aminu daga Arewa.
 • Dan Yalo daga Arewa ya yi nasara a kan Shagon Bahagon Kanawa daga Kudu.
 • Gudumar Dan Jamilu daga Arewa ya buge Dogon Aleka daga Kudu.
 • Bahagon Sisco daga Kudu ya doke Dan Aliyu Langa-Langa daga Arewa.

Dambatawar da aka yi canjaras kuwa:

 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Bahagon Dogon Aleka daga Kudu.
 • Nasiru Shagon Bahagon Gurgu daga Kudu da Shagon Aminu daga Arewa.
 • Bahagon Roget daga Arewa da Bahagon Jafaru daga Kudu.
 • Shagon Kunnari daga Kudu da Shagon Shagon Alhazai daga Arewa.
 • Dan Yalow Autan Sikido daga Kudu da Bahagon Alin Tarara daga Arewa.
 • Dogon Bahagon Sisco daga Kudu da Autan Dan Bunza daga Arewa.
 • Shagon Dogon Kyallu Guramada da Bahagon Dan Shago daga Arewa.

‘Yan taxi za su dauki tsofaffi kyauta a Afrika ta kudu


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An fi amfani da bus a matsayin taxi a Afrika ta kudu

Wasu ‘Yan taxi a Afrika ta kudu sun sanar da matakin daukar mutanen da suka haura shekaru 70 a kyauta.

Wani dan taxi da mai suna Yassen Abrahams ne ya fara sanar da daukar matakin a shafinsa na facebook.

Daga baya kuma abokan aikinsa su ma suka amince su dauki masu manyan shekarun kyauta a Bonteheuwel.

Abharams mai shekaru 25 ya sha yabo a shafukan sada zumunta na intanet musamman a garin Bonteheuwel, da ke kusa da Cape Town.

Ya ce daga karfe Tara na safe, duk fasinjan da ya haura shekaru 70, za a dauke shi ne a kyauta.

Daga karfe 10 kuma a ranakun karshen mako.

Abhrams ya ce ya lura da wadanda suka yi ritaya da kyar suke iya biyan kudin taxi, domin ya sha daukarsu a kyauta.

Sannan a cewarsa: “A kullum zauna-gari-banza na tilasta muna mu ba su kudi ko kuma mu dauke su a kyauta, wannan ya sa wani tunani ya zo min cewa, me ya sa ba za mu dauki tsofaffi a kyauta ba? Yawancinsu ba su da lafiya kuma ba su iya tafiya.”

Ya ce mutuwar mahaifiyarsa a 2016 ta girgiza shi, kuma daga lokacin ne ya fara lura da yanayin tsofaffi, inda yawancinsu ba su da kudin shiga taxi.

Bayan samun goyon baya a garinsa yanzu Mista Abraham yana kira ga ‘yan taxi a fadin kasar su taimakawa mabukata a cikin al’umma.

Dokar zabe: Saraki da Dogara sun hade kai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bukola Saraki da Yakubu Dogara za su dauki mataki guda kan sauya dokar zabe

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara sun bayyana matsayinsu kan batun sauya dokar zabe.

Shugabannin majalisun Tarayyar guda biyu a Najeriya sun ce za su dauki mataki da murya daya.

Saraki da Dogara sun bayyana haka ne a cikin sanarwar hadin guiwa da masu magana da yawunsu suka rabawa manema labarai.

Sun fitar da sanarwar ne domin mayar da martani ga labarin da wasu jaridun Najeriya suka buga cewa an samu sabanin ra’ayi tsakanin Saraki da Dogara kan batun sauya dokar zabe.

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya yi watsi da kudirin, a cikin wasikar da ya aikawa zauren majalisun tarayyar guda biyu.

Shugaban ya yi watsi da kudirin ne, duk da ya samu amincewar majalisun tarayyar guda biyu.

Sanarwar da shugabannin majalisar suka fitar ta ce “Muna son kowa ya sani cewa muna kan ra’ayi daya game da matakin da ya kamata mu dauka kan watsi da sauya dokar zabe da shugaba Buhari ya yi.”

Sanarwar ta kara da cewa, shugabannin majalisar sun tattauna kuma sun amince a kan matakin da ya kamata su dauka da yadda za su dauki matakin da lokaci da kuma dalilin daukar matakin.

Tuni dai ‘Yan majalisar suka ce za su yi gaban kansu su amince da dokar duk da shugaban bai amince ba.

Sun ce ba wai don bukatarsu ba suke son a sauya dokokin zaben, illa don a inganta mulkin dimokuradiya.

Shugabannin majalisar kuma sun ce doka ta ba majalisa dama da ‘yanci ta yi gyara ga dokokin.

Kudirin wanda majalisun biyu suka amince ya shafi sauya dokokin zaben Najeriya, ciki har da fara gudanar da zaben ‘yan Majalisar Tarayya kafin na shugaban kasa.

Amma cikin wasikar watsi da kudirin da shugaba Buhari ya aika wa majalisar, ya ce kudirin ya saba wa ‘yancin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke da alhakin shiryawa da gudanar da zaben, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Ana zaben shugaban kasa a Rasha


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tun a 1999, Vladimir Putin ke shugabanci a Rasha

An bude runfunar zaben shugaban kasa a Rasha, inda shugaba Vladimir Putin ke neman wa’adin shugabanci na hudu.

Tun a ranar Asabar aka soma zaben a gabashin Rasha, sa’a tara tsakani kafin a fara zaben a Moscow.

Shugaba Putin da ke neman sake wasu shekaru shida kan mulki, na fafatawa ne da ‘yan takara guda bakwai a zaben.

Bayan ya jefa kuri’arsa, a Moscow, Mista Putin ya ce yana ganin nasara a sakamakon da zai ba shi “hakkin gudanar da aikin shugaban kasa.”

Daga cikin masu hamayya da Putin a zaben, sun hada da attajirin Rasha Pavel Grudenin da kuma dan kishin kasa Vladimir Zhirinovsky.

An haramta wa babban mai adawa da gwamnatin Rasha, Alexei Navalny, shiga zaben.

Mista Navalny ya yi kira ga magoya bayan shi su kauracewa zaben.

Tun a 1999, Vladimir Putin mai shekaru 65, ke shugabanci a Rasha, ko dai a matsayin shugaban kasa ko kuma Firaminista.

Rahotanni sun ce a wasu yankuna, ana janyo ra’ayin mutane su fito su kada kuri’a ta hanyar ba su abinci kyauta ko kuma da rahusa a gidajen cin abinci da ke yankunan.

Kamfanin dillacin labaran kasar na Interfax ya ruwaito cewa mutane sun fito sosai domin kada kuri’a a gabashin kasar.

Wannan zaben shi ne na farko da aka taba gudanar wa a Crimea tun lokacin da yankin ya dawo ikon Rasha daga Ukraine.

Zaben na zuwa a daidai lokaci n da ake cika shekaru hudu da shugaba Putin ya kaddamar da yankin Crimea a matsayin ikon Rasha, matakin da Ukraine da kasashen yammaci ke ci gaba da adawa da shi.

Mohamed Salah ‘na iya maye gurbin Messi ‘- Jurgen Klopp


Hakkin mallakar hoto
Reuters/Getty Images

Image caption

An fara kamanta bajintar Mohamed Salah da ta Lionel Messi

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce Mohammed Salah na kan hanyar zama shahararren dan wasa kamar Lionel Messi bayan da ya zura wa Watford kwallo 4 a jiya Asabar.

Salah ne dan wasan da ke kan gaba a yawan kwallaye a dukkan manyan lig-lig guda biyar na Turai – inda ya tsere wa Lionel Messi na Barcelona da Harry Kane na Tottenham.

Amma klopp ya ce Salah mai shekara 25 da haihuwa ba ya damuwa da abin da wasu ‘yan wasan ke yi:

“Ba na jin Mo na son a rika kwatanta shi da Lionel Messi”.

“Messi ya shafe tsawon lokaci yana gogewa a wasan kwallo. Kai kace ya shafe shekara 20 yana taka leda.”

“Ina ganin dan wasan da ke da irin wannan tasirin a kan wata kungiya sai Diego Maradona.”

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mohammed “Mo” Salah

Shi ma tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya yi imanin cewa “muna shaida farkon faruwar wani shaharraren dan wasa”.

Kwarewar Salah da kamanninsa da Maradona sun sa har ana kamanta shi da yadda Messi ke cin kwallyensa.

It took just four minutes for Salah to open the scoring against Watford, jinking his way through the Hornets’ defence and leaving Miguel Britos on the floor before firing home.

It was eerily reminiscent of a goal Messi scored against Bayern Munich in the 2015 Champions League semi-final, when he left Jerome Boateng sprawled on the turf.

But Salah remains humble about his talents, thanking his team-mates and saying a clean sheet against Javi Gracia’s side was “most important”.

“Mo is in a fantastic way, that’s for sure,” Klopp added. “The boys love playing together with him, and he loves playing with them

‘Yan wasan Turai da suka fi cin kwallaye (Daga: Opta)
Sunan dan wasa Yawan kwallo
Mohamed Salah 36
Harry Kane 35
Lionel Messi 34
Ciro Immobile 34
Edinson Cavani 33
Cristiano Ronaldo 33
Robert Lewandowski 32
Sergio Aguero 30
Neymar 28

Salah – the record-breaker

 • Salah ya zura kwallo 36 a kungiyar Liverpool a dukkan wasannin da ya buga mata – a shekarasa ta farko a kungiyar.
 • Ya ci kwallo 28 a gasar firimiya ta bana – Didier Drogba ne kawai dan wasa daga Afika da ya fi shi kokari (Drogba ya ci kwallo 29 a kakar 2009-2010).
 • Salah shi ne dan Masar na farko da ya fara cin kwallaye uku aa wasa guda a gasar firimiyar Ingila.
 • Salah ya ci kwallo hudu daga shot hudu da ya buga – wannan ne karon farko da wani dan wasan firimiya ya yi haka tun 2009 da Andrey Arshavin ma ya kafa tarihi, shi ma a Anfield.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salah shi ne dan Masar na farko da ya fara cin kwallaye uku aa wasa guda a gasar firimiyar Ingila

An harbe wasu masunta a Tafkin Cadi


Hakkin mallakar hoto
BOKO HARAM

Image caption

Harin dai ya faru ne a tsibirin Tudun Umbrella a tafkin Cadi, wanda ke da iyaka da Najeriya, da Cadi da Kamaru

Wasu da a ke zargin mayakan boko haram ne sun harbe wasu masunta guda biyar a wani tsibiri a arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban kungiyar masunta na jihar Barno, Abubakar Gamandi ya ce an kashe mutanen ne saboda su na taimakawa sojoji wajen cigiyar daliban makarantar Dapchi da ‘yan boko Haram din suka sace a watan jiya.

Har yanzu dai ba a gano daliban ba.

Harin dai ya faru ne a tsibirin Tudun Umbrella a tafkin Cadi, wanda ke da iyaka da Najeriya, da Cadi da Kamaru.

Manchester United 2-0 Brighton & Hove Albion


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda aka fafata: Manchester United 2-0 Brighton

Romelu Lukaku ya ci kwallonsa ta 12 a gasar FA yayin da man U ta doke Brighton kuma kungiyar ta kai matakin dab da na karshe kenan.

Lukaku ya ci kwallo ta farko ne da ka bayan da Nemanja Matic ya aika masa da wani kuros, kuma shi ne ya ci kwallo ta biyu daga wani firikik daga Ashley Young.

Wanna na nufin cewa Manchester United na da damar cin wata gasa a kakar wasan bana bayan da Sevilla ta yi waje da ita daga gasar Zakarun Turai.

Kawo yanzu, babu kungiyar da ta saka wa United kwallo a raga a gasar ta FA a bana.

Brighton ta rika kai farmaki sau da yawa kafin a karshe Matic ya kwaci kungiyarsa.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Romelu Lukaku ya ci kwallo 25 a wasanni 44 da ya buga wa Manchester United a karkar wasa ta bana

Afrin: Siriya na dab da karbe birnin daga hannun YPG


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kurdawa na gudun daga birnin Afrin saboda yaki

Sojojin Tukiyya tare da ‘yan tawayen Syria na dab da karbe garin daga hannun mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.

An yi wa garin wanda ke arewacin Syria kofar rago, kuma mazauna garin su kimanin 350,000 na ta ficewa ta wata hanya daya da ta rage musu kafin abinci da ruwa su kare baki daya.

Turkiyya ta ce mayakan YPG ‘yan ta’adda ne, kuma ta ce suna da alaka da ‘yan tawayen Kurdawa da suka dade suna yakin neman kafa kasarsu a cikin Turkiyya.

Amma kasashen yammacin Turai na kallonsu a matsayin abokan tafiyarsu ne a yakin da su ke yi da kungiyar IS.

Wata mata mai suna Ranya na daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su a garin na Afrin:

“Jiya da rana an rika kai hari kan motocin da ke makare da mutanen da ke kokarin tserewa daga yakin. Ko ina ka duba sai gawarwaki, kuma cikin dare jiragen yaki sun kai wa asibitin Afrin hari.”

Kungiyar YPG da wata kungiyar masu sa ido sun ce wani harin jirgin yaki da Turkiyya ta kai a kan asibitin ya halaka fararen hula 16.

Amma Turkiyya ta musanta tuhumar da ake mata, kuma ta fitar da wani bidiyo da ke nuna cewa asibitin na nan kalau.

Majalisar Turai da ministan harkokin waje na Faransa sun nemi Turkiyya da ta dakatar da wannan yunkurin sojin na karbe garin da ta ke yi.

Adikon Zamani: Haihuwa da rainon ciki a karkara


Ku latsa alamar hoton da ke sama don sauraron cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zahra Umar ta yi da wasu matan a karkara:

A wannan makon shirin Adikon Zamani ya yi duba kan irin wahalhalun da matan karkara ke fuskanta yayin goyon cikin da haihuwa.

A don haka ne muka yi tattaki zuwa garin Sandamu da ke jihar Katsina, kuma na gamsu da yadda nag a mata na kokarin yin abubuwa masu muhimmanci don ci gaban rayuwarsu duk da irin kalubalan da suke fuskanta.

Matan da muka hadu da su gwaraza ne da ke tsaye a kan kafafunsu duk da dumbin matsalolin yau da kulllum da rashin ababen more rayuwa.

Da dukkan alamu dai kauyukan da ke arewacin Najeriya bas u samu ci gab aba tun shekarun 1960.

Har yanzu da hannu suke surfa tsabar da za su yi abinci, su daka, su girka da kara, sannan kuma su deebo ruwa a rijiya ko rafi.

Har yanzu a gida suke haihuwa ba tare da samun kulawar zamani ta likitoci ba.

Ga dukkan alamu dai gwamnatocinmu ba su mayar da hankali sosai ba don ci gaban kauyuka a shekarun nan, kuma hakan ya fi shafar mata kai tsaye.

Na hadu da wata matashiya wadda ta yi kaura daga wani babban gari zuwa kauye don kawai ta rayu da namijin da ta kamu da sonsa a waya! Labarinta na da matukar jan hankali.

Mai yiwuwa ne mu matan birni mu koyi wani abu daga matan karkara, kamar rike zumunci, da kyautatawa, saboda gaskiya mutanen kauye suna da kirki, ba munafunci sai aminci da yarda da juna.

Fatana shi ne mu hada hannu mu kyautata rayuwar mata da yaran da ke arewacin Najeriya.

Rasha za ta kori ma’aikatan jakadancin Burtaniya 23


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Gwamnatin Rasha ta sammaci jakadan Burtaniya a kasar Laurie Bristow

Hukumomin Rasha sun ce za su kori ma’aikatan jakadancin Burtaniya 23 daga kasar a lokaci da dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu sakamakon harin guba da aka kai kan tsohon ma’aikacin leken asirin Rasha da ‘yarsa a London.

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce za ta kori ‘yan kasar ta Burtaniya a mako daya.

Ta kara da cewa za ta rufe cibiyar raya al’adun Burtaniya, British Council, da ke Rasha sannan ta yi watsi da damar da ta bai wa Burtaiya ta bude karamin ofishin jakadancinta a St Petersburg.

Mahukuntan Rasha sun dauki matakin ne bayan gwamnatin Burtaniya ta kori ma’aikatan jakadancin Rasha 23 daga Burtaniya.

An ce su fice daga kasar ne bayan abin da ya faru ranar hudu ga watan Maris, wanda Burtaniya ta dora alhakinsa kan Rasha.

A wata sanarwa da ma’aikatar wajen Rasha ta fitar ta yanke shawarar rufe cibiyar raya al’adun Burtaniya a Rasha kana ta yi watsi da damar da ta bai wa Burtaiya ta bude karamin ofishin jakadancinta a St Petersburg.

Har yanzu tsohon jami’in leken asirin Rasha Sergei Skripal, mai shekara 66, ada ‘yarsa Yulia Skripal, mai shekara 33, na kwance magashiyan a asibiti, bayan an gano su cikin mummunan hali a kan wani benci a Salisbury da ke Wiltshire.

Gwamnatin Burtaniya ta ce an watsa musu wata guba da ke kashe laka da aka kirkira a Rasha mai suna Novichok, sanna Firai Minista Theresa May ta ce ta yi amanna mahukuntan Rasha na da hannu a lamarin.

Maciji ya kashe mutumin da ke ‘auren macizai’


Hakkin mallakar hoto
Abu Zarin Husin

Image caption

Abu Zarin Hussin ya sha daukar selfie da macizai

Dan kasar Malaysia din nan da ya yi suna saboda basirarsa ta iya wasa da macizai ya mutu bayan wata kububuwa ta sare shi.

Abu Zarin Hussin, wanda ma’aikacin kashe gobara ne, ya yi fice ne bayan wasu jaridun Burtaniya sun wallafa labaran da ke cewa shi dan kasar Thailand ne da ya auri macijiya.

Mr Hussin ya bai wa sauran ma’aikatan kashe gobara horo kan yadda za su iya sarrafa macizai.

Ranar Litinin aka kwantar da shi a asibiti bayan macijiyar ta sare shi lokacin da suke aikin kama macizai.

Jairdar The star da ake wallafawa a kasar ta ce mutumin, dan shekara 33 wanda ke zaune a jihar Pahang, yakan koya wa takwarorinsa yadda za su gane nau’uklan macizai daban-daban kuma yana kama su ko da yaushe ba tare da ya kashe su ba.

Ya taba fitowa a wani shirin talbijin da ke tattaunawa da hazikan mutane, Asia’s Got Talent, inda aka nuna shi ya sumbaci wani maciji.

Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Macijin da ya kowanne nau’in macizai dafi

A 2016, wani labari da kafofin watsa labaran Thailand- da ma na Burtaniya – ya ce Mr Hussin dan kasar Thailand ne da ya auri wata macijiya, yana mai cewa “budurwarsa” wacce ta mutu ta dawo a siffar maciji.

An yi amfani da hotunan da Mr Hussin ke wallafawa a shafinsa na sada zumunta wurin gina labarin da ke nuna shi yana wasa da macizai.

Mr Hussin, wanda ya ajiye macizai hudu a gidansa domin fahimtar halayensu, ya taba shaida wa manema labarai cewa: “Sun yi amfani da hotunana domin wallafa labaran kanzon-kurege cewa na auri macijiya.”

He later told the BBC he was “very disappointed” by the fake reports.

Xi Jinping zai kara shekaru biyar a kan mulki


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An kada kuri’ar ne a babban dakin taro na Great Hall of the People da ke birnin Beijing

Majalisar dokokin kasar China ta kada kuria’ar sake nada Xi Jinping a matsayin shugaban kasar a karo na biyu na wa’adin shekara biyar.

Haka kuma, majalisar ta nada Wang Qishan, wani makusancin Shugaba Xi kuma tsohon mai yaki da cin hancin da rashawa a matsayin mataimakin shugaban kasar.

An kada kuri’ar ne a babban dakin taro na Great Hall of the People da ke birnin Beijing.

A makon da ya gabata ne dai majalisar ta cire iyakance wa’adin shugabancin kasa daga kundin tsarin mulkin kasar, inda hakan ke nufin cewa Mr Xi na iya mulkin kasar har abada.

Robert Mugabe: A gayyace ni domin gyaran Zimbabwe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe ya gana da manema labarai inda ya ce rashin adalcin ne da aka tsige shi daga mulki a watan Nuwambar bara.

Yawancin ‘yan kasar ba su zaku da ganin ya koma kan mulki ba. Yawancin su na ganin lamarin kamar wani mafarki ne ya nuna yana son komawa kan mulki bayan ya shafe fiye da shekara 30 yana mulkin kasar.

Babban dalilin da ke bayan kalaman fatar Mugabe na neman ya koma kan mulki bai wuce na rarrabuwar kawunan ‘yan kasar ba.

A bayyane ta ke cewa bangaranci ya riga ya yi wa kasar illa – kamar yadda lamarin ya ke a makabciyar ta – Afirka ta Kudu.

Kuma a halin da ake ciki yawancin ‘yan kasar na fama da matsalolin yau da kullum, kuma fatar su ita ce sabon shugaban kasa Mnangagwa ya iya kawo sauyi mai ma’ana a rayukansu ta farfado da tattalin arzikin kasar.

Mugabe ya gana da manema labarai ne a gidansa da ke kusa da birnin Harare, inda yarika kokarin nuna cewa har yanzu yana da sauran iko a siyasar kasar.

Ya bukaci da lallai sai a gayyace shi ya shiga tafiyar mayar da kasar kan tafarkin tsarin mulki a siyasance, kuma ma ya ce dole sai da shi wannan gyara zai yiwu.

An kashe sojojin Isra’ila a West Bank


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

Al’amarin ya faru ne a yammacin kogin Jordan kusa da garin Jenin

Rundunar sojan Isra’ila ta ce an kashe wasu sojojinta biyu a wani hari na da gan-gan, inda maharin ya kutsa motar da ya ke ciki da karfi.

Al’amarin ya faru ne a yammacin kogin Jordan kusa da garin Jenin.

An tsare direban motar wanda dan asalin Falasdinu ne. A farkon watan nan ne wasu dakarun tsaron iyakar Isra’ila da sojoji biyu su ka raunata a wasu hare-hare guda biyu na kutsen mota a arewacin Isra’ila.

Daruruwan ‘yan Falasdinu ne su ka yi zanga-zanga ranar Juma’a domin cika kwanaki dari tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana birnin kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Afirka ta Kudu: Zuma zai fuskanci shari’a


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Tsohon shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu na fuskantar tuhume-tuhume makonni kadan bayan an tilasta masa sauka daga karagar mulkin kasar.

Tuhume-tuhumen da ake masa sun hada da cewa ya karbi wasu kudaden haram gabanin zamansa shugaban kasa.

Jacob Zuma ya shafe shekaru yana kauce wa tuhumar cin hanci da rashawa, kuma lauyoyinsa sun rika daukaka kararrakin da ak yi a kansa cikin nasara.

Masu sukar lamirin Mista Zuma sun rika zargin masu shigar da kara da cewa suna tsoron sa ne.

Amma a watan jiya sai gashi an tilastawa Mista Zuma sauka daga mukaminsa na shugaban kasa.

Cikin rana guda sai ya koma wanda ba shi da wata gata ta musamman, kuma yanzu yana fuskantar gagarumar matsala.

A halin yanzu, babban jami’i mai shigar da kara, Sean Abrahams ya ture koken Mista Zuma, kuma ya ce tsohon shugaban mai shekara 75 da haihuwa zai fuskanci shari’a akan laifukka 16 da suka jibanci zamba, halasta kudin haram da cin hanci da rashawa.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

Jacob Zuma faces counts of corruption, money laundering, fraud, and racketeering

Ana tuhumarsa da cewa a shekarun 1990 ya nemi wani kamfanin kera makamai na Faransa ya rika daukar nauyin bukatun Mista Zuma.

A wancan lokacin an sami wani mai ba shi shawara da laifin neman wanna cin hancin.

A yanzu dai gwamnatin ce za ta ci gaba da biyan kudaden da Mista Zuma zai bukata a wajen wannan shari’ar, kuma idan aka same shi da laifi, sabon shugaban kasar na iya yafe masa.

Duk da haka, wannan wani babban kalubale ne ga jam’iyyar ANC da take son nuna cewa ta juya wa dukkan batutuwan cin hanchi da rashawa baya gaba daya.

Shin me Buhari ya fada wa shugabannin Majalisa?


Hakkin mallakar hoto
@BashirAhmaad

Image caption

Sen Bukola Saraki ya fadi dalilin da ya sa ba su amince da kasafin kudi ba

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wata ganawa ta musamman da shugabannin majalisun dokoki na kasar.

Ganawar tsakanin bangaren zartawa da majalisa ta samu halartar shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara.

Sai kuma wasu shugabannin majalisa da suka hada da mataimakin kakakin majalisar wakilai Lasun Yusuf da Sen Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila.

Babu dai cikakken bayani game da hakikanin abubuwan da aka tattauna yayin ganawar da aka yi a daren Alhamis.

Amma bayan kammala ganawar, shugaban majalisar dattawa Sen Bukola Saraki ya yi magana da ‘yan jarida a madadin majalisa.

Sakataren gwamnati kuma Boss Mustapha ya yi magana a madadin bangaren zartawa.

Sun shaida wa manema labarai cewa batutuwan da aka tattauna sun hada da kasafin kudi da gyaran fuska ga dokokin zabe na kasa, da samar da ayyukan yi.

An yi ganawar ne a daidai lokacin da ake kai ruwa rana tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.

A kwanan nan ne shugaba Buhari ya yi watsi da kudirin gyara dokar zabe, duk da kudirin ya samu amincewar zauren majalisun Tarayya guda biyu.

‘Yan majalisar kuma sun ce za su yi gaban kansu su amince da dokar duk da shugaban bai amince ba.

Sannan akwai batun kasafin kudi da majalisa ba ta amince da da shi.

Hakkin mallakar hoto
@BashirAhmaad

Amma a yayin da yake zantawa da manema labarai, Bukola Saraki ya ce dalilin da ya sa ba su amince da kasafin kudin ba saboda wasu daga cikin hukumomin gwamnati ba su je sun kare kasafinsu ba.

Tun bayan gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa, shugaba Buhari ya bayar da umurni ga kowace ma’aikata ko hukumar gwamnati ta je gaban majalisa ta kare kasafin kudinta.

Da aka tambayi Bukuloa saraki ko sun tattauna kan batun sauya dokar zabe, sai ya ce ba su tattauna kan batun ba.

Amma wasu majiyoyi sun ce batun yana daga cikin abubuwan da aka tattauna a ganawar da shugabannin majalisar suka yi da Buhari.

Kudirin wanda majalisun biyu suka amince ya shafi sauya dokokin zaben Najeriya, ciki har da fara gudanar da zaben ‘yan Majalisar Tarayya kafin na shugaban kasa.

Amma cikin wasikar watsi da kudirin da shugaba Buhari ya aika wa majalisar, ya ce kudirin ya saba wa ‘yancin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke da alhakin shiryawa da gudanar da zaben, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

An kaddamar da ATM na sayen magani a Afrika ta kudu


Hakkin mallakar hoto
Reuters

An kaddamar da wata na’ura mai kama da ta diban kudi a banki ta ATM, wadda ita kuma ke bayar da kwayoyin magani.

Na’urar wadda jama’a suka yi mata lakabi da ATM Pharmacy, tana bai wa mutanen da likita ya rubutawa magani daga asibiti.

Sannan na’urar an samar da ita ne domin cututtuka masu tsanani kamar, tarin fuka da da ciwon suga da cuta mai karya garkuwar jiki, AIDS ko SIDA.

Na’urar ita ce irinta ta farko a Afirka, da aka fara kafa wa a garin Alexandra da ke Johannesburg.

Kuma tun kaddamar da na’urar ake samun cunkoso a asibitoci.

Na’urar tana fitar da magunguna ne maimakon kudi, sannan akwai tarho a jikinta.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mai bukatar magani zai yi magana da jami’in bayar magani ta tarho.

Mutane za su iya kiran kwararrun masu bayar da magani domin neman shawara.

Marassa lafiya a wasu asibitocin a Afirka ta Kudu su kan bi layi su jira sama da sa’a 12 domin karbar magani.

Amma idan layi ya kai ga mutum, cikin minti uku na’urar za ta ba shi maganin da ya bukata.

An shafe lokaci mai tsawo ana gwada na’urar kafin soma amfani da ita.

Wannan dai wani sabon ci gaban fasaha ne aka samu a fannin kiwon lafiya a duniya.

Liverpool za ta hadu Manchester City a gasar zakarun Turai


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Manchester City have won one of the past seven Premier League games against Liverpool

Manchester City zata hadu da Liverpool a zagayen daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai.

Liverpool ce dai ta doke Manchester City a premier a kakar bana a haduwar da suka yi a 14 ga Janairu, amma a watan satumba City ta lallasa Liverpool 5-0.

Liverpool ce za ta fara karbar bakuncin City a Anfield a ranar 4 ga Afrilu, kafin su sake haduwa a ranar 10 ga Afrilu a gidan City.

Wannan ne karon farko da kungiyoyin Ingila za su hadu a zagayen daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai tun haduwar Chelsea da Manchester United a kakar 2010-11.

Hada kungiyoyin biyu dai ya nuna cewa dole a samu kungiya daya daga Ingila a zagayen daf da na karshe.

Barcelona da ke jagorancin teburin La Liga an hada ta ne da Roma.

Sevilla kuma da ta fitar da Manchester United za ta hadu ne da Bayern Munich.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Jurgen Klopp ya doke Pep Guardiola a haduwa biyar da suka yi

Sauran kungiyoyin da aka hada.

Barcelona da Roma

Sevilla da Bayern Munich

Juventus da Real Madrid

Liverpool da Manchester City

Europa League: An hada Arsenal da CSKA Moscow


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal na son lashe kofin Europa domin shiga gasar zakarun Turai

Arsenal za ta hadu da CSKA Moscow ta Rasha a gasar zakarun Turai ta Europa League zagayen daf da na kusa da karshe

Arsenal ce za ta fara karbar bakuncin fafatawar a Emirates a ranar 5 ga Afrilu, kafin mako na gaba ta kai wa CSKA ziyara a Moscow.

Atletico Madrid ta biyu a teburin La liga za ta hadu ne da Sporting Lisbon ta Portugal.

RB Leipzig ta Jamus za ta hadu ne da Marseille, yayin da kuma aka hada Lazio ta Italiya da Salzburg ta Austria.

Arsenal dai ta tsallake ne bayan ta casa AC Milan da jimillar kwallaye 5-1 a fafatawar da suka yi gida da waje.

Wannan ne kuma karon farko da Arsenal ta kai zagayen daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai tun 2010.

Yanzu kuma babban kalubalen Arsenal shi ne lashe kofin gasar domin samun gurbi a gasar zakarun Turai a kaka ta gaba.

Maki 12 ne tsakanin Arsenal da matsayi na hudu a teburin Premier.

Sauran kungiyoyin da aka hada:

RB Leipzig da Marseille

Arsenal da CSKA Moscow

Atletico Madrid da Sporting Lisbon

Lazio da Red Bull Salzburg

Nigeria: Mutum miliyan 3.8 ba sa samun abinci – FAO


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rahoton ya nuna cewa ‘fiye da mutum miliyan 10 suna neman abin da za su ci, sannan fiye da miliyan 3.8 su na bukatar abinci da gaggawa

Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya tare da Shirin Samar da Abinci na Duniya WFP sun yi gargadi cewa karancin abinci zai shafi mutane miliyan 3.8 a jihohi 16 a arewacin Najeriya da Abuja, babban birnin kasar.

Sun bayyana hakan ne a lokacin da suka gabatar da sakamakon bincikensu na watan Maris din kan yanayin rashin abinci da ake ciki a kasar.

Jihohi 16 din sun hada da Bauchi da Benue da Gombe da Jigawa da Plateau da Niger da Kebbi da Katsina da Kaduna da Taraba da Sokoto da Kano da Yobe da Borno da kuma Adamawa.

Rahoton mai taken CH ya nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu a jihohi 16 da Abujan, fiye da mutum milayan 3.8 ba za su samu abinci ba kwata-kwata a tsakanin watannin Yuni da Agusta, saboda lokacin damuna ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rahoton ya ce an shiga wannan halin nan ne saboda matsalolin Boko Haram da fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya

Rahoton ya nuna cewa ‘fiye da mutum miliyan 10 suna neman abin da za su ci, sannan fiye da miliyan 3.8 su na bukatar abinci da gaggawa.

Ya kara da cewa wasu mutum fiye da miliyan 5.8 kuwa ba su da abinci kwata-kwata kuma ba su da hanyar samunsa, yayin da gidaje da dama suke da abincin ci na ‘yan watanni kawai, saboda haka suna bukatar taimaikon gaggawa kafin abubuwa su karasa lalacewa.

Rahoton ya kuma nuna ce wa an shiga wannan halin nan ne saboda ba a samu isasshen amfanin gona ba a sama da shekaru uku, sakamakon matsalolin Boko Haram da fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

An samu karuwar shigo da makamai a Najeriya – rahoto


Image caption

A shekarar da ta gabata an kama makamai da dama da aka shigo da su ta jihar Lagos

Wani rahoto na masana’antar kera makamai ta duniya wanda Cibiyar Binciken zaman lafiya ta Stockholm ta yi, ya ce shigo da makamai a kasashen Afirka ya ragu da kashi 22 cikin 100, a tsakanin shekaru hudu da suka gabata.

Amma rahoton ya ce a Najeriya kuwa an samu karin shigar da makamai ne da kashi 42 cikin 100 a wannan tsakanin.

Rahoton ya duba manyan masu shigar da fitar da kayayyaki kasashe a fadin duniya.

Amurka ce kan gaba wajen fitar da makamai wasu kasashen, yayin da Indiya da Saudiyya da Masar ne manyan masu shigar da makaman.

Kasashe uku ne kacal daga Afirka suka bayyana cikin manyan masu shigar da makamai, wadanda suka hada da Aljeriya da Moroko da Masar.

Amma wani abun mamaki shi ne yadda aka gano irin makudan kudaden da Najeriya ke kashewa a sayen makamai.

Daga shekarar 2008 zuwa 2012 da kuma 2013 zuwa 2017 Najeriya ta kara kudaden da take kashewa a sayen makamai da kashi 42 cikin 100.

Sai dai an san cewa rundunar sojin Najeriya na fama da manyan matsaloli uku a kasar da suka hada da yaki da kungiyar Boko Haram a arewaci, da fadan kabilanci tsakanin Makiyaya da Manoma a yankin tsakiyar kasar da kuma masu tayar da kayar baya a yankin da ke da arzikin man fetur a kudancin kasar.

Duk da cewa Najeriya ce kasar da ta fi ko wacce yawan al’umma a Afirka, har yanzu makaman da take saya bai kai na kasar Aljeriya ba da ke nahiyar.

Sauran kasashen da ke sayen makamai da yawa a Afrika sun hada da Sudan da Angola da Kamaru da kuma Habasha.

Faransa ta nemi a kama gimbiyar Saudiyya


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana zargin wannan lamarin ya faru ne a wani masauki a wani yanki a Paris a watan Satumba 2016

Wani alkali a kasar Faransa ya bayar da izinin kama diyar sarkin Saudiyya Gimbiya Hassa bint Salman.

Ana zargin Gimbiya Hassa da umartar wani mai tsaronta ya doki wani ma’aikaci a masaukinta da ke Avenue Foch a birnin Paris.

Kafofin watsa labarai na Faransa sun ce wanda aka azabtar din ya ce ya dauki hoton dakin da ya kamata yi gyara, kuma ana zarginsa a kan yana son ya sayar da hotunan.

Tuni dama an tuhumar mai tsaron nata da laifin wani abu makamancin wannan da ya faru a shekara ta 2016.

Kamfanin dillancin labarai na AFP sun shaida cewa wanda aka azabtar ya ce an naushe shi, an daure shi, kuma an tilasta masa ya sumbaci kafafun gimbiyar, kuma ba a bar shi ya bar masaukinta ba sai bayan sa’o’i.

An ruwaito cewa Gimbiya Hassa, wadda dan uwanta ne Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, ta tsere daga Faransa ba da jimawa ba bayan faruwar lamarin.