An sace matar wakilin VOA da Dansa a Kaduna


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mastalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya

Wasu ‘yan bindiga sun da ba a tantance ba sun sace matar wakilin kafar yada labarai ta VOA da kuma Dansa a Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Maharan kuma sun kashe wani jami’in hukumar kiyaye hadurra ta FRSC da suke makwabtaka da wakilin na VOA Nasir Birnin Yaro.

Birnin Yaro ya tabbatarwa da wakilin BBC Nura Muhammad Ringim da faruwar al’amarin, inda ya ce maharan sun shiga ne a tsakiyar dare.

Ya ce lokacin da suka shiga gidansa da ke Birnin Yaro, ba ya nan amma sun iske iyalinsa suna tambayar matarsa inda yake.

A lokacin ne kuma suka harbe makwabcinsa Sabitu Abdulhamid jami’in hukumar kiyaye hadurra FRSC bayan ya shiga gidan da nufin taimakawa iyalinsa.

Kuma ayan sun kashe shi ne suka tafi da matarsa da dansa.

Birnin Yaro ya ce yana tunanin sun shigo gidansa ne da nufin su yi garkuwa da shi, amma da ba su same shi ba suka tafi da iyalinsa.

Kaduna dai na cikin yankunan arewacin Najeriya da ke fama da matsalar sace-sacen mutane kuma matsala ce da ta ki ci ta ki cinyewa.

Neymar zai yi jinyar akalla mako shida


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Neymar ya ci bal 29 a wasa 30 tun da ya je PSG

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Neymar zai yi jinyar akalla mako shida kuma ba zai yi wasansu na biyu da Real Madrid ba na Zakarun Turai, na ranar Talata in ji mahaifinsa.

Dan wasan na Brazil mai shekara 26, ya ji rauni ne a idon sawunsa a wasan da suka doke Marseille 1-0 na gasar Faransa ta Ligue 1, ranar Lahadi.

A ranar Talata kociyan PSG Unai Emery ya ce Neymar yana da ‘yar karamar dama ta yin wasansu da Real, inda ya musanta rahotannin da ke cewa za a yi wa Neymar tiyata a kan raunin.

Kociyan ya ce ran Neymar ya dugunzuma saboda raunin domin yana son ya yi kowa ne wasa, musamman ma na Real Madrid wanda ya ci masa buri.

To amma a yanzu mahaifin dan wasan a wata hira da jaridar ESPN Brasil ya ce jinyar za ta dauki mako shida zuwa takwas ko da za a yi masa tiyata ko ba za a yi ba.

PSG ta ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 14 kuma a ranar 6 ga watan Mais za ta karbi bakuncin masu rike da kofin Zakarun Turai Real Madrid, wadanda suka ci su 3-1 a wasan farko na zagayen kungiyoyi 16.

An dage dakatarwar Rasha daga wasannin Olympic


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan wasan Rasha 168 ne suka shiga gasar ta huturu ta watan Fabrairu amma ba da sunan kasarsa

Kwamitin wasannin Olympics na duniya ya dawo wa da Rasha matsayinta na mamba a cikinsa bayan dakatar da kasar da aka yi daga wasannin Olympic na huturu da aka kammala a Pyeongchang ta Koriya ta Kudu ranar Lahadi.

Hukumar gasar ta Olympic ta haramta wa Rasha shiga gasar ta watan Fabrairu a kan laifin da aka samu hukumomin kasar da shi na hannu a ba wa ‘yan wasansu abubuwan kara kuzari.

Tun kafin bikin rufe gasar a ranar Lahadi a Koriya ta Kudu, kwamitin na gasar ta Olympic ya ce za a dage dakatarwar, in dai ba a sake samun Rashar da saba ka’idar dokokin amfani da abubuwan kara kuzarin ba.

Dukkanin sauran gwajin da aka yi wa ‘yan wasan Rasha a gasar ta Olympic, ba a same su da laifi ba, in ji kwamitin, wanda daga nan ne aka sanar da dage dakatarwar.

Shugaban kwamitin wasannin Olympic na Rasha Alexander Zhukov ya yi maraba da matakin na hukumar wasan Olympic din, IOC.

Ban zan damu ba sosai don na rasa aikina – Wenger


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Wenger ya damu da yadda ake yawan tambayarsa kan ci gaba da zamansa a Arsenal

Arsene Wenger ya ce tsira da aikinsa na kociyan Arsenal ba wani abu ne da ya dame shi ba sosai, bayan da aka doke su a wasa shida daga cikin 12 a shekarar nan ta 2018.

A ranar Alhamis Gunners din za su kara da ta daya a tebur Manchester City a gasar ta Premier, kwana hudu bayan Cityn ta casa su 3-0 a wasan karshe na cin kofin Carabao a filin Wembley.

Maki 27 ne tsakanin Arsenal din da City a tebur, sannan kuma maki 10 tsakaninta da ta hudu Tottenham, a fafutukar neman gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta kaka ta gaba.

Wenger wanda yake aikin horad da Arsenal tun 1996, ya ce yana mamakin yadda har yanzu ake tambayarsa irin wadannan tambayoyi game da ci gaba da rike aikin nasa.

Kociyan dan Faransa mai shekara 68 ya kulla sabuwar yarjejeniyar shekara biyu a watan mayu na 2017, bayan da ya jagoranci kungiyar ta dauki kofin FA na uku a kaka hudu, ko da yake sun kasa samun gurbin gasar Zakarun Turai a karon farko a shekara 20.

Wenger ya ce babban abin da ya dame shi a yanzu shi ne ya ga ya shirya ‘yan wasansa yadda za su tunkari wasan gobe, amma ba wai damuwa da matsayinsa ba.

Cin kofin Turai na Europa wata hanya ce da Arsenal za ta samu gurbin gasar Zakarun Turai, kuma za ta kara da AC Milan a matakin kungiyoyi 16 da za a tankade rabi zuwa wasan dab da na kusa da karshe.

Man City ba za ta yi sako-sako ba da matashi Phil Fode


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kociyan Man City Pep Guardiola ya ce ‘yan kallon da suka ga wasan Foden na farko a babbar kungiyar sun yi sa’a

Ga alama Manchester City na shirin kulla sabuwar yarjejeniya mai tsawo da matashin dan wasanta Phil Foden, wanda ya samu karbuwa sosai a wurin kociyansu Pep Guardiola, idan ya kai shekara 18 a watan Mayu.

Ba a dai fara magana a kan batun ba, amma bayan da kungiyar ta zuba makudan kudade a bangare matasan ‘yan wasanta, City ta zaku ta rike gwanin matashin dan wasan nata.

A kakar nan Foden ya samu shiga cikin ‘yan wasan da Pep Guardiola yake amfani da su, inda ya yi wasa har sau shida.

Foden wanda mai goyon bayan Manchester City ne tun yana dan karami, shi ne ya zama gwarzon dan wasan gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekara 17 wanda Ingila ta dauka a watan Oktoba, inda ya ci bal biyu a karawar karshe da Spaniya.

A watan Yuli an sa shi cikin tawagar Manchester City da ta je rangadin wasannin shirin tunkarar kakar bana a Amurka.

Nigeria za ta yi karar Jami’ar Alabama ta Amurka


Hakkin mallakar hoto
Alabama State University

Gwamnatin Najeriya za ta kai karar wata Jami’a a Amurka saboda ana zargin su da cinye kudin makarantar dalibai, da kudin masauki, littatafai, da kuma abincinsu.

Gwamnatin da hadin gwiwar wadansu daliban Najeriya da dama sun yi karar Jami’ar Jihar Alabama tun a shekarar 2016.

Kuma ana zargin jami’ar wadda take daukar dalibai bakaken fata, da amsar kudin masauki wanda ba su yi amfani da su ba, da cajansu kudin darasin da ba su dauka ba.

Jami’ar ta musanta cewa ta aikata ba daidai ba, kuma sun shaida wa kafofin yada labarai cewa, ba su saba kowace irin ka’ida da gwamnatin Najeriya ta gindaya musu ba a yarjejeniyar.

Ta bayyana cewa suna bin gwamnatin Najeriya $202,000 bayan da aka biya komai da komai, amma sun ce kuma an biya kudin.

Amma Anthony Ifediba wadda take wakiltar daliban ta ce jami’ar ta rike dala 800,00.

Ya shaida wa kamfanin Montgomery Advertiser cewa gwamnatin Najeriya ta biya jihar Alabama kimanin dala miliyan biyar, don biyan kudin makarantar dalibai da kudin kashewarsu.

Karanta wadansu karin labarai

BBC Media Action ta kori ma’aikata saboda kallon batsa


Bangaren tattalafawa kafafen watsa labarai na duniya na BBC, wato BBC Media Action ya ce ya kori ma’aikatansa shida saboda samunsu da laifin kallon fina-finan batsa a kwamfutocin wurin aikinsu.

Ya ce lamarin ya faru ne a ofisoshinsa da ke kasashen waje a cikin shekara goma da suka wuce kuma dukkan mutanen da aka kora ‘yan kasashen waje ne.

BBC Media Action ya samu tallafi na kimanin fam miliyan 70 daga hukumar ci gaban kasashe ta Burtaniya cikin shekara biyar da suka wuce.

Ya ce ba shi da wata shaida da ke nuna cewa ma’aikatan sun ci zarafin wani ko wata.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da aka kara sanya ido sosai kan BBC Media Action, bayan zargin lalata da aka yi wa ma’aikatan kungiyar ba da agaji ta Oxfam a Haiti.

Hukumar ci gaban kasashe ta Burtaniya ta bukaci dukkan kungiyoyin bayar da tallafin kasar da ke aiki a kasashen waje su bayar da tabbacin cewa za su kare mutunci da ka’idojin aiki.

BBC Media Action ya ce ya bayar da wannan tabbacin.

“Mun yi nazari kan abubuwan da suka faru a shekara 10 game da cin zarafi. An gano cewa ma’aikata shida sun kalli batsa kuma an gudanar da bincike,” in ji sanarwar da BBC Media Action ya fitar.

Ya kara da cewa zai ci gaba da kare dokokin da suka shafi ayyukan da yake yi.

An rufe coci 714 saboda karya doka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Majami’un ba su sabunta lasisinsu ba

Hukumomi a Rwanda sun rufe coci sama da 700 a Kigali, babban birnin kasar saboda sun karya dokokin tsaro da kiwon lafiya, in ji jaridar The New Times mai zaman kanta.

Sun ce an soma rufe majami’un ne a makon jiya kuma zuwa yanzu an rufe coci 714 da masallaci daya.

Wani jami’i, Justus Kangwagye, ya shaida wa jaridar cewa wuraren ibadar sun keta dokokin tsaro.

“Ya kamata a rika yin ibada a cikin yanayi mai aminci da tsaro. Bai kamata mutum ya karya doka ba a yayin da yake son gudanar da ibada. An ba su umarni su daina gina wuraren ibadar har sai sun cika sharudan tsaro,” in ji shi.

Ya kara da cewa wasu majami’un ba su sabunta lasisinsu ba don haka hukuma ba za ta bari su ci gaba da gudanar da ibada a wuraren ba.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin cocin suna yin ibadarsu ne a cikin tantuna kuma ba su da wuraren ajiye ababen hawa, inda masu ibada ke ajiye ababen hawarsu a kan titi abin da ke jawo cunkuso a hanya.

Rahotannin sun kara da cewa mazauna birnin Kigali sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan wannan mataki. Wasu sun goyi bayan matakin yayin da wasu suka ce bai dace ba.

Shugaban kungiyar majami’u na lardin Nyarugenge, Bishop Innocent Nzeyimana, ya roki gwamnati ta dakatar da matakin da ta dauka zuwa lokacin da cocin za su gyara matsalar.

An zargi Koriya Ta Arewa da bai wa Syria makamai masu guba


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana samun rahotannin cewa ana kai harin makamai masu guba gabashin yankin Ghouta

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana, ya nuna cewa Koriya ta Arewa na aikawa Syria wasu abubuwa da a ke amfani wajen sarrafa makaman nukiliya ta jiragen ruwa.

Rahoton da masana a MDD su ka rubuta, wanda kuma jaridu da dama su ka gani, ya ce abubuwan da a ke aikawa sun hada da tayil-tayil da wanda asid ba ya iya bata su da na’urorin auna yanayi wato thermometer.

Haka kuma, rahoton ya ce an sha ganin wasu ma’aikatan Koriya Ta Arewa su na aiki a wuraren sarrafa makamai a cikin Syria.

Gwamnatin Syria dai ta yadda a rushe ma’adanar kemical din ta bayan wani harin gas din Sarin da ya kashe daruruwan mutane a Ghout a shekarar 2013, amma ko bayan nan an tuhume ta da kai hare-haren kemikal.

Rahoton ya ce a baya an shigar da irin wadannan kaya sau 40 tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2017.

Wannan zargi dai ya biyo bayan sabon rahoton da aka samu cewa dakarun Syria su na amfani da makamai masu guba, amma gwamnatin kasar ta yi watsi da wannan zargi.

Sai dai an yi ta jin karar hare-haren sama a yankin Gabashin ghouta da ke wajen birnin Damascus bayan da aka shiga kwana biyu na dakatar da fadan da ake yi don a samu damar shigar da kayan agaji.

Masu fafutuka dai suna zargin hare-haren kasa da na sama da gwamnati ke kai wa ya hana a shigar da kayan agaji ga fararen hula, yayin da Rasha kuma ke zargin ‘yan tawaye.

Wadannan zarge-zarge ake yi wa Koriya Ta Arewa?

Kasashen duniya dai sun kakabawa Koriya Ta Arewa takunkumai kan shirin makami mai linzaminta.

Me zai faru idan aka fara yaki da Koriya ta Arewa?

Amma wani rahoton sirri da wata tawagar kwararru na Amurka ta hada, wanda ya yi duba kan yadda Koriya Ta Arewa ke yn biyayya ga dokokin MDD, ya gano cewa ta karya dokoki wajen aikewa da kayayyakin Syria.

Rahoton wanda BBC ta gani ya ce kayayyakin sun hada da tayil-tayil da wanda asid ba ya iya bata su da na’urorin auna yanayi wato thermometer.

An yi zargin cewa wata cibiyar kimiyya ta gwamnatin Syria SSRC ce ta biya Koriya Ta Arewa kudaden kayan ta hannun wasu kamfanoni.

Gwamnatin Syria na tallafawa cibiyar SSRC a matsayin cibiyar bincike ta farar hula, amma Amurka ta zargi cibiyar da mayar da hankali kan hada makamai masu guba.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli rawar sojojin Korea ta Arewa

Masoyan Sridevi sun yi wa gidanta tsinke


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Sridevi was an icon in Bollywood cinema

Dubban masoyan tauraruwar Bollywood sun taru a birnin Mumbai da ke Indiya don su yi jana’izar Sridevi Kapoor, wadda ta mutu a Dubai ranar Asabar.

Masoyan nata sun yi layi a wani wuri da ake kira Celebrations Sports Club kafin jana’izar ranar Laraba, kuma suna rike da furanni da hotuna.

A daren Talata ne aka kai gawarta Indiya.

‘Yan sanda sun ce ‘yar wasan kwaikwayon, mai shekara 54, ta rasu ne sakamakon nitsewa a wurin wanka bayan ta fita daga hayyacinta.

An gano gawarta a cikin kwamin wanka a otal din da ta sauka a Dubai.

Tunda farko an ba da rahoton cewa bugun zuciya ne ya kashe shi a lokacin da suka je bikin ‘yan uwanta a Dubai.

Ta soma fitowa a fina-finan Bollywood tana da shekara hudu kuma ta yi fina-finai sama da 300

Image caption

Mutane dayawa sun taru don su yi jana’izar ta

Actresses Aishwarya Rai and Kajol, were among the mourners at the club in the Andheri West area of Mumbai, home to Bollywood.

‘Yan wasan kwaikwayo Aishwarya Rai da Kajol na cikin mutanen da suka halarci makokinta a wani wurin rawa da ke Andheri West a Mumbai, inda ake kira gidan Bollywood.

Wata masoyiyar jarumar mai suna Nandini Rao ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “abin mamaki ne cewa Sridevi ta rasu, muna so mu yi mata kallon karshe a yau.”

An girke ‘yan sanda da dama a gidan tauraruwar, da kuma kan hanya da wajen Vile Parle Seva inda za a kona gawarta.

Ana sa rai dubban masoyanta za su halarci jana’izar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutuwar Sridevi ta girgiza mutanen Indiya

Hakkin mallakar hoto
AFP

Zakanya ta kashe wata mata South Africa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Babu cikakken bayani kan abin da ya sa zakanyar ta kai wa matar hari

Zakanya ta kashe wata mata a gidan kula da namun dajin birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.

Kakakin hukumar Netcare 911, wadda ke bayar da agajin gaggawa Nick Dollman, ya ce hukumarsa ta yi gaggawar kai dauki bayan da aka kira ta gidan namun dajin da ke garin Hammanskraal.

“Abin takaicin shi ne, matar ta samu munanan raunuka kuma nan take ta mutu,” in ji Mr Dollman.

Babu cikakken bayani kan abin da ya sa zakanyar ta kai wa matar hari.

Mr Dollman ya ce mutanen da suka je gidan kula da namun dajin ne suka kai wa matar, mai shekara 22, dauki ta hanyar daddanna kirjinta domin numfashinta ya dawo.

An ragewa Kushner ikon sanin bayanan sirri


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mr Kushner ba zai rika samun rahotannin sirrin ba daga yanzu

An ragewa sirikin Shugaba Donald Trump kuma babban mai bashi shawara Jared Kushner karfin ikon sanin bayanan sirri a fadar White House.

Wannan na nufin cewa zai rasa damar sanin wasu abubuwa masu muhimmanci ciki har da rahotannin leken asirin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa ana yi wa Jared Kushner lakabi da sakataren komai. Sirikinsa, Shugaba Trump ya sa shi a harkokin wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, ya hada kai da Mexico sannan ya jagoranci tattaunawa da China. Sai dai a yanzu dole ya yi wadannan ayyukan ba tare da sanin bayanan sirrin kasar ba.

Lauyansa ya ce Mr Kushner ya yi duk abunda ya kamata domin samun cikakken ikon sanin bayanan asiri, kuma ya ce wannan sauyi ba zai shafi ayyukansa masu muhimmanci ba.

An sake bude cocin Holy Sepulchre a Jerusalem


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

An sake bude cocin Holy Sepulchre a Jerusalem

Shugabannin coci a birnin Kudus sun sake bude cocin Holy Sepulchre a yau Laraba.

Wannan na zuwa ne bayan hukumomin Isra’ila sun dakatar da wani sabon tsarin haraji.

Shugabannin mabiya darikar Roman Catolika da na Greek Orthodox da kuma na cocin Armenia sun soki tsarin ta hanyar rufe wani coci a wajen da kiristoci da dama su ka yadda cewa a nan a ka gicciye Annabi Isa, a nan a ka rufe shi kuma a nan a ka tayar da shi.

Magajin garin Birnin Kudus Nir Barkat ya dakatar da sabon shirin harajin, kuma Piraim minista Benjamin Netanyahu ya kaddamar da wata tawaga domin warware matsalar.

Dapchi: Gwamnatin Nigeria zata kaddamar da kwamitin bincike


Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

Kwamitin zai duba yadda jami’an tsaro ke ayyukansu a Dapchi da kuma makarantar kafin sace daliban

Gwamnatin Nigeria za ta kaddamar da kwamiti domin gudanar da bincike kan yadda aka sace ‘yan matan sakandaren Dapchi 110 da ke jihar Yobe a arewacin kasar makon da ya gabata.

Kwamitin mai mabobin 12 ya kunshi sojojin kasa da na ruwa da na sama da kuma ‘yan sanda da hukumar tsaro ta SSS da ta Civil defence.

Daga cikin ayyukan kwamitin da za’a kaddamar ranar laraba sun kunshi binciken dalilan da ke tattare da sace wadanan ‘yan mata.

Haka kuma kwamitin zai duba yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu a Dapchi da kuma makarantar kafin sace daliban.

Har ila yau, ana saran kwamitin zai gabatar da shawarwari da za’ayi amfani da su wajen gano inda aka kai ‘yan matan da kuma yadda za’a ceto su.

Rahotanni sun ce an bai wa kwamitin zuwa ranar 15 ga watan Maris na 2018 ya gabatar da bayanan da ya tattara.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da sojoji da ‘yan sanda ke musayar yawu kan rundunar da ke da alhakin ba garin na Dapchi tsaro lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari.

Sirrin namun dajin da ke dazukan Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Chester Zoo

Image caption

Gwaggon Biri a gandun dajin Gashaka Gumti

An dauki hoton wani gwoggon biri a kamara wanda irinsa ba su da yawa a duniya, a wani babban gandun daji a Najeriya.

An ga gwoggon birin ne wanda aka fi samu a Najeriya da Kamaru a wurare daban-daban a gandun daji na Gashaka Gumti, kuma ana fatan zai ci gaba da rayuwa.

A karon farko masu kare dabbobi sun ce sun ga wani nau’in dabba jikinsa kamar kunkuru amma mai tsinin baki da ake kira Pangolin a Ingilishi a gandun dajin na Najeriya.

Ana dai danganta gandun dajin a matsayin arzikin kasa, amma namun dajin da ke cikinsa na fuskantar barazana daga mafarauta.

Masu bincike daga gandun dajin Chester, da ke aiki tare da Ofishin kula da gandayen daji a Najeriya, sun yi nazari kan girman gandun namun dajin a Najeriya.

Gandun dajin da aka sani a daji cikin tsaunuka cike da ciyayi na daga cikin gandayen dajin mafi hatsari a yammacin Afirka.

Kamarori sun dauki hotunan dabbobi da ba a taba gani ba a gandun dajin da ma yankin gaba daya, kamar su gwoggon biri da ba kasafai aka cika ganinsu ba.

Hakkin mallakar hoto
Chester Zoo

Image caption

Gandun dajin Gashaka Gumti na cikin gadayen dajin da aka yi watsi da su a Najeriya

Gwaggon Biri na fuskantar barazanar karewa a yankunan Kamaru da Najeriya. Adadin yawansu ya ragu zuwa kasa da 9,000, inda kimanin 1000 ake tunanin suna raye a iyakokin gandun namun dajin.

Gwaggon biri na fuskantar barazana da yawa, da suka hada da farautarsa a matsayin nama da kuma domin magani.

Yanzu masana kare namun daji suna gudanar da bincike a wasu sabbin wurare a gandun domin tantance adadin yawan namun dajin saboda babu wani bincike da aka yi game da yawan dabbobin a tsawon shekara 20.

Hakkin mallakar hoto
Chester Zoo

Image caption

An ga Pangolin mai tsinin baki a gandun dajin Gashaka Gumti

Kamarori sun dauki hotuna fiye da 50,000 na namun dawar a tsakanin shekara 2015 zuwa karshen 2017.

“Abu ne mai kyau da aka dasa kamarori domin daukar hotuna a gandun dajin wanda aka manta da shi a Najeriya, amma kuma yake dauke da wasu halittu masu muhimmaci a Najeriya da ma Afirka baki daya,” a cewar Stuart Nixon.

Masu binciken sun yi mamakin yadda aka samu dabbar Pangolin, wadda yana da wahala a samu nau’in dabbar.

“Babu wanda ya taba ganin babbar Pangolin, babu kuma wanda ya san inda suke,” in ji Stuart Nixon. Wannan ne karon farko da aka ga dabbar a Najeriya.

Wannan ya nuna yadda ba kasafai ake samunsu ba da kuma yadda ake shan wahala wajen nemansu da nazari akansu.”

Kamarorin da aka dasa sun samo hoton asali na farko kan Damisa, wanda zai iya kasancewa daya daga cikin mafi muhimmaci ga adadin yawansu a yammacin Afirka.

Hakkin mallakar hoto
Chester Zoo

Image caption

Akwai Damisa a Gashaka Gumti

Hakkin mallakar hoto
Chester Zoo

Image caption

Magen Daji

Sannan an ga Magen daji a cikin hotunan.

“Kamar wannan alama ce da ke nuna tana cikin yawan adadinsu da suka rage a Najeriya,” a cewar Stuart Nixon. “Tana da wahalar kamawa, kuma ba a santa ba sosai, kuma babu wani nazari mai zurfi da aka yi game da su.”

Gidan Zoo na Chester ya dade yana taimakawa gandun dajin Gashaka Gumti sama da shekaru 20, musamman kokarin baya-bayan nan da suke yi wajen magance barazanar da gandayen daji ke fuskanta.

Ana kare rayukan gandayen dajin amma kuma dabbobin na fuskantar barazana daga mafarauta. Gidan Zoo na Chester ne ke bayar da tallafi ga masu kare gandayen daji da kuma samar da horo na kare gandayen dajin.

Babban Jami’in kula da gandayen daji a Najeriya Yohanna Saidu ya ce yana da wahala a samu wasu gandayen daji da za su fi Gashaka Gumti musamman tsari da kyau.

‘Neymar na cike da burin wasan PSG da Real Madrid’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ciwon da Neymar ya ji a idon sawu, bai yi tsananin da za a yi masa tiyata ba in ji kociyansu Unai Emery

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Neymar yana da ‘yar karamar dama ne ta yin wasan karo na biyu na Zakarun Turai da Real Madrid ranar Talata mai zuwa.

Dan wasan na Brazil mai shekara 26 yana murmurewa ne daga raunin da ya ji a idon sawu a lokacin wasan da suka doke Marseille 1-0 ranar Lahadi.

Kociyan kungiyar ta PSG Unai Emery ya musanta rahotannin da ke cewa dan wasan mafi tsada a duniya yana bukatar a yi masa tiyata ne a kafar kan raunin da ya ji.

Kociyan ya ce Neymar yana son taka leda a kowa ne wasa kuma ya ci buri a kan wasan da za su sake da Real Madrid na kofin na Zakarun Turai, zagayen kungiyoyi 16.

To amma Emery ya ce abin takaicin shi ne dan wasan ba lalle ba ne ya samu yin wannan wasa saboda ‘yar damar da yake da ita ba ta da yawa saboda raunin.

Dan wasan na gaba ya koma PSG ne a kan kudin da ba a taba sayen wani dan wasa ba, fam miliyan 200 daga Barcelona, a watan Agusta, kuma ya ci bal 29 a wasa 30.

PSG tana saman teburin gasar Faransa da tazarar maki 14 tsakaninta da mai bi mata baya Monaco, kuma a ranar 6 ga watan Maris za ta karbi bakuncin Real Madrid, wadda ta ci su 3-1 a wasan farko a Santiago Bernabéu.

Espanyo ta doke Real Madrid 1-0


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Rabon da a doke Real Madrid a La Liga tun wasa bakwai baya

Gerard Moreno ya daga raga ana dab da tashi a wasan da Espanyol ta doke Real Madrid a karon farko a sama da shekara goma.

Real ta ci wasa biyar a jere, amma a wannan karon sai ta ajiye Cristiano Ronaldo, kuma ta dandana kudarta a sanadiyyar rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a wasan.

Dan bayan Real Sergio Ramos ya tafi neman ci a kusan karshen wasan, abin da ya bude kofa ga Espanyol, Sergio Garcia ya aika wa Moreno bal din da ya ci bakin nasu.

Zakarun na La Liga Madrid sun ci gaba da zama da tazarar maki 14 tsakaninsu da Barcelona, wadda za ta ziyarci Las Palmas a ranar Alhamis.

A haduwarsu 22 da Real Madrid Espanyol ta kasa doke zakarun inda ta yi canjaras da su sau uku tun daga watan Oktoba na 2007.

Espanyol din a yanzu ta zama ta 13 a tebur bayan wasan na mako na 26, da maki 31.

A wasannin da za a ci gaba na gasar ta La Liga na mako na 26 a ranar Laraba;

Getafe da Deportivo La Coruna

Athletic Club da Valencia

Málaga da Sevilla

Atlético Madrid da Leganés

Eibar da Villarreal

‘Anya damben boksin yana da amfani?’


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Scott Westgarth ya mutu ne a asibiti ranar Asabar bayan damben da ya yi nasara

Tsohon dan wasan kwallon kafa a Ingila kuma dan damben boksin a yanzu Curtis Woodhouse ya nuna tababarsa a kan amfanin damben bayan da Scott Westgarth ya mutu bayan damben da ya yi nasara.

Curtis Woodhouse ya ce mutuwar Scott Westgarth, ta sa shi yana tunani a kan cancantar wannan wasa na boksin, amma kuma ya ce ba zai taba shawartar wani ya daina damben ba.

Westgarth ya mutu ne a asibiti yana da shekara 31, bayan da ya kamu da rashin lafiya bayan damben da ya yi nasara a kan dan uwansa dan Ingila Dec Spelman a Doncaster ranar Asabar.

Woodhouse, mai shekara 37 wanda tsohon dan wasan kwallon kafa ne na tsakiya a kungiyar Sheffield United da Birmingham City wanda ya yi nasara a dambe 24 da ya yi daga cikin 31, ya ce boksin wasa ne mai ban mamaki matuka.

Tsohon zakaran damben na ajin manyan masu karamin nauyi na Birtaniya a da zai kara ne da John Wayne Hibbert a damben kambin matsakaita nauyi na Commonwealth a Doncaster, sai kuma aka fasa saboda mutuwar Westgarth .

Anya Harry Kane na son daukar kofi?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Harry Kane ya ci bal ta 150 a karshen makon da ya wuce

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya kafe cewa gwarzon dan wasansa na gaba Harry Kane yana jin dadin zama kuma zai iya daukar kofi a kungiyar.

Tsohon kociyan kungiyar Andre Villas-Boas, wanda aka kora a watan Disamba na 2013, ya ce dan wasan wanda yake kan gaba wajen cin bal a gasar Premier dole ne ya bar kungiyar in dai yana son ya dauki kofi.

To amma a martanin da ya mayar kan maganar kociyan kungiyar Pochettino ya ce dan wasan mai shekara 24, wanda ya ci bal 24 a Premier a shekarar nan yana jin dadin zamansa a kungiyar kuma ba shakka yana son daukar kofuna a kungiyar kamar kowa.

Ya ce suna kulob din ne domin su taimaka masa ya bunkasa har ya kai ga cimma buri ya dauki kofuna.

Kane, wanda a bara ya kawar da tarihin da Alan Shearer ya kafa na shekara 22, na dan wasan da ya fi cin kwallo a cikin shekara daya a Premier, yana kan hanyar kara cin kyautar dan bal din da ya fi ci kwallo ”Golden Boot” a karo na uku a jere, kuma a yanzu yana gaban Mo Salah na Liverpool da bal daya.

Jumulla a kakar nan Kane ya ci bal 35 kuma ya kama hanyar cimma tarihin da Clive Allen ya kafa a Tottenham wanda ya ci kwallo 49 a kaka daya ta 1986-87.

Jami’in kwastam ya harbe wani a Jigawa


Hakkin mallakar hoto
Custom

Image caption

Shugaban hukumar kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tace tana tsare da wani jami’in hukumar kwastam wanda ake zargi ya harbe wani mutum a garin Babura da ke cikin jihar Jigawa a arewacin Najeriya.

Wani mazaunin Babura ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru ne lokacin da mutumin mai suna Alhaji Ummaru da aka harba ke kokarin shiga tsakani, bayan jami’an kwastam sun biyo wani direba, kuma suka cim masa a cikin garin na Babura.

Ya ce sakamakon harbin ne ya sa ‘yan uwan mutumin suka yi gayya suka dauke shi kuma kafin su tafi asibiti Allah ya ma shi cikawa.

“Rasuwarsa ce ta hasala mutane suka shiga kona cibiyoyin hukumar kwastam da motocinsu a yankin,” a cewarsa.

Sannan ya ce yamutsin ya janyo kona rumfunan kasuwanci da ke kusa da cibiyoyin na kwastom a Babura.

Rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa dai ta tabbatar da faruwar al’amarin, kuma kakakinta SP Abdu Jinjiri ya ce suna tsare da jami’in hukumar kwastam wanda ya yi harbin.

Ya kuma ce tuni aka aike da jami’an tsaro domin kwantar da tanzomar.

Tsohon dan tseren duniya Bolt zai taka leda a Old Trafford


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Usain Bolt mai goyon bayan Manchester United ne

Tsohon zakaran tseren duniya Usain Bolt wanda ya yi ritaya zai yi wasan kwallon kafa a filin kungiyar da yake kauna Manchester United, Old Trafford.

Bolta wanda sau takwas yana cin lambar zinare a gasar Olympic zai jagoranci wasu fitattu ne ire-irensa da kuma ‘yan kwallon kafa a matsayin kyaftin dinsu, a wasan neman tallafi na Asusun yara na majalisar din kin duniya, Unicef, da ake yi, Soccer Aid, ranar 10 ga watan Yuni.

Dan tseren na Jamaica, ya ce tun ainahi burinsa shi ne ya zama kwararren dan kwallon kafa. Saboda haka wannan dama ta yin wasa tare da wasu daga cikin tsoffin fitattun ‘yan wasan ba karamin abu ba ne.

Mawaki kuma dan fim Robbie Williams shi ne zai zama kyaftin din daya tawagar, Ingila a wasan kwallon na Unicef.

Hakkin mallakar hoto
UNICEF/COOPER

Image caption

Burin Usain Bolt ya zama kwararren dan kwallon kafa bayan ya yi ritaya a wasan tsere

Daman Usain Bolt ya taba yin maganar cewa yana son ya shiga wasan kwallon kafa na kwararru bayan ya yi ritaya daga tsere a shekarar da ta wuce.

Wasan tamolar na neman tallafi wanda za a yi a Old Trafford zai hada shahararru da tsoffin gwanayen ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, inda za su taka leda tare.

Ana wasan ne duk bayan shekara biyu, kuma tun bayan da aka fara shi a shekara ta 2006, an tara fam miliyan 24.

‘Antonio Conte ne ya fi dacewa da kociyan Italiya’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Antonio Conte ya yi kociyan Italiya daga 2014 zuwa 2016

Kociyan Chelsea Antonio Conte shi ne ya fi dacewa da zama kociyan tawagar ‘yan wasan Italiya na gaba in ji mataimakin kwamishina a hukumar kwallon kafa na kasar, Alessandro Costacurta.

Conte ya horad da tawagar ta Italiya wadda ake wa lakabi da Azzurri daga shekara ta 2014-2016 kafin ya tafi Chelsea, inda ya ci kofin Premier a shekararsa ta farko.

Babban jami’in ya ce kawo yanzu bai zabi wanda za a ba aikin ba, amma yana ganin Conte shi ne wanda zai fi dacewa, kamar yadda ya bayyana a jaridar labaran wasanni ta Italiya, Gazzetta dello Sport.

Jaridar ta ce jami’in yana kuma duba yuwuwar daukar tsohon kociyan Manchester City Roberto Mancini da tsohon kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti da kuma tsohon kociyan Leicester Claudio Ranieri.

Costacurta ya ce lalle kam ba shakka zai yi magana da Conte nan da ‘yan watanni, inda zai yi masa tayin aikin.

Yanzu Conte, mai shekara 48, yana da ragowar wata 18 a kwantiraginsa da Stamford Bridge (Chelsea).

Italiya dai ta kori kociyanta Giampiero Ventura a watan Nuwamba, bayan da ya kasa sama wa kasar gurbin gasar cin kofin duniya da za a yi a wannan shekara ta 2018 a Rasha.

Amma kuma tsohon dan wasan na AC Milan ya ce tuni Conte ya nuna ya san yadda zai rike kungiya ta kasa, yayin da sauran ba su nuna ba.

Yadda mata ke yi wa jarirai bilicin tun suna ciki a Ghana


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mata ma su juna biyu na shan kwayar Glutathione don yi wa jarirai bilicin

An gargadi mata a Ghana game da shan wasu kwayoyin bilicin a yayin da suke dauke da juna biyu da nufin sauya fatar jariran da ke cikinsu.

Masana kiwon lafiya sun ce kwayoyin da matan ke sha za su iya haifar da illa a wajen haihuwa da yin lahani ga koda da kuma lalata gabban jikinsu.

Hukumar FDA da ke kula da ingancin abinci da magani ta ce shan kwayar Glutathione ga mata masu juna biyu abu ne mai matukar hatsari.

Hukumar ta gargadi jama’a cewa babu wani magani da ta amince da shi domin bilicin jaririan da ba a haifa ba.

Tabi’ar na ci gaba da girma a Ghana, a cewar hukumar, kuma mutane na shigo da kwayoyin ne da dama ta hanyar boye su cikin jikar kayansu a tasoshin jiragen sama.

Ko da yake babu wasu bayanai da aka tattara game da girman matsalar, amma hukumar ta ce binciken da ta gudanar ya taimaka wajen bayyana halin da matan ke ciki.

Yanzu haka jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin cafke kamfanoni da mutanen da ke hakarar shigo da kwayoyin.

A watan da ya gabata ne Hukumar shige da fice ta soke cancantar matan da fatar jikinsu ta nuna suna bilicin daga cikin sabbin ma’aikatan da za ta dauka aiki.

Hukumar ta dauki matakin ne saboda dalilai na tabbatar da lafiyar jami’anta.

Nigeria: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

PDP ta ce Shugaba Buhari da jam’iyyarsa ba su damu da sace matan Dapchi ba

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tattara kayansa ya koma garin Dapchi domin ya gano mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ta sace.

“PDP na son Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shakatawar da yake yi da jam’iyyar APC a fadar Aso Villa ya nuna yadda ake shugabanci ta hanyar tafiya Dapchi da ke Yobe, domin samun labari da dumi-duminsa kan abin da ya sa aka sace mata ‘yan makaranta 110 yana ji yana gani,” in ji wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya aike wa manema labarai.

Gwamnatin Najeriya ta tura karin dakarun tsaro da jirage domin nemo ‘yan matan da aka sace a makon jiya.

Sai dai PDP ta ce abin kunya ne ga shugaban kasar da jam’iyyarsa ta APC su rika biki da shirin zaben 2019 a fadarsa a lokacin da iyayen ‘yan matan ke juyayin rashin ganin ‘ya’yansu.

Mayakan Boko Haram sun shiga garin Dapchi ranar 19 ga watan Fabrairu, inda suka ya da zango a makarantar ‘yan matan, suka yi awon gaba da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce satar yaran wani “babban bala’i ne” sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.

Wannan lamari ya tuna wa duniya sacewar da ‘yan Boko Haram suka yi wa ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok a shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wata uwa da aaka sace wa ‘ya a Dapchi

Iyayen yaran sun nuna matukar rashin jin dadinsu a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.

Sojojin sun ce sun mika tsaron garin a hannun ‘yan sanda, ko da yake rundunar ‘yan sandan jihar ta musanta hakan.

An kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, ranar Litinin din makon jiya, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fahasa ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa

Mazauna yankin sun ce jami’an tsaron kasar, wadanda jiragen yaki ke rufa wa baya, sun dakile harin.

Da farko dai gwamnatin jihar ta ce babu wanda aka sace, tana mai cewa daliban sun buya ne domin gudun kada maharan su kama su.

Amma daga bisani sun amince cewa an sace mata 110 bayan harin.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Iyayen matan da aka sace a Dapchi na duba jerin sunayen ‘ya’yansu

Jirgin sama ya jawo cunkoso a titin motoci a Afirka Ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
Nasidi Yahaya

Al’ummar birnin Johannesburg a kasar Afrika Ta Kudu sun tashi sun iske tsananin cunkoson ababen hawa sakamakon jan wani jirgin sama da ake yi a kan titin.

An ce mazaunan garin sun saba da samun cunkoson ababen hawa, amma ba su taba ganin inda jirgin sama ya janyo hakan ba.

An yi ta jan jirgin saman mai tsawon kilomita 40 daga wani wuri mai suna Jet Park daga gabas, zuwa Fourways Mall a arewa, inda zai zama wani ɓangare na sabon filin wasa da ake kira Kidzania.

Abun ya bai wa yara da dama sha’awa ganin jirgin sama a titin motoci, amma ya zama abun takaici ga masu tafiya, wadanda suke korafin me ya sa aka zabi ranar Talata don jan jirgin.

Hakkin mallakar hoto
Nasidi Yahaya

Hakkin mallakar hoto
Nasidi Yahaya

An mika gawar Sridevi Kapoor ga ‘yan uwanta


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Sridevi ta shahara sosai a Bollywood

‘Yan sandan birnin Dubai sun kammala binciken da suka yi a kan gawar jarumar Bollywood Sridevi Kapoor sannan suka mika ta a hannun iyalinta.

Jarumar, mai shekara 54, ta mutu ne ranar Asabar “sakamakon nitsewar da ta yi a cikin ruwa”, in ji ‘yan sandan. An gano gawarta a wurin wankan da ke otal din da ta sauka.

Tunda farko an ba da rahoton cewa bugun zuciya ne ya kashe shi a lokacin da suka je bikin ‘yan uwanta a Dubai.

Yanzu za a kona gawarta kafin a kai ta India inda za a yi mata jana’iza.

Tuni dandazon jama’a ya taru a kofar gidan Sridevi da ke Mumbai domin yi mata girmamawar karshe kafin a yi mata jana’iza.

Ta soma fitowa a fina-finan Bollywood tana da shekara hudu.

Sridevi ta soma fitowa a manyan fina-finai a 1978, inda daga nan ne ta zama daya daga cikin manyan jaruman India.

Dakarun sojin Nigeria da Kamaru ‘sun kashe mayakan Boko Haram 35’


Hakkin mallakar hoto
BOKO HARAM VIDEO

Image caption

Rundunar ta sha ba da labarin kashe mayakan Boko Haram

Rundunar Operation Lafiya Dole, da ke yaki da ‘yan Boko Haram, ta ce dakarunta da na Kamaru sun kashe mayakan kungiyar 35.

Sanarwar da mai magana da rundunar Kanar Onyema Nwachukwu ya aike wa manema labarai ta ce lamarin ya faru ne a tsuburan da ke yankin Chadi da kuma yankin Sambisa ranar Litinin.

A cewarsa, dakarun sun far wa yankunan da mayakan Boko Haram ke buya irinsu Kusha-Kucha da Surdewala da Alkanerik da Magdewerne da kuma Mayen, wadanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda suka kashe mayaka 35 sannan suka kwace bindigogi 15 daga wurinsu.

Kanar Nwachukwu ya kara da cewa dakarunsu sun ceto farar hula 603 wadanda Boko Haram ta yi garkuwa da su inda suka kai su Bäma Pulka Towns, kafin a mika su sansanonin ‘yan gudun hijira.

“A wani mataki irin wannan, gamayyar dakarun soji sun bi masu tayar da kayar bayan zuwa kauyukan Bokko, Daushe da kuma Gava inda suka kashe biyu daga cikinsu,” in ji kakakin rundunar.

Ya ce sun ceto farar hula 194 da aka yi garkuwa da su a kauykan sannan suka rusa gidajen wucin gadin da ‘yan Boko Haram suka gina a kauyukan.

“Kazalika, gamayyar dakarun ta kwato kauyukan Miyanti da Wudila, inda suka ceto maza uku, mata 121 da kuma kananan yara 209,” a cewar mai magana da yawun rundunar ta Operation Lafiya Dole.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labari. Sai dai a baya, rundunar ta sha bayar da labarin kashe mayakan Boko Haram tare da ceto mutane da dama.

Yadda Boko Haram da talauci suka ‘wawure’ kudin JAMB

‘Sayyadina Umar ya taba aika sako Daular Borno’

An yankewa ‘yan BH 20 hukuncin zaman gidan yari

Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN ARMY

Image caption

Rundunar ta sha ba da labarin kashe mayakan Boko Haram tare da ceto mutane da dama

Sarki Salman ya kori manyan hafsoshin sojan Saudiyya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sarki Salman ya hau mulki a shekara 2015

Saudiyya ta kori manyan kwamandojin sojinta, ciki har da shugaban ma’aikata, a jerin matakan da masarautar ta dauka da tsakar dare.

Sarki Salman ya maye gurbin manyan hafsoshin sojin kasa da na sama.

Kamfanin dillancin labaran kasar ne ya wallafa jerin sunayen mutanen da aka kora, amma ba a fadi dalilin sallamarsu ba.

Lamarin na faruwa ne a lokacin da yakin da ake yi a Yemen, inda Saudiyya ke jagorantar gamayyar rundunar yaki da masu tayar da kayar baya, ke shiga shekara ta uku.

An yi amannar cewar yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda shi ne ministan tsaron kasar, ne ke sa wa ana gudanar da sauye-sauye a kasar.

A bara dai, an daure fitattun ‘yan kasar Saudiyya a wani babban otal da ke Riyadh mai suna Ritz-Carlton, ciki har da shugabanni, ministoci da attajirai, a yunkurin da Mohammed bin Salman ke jagoranta na kawar da cin hanci da rashawa.

Burkina Faso: Za a fara shari’ar wadanda suka kitsa juyin mulki


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An girke daruruwan jami’an tsaro a wajen harabar kotun da za a yi shari’ar mutanen da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso

A ranar Talata ne za a fara shari’ar mutanen da ake zargi da yunkurin juyin mulki a shekarar 2015 a kasar Burkina Faso.

Fiye da mutum 80 ne za su bayyana gaban kotu a shari’ar da aka bayyana a matsayin zakaran gwajin dafi a tsarin shari’ar kasar.

Daruruwan jami’an tsaro aka girke a harabar kotun wadda za a fara shari’ar wadannan mutane.

Daga cikin mutum 80 din da zasu bayyana gaban kotun har da wasu manyan janar biyu fitattu wato Gilbert Diendere da kuma Djibril Bassole, wadanda na hannun daman tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ne.

A waccan gwamnatin da ta shude, Gilbert Diendere, shi ne shugaban masu tsaron fadar shugaban kasar.

Ana kuma zargin sa shi da sojojin da ke karkashinsa da yunkurin hambarar da gwamnatin rikon ta Burkina Faso, shekara guda bayan tsohon shugaban kasar ya bar kasar.

Yayin da Janar Bassole, da sauran mutanen da za su bayyana gaban kotun kuma ake tuhumarsu da cin amanar kasa da yin zagon kasa ga harkar tsaron kasar da kuma kisa.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar na kallon wannan shari’a a matsayin zakaran gwajin dafi dangane da sahihancin tsarin shari’ar kasar.

A watan Satumbar shekarar 2015 ne, wasu daga cikin dakarun da ke tsaron fadar tsohon shugaba kasar suka kama wasu jami’an gwamnatin rikon kwarya.

To amma yunkurinsu na juyin mulkin da suka so yi, bai samu nasara ba saboda zanga-zangar da aka rinka yi a kan tituna da ta samu goyon bayan sojojin kasar.

Akalla mutum 14 sun rasa ransu, yayin da wasu fiye da 200 kuma suka samu raunuka a yayin zanga-zangar.

BBC: ‘An ci zarafin mata a kudancin Syria’


Image caption

Yakin da ake a Syria ya raba miliyoyin mutane da muhallansu

BBC ta gano masu kai kayan agaji, da majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji suka wakilta dan shiga kasar Syria sun ci zarafin mata ta hanyar lalata da su.

Kungiyoyin Care da kuma International Rescue Committee, sun yi gargadi kan cin zarafin a shekarar 2015.

Amma rahoton da hukumar kula da yawan al’uma ta majalisar dinkin duniya ta gudanar ya gano ana yin lalata da matan ne sannan a ba su kayan abinci a kudancin Syria.

Sai dai wani ma’aikacin agaji ya yi ikirarin ba su da hurumin bada kayan agaji kai tsaye har sai masu sa ido sun iso.

Binciken da BBC ta yi ta hanyar tuntubar kungiyoyin agajin na majalisar da masu zaman kansu, sun ce sam ba su san takwarorinsu na aiki na gudanar da mummunar dabi’ar.

Nan da lokaci kadan, yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’i 5 za ta fara aiki a gabashin garin Ghouta na Syria, yankin da ‘yan tawaye suka makale.

Rasha ce dai ta bada wannan umarni, ta kuma ce za a dinga tsagaita wuta na sa’o’i 5 a kowacce rana dan fararen hula su samu damar tserewa daga yankin da aka yi wa kawanya.

Ba tabbas ko kungiyoyin agaji za su shiga da kayan abinci da magani garin.

Wani likita da bai so a bayyana sunan sa ba yace babu magani da kayan aiki a asibitin garin, ya yin da likitoci da ke aikin sadaukar da kai su na rayuwa tsakanin rai da ajali.

Likitan ya ce yakin da aka dauki sama da shekara 4 ana yi a Syria, ya sanya daukacin kasar cikin zullumi da tashin hankali. Sannan abin da ke faruwa na shigen kama da labarin yakin duniya na biyu da suka karanta.

Abun da muka sani game da sace ‘yan Matan Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Makarantar Dapchi nada yawan dalibai sama da 900

Sace dalibai ‘yan mata sama da 100 daga makarantar kwana a arewa maso gabashin Najeriya na tattare da rudani.

Mun san cewa wasu gungun mayaka, da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun shiga garin Dapchi a jihar Yobe da yammacin Litinin, 19 ga Fabrairu.

Sun tunkari makarantar Sakandaren kimiya da fasaha ta mata, suna ficewa a hankali.

Da farko, an yi ikirarin cewa yawancin matan sun tsere kuma babu daya daga cikinsu da aka sace.

Amma daga baya kuma sai gashi hukumomi sun amsa cewa an sace ‘yan Matan.

To shin wai menene ainihin abin da ke faruwa?

Me ya sa ba mu san me ya faru ba?

Tun da farko dai an fara shiga rudani ne daga wani malami, wanda ya zanta da manema labarai bayan an kai harin.

Ya ce mayakan suna neman abinci ne, ba sun je ba ne da niyyar garkuwa da wani. Ya kuma ce ‘yan matan sun shuga daji ne domin buya.

Wasu na ganin kamar da farko gwamnati ta amince da bayanin malamin kafin daga baya ta yarda da cewa sace ‘yan matan aka yi.

Amma duk da haka, rudanin ya kara yawa a labarin, a yayin da bayanai daga bangarorin gwamnati da sojoji suka yi ta karo da juna, har ta kai aka fito aka bayar da sanarwar ceto daliban, a dai dai lokacin da babu wani jami’in gwamnati ko na tsaro da ya fito ya sanar da cewa an sace su.

‘Yan mata nawa aka sace?

Babban batun da ya fi jan hankali a rudanin labarin tsakanin iyayen ‘yan matan da hukumomi shi ne yawan adadin daliban da aka sace.

Tun da farko iyayen sun dage cewa ‘yan mata sama da 100 ne aka sace daga makarantarsu, da ke da yawan dalibai 926, yayin da kuma hukumomi suka ce adadin bai kai 50 ba.

Sannan hukumomin sun ci gaba da ikirarin cewa ‘yan matan da dama sun gudu sun shiga daji, tare da cewa za su fito.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan uwan daliban sun taru a makarantar Dapchi a yayin da suke jiran tsammani

Domin kawo karshen dambarwar, iyayen ‘yan matan sun hada kansu inda suka fitar da jerin sunaye 105 na ‘ya’yansu da aka sace.

Wannan ya sa gwamnati ta yi amai ta lashe, inda ta fito ta ce adadin ‘yan matan da aka sace 110 ne.

Ko menene kamannin batun Dapchi da Chibok?

Editan BBC a Afirka Will Ross, ya lura da wasu abubuwa daga batun sace ‘yan matan Chibok a watan Afrilun 2014 da ke kama da batun sace ‘yan Mata a Dapchi.

Ya ce a lokacin, sojoji da gwamnati sun musanta labarin Chibok kuma ba tare da fitar da wani bayani ba a yayin da Boko Haram ta kwashi ‘yan mata sama da 279 ta shiga daji da su.

A wannan karon ma an samu rudani, inda aka yi ikirarin ceto ‘yan matan, kafin daga baya kuma gwamnati ta fito ta nemi afuwa.

Bayan shekaru hudu da suka gabata, a yau kuma duniya ta sake cin karo da irin wannan al’amari na rudanin bayanai da kuma fushi daga iyaye.

Har yanzu akwai ragowar ‘yan matan Chibok sama 100 da ake ci gaba da garkuwa da su.

Ko da ace hukumomi za su iya kubutar da su, amma har yanzu ba a ji duriyar ‘yan matan Dapchi ba.

Me ya sa babu wani jami’in tsaro a Makarantar?

Duk da darasin da ya kamata ace an koya daga sace ‘yan matan Chibok a 2014, amma kuma sai gashi yanzu ya kasance babu wani jami’in tsaro a makarantar Dapchi.

Kuma duk da haka iyaye na tura ‘yayansu.

Wakilin BBC ya ce wannan na da nasaba ne daga fatan da mutane suke cike da shi bayan zaben shugaba Muhammadu Buhari a 2015, da kuma yadda sojoji suke ta nanata samun galabar yaki da ‘yan Boko Haram.

Ya ce, sun san cewa akwai sojoji da shingayen bincikensu a kusa da garin, saboda gwamnan Yobe Ibrahim Gaidam ya shaidawa manema labarai cewa mayakan sun kai hari, sa’o’i bayan sojoji sun fice daga shingayen bincike a Dapchi.

Ko da yake rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin.

Me ya sa ba za su iya gano ‘yan matan ba?

Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince cewa an sace ‘yan matan, kuma daga karshe ta kaddamar da farautar gano su.

Shugaba Buhari ya ce rundunar soji da da jiragen sama za a yi amfani da su domin gano ‘yan matan. Sai dai babu wani karin bayani game da binciken.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wasu daga cikin Kayan daliban da aka sace a Dapchi

Sai dai kuma jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa tuni Mayakan Boko Haram suka fice da ‘yan matan daga Najeirya zuwa makwabciyarta Nijar.

Amma idan har suna cikin Najeriya, wakilin BBC ya yi imanin cewa za a bi da su ne ta Dajin Sambisa, domin anan ne kawai za su iya boye wa saboda girman dajin.

A nan ne hedikwatar Boko Haram inda ta boye ‘yan Chibok.

An yi ikirarin murkushe Boko Haram – Shin gaskiya ne

A watan Janairu ne Janar roger Nicholas kwamandan da ke jagorantar yaki da Boko Haram a arewa maso gabashi ya sanar da cewa an murkushe kungiyar Boko Haram.

Amma sace ‘yan matan Dapchi ya nuna ba haka ba ne.

Bidiyon yarinyar da ke kukan jini


A duk lokacin da Nikki Christou mai shkera 13 ke kuka sai jini ya dinga fitowa daga idonta maimakon hawaye.

Nikki na fama ne da wata cuta da ke da alaka da jijiyoyin da jini ke bi wacce ake kira arteriovenous malformation, AVM, al’amarin da ke sa take kukan jini wanda hakan ke barazana ga rayuwarta.

A yanzu masana kimiyya sun gano abun da ke jawo wannan cutar da ba a saba gani ba, kuma sun yi amanna magunguna sankara za su iya taimakawa Nikki, don haka a yanzu ana amfani da ita wajen gwajin da masana kimiyya ke yi a Cibiyar Lafiyar Yara da ke Jami’ar Landan da kuma Asibitin Ormond Street.

Dapchi: ‘Gara karatun islamiyya da na koma makarantar Dapchi’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba za a bude makarantar sakandiren Dapchi ba har sai randa hali ya yi inji gwamnatin jihar Yobe

A Najeriya, mahukunta a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar sun ce ba za a bude makarantar sakandiren da aka sace ‘yan mata a ciki ba har sai abin da hali ya yi.

A ranar Litinin din data gabata ne aka cika mako guda da sace ‘yan matan makarantar ta Dapchi wanda ake zargin wasu mahara sun sace su.

Daya daga cikin ‘yan matan sakadiren da ta tsira daga kamun maharan da BBC ta tattauna da ita, ta ce gara ta koma makarantar islamiyya maimakon ta koma makarantar.

Dalibar ta ce, ko da an sanya jami’an tsaro a makarantar tasu, ita kam ta hakura da karatun.

Don haka ko da an bude makarantar tasu ta Dapchi ma, ita kam ta sallama karatu a ciki.

Kimanin ‘yan mata 110 gwamnati ta tabbatar da an sace su.

An kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, ranar Litinin din makon jiya, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fahasa ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa.

Iyayen yaran da aka sace sun nuna matukar rashin jin dadinsu a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.

Shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari, ya ce satar yaran wani “babban bala’i ne” sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.

Kuma gwamnatin Najeriyar, ta ce ta tura karin dakarun tsaro da jiragen yakin domin nemo ‘yan mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace su a makon jiya.

Ba zan so Wenger ya zauna a Arsenal ba – Ian Wright


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba zan iya cewa Arsene Wenger ya ci gaba da zama a Arsenal ba bayan kakar nan

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Ian Wright ya ce ba zai iya bayar da goyon baya Arsene Wenger ya ci gaba da zama a matsayin kociyan kungiyar ba bayan kakar nan.

Wright ya ce ko kociyan ya ci gaba da zama a karshen kakar nan, shi kam ba zai goyi da bayan hakan ba, kuma ya san cewa da wuya a ce wani zai nemi ya ci gaba da zama.

Ya ce dole ne a kawo karshen wannan abin da ake yi a kungiyar na bambadanci da ganin ido.

Tsohon dan wasan ya kuma zargi wasu ‘yan wasan da samun kudin banza a kungiyar ba tare da cin guminsu ba yana mai cewa mai kungiyar Stan Kroenke bai damu da hakan ba.

Arsenal ta sha kashi a wasanninta shida daga cikin 12 a shekarar nan ta 2018, na baya bayan nan shi ne wanda Manchester City ta doke ta a wasan karshe na cin kofin Carabao ranar Lahadi.

Wright ya ce har kullum Wenger ba ya rasa ta cewa, sannan kuma yana shagwaba ‘yan wasa

Kwallon Kwando: Najeriya ta kama hanyar gasar duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya ta yi nasara a dukkanin wasanninta na karon farko a rukuninta

Tawagar ‘yan wasan kwallon kwando na Najeriya maza, kamar yadda aka yi tsammani ta yi nasarar tsallake wasannin karon farko na rukuni na biyu, Group B, na neman gurbin gasar kofin duniya ta 2019, ba tare da an ci ta ba.

‘Yan Najeriyar sun doke Uganda suka yi awon gaba da Rwanda kana kuma suka casakara mai masaukin baki Mali, da akasari bambancin kwallo 33.

A wasannin rukuni na hudu, Group D, wadanda aka yi a babban birnin Mozambique, Maputo, mai masukin baki Mozambique da Senegal su ne suka zama gaba a rukunin, inda kowacce daga cikinsu ta yi nasara sau biyu aka kuma doke su sau daidai.

Zakarun Afrika Tunisia sun gama wasansu na rukuni na daya Group A ba tare da an doke su ko sau daya ba.

Kamar yadda su ma ‘yan Angola suka kammala wasan nasu na rukuni na biyu, Group B ba tare da an cinye su ko sau daya ba, dukkanin rukunan biyu sun yi wasanninsu na zagayen farko ne a watan Nuwamba.

Yanzu sai a watan Yuni da na Yuli za a yi zagaye na gaba na neman gurbin zuwa gasar ta cin kofin duniya na kwallon kwandon, inda ake da gurbi biyar daga Afirka, a gasar da za a yi a karon farko da kasashe 32 a China a watan Agusta.

Sojoji sun fice Dapchi ba da saninmu ba- ‘Yan sanda


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An sace ‘yan matan makarantar Dapchi bayan sojoji sun fice

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta musanta ikirarin da rundunar sojin Najeriya ta yi cewa ta hannunta ragamar tafiyar da tsaro ga ‘yan sanda kafin ta janye jami’anta.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe Sumonu A Abdulmaliki ya ce sanarwar da rundunr lafiya dole ta fitar game da mika ragamar tafiyar da tsaron Dapchi ga ‘yan sandan ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ta ce babu wani lokacin da Sojojin suka sanar da ‘yan sanda, ko tuntubar su kafin su fice a hukumance daga garin Dapchi balle har su hannunta ma su ragamar tafiyar da tsaron garin.

Sanarwar kuma ta bukaci jama’ar Yobe su yi watsi da ikirarin na sojojin, domin ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ‘yan sandan na zuwa ne bayan, rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa da ke dauke da bayani a kan dalilin da ya sa sojoji suka janye kafin harin da aka sace ‘yan matan makarantar Dapchi sama da 100.

Rundunar Lafiya dole ta ce jami’anta sun janye ne kasancewar kura ta lafa a yankin na Dapchi, kuma yanzu aikin ‘yan sanda ne su ci gaba da samar da tsaro a yankin.

Tun da farko dai gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam yi fito ya dora laifin a kan gazawar sojoji na rashin kula da tsaron makarantar da har ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka samu kwarin guiwar shiga su sace daliban.

Mohamed Diame ya yi watsi da bukatar dawo wa Senegal wasa


Hakkin mallakar hoto
Khaled Desouki

Image caption

Mohamed Diame ya zama kusan dan wasan wucin-gadi a karkashin kociyan Senegal Aliou Cisse

Bi sa ga dukkan alamu dan wasan gaba na Senegal Mohamed Diame yana jin dadin kasancewarsa a kungiyar Newcastle ta Premier, kuma ya kara jaddada aniyarsa ta daina yi wa kasarsa kwallo.

Dan wasan mai shekara 30 ya yi wa kungiyar wasan Premier 21 a bana inda ya ci mata kwallaye biyu masu matukar muhimmanci.

To ganin yadda dan wasan yake taka-leda a yanzu ba kama hannun yaro, kasarsa Senegal take neman ya yi mata kome, bayan da ya ce ya yi ritaya daga yi mata wasa a watan Maris na bara.

Sai dai Mohamed Diame ya kekasa kasa ya ce ai aikin gama ya gama, ba zai sake dawowa wasan kasa da kasa ba.

A lokacin da ya yi ritaya ya ce ya yi amanna ba ya daga cikin gwanayen ‘yan wasan Senegal kuma, ya ce akwai ‘yan wasan Senegal 23 da suke kan ganiyasrsu.

Dan wasan mai shekara 29 ya taka wa tawagar kasar tasa, Teranga Lions wasa sau 36 sannan ya yi mata wasa a gasar Olympics ta 2012.

Ya ce bayan tunani mai zurfi da kuma shawara yanzu ne lokacin da ya kamata ya mayar da hankali sosai a kan kungiyarsa.

Tun lokacin da Aliou Cisse ya kama aikin kociyan kasar a watan Maris na 2015, ya rika amfani da Diame a matsayin dan wasan wucin gadi.

An yi hatsaniyar addini a Kaduna


Hakkin mallakar hoto
Kaduna State Government

Image caption

Gwamnatin Kaduna ta kaddamar da bincike kan rikicin Kasuwar Magani

An kona gidaje bayan barkewar rikici mai nasaba da addini a kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Babu dai wani cikakken bayani game da dalilin faruwar rikicin amma wasu rahotanni sun ce rikici ne tsakanin mabiya addinin kirista da musulmi.

Rahotannin da muka samu sun ce, sabani na soyayya tsakanin wata budurwa kirista da musulmi ne ya tayar rikicin tun a ranar Laraba, inda kiristoci suka bukaci duk wata da ke son musulmi ta daina.

Kuma Kiristocin sun bukaci duk macen da ta yi aure a gidan musulmi ta fita ko su fitar da ita da karfi.

A yau litinin kuma wasu matasa sun fantsama cikin gari inda rikici ya kaure.

‘Yan sanda ba su bayyana mutanen da suka rasu ba, amma hausawa mazauna garin sun ce sun kirga gawarwakin mutanen 12 yayin da suka ce ana ci gaba da tattara gawarwakin wadanda suka mutu.

Gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da al’amarin, inda ta bayyana cewa ta tura jami’an tsaro domin magance rikicin da ruruwarsa.

Sai dai a cikin sanarwar da Samuel Aruwan kakakin gwamnan Jihar Kaduna ya fitar bai fadi adadin mutanen da suka mutu ba da adadin wadanda suka jikkata.

Sanarwar ta ce gwamnan Jihar Malam Nasir El Rufa’i ya umurci jami’an tsaro su gudanar da bincike tare da kame duk wadanda ke da hannu a rikicin da ya faru a Kasuwar Magani.

Tazarar nisan kilomita 31 ne tsakanin Garin Kasuwan Magani da birnin Kaduna.

‘Yan wasan Arsenal ba su da kishi – Ian Wright


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba wata kungiyar Premier da ta taba cin wata ta gasar da yawan kwallo har 3-0 a wasan karshe na gasar ta kofin League tun 2006

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Ian Wright ya ce ‘yan wasan kungiyar ba su nuna kwazo da kishi ba a fafatawar karshe da suka yi na cin kofin Carabao wanda Manchester City ta casa su 3-0, ranar Lahadi.

Wright wanda ya ci wa Arsenal bal 185, ya ce sam-sam ‘yan wasan ba su yi komai ba, wasan da suka yi lami ne kawai.

Ya kara da cewa kowa ya riga ya gane cewa magana ce ta jagoranci da kishi, kuma Arsenal ba ta su.

Tsohom dan wsan na Arsenal ya ce, daman an san cewa haduwa da Manchester City ba abu ne mai sauki ba, saboda kungiya ce da take kokari a duk kakar nan, amma kuma abin takaici ne yadda Arsenal ta yi wasan.

Ya ce wasan karshe ne amma wai sai ka ga dan wasa yana tafiya kawai. Ai ba za ka so ka ga kungiyar da kake goyon baya tana wasa haka ba ba wani kuzari.

Sanna ya ce: ”Koma me muka fada a kan Alexis Sanchez da yadda yake a dakin sa jesi, ya ga cewa ba shi da ta yi dole ne ya tafi, saboda shi yana son ya yi nasara ne, ya kasance tare da mutanen da suke son yin nasara.”

Arsenal wadda maki 27 ne tsakaninta da jagorar Premier Manchestrer City, za ta kara da AC Milan a wasan matakin kungiyoyi 16 na gasar Europa a watan Maris.

An doke kungiyar ne ta Arsene Wenger a karawar ta Wembley, inda Pep Guardiola ya dauki kofinsa na farko a matsayin kociyan Manchester City.

‘Ba za a yi amfani da fasahar bidiyo mai taimaka wa lafiri ba a gasar Zakarun Turai’


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, Aleksander Ceferin ya ce yana goyon bayan amfani da fasahar, amma ba ya so a yi gaggawa

Ba za a yi amfani da fasahar bidiyo mai taimaka wa alakalin wasa warware takaddama ba a gasar cin kofin zakarun Turai saboda akwai alamun rudani da yawa in ji shugaban Uefa.

Hukumar gudanarwar kwallon kafa ta duniya wadda ke yanke hukunci kan dokokin wasan za ta gana ranar Asabar domin yanke hukunci ko za ta amince da amfani da fasahar dindindin.

Idan hukumar ta amince to ya zama dole ke nan hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta yi amfani da fasahar a gasar cin Kofin Duniya.

To amma kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, Aleksander Ceferin ya ce: ”A ko da yaushe ‘yan kallo na ganin allon talabijin na fasahar, amma kuma ba wanda ya san yadda take aiki.”

Ya kuma kara da cewa, ba za su yi amfani da ita ba a gasar cin kofin Zakarun Turai a kaka mai zuwa ba.

Ya ce shi dai a wurinsa za ta iya kasancewa fasaha mai kyau, amma bai kamata a gaggauta amfani da ita ba.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Kofin FA: An yi amfani da fasahar wajen hana bal din da mata ya ci Huddersfield a wasan cin kofin FA zagaye na biyar

An yi gwajin amfani da fasahar a wasu wasannin cin kofin FA a Ingila. Sannan an yi amfani da ita a gasar kofin Carabao, inda aka yi amfani da ita a wasan karshe na gasar ranar Lahadi, har ma kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya nuna rashin jin dadinsa kasancewar ba ta hana bal ta biyu da Manchester City ta ci su ba.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino a ranar Litinin ya ce yana ci gaba da bayar da goyon bayan ganin an yi amfani da fasahar a gasar cin kofin duniya da za a yi a wannan shekarar.

Saudi Arabia ta kyale mata su shiga aikin soja


Hakkin mallakar hoto
AFP

A karon farko Saudiyya ta bude cibiyoyin karbar takardun nemai aikin soja ga matan kasar.

An bai wa mata zuwa ranar Alhamis domin su aike da takardun nemai aikinsu a lardunan Riyadh da Makka da al-Qassim da kuma Madina.

Sai dai aikin nasu ba zai ba su damar zuwa fagen daga ba, sai dai kawai ya ba su damar shiga aikin tsaron kasar.

An sanya sharuda 12 ga duk macen da ke son zama soja ta cika su kafin a dauke ta aikin, ciki har da: dole ne ta kasance ‘yar kasar, da kuma zama ‘yar shekara tsakanin 25 zuwa 35, sannan kuma tana da matakin ilimi na babbar difiloma.

Dole ne matan – da kuma muharramansu – akasarinsu mazajensu, ko iyayensu ko kuma ‘ya’yansu maza – su kasance suna zaune a yankin da za a bai wa macen aiki.

Matakin daukar mata a aikin soja na cikin sauye-sauyen da kasar ke gudanarwa a watannin baya-bayan nan domin inganta damar mata a kasar da ake yi mata kallon mai cike da ‘tsattsauran ra’ayi.’

A watan Yuni ne Sarki Salman ya amince mata su soma tuka mota, sannan ya amince mata su rika zuwa kallon wasan kwallon kafa.

Saidai masu fafutika suna suka, inda suka ce har yanzu ba a barin mata su yi tafiya ba tare da maza ba.

A karkashin dokar kasar, dole mace ta nemi izini kafin ta yi tafiya ko aure ko kuma gidan yarin.

Zakunan Syria da Iraki sun koma Afirka Ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
Twitter

Wasu zakuna biyu da aka yi watsi da su a wasu gidajen namun daji da ke kasashen Syria da Iraki sun koma Afirka Ta Kudu, bayan yaki ya daidata gidajen adana su da ke kasashen.

A yanzu dai an mayar da zakunan Afirka Ta Kudu ne inda ya zama sabon gidansu.

Kungiyar da ke kula da dabbobi ta Four Paws ta wallafa hotunan zakunan a shafinta na Twitter gabannin kai su Afirka Ta Kudun

A shekarar 2017 ne kungiyar Four Paws ta ceto zakunan daga wasu gidajen ajiye namun daji da ke biranen Mosul da kuma Aleppo.

Mafi yawan namun daji da ke gidan zoo na Mosul sun mutu sakamakon yunwa ko kuma hare-haren bama-baman da ake kai wa, yayin da aka ceto wasu namun dajin 12 daga gidan zoo na Aleppo.

Sai da aka kai zakunan masu suna Simba da Saeed cibiyar bayar da kulawa ta musamman a kasar Jordan kafin a kai su Afirka Ta Kudun.

Za a kai su sabon matsuguninsu mai girman ekta 1,250 da ake ajiye zakuna mai suna Lions Rock, da misalin karfe 1.00 na ranar Litinin.

Kungiyar da ke kula da dabbobi ta Four Paws ta wallafa hotunan zakunan a shafinta na Twitter gabannin kai su Afirka Ta Kudun

Ruwa ne ‘ya yi ajalin jarumar Bollywood Sridevi Kapoor’


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Sridevi ta yi fice a fina-finan Bollywood

Ruwa ne ya ci tauraruwar fina-finan Bollywood Sridevi Kapoor, in ji wani bincike kan gawarta da aka yi a Dubai.

A farko dai an ba da rahoton cewa jarumar, mai shekara 54, ta mutu ne sakamakon bugun zuciya ranar Asabar lokacin da take halartar bikin ‘yan uwanta a Dubai.

Wasu majiyoyi sun shaida wa kafafen watsa labarai cewa an gano ta a cikin wurin wankan otal din da suka sauka ba ta motsi.

Sridevi ta shafe sama da shekara 50 tana yin fim, inda ta fito a kusan fina-finai 300. Jaruman Bollywood, da fitattun ‘yan kwallon kafa da ,amya ‘yan siyasa sun yi matukar kaduwa da jin labarin mutuwarta.

‘Yan sandan da ke bincike kan gawa na Dubai ne suka ba da rahoton abin da ya yi ajalin jarumar ga iyalinta da kuma ofishin jakadancin India da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, in ji jaridar the Gulf News.

Jaridar ta kara da cewa fitar da rahoton ka iya jinkirta kai gawar Sridevi gida. An sa ran cewa za a kai gawar tata India ranar Litinin.

Hotunan ban mamaki wadanda suka sauya rayuwa


An yi gwanjon hotuna 24 na kundin hotunan the Lewis Hine a New York. Mai daukar hoto Isador Sy Seidman ne ya dauki wadannan hotunan da ba safai a kan ga irinsu baa New York.

Dan Amurkar, masanin ilimin halayyar dan adam na cikin manyan masu daukar hotunan tarihi a karni na 20.

A wancan lokacin ba a nuna muhimmanci ilimin daukar hoto da ajiye su a zaman tarihi, don haka ne Hine ya bayyana nasa hotunan a matsayin “labaran hotuna”, inda ya yi amfani da daukar hotuna da bayanan da ke cikinsu domin yin fafutika kan abubuwan da ya yi amanna da su.

Hotunan sun nuna irin jajircewar da Hine ya yi kuma yawancin ayyukansa da aka fi sani, sun fi mayar da hankali kan talakawa da marasa galihu da ke biranen Carolina, New York da Pittsburgh.

Hakkin mallakar hoto
COURTESY OF SWANN AUCTIONS GALLERIES

Image caption

Wani ma’aikaci a kamfanin samar da hasken lantarki na Steam Pump, circa a 1921. An sayar da wannan hoton a kan $80,000

A baby lies in a blanket.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Wata ran da aka shiga matsi a New York, a 1908.

A mother holds her child in her lap.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Uwa da ‘ya a Tsibirin Ellis a 1907.

Hine ya kwashe shekaru da dama yana daukar hotuna, inda yake daukar hotunan da ke nuna mutane cikin karama da shaukin rayuwa. A shekarar 1904, ya soma adana rayuwar ‘yan ci-ranin da suka isa Tsobirin Ellis.

Babban burinsa shi ne ya yi haba-haba da sabbin mutanen da suka isa Tsibirin, wadanda mazauna birnin New York ke jin tsoronsu.

Hine yana daukar hotunansa ne bayan ya samu izini daga wurin mutanen da yake so ya dauki hotonsu, inda za ka ji wata kara a lokacin da yake dauka.

A family together with their bags.Hakkin mallakar hoto
COURTESY OF SWANN AUCTIONS GALLERIESs

Image caption

Wasu iyalai ‘yan asalin Italiya a Tsibirin Ellis, 1905.

A group of three children eating.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Wani yammaci a New York a shekarar 1912.

An immigrant sleeps on her case.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Wata ‘yar asalin Rusasshiyar Daular Sibiyet a Tsibirin Ellis Island a 1907.

Wasu hukumomin jin dadin al’umma ne suka bukaci Hine ya dauki hotuna. Wasu daga cikin fitattun hotunan da ya dauka sun hada da na ma’aikatan gine-gine na The Empire State Building.

A lokacin da yake daukar wa Kwamitin Kasa na Yaki da Bautar da kananan yara a shekarar 1908, ya dauki hotuna a ma’aikatu wadanda daga bisani aka yi amfani da su a matsayin shaida wajen daure masu bautar da yara.

Ma’aikatun da ke bautar da yaran sun tsane shi saboda yadda yake yin shigar burtu wajen gano su domin kare lafiyarsa. An sha yin barazanar kashe shi.

Hotunan da ya dauka ne suka sa aka sauya dokokin bautar da yara na Amurka.

A labourer hangs on a connector in the sky.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Wani ma’aikaci a ginin Empire State tsakanin 1930-31.

A small girl working at a mill.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Daya daga cikin yaran da ke aiki a ma’aikatun yin auduga na Carolina a 1908.

Children making artificial flowers.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Furannin roba a New York a shekarar 1912.

Small boys breaking coal.Hakkin mallakar hoto
Courtesy of Swann Auction Galleries

Image caption

Ma’aikatan kwal a Pennsylvania a 1912.

Dukkan hotunan na Swann Auction Galleries ne.

Manchester City: Guardiola zai ci gaba da sanya zirin kyalle


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Guardiola ya sanya ruwan dorawar kyallen a wasan karshe na cin kofin Carabao

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce zai ci gaba da sanya zirin kyalle ruwan dorawa abin da ya sanya hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhume shi da karya dokar tallata wata manufa.

Guardiola ya ce ya sanya kyallen ne – wanda ake ganinsa tamkar wani sakon siyasa ne – domin nuna goyon bayan ‘yan adawar Catalonia da aka daure.

“Ni dan adam ne kafin na zama koci,” in ji dan kasar ta Spain mai shekara 47.

“Su (jami’an FA) sun san cewa zan rika sanya ruwan dorawar kyallen nan a ko da yaushe.”

Tsohon kocin na Barcelona ya kara da cewa: “Ban yi haka domin siyasa be, na yi ne domin dimokradiyya: na yi ne domin na taimaka wa mutanen da aka gallazawa ba tare da sun yi laifin komai ba.”

An ba shi zuwa karfe shida na yammacin ranar Litinin, biyar ga watan Maris domin ya ba da amsa kan tuhumar da FA ke yi masa.

FA ta tattauna da Guardiola a kan batun a tsakiyar watan Disamba sannan ta yi masa gargadi kan ya daina sanya kyallen sau biyu amma bai daina ba.

Daga nan ne aka tuhume shi, lokacin da ya ake sanya kyallen a cikin filin wasa – a karawar da Wigan ta doke City ranar Litinin.

Jami’an tsaron Nigeria sun bazama neman ‘yan matan Dapchi 110


Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

An bar takalma a warwatse bayan sace ‘yan matan na Dapchi

Gwamnatin Najeriya ta tura karin dakarun tsaro da jirage domin nemo ‘yan mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace su a makon jiya.

Mayakan Boko Haram sun shiga garin Dapchi da ke jihar Yobe ranar 19 ga watan Fabrairu, inda suka ya da zango a makarantar ‘yan matan, suka yi awon gaba da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce satar yaran tamkar wani “babban bala’i ne” sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.

Wannan lamari ya tuna wa duniya sacewar da ‘yan Boko Haram suka yi wa ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok a shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wata uwa da aaka sace wa ‘ya a Dapchi

Iyayen yaran sun nuna matukar rashin jin dadinsu a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.

An kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, ranar Litinin din makon jiya, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fahasa ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa

Mazauna yankin sun ce jami’an tsaron kasar, wadanda jiragen yaki ke rufa wa baya, sun dakile harin.

Da farko dai gwamnatin jihar ta ce babu wanda aka sace, tana mai cewa daliban sun buya ne domin gudun kada maharan su kama su.

Amma daga bisani sun amince cewa an sace mata 110 bayan harin.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Iyayen matan da aka sace a Dapchi na duba jerin sunayen ‘ya’yansu

Fararen hula na fama da sarkewar numfashi a Syria


Image caption

Fararen hula na kwance a asibiti, bayan zargin gwamnati ta yi amfani da makami mai guba na sinadarin Chlorine

Jami’an lafiya a yankunan da ‘yan tawaye suka yi wa kawanya a gabashin garin Ghouta na kasar Syria, sun ce daruruwan mutane na fama da matsalar toshewar numfashi sakamakon shakar iskar gas mai sinadarin Chlorine a hare-haren da dakarun gwamnati da na ‘yan tawaye suka kai wa juna.

A wata sanarwa da ministan lafiyar kungiyar ‘yan a ware ya fitar, ya ce mutanen da lamarin ya rutsa da su da suka hada da fararen hula da direbobin motocin daukar marasa lafiya sun kwanta a asibiti sakamakon shakar iskar da suka yi bayan fashewar wani abu.

Wani mazaunin garin Ghouta ya shaidawa BBC cewa dakyar wani yaro ya rayu sakamakon numfashinsa da ya sarke, ana dai zargin gwamnatin Syria da amfani da makamai masu guba kokarin fatattakar ‘yan tawayen daga maboyarsu.

A ranar asabar ne aka kada kuri’ar amincewa da dakatar da bude wutar tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawaye, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a birnin New York na Amurka.

Amma duk da hakan an ci gaba da kai hare-hare nan da can. Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kananan yara sun fi shan wahala a yakin da ake yi a Syria.

Sama da shekara 4 kenan ana yakin na Syria, tun bayan kadawar guguwar sauyi a yankin gabas ta tsakiya. A bangare guda kuma ‘yan tawaye sun sha damarar kawo karshen mulkin shugaba Basharul Assada na Syria amma har yanzu hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Bam ya hallaka mutum hudu a Leicester


Image caption

Wakilin BBC da ke wurin ya ce jami’an tsaro sun yi shirin kar ta kwana a yankin

‘Yan sanda a birnin Leicester sun tabbatar da mtuwar mutane hudu, a lokacin da wani abu ya fashe a wani kanti.

Lamarin ya faru ne a kan titin Hinckley da misalin karfe bakwai na yamma a jiya Lahadi, kamar yadda shugaban ‘yan sandan yankin Supt Shanes O’Neil ya bayyana.

‘Yan sandan sun ce wasu mutane hudu na kwance a asibiti sakamakon mummunan raunin da suka ji.

Mista O’Neill ya kara da cewa ta yi wu akwai karin wasu ababen fashewar, dan haka an girke jami’an tsaron kar ta kwana da ma’aikatan agaji dan kar lamarin ya dagule.

Ana ci gaba da alhinin rasuwar jaruma Sridevi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sridevi ta fito a fina-finai kusan 300 na Hindi da Telugu da kuma Tamil

Dubban masoya da jarumai da ma masu ruwa da tsaki a bangaren fina-finan Bollywood ne ke kwarara gidan marigayiya Sridevi, wadda ta rasu a daren ranar Asabar a Dubai.

Jarumar, ta rasu ne sakamakon bugun zuciya tana da kimanin shekara 54 a duniya a lokacin da ta je Dubai domin halartar bikin daya daga cikin ‘yan uwansu.

Sridevi, ta je bikin ne tare da mijinta Boney Kapoor da kuma ‘yarta Khushi.

Marigayiyar ta fito a cikin fina-finai kusan 300, da suka hadar da na Hindi da Tamil da kuma na Telugu a cikin shekara 50 da ta shafe tana fim.

Ta fara fim ne tun tana karama, wato shekara hudu da haihuwa.

Ana dai ganin jarumar ta na daga cikin jarumai mata na India da suka samu nasara a sana’arsu ta fim, saboda irin nasarorin da ta samu.

Labarin rasuwarta ya tayar da hankulan mutane da dama, ba ma a kasar India kadai ba, har ma da sauran kasashen da ke kallon fina-finan India kamar Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
CITY TIMES INDIA

Image caption

Mutane sun hallara a kofar gidan jaruma Sridevi domin jiran isowar gawarta daga Dubai

A yanzu haka, mutane sun yi dafifi a kofar gidan jarumar da ke Mumbai, domin jiran isowar gawarta, wadda majiyoyi suka ce za a kawo ta a ranar Litinin daga Dubai, bayan kammala gwaje-gwajen da likitoci suka yi.

Jaruman Bollywood da dama sun hallara a gidan kanin mijin Sridevi, wato Anil Kapoor, inda suke lallashin babbar ‘yarta, Jhanvi Kapoor, wadda suka bari a gida.

Jarumai kamar Rekha da Karan Johar da Arjun Kapor wanda yayane ga ‘yar Sridevin da suka hada uba da Sonam Kapoor da Rani Mukherje da dai sauransu duk suna tare da ‘yar gidan marigayiyar.

Kazalika sauran jarumai kamar Priyanka Chopra da Shahruk Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Kajol da Akshay Kumar da Madhuri Dixit da Rishi Kapoor, daya daga cikin jarumai mazan da ta yi fina-finai da dama dashi da Jeetandra wanda ta fara fim din Hindi tare da shi da Amita Bachchan da Hema Malini da Kamal Hassan da Anupam Kher da Farhan Akhtar da Vivek Oberoi da dai sauransu duk sun wallafa alhininsu game da rasuwar jarumar a shafukan su na twitter.

A ranar Litinin ne dai ake sa ran isowar gawar jarumar gida India domin yi mata jana’iza.

Sridevi ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya biyu mata wato Jhanvi da Khushi Kapoor.

Hakki ne ya kama gwamnatin Buhari — PDP


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

PDP ta ce yakamata gwamnatin APC ta fito ta fayyace gaskiya game da sace ‘yan matan sakadiren Dapchi a jihar Yobe

A yayin da gwamnatin Najeriya, ta ce kawo yanzu ta samu adadin ‘yan matan da ake zargin kungiyar Boko Haram ta sace a makarantar ‘yan mata ta Dapchi da ke jihar Yobe da ya kai 110, jam’iyyar adawa ta PDP a kasar ta ce haki ne ya kama gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta yi kira ga gwamnatin shugaba Buharin da kada ta yi wasa da rayukan ‘yan kasar.

Sakataren jam’iyyar na kasa, Ibrahim Tsauri, ya shaida wa BBC cewa, a lokacin da aka kama ‘yan mata na farko, PDP ke mulki, kuma ba su musanta cewa ba a sace ‘yan matan ba, hasali ma sun bi duk matakan kubutar da ‘yan matan har suka bar mulki.

Ibrahim ya ce ” To yau gashi an sake kwatanta irin abinda ya faru a lokacin gwamnatinmu, kuma a lokacin gwamnatin da ta ce ba bu sauran Boko Haram, to mu abinda muka ce shi ne a gayawa mutane gaskiya”.

Sakataren jam’iyyar ta PDP, ya ce ba su gamsu da bayanan da gwamnati ke fada a kan satar ‘yan matan ba.

Ibrahim Tsauri, ya ce su sun dauki wannan al’amari da ya faru a Dapchi a matsayin kaddara, amma kuma ga dukkan alamu gwamnatin yanzu ta mayar da shi siyasa, shi yasa ma ba sa daukar shawara kowa sai ta ‘yan jam’iyyar su ta APC wadda kuma ta gaza.

Gwamnatin Najeriyar dai, ta fitar da wata sanarwa daga ofishin ministan yada labaran kasar, Lai Muhammad, inda ta ce ta samu alkaluman adadin ‘yan matan da aka sacen ne bayan tattaunawa da malaman makarantar ta Dapchi da kuma iyayen ‘yan matan.

Sanarwar ta kara da cewa, ministan yada labaran kasar, Lai Muhammad, ya ce gwamnati ta dukufa wajen ganin an ceto ‘yan matan 110, sannan ta sada su da iyayensu cikin koshin lafiya.

Ya kuma kara da cewa, jami’an tsaro na samun bayanai dangane da inda aka kai ‘yan matan kuma tuni sun fara bin sahu.

Za a iya cewa wannan dai shi ne karon farko da gwamnati ta fito ta amsa cewa an sace ‘yan matan makarantar ta Dapchi.

Domin da farko dai gwamnatin ba ta amince ba, amma daga bisani ta sanar da cewa an ceto yaran kuma za a sada su da iyayensu.

Sai dai kasa da sa’oi 24, sai labari ya sha bambam cewa yaran nan fa sun yi batan dabo al’amarin da ya dugunzuma iyayensu har ma rahotanni suka ce wasu iyayen sun samu hawan jini sakamakon labarin da ya fito daga bakin gwamnan jihar Yobe .

Nigeria: Makiyaya sun tashi dan mallakar katin zabe


Image caption

Fulanin sun ce an kwace musu abubuwan da suka gada tun lokacin turawan mulkin mallaka, kamar Burtali da filayen kiwo

Wasu fulani makiyaya a Najeriya, na korafin cewa babu wani abin kirkin da suke mora daga mulkin demokuradiyya a kasar, sai ma zargin da suke yi cewa ana kwace musu abin da suka gada tun zamanin Turawan mulkin mallaka, irin su burtali da filayen kiwo.

Wannan ta sa wasu kungiyoyin makiyaya da ke jihar Jigawa suka fara wani gangamin wayar da kan mutanensu a kan muhimmancin mallakar katin zabe da nufin amfani da shi wajen zabar shugabannin da za su kare muradansu a nan gaba.

Alhaji Ya’u Haruna Malam madori na daga cikin wadanda suka jagoranci gangamin, ya kuma shaidawa BBC cewa sun gaji da turawa ‘yan siyasa mota amma su na bada musu kura.

Dan haka yanzu sun umarci duk wanda shekarunsa suka kai yin zabe, mata da maza, har da tsaffi su je dan yin rijistar mallakar katin yin zabe.

Ya ce a yanzu ta kai kawai su ke yi, babau ruwansu da kabilar da mutum ya fito. Fatansu kawai wanda zai kare muradunsu da ciyar da al’umar fulani makiyaya gaba dan su ma su dandani romon dimukradiyya.

Fulanin dai na kokawa kan yadda idan asara ta afka musu ba bu wanda ya ke musu jaje bare kuma tallafi, amma da zarar ambaliyar ruwa ta afkawa takwarorinsu manoma ba a daukar lokaci ake tara musu tallafi ta kowacce fuska.

Dan haka su ma a yanzu, za su bude ido dan zaben shugaban da zai tabbatar da mafarkinsu na samun ingantacciyar rayuwa.

Ina mamakin kaina da yawan cin kwallo – Harry Kane


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Harry Kane ya ci kwallo 14 a wasan Premier 13 da ya yi a watan Fabrairu

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane ya ce ya ba wa kansa da kansa mamaki yadda cikin sauri a bana ya ci yawan kwallon da ya ci a bara, bayan da ya ci bal din da a kusan karshen tashi suka doke Crystal Palace, wadda ke cikin hadarin faduwa daga Premier, 1-0.

Kane ya zura kwallo a raga sau 35 a wasa 38 a kakar da ta wuce ta 2016-17, kuma a bana ya yi wannan bajinta a wasansa na 36 a ranar Lahadin nan, lokacin da ya ci West ham da ka a minti na 88.

Da farko ana ganin kamar Tottenham za ta kasa cin moriyar kankane wasan da ta yi da kashi 76 cikin dari, inda dan wasan na Ingila ya barar da damar da ya samu ta kurkusa a farkon dukkanin kashi biyu na wasan.

Kane mai shekara 24, ya ce shi ya san yana kan kwazonsa, wanda hakan ke ba shi kwarin guiwa a duk lokacin da za su shiga fili.

Dan wasan yanzu ya sake dawowa kan matsayinsa na wanda ya fi cin bal a gasar Premier, da bal ta 24 da ya ci a kakar nan, ya zarta Mohamed Salah na Liverpool.

Kungiyar ta kociya Mauricio Pochettino ita ce daya da har yanzu ba a doke ta ba a gasar Premier a wannan shekara ta 2018, ko da yake wannan ce kuma nasara ta uku a wasansu goma na baya bayan nan

Manchester City ta doke Arsenal 3-0 ta ci kofin Carabao


Hakkin mallakar hoto
Empics

Image caption

Shekarar Vincent Kompany wanda ya ci ta biyu, kusan goma a Manchester City

Manchester City ta ci kofinta na farko kakashin jagorancin Pep Guardiola, inda suka caskara Arsenal 3-0 a wasan karshe na kofin Carabao (EFL), wanda karo na uku ke nan da ya gagari Arsene Wenger, a filin wasa na Wembley.

Sergio Aguero ne ya fara daga ragar Arsenal minti 18 da fara wasa haka aka ci gaba da taka leda hai sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci kyaftin din City Vincent Kompany ya kara ta biyu a minti na 58.

Haka kuma bayan minti bakwai sai David Silva ya biyo baya da ci na uku da bal din da Danilo ya ba shi.

‘Yan Arsenal dai ba su taka wata rawar a-zo-a-gani ba a wasan in ban da wani hari da Pierre-Emerick Aubameyang ya kai tun ana farko-farkon wasan kafin a fara cinsu.

Wannan kofin na League shi ne har yanzu kofin Ingila wanda Arsene Wenger bai dauka ba a Arsenal, wanda wannan shi ne karo na uku da yake kuskurewa a wasan karshe a shekara 21 da yake jagorantar kungiyar.

Guardiola, wanda kungiyarsa Manchester City take jagorantar gasar Premier da tazarar maki 13, ya sake sanya robar hannun nan mai ruwan dorawa, ta alamar goyon bayan ‘yan awaren yankin Kataloniya na kasarsa Spaniya wadanda aka daure, abin da a baya ya jawo masa fushin hukumar kwallon kafa ta Ingila.

A kaka ta biyu da ya yi yanzu a City, ya ci kofin na League (EFL), wanda zai zama kari a kan kofuna 21 da ya ci a matsayin kociya a Barcelona da Bayern Munich.

Manchester United ta doke Chelsea 2-1


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jesse Lingard ya ci bal dinsa ta 13 a bana, bayan da ya shigo wasan daga baya

Manchester United ta sake koma wa matsayi na biyu a teburin Premier bayan da Jesse Lingard wanda ya shigo daga baya ya ci musu bal din da ta sa suka doke Chelsea 2-1 a Old Trafford.

Willian ne ya fara sa Chelsea a gaba tun kafin tafiya hutun rabin lokaci ana minti 32 da fara wasa, sai dai minti bakwai tsakani sai Romelu Lukaku ya rama wa United.

Wasa ya yi nisa ana minti 75 sai Lukakun wanda ya ci tsohuwar kungiyar tasa, ya aika wa Lingard wata bal daga bangaren dama, shi kuwa bai yi wata-wata ba , ya ci da ka, bayan nan ne kuma Alvaro Morata ya ci wa Chelsea bal din da za ta zama an yi 2-2, amma bisa kuskure aka haramta ta da cewa an yi satar gida.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wannan ne karon farko a wasa takwas da Lukalu ya ci tsohuwar kungiyar

Saboda wasa daya kawai da ta ci daga cikin hudu da suka wuce a gasar ta Premier hadi kuma da wasa goma da Tottenham ta yi ba tare da an doke ta ba, hakan ya sa Chelsea yanzu ta fice daga cikin kungiyoyi hudu da ke gaba-gaba, inda ta zama ta biyar, yayin da ya rage saura wasa goma a kammala gasar.

Chelsea za ta sake koma wa birnin na Manchester a lokacin da za ta fafata da a Etihad da Man City ranar Lahadi, 4 ga watan Maris da karfe 5:00 agogon Najeriya da Nijar.

Ita kuwa United sai washegarin ranar (Litinin 5 ga watan Maris) za ta je gidan Crystal Palace, Selhurst Park, inda za su fara taka leda da karfe 9:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.

Za a ‘haramta wa Samir Nasri buga kwallon wata shida’


Hakkin mallakar hoto
Twitter

Tsohon dan wasan Manchester City Samir Nasri na fuskantar haramcin buga kwalo tsawon wata shida da aka same shi da laifin yin karin ruwan da ya keta dokokin hukumar a wani asibitin Los Angeles a 2016, a cewar lauyansa.

An yi wa Nasri, mai shekara 30, karin ruwan ne a lokacin da yake hutu, sai dai hakan ya saba dokar hukumar hana shan abubuwan kara kuzari, lamarin da ya sa hukumar da ke Spain ta bincike shi.

Lauyan Nasri ya shaida wa BBC Sport cewa Uefa ce da kanta za ta yi masa wannan haramcin.

BBC Sport ta tuntubi Uefa domin jin karin bayani.

Rahotanni a Spain sun ce za a sanar da hukuncin da aka yanke wa dan wasan ranar Litinin.

Wani kamfani mai zaman kansa na likitoci mai suna Drip Doctors ya yi wa Nasri, wanda ba shi da kulob din da yake buga wa kwallo tun bayan barinsa Antalyaspor na kasar Turkiya a watan Janairu, karin ruwan a otal dinsa.

A wancan lokacin, Manchester City ta bai wa Sevilla aron dan wasan kuma hoton da ya dauka da daya daga cikin shugabannin kamfanin Jamila Sozahdah ya jawo ce-ce-ku-ce.

Xi Jinping ‘zai zama shugaban mutu-ka-raba’ a China


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Xi Jinping ya zama shugaban kasar China a 2013 kuma wa’adin mulkinsa zai kare a 2023

Jam’iyyar Kwaminisanci da ke mulkin China ta gabatar da shawarar cire wata sadara daga kundin tsarin mulkin kasar wacce ta iyakancewa shugaban kasa ya yi wa’adi biyu na shekara biyar-biyar a kan mulki.

Wannan yunkurin zai bai wa Xi Jinping damar ci gaba da zama a matsayin shugaban kasar har bayan lokacin da ya kamata ya sauka.

Ana rade-radin cewa Mr Xi zai nemi tsawaita mulkinsa bayan shekarar 2023.

Babban taron da jam’iyyar ta yi a shekarar da ta gabata ya tabbatar masa da mukamin Shugaba mafi karfin iko a kasar tun bayan mulkin Mao Zedong.

Kazalika an sanya manufofinsa a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma ba kamar yadda aka saba ba, ba a fadimutumin da zai gaje shi ba

Me aka sani game da wannan yunkuri?

“Kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminisanci ta China ya gabatar da shawarar cire wa’adin shugabanci karo biyu da aka sanya wa shugaban kasa da mataimakinsa a kundin tsarin mulkin kasa,” in ji wasu rahotanni.

Babu cikakken bayani kan dalilin bayar da wannan shawara, amma ana sa ran za a yi cikakken bayani nan gaba kadan.

An gabatar da wannan shawarar ce a daidai lokacin da jiga-jigan ‘yan kwamitin na tsakiya ke shirin yin taro ranar Litinin a Beijing.

Za a gabatar da shawarar ga ‘yan majalisar dokoki, wadanda za su yi taronsu na shekara-shekara ranar biyar ga watan Maris, domin amincewa da ita.

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya


Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da ‘yan Afirka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ba ko yaushe ne ake ganin giwa a rigingine kuma a sama ba – amma abin da ya faru kenan ranar Laraba a lardin Nyeri na kasar Kenya.

Canada Carpe Diem Circus performs at the French Institute on Febuary 15, 2018 during 1st Circus Festival in Abidjan in Ivory Coast.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A can birnin Abidjan da ke Ivory Coast, mutane ne ke tashi sama lokacin bikin Circus karon farko.

Mourners and supporters of the Movement for Democratic Change (MDC) party wave good bye to Zimbabwe's iconic opposition leader Morgan Tsvangirai who died last week after a battle with cancer, on February 20, 2018, during his burial at his rural village Humanikwa in Buhera.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A Zimbabwe, mutane ne suka taru domin yin alhinin mutuwar jagoran jam’iyyar Movement for Democratic Change (MDC) Morgan Tsvangirai, wanda ya mutu yana da shekara 65.

A newborn at the Juba Teaching Hospital in Juba, the South Sudanese capital's only fully functioning maternity ward which has five beds and only solar-powered electricityHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar ne kuma wata mata ta haifi sambacecen jaririnta a wani asibitin da ke Juba, babban birnin Sudan ta Kudu. Kasar na cikin kasashen da suka fi hatsari a rayu a cikinsu, in ji hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, Unicef, a wani sabon rahoto da ta fitar.

Two Ethiopian war veterans sporting military regalia walk down a path during a memorial service commemorating the anniversary of the 'Addis Ababa Massacre'Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A Habasha, tsofaffin sojoji sun yi alhinin tunawa da kisan kare-dangin da aka yi a Addis Ababa, inda sojojin mamaye na Italiya suka kashe akalla ‘yan kasar 20,000 ranar 19 ga watan Fabrairun 1937.

Libyans wave national flags as they attend a celebration marking the seventh anniversary of the Libyan revolution which toppled late leader and strongman Moamer Kadhafi, in the capital Tripoli's Martyrs Square on February 17, 2018.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Su ma ‘yan kasar Libya sun yi bikin tunawa da wata muhimmiyar rana a makon jiya. 17 ga watan Fabrairu ce ranar da aka cika shekara bakwai da tumbuke gwamnatin Kanar Muammar Gaddafi.

An election campaign banner erected by supporters of Egyptian President is seen in the capital Cairo on February 21, 2018.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A can Masar kuwa, shirye-shirye ake yi na gudanar da zabe. Magoya baya sun kafa kyallayen yakin neman zabe a birnin Alkahira, cikin har da na yakin neman zaben Shugaba mai-ci.

South Africa's newly-minted president Cyril Ramaphosa (centre) arrives to deliver his State of the National address at the Parliament in Cape Town, on February 16, 2018.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ba a yi zabe a Afirka ta Kudu ba, amma an nada sabon shugaban kasa. Wannan hoton Cyril Ramaphosa ne kafin ya yi jawabi ga ‘yan kasar. Za mu so sanin abin da wannan matar da ke kusa da shi ta hango.

Ghana"s skeleton slider Akwasi Frimpong exits after his race in the Men"s Skeleton competition at the Olympic Sliding Centre during the PyeongChang 2018 Olympic Games, South Korea, 16 February 2018Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A Korea ta Kudu, wannan dan kasar ta Ghana dan wasan Sululun tafi-da-ká, Akwasi Frimpong, ya shiga filin wasa dauke da ‘yarsa.

Athletes compete in the final of Men's 800m during the trials for the 2018 Commonwealth Games, at Kasarani Stadium in Nairobi, Kenya, on February 17, 2018Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A Kenya, an mayar da hankali ne kan gasar da ke tafe – wato gasar cin kofin kasashen kungiyar Commonwealthda za a yi a Australia a watan Afrilu.

Images courtesy of AFP and EPA

Ana bincike kan yadda kafafen sada zumunta da wayoyi ke yi wa matasa illa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shin ka damu da illar da shafukan sada zumunta na internet, da hasken fuskar wayar salula ke yi ga rayuwar matasa?

Idan haka ne, ga wata dama ta samu don kuwa ‘yan majalisu na gudanar da bincike kan hakan da lalubo hanyoyin magance su.

Kwamitin kimiyya da fasaha ya sanar da fara wani bincike kan hakan, musamman ta fuskar lafiyarsu.

Kwamitin ya bukaci jin ta bakin matasan da kansu, da malaman makarantu da kuma matasa ma’aikata.

Shugaban kwamitin Norman Lamb, ya ce ya na da muhimmanci a bincika don gano alfanu ko kuma illar hakan.

“Shafukan sada zumunta na zamani da wayoyin komai da ruwanka, sun zamewa matasa wani abu da dole su yi amfani da shi har ma da yara kanana,’ in ji shi.

Ya kara da cewa: “Mu na son sanin girman matsalar, da ware alfanu da akasin hakan don mu san ta inda za mu shawo kan matsalar kafin wankin hula ya kai mu dare.

Sannan mu san matakan da ya kamata mutane su fara dauka, don kare lafiyarsu, anan ina magana akan matasa da yara har da manya.”

“Za mu so jin ta bakin matasa, da ‘yan makaranta, da gwamnati kai har da ma’aikatun da sauransu,” in ji Mista Lamb.

Kwamitin dai zai mayar da hankali ne don jin cikakken bayanin yadda matasa suke ji idan su na yawan kallon hasken fuskar wayoyinsu, da abin da suke karauwa da su a shafukan.

Su ma malaman makaranta za mu so jin ta bakinsu, da kungiyoyin matasa wadanda su muke son hada karfi da karfe don magance illar da duniyar yanar gizo ka iya yi ga lafiyarsu.”

Cikin batutuwan da ‘yan majalisun za su amince da su sun hada da:

 • alfanun da shafukan sada zumunta ke yi ga wadanda ke amfani da su, ciki har da samar da wata manhaja da za ta kula da lafiyar masu amfani da shafukan.
 • illollin da wayar komai da ruwanka ke yi na zahiri da boye, ciki har da matakan da za a bi don kaucewa hakan da samar da wani abu da zai zama kamar tunatarwar lokacin dauke ido daga fuskar wayar ya yi.
 • karin matakan rage hasken fuskar waya, ciki har da bayyana illar kallon kurulla da ake yi wa fuskar wayar.
 • wadanne madannai, ko alamu za a sanyawa wayoyin da ke nuna illa ko akasin hakan.
 • a karshe wanne bangare ya kamata a fi maida hankali a kai a binciken da ake son yi da matakan kariya na dindindin, da kuma amfani da su.

Kwamitin zai bai wa mutane damar da aiko shawara ko korafi a rubuce, su na da damar yin rubutun da ya kai kalmomi 3,000 amma kar ya wuce hakan, daga yanzu zuwa 6 ga watan Afirilu.

Wani rahoto da hukumar ilimi ta wallafa a shekarar 2017, ya nuna kashi 95 cikin 100 na yara ‘yan shekara 15 a Birtaniya sai sun yi amfani da shafukan sada zumunta kafin su tafi makaranta ko bayan sun tashi daga makarantar.

Sannan kuma rabin yara ‘yan shekara 9 zuwa 16 na amfani da wayoyin komai da ruwanka a ko wacce rana.

A watan Janairun shekarar nan kwamishinar yara ta birnin London, Anne Longfield, ta yi gargadin cewa matakin da ake so a dauka na takaita amfani da wayoyin salula ko shafukan sada zumunta zai kawo nakasu ga ‘yan makarantar firamare da sakandare, saboda su na amfani da shafukan don amfanin kansu da kuma fadada ilimi.

Rahoton ya yi nazari kan illar shafukan sada zumunta na zamani kan wasu yara ‘yan shekara 9 zuwa 12, ya nuna yawancin yaran kan wallafa wani abu ne don su samu wadanda za su so shafukan na su da tsokaci kan wani rubutu da suka yi da kuma su ka wallafa a shafin.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Syria


Image caption

Yara kanana na tsananin bukatar taimako a yankunan da aka yi wa kawanya a Syria

Manyan kungiyoyin ‘yan a ware a Syria da ke iko da gabashin garin Ghouta sun amince da matakin tsagaita wuta da kwamitin tsaro na MDD ya jagoranta dan kai kayan agaji ga fararen hula a yankunan da suka kamale a kasar.

Kungiyoyin biyu sun yi alkawarin za su bai wa ayarin motocin agajin kariya, su kuma raka su har sai sun shiga yammacin birnin Damuscus.

Shugaban kungiyar likitocin Amurka a Syria Dr Ahmad Tarakji ya yi maraba da dakatar da bude wutar na wata guda.

Ya kara da cewa tuntuni ya kamata a dauki matakin ina ganin wannan mataki ne mai kyau, fararen hula da ke gabashin Ghouta sun damu matuka kan ko bangarorin za su bada hadin kai a dakatar da bude wutar.

A makon da ya gabata ne dakarun gwamnatin Syrian suka kaddamar da hare-hare a yankunan da ‘yan tawayen suke da ke gabashin Ghouta a kusa da birnin Damascus.

Bayan kada kuri’ar amincewar da aka yi a birnin New York, masu fafutuka sun ce an cigaba da kai hare-hare ta sama.

Tun ranar alhamis yakamata ace an kada kuri’ar, amma aka rinka jan kafa kafin a amince.

Rasha wadda babbar kawar Syria ce, na bukatar a samu sauye-sauye, yayinda Jami’an diflomasiyya dake wakiltar manyan kasashen duniya a majalisar dinkin duniya suka zargi Rashan da kawo tsaiko.

Rahotanni sun ce dakarun gwamnatin Syrian sun kashe mutane kusan 500 da ke yankunan da ‘yan tawayen suka mamaye a yayin hare-haren da suke kai wa ‘yan tawayen, yayinda su kuma ‘yan tawayen suka kashe fararen hula 16 a sakamakon bude wutar da suka yi a Damascus.

Ana dai son tsagaita wutar ne na tsawon wata guda domin bayar da damar kai kayan agaji ga mutanen da suka makale a yankunan da ‘yan tawayen su ke.

Nan gaba kadan ne dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za su tattauna akan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Kyautar aure ta hallaka ango a India


Image caption

Tsautsayi ya fada kan wasu ma’aurata a India

Wani ango tare da kakarsa sun rasa ransu bayan sun bude wani kunshin kyautar auren da aka ba su ya fashe wanda ake kyautata zatan bam ne aka rufe a ciki.

Wannan lamari dai ya faru ne a jihar Odisha da ke gabashin kasar India a ranar Jumma’ar da ta gabata.

‘Yan sanda sun ce amaryar ma ta samu munanan raunuka bayan fashewar kunshin kyautar.

Soumya Sekhar da Reema Sahu, sun yi aure ne a ranar 18 ga watan da muke ciki, kuma daga baya ne aka kawo musu kunshin kyautar wanda ke dauke da bam, kuma ba bu suna ko adireshin wanda ya aiko da sakon inji ‘yan sanda.

Yadda wani ango ya bata kwalliyar angwancinsa wajen ceto yaro

An kama wani ango saboda gayyatar baƙin bogi a bikinsa

Kafofin yada labarai na kasar sun rawaito cewa, ana bude kunshin kyautar ne sai kawai bam din ya tashi kuma a lokacin akwai amarya da ango da kuma ‘yan uwansu da dama a wajen.

Angon tare da kakarsa mai kimanin shekara 85 sun rasu a asibiti, yayin da amarya da wasu mutanen da ke wajen kuma yanzu ke kwance a asibiti suna karbar magani.

‘Yan sanda sun ce har yanzu ba a san dalilin da ya sa aka kai wannan kunshin kyauta ba, kuma ba a kai ga gano wanda ya aikata ba.

India: Uwa ta samu jikoki da miniyyin dan ta da ya mutu


Hakkin mallakar hoto
Sagar Kasar

Image caption

Rajashree Patil sits next to a photo of her son, Prathamesh who died of brain cancer.

Wannan dai abu ne da ba safai ake ganin an yi ba, matar mai shekara 49 ‘yar asalin kasar India, malamar makaranta ce da dan ta ya rasu ya na da shekara 27 bayan fama da cutar Kansa shekaru biyu da suka gabata.

Ta samu wata mace mai shekara 35, inda aka debi maniyyin dan na ta kafin a binne shi aka dasawa a mahaifar matar. Kuma Allah cikin ikonsa matar ta haifi ‘yan biyu, aka radawa daya daga ciki sunan mahaifinsa.

Ta ce ta dauki matakin ne dan kar a manta da dan na ta baki daya, saboda ya rasu ko auren fari bai yi ba.

Bayan kammala digiri kan aikin injiniya a jami’ar Pune da ke kasar, matashi Prathamesh ya wuce kasar Jamus dan yin digiri na biyu a hekarar 2010.

Hakkin mallakar hoto
Sagar Kasar

Image caption

A shekarar 2013 aka gano Prathamesh ya na dauke da cutar Kansar kwakwalwa, ya kuma mutu bayn shekara 3

A shekarar 2013, aka gano ya na fama da cutar Kansar kwakwalwa, kuma bayan shekara uku ya rasu. Ga bannin mutuwarsa ne aka samu diban maniyyinsa aka adana a sibiti daga bisani aka dasa a mahaifar wata mace ta kuma haifi ‘yan biyu.

A lokacin da aka haifi ‘yan biyun, mahaifiyarsa ta yi farin ciki inda ta kara da cewa ”Prathamesh di na ya sake dawowa,” inji ta.

Ta kara da cewa ” Na yi matukar shakuwa da Da na. Yaro ne mai kaifin basira, tun da ya shiga makaranta na ke alfahari da shi.

Ya na karatun digiri na biyu ne ya kamu da wannan cuta a kasar Jamus, dan haka na dauki matakin gaggawa na adana maniyyinsa da nufin na samu jikokin da za su dinga tuna min da shi.”

Tun da fari daman likitoci sun bada shawarar ayi gaggawar dibar maniyyin matashin, kafin a fara masa maganin cutar Kansar.

Gabannin mutuwar Prathamesh, ya amince mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa mai suna Dnyanashree, su debi maniyyin sa dan amfani da shi ga wata macen.

Hakkin mallakar hoto
Sagar Kasar

Image caption

‘Yan biyun da aka haifa bayan mutuwar Prathamesh , inda aka sanyawa macen suna suna Preesha namijin kuma ya ci sunan mahaifinsa Prathamesh

A lokacin da Rajashree ta dauki matakin, ta na ganin kamar ba zai yiwu ba.

Shekaru biyu bayan mutuwar dan na ta, Rajashree ta ki yadda ta yi kukan mutuwarsa, saboda ta na ganin ‘ya’yansa da suke tuna ma ta da shi. A ranar 12 ga watan Fabrairu 2018 aka haifi tagwayen masu cike da tarihi.

Hakkin mallakar hoto
Sagar Kasar

Image caption

Dakta Supriya Puranik, da ta jagoranci aikin ta ce abu da ba a saba gani an yi ba

Bayan ta yanke shawarar yin dashen, suka daidaita da asibitin Jamus din. Suka aike da maniyyin dan na ta, babban asibitin Sahyadri da ke Pune wadanda suka jagoranci aikin.

Dakta Supriya Puranik, kwararriyar likita ce a asibitin ta ce ba ta taba ganin irin wannan kauna da ke tsakanin Uwa da Danta ba. Ta nuna farin ciki da suka yi nasara aikin, kuma uwar Dan na cike da farin ciki.

Jarumar fina-finan India Sridevi ta rasu


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Sridevi na daga cikin jaruman fina-finan kasar India mata da suka yi fice

Fitacciyar jarumar fina-finan Bollywood Sridevi Kapoor, ta rasu a daren ranar Asabar a Dubai sakamakon bugun zuciya.

Kanin mijin jarumar, wato Sanjay Kapoor, shi ne ya tabbatar wa da manema labarai na India labarin mutuwar ta , inda ya ce ta mutu ne Dubai, bayan sun je biki tare da mijinta Boney Kapoor da kuma ‘yar ta Khushi.

An dai haifi Sridevi ne a ranar 13 ga watan Augustan shekarar 1963 a Tamil Nadu.

Sridevi ta fara fitowa a fina-finan Tamil ne tun tana karama wato tana da shekara hudu a duniya , amma a shekarar 1975 ne ta fito a fim da girmanta wato fim din Julie, daga nan ne ta ci gaba da fitowa a fina-finai amma na Tamil.

Fim din ta na farko da ta yi wato na Hindi shi ne fim din Solva Sawan wanda aka yi shi a shekarar 1979.

Jarumin fina-finan India Shashi Kapoor, ya mutu

Vinod Khanna ya rasu bayan gajeruwar jinya

Shekara hudu bayan nan kuma sai aka hadata fim da Jeetandra wato fim din Himmatwala wanda kuma ya yi matukar fice a shekarar da aka sake shi wato 1983.

Daga nan ne fa Sridevi ta koma fitowa a fina-finan Hindi.

Tayi fina-finai fiye da 150 ciki har da wadanda da suka yi fice kamar, Mawali da Sadma da Mr India da Chandni da Nagina da Chalbaaz da Janbaaz da English Vinglish da Chandra Mukhi da kuma fim din ta na karshe da ya fita bara wato Mom.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sridevi da mijinta Boney Kapoor da ‘ya’yanta Jhanvi da Khushi Kapoor

Ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya mata biyu wato Jhanvi da Khushi Kapoor.

Sridevi ta bayar da muhimmiyar gudunmuwa a fina-finan Bollywood.

Ta karbi lambobin yabo da dama bisa rawar da ta taka a fina-finan.

Tana daga cikin jarumai mata da suke da kyau sosai, da kuma iya rawa.

Ta fara auren jarumi Mithun Jakraborty ba su haihu ba, daga baya kuma ta auri mai shirya fim da bayar da umarni Boney Kapoor, inda suka haifi ‘ya’ya biyu mata Jhanvi da Khushi Kapoor.

Tuni jarumai irinsu Priyanka Chopra da Reteish Deshmukh da Sharukh Khan da sauransu suka wallafa alhininsu bisa rasuwar jarumar a shafukan sada zumunta.

An fitar da sunayen dalibai 105 da aka sace a Dapchi


Hakkin mallakar hoto
GGSS

Image caption

Daliban Makarantar Sakandiren mata dake Dapchi

A Najeriya, kwana biyar bayan ‘yan bindiga da ake zargi ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kan wata makarantar mata a garin Dapchi na jihar Yobe, an fitar da sunaye dari da biyar da aka ce na dalibai mata da ba a gani bane sakamakon harin.

A ranar Juma’a ne gwamnatin jihar Yobe ta ce adadin daliban da ba a gani ba, tamanin da hudu ne.

Mako guda kenan da ake ci gaba da samun bayanai da suka sha banban, da kuma rudani daga hukumomi, dangane da adadin dalibai mata da aka yi gaba da su daga makarantarsu a Dapchi.

A karon farko, iyayen ‘yan matan sun fitar da jerin sunayen ‘ya’yansu da har yanzu ba a gani ba.

Sunaye dari da biyar ne iyayen ‘yan matan suka fitar.

Tun da farko dai, gwamnatin jihar ta ce daliban hamsin da daya ne ba a gani ba, sannan daga baya ta ce adadin daliban da ba a gani din ba tamanin da hudu ne.

An ce ‘yan matan sun gudu ne zuwa cikin daji a lokacin da aka kai wa makarantar ta su hari.

Sai dai da yawa daga cikin ‘yan matan ba su koma gida ba, abin da yasa iyayensu suka shiga fargabar ko an sace su ne.

A ranar Juma’a, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace ‘yan matan a matsayin wani bala’i da ya samu kasar, sannan ya ce sojoji suna yin komai domin gano ‘yan matan.

Halin da ake ciki a Dapchi, ya sa sace dalibai mata 276 da ‘yan bindiga suka yi a 2014, dawowa zukatan mutane.

Bama-bamai sun kashe mutane a kusa da fadar shugaban Somali


Hakkin mallakar hoto
Universal TV / Reuters

Jami’ai sun ce hari biyu na bama-bamai da aka kai a Mogadishu, babban birnin Somalia sun yi sanadin mutuwar akalla mutum 38.

Hari na farko ya faru ne a kusa da fadar shugaban kasar ranar Juma’a. Na biyu kuma ya faru ne a wani otal da ke kusa da fadar. Mutane da dama ne suka jikkata.

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta al-Shabab, wadda ta sha alwashin kawar da gwamnatin kasar, ta ce ita ta kai hare-haren.

An yi ta gumurzu da bindigogi bayan harin da aka kai kusa da fadar shugaban kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar masu tayar da kayar baya biyar, in ji jami’ai.

Hare-haren su ne na baya bayan nan da ake dangantawa da kungiyar al-Shabab, wacce ta taba karbe iko da birnin na Mogadishu kafin a kore ta a shekarar 2011 da taimakon dakarun kungiyar tarayyar Afirka.

A watan Oktoban da ya gataba, an kashe sama da mutum 500 bayan wani hari da aka kai da motar daukar kaya a birnin. Jami’ai sun dora alhakin kai harin kan al-Shabab sai dai kungiyar

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An kai mutanen da suka jikkata asibiti

Daya daga cikin hare-haren da aka kai ranar Juma’a ya faru ne bayan wata mota ta ki tsaya a wurin binciken ababen hawa da ke wajen fadar shugaban kasar inda aka tayar da bama-baman da ke cikinta, a cewar kafafen watsa labaran kasar.

Daga nan ne aka soma musayar bude wuta tsakanin masu tayar da kayar bayan da jami’an tsaro.

Daga bisani kuma wata mota da ke ajiye kusa da otal din ta tashi bayan bama-baman da ke cikinta sun tarwatse.

Sai dai al-Shabab ta ce ta hari jami’an tsaro ne.

Ta kara da cewa biyar daga cikin mayakanta, ciki har da direbobi biyu, sun yi shahada sanna ta kashe sojoji 35.

A police spokesman told Reuters news agency: “There were many military soldiers who guarded the street adjacent to the palace.”

An kashe wasu mahara a cocin Afirka ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kama mutum goma da ake zargi da hannu a harin sannan wasu kuma sun tsere.

Jami’ai a Afirka ta Kudu sun ce ‘yan sandan kasar sun harbe har lahira mahara bakwai a ba-ta-kashin da suka yi a wani cocin da ke Eastern Cape.

Sun ce maharan da aka kashe sun buya ne a cikin cocin bayan sun kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda biyar da wani soja.

An kama mutum goma da ake zargi da hannu a harin sannan wasu kuma sun tsere.

Hukumomi sun ce har yanzu ba a san dalilin da ya sa maharan suka kai farmakin ba, ko da yake sun saci makamai a lokacin da suka kai harin.

Ana kashe jami’an tsaro da dama a duk shekara a Afirka ta Kudu, sai dai harin da aka kairanar ta Laraba ya janyo tofin Alla-tsine kuma shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya yi kira da a kama maharan sannan a yi bayani kan batun.

Buhari ‘yana yi wa ‘yan Nigeria romon-baka’


Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Buhari ‘yana yi wa ‘yan Nigeria romon-baka’

Wani fitaccen dan siyasar Jamhuriya ta biyu a Najeriya, Dr Junaidu Muhammad ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana yi wa ‘yan kasar romon-baka a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Dr Muhammad ya shaida wa BBC cewa shugaban kasar da manyan hafsoshin rundunar sojin sun sha yi wa ‘yan kasar karya kan hakikanin halin da ake ciki a yakin, shi ya sa bai yi mamakin sace ‘yan makarantar sakandare ta Dapchi da ke jihar Yobe ba.

“Satar yaran da aka yi ta ba da tabbataccen yakinin cewa babu tsaro a kasar nan; ya nuna cewa abubuwan da ke fitowa daga shugaban kasa da fadarsa romon-baka ne, ba gaskiya ba,” in ji dan siyasar.

Dan siyasar ya kara da cewa ce nade-naden da Shugaba Buhari ya yi a rundunonin sojin kasar ya yi su ne bisa son rai ba cancanta ba.

A cewarsa, mafita ga halin da kasar ke ciki ita ce Shugaban kasa ya sallami dukkan hafsan hafsoshin tsaron kasar “idan ba haka ba babu abin da zai sauya.”

Adikon Zamani: Mene ne yake hana matan karkara zuwa awon ciki?


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Mene ne yake hana matan karkara zuwa awon ciki?

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:

Yin awo ga mata masu juna biyu abu ne mai matukar muhimmanci, inda ake duba lafiyarsu da ta jariran da ke cikinsu kafin haihuwa.

A ka’ida kamata ya yi a ce mace ta fara zuwa asibiti don yin awo da zarar ta fahimci tana da juna biyu, don sanin yadda za ta kula da kanta da jaririnta.

Haka kuma a lokacin da take zuwa awon ciki za ta yi wasu alluran rigakafi, da sanin yadda za ta shiryawa haihuwa, da irin yadda za ta samu taimako kan laulayin ciki.

Sai dai abun takaicin shi ne a arewacin Najeriya akwai matsloli da dama da suka baibaye batun zuwa awon ciki da haihuwa a yawancin asibitoci.

Wadannan matsaloli su suke haifar da sanadin da ke sa ana yawan samun mace-macen mata masu ciki yayin haihuwa da ma jariransu.

A wasu wuraren sam mata ba sa son zuwa asibiti don duba lafiyarsu a yayin da suke da juna biyu, sun gwammace su sha jike-jike da wasu saiwoyi na gargajiya a matsayin abun da zai taimakawa lafiyarsu da ta jariran.

Sai dai matsalar ita ce, duk mai juna biyun da ba ta zuwa asibiti don yin gwaji, to tamkar makaho ne da ke tsallaka titi ba dan jagora. Wannan abu da suke yi kasada ce kuma hadari ne ga lafiyarsu.

Kwararru a fannin lafiya sun sha nanata cewa idan har mace na son haihuwa lafiya kalau ba tare da tangarda ba, to hakika tana bukatar ta dinga zuwa asibiti domin a duba lafiyarta da ta jaririn.

Kuma a asibitin ne za a gane yanayin da jaririn yake ciki a ciki, da lafiyar ita kanta uwar, sannan ana iya gane ko za ta ci karo da wata tangarda kafin lokacin haihuwa ya zo, wanda hakan zai sa a shirya duk wani taimako da za ta bukata a ranar haihuwar.

A wannan makon shirin Adikon Zamani ya bi diddigin dalilin da ya sa mata ba sa son zuwa awon ciki musamman a yankunan karkara, inda muka ganewa idonmu matsaloli daban-daban da mata ke ciki dangane da rashin zuwa awo da kuma wadanda suke cin karo da su a lokacin haihuwa.

Ta yiwu a tsagaita wuta a garin Ghouta na Syria


Image caption

Kananan yara ne suka fi shan wahala a yakin da ake a Syria

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a dan dakatar da bude wuta a garin Ghouta na Syria, dan kai agaji ga dubban fararen hula da ke tsananin bukatar taimako.

Kasar Rasha dai na bukatar a samu sauyi a daftarin da ya yi kiran da a samu tsagaita wuta a Syria, domin bayar da damar kai kayan agaji da kuma taimakawa marassa lafiya.

Jami’an diplomasiyya na kasashe waje sun zargi Rasha da, babbar kawar Syria da kawo tsaiko, yayinda kasar Fransa ta ce duk wani yunkuri na bata lokaci zai iya kawo karshen majalisar dinkin duniyar ita kanta.

Hankulan kasashe da dama ya koma kan irin halin matsin da fararen hula ke ciki a gabashin Ghouta, matattarar ‘yan tawaye..A jiya Jumma’a jiragen yaki sun kai hare-hare a wurare da dama ciki har da yankunan Hamouriyeh da Douma.

Kasashen yamma dai na zargin Rasha da son a bawa Syria lokaci ta kaddamar da hare-hare a wuraren da yan tawayen suka mamaye da ke Damascus da ma wajen birnin.Amurka da Birtaniya da Fransa sun yi kira da a amince da matakin tsagaita wutar domin kai kayan agajin ba tare da bata lokaci ba.

A jiya jumma’a ne shugaba Trump na Amurka ya dora alhakin matsalar kai kayan gajin da ake fama da ita a Syria akan Rasha da Iran.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for human rights ta ce adadin wadanda aka kashe tun daga ranar Lahadin data gabata kawo yanzu ya kai 462, ciki har da yara 99.Yanzu haka dai akwai mutane kusan dubu 393 da suka makale a yankunan da dakarun gwamnatin Syria ke kaddamar da hare-hare kan ‘yan tawaye.

Tuni dai gwamnatin Syria ta musanta cewa tana kai wa fararen hula hari, inda ta hakikance cewa tana so ta kawar da ‘yan ta’addan da ke zaune gabashin Ghouta ne shi ya sa ta ke kai hare-haren.Hukumomin agaji dai sun ce akwai asibitoci da dama a yankin da tun ranar Lahadin da ta wuce ba a aiki a ciki saboda hare-haren da ake kai wa.

Amurka za ta bude ofishinta na Kudus a watan Mayu


Image caption

A watan Disambar bara ne aka kafa tutar Amurka da Israila a birnin Kudus

Ma’aikatar cikin gida a Amurka ta sanar da cewa a watan Mayu mai zuwa ne za ta bude ofishin diflomasiyyarta a birnin Kudus.

Ranar bude ofishin za ta zo daidai da ranar bikin tunawa da kfa kasar Israela shekara 70 da ta wuce kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin kura ta dan lafa, kan takaddamar da ake yi na maida ofishin jakadancin Amurkar birnin Kudus.

Shugaba Donald Trum ya sha alwashin tabbatar da hakan, ko da yake kasashe da dama ciki har da na tarayyar turai sun nuna rahin amincewa.

Wani babban jami’in gwamnatin Falasdinu, Sa’eb Erekat, ya kira matakin na tsokanar fada.

Shugaba Benjamin Netanyahu ya yi murna da sanarwar bude ofishin Diflomasiyyar, ya kara da cewa wannan rana ce mai matukar muhimmanci a tarihin Isra’ilawa.

A shekarar da ta gabata ne dai shugaba Donald Trump ya sanar da maida ofishin jakancin Amurka birnin Kudus, maimakon Tel Aviv.

A yanzu kuma sabon ofishin zai kasance ne a gundumar Arnona da ke tsakiyar Kudus.

‘Sayyadina Umar ya taba aika sako Daular Borno’


Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku a kan tarihin daular Borno. BBc ta dauki lokaci don samo amsar tambayoyin naku daga wajen masana tarihi na Daular Borno.

Hakkin mallakar hoto
Zanna Hassan Boguma

Image caption

Shehun Borno na yanzu Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi

Daular Borno tsohuwar Daula ce a Afirka da aka kafa tun kafin karni na 10 wacce ta hada da yankunan da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Sudan har Libya.

Daular Kanem ta El Kanemi ta samo asali ne daga daular Saifuwa.

Masana tarihi sun ce mutanen Saifuwa daga Yemen ne suka fara kafa daular musulunci a Borno, tsawon shekaru 1000 da suka gabata.

Muhammad al-Amin ElKanemi ya kafa Daular Kanem ne a karni karni na 18, bayan kawar da daular Saifuwa wadanda sarakunanta suka yi mulki shekaru da dama.

BBC Hausa ta duba tarihin Daular Borno ta hanyar tattaunawa da Masana tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma daraktan da ke kula da al’amuran masarautu a Borno, da Farfesa Adam Muhammad Ajiri na sashen nazarin addinin Islama a Jami’ar Maiduguri, wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.

Asalin kalmar Borno – Tambaya ce da muka samu daga Umar Abubakar da Sani Garba da Ishaq Abubakar Kazaure.

Rubuce-rubucen masana tarihi sun nuna cewa Kalmar Borno ta samo asali ne daga kalmomin Larabci, “Bahar Nur” wato ma’ana kogin haske.

Kuma saboda kasancewar Borno gidan Al Qur’ani gidan Musulunci ne dalilin ke nan da ya sa sarakunan farko suke kiranta “Bahar Nur”, ma’ana kogin haske na musulunci.

Masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce Ibn khaldun ya ambaci “Bahar Nur” a rubuce-rubucensa na tarihin musulunci a Afirka.

Image caption

Daular Borno ta kafu sama da shekaru 1000

Tushen Borno – Wannan Tambaya ce da muka samu daga Umar Musa Dambam daga Bauchi a Najeriya da Buhari Yusuf da Abdulmumin Adamu da Ahmad Adamu Tamadina da Shu’aibu Idris Kofar fada Balangu a jihar Jigawa da Garba Saleh.

Tarihi ya nuna cewa Kanuri da suka kafa Borno daga Yemen suka fito, wato tsatson wani sarki da aka yi a Yemen Said Ibn Dhi Yazan da ake kira Malik al-Himyari tun kafin zamanin Annabi SAW, wanda ya kafa dauloli a India da Fasha.

Tarihi ya nuna mutanen Ibn Dhi Yazan suna cikin wadanda suka amince su ba sahabban Annabi SAW mafaka bayan hijirarsa daga Makkah zuwa Madinah.

Yemen ne asalin Kanurin da suka kafa mulki a Borno daga daular Saifuwa’ a cewar Zanna Hassan Boguma.

Hakkin mallakar hoto
Zanna Boguma/Borno Emirate

Image caption

Shehu Umar Kura Ibn Shehu Muhammad Al-Amin Elkanemi sarki na biyu a Daular Elkanemi

Borno a zamanin Sahabbai – Tambaya ce da muka samu daga Jamilu Bagaraje da Magaji Rabiu da Abubakar Umar Usman da Nasir Abubakar Jaja.

Daular Borno ta yi zamani da Sahabbai, kuma masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce daular ta kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW.

A cewarsa tarihi ya nuna sarakunan Borno sun aika da wasika suna neman malamai da za su koyar da addini zuwa ga Amr al-As gwamnan Misra, wanda shi kuma ya tura Uqba Ibn Nafi.

“Sarakunan Borno sun karbi malamai daga wajen Ibn Nafi a zamanin Sayyadina Umar RA”.

Amma Zanna Hassan Boguma ya ce wasu litattafan tarihi sun nuna cewa a zamanin Sayyadina Usman RA ne.

Sai dai Farfesa Adam Muhammad Ajiri ya ce Gwamnan daular Maghribi a arewacin Afirka Uqba Ibn Nafi yakinsa har ya kawo Borno a shekarar 666, kuma zamanin Khulafa’ur Rashidun ya fara ne daga 632 har zuwa 660.

Ya ce ba za a iya cewa sun yi zamani da sahabbai ba, amma ana ganin watakila a lokacin akwai daular musulunci a Borno, ko da yake an fi tabbatarwa a zamanin Umayyad daga 661 zuwa 750.

“A lokacin akwai binciken da ya nuna daga shekarar 661 zuwa 670 akwai malamai daga daular Umayyad da suka shigo yankin Maghrib har suka iso Borno,” in ji Farfesa Ajiri.

Image caption

Taswirar yankunan Tsohuwar Daular Borno

Saifuwa a Borno da kafuwar ElKanemi – Tambaya ce da muka samu daga Abdurahman Salisu Zaria da Abubakar Goni Kolo da Hassan Yarima K/Huguma da Baba Ali Kabir

Saifawa su ne asalin sarautar Borno, kuma Zanna Boguma ya ce dalilin da ya sa ake kiransu Saifuwa saboda sun fito ne daga Said Ibn Dhi Yazan.

Tarihi ya nuna Saifuwa sun yi sarauta sama da shekara 1000 inda suka yi sarakuna kimanin 113, tun kafin karni na bakwai.

Farfesa Ajiri ya ce bayan Saifuwa sun ci Zaghawa da yaki ne suka kafa daular musulunci a Borno, kuma sun kafa daula ne daga wajajen karni na shida.

Sarakunan farko a daular Saifuwa sun hada da Mai Dugu a shekarar 785 da Mai Fune a shekarar 835 da Mai Aritso a 893, da Mai Katuri a 942 da Mai Ayoma a 961 da Mai Bulu a 1019 da Mai Arki a 1035 da Mai Shu a 1077.

Hakkin mallakar hoto
Zanna Hassan Boguma/Borno Emirate

Image caption

Fadar Shehu Umar Sanda Kyarimi da Majalisarsa a Dikwa

“Tun zamanin Sarkin Saifuwa Mai Hume Djilme a wajajen 1080 aka fara daula ta musulunci har zuwa sauran sarakunan da aka yi”, a cewar Zanna Boguma.

Ya ce, a zamanin daular musulunci ta Saifuwa an yi Sarakuna da suka hada da Mai Dunama Humemi da ya yi mulki daga shekarar 1098 zuwa 1150 da Mai Biri Ibn Dunoma da ya yi mulki daga shekarar 1150 zuwa 1176 da Mai Bikoru Ibn Biri Dunomami da ya yi zamani daga 1176 zuwa 1193.

Mai Ahmad ne Sarkin Saifuwa na karshe, kafin zamanin daular ElKanemi.

Farfesa Ajiri ya ce karshen mulkin Saifuwa ya zo karshe ne a lokacin da Fulani suka kawo hari suka ci garin Gazargamu da yaki tsohon babban birnin Daular Borno.

Goni Mukhtar ne ya yaki Gazargamu, inda ya kori Mai na Saifuwa tare da taimakon Shehu El Kanemi.

ElKanemi ne ya taimaka aka kori Fulani daga Borno.

Farfesa Ajiri ya ce bayan an kashe Goni Muktar a Damaturu ne kuma Mai Ahmad na Saifuwa ya rasu, daga nan El Kanemi ya zama Sarki a wajajen 1810 zuwa 1814.

ElKanemi ya ci gaba da mulki a daular Saifuwa duk da cewa shi ba daga zuriyar Saifuwa ba ne.

Farfesa ya ce ElKanemi ya kafa daular ElKanemi 1814 a birnin Kukawa, wato shekaru sama da 200 a yanzu.

Hakkin mallakar hoto
Zanna Hassan Boguma

Image caption

1809- Kasuwar Kukawa a tsohuwar Borno

“Idan an hada shekaru kusan 800 na Daular Saifuwa da shekaru sama da 200 zai kasance shekarun daular Borno sama da 1000”.

Shehu Mohammed el Amin Elkanemi ya fara kafa daula ne a Ngurno tare da ba Mai Dunoma na Tara Lefami matsayin sarki a Kanem daga daular Saifuwa daga 1814 zuwa 1817.

Mai Ibrahim na hudu Ibn Dunoma Lefami ne ya gaji Dunoma a matsayin Sarkin Saifuwa a Kanem.

Bayan El Kanemi ya karbi mulki ne sarautar Borno ta sauya daga Saifuwa zuwa Shehu ElKanemi.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce lakabin sarautar Borno ya sauya daga “Mai” ma’ana “Sarki” zuwa “Shehu” bayan kafuwar ElKanemi, sabanin sarakunan farko.

“Bayan ElKanemi ya samu mulkin Borno, daga nan ne ya ce shi ba zai amince a kira shi da “Mai” ba saboda shi malami ne”.

“Don haka ya ce zai kira kansa a matsayin Shehu, wato Malami, inda ya hada mulki da malamanta”, a cewar Zanna Boguma.

Ya kuma ce: “Wannan ne dalilin da ya sa duk wadanda suka zama sarakuna a Borno ake kiransu Shehu daga gidan El Kanemi.”

Shehu Umar Kura ne ya gaji mahaifinsa Shehu Muhammad El Amin ElKanemi a matsayin Sarkin Borno daga 1835 zuwa 1853.

Hakkin mallakar hoto
Zanna Hassan Boguma/Borno Emirate

Image caption

Shehu Abubakar Garbai Ibn Shehu Ibrahim Elkanemi Kakan Shehun Borno na yanzu Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi

Sarakunan El Kanemi – Tambaya ce da muka samu daga Naziri Aliyu Abubakar da Hussaini Aminu da Mohammed Mala Ngarannam da Abdullahi Bala da Shafi’u Idris Umar da muhammad Ali.

Kamar yadda bayanai suka gabata an yi shekaru da dama da kafuwar Daular Borno kafin zuwan ElKanemi. Sarakunan Borno zamanin daular Elkanemi kafin Rabeh ya ci Borno da yaki sun hada da:

 • Shehu Mohammed Al-Amin Elkanemi 1814- 1846
 • Shehu Umar Kura Umar (1835 – 1853) Dan Shehu Mohammed Elkanemi
 • Shehu Abdul Rahman Ibn Muhammad Elkanemi – 1853 – 1854
 • Shehu Umar Kura Ibn Muhammad Elkanemi- 1854 – 1880
 • Shehu Bukar Zarami Kura Ibn Umar – 1880 – 1884
 • Shehu Ibrahim Ibn Umar – 1884 – 1885
 • Shehu Hashimi Ibn Umar – 1885 – 1893
 • Shehu Kyari Ibn Bukar Zarami – 1893-1894
 • Shehu Sanda Limananbe Wuduroma Ibn Bukar Zarami – 1894

Shehu Umar Kura na cikin Sarakunan Borno da suka fi dadewa a mulki.

Sai Shehu Sanda Kyari wanda ya shafe shekara kusan 40 yana mulki.

Shehu Mustapha Umar El Kanemi shi ma sarki ne da ya dade inda ya yi shekara 34 yana mulki.

Shehu Garbai kakan Shehu na yanzu ma ya dade inda ya yi shekara 24 yana mulki.

Hakkin mallakar hoto
Zanna Bugoma/Borno Emirate

Image caption

Daular Borno ta yi zama a karkashin turawan Birtaniya da Jamus

Wanene Rabeh? Tambaya ce da muka samu daga Sani Ali da Nura Bala da ahmad Adam Bagas Minna da Adam Musa Ladan Fulata.

Rabeh Zubair Ibn Fadlallah mutum ne da ya taso daga Sudan, wanda ke sana’ar fataucin bayi, inda yake saye ya kuma sayar da bayi.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce fataucin bayi ne dalilin da ya sa Rabeh ya yaki Borno .

A 1893 ne Rabeh ya kawo wa Borno hari.

“Rabeh Zubair Ibn Fadlallah ne ya rushe tsohuwar daular Borno bayan ya kaddamar da yaki kuma ya samu galabar kwace iko ya mayar da Dikwa a matsayin babban birnin daularsa”.

Rabeh ya kashe sarakunan Borno guda biyu, Shehu Kyarimi da Shehu Sanda Wudoroma.

A 1900 sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kashe Rabeh bayan ya yi mulki a shekaru bakwai da watanni bakwai da kwanaki bakwai a Borno.

Bayan sun kashe Rabeh ne suka aza Shehu Sanda Kura daga zuriyar Elkanemi a matsayin Shehun Borno a Dikwa a 1900.

A 1901 suka tube shi suka kuma daura dan uwansa Umar Abubakar Garbai, kakan Shehun Borno na yanzu.

Hakkin mallakar hoto
BBC/Zanna Hassan Boguma

Image caption

Sarakunan Borno bayan kashe Rabeh

Lokacin Turawan mulkin Mallaka, tsohuwar Masarautar Borno ta rabu gida biyu inda Dikwa ta koma karkashin ikon turawan mulkin mallaka na Jamus, bisa wata yarjejeniya tsakanin turawan Faransa da Birtaniya da kuma Jamus na mulkin mallaka.

Daga baya Abubakar Garbai ya koma Sarkin Borno a yankin da turawan Birtaniya ke iko.

A shekarar 1902 ya fara yin hijira zuwa Monguno kafin daga baya ya koma Maiduguri.

Lokacin da Dikwa ta koma karkashin ikon Birtaniya, an samu Shehu guda biyu, Shehun Borno a Maiduguri da kuma Shehun Dikwa.

Hakkin mallakar hoto
Hassan Zanna Bugoma

Image caption

Shehu Umar Ibn Abubakar Garbai Elkanemi mahaifin Shehun Borno na yanzu.

Tsarin sarautar Borno. Wannan tambaya ce da muka samu daga Aminudden Ali Dan Hassan.

An kafa masarautar Borno da al’adunta ne a kan tsari na musulunci.

Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce a zamanin farko na El Kanemi an bi tsari ne irin na khalifancin Manzo SAW.

Ya ce El Kanemi yana da mashawarta guda hudu wadanda kuma suka kasance kamar majalisar Koli.

“Mutanen sun hada da Malam Muhammed Terab da Malam Ahmad Gonimi da Ibrahim Wadaima da Aji Sudani wadanda suka taimaka masa wajen shinfida tsari na shari’a da adalci a Borno”.

Amma ya ce bisa tsari na al’ada Borno tana da tsarin sarautu 3,333, wadanda suka kunshi na ‘ya’yan gidan sarki da fadawa da bayi da na Malamai.

Sannan akwai sarautu na sana’o’i kamar na wanzanci da kira da rini.

Amma sarautun da suke da girma da kima sun kai 313.

Yadda ake zaben Sarki a Borno – Tambaya ce da muka samu daga Aminudden Ali Dan Hassan

Idan Sarki ya rasu, bayan an yi jana’izarsa za a sanar da hukuma a rubuce cewa Sarki ya rasu.

Daga nan wadanda ke da alhakin zaben sabon Sarki za su zauna su yi shawara sannan su fitar da sunaye daga gidajen saraurar Borno.

Idan sun zabi sabon sarki za su mika wa gwamnati ta sanar.

“Masu zaben sabon Sarki guda bakwai ne da suka hada da Shettima Kanuribe da Shettima Kuburibe da Yarima da Kaigama da Mallam Terab” a cewar Zannah Boguma.

Ko Daular Usmaniya ta yaki Daular Borno? Tambaya ce da muka samu daga Abdulmajid Abubakar da Muhammd Yusuf da Umar abubakar Zamfara da Mudassiru Yusuf S/Fada da Kamal Y Iyantama da Ahmed Rufa’i Abdullahi da Musa Yayan Baba

Jihadin Shehu Usman Danfodio ya faru ne a 1804, inda ya kafa tuta da daulolinsa a kasashen Hausa a 1805.

Danfodio bai yi niyyar ya yaki Borno ba, amma Fulani da suke zaune a Borno da ake kira Fulata Borno karkashin wani babban malami Goni Mukhtar suka kaddamar da yaki.

Malam Goni Muktar ya rubutawa Danfodio wasika yana son a ba shi tuta, yana ganin Borno na bukatar a kaddamar da yaki na jihadi saboda a ganinsa akwai wasu abubuwan da ake yi na al’adu.

Danfodio ya amince da bukatarsa aka yaki Borno.

“Amma bayan yakin, El Kanemi ya rubutawa Danfodio da takarda cewa bai kamata a yaki Borno ba domin kasa ce ta musulunci da sarakunanta”, a cewar Zanna Boguma.

Ya kara da cewa akwai rubutun wasikar El Kanemi zuwa ga Danfodio a cikin litaffin Infakul Maisuri na Muhammadu Bello Danfodio.

“A cikin wasikar El kanemi ya nuna cewa yakin da aka kaddamar ba jihadi ba ne illa neman mulki da son duniya”.

“Daga baya Danfodio da El Kanemi sun dawo sun fahimci juna inda suka amince kuma suka tabbatar da cewa babu abin da ke tsakaninsu illa aminci da ‘yan uwantaka ta addinin musulunci”.

Zanna Boguma ya ce Borno ba ta taba zama a karkashin tutar daular Usmaniya ba domin Borno tana da tarihi na musulunci da malamanta sama da shekara 1000 kafin kafuwar daular Usmaniya a Sokoto.

“Hakan ya sanya da aka yi bikin cika shekaru 200 da kafuwar Daular Usman Danfodio muka ce bai shafe mu ba, sai mu muka yi bikin shekaru 1000 da kafuwar daular musulunci ta Borno”.

Sace yammatan Dapchi bala’in da ya shafi kasa ne — Buhari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya sha alwashin ceto yammatan sakandiren Dapchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana zargin sa ce yammatan sakandiren Dapchi da aka yi a kwanakin baya-bayan nan a matsayin wani bala’i da ya shafi kasa baki daya.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, shugaba Buharin, ya ce gwamnatinsa za ta tura da karin sojoji da kuma jiragen saman yaki zuwa yankin domin kubatar da ‘yammatan.

Sanarwar ta fito ne bayan kwana hudu da aka sace wasu dalibai mata da ke karatu a wata sakandiren gwamnati da ke jihar Yobe.

Har yanzu dai ba san iya adadin yammatan da suka bace ba, amma kuma wasu iyayen yaran sun shaidawa BBC cewa, yammatan da aka sacen sun fi 100.

Shugaban Najeriyar, ya ce sojoji na nan na neman yammatan sakandiren. Ya ce jiragen saman yaki na ta shawagi a yankin ba dare ba rana.

Kimanin kwanaki hudu ke nan tun bayan da wasu masu tayar da kayar baya suka kai hari makarantar, kuma har yanzu ba bu wani cikakken bayani daga gwamnati a kan adadin daliban da maharan suka yi awon gaba da su.

Iyayen yaran sun kasance cikin bacin rai da damuwa.

PDP ta dora laifin sace ‘yan matan Dapchi kan Buhari

Nigeria; Sojoji sun ceto ‘yan matan makarantar Dapchi

Kwanaki biyu tun bayan sace yammatan, mahukuntan jihar ba su yarda da cewa an sace su ba.

A ranar Larabar data gabata ne, gwamnatin jihar ta Yobe ta ce an kubutar da wasu daga cikinsu, amma kuma ba gaskiya ba ne.

Iyayen yaran wadanda suke a fusace sun jefi ayarin motocin gwamnan jihar da duwatsu bayan da suka samu wannan labari.

Yayin da a jiya Jumma’a kuma daya daga cikin iyayen yammatan ya shaida wa BBC cewa, yana boye a wani waje saboda ‘yan sanda na nemansa ruwa a jallo saboda jifan da aka yi.

Tuni dai aka kama mutum uku sakamakon jifan ayarin motocin gwamnan ciki har da mahaifin daya daga cikin yammatan.

Wasu ‘yan Najeriya na kallon lamarin da kamar yadda ya faru a shekarar 2014 inda aka sace yammatan sakadiren Chibok, da gwamnati ba ta amince da an sace yammatan sakandiren ba.

PDP ta dora laifin sace ‘yan matan Dapchi kan Buhari


Image caption

Fiye da ‘yan matan Dapchi 100 ne har yanzu ba a gani ba

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce kamata ya yi ‘yan kasar su dora alhakin yin sakaci wajen sace ‘yan matan makarantar Dapchi da ke jihar Yobe a kan Shugaba Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, PDP ta kuma ce ba ma batun sace ‘yan matan kawai ba, kamata ya yi ‘yan kasar su dora laifin duk wasu abubuwa da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a arewa maso gabashin kasar, kan gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ce: “Gwamnatin Shugaba Buhari ta sa rayuwar ‘yan Najeriya cikin hadari ta hanyar yaudarar mutane wajen ba su bayanan karya na cewa sun kawar da masu tayar da kayar bayan, al’amarin da ya sa mutane suka yarda da wannan karya suka kuma daina fargabar cewa akwai abun da ke barazana ga rayuwarsu.

“Idan da a ce gwamnatin APC ba ta yi ta kirkirar karya tana yadawa mutane don samun tagomashin siyasa a 2019 ba, da tuni mutanen wadannan al’ummomi sun dauki matakan kare kansu daga fadawa irin wannan halin.”

Sai dai ko a ranar Juma’a fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa ana bai wa batun sace ‘yan matan mhimmanci sosai ta ko wanne bangare.

PDP ta kuma kara da cewa gwamnatin ta yi ta kawo rahotanni daban-daban masu rudarwa a kan batun sace ‘yan matan, don kawai kokarin boye laifinsu na gazawa wajen kare mutane.

“Abun takaici ne yadda ‘yan Najeriya a yau suke fama da gwamnatin da ke cike da farfaganda, take kuma wasa da al’amarin ‘yan kasarta.

“A lokacin gwamnatin PDP ba a taba yi wa ‘yan Najeriya karya ko boye musu gaskiyar wani al’amari ba. Ana sanya masu ruwa da tsaki a duk wani abu da ya shafe su don kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An samu ceto ‘yan matan Chibok da dama a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari ta APC

A karshe PDP ta mika sakon jajenta ga iyayen yaran da aka sace tare da addu’ar Allah ya dawo da su lafiya.

Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro su daina biye wa ‘farfagandar APC’ su dauki matakan da suka dace don ceto yaran nan.

A ranar Litinin da yamma ne mayakan Boko Haram suka kai hari garin Dapchi inda suka shiga makarntar ‘yan mata da ke garin suka sace kayan abinci, malamai da dalibai kuma suka bazama jeji neman wajen buya.

Sai dai bayan kwana biyu da faruwar hakan ba a ji duriyar ‘yan mata da dama ba kuma har yanzu babu labarinsu.

Ana yi wa wannan al’amari kallon irin abun da ya faru ga ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sace a 2014 a lokacin mulkin jam’iyyar PDP.

A wancan lokacin ma sai da aka shafe tsawon lokacin kafin gwamnatin wancan lokacin ta yi bayani kan ainihin abun da ya faru, har ma aka dinga zarginta da rashin mayar da hankali kan lamarin.

Kuma a lokacin gwamnatin ba ta smau damar ceto ko daya daga cikin fiye da ‘yan mata 200 da ak sace ba.

An tilasta wa yara kallon yadda ake yi wa iyayensu fyade a Sudan ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A watan Disamban da ya wuce ne aka yi zanga-zangar adawa da wahalar da mata da yara suke fuskanta a kasasr

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce ana tilastawa yara a kasar Sudan Ta Kudu kallon yadda ake yi wa iyayensu fyade.

Wani rahoto da masu binciken kare hakkin bil adama na MDD suka fitar, ya ce wasu jami’ai 40 na iya zama wadanda ke da alhakin aiwatar da laifukan yaki da kuma laifukan cin zarafin bil adama.

Rahoton ya ce ana azabtar da fararen hula da cin zarafinsu, kuma an lalata kauyuka da dama.

Ana ci gaba da rikici tsaknain bangarorin gwamnati biyu masu adawa da juna a Sudan ta Kudu, duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanyawa hannu a shekarar 2015.

Daga cikin manyan jami’an 40 da aka samu da hannu a aikta wadannan miyagun laifuka, har da wadansu kanal din soji biyar da kuma gwamnonin jihohi uku.

Sai dai rahoton bai ambaci sunayensu ba, amma za a bayyana hakan idan aka fara shari’ar a nan gaba.

MDD ta ce hujjojin da aka tattara daga wadanda abin ya shafa “suna da ta da hankali” ciki har da yadda wadansu ‘yan uwa aka tilasta musu su yi wa danginsu fyade “kamar yadda ya faru a Bosniya.”

Wata mata ta ce an tilasta wa danta mai shekara 12 ya tara da kakarsa a bakin ransa, kafin daga bisani aka yi wa mijinta dandaka a gabanta.

Shi kuwa wani mutum ya ga yadda aka yi wa dan uwansa fyade ne, kafin daga bisani a jefar da gawarsa a daji.

“Cin zarafin maza ya zama ruwan dare a Sudan ta Kudu,” in ji shugabar hukumar da ke kula da kare hakkin dan Adam a Sudan ta Kudu, Yasmin Sook.

“Abin da muke gani yanzu kadan ne daga cikin abin da ke faruwa,” a cewarta.

Wata mata mai dauke da juna biyu a yankin Lainya ta ce ta gane wa idonta yadda mayakan SPLA suke azabtarwa da kuma fulle kawunan wadansu da ake zargi magoya bayan ‘yan adawa ne.

Kuma an tilasta mata zama a daki guda da gawawwakin mutanen da ke rubewa – guda daga cikinsu kuma gawar mijinta ta ce.

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya suna ci gaba da tattara hujjoji wadanda za su gabatar a kotunan da ke sauraron shari’ar manyan laifukan yaki.

Kuma sakamakon binciken za a gabatar da shi ne a gaban kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva.

Sai dai zuwa yanzu ba a kafa kotun ba saboda majalisar dokokin Sudan ta Kudu ba ta amince da bukatar kan ba tukuna.

BBC ta kaddamar da gasar Komla Dumor ta 2018 ga ‘yan jaridar Afirka


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Gasar Komla Dumor ta BBC ta 2018

BBC na neman ‘yan jaridar Afirka masu tasowa don shiga gasar tunawa da Komla Dumor ta 2018, wadda wannan ne karo na hudu a jere da aka yi gasar.

Ana gayyatar ‘yan jarida daga nahiyar Afirka da su shiga gasar, wadda aka kirkire ta da nufin zakulo da kuma taimakawa ‘yan jarida masu fasaha daga Afirka.

Wanda ya yi ko ta yi nasara za sushafe wata uku a hedikwatar BBC da ke London, don kara gogewa da sanin makamar aiki.

Za a rufe shiga gasar ranar 23 ga watan Maris na 2018, da misalin karfe 11:59 agogon GMT.

An kikrkiri gasar ce domin tunawa da kuma girmama dan kasar Ghana Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a tashar labarai ta BBC, wanda ya yi mutuwar farat daya a shekarar 2014, a lokacin yana da shekara 41 a duniya.

A wannan shekarar za a kaddamar da gasar ne a Accra, babban birnin kasar Ghana.


 • Za ku iya latsa nan don samun karin bayani game da gasar da kuma sanin ko kun dace da shiga (Ku latsa nan)

It will be made to an outstanding individual living and working in Africa, who combines strong journalism skills, on-air flair, and an exceptional talent in telling African stories with the ambition and potential to become a star of the future.

Bayan shafe wani lokaci da wanda ya yi nasara zai yi a London, zai/za ta kuma je wata kasa a Afirka don yin labari kan wani abu – za kuma a rarraba labarin ga kasashen Afirka da ma duniya baki daya.

Image caption

2017 winner Amina Yuguda reported on environmental issues during her time at the BBC

Wadanda suka yi nasara a baya sun hada da Nancy Kacungira daga Uganda da Didi Akinyelure daga Najeriya da kuma Amina Yuguda ita ma ‘yar Najeriya.

A nata aikin, Amina ta je kasar Uganda ne inda ta yi labarin kan: Yadda Tafkin Victoria ke fuskantar barazana, wanda shi ne tafki ma fi girma a Afirka, wanda masana kimiyya suka yi gargadin cewa yana mutuwa.

Amina ta ce: “Samun nasarar da na yi a gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017 ta sa na ji tamkar a lokacin ne na fara aikin jarida. Cin gasar babar kafar yada labarai ta duniya, da samun girmamawa a wajen, sun sa na ji tamkar yanzu ne ma nake jin na fara aikin jarida.”

Ta kara da cewa: “A lokacin da na je Landan don kara samun kwarewa, na gane muhimmancin yin labaran gaskiya, da tsage gaskiya, da jin ko wanne bangare da yin adalci yayin rubuta labarai, da kuma sanin yadda zan rubuta labaran da suka shafi Afirka da kyau ta yadda sauran duniya za su fahimta.

“Muna alfahari da yadda Komla ya wakilci nahiyarmu da ma duniya, kuma na ji dadi da na zamo cikin wadanda za su dora daga inda ya tsaya.

Amina za ta kasance cikin wadanda za su kaddamar da gasar ta 2018, tare da daraktan yada labarai na BBC Jamie Angus.

Da yake magana gabanin kaddamarwar ya ce: “Abun alfahari ne kasancewata a Ghana, kasar su Komla, cikin ‘yan uwansa da abokansa, don karrama shi, da kuma zakulo wani ko wata sabuwar tauraron ‘yan jarida na Afirka.

Mutane ukun da suka taba lashe gasar – Nancy da Didi da Amina – duk sun suna basirarsu ta aikin jarida, da matukar sanin nahiyar Afirka, da kuma sanin yadda za su bai wa masu sauraro labari irin yadda suke so.

“Muna ci gaba da neman ‘yan jarida masu kwazo daga nahiyar da kuma yi musu maraba a BBC a matsayin wadanda suka lashe gasar Komla Dumor.”

Yaran Rohingya na cikin hadari-UNICEF


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kananan yara na cikin hadari

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi gargadin cewa kananan yara ‘yan Rohingya kashi uku bisa hudu na fuskantar babbar barazana har na tsawon wasu shekaru masu zuwa.

An bayyana hakan ne a wani rahoton UNICEF yayin cika watanni shida tun bayan fara rikicin daya tilastawa ‘yan Rohingya fiye da miliyan daya tserewa zuwa Bangladesh don gujewa tashe tashen hankula a Myanmar.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce akwai dubban kananan yara da yanzu haka suke rabe a wasu sansanoni na wucin gadi.

Kuma basa samun ilimi tare da fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka da kuma tashe tashen hankula.

Bangladesh ta hana Msulimin Rohingya zuwa ko’ina

Bangladesh ‘za ta mayar da Musulmin Rohingya 300’ Myanmar

Mai kungiyar Sunderland zai bayar ta ita kyau


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A kakar da ta wuce ne Sunderland ta fadi daga gasar Premier

Attajirin da ya mallaki Sunderland Ellis Short ya ce zai bayar da ita kyauta idan har wanda zai saye ta zai yarda ya karbe ta da dimbin bashin da ke kanta.

Short ya ce duk da ya sa kungiyar ta gasar kasa da Premier, Championship, wadda kuma ke neman faduwa daga gasar a kasuwa har yanzu ya rasa wanda zai saye ta.

Rahotanni sun ce attajirin dan Amurka a da yana neman fam miliyan 50 ne na hannun jarinsa a kungiyar.

To amma kuma yanzu ya hakura da hakan, inda ya ce zai bayar da ita kyauta, muddin wanda zai karbe zai yarda ya gaji tarin bashin da ke kanta, wanda a shekara ta 2016 ya kai fam miliyan 137 da dubu 300.

Kungiyar ta gamu da faduwar daraja ne domin a lokacin da tana gasar Premier a 2016, attajirin ya sa mata farashin fam miliyan 170 ne ga duk mai so.

Daliban jami’ar Moscow sun yi korafi kan gasar Kofin Duniya


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Daliban na Jami’ar Moscow State University sun rika sanya hannu a wata takardar intanet ta nuna kin amincewarsu da matakin hukumomin kasar

Dalibai a fitacciyar jami’ar Rasha suna murnar samun kwaryakwaryar nasara a kan shirinsu na yakar matakin hukumomin kasar na tilasta musu ficewa daga harabar makarantar a lokacin gasar cin kofin duniya ta shekarar nan.

Daliban sun nuna bacin ransu ne kan shirin kafa dandalin ‘yan kallo a lokacin gasar a kusa da wuraren kwanansu, na jami’ar ta Moscow State University, inda za a girke manyan allunan majigi, wadanda mutane za su rika taruwa suna kallon wasannin na kofin duniya.

Wasu daliban ma har sai ta kai an tashe su daga dakunan kwanan nasu domin a ba wa jamia’n tsaro da za su tabbatar da doka da oda, a lokacin gasar wadda za a fara a watan Yuni har zuwa wata daya.

Sannan kuma wasu daliban da dama sun nuna bacin ransu saboda za a matsar da jarrabawarsu gaba zuwa watan Mayu, yayin da wasu kuma ke kukan za a takura musu ta yadda za su yi jarrabawa shida a kasa da mako biyu.

Sakamakon korafin daliban a yanzu hukumomin kasar ta Rasha, sun fitar da wata sanarwa, wadda a ciki suke tabbatarwa tare da yi wa daliban jami’ar ta Moscow alkawarin cewa, za a samarwa daliban da tagogin dakunan kwanansu ke kusa da inda za a girke majigin wuraren kwana na wucin-gadi.

Shi kuma shugaban makarantar ya fitar da tasa sanarwar wadda a ciki yake sheda wa daliban da aka so sauya lokacin jarrabawarsu cewa za a dawo da ita ainahin lokacin da aka tsara tun da farko.

Dapchi: Shin ba a koyi darasi ba ne daga Chibok?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Harin makarantar mata a Dapchi a Jihar Yobe yana kara zama kamar na makarantar garin Chibok da mayakan Boko Haram suka abka suka sace dalibai 276 a 2014.

Yayin da ake amai ana lashewa game da batun sace ‘yan matan makarantar a Jihar Yobe da ke arewa maso gabacin Najeriya, hakan ya nuna kamar ba a koyi darasi ba ne daga Makarantar garin Chibok da aka sace mata sama da 200 a Jihar Borno.

Batun Dapchi a yanzu yana son ya yi kama da na Chibok.

‘Yan kwanaki bayan sace ‘yan Matan Chibok, gwamnati ta yi shiru ba ta ce komi, kafin daga baya kuma rundunar sojin Najeirya ta sanar da cewa an ceto dukkanin ‘yan Matan kafin ta yi amai ta lashe.

Da farko hukumomin Najeriya ba su yi la’akari da girman al’amarin ba har sai da batun ya ja hankalin duniya bayan kaddamar da kamfen na a dawo da ‘yan matan na Chibok wato BringBackOurGirls.

A wannan karon ma an samu rudani, inda aka yi ikirarin ceto ‘yan matan, kafin daga baya kuma gwamnati ta fito ta nemi afuwa.

Sannan har yanzu ba a tantance gaskiyar adadin yawan ‘yan matan da aka sace ba.

Wasu sun ce ‘yan mata kimanin 50 ne, yayin da wasu kuma ke cewa ‘yan matan sun haura 100.

Kuma har yanzu ba a tabbatar da ko mayakan Boko Haram ne suka yi awon gaba da daliban ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Har yanzu akwai ragowar ‘yan matan Chibok kusan 100 da ba a gano ba

Iyayen ‘yan matan makarantar Dapchi dai sun shiga wani hali da damuwa a yanzu, inda babu wani abu da suke fata illa labarin ceto ‘yayansu.

Duk da cewa ‘iyayen Dapchi ba za su cire tsammani ba, amma har yanzu akwai iyayen ‘yan matan Chibok da ke jiran tsammanin yin tozali da ‘yayansu wadanda Boko Hram ta sace yau kusan shekaru 4.

Masharhanta dai na ganin akwai sakaci na hukumomi domin ya kamata ace an dauki darasi daga abin da ya faru a Chibok.

Malam Kabiru Adamu mai sharhi kan al’amuran tsaro a Najeriya, ya ce hakan ya nuna ba wani tanadi ko tsari da aka yi a makarantu domin tsaron dalibai duk da gidauniyar kudi da aka tara domin kare makarantu a taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a Birtaniya.

“Ya dace a dauki matakan tsaro na shiga ta fita a makarantu domin kare sake aukuwar abin da ya faru a Chibok” a cewar Malam Kabiru.

Saudiyya za ta zuba jarin $64bn a bangaren nishadantarwa


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

tun tuni Saudiya ta sanar da bayar da damar bude gidajen nuna fina-finai

Saudiyya ta ce za ta ware kudi $64bn domin bunkasa masana’antunta na nishadantarwa a cikin shekaru goma masu zuwa.

Shugaban hukumar da ke kula da harakokn nishadi a kasar ya ce an tsara shirya abubuwa kimanin 5,000 a bana kawai da suka kunsh har bikin cashewa na Maroon 5 kamar irin wanda ake gudanarwa a Amurka.

Akwai kuma bikin casu na Cirque du Soleil irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai.

Tuni dai Saudiya ta fara aikin gina wajen casu a birnin Riyadh.

Shirin zuba jarin na cikin sabbin manufofin bunkasa tattalin arziki da ake kira Vision 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar shekaru biyu da suka gaba.

Yariman mai shekaru 32 na son karkatar da tattalin arzikin Saudiyya daga dogaro da arzikin fetir, inda aka kara ware kudi a bangaren bunkasa al’adu da nishadi a kasafin kudin kasar.

A watan Disemba ne, gwamnatin Saudiya ta dage haramci kan gidajen sinima.

Kafofin yada labaran Saudiya sun ambato Ahmed bin Aqeel al-Khatib shugaban hukumar harakokin nishadi yana cewa, yana fatar za su dauki mutane 220,000 aiki a bangare nishadi kafin karshen 2018.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan Cirque Eloiz sun yi casu a watan Janairu wanda shi ne karon farko a Saudiyya

“A baya masu zuba jari suna fita saudiya ne su gudanar da ayyukansu, amma a yanzu za a samu sauyi kuma duk wani abu da ya shafi nishadantarwa a nan za a yi shi”, a cewarsa.

Mista Aqeel ya ce zuwa 2020 za a ga canji a Saudiya.

Saudiya dai na fatar bunkasa bangaren yawon bude ido domin samun kudaden shiga.

Wadannan dai sabbin abubuwa ne ake gani a kasa irin Saudiya, inda a watan da ya gabata gwamnatin kasar ta sanar da ba mata shiga filayen kwallon kafa domin kallon wasanni da kuma ba mata izinin tukin mota daga watan Yuni.

A bara, Yarima Mohammed bin Salman ya ayyana kudirinsa cewa yana son mayar da Saudiya “matsayin kasa mai sassacin ra’ayin addini tare da bude kofa ga dukkanin addinai da al’adu da mutanen duniya”.

Gidan Sarautar Saudiyya, da tsarin tafiyar da lamurran addinin kasar na bin akidar Sunni ne ta Wahabiyanci, inda wasu dokokin musulunci ke da tsauri sosai.

Gwamnatin Yobe ta nemi afuwa kan batun ‘yan Matan Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Abdullahi Bego

Image caption

Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan batun ‘yan matan Dapchi

Gwamnatin jihar Yobe ta nemi afuwa kan labarin ceto ‘yan matan makarantar sakandaren Dapchi da mayakan Boko Haram suka abka makarantarsu suka yi awon gaba da su.

A sanarwar afuwa da Abdullhi Bego kakakin gwamnan jihar Yobe ya rabawa manema labarai ciki har da BBC, ya ce sun bayar da sanarwar ceto ‘yan matan ne bisa bayanin da suka samu daga daya daga cikin hukumomin tsaro da ke yaki da Boko Haram.

Kuma ya ce sun fadi an ceto ‘yan matan ne, domin ba su da wani shakku a kan labarin da suka samu daga hukumar tsaron.

“Yanzu mun fahimci cewa labarin da muka dogara da shi da har ya sa muka fitar da sanarwa ba gaskiya ba ne, gwamnatin Yobe na neman Afuwa”, a cewar sanarwar da ke dauke da sa hannun Abdullahi Bego, kakakin gwamnan Jihar Yobe.

Sannan sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya gana da iyayen ‘yan matan da aka sace a garin Dapchi, kamar yadda wasu daga cikin iyayen suka shaidawa BBC tun da farko.

Gwamnan ya bukaci ma’aikatar ilimi da hukumomin makarantar su hada hannu da jami’an tsaro domin tabbatar da adadin yawan ‘yan matan da aka sace tare da tuntubar iyayensu domin samun wasu bayanan da za su taimaka wa binciken da ake yi domin gano su.

Tun da farko ne daya daga cikin iyayen ‘yan matan ya shaidawa BBC cewa gwamnan Yobe ya same su inda ya shaida masu cewa babu daya daga cikin ‘ya’yansu da aka kwato.

Kuma nan take ne wasu daga cikin iyayen suka suma, bayan jin labarin daga gwamna.

Wata majiya ta kuma shaida wa BBC cewa an yi ta jifan gwamna Ibrahim Gaidam tare da yi masa ihu bayan da ya shaida musu wannan labari.

A ranar Laraba ne Gwamnatin jihar Yobe ta ce sojojin Najeriya sun ceto ‘yan matan makarantar sakandaren garin na Dapchi wadanda mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da su, bayan da fari sun ce ba sace su aka yi ba.

A sanarwar da Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya fitar ya ce sojojin Najeriya sun bi ‘yan Boko Haram tare da kwato daliban sama da 50.

Jose Mourinho: Kila raunin Marcos Rojo ya yi muni


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Daman Ander Herrera ya dawo daga jinya ne bayan rasa wasansu da Newcastle da Huddersfield

Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce kila raunin da Ander Herrera ya ji a wasansu na jiya Laraba na kofin zakarun Turai da suka yi canjaras ba ci da Sevilla, ya yi tsanani.

Dan wasan tsakiyar na Spaniya ya ji ciwon ne minti 17 da shiga fili a karawar ta farko ta matakin kungiyoyi 16, abin da ya sa United ta maye gurbinsa da Paul Pogba.

Daman Herrera ya dawo daga jinya ne bayan da ya rasa damar buga wasanninsu a watan Fabrairu da Newcastle da kuma Huddersfield.

Kociyansu Jose Mourinho ya ce daman kamar dan wasan bai warke ba sarai, amma likitoci suka ce ya samu lafiya dari bisa dari, kuma zai iya wasansu da Huddersfield na kofin FA, ranar Asabar da ta wuce.

Manchester United daman ta rasa ‘yan wasanta na baya Phil Jones da Marcos Rojo, da na tsakiya Marouane Fellaini da dan gaba Zlatan Ibrahimovic wadanda duk suke jinya.

Deportivo ta dauki Sulley Muntari domin tsira a La Liga


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon dan wasan na tsakiya na AC Milan ya tsawaita zamansa ke nan a Spaniya

Kungiyar Deportivo La Coruna wadda ke neman tsira a gasar La Liga ta dauki dan wasan tsakiya na Ghana Sulley Muntari har zuwa karshen kakar da ake ciki.

Tsohon dan wasan na Sunderland da Portsmouth mai shekara 33, ba wani kwantiragi a kansa bayan da yarjejeniyarsa da kungiyar Pescara ta kare a kakar da ta wuce.

Bayan gwajin da aka yi masa a Deportivo La Coruna, ya yi nasara tare da burge sabon kociyan kungiyar Clarence Seedorf, wanda sun yi wasa tare a AC Milan.

Tsohon dan wasan na Holland ya kuma zama kociyan Muntari a lokacin da ya yi aikin horar da kungiyar ta Italiya.

Muntari ya yi fice a Italiya a kungiyar Udinese sannan ya yi wasa a Inter Milan, abin da ya sa ya zama cikin wani rukuni na ‘yan wasa da suka taka leda a manyan kungiyoyi biyu na Milan.

Deportivo, wadda take ta biyun karshe a teburin La Liga, da kuma shi Seedorf za su yi fatan amfana da kwarewar dan wasan bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a wasa biyu da sabon kociyan ya jagoranta.

A ranar Juma’a ne Deportivo za ta karbi bakuncin Espanyol yayin da take neman tsira daga gasar ta Spaniya da bukatar maki uku a yanzu, kafin ta fice daga rukunin masu faduwa.

Muntari wanda ya yi wa Ghana wasa sau 84 bai sake taka wa kasar leda ba tun bayan da aka kora shi gida daga tawagar a lokacin gasar cin kofin duniya ta 2014 a Brazil, saboda laifin rashin da’a.

Kun san dalilin komawar Wayne Rooney Everton?


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Burina shi ne na ci gaba da cin kwallo tare da taimaka wa Everton, amma ba wai karbar makudan kudade ba, in ji Rooney

Wayne Rooney ya ce ya zabi ya koma tsohuwar kungiyarsa Everton ta tun yana yaro domin ya fuskanci matsin lamba maimakon ya tafi kasa kamar China, inda zai samu kudi mai yawa.

Tsohon dan wasan na gaba na Manchester United ya sake komawa Everton a kwantiragin shekara biyu a kan kudin da ba a bayyana ba, a kakar da ta wuce.

Dan wasan mai shekara 32 ya ce yana da zabin tafiya kasar waje a kwantiragin da zai samu makudan kudade amma ya ki.

Ya ce wannan ba ra’ayinsa ba ne, saboda yana bukatar cin kwallo, yana bukatar matsin lamba, ya ce da ya zabi tafiya, to da ya rasa wannan bukata.

Da yake tattaunawa da tsohon abokin wasansa a Everton Kevin Kilbane, Rooney ya ce ya zabi komawa tsohuwar kungiyar tasa bayan shekara 13, maimakon ya je inda zai kawo karshen wasansa yana karbar kudade da yawa.

Rooney ya kara da cewa ya kaunaci komawa Everton din kuma domin ya kara nuna kansa ga magoya bayan kungiyar tare da taimaka mata ta ci gaba har ma ta dauki kofi.

Rooney ya yi wa Manchester United wasa 559, inda ya ci mata kwallo 253.

Sannan ya yi ritaya daga buga wa Ingila wasa a watan Agusta da ya wuce, a matsayin dan wasan da ya fi ci mata kwallo a tarihi da 53.

Me ya sa ake yawan kashe dalibai a makarantu a Nigeria?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kaddamar da bincike kan rahoton wani malami da ya yi wa dalibi duka har ya mutu a makarantar Sankalawa cikin karamar hukumar Bungudu.

A ranar Laraba ne Mataimakin Shugaban Majalisar dokokin Jihar Alhaji Muhammad Abubakar Gummi, ya bayyana wa majalisar faruwar lamarin.

Kuma ya ce sun samu labarin wata daliba da ta samu mummunan rauni a makarantar sakandaren mata ta Kwatarkwashi sakamakon duka da azabtarwa daga mataimakiyar shugabar makarantar.

Wannan na zuwa ne a yayin da a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar ma, rahotanni suka ce wata daliba ta mutu a makarantar sojoji ta Obinze, bayan da wasu sojoji biyu suka yi wa dalibar duka saboda ta yi lattin zuwa makaranta.

Rahotannin sun ce sojojin sun sa dalibar mai shekara 15 tsallen kwado har sai da ta kasa tashi, daga baya ne kuma ta rasu bayan an ruga da ita asibiti.

Kisa da dukan dalibai a makarantu ko dai daga malamai da manyan dalibai ba sabon abu ba ne a Najeriya.

A watan Janairun da ya gabata, hukumomin ilimi a jihar Nasarawa sun dakatar da wani shugaban makarantar GSS Nasarawa Eggon, kan dukan dalibai.

Wani hoton bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda shugaban makarantar ya sa ake yi wa dalibai dukan tsiya.

A cikin hoton bidiyon, an nuna yadda malamin ya daddage yana dukan wasu dalibai da bulala.

A watan Nuwamba ma ‘Yan sanda a Kano arewa maso yammacin Najeriya sun taba kama wasu dalibai bakwai a Kwalejin Fasaha ta Ungogo, wadanda aka yi zargi da halaka wani abokin karatunsu da ke ajin karshe.

Haka ma a kwalejin gwamnati da ke karamar hukumar ‘Yankwashi a jihar Jigawa, a watan Agustan bara ‘yan sanda sun taba kama dalibai 15 da ake zargi da hannu a kisan abokin karatunsu.

An zargi daliban da jefar da gawar dalibin bayan sun kashe shi a ranar 6 ga watan Agusta kan zargin wai dan luwadi ne.

Masharhanta dai na ganin rashin cibiyoyi na jagoranci da bayar da shawara a makarantun sakandare na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da wadannan matsalolin.

Sannan da yadda gwamnati ba ta damu da ba bangaren muhimmaci ba a makarantun na sakandare, musamman wajen ilmantar da iyaye da malamai kan muhimmacin ilimin domin halayyar ‘yayansu a makarantu.

Wasu na ganin za a iya ladabtar da dalibai ta hanyoyi da dama ba lalle sai an dauki mataki mai tsauri a har zai kai a yi wa dalibai dukan da zai yi sanadin ajalinsu ba.

Nigeria: An sake gurfanar da shugaban Ansaru a kotu, al-Barnawi a kotu


A ranar Alhamis ne aka gabatar da shugaban kungiyar Jama’atu Ansarul musulimina fi biladil Sudan, wadda ta balle daga kungiyar Boko Haram, wato Khalid al-Barnawi a gaban wata babbar kotun tarayya a birnin Abuja, Najeriya.

Ana dai zarginsa ne tare da wasu mutum bakwai da aikata laifuka da suka shafi ta’addanci, ciki har da sacewa da yin garkuwa da wasu ‘yan kasashen waje su 10, da kuma kashe su.

‘Yan kasashen wajen sun hada da Turawa da Larabawa wadanda aka sace a jihohin Bauchi da Kebbi da kuma Kano daga 2011 zuwa 2013.

Wadanda ake tuhuma dai sun musanta zarge-zargen yayin da aka dage sauraren karar zuwa watan Afrilu.

A bara ma da aka gurfanar da shi ya yi watsi da tuhumar da ake masa, Sai aka sake yi masa irin tuhumar bayan da wani sabon alkali ya karbi ci gaba da shari’ar.

Ainihin alkalin da ke shari’ar ya fitar da kansa daga shari’ar ne bayan da al-Barnawi ya ce bai yarda da shi ba.

Sojoji ne suka kama Barnawi a shekarar 2016 a jihar kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Amurka ta yi alkawarin bayar da tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya taimaka aka kama shi, bayan da suka sanya shi a jerin ‘manyan ‘yan ta’adda’ uku na duniya a sjekarar 2012.

Ansaru wata kungiya ce wadda ta balle daga kungiyar Boko Haram.

Kungiyar na alakanta kanta da kungiyar al-Qaeda.

An daga shari’arsa har zuwa 9 ga watan Afrilu.

Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan ‘yan Matan Dapchi


Hakkin mallakar hoto
Abdullahi Bego

Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan batun ceto ‘yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi, inda a yanzu ta shaidawa ‘iyayen daliban cewa ba a kubutar da su ba.

Daya daga cikin iyayen ‘yan matan ya shaidawa BBC cewa gwamnan Yobe ya same su inda ya shaida masu cewa babu daya daga cikin ‘ya’yansu da aka kwato.

Gwamnan ya ce Sojoji har yanzu na ci gaba da farautar mayakan Boko Haram da ake zargi sun yi awon gaba da daliban.

Nan take ne dai wasu daga cikin iyayen suka suma, bayan jin labarin daga gwamna, kamar yadda daya daga cikinsu ya shaidawa BBC.

Wata majiya ta kuma shaida wa BBC cewa an yi ta jifan gwamna Ibrahim Gaidam tare da yi masa ihu bayan da ya shaida musu wannan labari.

A ranar Laraba ne Gwamnatin jihar Yobe ta ce sojojin Najeriya sun ceto ‘yan matan makarantar sakandaren garin na Dapchi wadanda mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da su, wadanda da fari suka ce ba sace su aka yi ba.

Kuma tun bayan sace su a ranar Litinin bayakan Boko Haram suka kai hari a Makarantarsu ba a sake jin duriyarsu ba.

Amma a ranar Laraba Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya fitar da sanarwar cewa sojojin Najeriya sun bi ‘yan Boko Haram tare da kwato daliban.

Tun da farko dai hukumomi sun ce ‘yan matan sun bazama daji ne don neman wajen buya yayin da maharan suka dirarwa makarantar.

Wani malamin makarantar ma ya shaida wa BBC cewa mayakan ba su kai harin don sace ‘yan mata ba sai don ‘satar abinci,’ kuma sun saci kayan abincin da dama.

Sai dai gwamnatin jihar Yoben ta tabbatar da rashin bayyanar ‘yan matan a ranar Laraba da safe, inda ta ce ba a ji duriyarsu ba, sai dai ana ci gaba da neman su a dazuzzukan da ke kusa da garin.

An yi ta samun rahotanni masu karo da juna dangane da batan ‘yan matan makarantar sakandaren Dapchi da ke jihar Yobe.

Tun da fari kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato iyayen yaran da jami’an gwamnati na cewa ‘yan mata 76 aka ceto, kuma har yanzu akwai 13 da ba a gani ba.

Reuters ya kuma ce an gano ‘yan mata biyu da suka mutu, amma ba a bayyana abun da ya yi sanadin kashe su ba.

A ranar Litinin ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari makarantar inda suka yi ta harbe-harbe tare da tayar da abun fashewa.

Rahotanni sun ce maharan sun sace kayayyaki daga makarantar bayan sun tarar wasu daliban da malaman sun tsere.

Hakkin mallakar hoto
GGSS

Ghana: ‘Yan mata sun rungumi kwallon zari-ruga


A Ghana, kasar da aka kiyasta cewa tana da mutane sama da miliyan 28 a shekarar 2016, ba kowa ne ya san kwallon zari-ruga ba, ko da da sunan wasan na Ingilishi, wato Rugby.

Sai dai masu sha’awar wasan a karkashin jagorancin Hukumar Kwallon Zari-ruga ta Ghana sun dukufa don ganin labarin ya sauya.

“Tun baya da muka rungumi zari-ruga, sai [muka ga ya wajaba] mu kirkiri wani tsari…[wanda] a karkashinsa za mu bunkasa wasan a tsakanin matasa, da mata, kuma a fadin kasar nan”, in ji Shugaban Hukumar, Herbert Mensah.

Wannan yunkuri da kuma burin da suke da shi na samar da ‘yan wasa akalla 1,500 su suka aka daura damarar ganin an koyar da zari-ruga a makarantu 120 nan da shekarar 2020.

Wasan zari-ruga a makarantu

Hakan ne kuma ya kai ga horar da wasan a wata makarantar firamare ta Islamiyya mai suna Al-Walid da ke unguwar Kanda a birnin Accra.

Wakilinmu Muhammad Fahd Adam ya ziyarci makarantar inda ya tarar dalibai mata na atisaye, a filin wasa na makarantar mai jar kasa, galibinsu sanye da hijabi, wasu da takalmi wasu kuma babu ma takalmin a kafarsu.

Mai horar da su, Rafatu Inusa, ma’aikaciya ce a Hukumar Zari-Ruga ta Ghana ta kuma shaida wa BBC cewa: “Muna so a cikin unguwanninmu da makarantunmu kowa ya rungumi rugby, musamman yara mata saboda rugby wasa ne na kowa da kowa.

“Ba [wasa ne da za a ce mai] jiki ba za ta iya ta bugawa ba, ko [a ce] wata guntuwa ce; [ko] kana da jiki, [ko] ba ka da jiki, kowa na da [rawar da zai taka] a wasan rugby.

“A cikin yaran makarantun mun samu wadanda suke shiga kulob-kulob, don su samu damar buga wa tawagar kasa, don haka…mata duka muna son su rungumi wasan rugby”.

A yanzu haka dai akwai kungiyoyin zari-ruga guda 13 a kasar ta Ghana.

Burin Hukumar Zari-Ruga

Burin Hukumar Kwallon Zari-Ruga ta Ghana shi ne samar da kwararrun ‘yan wasa, musamman mata ‘yan kasa da shekara 14, wadanda za su wakilci kasar a duniya.

Ga alama kuma sai sun dauki hanyar cimma wannan buri, don kuwa ‘yan mata da dama a makarantar Alwalid tuni suka shiga buga wannan gasa ka’in da na’in.

A cewar Zainab Abdulrahman, “Na iya [wasan zari-ruga] sosai; ina so na zama kwararriyar ‘yar wasan rugby”.

Amma ba a nan burinta ya tsaya ba, tana kuma “so in gwada ma yayana da kannena”.

“Wasa ne na maza?”

Wasu dai na ganin kwallon zari-ruga wasa ne na maza majiya karfi, musamman saboda yadda ake turereniya da sheka gudu da sauransu..

Amma wadannan ‘yan mata da suka rungumi wasan sun ce ba haka lamarin yake ba.

A cewar Maimuna Muhammad Dawud, “Ni a ganina ba na maza ba ne [su kadai]; har da mata ma za su iya bugawa.

“Shi yasa nake sha’awarsa, kuma ina buga rugby [saboda] idan ‘yan uwana mata suka gani, za su so su ma su buga.”

To ko me ya sa aka zabi makarantar Islamiyya, kuma ta mata, don koyar da wannan wasa na zari-ruga?

Koci Rafatu, wadda ita ma Musulma ce, cewa ta yi wannan ba abin mamaki ba ne, “Saboda [duk da cewa] yaran musulmi [ne], kar ku duba wai addini kaza kaza…ke mace ki sanya hijabinki, ki tabbatar ko ina naki yana rufe, idan yana rufe babu abin da ba za ki iya yi ba.

“Tun da dai ba ku da maza za ku buga ba—mu mata zallanmu ne—ba [wata] mishkila”.

Hukumar Kwallon Zari-Ruga dai ta ce zuwa yanzu a yunkurin tallata wannan wasa sai hamdala.

A cewar Mista Mensah, “Kamar kowanne shiri, za ka samu nasara ne idan akwai wadanda suka jajirce, kuma tabbas ni na jajirce.

A wannan shekara, a karo na farko, mun kaddamar da league na mata wanda aka samu nasarar kammalawa.

“An samu nasara a bangaren yawan kungiyoyin da suka fafata, an kuma yi nasara dangane da irin mutanen da suke buga wasan daga addinai daban-daban da kabilu daban-daban da sauransu.

“An samu gagarumar nasara saboda wasan ya yi armashi, an bi dokoki, an samu karancin raunuka, [kuma] akwai hamasa sosai, saboda haka abin ya burge matuka”.

Ma’aikaciyar rediyo ta haihu yayin gabatar da shiri


Hakkin mallakar hoto
@radiocassiday/Instagram

Image caption

Cassiday Proctor’s baby boy has been named Jameson

Wata mai watsa shirye-shiryen rediyo a Amurka ta haihu yayin da take gabatar da shiri.

Cassiday Proctor, mai gabatar da shirin safe na ranakun aiki na mako a wata tashar da ake kira The Arch a birnin St. Louis na Amurka, ta watsa labarin yadda aka yi mata tiyatar cire jaririnta a ranar Talata.

Ms Proctor ta fara jin nakudar haihuwa ne tun a ranar Litinin. Gidan rediyon da take aiki sun hada kai da asibitin da ta haihu kan yadda za a watsa yadda haihuwar ta kasance a rediyo.

Ta gaya wa BBC cewa ba su shirya zuwan jaririn ba saboda ya zo makonni biyu kafin lokacin da ake tsammanin sa.

Ms Proctor ta ce ta ji dadin iya bayar da labarin daya daga mafi abubuwan da suka fi sa ta farin ciki a rayuwarta ga masu sauraronta a rediyo.

Ta ce “haihuwa a lokacin da take gabatar da shiri tamkar, “kari ne a kan abun da ta saba yi a ko wacce rana a gidan rediyonmu, saboda kullum ina ba da labarin dukkan rayuwata ga masu sauraro.”

An sanyawa jaririn suna Jameson, bayan da masu sauraro suka zabi sunan jaririn a cikin wata gasa da aka gabatar a rediyon a watan Janairu.

‘Barin malamai su rike bindiga zai magance matsalar harbe-harbe’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Trump ya ce barin malamai su rike bindiga zai kawo karshen matsalar harbe-harbe

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a ganinsa abun da ka iya kawo karshen matsalar yawan harbe-harbe a makarantu a Amurka, shi ne horar da malamai su iya amfani da bindigogi.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da ba a taba yin irinsa ba a Amurka, inda wadanda su ka tsira a harbe-harben da a ka sha yi a makarantu da iyayen wadanda su ka mutu su ka gana da Shugaban ido da ido.

Taron wani yunkuri ne na jawo hankalin shugabannin siyasa su sauya ra’ayi a kan manufofin amfani da bindiga a kasar.

A taron da a ka watsa a gidajen talabijin, daya daga cikin mahaifan wadanda su ka mutu a wani harbi da a ka yi a wata makaranta, ya nuna bacin ransa ga kalaman Mr Trump. Inda ya bayyana su a matsayin masu tsananin rauni.

Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki

Masana sun gudanar da wani bincike da ya tabo fannoni da dama a jami’ar Oxford wanda ya musanta bayanan da ke nuna cewa magungunan warkar da ciwon tsananin damuwa ba sa tasiri.

Binciken mai zurfi ya nuna cewa ashirin da daya daga cikin magungunan sun taimaka wajen baiwa marassa lafiya sauki.

Masu binciken sun duba sama da gwaje-gwaje dari biyar kuma sun hada da wasu bayani da aka yi a baya da wasu kamfanonin magunguna su ka ki fitarwa.

Sakamakon da a ka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya, The Lancet ya nuna cewa magungunan su na tasiri. Haka kuma, kungiyar likitoci masu kula da masu tabin hankali a Birtaniya ta ce binciken zai kawo karshen duk wani rikici.

Rashawa: ‘Har yanzu babu sauyi a Nigeria’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya ce kasa ta 148 daga cikin jerin kasashe 180

Sabon rahoton kungiyar Transperancy International da ke yaki da cin hanci da rashawa a duniya ya ce, har yanzu babu wani sauyi da aka samu a Najeriya a kan yaki da matsalar.

A rahoton da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kasa ta 148 daga cikin jerin kasashe 180 da kungiyar ta yi nazarin girman matsalar a 2017.

Transparency ta ce Najeriya ta samu maki 27 ne kacal daga cikin maki 100 da ya kamata ace kasa ta tsira daga matsalar rashawa.

Rahoton kungiyar ya ce matsalar ta kara tsanancewa a Najeriya ne idan aka kwatanta da alkalumman shekarar 2016 inda kasar ta samu maki 28. kuma a matsayin kasa ta 136 a duniya.

Daga matsayi na 136 a 2016 a bana Najeriya ta koma ta 148 a cewar rahoton.

Rahoton kuma ya ce a Nahiyar Afrika Najeriya ce ta 32 daga jerin kasashe 52 da Transperency ta yi nazari kan girman matsalar rashawa.

A cewar rahoton na 2017, Najeriya ce ta biyu a kasashen da matsalar ta fi yin kamari a Afirka bayan Botswana.

Kungiyar CISLAC reshen kungiyar Transparency International da ke yaki da rashawa a Najeriya ta ce sakamakon rahoton abin damuwa ne.

A wata sanarwar bayan fitar da rahoton, CISLAC ta ce tun hawan gwamnati mai ci a yanzu da ke da’awar yaki da cin hanci da rashawa, babu wani hukunci da aka yanke kan ‘yan siyasar da aka samu da laifin rashawa.

CISLAC ta ce wannan koma-baya ne a yaki da cin hanci da rashawa, kuma hakan ya tabbatar da girman cin hanci da rashawa musamman rashawa a siyasa da alfarma da azurta dangi.

Kungiyar ta ce duk da akwai dubarun yaki da rashawa gwamnati mai ci ta tsara a 2017 da wasu kudururruka da ta yi alkawali a cikin gida da kasashen waje amma har yanzu ba wani abin azo gani da aka aiwatar.

A cikin sanarwar, CISLAC ta bayar da wasu shawarwari da ta ke ganin idan an bi za a iya shawo kan girman matsalar rashawa a Najeriya.

Shawarwarin sun hada da fadada dubarun yaki da cin hanci da rashawa zuwa karkara tare da hada hannu da kungiyoyin fararen hula domin su sa ido tare da aiwatarwa.

Da kafa kotuna na musamman kan yaki da rashawa tare da nada alkalan da aka tabbatar tsabtatattu ne.

Sannan da karfafawa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da kariya ga masu kwarmato da kuma karfafawa kafofin watsa labaru.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan Najeriya sun zabi Buhari don yaki da rashawa

Tun a hawansa kan mulki, shugaba Buhari ya bayyana cewa cin hanci da karbar rashawa ba su da wuri a gwamnatinsa, abin da ya sa wasu ke tunanin zai yi irin ba-sani ba-sabon da ya yi a lokacin yana mulkin soja a shekarar 1984.

Gwamnatin Buhari ta kwato kudade da wasu jami’an gwamnatin da suka gabata suka kwace, sai dai har yanzu babu wanda aka gurfanar a kotu.

Sannan gwamnatin Buhari ta sha musanta zargin cewa ta fi karkatar da yaki da cin hanci da rashawa ga ‘yan adawa, maimakon yakar matsalar da shugaban ya ce ita ce ta hana kasar ci gaba.

A watan Oktoban 2017 ne Buhari ya kori sakataren Gwamnatinsa Babachir Lawal, da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambasada Ayo Oke da aka samu da almundahana.