CHAN: Nigeria za ta kara da Morocco a wasan karshe


Hakkin mallakar hoto
Caf

Image caption

Nigeria za ta kara da Moroccio a ranar Lahadi

Super Eagles ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta yan wasan da ke murza leda a nahiyar da ake kira Chan.

Nigeria ta yi nasarar cin Sudan 1-0 a wasan daf da karshe da ta buga a ranar Laraba.

Super Eagles ta ci kwallo ta hannun Gabriel Okechukwu a minti na 16 da fara tamaula.

Nigeria ta karasa wasan da ‘yan was 10 bayan da aka korar mata Ifeanyi Samuel Nweke, ita ma Sudan an bai wa Bakri Basheer jan kati.

Ita kuwa Morocco nasarar cin Libya 3-1 ta yi.

Za a fara buga wasan neman mataki na uku tsakanin Sudan da Libya a ranar Asabar, sannan a buga wasan karshe tsakanin Morocco da Nigeria a ranar Lahadi.

Nigeria: An sa dokar hana fita a garin Gboko na Benue


Hakkin mallakar hoto
BENUE STATE GOVERNMENT

Gwamnatin jihar Benue wadda take tsakiyar Najeriya ta ce ta sanya dokar hana zirga-zirga daga dare zuwa safiya a garin Gboko daga ranar Laraba.

Gwamnan jihar Samuel Ortom ya ce sun dauki matakin ne saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a yankin, inda ya ce dokar za ta fara aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Daga nan ya bukaci jami’an tsaron da ke jihar musamman ‘yan sanda da sojoji da su dukufa wajen ganin sun tabbatar da tsaro a garin.

A baya-bayan nan rikici tsakanin makiyaya da manoma ya janyo asarar rayuka a jihohin Benue da Taraba da kuma Adamawa.

Rikicin yana daga cikin manyan kalubalen tsaro da kasar yanzu ke fuskanta, baya ga rikicin Boko Haram, da matsalar sacewa da garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka addabi kasar.

Italy da Argentina za su buga wasan sada zumunta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rabon da Italy da Argentina su kara tun a watan Agustan 2013, inda Italy ta ci 2-1

Tawagar kwallon kafa ta Italiya da ta Argentina za su buga wasan sada zumunta a filin wasa na Ettihad a ranar Juma’a 23 ga watan Maris.

Bayan Italiya ta buga da Argentina, kwana hudu tsakani za ta fafata da Ingila a wasan sada zumunta a Wembley.

Italiya ta kasa samun shiga gasar cin kofin duniya a karon farko tun bayan 1958, bayan da Sweden ta doke ta a wasan cike gurbi da suka yi a watan Nuwamba.

Ita kuwa Argentina ta kai gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a bana, tana rukuni da ya kunshi Croatia da Nigeria da Iceland.

Wannan ne karon farko da tawagar kwallon kafar Italiya za ta yi wasa tun bayan da Sweden ta ci ta daya mai ban haushi a wasan cike gurbin shiga gasar kofin duniya da ta yi.

Chelsea ta dauki Olivier Giroud


Hakkin mallakar hoto
ChelseaFC

Image caption

Giroud ya buga wa Arsenal wasa 253 ya kuma ci kwallo 105

Chelsea ta dauki Olivier Giroud daga Arsenal kan yarjejeniyar wata 18, kan kudi fam miliyan 18.

Giroud dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 31, ya bar Arsenal wadda ya yi wa wasa 253 ya ci kwallo 105 tun komawarsa Emirates daga Montpellier kan fam miliyan 12 a Yunin 2012.

Borussia Dortmund ta tabbatar da daukar aron dan wasan Chelsea, Michy Batshuayi wanda zai yi mata wasanni zuwa karshen kakar bana.

Tun farko Arsenal ce ta dauki Pierre-Emerick Aubameyang daga Dortmund wadda ta ce sai ta samu wanda zai maye gurbin Aubameyang kafin ya bar Jamus.

Arsenal ta dauki dan kwallon tawagar Gabon ne, domin ya maye gurbin Alexis Sanchez wanda ya koma Manchester United da taka-leda.

Pillars ta hada maki uku a kan Plateau United


Hakkin mallakar hoto
NPFL Twitter

Image caption

Kano Pillars tana ta uku a kan teburi da maki 11, bayan da ta buga wasa 6

Kano Pillars ta yi nasarar cin Plateau United 2-0 a gasar cin Kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na shida da suka kara a ranar Laraba.

Pillars ta ci kwallayen ta hannun Lokosa a minti na 21 da fara wasa, sannan minti shida tsakani ya kara na biyu a fafatawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano.

Da wannan sakamakon Kano Pillars tana ta uku da maki 11 a kan teburi, ita kuwa Plateau United tana ta biyu da maki 12, Akwa United ce ta daya da maki 13.

Mesut Ozil ya tsawaita zamansa a Arsenal


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ozil ya koma Gunners daga Real Madrid a shekarar 2013

Mesut Ozil ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a Arsenal zuwa shekara uku da rabi.

Ozil mai shekara 29, ya zama dan wasan Arsenal da ke kan gaba wajen karbar albashi mai tsoka, inda zai karbi fam 350,000 a duk mako, bayan an cire haraji.

Dan wasan tawagar Jamus wanda ya saka hannu a ranar Laraba, ya kawo karshen rade-radin da ake cewar zai bar Arsenal, bayan da kwantariginsa zai kare a karshen kakar bana.

Ozil ya buga wa Arsenal wasa 21 a bana, ya ci kwallo hudu ya kuma taimaka aka zura shida a raga, zai kuma bar Gunners a karshen kakar 2021 a sabuwar yarjejeniyar da ya kulla.

Dan wasan ya koma Arsenal daga Real Madrid a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 42.4.

Dortmund ta dauki aron Batshuayi na Chelsea


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Batshuayi ya koma Chelsea daga Merseill a watan Yulin 2016

Borussia Dortmund ta amince ta dauki aron dan kwallon Chelsea, Michy Batshuayi domin ya buga mata tamaula zuwa karshen kakar bana.

Dortmund ta sayar da Pierre-Emerick Aubameyang ga Arsenal, bayan da ta ce sai ta samu wanda zai maye gurbin dan kwallon tawagar Gabon kafin ya bar Jamus.

Watakila Chelsea ta dauki Olivier Giroud daga Arsenal kan yarjejeniyar shekara uku, domin ya maye gurbin Batshuayi.

Kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan tamaula ta Jamus za ta karkare a ranar Laraba da karfe 17:00 agogon GMT.

Batshuayi dan kwallon Belgium ya buga wa Chelsea wasan Premier 32, ya ci kwallo bakwai tun lokacin da ya koma can da taka-leda daga Marseille a watan Yulin 2016

Sanchez zai fuskanci kalubale — Mourinho


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sanchez ya koma United, bayan da Mkhitaryan ya koma Gunners

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce Alexis Sanchez ya kwan da sanin zai fuskanci rashin tarbar girma a duk inda United za ta buga wasa.

Mourinho ya ce watakila magoya bayan Tottenham ba za suyi wa Sanchez tarbar girma ba, a karawar da za su yi a ranar Laraba a gasar Premier wasan mako na 25 a Wembley.

Magoya bayan tamaula sun yi wa dan kwallon Chile ihu a Yeovil a karawar da United ta yi nasara a gasar cin kofin FA.

Sanchez ya koma United daga Arsenal kan yarjejeniyar shekara hudu da rabi, zai dunga karbar fam miliyan 14 a duk shekara bayan an cire haraji.

Manchester United tana ta biyu a kan teburin Premier da makinta 53, ita kuwa Tottenham tana da maki 45 tana ta biyar a kan teburin gasar.

Majalisa ta gargadi ‘yan Nigeria kan amfani da kudin intanet, Bitcoin


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Majalisar dattawan Najeriyar ta nuna matukar damuwarta a kan yadda ake jan hankalin ‘yan kasar don rungumar tsarin amfani da kudin intanet na Bitcoin din, musamman a matsayin wata hanyar zuba jari da ke rubbanya riba cikin sauri.

Majalisar ta nuna damuwar ne bayan wata muhara a ranar Talata a kan wani kudurin da wani dan majalisar, Sanata Benjamin Uwajumogu ya gabatar.

Majalisar ta ce tana sane da cewa jaridar The guardian ta Amurka ta taba wallafa cewa, babban bankin zuba jarin nan na duniya, JP Morgan, ya bayyana cewa kudin gizon ya fi dacewa da masu safarar miyagun kwayoyi kuma ba zai kai labari ba.

Haka kuma babban bankin kasar wato CBN bai amince da amfani da kudin na Bitcoin a hukumance ba, duk kuwa da cewa bankin da kasuwar shunku ta kasa da kuma hukumar inshora na kasa ba su yi wani hobbasa ba na wayar da kan jama’a a kan hadduran da ke tattare da kudin gizon.

Majalisar dattawan ta kuma yi la’akari da cewa a shekarar 2016 miliyoyin ‘yan kasar sun yi asarar, inda har ta kai wasu ma suka rasa jarinsu dungurungum a sanadin tsarin nan na MMM.

Sannan ganin kasar na farfadowa ne daga matsin tattalin arzikin da ta shiga, majalisar ta nuna damuwar cewa tsarin amfani da kudin gizon zai iya mummunan tasiri idan mutane suka yi asarar kudaden shigarsu.

Hasalima dai tsarin zai iya illa ga tattalin arzikin kasar saboda za ta iya asarar kudaden asusun ajiyarta na kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A don haka, wadannan dalilai da ma wasu ne suka sanya majalisar ta bukaci CBN da hukumar inshora ta kasa NDIC, da hukumar wayar da kan al’umma, su yi gagarumar yekuwa ga ‘yan kasar don fadakar da su hadarin da ke tattare da amfani da kudin na Bitcoin.

Haka kuma majalisar ta bai wa kwamitinta kan fannin banki da sauran hukumomin hada-hadar kudade makonni biyu ya yi bincike a kan ko za a iya amfani da Bitcoin wajen zuba jari da hanyoyin da za a iya sa ido a kan masu cinikayya da shi.

Sai dai masu iya magana na cewa abincin wani gubar wani, a yayin da wasu ke dar-dari dn amfani da kudin gizon, wata kungiyar kwallon kafa a Turkiyya ta bugi kirjin zama kungiya ta farko da ta sayi Omer Faruk Kıroglu da kudin na intanet wanda darajarsa ta kai sama da fam 384.

Kuma a baya-bayan nan ne kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shiga wata yarjejeniya ta daukar nauyin da kuma sanya sunan kamfanin kudin intanet na Cashbet a jikin rigar ‘yan wasa.

Me ya sa Turawa ke tururuwar wankan tururin ruwan dumi?


Hakkin mallakar hoto
(Credit: Kristof Minnaert)

Image caption

Kristof Minnaert dan Belgium da yanzu ya samun natsuwa da yin hutu a dakin wankan suracen rufin daki tare da abokan aikinsa na kamfanin sarrafa dabarun wasannin na’ura don nishadi da ke Helsinki

Daga Lennox Morrison

21 ga Oktobar 2016

Sakon Edita (23 ga Disambar 2016): Zuwa karshen wannan shekarar, BBC zai dawo muku da wasu daga jerin labaran da kuka fi sha’awarsu daga 2016

Ba zan taba mantawa da karon farko da na zauna zindir, kugu-da-kugu a kan bencin katako tare da shugaban wajen aikina.

Wannan shi ne makon farko na sabon aikina a kamfanin sarrafa na’urar kwamfuta da ke kusa da Heidelberg a kasar Jamus.

Ni dan asalin kasar Scotland ne, inda gwamutsuwar shakatawar aiki ke nuni da zuwa mashaya. Ban taba mafarkin zan kasance a waje tunbur tare da abokan aikina, balgacen kankara na fadowaa fatata.

A gareni wannan al’ada na da matukar rikirkitarwa. Amma a Jamus da Holland ko Finland ba wani abu ba ne bambarakwai (ko sabon abu zama zigidir tare ) da abokan aiki.

Kuma a Finland al’amari ne da aka yarda da shi ka zauna kugu-da-kugu tare da shugabanka na wajen aiki zindir babu tufafi.

Lamari ne da aka saba da shi ka je ka zauna a dakin surace tare da shugabanka na wajen aiki.

“Finland kasa ce da ba a nuna fifikon matsayi. Ba ma tsaurara tsarin zamantakewa bisa kimar matsayi (fifiko),” inji Katariina Styman, Shugbar kungiyar wankan surace ta Finland da ke Helsinki.

“Lamari ne da aka saba da shi ka zauna tare da shugabanka na wajen aiki. . Wuri da ake watsi da da kimar matsayin aiki ko matakin albashi.

A wannan kasa ta Arewacin Turai da ke da yawan al’umma kimanin miliyan 5.5, akwai gidan surace guda ga kowane rukunin mutane biyu, a cewarta. Mafi yawan kamfanoni suna da gidajen wankan suracensu.

Ka taba yin mamaki ko rikirkicewa ko kaduwa da tsarin al’adun wata kasa ta daban? Baza labarinka a kafarmu don bibiyarsa tare da mu.

Sabanin Jamus, inda ake gwamuwa (maza da mata) a gidan wankan surface, al’adar mutanen kasar Finland ita ce idan ka fita daga da’irar iyalanka – maza da mata sukan ziyarci wajen wankan surface daban-daban.

Ko a hakan ma, sababbin zuwa wadanda ba ‘yan asalin Finland ba a karon farko kasancewa tare da abokan aiki a bukokin shakatawa ba lallai ba ne mutum ya samu cikakkiyar natsuwar hutu yadda ya kamata.

“Lamarin tamkar matakin kaiwa ga gaci ne don shawo kan lamarin.” Inji Kristol Minnaert, dan kasar Belgium da ya koma Helsinki a shekarar 2013 ya kama aiki da kamfanin tsara wasannin na’ura don nishadantarwa.

Dakin shirye-shiryen kamfanin da ofisoshinsa da ke Espoo suna dakin wankan surace a rufinsu. “Sai ka tube zindir sannan ka isa wajen.

Za ka ji an yi maka tsawa ko wulakantaka idan harka daura mayafin wanka (tawul) ko gajeren wandon ninkayar kurme,” a cewar Minnaert, mai shekara 30 babban jami’in fasahar zayyanar wasanni

Bayan shafe shekar auku, sai kawai ya ji ya samu natsuwa, ta yadda kowane yammacin ranar Juma’a sai ya yi wankan surface tare da abokan aikinsa, inda aka saba da surbar barasa sannan a fito waje a tube ba tare da sutura ba.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: The Finnish Sauna Society)

Image caption

Kungiyar masu ta’ammali da gidan surface da ke kusa da birnin Helsinki

Shi da rukunin abokansa sukan shafe tsakanin sa’a guda zuwa uku a dakin wankan surace kowane mako, yayin da ba sa gudanar da taro, sai dai su yi ‘yar tattaunawa kan aiki, a wani lokaci kuma su fito da wata kyakkyawar dabarar aiki da zarar su koma sun zauna kan teburansu.

“Lamarin ya yi dna kwatankwacin zuwa mashaya, amma kadan ake sha, a wurin da ake gumi,” inji shi. “”Ya fi kyau a lokacin hunturun sanyi sabon yanayin kan kai – 30 digiri bisa ma’aunin Salshiyos a wajen farfajiyar. Idan ka koma ciki sai ka kara samun kuzari.

Madallah da gayyatar da shugaban wajen aikinsa ya yi masa, Minnnaert ya kuma shiga kungiyar masu wankan surface ta kasar Finland da ke kusa da Helsinki, inda ake yin al’adar tafasa ruwan zafi maitururi da itace “hayakin dakin surace” ana sanya murhun azurfa da gungumen itace yana kallon ruwan (tekun) Baltic.

A nan ttsofaffin shugabannin kasa da sauran hamshakan mutane ke haduwa a tunbur tare da sauran masu zuwa wankan surace, inda suke samun damar yin tsallen tsundumawa cikin ruwa ko da a lokacin hunturu ne, inda ake huda kafar kankara.

Tommi Uitto, babban jami’in mataimakin shugaban kamfanin hada-hadar kasuwancin kayan sadarwa a kamfanin sadarwar duniya na Nokia, ya bayyana cewa: “A dakin wankan surace babu abin da ke nuni da mukamai, babu sutura.

Ba a nuna jiji da kai, don haka wurin na da mutuntawa, kuma tunaninka da kalmominka aka barka da su, haka lamarin yake ga wani mutumin, ta yadda alakar kawai ta mutum da mutum ce kawai, kuma daukacin wata kawai an kawar da ita.”

Kamfanin Nokia yana da dakunan surace a daukacin rassansa uku dd akle kasar Finnalan. “An ware su,” inji Uitto. “Kowane dan kasar Finland da ya nemi aiki a kamfanin Finland yana sa ran akwai wajen wankan surface a kamfnain.”

Farko fara aikin Uitto an dauki dakin surface a matsayin wajen gudanar da kasuwanci, a cewarsa. Kuma rukunin ma’aikata kan taru gaba daya a dakin surace don bikin murnar samun nasarar kamfanin da koluluwar nasar ko kimar matsayin da ya kai, sabanin zuwa gidan sayar da abinci ko mashaya.

Amma a shekarun baya-bayan nan, sai dai an rage bai wwa gidajen wankan surace muhimmanci, saboda ta wani bangaren kamfanonin Finland sun zama na duniya, sannan harkokinsu na kara cukurkudewa, a cewarsa.

Sannan tun da mata da maza na ziyarar gidajen wankan surace daban-daban, a wajen mutane da dama ba sa jin dadin taruwa don tattunawa kan harkokin kasuwanci.

“Lamarin na nuni da cewa ba daidai ba ne a raba rukunin mutane gida biyu,” in ji Uitto.

Kasan al’adu

Yayayin da gidanjen wankan surrace (saunas) suka shahara a Arewacin Turai, a kasashe irin su Sweden da Rasha da Netherlands al’adu da dabi’u sun yi matukar bambanta.

Jan Feller, mukaddashin manajan Daraktan Cibiyar hadin gwiwar ciniki ta Jamusawa da mutanen Finland da ke Helsinki, ya yi aiki a daukacin kasashen.

A wajen ‘yan Finland, wajen wankan surace wurri ne da kake zuwa a kashin kanka tare da wasu mutane,” a cewar mutumin mai shekara 41.

“A Jamus kuwa al’amarin da ya ta’allaka da kyautata ingancin lafiya.”

A lokuta da daman a sha yin kokarin kare al’aura da ke tsakanin mahadar cunar kafafuna.

A kasar Finland, masu zuwa wankan surace (da tururin ruwan zafi) har kwara wa gawayi ruwa suke yi da kanbsu, amma a Jamus har ma akwai babban jami’i mai kula da wajen wankan surace da ke yin wannan aiki akai- a kai, lokuta daban-daban, a cewarsa.

“Kawai a hakikanin gaskiya za ka samu rubutattun dokoki manne a jikin bango dakin wankan surface a Jamus, al’amarin da idan mutanen Finland sun gani sai dai su yi murmushi kan lamarin,” inji Feller.

A Jamus da Netherland kada ka sa ran samun gidan wankan surace a wajen aikinka.

Sai dai idan kana shiga wajen wasannin motsa jiki bayan an tashi daga aiki tare da abokan aikinka, akwai yiwuwar ka samu wajen wankan surace a wuraren wasannin motsa jiki.

Hakkin mallakar hoto
Hill Creek Pictures

Image caption

Yayayin da gidanjen wankan surrace (saunas) suka shahara a Arewacin Turai, a kasashe irin su Sweden, Rasha da Netherlands al’adu da dabi’u sun yi matukar bambanta

Lokacin da Sam Critchley wanda ya kafa kamfanin tallat ahajar kayan sadarwa na Spaaza ya fara zuwa Amsterdam daga aslain kasarsa ta Birtaniya shekaru 18 da suka wuce ya je yin wasan kwallon squash da abokan aikinsa.

Bayan kammala wasan, kowane (dan wasa) sai kawai ya fi zuwa wajen wankan surface ya tube zigidir. Babu wanda ma ya damu da ko kamfai da ‘yar rigar ninkayar kurme, amma a matsayi na dan asalin Holland (Dutchland) guda sai na far son sanya wani abu. Sai ya zauna a dakin tururin ruwan zafi ya yakice lullubin tawul dinsa, a cewarsa.

“Kwatsam sai wannan mata abokiyar aikinmu ta fito daga wajen suracen ta tambayeni za ka zo cin abinci bayan ka kammala?

Daga nan sia ta bude kofa, inda nike iya ganin abokan aikina mata uku ko hudu a kan bencina suna zaune kan layi,” kamar yadda wnai mai shekara 43 ya tuno da lamarin.

Matakin farko da na dauka shi ne dora hannuna a kan mahadar cunar kafafu.”

Taliban na barazanar mamaye kashi 70 cikin 100 na Afghanistan


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Auliya Atrafi ta je yankin Helmand inda ‘yan Taliban suka fi karfi

Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa mayakan Taliban, wadanda dakarun da Amurka ta kashe makudan kudi don murkushe su, a yanzu haka sun dawo da karfinsu inda suke barazanar mamaye kashi 70 cikin 100 ma kasar.

Watannin da aka shafe ana bincike a fadin kasar ya nuna cewa a yanzu haka Taliban ke iko da ko kima take barazanar mamaye yankuna da dama fiye da lokacin da dakarun kasashen waje suka bar kasar a 2014.

Gwamnatin Afghanistan ta ce rahoton ba abun da za a damu a kansa ba ne, saboda tana iko da yawancin yankunan kasar.

Amma wasu hare-hare da aka kai a baya-bayan, wadanda kungiyoyin Taliban da IS, suka yi ikirarin kai wa sun yi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Kabul da ma wasu wuraren.

Jami’an gwamnatin Afghanistan da Shugaba Donald Trump na Afirka, sun mayar da martani ta hanyar kawar da yiwuwar yin duk wata tattaunawa da Taliban.

A shekarar da ta gabata ne, Mista Trump ya sanar da cewa dakarun Amurka za su ci gaba da zama a kasar har sai baba ta gani.

Binciken BBC din ya kuma gano cewa kungiyar IS ta fi karfi sosai yanzu a Afghanistan fiye da baya, duk da cewa dai karfinta bai kai na Taliban ba.

Yankuna nawa ke karkashin ikon Taliban?

Binciken na BBC ya nuna cewa a yanzu Taliban suna da cikakken iko da gundumomi 13, wato kashi 4 cikin 100 na kasar kenan.

Kusan mutum miliyan 15 – rabin al’ummar kasar -su na rayuwa a yankunan da ko dai suna karkashin ikon Taliban ko kuma Taliban din na kai hare-haerenta a bayyane.

Wani mutum mai suna Sardar da ke zaune a Sardar na gundumar Shindand da ke yammacin kasar, wanda ke fama da hare-haren Taliban duk mako ya ce, “A duk lokacin da na bar gida ba ni da tabbas din cewa zan koma gida a raye.”

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

BBC ta samu damar da ba a cika samu ba inda ta ga yadda rayuwa take karkashin Taliban a Taliban in 2017

Binciken BBC din ya nuna cewa a bayyane yake yanzu Taliban ba a yankin kudancin kasar da a da shi kadai ke karkashin ikonsu kawai suke ba, sun kara dannawa har gabashi da yammaci da arewacin kasar.

Yankunan da suka koma karkashin ikon Taliban tun shekarar 2014 sun hada da na gundumar Helmand irin su Sangin da Musa Qala da Nad-e Ali, amma dakarun kasashen waje sun yi kokarin dawo da su karkashin ikon gwamnati, al’amarin da ya sa Taliban ta rasa karfinta a 2001.

Fiye da sojojin Birtaniya 450 ne suka mutu a Helmand a tsakanin 2001 zuwa 2014.

Image caption

Hedikwatar ‘yan sanda ta Sangin

Su waye ‘yan Taliban?

 • Kungiya ce mai da’awar kafa daular musulunci da ta fara ayyukanta a shekarar 1998 a Afghanistan in 1996, bayan yakin basasar da ya biyo bayan yakin da aka yi tsakanin tsohuwar tarayyar Soviet da Afghanistan, amma rundunar sojin da Amurka ta jagoranta sun tumbuke su shekara biyar bayan nan
 • A lokacin da suke da karfi, sun kaddamar da abun da suka kira tsarin Shari’a kamar kashe mutane masu laifi a bainar jama’a da yanke musu hannaye da haramtawa mata fita bainar jama’a
 • Sun tilastawa maza tsayar da gemu da kuma sa mata rufe jikinsu ruf da hijabi da nikabi; sun kuma haramta kallon talbijin, kida da waka da kuma zuwa sinima
 • Sun bai wa shugabannin al-Qaeda mafaka kafin da kuma bayan an kore su – tun daga lokacin suke yakin da ake zubar da jini har zuwa yau
 • A shekarar 2016, yawan fararen hular da suka jikkata a Afghanistan ya karu – al’amarin da Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakinsa a kan Taliban

Image caption

Yara ma na cikin barazana a Afghanistan

Rundunar sojin Nigeria na gina titi a dajin Sambisa


Hakkin mallakar hoto
Nigerian Army

Rundunar sojin Najeriya ta fara wani aikin gina titi a tsakiyar dajin Sambisa da garuruwan da ke makwabtaka da shi a jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce ta fara wannan aiki ne a kokarin ta na mayar da dajin wajen da mutane za su iya zama da kuma dandalin da sojoji za su dinga atisaye.

Wannan aiki wani bangare ne na ci gaba da kakkabe duk wani abu da bai dace ba a dajin na Sambisa, kamar yadda sanarwar ta ce.

Tuni dai an fara wannan aiki ta hanyar sare daji a hanyar garuruwan Gwoza da Yamteke da Bitta.

Kazalika an kuma fara aikin shimfida titi a hanyar Gwoza da Yamteke da Bitta da Tokumbere, wanda zai mike har zuwa cikin dajin Sambisa.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Army

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Amry

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Army

Akwai ‘yan mata 21m da ‘ba a bukatarsu’ a India


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mawallafa rahoton sun ce ya kamata Indiya ta sake duba halayyar fifita ‘ya’ya maza kan mata

Bukatar da iyaye ke da ita ta samun ‘ya’ya maza a Indiya a maimakon ‘ya’ya mata ya janyo yanayin cewa akwai wasu ‘yan mata miliyan 21 da ba a so a haifesu ba, inji wani rahoton gwamnatin kasar.

Rahoton da ma’aikatar kudade ta wallafa ya nuna cewa iyalai da dama na rika haihuwar ‘ya’ya a jere har sai sun sami da namiji.

Mawallafan rahoton sun kuma ce wannan wani tsari ne na zabar irin jinsin da aka fi so maimakon zubar da ciki, amma sun yi gargadin cewa matakin ka iya rage yawan kayan more rayuwa ga ‘yan mata.

Sun kuma ce, “Fifiko ga samun da namiji abu ne da ya kamata al’ummar Indiya ta sake dubawa”.

Mawallafa rahoton sun gano cewa mata miliyan 63 “sun bace” daga cikin jumillar alkaluman mutanen Indiya.

Sun ce wannan halayyar ta sa ana zubar da cikin ‘ya’ya mata, kuma an fi bai wa ‘ya’ya maza kulawa.

Gwaje-gwaje domin zabar jinsin ‘ya’ya laifi ne a Indiya, amma duk da haka ana gudanar da su.

Wasu daga cikin dalilan da aka fi son ‘ya’ya maza sun hada da:

 • Gado – maza ne kawai ke gadon iyayensu ba mata ba
 • Bukatar iyayen mata su biya sadaki domin aurad da ‘ya’yansu mata
 • Mata na komawa gidan mijin da suka aura bayan aure

Wannan halayyar ta fifita ‘ya’ya maza kan mata ya sa wata jarida ta wallafa wasu dalilai da ba su da tushe a kimiyya, don a sami haihuwar ‘ya’ya maza, inda ta ke ba da shawarar a rika fuskantar yamma a yayin da ake barci, da kuma yin jima’i a wasu ranaku na mako.

Jihohin da wannan lamarin ya fi shafa su ne Punjab da Haryana, inda jihar Meghalaya ce wadda lamarin bai shafa ba sosai.

A jihohin Punjab da Haryana, akwai yara maza da shekarunsu basu wuce bakwai ba ga ‘yan mata 1,000 idan aka kwatanta shekarunsu, in ji mawallafan rahoton.

Kun san shugabannin “bogi” na kasashen Afirka?


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Raila Odinga ya ce yana son kirkiro da dumokuradiyya ta sosai a Kenya

A ranar Talata ne jagoran ‘yan hammayya na kasar Kenya Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, bayan da ya sha kaye a zaben da aka sake gudanarwa a watan Oktobar shekarar da ta gabata.

Ba wannan ne dai karo na farko da wani ya taba rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa ba a nahiyar Afrika bayan shan kaye a zabe.

A wannan makala dai mun kawo muku jerin mutanen da suka taba kokarin rantsar da kansu a matsayin shugabannin kasa a nahiyar.

A Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo akwai Etienne Tshisekedi da Moshod Abiola a Najeriya, da Kiza Besigye na Uganda, da kuma Jean Ping na Gabon.

Wadannan nan daga cikin jagororin hamayya na kasashen Afirka wadanda suka yi kokarin ayyana kansu a matsayin shugabannin kasashensu, bayan kuma a lokacin kasashen suna da shugabanni da ke kan kujera. A ranar talatar nan Raila Odinga, shugaban ‘yan hamayya na Kenya ma ya bi layin wadannan ‘yan siyasa.

A Uganda jagoran ‘yan hamayya na kasar Dakta Kizza Besigye, wanda ya dade yana adawa da Shugaba Yoweri Museveni, ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, inda aka nuna bidiyon rantsuwar da aka yi a wani wuri na sirri a shekarar 2016, kwana daya kafin rantsar da Museveni.

Daga baya an kama shi aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa, inda aka rika gurfanar da shi a gaban shari’a.

Etienne Tshisekedi shi ne shugaban ‘yan hamayya a lokacin mulkin Shugaba Mobutu Sese Seko na Zaire, kasar da shi kuma Laurent Kabila ya sauya wa suna zuwa DRC (Jamhuriyra Dumokuradiyyar Congo), daga baya kuma har zuwa yanzu ta kasance karkashin dansa Joseph Kabila.

Wata kamanceceniya tsakanin Tshisekedi da Odinga ita ce, dukkaninsu an taba tsare su ba tare da an yi musu shari’a ba, sannan kowanne cikinsu ya taba zama Firaiminista, kuma duka sun kaurace wa zaben shugaban kasa; Tshisekedi a 2006 sannan Raila a 2017.

A watan Nuwamba na 2011, Tshisekedi ya yi takara ya kalubalanci dan Laurent Kabila kuma ya zama na biyu a zaben. Daga nan sai ya shirya karbar rantsuwa a matsayin shugaban kasa, a wani biki da ya shirya a garinsu, karkashin shugaban ma’aikatansa Albert Moleka bayan da kokarin ganin an rantsar da shi a filin wasa na Martyr a babban birnin kasar, Kinshasa ya ci tura.

Daga bisani an yi masa daurin talala a gidansa.

A Najeriya, Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa lokacin Sani Abacha na kan mulki. Ya yi hakan ne bayan da ya ziyarci kasashen Turawa na yammacin duniya, yana neman goyon bayansu a kan gwamnatin Abacha. An kama shi aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa, sannan aka yi masa daurin shekara hudu, zuwa shekara ta 1995.

A 2016 a Gabon, shugaban ‘yan adawa Jean Ping ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, kuma ya bukaci da a sake kirga kuri’un zaben shugaban kasar, kirgen da aka sake yi ya tabbatar da Shugaba Ali Bongo mai ci a matsayin wanda ya yi nasara. sai dai duk da haka, Ping ya kafe yana cewa, ”ai duk duniya ta san shi ne shugaban kasar.”

Kalli hotunan abubuwan ban al’ajabin da suka faru a duniya a makon jiya 20 – 26 Janairu


Zababbun hotuna da muka samo daga sassa daban-daban na duniya da aka dauka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto
Ilya Naymushin/REUTERS

Image caption

Hoto daga sama na nuna wata mota tana tafiya a gabar kogin Yenisei, a wajen birnin Krasnoyarsk na kasar Rasha, inda sanyi ya kai kasa da celsius 30.

A view of Mount Mayon volcano. as it erupted, from Our Lady of the Gate Parish church in Daraga, Albay province, south of Manila, Philippines, 25 January 2018.Hakkin mallakar hoto
Romeo Ranoco/REUTERS

Image caption

Dutse mai amon wuta na Mount Mayon ke amon wuta a kasar Philippines, inda ya sa mutum 40,000 suka yi kaura daga muhallansu.

Britain's Duchess of Cambridge, speaks to a patient during a visit to the sensory room of the Mother and Baby Unit at the Bethlem Royal Hospital in south London, Britain, 24 January 2018.Hakkin mallakar hoto
Hannah McKay/REUTERS

Image caption

‘Yar gidan sarautar Ingila, Catherine ta Cambridge ta ziyarci asibitin Bethlem Royal dake kudancin birnin Landan. Catherine na dauke da cikin dan ta na uku, wanda zai zama na uku a masu jiran gadon sarautar Ingila bayan Yarima Charles da Yarima William da Prince George da kuma ‘yar gidan sarauta Charlotte.

Bangladeshi Muslim devotees return home on an overcrowded train after attending the Akheri Munajat in Dhaka, Bangladesh, 21 January 2017.Hakkin mallakar hoto
ABIR ABDULLAH/EPA

Image caption

Musulmi ‘yan kasar Bangladesh na komawa gida bayan sun kammala sallah a rana ta uku da ake gudanar da ibadar Biswa Ijtema a birnin Dhaka babban birnin kasar. Wannan ne taro na biyu a yawan jama’a bayan na aikin Hajji.

Cloned monkeys Zhong Zhong and Hua Hua are seen at the non-human primate facility at the Chinese Academy of Sciences in Shanghai, China,, on 20 January 2018.Hakkin mallakar hoto
China Daily via REUTERS

Image caption

Birrai biyu da masana kimiyya suka samar ta hanyar hada ‘ya’yan halitta a wani dakin bincike. An haifi birran ne masu suna Zhong Zhong da Hua Hua a wani dakin bincike a kasar Sin.

Orla Dean, 5, holds a placard during the Time's Up rally at Richmond Terrace, opposite Downing Street on 21 January 2018 in London, England.Hakkin mallakar hoto
Chris J Ratcliffe/Getty Images

Image caption

Mutane sun taru a daura da titin Downing a ranar farko ta tunawa da macin da mata suka yi a birnin Landan.

Revellers in costumes take part in the traditional "Correfoc" festival in Palma de Mallorca on 21 January 2018.Hakkin mallakar hoto
JAIME REINA/afp

Image caption

Bikin na Carrofec ana yin sa ne cikin dare, kuma ‘yan bikin na shigar dodanni ne inda suke yin fareti a titunan garin suna wasan wuta.

Italy's Federica Brignone competes during the FIS Alpine World Cup Women's Giant Slalom on 23 January 2018 in Kronplatz, Plan de Corones, Italian Alps. Germany's Viktoria Rebensburg won the race ahead of Norway's Ragnhild Mowinckel, and Italy's Federica Brignone.Hakkin mallakar hoto
TIZIANA FABI/AFP

Image caption

Federica Brignone ta kasar Italiya na faftawa a gasar duniya ta kankara a bisa duwatsun Alps na Italiya. Viktoria Rebensburg ta Jamus ce ta yi na daya, kuma ‘yar Norway Ragnhild Mowinckel ce tayi na biyu. Brignone ce ta uku.

A portrait of Robert Burns is projected on to the front of Prestonfield House in Edinburgh on Burns Night, 25 January 2018Hakkin mallakar hoto
Jane Barlow/PA

Image caption

Ga hoton Robert Burns da aka haska a gaban gidan Prestonfield a birnin Edinburgh domin tunawa da rayuwar Burns din. Ana bikin tunawa da Burns a kowace ranar 25 ga watan Janairu musamman rubutattun wakokinsa da shan giyar Whisky.

A starling murmuration near the southern Israeli city of Rahat, in the Negev desert.Hakkin mallakar hoto
MENAHEM KAHANA/afp

Image caption

Wannan hoton tarin tsuntsaye an dauke shi ne a kusa da birnin Rahat na kasar Isra’ila a yankin hamadar Negev. Wannan abin burgewan na faruwa ne a lokacin da dubban tsuntsaye suke shawage a daidai faduwar rana.

Dukkan hotunan mallakin masu su ne.

Saudiyya ta kwato dala biliyan 106


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An tsare mutanen ne a otel din Ritz Carlton da ke Riyadh

Antoni janarar na kasar Saudiyya ya ce gwamnati ta kwato kudi fiye da dala biliyan 106 karkashin shirinta na yaki da cin hanci da rashawa.

Sheik Saud al mojeb ya ce daga cikin mutum 381 da aka kira a watan Nuwamban daya gabata domin an yi mu su tambayoyi, har yanzu ana tsare da 56 daga cikinsu.

Ya ce an wanke sauran daga aikata laifi ya yinda an saki wasu ne bayan da suka amsa aikata laifi tare da mika kadarorinsu da kudi ga gwamnati.

Sai dai Sheik Mojeb be bayanna sunnayen wadanda ake zargi ba , sai dai rahotanni sun ce a cikinsu akwai yarimomi da ministoci da kuma yan kasuwa.

A kwanakin baya bayanan ne aka sako hamshakin dan kasuwanan yerima Alwaleed bin Talal da kuma Alwalid al Ibrahim, wanda ya malaki kafar watsa shirye shirye ta MBC daga otel din Ritz-Carlton da ke garin Riyadh.

Sai dai mutanen biyu sun musanta zargin da ake yi mu su amma kuma wasu majiyoyi na gwamnatin Saudiyyar sun ce mutunen sun yada su bada wasu kudade bayan da suka amince da aikata laifi.

Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Messenger Aika wannan shafi Email Aika

Sauran da ake tsamanin cewa an sakosu sun hada da yerima Mitleb bin Abdullah wanda da ne ga mariyagi sarki Abdullah wanda majiyoyin suka ce ya mika kadarori da aka yi kiyasin cewa adadinsu ya wuce dala biliyan daya da kuma Ibrahim al Assaf wanda minitsa ne wanda kuma rahotani suka ce ba a same shi da laifi ba.

Sai dai Sheik Mojen ya ce ya ki cimma masalaha da sauran mutane 56 da ake tsare da su saboda binciken da ake cigaba da yi akansu game da zargin cin haci da rashawa.

Ana dai tsamammin cewa an wuce da su zuwa wani gadan yari daga otel din Ritz Carlton da ake tsare da su wanda zaa sake bude wa a watan gobe. A makon daya gabata ne dai ministan kudi na kasar Mohammed al Jadaan ya ce za a yi amfani da kudaden da aka kwato a wani shiri da aka ware ma kudi dala biliyan 13 domin tallafawa yan saudiyya samun saukin tsaddar rayuwar.

Sai dai wasu masana sun soki shirin yaki da cin hanci da rashawa na Yerima mai jiran gado Mohammen bil Salman mai shekara 32 wanda da ne ga sarki Salman, inda suka bayana shi a matsayin wani shiri na neman iko.

Ko daya ke yerima Mohammed din ya ce da dama daga cikin wadanda ake tsare sun yi ma sa muba’ya’a tun bayan da aka nada shi yerima mai jiran gado a watan yunin daya gabata.

Ko kifi zai iya maye gurbin nama?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kifi na neman yafi nama saukin samu da saukin farashi a Najeriya

A yayin da fulani makiyaya ke fuskantar matsaloli, masu su da kuma kiwon kifi a Najeriya, na ganin da sannu a hankali kifi zai iya maye gurbin nama a kasuwanni da ma gidaje.

Alhaji Sani Usman Rilwanu, shi ne shugaban kungiyar masu kiwon kifi a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, a yanzu mutane da dama sun shiga harkar kiwon kifi.

Don haka kifi ke wadata sosai fiye da nama.

Ya ce, wani abu kuma da ya ke gani zai sa kifi ya fi nama wadata a ko ina, shi ne kifi daya zai iya kyankyashe dubu biyar ko ma fiye da haka, amma dabba ita haihuwarta ba ta wuce daya ko biyu sai lokaci-lokaci ake samun wacce zata haifi uku.

Don haka bisa la’akari da yawan kifin da ake kyankyashewa da kuma yadda a yanzu dabbobi ma ke nema su yi wuya, kifi ya maye gurbin nama, domin yafi nama saukin samu da saukin farashi.

Shi ma wani mai sayar da kifin a Kadunan, yace “A yanzu ko ba nama, su masu sayar da kifi zasu rike masu cin naman da kifi saboda wadatarsa”.

Kiwon kifi dai a yanzu na samar wa da matasa da dama aikin yi a jihohin Najeriya.

‘Facebook ba wurin kananan yara ba ne’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bincike da dama na nuna tababar amfanin shafukan sada zumunta da muhawara ga lafiyar yara

Sama da kwararru 100 na lafiyar yara na bukatar hukumar shafin Facebook ta janye manhajar da ta kirkiro ta amfanin yara ‘yan tsakanin shekara 13.

A wata budaddiyar wasika da suka aika wa shugaban Facebook Mark Zuckerberg, kwararrun sun kira manhajar mai suna ”Messenger Kids” a matsayin wani yunkuri da bai dace ba na karfafa wa yara amfani da Facebook.

Masanan suka ce lokaci bai kai ba da yara za su mallaki shafukan sada zumunta da muhawara nasu.

Hukumar ta Facebook ta ce an tsara manhajar ne tare da shawarar kwararru kan kariya ga miyagun abubuwa, kamar yadda iyaye suka bukata kan yadda za su kasance da iko da kuma sanin abin da ‘ya’yansu ke yi a shafukan sada zumunta da muhawara.

Manhajar samfurin Messenger ta Facebook an saukakata ba kamar ta manya ba, kuma tana bukatar a samu izinin iyaye kafin a yi amfani da ita, sannan bayanan da ake samu daga cikinta ba za a iya amfani da su ba wajen talla.

Budaddiyar wasikar na dauke da bayanin da ke cewa: “Manhajar ”Messenger Kids” za ta iya kasancewa shafin sada zumunta da muhawara na farko da yara da yawa ‘yan tsakanin shekara hudu zuwa 11 za su yi amfani da shi.

Bayanin ya kara da cewa bincike da aka gudanar kuma har yanzu ake kara zurfafa shi ya nuna cewa yawan amfani da waya da kwamfuta da sauran na’urori ire-irensu da kuma shafukan sada zumunta da muhawara na da illa ga yara da matasa, wanda hakan ke nuna cewa wannan manhaja za ta iya haifar da matsala ga bunkasar lafiyar yara.

Ya ce, “A takaice kananan yara a yanzu ba su da bukatar samun shafukan sada zumunta da muhawara na kansu.”

“Girmansu bai kai yadda za su iya shiga da jure matsalolin da ke tattare da mu’amullar da ke a shafukan sada zumunta da muhawara ba, abubuwan da kan kai hatta manya ma ga sabani da rikici.”

Sai dai a martanin da Facebook ya yi kan wannan korafi ya ce: “Tun lokacin da muka kaddamar da manhajar a watan Disamba, mun samu sakonni daga iyaye cewa manhajar ta Messenger Kids ta taimaka musu kasancewa da ‘ya’yansu ta intanet, kuma ta taimaka wajen sada ‘ya’yansu da danginsu na kusa da na nesa.

“Misali, mun samu bayanai cewa iyayen da suke aikin dare sun samu damar kasancewa da kananan ‘ya’yansu ta manhajar har suna musu tatsuniya kafin ‘ya’yan su yi barci su kuma sun abakin aiki, sannan iyaye mata da suke zuwa aiki wani gari suna samun bayanai kullum daga ‘ya’yansu kan halin da suke ciki.”

Wasikar ta bukaci sanin ko akwai bukatar Facebook ya gamsar da wannan bukata, inda ta ce: “Batun wai ana iya magana ko sadarwa tsakanin abokai ko iyaye da ‘ya’ya daga wurare masu nisa wannan ba ya bukatar lalle sai an samu wannan manhaja ta ”Messenger Kids”.

“Yara za su iya amfani da shafin iyayensu na Facebook ko Skype ko wasu shafukan su tattauna da su. kai za ma su iya amfani da waya kawai.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akwai binciken da ke nuna cewa akwai alaka tsakanin yawan amfani da shafukan sada zumunta da matasa ke yi da kuma matsalar damuwa

Wasikar ta bayar da misalai na bincike da nazarce-nazarce da aka yi da dama da ke nuna alaka tsakanin yawan amfani da matasa ke yi da shafukan sada zumunta da damuwa da kuma zakuwa ko ci-da-zuci.

“Matasan da suke yin akalla sa’a daya kullum suna amfani da shafukan sada zumunta da muhawara kan yi korafi da rashin gamsuwa da kusan dukkanin wani fanni na rayuwar da suke ciki.

“Matasa ‘yan makaranta da ke tsakanin shekara 13 zuwa 14, wadanda suke amfani da shafukan sada zumunta da muhawara tsawon sa’a shida zuwa tara a mako, kusan kashi 47 cikin dari ba sa cikin farin ciki kamar takwarorinsu wadanda ba sa yawan amfani da shafin kamarsu akai akai.

Wasikar ta kuma bayar da misalin wani nazari a kan wasu yara ‘yan mata masu shekara 10 zuwa 12 wadanda ke damuwa da kibarsu wadanda bincike ya nuna za su iya neman kwaikwayon hanyoyin rage kiba ta intanet.”

Sauran alkaluma na bincike da wasikar ta kawo misali da su sun hada da:

 • Kashi 78 cikin dari na samari suna duba wayarsu kusan duk bayan sa’a daya
 • Kashi 50 cikin dari sun ce sun kamu da jarabar amfani da waya
 • Rabin yawan iyaye sun ce kokarin hana ‘ya’yansu yawan amfani da waya ko intanet abu ne da suke fama da shi kullum

Kwarrarun sun kuma karyata ikirarin hukumar Facebook cewa manhajar ta ”Messenger Kids” na samar da dama maras matsala ga yaran da suke bayar da shekarun karya domin samun shiga shafukan sada zumunta da muhawara, ta hanyar nuna cewa su manya ne.

Kwararrun suka ce: “Yara ‘yan shekara 11 zuwa 12 wadanda a yanzu suke amfani da shafin Snapchat ko Instagram ko Facebook ba lalle ba ne su koma kan wata manhaja wadda aka yi ta domin yara.

“Manhajar Messenger Kids ba wai magance wata matsala take yi ba, sai ma dai a ce wata sabuwar matsalar ta kawo,” in ji masanan.

Kungiyoyin jin dadin yara daban-daban ne suka sanya hannu a kan wasikar, babba daga cikinsu ita ce ta ”Campaign for a Commercial-Free Childhood”. Sauran sun hada da ”Massachusetts American Civil Liberties Union” da ”Parents Across America”.

Akwai kuma wasu daidaiku da su ma suka rattaba hannu, wadanda sun hada da ”British scientist Baroness Susan Greenfield”.

Gwamnatin Birtaniya ta zauna da kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara da kuma masu yin manhajoji da kwamfuta da sauransu, irin su Apple a watan Nuwamba na 2017 inda ta bukace su da su duba wasu jerin batutuwa kamar:

 • Yadda za a hana kananan yara shiga wadannan shafuka
 • Mene ne cin zarafi ta intanet da yadda za a magance shi
 • Ko akwai yadda za a iya kirkiro wata alama ta gargadi ga matasa waddda za ta rika bayyana a duk lokacin da wani matashi ya dade yana amfani da intanet

Swansea ta bar ta karshe bayan da ta ci Arsenal


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Swansea City ta ci Liverpool 1-0 a wasan mako na 24 a gasar ta Premier

Swansea City ta ci Arsenal 3-1 a gasar Premier wasan mako na 25 da suka kara a ranar Talata.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Nacho Monreal minti 33 da fara tamaula, sai dai kuma minti daya tsakani Swansea ta farke ta hannun Sam Clucas.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Swansea ta kara na biyu ta hannun Jordan Ayew kuma daf da za a tashi daga karawar Sam Clucas ya ci na uku, kuma kwallo na biyu da ya ci.

Da wannan sakamakon Swansea wadda ta yi wasa 25 ta koma ta 19 da maki 20, yayin da West Brom wadda ta yi wasa 24 ta koma ta 20 da maki 20.

West Ham United da Crystal Palace tashi suka yi kunnen doki 1-1.

Ita kuwa Liverpool cin Huddersfield 3-0 ta yi.

Za a ci gaba da wasa a ranar Laraba:

 • Chelsea da Bournemouth
 • Everton da Leicester City
 • Newcastle United da Burnley
 • Southampton da Brighton & Hove Albion
 • Manchester City da West Bromwich Albion
 • Tottenham Hotspur da Manchester United
 • Stoke City da Watford

CHAN: Nigeria za ta kara da Sudan a wasan daf da karshe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a buga wasan karshe a ranaer Lahadi, kafin nan za a yi wasan neman mataki na uku a ranar Asabar

Tawagar kwallon kafar Nigeria za ta kara da ta Sudan a wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta ‘yan wasan da ke murza-leda a nahiyar wato Chan a ranar Laraba.

Tun kafin wasan Super Eagles da Sudan, mai masaukin baki Morocco ce za ta kece-raini da Libya a Casablanca.

Morocco ta kai wannan matakin bayan da ta ci Namibia 2-0, ita kuwa Libya Jamhuriyar Congo ta ci 5-3 a bugun fenariti, bayan da suka tashi kunnen doki.

Nigeria kuwa ta kai wasan daf da karshe ne, bayan da ta doke Angola 2-1, ita kuwa Sudan, Zambia ta ci daya mai ban haushi.

Duk wadda ta yi nasara za ta buga wasan karshe a ranar Lahadi, yayin da za a fafata a wasan neman mataki na uku a ranar Asabar.

Tsoro ne ya hana Kwankwaso zuwa Kano – Gwamnatin Kano


Hakkin mallakar hoto
Facebook/Kano State Govt

Image caption

Ganduje ya kasance abokin tafiyar Kwankwaso a baya, amma yanzu ba sa ga-maciji

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi watsi da hanzarin da tsohon gwamnan jihar Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya gabatar, cewa magabata ne suka shawo kansa har ya janye aniyarsa ta ziyartar Kanon.

A ranar Talata ne aka tsara Kwankwaso zai kai ziyarar don halartar wani gangami, ziyarar da ta zo daidai da wani taron bangaren gwamnatin Jihar ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba sa ga-maciji da juna, lamarin da ya jefa al`umma cikin fargabar barkewar yamutsi.

A hirarsa da BBC kwsamishinan watsa labaran jihar, Mallam Mohammed Garba ya sheda wa wakilinmu Ibrahim Isa cewa barazana ta fi yawa a cikin al`amarin Sanata Kwankwaso, don haka bai yi mamakin soke ziyarar tasa ba:

Latsa alamar lasifika da ke kasa domin sauraron hirar

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kwamishinan watsa labaran jihar Kano Mohammed Garba

An haramta hawa mota a wasu yankunan Borno na mako daya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An haramta zirga-zirgar ababen hawa na fararen hula a kan titunan da suka ratsa wasu garuruwa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na wani dan lokaci.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da watsa labarai da al’adu Mohammed Bulama, ta ce an dauki matakin ne saboda tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu a jihar, bisa shawarar da Kwamandan Rundunar Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ya bayar.

Titunan da aka sanya wa haramcin yin zirga-zirga a kansu sun hada da wadanda suka ratsa daga garin Konduga zuwa Bama da Banki da Gwoza har Maiduguri daga Moloi, sannan zuwa Dambuwa da Gwoza.

Haramcin ya rafa aiki ne a ranar Litinin 30 ga watan Janairu, kuma zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairu.

Gwamnatin jihar ta bai wa al’ummomin yankin hakuri a kan duk wani matsi da hakan zai jawo musu, ta kuma ce kula da tsaron al’umma da kokarin dawo da zaman lafiya yankin su ne manyan burikanta.

Sanarwar ta kara da cewa, sakamakon ci gaba da matsawa kungiyar Boko Haram lamba da sojojin kasar ke yi, ya sa mayakan na neman tsira ko ta halin ka-ka, tare da kokarin yin badda kama suna shiga yankunan fararen hula.

A don haka ne gwamnatin ta bukaci jama’a da su kara sa ido sosai wajen lura da abubuwan da ke faruwa a kewayensu, tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yar da da shi ba ga hukumomin da suka dace.

Jihar Borno dai ta shafe kusan shekara tara tana fama da rikicin kungiyar Boko Haram, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Sai dai a baya-bayan nan rundunar sojin kasar ta ce tana dakile karfin kungiyar ta yadda a yanzu ba sa iya kai manyan hare-hare da manyan makamai, sai dai harin kunar bakin wake.

Sanchez zai buga wa United Premier ranar Laraba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester United tana ta biyu a kan teburin Premier

Ana sa ran Alexis Sanchez zai buga wa Manchester United wasan Premier na farko a karawar da za ta yi da Tottenham a Wembley a ranar Laraba.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Chile ya buga wa United wasan zagaye na hudu a kofin FA da ta doke Yeovil a ranar Juma’a tun komawar sa daga Arsenal.

Babu wasu ‘yan wasan da suka ji sabon rauni a United, hakan na nufin Zlatan Ibrahimovic da kuma Eric Bailly ne suke yin jinya har yanzu.

‘Yan wasan da ake sa ran za su buga wasan United:

De Gea da Romero da Young da Jones da Smalling da Lindelof da Valencia da Shaw da Rojo da Darmian da Matic da Pogba da kuma, Blind.

Sauran sun hada da Fellaini da Carrick da Herrera da McTominay da Martial da Rashford da Lingard da Mata da Sanchez da kuma Lukaku.

Ahmed Musa ya koma CSKA Moscow


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ahmed Musa ya ci kwallo uku a wasa 33 da ya buga wa Leicester City

Dan wasan Leicester City, Ahmed Musa ya sake komawa CSKA Moscow domin ya buga mata wasanni aro zuwa karshen kakar shekarar nan.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, mai shekara 25 ya koma Leicester City daga CSKA kan yarjejeniyar shekara hudu kan fam miliyan 16 a matsayin wanda aka saya mafi tsada a kungiyar a Julin 2016.

Sai dai dan wasan ya kasa tabuka abin azo a gani tun lokacin da ya koma Ingila da murza-leda, inda ya ci kwallo uku a wasa 33 da ya buga wa Leicester City.

CSKA ta ce za ta saka sunan Musa a cikin ‘yan wasan da za su buga mata gasar cin Kofin Europa a karawar da za ta yi nan gaba.

Man City ta dauki Laporte mafi tsada a kungiyar


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Man City tana tra daya a kan teburin Premier ta kai wasan karshe a League Cup

Manchester City ta dauki dan kwallon tawagar Faransa mai tsaron baya, Aymeric Laporte daga Athletic Bilbao kan fam miliyan 57 a matsayin mafi tsada da ta saya a tarihi.

Laporte wanda har yanzu bai buga wa babbar tawagar Faransa tamaula ba, shi ne wanda aka dauka mafi tsada a Janairu, kuma kawo yanzu kungiyoyin Premier sun kashe fam miliyan 252 wajen daukar ‘yan kwallo a watan.

Bayan da City ta sayi Laporte mai shekara 23, Pep Guardiola ya kashe kudi fam miliyan 215.5 wajen daukar masy tsaron baya da mai tsaron raga tun daga karshen kakar bara.

Dan kwallon da City ta saya mafi tsada a tarihi a baya shi ne Kevin de Bryne kan fam miliyan 55 a shekara 2015.

Laporte mai tsaron baya daga tsakiya ya buga wa matasan tawagar Faransa ‘yan 21 wasa 19.

Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban Kenya


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Magoya bayansa sun fara taruwa domin a rantsar da madugun ‘yan adawa Raila Odinga a matsayin “shugaban kasa”

An rantsar da madugun ‘yan adawa a Kenya, Raila Odinga a matsayin ‘shugaban kasa na jama’a’ – duk da gargadin da gwamnatin kasar ta yi na cewa matakin – cin amanar kasa ne.

Mista Odinga ya yi rantsuwar dauke da koren baibul a gaban dubban magoya bayansa da suka taru a dandalin Uhuru Park da ke Nairobi, babban birnin Kenya.

Mista Odinga ya sha kaye a hannun Shugaba Uhuru Kenyatta a zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen shekarar da ta gabata.

Amma shi da magoya bayansu sun yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben.

Uhuru Kenyatta ya sake lashe zaben Kenya

Kalli yadda ake zabe a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Daruruwan mutane sun taru domin kallon bikin, amma wasu mazauna birnin Nairobi sun zabi su ki fita zuwa wajen aiki domin suna tsoron barkewar tashin hankali.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya fada wa kafofin watsa labarai da kada su nuna bikin, inda har aka rufe wasu tashoshin talabijin.

Mista Odinga ya ce haramcin da aka sanyawa kafafen watsa labaran ya nuna cewa mun bi sahun kasar Uganda, wacce ta hana watsa zabukan da aka gudanar a kasar a 2016.

Kazalika Shugaba Kenyatta ya zargi Mista Odinga da cin amanar kasa.

Sai dai cacar-bakan da aka yi tsakanin su bai hana tururuwar mutane zuwa dandalin Uhuru don shan rantsuwar mulkin Mista Odingan ba.

An yi mummunar gobara a Kenya

An kama mutumin da ya yi jima’i da akuya a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Magoya bayan Raila Odinga na gamayyar jam’iyyun siyasa na NASA suna fareti a cikin shirye-shiryensu na rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a Nairobi

Jiragen yaki sun kashe fararen hula 35 a Nigeria — Amnesty


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hare-haren sojin sun lalata gidaje da dama

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta ce hare-haren jiragen yakin Najeriya sun kashe fararen hula 35 a watan Disambar da ya gabata na 2017.

Kungiyar ta ce jiragen yaki sun harba rokoki a kauyukan Lawaru da Dong da Shafaron da Nzuruwei a jihar Adamawa domin dakile fada tsakanin manoma da makiyaya.

A kalla kauyuka takwas ne wadannan hare-haren suka lalata.

Sai da kuma duk da haka ba a samu sauki fada tsakanin makiyaya da manoma ba a jihar Adamawan.

Rikicin manoma da makiyaya ya kashe mutum 168 a jihohin Adamawa da Benue da Ondo da kaduna a wannan watan na Disamba.

Duk da haka, Amnesty ta ce matakin da gwamnatin Najeriya ke dauka “bai isa ba kuma a wasu lokutan yana saba wa doka.”

Aikin da sojin saman kasar ta yi ranar 4 ga watan Disamba ya biyo bayan hare-haren da makiyaya suka kai kauyuka biyar bayan an kashe musu mutum 51 a watan Nuwamba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin sama ta Najeriya, Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya shaida wa kafafen watsa labarai na kasar cewa hare-haren saman da rundunar ta kai na gargadi ne ba da niyyar kisa ba.

Ya kara da cewa hare-haren sun sa mutane sun tsere daga wajen kuma sun samar da tasiri mai kyau.

Amma Amnesty tana kira ga gwamnatin Najeriya da ta fitar da bidiyon yadda ta kai harin.

A shekarar da ta gabata, fada tsakanin makiyaya da manoma ya yi sanadin mutuwar mutum 549 tare da raba dubban mutane da muhallansu a fadin Najeriya.

An yi wa jaririya ‘yar wata takwas fyade a India


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

There is growing anger in India against rape and sexual violence

An yi wa wata jaririya ‘yar wata takwas fyade a Delhi babban birnin Indiya, inda ake zargin wani dan uwanta, abokin wasanta ne ya yi mata.

Rahotanni sun ce a yanzu haka yarinyar tana cikin mawuyacin halin a asibitin da aka kai ta bayan da ta samu munanan raunuka a ranar Lahadi.

‘Yan sanda sun shaida wa manema labarai cewa sun kama matashin da ake zargi da aikata laifin mai shekara 28.

Kwamishinar kula da al’amuran mata ta Delhi wati Maliwal, wacce ta ziyarci jaririyar a asibiti ranar Litinin da daddare, ta bayyana irin raunukan da ta gani a jikin yarinyar da cewa abun tsoro ne matuka.

Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi, amma sai a ranar Litinin ne kafofin yada labarai suka samu labarin.

Ms Maliwal ta aika da sakon Twitter cewa, sai da aka yi wa yarinyar tiyata ta tsawon sa’a uku.

Yadda fyade da kisan ‘yar shekara 6 ya harzuka India

Mata ta gantsara wa mai fyade cizo a mazakuta

India: Kotu ta yarda a zubar da cikin ‘yar shekara 13 da aka yi wa fyade

Ta kara da cewa: “Kukan da jaririyar ke yi mai tsinka zuciya ya karade daukacin wajen kula da marasa lafiya na musamman na asibitin.

“Ta smau munanan raunuka ta ciki da wajen jikinta.”


Sharhi daga Geeta Pandey, BBC News, Delhi

Irin wannan lamari mai muni na cin zarafin yara ya girgiza Indiya, kuma irin raunukan da jaririyar ta ji sun bai wa mutane da dama tsoro da har wasu ke tunanin ko an zo wani zamani ne da mutane ke abu tamkar dabbobi.

Sai dai wani kiyasi da gwamnati ta fitar ya nuna cewa ba a faye samun irin wannan mugun laifi ba.

Sai dai abun damuwar shi ne yadda a baya-bayan nan haka ke dan karuwa.

Wata kididdiga daga hukumar tattara bayanan laifuka ta kasa ya nuna cewa a shekarar 2016, an samu laifukan yi wa yara kanana fyade da aka yi rijistarsu har sau 19,765 a Indiya – abun da ya karu da kashi 82 cikin 100 daga 2015, inda a lokacin aka samu laifuka 10,854.

Shekaru biyu da suka gabata ma wani mutum ya sace jaririyar makwabciyarsa ‘yar wata 11, yayin da take bacci a gaban mahaifiyarta, ya kuma shafe sa’a biyu yana mata fyade.

Sannan kuma a watan Nuwambar 2015, an sake sace wata jaririyar aka kuma ci zarafinta ta hanyar yi mata fyade a birnin Hyderabad na kasar Indiya.


Ms Maliwal ta sake wallafa wani sakon Twitter tana bayyana bakin cikinta.

“Me za mu yi? Ta ya ya za a iya bacci a Delhi a yau bayan da aka yi wa jaririya ‘yar wata takwas fyade.

“Yanzu rashin tausayinmu har ya kai haka, ko kuwa kawai mun karbi hakan ne a matsayin kaddara?”

Ta kuma wallafa wani sakon inda take rokon Firai Minista Narendra Modi da cewa “ana bukatar a tsaurara dokoki a kuma kara samar da karin ‘yan sanda don kare yara mata da ke kasar.”

An ci gaba da samun karuwar fyade a Indiya ne tun bayan da wasu gungun mutane suka yi wa wata daliba mai shekara 23 fyade a motar bas cikin shekarar 2012 a Delhi babban birnin kasar.

Wannan al’amari ya jawo an shafe kwanaki ana zanga-zanga, aka kuma tursasawa gwamnati samar da wasu dokoki masu tsaurari dangane da fyade, da suka hada da kashe duk wanda aka kama da laifin.

Sai dai hakan bai hana ci gaba da samun karuwar yi wa mata da kananan yara fyade ba a fadin kasar.

An dage dokar hana wa baki musulmi shiga Amurka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu ‘Yan kasashen za su fuskanci bincike mai tsanani kafin shiga Amurka

Kasashe 11 da gwamnatin Trump ta haramta wa shiga Amurka, yanzu suna iya shiga kasar bayan dage haramcin.

Sai dai kuma ‘yan kasashen da gwamnatin Trump ta kira masu hadarin gaske, yanzu za su fuskanci bincike mai tsanani.

Sakatariyar tsaron kasa Kirstjen Nielsen ta ce duk wanda ya nemi shiga Amurka zai fuskanci sabbin matakan tsaro.

Ta ce abu ne mai muhimmaci su tantane duk wanda zai shiga kasar.

“Matakan tsaron da aka dauka za su yi wahala ga bata-gari, kuma matakai ne da za su tabbatar da tsaron kasa”, a cewar Jami’ar.

A watan Oktoban bara ne gwamnatin Trump ta sanar da haramtawa ‘yan gudun hijira daga kasashen musulmi 10 da kuma Koriya ta arewa shiga Amurka.

Tun daukar matakin, ‘yan gudun hijira 23 ne kawai daga kasashen suka shiga kasar, lokacin da alkalin wata kotu ya dage haramcin.

Ko da yake ba a ambaci sunayen kasashen da matakin yanzu ya shafa ba, amma tuni ya yi tasiri ga ‘yan gudun hijirar kasashen Masar da Iran da Iraqi da Libya da Mali da Koriya ta arewa da Sudan ta kudu da Sudan da Syria da Yemen.

Fursunoni 430 sun samu shiga jami’a


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An bai wa fursunoni 430 guraben karatun digiri daban-daban a jami’ar karatu daga gida ta Najeriya (NOUN) domin su inganta rayuwarsu.

An kuma sallami wasu fursunonin 951 bayan da wasu masu ruwa da tsaki kan gyara ga gidajen yari suka tallafa musu.

A cikinsu akwai fursunoni uku da suke dab da kammala karatun digirinsu na uku a wasu jami’o’in Najeriya.

An kyale fursunonin su ci gaba da karatun jami’a ne, a wani bangare na gyare-gyaren da gwamnatin Najeriya ke yi ga ayyukan shari’a, musamman ma na inganta rayuwar fursunoni.

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta najeriya Mista Francis Enebore ne ya bayyana wannan a Abuja yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai.

Ya kuma sanar da wani taro da babban daraktan hukumar gyara ga gidajen yari na kasa, Dr. Uju Agomoh ya halarta cewa an sallami fursunoni 951 bayan da suka cika dukkan ka’idojin da aka gindaya masu.

‘Abin da ya sa aka zabi Buhari jagoran yaki da rashawa na Afirka’


Image caption

Buhari ya ce cin hanci babbar barazana ne ga tsaron kasa da hadin kanta da kuma rayuwar kasashen Afirka da al’ummarta

Gaba dayan nahiyar Afirka na kallon kyawawan matakan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke dauka na yaki da cin hanci da rashawa, kuma kasashen nahiyar na son su yi koyi da kasar a wannan fanni.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban na Najeriya a kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu shi ne ya bayyana haka da cewa wannan ne dalilin da ya sa kungiyar tarayyar Afirka, AU, ta nada shugaban a matsayin jagoran yaki da cin hanci da rashawa na Afirka.

A ranar Litinin din nan ne a wurin taron shugabannin kungiyar a birnin Addis Ababa na Habasha, inda hedikwatar kungiyar take, Shugaban na Najeriya ya kaddamar da shirin yaki da cin hanci da rashawa na Afirka.

Daman tun a ranar Juma’a bayan da Buhari ya je taron na shugabannin kungiyar ta AU karo na 30, kakakin nasa a yayin wani taron manema labarai ya bayyana cewa Shugaban zai kaddamar da shirin tare da bude tambarin shirin yaki da rashawar na Afirka.

Mallam Garba Shehu ya ce, Shugaba Buhari ya shirya sosai domin taron na shugabannin Afirka na wannan karon wanda ke karewa ranar Litinin din nan, wanda aka yi wa take da sunan,” Nasara a Yaki da Cin Hanci da Rashawa: Hanya mai Dorewa ga Bunkasar Afirka.”

“Kasancewar nahiyar ta ga cewa samun nasara a yaki da cin hanci da rashawa shi ne zai kai ta ga samun kyakkyawan sauyin da zai kai ta ga cigaba, kuma ganin cewa kusan babban abin da Shugaba Buhari ya sa a gaba kenan wanda kuma yake samun gagarumar nasara, shi ya sa kungiyar ta Afirka ta ga abin ya zo daidai da manufarta.”

“Wannan ne ya sa kungiyar ta ba Shugaban na Najeriya ya cancanci ya jagoranci manufar tata, in ji Garba Shehu.

A yayin jawabin da Shugaba Buhari ya gabatar ga taron shugabannin Afirkar, bayan ba shi matsayin na jagoran shirin yaki da cin hanci da rashawar, ya yi alkawarin yin iya bakin kokarinsa domin ganin shirin kungiyar ta AU ya samu nasara da yin tasiri a shekara ta 2018 da ma bayanta.

An yi mummunar gobara a Kenya


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani mutum na neman ruwan da zai kashe gobarar

An bayar da rahoton cewa dubban mutane ne suka rasa gidajensu bayan da wata gobara ta mamaye gidajen unguwar marasa galihu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum hudu.

Mazaunan yankin sun yi amfani da ruwan amfaninsu na yau da kullum a kokarin da suke na kashe gobara, wacca ta mamaye gidajensu da ke yankin Lang’ata a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin, Nixon Korir ya ce, babu wadataccen ruwa ne a injin da ake amfani da shi wajen kashe gobarar.

Wutar ba ta daina ci ba sai da misalin karfe 06:00 na safiyar Litinin agogon kasar.

‘Yan sanda sun fara gudanar da bincike game da gobarar wacce ta fara ci da misalin karfe 8:00 na ranar Lahadi, inda ta shafe sa’a goma tana ci.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mutane sun yi amfani da ruwan da suke amfani da shi a gida wajen kashe gobarar

Ba wannan ne karon farko da aka rasa ruwa a injin kashe gobarar ba.

Kuma idan za a zuba a ruwa a cikin injin sai an yi tafiya mai nisan kilomita 20 daga yankin Kijiji kafin a dawo cikin garin.

Pius Masai shi ne shugaban hukumar kula da annoba ta kasa, ya ce, yankin ba su abin kashe gobara.

Mazaunan yankin sun shiga tashin hankali, inda suke amfani da duk wani da hannunsu zai kai wajen kashe gobarar.

Wanda ya hada da ruwan da suke amfani da shi a gida na yau na kullum.

Injinan kashe gobara hudu kawai a kai musu. Wanna kuwa ya yi kadan a yankin da aka bayar da rahoton kusan mutum 6,000 suka rasa muhallansu.

An samu tambayoyi da dama da suke cewa me ya sa hukumomi ba su tura wadansu karin injinun ba.

Sojin kasar Kenya sun saba kai wa farar hula dauki a lokacin da wata annoba ta taso.

Amma a wannan lokacin sojoji ba su kai dauki, kodayake barikin sojin Langata na da tazara kadan daga yankin.

Sai dai ba a san dalilin rashin zuwansu wannan lokacin ba, alahali za su iya hango tashin gobarar daga inda suke.

Barca ta yi wasa 21 ba a doke ta ba a La Liga


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 57

A ranar Lahadi Barcelona ta ci Deportivo Alaves 2-1 a wasan cin Kofin La Liga, hakan ne ya sa kungiyar ta yi wasa 21 ba tare da an doke ta ba a gasar a bana.

Hakan kuma ya sa ta yi kan-kan-kan da tarhin da Pep Guardiola ya kafa a kungiyar na yin wasa ba a ci Barcelona ba a 2009/10.

Sai a wasan mako na 22 ne Atletico Madrid ta doke Barcelona 2-1 karkashin Guardiola wanda hakan ya kawo karshen wasa 21 da aka kasa cin kungiyar.

Kocin da ke jan ragamar Barcelona a yanzu Ernesto Valverde ya yi nasarar wasa 18 da canjaras uku, sannan ya ci kwallo 59 aka zura 10 a ragar kungiyar da yake jagoranta a kakar nan.

Barcelona za ta ziyarci Espanyol a wasan La Liga na mako na 22 a wasan hamayya a ranar 4 ga watan Fabrairu.

Kungiyar da ke Camp Nou ta taba yin wasa 31 a gasar ba tare da an doke ta ba a 2010/11 karkashin Pep Guardiola tun daga mako na uku zuwa na 33.

Real Sociedad ce ke rike da tarihin wasa 32 ba a doke ta ba a La Liga da ta kafa a 1979/80.

”United ba za ta hana Ibrahimovic barin ta ba”


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester United tana ta biyu a kan teburin Premier

Jose Mourinho ya ce Manchester United ba za ta hana Zlatan Ibrahimovic barin Old Trafford ba idan har ya bukaci hakan.

Ana alakanta dan wasan mai shekara 36, wanda bai buga wasan karshe bakwai na United ba a bara, sakamakon raunin da ya yi cewar zai koma Amurka da taka-leda a kungiyar Los Angeles Galaxy.

Ibrahimovic ya tsawaita zamansa a Old Trafford zuwa shekara daya a bara, amma wasa bakwai ya buga a kakar bana.

Mourinho ya ce ”Zlatan yana cikin yarjejeniyar shekarar karshe a United, amma bai ce min komai ba kan batun, amma idan har da gaske ne yana son gwada sa a to ba za mu hana shi ba”.

Kocin ya ce Ibrahimovic dan kasar Sweden bai sheda masa cewar yana son barin Manchester United ba.

Kwankwaso ya fasa zuwa Kano


Image caption

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya fasa kai ziyarar da ya shirya kaiwa Kano gobe Talata.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda kauce wa rikicin siya da ka iya biyo bayan ziyarar ta sa, kamar yadda Alhaji Rabi`u Sulaiman Bichi, magana da yawun bangaren kwankwasiyya ya shaida wa BBC.

Dan siyasar ya ce ya samu shawarwari daga bangarori da dama kan ya janye kai ziyarar.

A ranar Jumma’a ce rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta shawarci tsohon gwamnan da ya soke ziyarar da ya yi niyyar kai wa jihar a ranar Talata 30 ga watan Janairu, saboda barazanar tashin hankalin da za a iya samu.

Akwai sabani mai tsanani tsakanin tsohon gwamnan da gwamna mai ci Abullahi Ganduje wadanda a da su kayi tafiya daya a siyasance.

Zuwan Kwankwaso Kano na da hadari —’Yan sanda

Ba abin da zai hana ni zuwa Kano — Kwankwaso

Yadda aka sace wa wata kurma jaririnta a Kaduna


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An sace jaririn wata mata kurma wadda mijinta kurma ne bayan an yi wa matar tiyatar haihuwa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Lamarin dai ya faru ne a asibitin dan tsoho da ke cikin birnin Kaduna.

Shugaban kungiyar guragu na jihar Kaduna, Rilwanu Muhammad Abdullahi, ya ce kungiyarsu na zargin wata mata wadda take haba-haba da kuramen a lokacin da aka kai ta asibiti da sace jaririn.

Da aka yi wa kurmar aiki sai aka bai wa mijin kurmar, wanda shi ma kurma ne, ya je ya sayo mata magani.

Ana ba shi takardar maganin da zai sayo din kuwa, sai shi mijin kurmar ya yanke jiki ya fadi.

Kuma da hankalin mutane ya koma kan mijin, sai wata mata wadda ta yi kamar tana taimaka wa kuramen ta tafi. Kuma daga nan aka nemi jaririn aka rasa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, Aliyu Mukhtar, ya shaida da wa BBC cewar a iya binciken da rundunar ta yi, ma’aikatan asibitin ba su da laifi cikin lamarin satar jaririn.

Sai dai kuma, rundunar ta ce tana iya kokarinta wajen samun wannan matar wadda ta zo ta yi wa iyayen jaririn da aka sacen hidima domin gano inda yaron yake.

Sace-sacen mutane dai a jihar ta Kaduna an fi yi ne domin garkuwa da mutane da zummar neman kudin fansa.

Hakkin mallakar hoto
NIGERIA POLICE

Image caption

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Idris Kpotum ya kafa runduna ta samusamman kan dakile sace-sacen mutane

Me ya sa Jay-Z da Trump ba su dasawa?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jay-Z ya dade yana adawa da Trump

Shugaban Donald Trump ya mayar wa Jay-Z da martani bayan mawakin na Amurka ya bayyana shi da cewa “kamar kudin cizo ne da ba ya jin magani”.

Jay-Z ya soki Trump ne domin nuna rashin jin dadinsa da yadda shugaban ke nuna wariya ga Amurkawa tsiraru.

A sakon martani da ya wallafa a shafin Twitter, Mista Trump ya ce ” alkalumman da aka ruwaito sun nuna ba a taba samun raguwar rashin ayyukan yi tsakanin bakaken fata ba kamar yanzu”.

An samu raguwar rashin ayyukan yi ga Amurkawa bakaken fata da kashi 6.8, adadi mafi kankanta da aka taba samu.

Sai dai kuma wasu da ke sukar gwamnatin Trump sun ce ci gaban ya samo asali ne tun a gwamnatin toshon shugaban kasa Obama, kuma rashin ayyukan yi ga bakaken fata ya fi yawa fiye da fararen fata.

A Kafar CNN Jay-Z ya mayar da martani da cewa mayar da hankali ga batun matsalar rashin ayyukan yi ba shi ne abin dubawa ba.

Ya ce ba kudi ba ne damuwar, domin ba a iya auna girman farin-ciki da kudi. “girmama mutane a matsayin ‘yan adam, shi ne ake magana”, a cewar Jay-Z.

Mawakin dai ya marawa Barack Obama baya ne a lokacin shugabancinsa, sannan ya fito ya goyi bayan Hillary Clinton da Donald Trump ya kada a zaben 2016.

Najeriya: Fulani sun yi zargin kashe musu shanu sama da 200


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Rikicin Fulani makiyaya da manoma ya kara ta’azzara a kwanakin nan a Najeriya

Fulani a garin Kadarko da ke karamar hukumar Keana ta jihar Nassarawa a Najeriya sun yi zargin cewa an kashe musu shanu sama da 200 tare da sace wasu daruruwa, sannan kuma ba su ga wasu mutanensu ba, sakamakon wani hari da suka ce an kai musu wayewar garin ranar Asabar.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar, wadda ke tsakiyar kasar, ta ce adadin bai kai haka ba, a yayin da zaman dar-dar ya sanya wasu al’ummomi barin gidajensu a yankin na Kadarko, wanda ke daf da kan iyaka da Binuwai, jihar da take fama da rikicin makiyaya da Manoma.

Fulanin sun sheda wa BBC cewa maharan sun shafe kimanin sa’a uku suna karkashe dabbobi a rugage sama da 15, ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.

Daya daga cikin Fulanin Mallam Ibrahim Adamu ya kara da cewa bayan ta’annatin ne sai maharan suka yi awon gaba da saniya 560, kuma 120 daga ciki nasa ne.

Ya yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga Binuwai daya daga cikin jihohin da suka fi fama da rikicin makiyaya da manoma.

Ibrahim Adamu ya ce an kai musu harin ne a Kadarko bayan sun guje wa rikici da dokar hana kiwon sake da aka kafa a jihar Binuwai.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Ana zargin Fulani makiyaya da bannata gonakin manoma, yayin da su kuma kan ce suna daukar matakan kare kansu ne da dukiyarsu

Ana dai zargin Fulani makiyaya da shiga gonakin jama’a da dabbobinsu har ma kuma su rika kai hari kan masu gonakin.

Yayin da su kuma makiyayan ke zargin mamaye burtalai da manoma ke yi har ma da satar musu dabbobi da suke korafi a kai.

A martaninta rundunar ‘yan sandan jihar ta Nassarawa ta ce a iya saninta saniya 73 aka kashe kuma an jikkata 18 amma an yanka daya daga bisani a cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, Idrisu John Kennedy

BBC ta tuntubi wani jagoran kabilar Tibi a yankin na Kadarko Mista Chahu Titus kan zargin da wasu Fulani ke musu cewa mutanensu ne suka kai harin, sai ya ce ba za su iya gaskata ikirarin ba, don kuwa babu wata kwakkwarar shaida kan haka.

Mista Titus ya kara da cewa ; “kamar yadda na fada mutane shida ne da aka kawo harin duka-duka aka ce sun bata, amma daga baya mutum hudu sun dawo gida, biyu ne kadai har yanzu ba za mu iya cewa ga inda suka shiga ba. Amma dai mun riga mun fara bincike a kan maganar.”

Rikicin Makiyaya da Manoma dai ya zame wa Najeriya alakakai, inda lokaci-lokaci bangarorin kan zargi juna da far wa dan’uwansa.

Su kuwa hukumomi a kullum cewa suke sun dukufa wajen lalubo maganin rikice-rikicen, wadanda ke kara wargaza kan al’ummomin da tsawon lokaci a baya ke zaune lafiya cikin mutunci da juna.

BBC sun ci wa Real Madrid kwallo 400


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga da maki 38

‘Yan wasan Real Madrid uku da ake yi wa lakabi da BBC wato Karim Benzema da Gareth Bale da kuma Cristiano Ronaldo sun ci wa kungiyar kwallo 400.

Kawo yanzu Cristiano Ronaldo ya ci 225, shi kuwa Benzema ya zura 99, yayin da Gareth Bale ya ci 76, jumulla 400.

Ronaldo ya koma Real Madrid a 2009 inda ya yi wasa 281, shi ma Benzema a 2009 ya je Santiago Bernabeu inda ya yi wasa 258, shi kuwa Bale a 2013 ya tafi Spaniya zuwa yanzu ya buga karawa 110.

A ranar Asabar Real Madrid ta je ta doke Valencia 4-1, inda Ronaldo ya ci biyu, sai Toni Kross da Marcelo kowannensu ya ci daidai.

Real Madrid mai kwantan wasan La Liga daya tana ta hudu a kan teburi da maki 38, za kuma ta ziyarci Levante a wasan mako na 22 a ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu.

CHAN: Nigeria ta kai wasan daf da na karshe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nigeria za ta buga wasan daf da karshe da Sudan a ranar Laraba

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta kai wasan daf da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta ‘yan wasan da ke taka leda a nahiyar da ake yi a Morocco.

Nigeria ta kai wasan zagayen gaba ne, bayan da ta doke Angola da ci 2-1 a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Angola ce ta fara cin kwallo ta hannun Vladimir Etson Antonio Felix, bayan da aka koma daga hutun da kungiyoyin suka yi.

Super Eagles ta farke ta hannun Anthony Okpotu daf da za a tashi daga fafatawar.

Hakan ya sa aka tafi karin lokaci, inda Nigeria ta kara na biyu ta hannun Gabriel Okechukwu wanda hakan ya kai Super Eagles wasan daf da na karshe a gasar.

Nigeria za ta buga wasan daf da na karshe da Sudan a ranar Laraba a filin wasa na Marrakech.

Ka san tsibirin da Faransa da Spaniya ke karba-karbar mallakarsa duk wata shida?


Hakkin mallakar hoto
Alamy

Image caption

Ba mutumin da ke zaune a tsibirin na Faisans da ke iyakar Faransa da Spaniya a Kogin Bidasoa

A mako mai zuwa ne Faransa za ta mika wani sashe na kasarta mai fadin murabba’in sama da kafa 32,000 ga kasar Spaniya ba tare da wani yaki ba. Amma kuma bayan wasu watanni shidan ita ma Spaniya za ta sake dawo wa da Faransar wannan yanki bisa radin kanta.

Kamar yadda Chris Bockman ya hada mana wannan rahoton haka kasahen biyu ke karba-karbar mallakar wannan yanki sama da shekara 350, wanda tsibiri ne da ke tsakanin kasashen biyu.

Wurin shakatawa na bakin teku na Hendaye shi ne gari na karshe da ke kan iyakar Faransa da Spaniya. A lokacin sanyi duk da tsananin huturu za ka ga gwanin ban sha’awa halittun ruwa sun baibaye rairayin bakin tekun.

Daga ‘yar tazara kadan sai garin nan mai tarihi na Hondarribia na Spaniya, da kuma can gefe daya da makwabcinsa wato garin Irun.

Iyakar da ke tsakanin wadannan garuruwa ita ce ta kogin Bidasoa, wanda ruwansa ya raba kasashen na Turai biyu.

Idan ka yi tafiya daga bakin kogin, sai ka ga yanayinsa ya sauya. Kana tafiya sai ka ga gine-gine masu ban sha’awa har ka daina ganinsu sai kuma manyan gidajen ajiya na masana’antu a bangarin kasar ta Faransa, yayin da a bangaren kasar Spnaiya kuwa za ka ga dogayen gidajen jama’a.

Hakkin mallakar hoto
Google

Image caption

An fafata yaki tsakanin Faransa da Spaniya a kan mallakar tsibirin, wanda aka yi yarjejeniyar sulhu a shekarar 1659

To amma ni duka ba wadannan na zo na gani ba, abin da na yo takakakka dominsa shi ne tsibirin Faisans. Ba abu ne mai sauki ba gano wannan wuri, saboda kusan duk wanda na tambaya, ba wanda ya san dalilin da ya sa nake son zuwa can. Sai kawai su ce min, ”ba wani abin kallo a can, saboda ba wani mutum da ke zaune yake rayuwa a can, ba wani wurin yawon bude idanu ba ne kamar tsaunin Mont St Michel.”

Duk da haka shi wannan wuri yana nan yadda yake, tsibiri ne a tsakiyar kogi tsakanin wadannan kasashe biyu, shiru kake ji ba wata hayaniya a cikinsa, ga bishiyoyi da kuma ciyayye da aka gyara su da kyau, da kuma wani tsohon gini na tarihi inda aka yi wata yarjejeniyar sulhu ta tarihi a shekarar 1659.

Tsawon wata uku kasashen Spnaiya da Faransa suka yi yarjejeniyar kawo karshen yakin da suka dade suna fafatawa tsakaninsu a kan tsibirin, inda a karshe aka ayyana shi a matsayin yankin da ba wanda zai mallake shi dindindin a tsakaninsu. An yi gadojin katako daga bangaren kasashen biyu zuwa cikin tsibirin, yayin da dakarun kowace kasa suka zauna cikin damara a lokacin da aka fara tattaunawar.

A karshe dai an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya wadda aka yi wa lakabi da yarjejeniyar Pyrenees. A bisa yarjejeniyar aka shata iyaka, sannan kuma aka tsara yin karba-karbar iko da yankin. An kammala yarjejeniyar ne da kulla auren saraki, tsakanin Sarkin Faransa Louis na 14 wanda ya auri ‘yar Sarkin Spaniya Philippe na hudu.

Na koma PSG don na kafa tarihi — Neymar


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

PSG ce ta daya a kan teburin gasar cin kofin Faransa

Dan kwallon tawagar Brazil, Neymar ya ce ya koma Paris St-Germain ne domin ya kafa tarihi, kuma yana jin dadin taka-leda a Faransa.

A labarin da jaridar Marca ta wallafa ta ce Neymar ya saba jin rade-radi a koda yaushe, saboda haka ba bakon abu bane a wajensa.

Dan kwallon ya kara da cewar duk lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo sai an saka sunansa, babu abinda ba a ce a lokacin da yake Barcelona ba.

Neymar wanda ya koma PSG a matsayin mafi tsada a tarihi a bana, ya ci kwallo biyu a karawar da PSG ta doke Montpelier a gasar cin Kofin Faransa da suka buga a ranar Asabar.

A wasan ne Edison Cabani ya kafa tarihin dan wasan da yafi ci wa PSG kwallaye, sai dai Neymar ya ci gaba da buga wa kungiyar fenariti.

A baya can an samu takaddama kan wanda zai dunga buga wa PSG fenariti tsakanin Edison Cabani da Neymar.

Daga baya aka bukaci su sasanta a tsakaninsu, kuma hakan bai yi wu ba, har sai da kocin kungiyar ya bai wa Neymar alhakin buga fenariti a PSG.

Afirka a makon nan cikin hotuna


Zababbun hotunan al’amuran da suka faru a Afirka a makon nan.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani dan Zimbabwe na shan ruwa a wani famfon tuka-tuka a Chegutu, mai nisan kilomita 100 daga yammacin Harare babban birnin kasar.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani kifi ya fara bushewa a gefen wani kogi da ke lardin yammacin Cape a Afirka ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani yaro mai yi wa coci hidima na fesa wa mabiya addinin Kirista abin da suke kira “ruwan rahama”, lokacin bikin murnar ‘Epiphany’ a Addis Ababa

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu ‘yan matan da suke yin hidima a coci ma sun halarci taron bikin

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani yaro rike da kyandir lokacin murnar bikin a Addis Ababa.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Yan Afirka na gudanar da zanga-zanga game da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na fitar da ‘yan gudun hijirar Afirka dsa masu neman mafaka daga kasar.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wata mata na rataye atamfa a babban birnin Abidjan Ivory Coast.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wasu ‘yan kasar Ghana masu nakasa na gudanar da gasar (IFSS) a babban birnin kasar Accra.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani mutum na hura kaho a wajen rantsar da fitaccen tsohon dan kwallo George Weah a matsayin shugaban kasar Laberiya

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani dan kasar Togo ya yi wa jikinshi fenti da launin tutar kasar inda suke zanga-zanga don nuwa bukatarsu ta kawo karshen mulkin shugabana kasar .

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wasu mata a Kenya nayin zanga-zanga a kan zargin da ake yi na yi wa wasu mata mazu jego fyade a wani babban asibitin kasar.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Biyu daga cikin dalibai 14,000 da suka kammala karatun digiri a jami’ar Makerere da ke Kampala, babban birnin Uganda

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mutum-mutumin King Ramses II wanda ya yi kusan shekara 3,000. A nan ga shi a kan hanyar zuwa gidan adana kayan tarihi a Masar

Buhari ya gana da Obasanjo a Addis Ababa


Hakkin mallakar hoto
Twitter/@MBuhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo a birnin Addis Ababa yayin da ake bude babban taron Kungiyar Afirka, wato AU na 2018.

Shugabannin sun gaisa kuma sun yi magana da juna na kimanin minti biyu.Tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar, wanda shi ma yana halartar taron ya dauki hoto tare da shugabannnin biyu.A makon jiya ne tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wata wasikar wadda a cikinta yake kira ga shugaba Buhari da kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.Obasanjon ya kuma tuhumi Buhari da kasa farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma nuna fifiko ga wasu na kusa da shi.

‘Iyayena ne suka kashe mijina’


Hakkin mallakar hoto
NATHAN G

Image caption

Kausalya ta yanke gashin kanta bayan an kashe mijinta

A watan Mayun 2016 ne aka kai wa wani matashi mai shekara 22 hari har sai da ya mutu da tsakar rana a wani babban titi mai cike da hada-hada a kudancin Indiyasaboda ya auri ‘yar babban gida. Matar ta shi ta tsallake rijiya da baya, ta kuma bayar da tabbacin cewa iyayenta na da hannu a cikin lamarin.

A ranar da zai mutu, Shankar da Kausalya sun tashi ne da misalin karfe tara na safe a gidan da suke da zama, bayan wata takwas da aka daura musu aure.

Ranar kuwa Lahadi ce, inda suka shiga motar haya suka tafi wata kasuwa a Udumalpet mai nisan kilomita 14.

Sun tafi ne da niyyar saya wa Shankar kayan sakawa, wanda zai saka ya halarci wani taron makarantarsu da za a yi washegari.

A lokacin da suka isa shagon sayar da kayan rana ta take. Sai ta zabo wa mijin nata riga ruwan hoda wacce take ganin ita ce zata fi dacewa da shi.

A lokacin da suke fitowa waje ne, sai Shankar ya dauko wata riga koriya da aka rataye a tagar shagon.

Sai ya ce, “Ina ganin wannan zata fi mini kyau”.

“Sai muka koma cikin shagon muka musaya ruwan hodar da koriyar, bayan mun fito ne muka fara tattaki ta wata hanya mai cunkosu inda zamu shiga motar da zata mayar da mu gida. Dama tun da farko Shankar ya shaida min washegari yana so mu sayo wani cincin da nake matukar so,” inji ta.

Kudin Indiya Rupee 60 kawai ne da ita , kuma ba zai ishesu ba.

Saboda haka sai suka yanke shawarar su koma gida sai Shankar ya yi mata alkawarin zai dafa mata abinci mai dadi na musamman.

Kyamarorin tsaro sun nuna cewa ma’auratan na cikin tafiya inda suka nufi kan babbar hanyar. Sai dai kafin su tsallaka ne sai wasu maza biyar suka tunkarosu.

Hudu daga cikinsu suka far musu da wasu dogayen wukake.

“Me yasa kike sonsa? Saboda me?”, inji daya daga cikin wadanda suka kai musu harin.

Image caption

Babbar hanya ce mai cike da hada-hada

“Ma’aikatan lafiya sun samu yanka 34 a jikin Shankar, inda ya mutu sakamakon razana da kuma yankan wuka da dama hade da raunuka da ya samu.”

Kausalya ta shafe kwanaki a asibiti, inda aka nannnade fuskarta da bandeji, kuma tana jinyar dinki 36 da aka yi mata, da kuma karaya.

Tana kwance a gadon asibiti ne ta shaida wa ‘yan sanda cewa iyayenta ne suka kai musu harin.

Image caption

Kausalya lokacin tana jinya a asibiti

Ana kiran Shankar da “Dalit” ma’ana shafaffe da mai, kuma mahaifinsa talaka ne wanda yake aikin leburanci a gona, su hudu suke zaune a daki daya a kauyen Kumaralingam.

Ita kuwa Kausalya ‘yar babban gida ce, mahaifiyarta kuma mai shekara 38 na da motocin haya kuma tana bayar da bashin kudi, wacce suke zaune a wani gidan bene mai hawa biyu a wani karamin birni da ke Palani.

A lokacin da ta shaida wa iyayenta tana so ta zama ma’aikaciyar jirgin sama, sai suka nuna rashin amincewarsu, inda suka ce,”Ba zamu yarda ki dinga saka guntun siket ba”.

Bayan ta kammala makaranta a 2014, sai suka kai ta gidan kakanninta don ta hadu da mazan da suke son aurenta.

Da ta ki amincewa ne sai suka tura ta wata makarantar koyar da kimiyyar na’ura mai kwakwalwa.

Ba ta son makarantar.”An hanamu abubuwa da dama. Ba zamu fita wajen makarantar ba, ba zamu yi magana da maza ba. A aji ma mata da maza dabam-dabam ke zama.

Ko a motar makaranta ma wurin zamanmu dabam da na maza. Idan masu tsaronmu suka ga munyi magana da maza sai su fada wa iyayenmu. An takuremu matuka”, inji ta.

Ranar da aka yi wani taron gabatar da sabbin dalibai ne Shankar ya gabatar da bukatar soyayyarshi ga Kausalya.

Da farko ba ta amsa masa ba, inda ta ba shi shawara da ya nemi wata.

Daga nan Shankar bai kara mata maganar soyayya ba, sai suka ci gaba da gaisawar mutunci amma daga baya kuma sai soyayarsu tayi karfi.

Hakkin mallakar hoto
NATHAN G

Daga wannan lokacin ne suka fara tadi ta wayar salula, da kuma musayar sakonni.

Wata rana a watan Yulin 2015 yaron motar makarantarsu ya gansu suna tadi, sai ya nemi gidan iyayenta ya fada wa mahaifiyarta.

A yammacin ranar kuwa iyayenta suka kwace wayarta, kuma suka kira Shankar suka yi masa gargadin cewa ya fita daga harkar ‘yarsu. Sun kuma shaida mata cewa “Shankar zai iya yi mata ciki ya gudu”.

Washegari kuwa suka dauketa daga makarantar.

Haka ta kwana tana kukan bakin ciki, da safe ta tashi gidan ba kowa, iyayenta duk sun fita. Ta shiga neman wayarta, sai kuwa ta samota, ta kira Shankar ta shaida masa cewa sun samu sabani da iyayenta.

Daga nan ta bukaci cewa su shirya yadda zasu gudu.

Shankar ya fada mata cewa “Idan kina ganin hakan shi ne mafita, ko yanzu ma zamu iya guduwa mu je muyi aure”.

Daga nan kuwa sai Kausalya ta hada kayanta ta fice daga gidan.

Washegari kuwa suka tafi wurin bautarsu aka daura musu aure. Sannan kuma suka tafi ofishin ‘yan sandan da ke kusa, suka bayar da rahoton aurensu don a ba su kariya.

Hakkin mallakar hoto
The News Minute

Image caption

Mahaifin Kausalya (wanda aka yanke mishi hukuncin kisa), da kuma mahaifiyarta wacce kotu ta saki)

Iyayenta da ‘yan uwanta sun yi kokarin su rabasu ta karfi, inda suka kai korafi ofishin ‘yan sanda cewa Shankar ya sace ‘yarsu.

Bayan mako daya da auren nasu kuma suka dauketa suka kai ta wani wuri don su tilasta mata rabuwa da mijinta.

Amma duk abin da suka yi bai yi tasiri haka suka hakura Shankar ya dauketa suka koma gida.

Daga nan ne iyayenta suka ce zasu ba shi kudin Indiya Rupee miliyan daya don ya rabu da ita amma ya ce ba ya so.

Kausalya ta ce, “Mako daya kafin kashe shi iyayenta suka je gidanta suka ce mata ta bi su su tafi gida. Amma sai naki amincewa.”

Kafin su fita daga gidan sai mahaifinta ya ce, “Daga yau duk abin da ya sameki ba ruwanmu”.

‘Yan sanda sun gano cewa mahaifinta ya yi hayar maza biyar, ya ba su Rupee 50,000 don su kashe mijin ‘yarsa.

An samu mutum 120 da suka bayar da shaidar ganin kisan. Ita kanta Kausalya sau 58 tana kin amincewa da bayar da belin iyayenta a kotu.

Kausalya ta shaida wa alkali cewa,”Mahaifiyata ta sha yi min barazanar za ta kasheni, ta ce mutuwata ta fi alheri da na auri Kanshar”.

Hakkin mallakar hoto
NATHAN G

Image caption

Kaushlaya na kada gangar gargajiya wacce mijinta yake bugawa

A watan Disamba ne alkali Alamelu Natarajan ya yanke wa wasu maza shida hukuncin kisa ciki har da mahaifin Kausalya.

Amma kotu ta wanke mahaifiyarta da wasu mutum biyu. sai dai Kausalya ta shirya daukaka karar inda ta yi amannar cewa mahaifiyarta ma na da hannu a cikin lamarin.

Kausalya ta ce bayan an kashe mijinta ta ti yunkurin kashe kanta sau da dama.

Yanzu kuma ta shiga yin aikin zagaye yankin Tamil Nadu, inda take wayar da kai akan wannan mummunar al’ada ta hana auren wadanda ba su da karfi, tare da nuna muhimmancin soyayya.

“So abu ne daga Allah, kuma gamon jini ne, kuma idan so ya shiga zuciya fitarshi abu ne mai wahala, kuma ya kamata mata su tashi tsaye wajen yaki da wannan al’adar, don kawo karshenta”, inji ta.

Sai dai mutane da dama ba sa son wannan gangami da take yi, inda wasu ma suke mata barazanar mutuwa a shafinta na Facebook, saboda haka ne ma jami’an tsaro suke kula da lafiyarta.

Chelsea ta kai wasan gaba a kofin FA


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chelsea tana ta uku a kan teburin gasar Premier bayan wasa 24

Chelsea ta kai zagaye na hudu a gasar cin Kofin FA, bayan da ta doke Newcastle United da ci 3-0 a karawar da suka yi a Stamford Bridge a ranar Lahadi.

Chelsea ta ci kwallo biyu ta hannun Michy Batshuayi a minti na 31 da kuma na 44, sannan Marcos Alonso ya ci na uku bayan da aka dawo daga hutu.

A makon jiya ne Arsenal ta fitar da Chelsea a gasar League Cup wasan daf da karshe.

Chelsea tana ta uku a kan teburin Premier da maki 50, bayan wasa 24 da ta kara a gasar.

A ranar Laraba Chelsea za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasan mako na 25 a gasar ta Premier.

‘Yan Barcelona 18 da za su kara da Alaves


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga bayan wasa 20 da ta yi a gasar

Kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana ‘yan wasa 18 da za su kara da Deportivo Alaves a gasar La Liga a Camp Nou a ranar Lahadi.

A wasan farko da Barcelona ta ziyarci Alaves a kakar bana ta ci 2-0 a karawar da suka yi a ranar 26 ga watan Agustan 2017.

Sabbin ‘yan wasan Barcelona, Philippe Coutinho da kuma Yerry Mina suna cikin ‘yan kwallon da kocin ya bayyana.

Sai dai kuma Denis Suarez da Gerard Deulofeu suna cikin ‘yan kwallon Barca da ke yin jinya da suka hada da Ousmane Dembele da kuma Thomas Vermaelen.

Ga jerin ‘yan wasa 18 da za su fuskanci Alaves.

Ter Stegen, Semedo, Piqué, Rakitic, Sergio, Iniesta, Luis Suárez, Messi, Cillessen, Coutinho, Paulinho, Paco Alcácer, Jordi Alba, Digne, Sergi Roberto, Aleix Vidal, Umtiti and Yerry Mina.

”City ba za ta iya sayen fitattun ‘yan wasa 22 ba”


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester City tana ta daya a kan teburin Premier ta kai wasan zagaye na biyu a Kofin Zakarun Turai

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ba za su iya sayen ‘yan kwallon kafa fitattu guda 22 ba domin su buga musu tamaula ba.

City ta kashe fam miliyan 215 a kakar bara, kuma a wani jadawali da aka fitar ya bayyana cewar kungiyar ce ta daya a karfin arzikin sayen ‘yan kwallo a duniya.

Guardiola wanda ke harin lashe kofi hudu a bana da suka hada da na Zakarun Turai da Premier da FA da League Cup ya ce dole sai ka samu zakakuren ‘yan wasa kan ka cimma buri.

Kocin ya kara da cewar sayo ‘yan kwallo 22 za suyi tsada, kuma City ba za ta iya sayen su ba, domin farashin ‘yan wasan tamaula kullum sama yake yi.

Guardiola ya ce ba za su iya sayen dan kwallo daya kan fam miliyan 100 ko 90 ko 80 ba, domin babu yadda za su iya biyan albashi da sauran dawainiya, amma bai san nan gaba ba.

City ta hakura da sayen Alexis Sanchez daga Arsenal domin tana ganin ba za ta iya biyan kunshin yarjejeniyar dan wasan ba, hakan ya sa ya koma taka-leda a Manchester United.

Manchester City tana ta daya a kan teburin Premier ta kuma kai wasan zagayen gaba a kofin Zakarun Turai za ta buga wasan karshe a League Cup.

Roger Federer ya lashe gasar Australian Open na shida


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Roger Federer ya lashe gasar Australian Open ta shida a rayuwarsa bayan ya lallasa Marin Cilic.

Wannan ne kuma gasar Grand Slam ta 20 da ya lashe a dukkan wasannin da ya shiga a tsawon rayuwarsa ta dan wasan Tennis.

Dan wasan wanda dan asalin kasar Suwizaland ne ya sami wannan nasarar ce bayan da a farko ya fara wasan da rashin sa’a, inda ya fadi a jerin sabis biyar a set na hudu.

Amma daga baya ya lashe wasan da 6-2 6-7 (5-7) 6-3 3-6 6-1.

Federer mai shekara 30 da haihuwa, ya kasance dan wasan Tennis na hudu a tarihin wasan da ya taba lashe gasar Grand Slam 20 ko fiye.

Wadanda suka sami wannan mukamin da ya samu a yau sun hada da Margaret Court, da Serena Williams da kuma Steffi Graf.

“Wannan ya kasance cikon burin da na dade ina rike da shi, kuma sai gaba daga nan,” inji Federer.

Hanyar da Federer ya kai ga nasara

Wasanni Aboki wasa (mukami) Sakamako
Zagayen farko Aljaz Bedene 6-3 6-4 6-3
Zagaye na biyu Jan-Lennard Struff 6-4 6-4 7-6 (7-4)
Zagaye na uku Richard Gasquet (29) 6-2 7-5 6-4
Zagaye na hudu Marton Fucsovics 6-4 7-6 (7-3) 6-2
Zagayen kusa da na karshe Tomas Berdych (19) 7-6 (7-1) 6-3 6-4
Zagayen dab da kusa da na karshe Chung Hyeon 6-1 5-2 retired
Zagayen karshe Marin Cilic (6) 6-2 6-7 (5-7) 6-3 3-6 6-1

An kubutar da ‘yan Afirka ta kudu da aka sace a Najeriya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matsalar satar mutane ta zama ruwan dare a Najeriya

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta ce ta kubutar da wasu ‘Yan Afirka ta Kudu biyu da aka sace su a wani wurin aikin hakar ma’adanai cikin kauyen Maidaro a jihar Kaduna.

Wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar, ta ce sai da jami’an tsaro suka yi amfani da jirgi mai saukar Ungulu da wasu ‘yan sanda na musamman kafin cimma sako mutanen guda biyu.

Mutanen da aka kubutar sun hada daThomas Arnold Pearce da Mista Hendrik Gideon bayan sace su a ranar Talata 23 ga watan Janairu a kauyen Maidaro.

Sanarwar kuma ta ce an sako mutanen ne ranar asabar ba tare da wani rauni a jikinsu ba.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ba ta yi bayani ba ko sai da aka biya kudin fansa kafin a sake su ba.

Al’amarin dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan kubutar da wasu turawa ‘yan Amurka biyu da kuma ‘yan Canada biyu da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Satar mutane dai don neman kudin fansa na kara zama ruwan dare a Najeriya, domin har mutanen karkara ma ba su tsira ba.

‘Yan tawaten FARC sun kaddamar da yakin neman zabe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon shugaban ‘yan tawayen, Rodrigo Londono ne dan takarar jam’iyyar

Kungiyar ‘Yan tawayen FARC a Colombia ta kaddamar da yakin neman zabe na farko a matsayin jam’iyyar siyasa domin shiga zaben ‘yan majalisa da na shugaban kasa.

Dan takarar kungiyar kuma Tsohon shugaban ‘yan tawayen, Rodrigo Londono da ake kira Timochenko ya yi alkawalin yakar talauci da rashawa.

Sannan manufofin ‘yan tawayen sun hada da ilimin jami’a kyauta da kyautata kiwon lafiya ga ‘yan kasa.

Sai dai kuma ‘yan colombia yawanci na tuna barnar da ‘yan tawayen ne suka aikata, ta garkuwa da hare hare a rikicin kasar da aka dauki tsawon lokaci ana yi, kafin a sasanta, shekaru biyu da suka gabata.

Kungiyar ta FARC ta shafe shekaru tana gwagwormaya da makamai kafin ta saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakaninta da gwamnatin kasar.

A 2016 ne ‘Yan tawayen kungiyar FARC a Colombia suka sanar da kawo karshen yakin da suke yi na sama da shekaru 50.

Ana binciken kamfani da cuwa-cuwar mabiya a shafin twiiter


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana bincike kan kamfanin Devumi a Amruka da laifin kirkirar jabun mabiya da ke bin fitattun mutane a shafukan sada zumunta

Hukumomi a New York sun kaddamar da bincike a kan wani kamfanin Amurka da ake zargi ya sayar da miliyoyin mabiya na jabu a shafukan sada zumunta.

An kaddamar da binciken ne kan kamfanin a ofishin alkalin alkalan New York.

Ana zargin Kamfanin mai suna Devumi da kirkirar jabun mabiya da ke bin fitattun mutane da ‘yan siyasa da ‘yan wasa da ‘yan jarida ga wadanda ke neman suna a shafukan sada zumunta.

Wani bincike da New York Times ta gudanar ta gano akalla mabiya 55,000 da kamfanin ya sauya na jabu daga shafukan mutane na twitter.

A cikin wata sanarwa, kamfanin Twitter ya bayyana cewa wannan abu ne da ba zai amince da shi ba.

Sai dai kuma Kamfanin na Devumi ya musanta zargin yana sayar da mabiyan shafukan sada zumunta na jabu da kuma satar bayanan mutane na asali.

Cavani ya zama kan gaba a ci wa PSG kwallaye


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Cavani ya ci wa PSG kwallo 157 jumulla

Edison Cabani ya zama dan wasan Paris St Germain da babu kamarsa a ci wa kungiyar kwallaye, bayan da ta ci Montpellier 4-0 a ranar Asabar.

Wadanda suka ci wa PSG kwallayen sun hada da Edison Cavani da Angel Di Marid da Neymar wanda ya ci biyu, daya ma a bugun fenariti.

Cavani ne ya fara cin kwallo a minti na 11 da fara wasan, kuma na 157 jumulla da ya ci wa kungiyar, inda ya doke Zlatan Ibrahimovic wanda ya ci 156 a tarihi.

Da wannan sakamakon PSG wadda ta yi wasa 23 ta bayar da tazarar maki 11 tsakaninta da Lyon ta biyu a kan teburi wadda ta buga karawa 22.

A ranar Lahadi ne Lyon za ta ziyarci Bordeaux a wasan mako na 23 a gasar ta cin kofin Faransa.

Dortmund ta shirya sayar da Aubameyang


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau biyu Dortmund na dakatar da Aubameyang kan halin rashin da’a

A karon farko dan wasan da Arsenal ke son saya Pierre-Emerick Aubameyang ya buga wa Borussia Dortmund tamaula a ranar Asabar.

Dortmund ta tashi wasa 2-2 da Freiburg a gasar Bundesliga da ta fafata a wasan mako na 20.

Rabon da Aubameyang ya buga wa Dortmund kwallo tun ranar 16 ga watan Disamba, bayan da ta dakatar da shi, sakamakon kin halartar taron ‘yan wasan kungiyar.

Dortmund ta ce a shirye take ta sayar da dan wasan na tawagar kwallon kafar Gabon idan har za a amince da abubuwan da ta gindaya kan cinikin dan kwallon.

Wata majiya ta kusa da Dortmund ta ce kungiyar na bukatar Arsenal ta sayi Aubameyang kan fam miliyan 50.

Arsenal na neman mai cin kwallo bayan da ta sayar da Alexis Sanchez ga Manchester United ta karbi Henrikh Mhkitaryan daga United.

South Africa na fuskantar matsanancin rashin ruwa


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Cape Town na fuskantar fari da karancin ruwan sama tun tsawon shekara uku da suka gabata.

An gargadi mazauna birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu da su “Adana ruwa tamkar rayuwarsu ta ta’allaka akan shi”.

Hukumomi kuma sun ce duk wanda ya toshe kunnensa bisa wannan gargadin na iya fuskantar a yanke masa ruwan.

Tsananin karancin ruwan da ake fuskanta ya tilasta wa mazauna kewayen birnin takaita amfani da ruwan, inda ake ba wa mutum daya litar ruwa 50 kawai a kowacce rana.

Jami’ai sun bukaci jama’a su takaita yin amfani da ruwa wajen kora ba-haya don adana ruwan.

Shugaban gwamnatin yankin ta ce, idan aka samu daukewar ruwa a famfuna “Annobar da za ta biyo baya ta wuce wadda muka taba fuskanta”.

Helen Zille ta ce har yanzu akwai yiyuwar kauce wa daukewar ruwa ta wuni guda.

Ta kuma ce za a ci gaba da kau da kai daga matsalar idan kowane mutum yana amfani da ruwa lita 50 ko kasa da haka a kowane yini.

“Wannan ba abu ba ne mai wahala idan muka sa hakan a ranmu wajen yin amfani a gidajenmu da wuraren aikinmu”, inji ta.

Mis Zille ta bayar da wasu shawarwari kan yadda za a adana ruwa.

“Ku kashe mazubin ruwan bandakunanku, ku dinga amfani da ruwan da kuka yi wanki wajen kora ba-haya, kuma ku dinga tara ruwan wankin kuna amfani da shi a bandakin maimakon zubarwa”.

Ta kara da cewa,”A halin da ake ciki yanzu ba wanda zai iya samun damar yin wanka sama da sau biyu a mako. Akwai bukatar adana ruwa tamkar a kanshi rayuwarka ta ta’allaka”.

A bara, Mis Zille ta bayyana cewa sai bayan kwana uku-uku take wanka.

Birnin Cape Town ya shahara da zuwan masu yawon bude ido, amma yana fuskantar matsanancin fari na tsawon lokaci.

Yawancin ‘yan Afirka ta Kudu sun farfado daga wahalar farin da suka fuskanta wanda dumamar yanayi ya haddasa.

An saki attajiran Saudi Arabia bayan sun biya makudan kudade


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Otel din Ritz da ke birnin Riyadh

An saki wasu daga cikin attajiran Saudiyya da ake tsare da su tun watan Nuwamba sabili da tuhumar su da ake da cin hanci da rashawa.

Cikin wadanda aka sakin akwai Waleed al-Ibrahim, shugaban kamfanin talabijin na MBC da Khalid al-Tuwaijiri wanda shi ne sarkin fadar kasar.

Rahotanni na cewa sun biya makudan kudade – amma ba a bayyana yawan kudaden da suka biya ba.

An dai tsare yarimomi da ‘yan siyasa da attajiran ‘yan kasuwa fiye da 200 a wannan kokarin da hukumomin Saudiyya ke yi na kwato dukiyar kasar da ta ce sun wawure.

Tun wancan lkokacin suke tsare a hamshakin otel na Ritz da ke birnin Riyadh, wanda za a sake budewa ranar 14 ga Fabrairu.

Da alama kudaden da suka biya masu yawa ne sosai.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Otel din Ritz na birnin Riyadh, inda ake tsare da attajiran Saudiyyan

An saki yarima Miteb bin Abdullah a watan Nuwamab bayan da ya biya fiye da dala biliyan 1.

Rahotanni sun ce al-Ibrahimi na iya rasa hannun jarinsa a kamfanin talabijin na MBC – wanda shi ne mafi girma a Gabas ta Tsakiya.

Sauran wadanda ake tsare da su za su kasance a otel din na Ritz zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu.

Duk wadanda ba su iya biyan kudaden da ake bukatarsu da su amayar ba, za a kai su kurkuku domin su jira shari’a.

A wani bangaren, Yarima Alwaleed bin Talal, daya daga cikin manyan mutanen da ake tsare da su ya fada wa kamfanin dillancin labaria na Reuters cewa yan sa ran za a sake shi “cikin kwanaki”.

Attajirin ya kuma bayyana cewa yana sa ran a wanke shi daga dukkan zargin da ake masa, kuma ya cigaba da mallakar kamfaninsa na zuba jari.

Kabul: Harin bam ya kashe mutum uku kana ya raunata 79


Hakkin mallakar hoto
BBC Afghan

Image caption

Ana iya hango hayaki daga inda harin ya auku a sassa babn-daban na birnin Kabulk

Akalla mutum uku suka rasa rayukansu inda kuma 79 suka raunata a wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai a tsakiyar birnin Kabul na Afghanistan, inji jami’ai.

Harin ya auku ne kusa da tsohon ginin ma’aikatar harkokin cikin gida, wanda ke kusa da ofisoshin Tarayyar Turai da Babbar Majalisar Zaman Lafiya.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin wannan harin. Akwai rahotannin da ke cewa anyi amfani da motar daukar marasa lafiya ne wajen kai harin.

A makon jiya ma kungiyar ta Taliban ta kashe mutum 22 a wani katafaren otel da ke Kabul.

Wadanda suka gane wa idonsu al’amarin sun ce wurin – wanda cibiya ce ta ofisoshin jakadancin kasashen waje da shalkwatar ‘yan sandan kasar – yana cike makil da jama’a a daidai lokacin da bam din ya fashe.

An rika gain hayaki a sassa daban-daban na birnin.

Yadda Boka ya hana masu jinin al’ada zuwa makaranta


Ana samun matsalolin kyara da tsangwama ga masu al’ada a fadin duniya. A wasu bangarorin Afirka, ana nuna wa mata masu jinin al’ada wariya saboda ana daukarsu marasa tsarki. Wannan ne halin da wasu ‘yan mata dalibai ke ciki a yankin tsakiyar Ghana. An haramtawa ‘yan mata masu jinin al’ada tsallaka kogin Ofin don zuwa makaranta, bisa dokar da wani boka da ake bauta wa a kogin ya bayar, hakan kuma yana shafar neman iliminsu.

A sakamakon haka, ‘yan matan yankin suke samun koma baya a zangon karatunsu- Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa yarinya daya cikin goma ba ta samun zuwa makaranta a yankin saboda batun jinin al’ada.

Wainar da matan Hausawa ke toyawa a shafukan sada zumunta?


Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin tare da Fatima Zahra Umar:

Adikon Zamani na wannan mako ya yi duba ne kan irin abun da ke jan hankalin mata a shafukan sada zumunta, kamar taimakon al’umma da tsegumi, da tallace-tallace, da cin zarafin juna da dai sauran su.

Amfani da shafukan sada zumunta na zamani (Social Media), a tsakanin matan al’ummar Hausawa ya yadu tamkar ruwan dare gama duniya.

A shirin Adikon Zamani na wannan makon za mu duba dalilan da yasa amfani da shafukan sada zumunta na zamani ke sa mata ke shagaltuwa.

Wasu na amfani da wadannan shafukan ne, musamman ma Facebook da Instagram domin tallafa wa al’umma da fadakar da mata a kan batutuwan da suke damunsu.

Misali akwai shafin Open Diaries a Instagram, wanda Fatima Fouad Hashim da wasu bayin Allah su ka bude domin taimakawa da shawarwari akan harkokin rayuwa na yau da kullum.

Sun kware sosai a harkar har suna shiga cikin al’umma su tallafa musu da kudaden da aka hado daga mabiya shafin.

Wasu kuma kamar Hajiya Aisha Falke mai wallaffa shafin Northern Hibiscus a Instagram, su na amfani da shafukansu domin kasuwanci da nishadantarwa.

Ta kan saka labarai masu kalar tsegumi da abun dariya da kuma tallace-tallacen kayan sayarwa irin jakukuna, atamfofi da sauransu.

Akwai wasu kuma wadanda suka shahara a harkar sayar da kayan mata domin taimakawa mata a fagen aure.

Suna tallan irin hade-hadensu da labaran matan da suka yi amfani da kayan kuma suka gamsu da hakan.

Wasu kuma nasu shafukan na ilmantarwa ne da karfafa wa mata gwiwa irin su shafin The Almajira da ke Instagram.

Amma kuma abun takaici shi ne, akwai wasu shafukan da mata ke kafawa domin gulma, zagi da cin mutuncin sauran ‘yan uwa mata.

Abun takaicin shi ne mafi yawancin masu bin wadannan shafukan mata ne, kuma sai mutum ya ga suna jin dadin zagin da wulakanta matan da ake yi a wadannan shafukan.

Ni a ganina wannan ba abun da ya dace ba ne a al’adance ko a addinance. Ina fatan za mu gyara wannan yayi na bude shafukan sadarwa domin zage-zage da cin mutuncin wasu.

Sau nawa Obasanjo na yi wa shugabannin kasa baki?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua na cikin mutanen da Cif Obasanjo ya soka

Masana harkokin siyasa sun ce wasikar da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari tamkar wata al’ada ce ta tsohon shugaban.

A farkon makon nan ne Cif Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari budaddiyar wasika inda ya soke shi bisa abin da ya kira rashin iya shugabancinsa.

Mr Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ba zai iya fitar wa Najeriya kitse a wuta ba don haka bai cancanci yin wa’adi biyu na shugabancin kasar ba.

Daga nan ne tsohon shugaban ya yi kira a gare shi da ya ajiye mulki idan wa’adinsa na farko ya kare sannan ya bi sahun tsoffin shugabannin kasar wajen bayar da shawarwari kan yadda za a gyara Najeriya.

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa Bashir Baba ya shaida wa BBC cewa tsohon shugaban kasar “tamkar tauraruwa mai wutsiya ce, wacce Hausawa kan ce ganinki ba alheri ba.”

“Wannan ba shi ne karon farko da wannan dattijo ke sukar shugabannin da ke mulki ba. Ya soji Alhaji Shehu Shagari da Janar Ibrahim Babangida da Janar Sani Abacha. Sukar da ya yi wa Abacha ce ta sa aka daure shi.

“Bayan ya sauka daga shugabancin kasa a shekarar 2017, Marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua, wanda shi ya dora shi a mulki, ya hau sai da Cif Obasanjo ya soke shi. Haka kuma ya soki Dr Goodluck Jonathan,” in ji Bashir Baba.

Ya kara da cewa kusan duk lokacin da Cif Obasanjo ya soki shugaba mai-ci shi ne da gaskiya, amma duk da haka “shi kansa bai iya yin mulki irin wanda yake son wasu su yi ba. Da alama yana ganin shi ne ya fi kowa iya mulki.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Janar Abacha ya daure Cif Obasanjo

Jirgin sama ya bace dauke da mutane 50 a Kiribati


Image caption

Jirgin ya taso ne daga Nonouti zuwa Betio

Masu aikin ceto na ci gaba da binciken wani karamin jirgin sama da ya bata a tsibirin Kiribati dauke da mutane 50.

Jirgin mai suna MV Butiraoi ya taso ne daga tsibirin Nanouti a ranar 18 ga watan Janairu, inda ake sa ran zai shafe kwanaki biyu a sama.

Amma a daren alhamis aka fara samun labarin ya bata, kuma jami’ai daga New Zealand da Fiji sun shiga aikin neman jirgin.

Jami’an ceto a New Zealand da ke taimakawa da aikin binciken, sun ce jirgin ya baro Nanouti ne da ke tsakanin kilomita 260 zuwa Betio, babbar tashar kasar.

New Zealand ta kuma aika da wani jirgin sojin sama domin aikin ceto jirgin da ya bata.

Babban jami’in da ke jagorantar binciken, John Ashby ya ce suna iya kokarinsu domin gano jirgin da kuma fasinjan da ke cikinsa.

Ya ce sun fahimci cewa ashe an yi gyaran daya daga cikin fankar jirgin kafin ya tashi, kuma a cewarsa wannan na iya kasancewar sanadin halin da jirgin ya shiga a yanzu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

New Zealand ta tura wani jirgin sojin sama domin aikin ceto jirgin da ya bata.

Me ya sa ‘yan BH suka fi kai hari a watan Janairu?


Hakkin mallakar hoto
Boko Haram

Image caption

Kungiyar Boko Haram ta fara hare-hare a shekarar 2009

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nanata cewa gwamnatinsa ta sami galaba kan kungiyar Boko Haram, amma binciken da BBC ta yi ya bayyana cewa lamarin bai sauya ba.

Binciken da BBC ta gudanar ya bayyana cewa kungiyarta hallaka fiye da mutum 900 a 2017, wanda kadan ya wuce yawan wadanda ta kashe a 2016.

Kungiyar ta kai hare-hare a duk tsawon shekarar, wanda ya ci karo da ikirarin shugaba Buhari da yake cewa an sami galaba akan maharan.

Mun duba alkaluman cikin natsuwa, kuma mun fitar da wani jerin bayanai, da irin hare-haren na Boko Haram daki-daki, da kuma wuraren da suka fi kai wa hari, kana mun duba wane wata ne suka fi kai hare-hare a ciki.

Su wane ne Boko Haram?

Boko Haram ta fara tayar da kayar baya ne a 2009 bayan da ta fara kai hare-hare a wani yunkurin kafa wata daula ta musulunci a yankin Afirka ta yamma.

Rikicin da ya biyo baya ya fi kamari a yankin arewa maso gabashin kasar kuma ya janyo mutuwar mutum akalla 20,000 kuma ya tarwatsa wasu mutum miliyan biyu daga muhallansu.

Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Birnin Maiduguri ya kasance wata cibiya ta rikicin na Boko Haram

A karkashin jagorancin Abubakar Shekau, Boko Hrama ta yi wa kungiyar IS mubaya’a a watan Maris na 2015.

A watan Agustan 2016 kungiyar ta dare, inda aka sami bangarori daban-dabam, bayan da kungiyar ta IS ta bayyana cewa an tunbuke Shekau daga jagaorantar kungiyar.

Yadda muka tattara alakluman

Kungiyar Boko Haram na daya daga cikin kungiyoyin da duniya ba ta fahimta ba.

Domin gane yadda kungiyar ke tafiyar da ayyukan ta’addancinta, BBC ta duba rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida da na waje suka wallafa game da hare-haren 2016 da 2017, kuma mun yi la’akari da ainihin abubuwan da suka faru a lokacin kowane hari.

Amma dole ne a samar da daidaito tsakanin sakamakon wannan binciken da matsalar tara bayanai a yankin na Afirka ta yamma.

Andrew Walker dan jarida ne da ya dade yana yin rahotanni akan Najeriya, kuyma ya fada wa BBC cewa ba za a iya samun ainihin alkaluman ababen da suka faruba saboda yayanyin rikicin.

Amma ta hanyar duba rahotanni daga kafafen watsa labarai 48 daga harsunan Ingilishi, da Farnsanci, da Larabci da harsunan Kanuri da Hausa da Zarma a yankin Afirka ta yamma, wannan rahoton ya ba da haske ga yanayin munanan hare-haren da kungiyar ta ke kai wa.

Hare-hare na karuwa, amma wuraren da ake kai harin basu sauya ba

Boko Haram ta kai jimillar hare-hare 150 a 2017, inda aka sami karuwar hare-hare 127 idan aka kwatanta da wadanda ta kai a 2016.

A dukkan wadannan shekarun biyu, kungiyar ta kai mafi yawan hare-haren nata a watan Janairu ne, inda BBC ta gano cewa ana samun karuwar hare-haren ne bayn kalaman shugaba Buhari na cewa an gama da kungiyar.

Amma wuraren da kungiyar Boko haram din tafi kai hare-harenta basu sauya ba sosai a cikin wadannan shekarun biyu.

Najeriya ta fuskanci mafi yawan manyan hare-hare a cikin shekarun 2016 da 2017 ne, inda jihar Borno ta kasance wadda ta fi jin jiki.

Kungiyar ta kuma nuna ikonta na kai wasu hare-hare nesa ta inda aka zsaba gani, domin ta kai hari a yankin Arewa mai nisa na Kamaru da yankin Diffa na kasar Nijar da kuma yankin tafkin Chadi.

Wannan ya yi kama da jerin hare-haren shekarar 2016, amma akwai bambanci, domin Najeriy ata fuskanci karuwar hare-haren inda a Nijar lamarin yayi sauki.

Yanayin hare-haren

Boko Haram ta kai hare-hare 90, na kunar-bakin-wake kuma guda 59 a 2017.

Najeriya ce ta fuskanci mafi yawan hare-haren.

A tsallaken iyaka kuwa, kungiyar ta rika kai wa Kamaru harin kunar bakin wake ne fiye da na gaba gadi.

A shekarar 2016, kungiyar ta aiwatar da hare-haren da masu kama da wadannan.

Alkaluma sun bayyana karuwar kai hare-haren kunar bakin wake.

A Najeriya, kungiyar ta kara kai hare-haren kunar bakin waken daga 19 a 2016 zuwa 38 a 2017, inda Kamaru ma ta sami irin wannan karuwar hare-haren.

Harin kunar bakin wake shi ne yafi yawa a birnin Maiduguri na tarayyar Najeriya, inda birnin ya cigaba da zama cibiyar wannan ta’addancin.

Rashin rayuka bai sauya ba sosai

Akalla mutum 967 aka bada rahoton sun rasa rayukansu a hare-haren na Boko Haram a 2017, inda aka sami karuwar mace-mace idan aka kwatanta da 2016 inda aka sami mutum 910 da suka mutu.

Mafi yawan mace-mace a 2017 sun auku a Maiduguri ne, kuma an sami karuwar mutanen da ke szaune a birnin zuwa kimanin mutum miliyan biyu saboda masu neman mafaka daga hare-haren kungiyar Boko Haram.

A wasu sassa na najeriya kuwa, an sami karuwar mutuwar mutane a Magumeri, da Konduga da Damaturu da kuma Mubi.

Ba a sami sauye-sauye masu yawa ba a yadda Boko Haram ke kai hare-hare a shekaru biyun da suka gabata.

Mafi akasarin hare-haren da ta kai a shekarun 2016 da 2017 sun kasance a kan kauyuka ne da sojin kasashen.

Boko Haram ta cigaba da kai hari akan masallatai da cibiyoyin ‘yan gudun hijira masu tserewa tashin hankalin.

Dangantakar Boko Haram da IS

Babu takamaiman bayani game da dangantakar Boko Haram da IS.

Hare-hare 13 ne cikin 151 da Boko Haram ta kai suka sami goyon bayan IS, wanda ke nuna cewa babu wata alaka mai karfi tsakanin kungiyoyin biyu.

Yana yiwuwa dalilan haka sun biyo bayan matsin lambar da IS ta ke fuskanta a Iraki da Siriya na da tasiri domin IS ta rasa daular ta ta kafa a can.

Me yasa aka kasa gama wa da Boko Haram?

A shafe shekaru masu sukar lamirin gwamnatocin Najeriya na tuhumarsu da kin ba rundunonin sojin kasar isassun makaman da suke bukata a fagen yaki da Boko Haram.

Amma da alama wannan zai sauya a 2018, bayan da Amurka ta yarda za ta sayar wa Najeriya makamai.

Amma kafin zuwa wannan lokacin, da alama Boko Haram na nan da sauran karfinta, inji Tomi Oladipo, wakilin tsaro na BBC.

Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Nigeria’s military has struggled to defeat the Boko Haram threat

“Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta sha fadin cewa ta ga bayan Boko Haram, amma bangarorin kungiyar sun ci gaba da janyo matsalolin tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma yankin tafkin Chadi,” inji shi.

A ganin Oladipo, Boko Haram ta na dogaro da dabarun yakin sunkuru ne wajen cigaba da fuskantar hare-haren dakarun gwamnati.

Ba abin da zai hana ni zuwa Kano — Kwankwaso


Hakkin mallakar hoto
HALILU DANTIYE

Wani na hannun daman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Comrade Aminu Abdussalam ya ce babu gudu babu ja da baya game da ziyarar da tsohon gwamnan Kanon ya shirya kai wa kano a karshen wannan watan.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya “Rubuto wa Sanata Kwankwaso cewa suna ba shi shawara cewa akwai wasu mutane da ka ce sun yi shiri za su je su tayar da tarzoma a wurin taron da zai haifar da wani abu mara dadi”.

Ya kuma kara da cewa: “Saboda haka ‘yan sanda suna ba shi shawara da ya janye zuwansa Kano.”

Ya kuma ce ‘yan sandan sun rubuta watohon gwamnan takarda inda suke ba shi shawarar dage wannan ziyara da ya shirya kaiwa Kano.

Amma da alama Sanata Kwankwason bai karbi wannan shawarar ta ‘yan sanda hannu bibiyu ba:

“A matsayinsa na dan kasa kuma daya daga cikin jagorori na siyasar Najeriya, ya rubuta musa cewa ya ga takardarsu, kuma a iya fahimtarsa, aikin jami’an tsaro ne su tabbatar da tsaro, ba ma nasa ba, amma na al’ummar kasa duka,” inji Comrade Aminu Abdussalam.

Ya kara da cewa kamata yayi ‘yan sanda su dauki mataki akan wadanda suke kitsa wannan tashin hankalin.

Dangane da ko sun dauki shawarar ta ‘yan sanda na cewa su dage wannan taro a Kano, ya ce: “Matsayin da muka dauka shi ne, a bisa doka da tsarin mulkin Najeriya, wajibi ne ga jami’an tsaro da kwamishinan ‘yan sanda na Kano ya tabbatar da tsaro ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ma duk wani mutumin Kano da tabatar da cewa sun yi harkokinsu ba tare da tsangwama ba”.

Takardama

Comrade Aminu Abdussalam ya bayyana cewa “kwamishinan ‘yan sanda ya hana jami’ansa karbar wannan takardar da muka kai musu.”

Ya musanta cewa ‘yan sanda sun ba su shawarar janye nasu taron ne saboda bangaren gwamna Ganduje sun riga su mika bukatar gudanar da nasu taron gabanin mika bukatar da bangaren Sanata Kwankwaso ya yi.

“Ba haka suka gaya mana ba. Kuma a rubuce suka ba mu takarda. Cewa suka yi wasu sun shirya za suyi ta’adda a wannan lokaci, ba zasu so Sanata Kwankwaso ya shigo a yi masa ta’adda ba.”

Ya kuma ce ‘yan sandan “Suna ba shi shawara kada ya zo, har sai yanayi ya inganta. Har sai yanayi ya inganta. Ba inda suka yi mana zancen wani ya ce zai yi taro a ranar da za muyi taro, ko a gurin da za muyi taro.”

Ya bayyana makasudin wannan ziyara: “Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai zo jiharsa ta haihuwa… Zai kuma je gidansa a Gandun Albasa, ya gaisa da masoya da magoya bayansa da sauran al’ummar jihar Kano manya da kanana”.

Comrade Aminu ya kuma musanta cewa bangaren Kwankwasiyya sun shirywa wani taro ne a Kano.

“Mu ba mu fasa ko wane shiri ba, kuma muna kara jaddadawa hukumar ‘yan sanda da jami’an tsaro na Kano cewa wajibinsu ne su bada tsaro ga Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da al’ummar da zasu zo tarbarsa.”

‘Yan gudun hijirar Kamaru sama da 43,000 sun shiga Najeriya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yawancin ‘yan gudun hijirar mata ne da kuma kananan yara.

Wasu alkaluma da hukumomin agaji suka bayar sun nuna cewa ‘yan kasar Kamaru fiye da dubu arba’in da uku ne suka tsere zuwa Najeriya.

Tserewar ta biyo bayan dirar mikiyar da gwamnatin Kamarun ke yi wa ‘yan a-ware na yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammaci, masu amfani da turancin Ingilishi a kasar ta Kamaru.

‘Yan gudun hijirar, wadanda yawansu ke ci gaba da karuwa, sun fantsama jihohin Kuros Riba, da Binuwai,da Enugu da kuma Akwa Ibom.

Adadin ‘yan gudun hijirar yanzu ya nunka kusan sau uku, bisa adadin da jami’an majalisar dinkin duniya da na Najeriya suka bayar makwanni biyu da suka gabata.

Daraktan hukumar agajin gaggawa na jihar Binuwai, Mista John Inaku ya shaida wa BBC cewa, “A yanzu haka kuma akwai ‘yan gudun hijirar Kamaru fiye da dubu talatin da uku, wadanda suka sami mafaka a jihar Kuros Riba ta Najeriya, mai makwabtaka da yankin kudu maso yammacin Kamarun.”

Shugaban bayar da agajin gaggawa na jihar Binuwai ya yi bayanin cewa,”Yawancin ‘yan gudun hijirar mata ne da kuma kananan yara. Kuma wasu matan ma suna da tsohon ciki, wasu kuma tsofaffi.”

Shugaban kwamitin kula da batutuwan ‘yan gudun hijira na majalisar wakilai ta Najeriya, Honarabul Sani Zorro, ya kara da cewa,”Su wadannan ‘yan gudun hijira a yanzu haka suna kauyuka da garuruwan da suke ciki suna nisan kilo mita daya zuwa biyu daga iyakarmu da Kamaru.

“Abin da yake faruwa shi ne jami’an tsaron Kamaru na yin kutse suna kama wasu daga cikinsu suna cewa ‘yan ta’adda ne a tafi da su to an hana wannan, kuma yin irin wanann kutsen na jami’an tsaro zuwa wata kasar zai iya kawo takaddama har ayi yaki.”

Masu lura da al’amura dai na ganin batun wadannan ‘yan gudun hijira wani babban kalubale ne, ba wai ga kasar ta Kamaru ba, har ma ga makwabtanta da sauran yankin Afirka ta yamma.

Gobara ta kashe mutum 37 a asibiti a Koriya Ta Kudu


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda masu kashe gobara suka dinga fama da wutar

A kalla mutum 37 ne suka mutu, wasu 70 kuma suka jikkata a wata mummunar gobara da aka shafe kusan shekara 10 ba a yi irin ta ba a Koriya Ta Kudu.

Rahotanni sun ce gobarar ta faro ne daga dakin bayar da kulawar gaggawa na Asibitin Sejong da ke birnin Miryang a kudu maso gabahsin kasar.

Kusan marasa lafiya 200 ne suke cikin asibitin da kuma wasu da ke cibiyar kula da tsofaffi na asibitin a lokacin.

Wannan gobara dai ita ce mafi muni da aka yi a Koriya Ta Kudu cikin shakara 10 da suka gabata, kuma ana tsammanin yawan wadanda suka mutu zai karu, saboda yadda wadanda suka jikkata ke cikin halin ha’u’la’i.

Masu aikin kashe gobara sun ce yawancin wadanda suka mutun hayakin da suka shaka ne ya kashe su.

Daga cikin wadanda suka mutu har da wasu ma’aikatan asibitin uku da suka hada da wani likita da ma’aikaciyar jinya da mataimakiyarta.

Hukumomi sun bayar da mabambantan alkaluma na yawan wadanda suka mutu, inda da fari ‘yan sanda suka ce mutum 41 ne suka mutu, amma ma’aikatan kashe gobara da majiyoyin asibiti sun ce mutum 37 ne suka mutu.

Birnin Miryang yana da nisan kilomita 270 daga babban birnin kasar Seoul.

Asibitin dai ya kware wajen bai wa tsofaffi kulawa da ma sauran marasa lafiya, in ji wata kafar watsa labarai ta intanet.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wannan gobara dai ita ce mafi muni da aka yi a Koriya Ta Kudu cikin shakara 10 da suka gabata

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Gobarar ta faro ne daga dakin bayar da kulawar gaggawa na Asibitin Sejong

ta kara da cewa wani majinyaci da ya tsira Jang Yeong-jae, ya ce yana hawa na biyu na benen asibitin sai ya jiwo ihun ma’aikatan jinya suna cewa wuta, wuta, don sanar da mutane halin da ake ciki.

Iface-ifacen neman dauki

“Amma da na bude kofa don guduwa sai na ga hayaki ya turnuke wajen.”

Mista Jang ya ce sai ya bude taga ya sauka ta kan tsanin da masu kashe gobara suka ajiye.

Ya kara da cewa akwai tsofaffi da ba su da lafiya sosai a sauran hawan benayen…. Ina tababa idan har sun samu tsira.”

Shugaban hukumar kashe gobara Choi Man-woo, ya ce har yanzu ba a san me ya jawo gobarar ba.

Kafofin watsa labarai sun ce ba bu abubuwan kashe gobara na gaggawa a baki daya ginin asibitin.

Mr Choi ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 07:30 na sfaiyar kasar da ranar Alhamis, kuma an shafe sa’a uku an kashe ta.

An samu nasarar fitar da marasa lafiya 94 da ke kusa da ginin cibiyar kula da tsofaffin.

Shugaban kasar Koriya Ta Kudu dai ya yi wani taron gaggawa don tattauna yadda za a shawo kan gobara irin wannan nan gaba.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ba a san abun da ya jawo wutar ba

Hakkin mallakar hoto
Reuters

‘Yan sanda sun dakatar da Kwankwaso daga zuwa Kano


Hakkin mallakar hoto
KANO GOVERNMENT HOUSE

Image caption

Masana harkokin siyasar Najeriya sun ce rikicin bangar da ake yi a Kano babban koma-baya ne da ka iya rage kimar jihar a idon sauran jihohin Najeriya kasar

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta shawarci tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya soke ziyarar da ya yi niyyar kai wa jihar nan ba da jimawa ba saboda barazanar tashin hankalin da za a iya samu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabi’u Yusuf ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi a birnin Kanon ranar Juma’a.

Mista Yusuf ya ce ya zama wajibi a shawarci Sanata Kwankwaso ya soke ziyarar tasa, duk kuwa da cewa yana da cikakkiyar dama da ‘yancin walwala a matsayinsa na dan asalin jihar.

Ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa akwai matukar tsoro a zukatan al’ummar jihar na irin tashin hankalin da za a iya samu.

“‘Yan sanda sun samu bayanan da ke nuna cewa mutane suna fargabar wasu bata-garin ‘yan siyasa za su iya fakewa da ziyarar tasa su yi abun da bai kamata ba na tashin hankali.

“Wannan ne ya sa ya zama dole hukuma ta dauki mataki na dakile duk wani abu da zai kawar da zaman lafiyar da ake da shi a jihar, in ji Kwamishina Rabi’u Yusuf.

An raba gari tsakanin Ganduje da mataimakinsa ne?

An hana Ganduje da Kwankwaso tarukan siyasa

Yadda Kwankwaso da Ganduje ‘ke siyasar banga a Kano’

Ya kuma jaddada aniyar rundunar ta ci gaba da jajircewa da tsayawa tayin daka da yin adalci ga da bai wa ko wanne dan siyasa damar yin al’amuran siyasrsa ba atre da tsoro ko faragaba ko cin zarafi ba.

Tun da fari dai Sanata Kwankwaso ya shirya kai ziyara jiharsa ta Kano ne a karshen makon nan, inda rabonsa da kai ziyara tun lokacin da ya je yi wa Gwamna Abdullahi umar Ganduje ta’aziyar rasuwar mahaifiyarsa a watan Maris 2016.

Tun daga wannan ziyara ce kuma aka fara samun takun-saka tsakanin magoya bayansa da na Gwamnan Ganduje, wanda a baya kansu a hade yake.

Ko a lokacin bikin karamar sallar 2017 ma sai da aka yi fito-na-fito tsakanin magoyan bayan shugabannin biyu, inda har aka jikkata wasu da dama.

Shin Obasanjo yana shirin kafa wata kungiyar siyasa ce?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Obasanjo ya ce APC da PDP sun gaza

Akasarin jami’an gwamnati da masu sharhi kan budaddiyar wasikar da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari sun fi mayar da martani ne kan kiran da ya yi cewa kada Shugaban ya sake tsayawa takara a 2019.

Watakila hakan ba ya rasa nasaba da tsammanin da ake yi cewa, kamar sauran shugabannin da suka gabace shi, Shugaba Buhari zai so sake yin takarar karo na biyu ko da yake har yanzu bai bayyana sha’awarsa kan hakan ba.

Sai dai daya daga cikin manyan batutuwan da suka fito fili a wasikar shi ne bukatar da ya nuna ta kafa sabuwar gamayyar kungiyoyi da za ta kawar da jam’iyyar APC da PDP daga mulki.

“Me za mu yi idan APC da PDP ba su kai Najeriya gaci a wannan mawuyacin halin ba?

“Kamar yadda wani Farfesa a Jami’ar Kennesaw ta Amurka Farooq Kperogi, ya fada, “zabin da ke gabanmu na da wahala; tamkar ka ce ne zabi tsakanin shaidanu biyu. Babu wani bambanci.

“Ba za mu nade hannu mu zauna muna ta kokawa ba…Muna bukatar gamayyar kungiyoyi, ba kawai jam’iyyar siyasa ba, wacce kowanne dan Najeriya nagari zai iya shiga.”

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa yana fatan gamayyar kungiyoyin za ta zama wata hanya ta fitar da Najeriya daga kangin da take ciki.

Gabanin wannan wasika dai, wasu ‘yan kasar da dama sun yi kira a samar da wata kungiya da za ta kawar da APC da PDP daga mulki.

Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili na cikinsu, inda ta fito da wani maudu’i ma taken #RedCardMovement da ke da zummar zaburar da ‘yan Najeriya su yi fatali da jam’iyyu irinsu APC da PDP sanna su kafa kungiyar da za ta maye gurbinsu.

A cewarta, hakan ne kawai zai sa ‘yan kasar su kafa gwamnatin da za ta kula da su kana ta yi ayyukan ci gaban kasa.

Sai dai wani Malamin da ke nazari kan harkokin siyasa a Jami’ar Abuja, Dr Abubakar Kari, ya shaida wa BBC cewa da wahala a samu irin wannan kungiya a Najeriya.

Ya ce Najeriya kasa ce da ba a cin zabe ba tare da an shiga wata jam’iyyar siyasa ba, don haka ko menene zai faru, ya zama wajibi ga masu rajin kafa gamayyar kungiyar su sani cewa bukatarsu ba za ta biya ba sai sun koma kan turbar da aka sani.

Da alama dai za a ci gaba da yin muhawara kan wannan batu har zuwa zaben 2019 – ko ma bayansa – kuma masana na ganin hakan a matsayin ci gaban dimokradiyya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jirgi ya kade wani mai daukar hoton ‘selfie’


Image caption

Mr T Siva, a lokacin da ya ke kokarin daukar kansa a hoton selfie

Dubban Indiyawa sun kalle hoton bidiyon wani mutum da jirgin kasa ya kade shi a lokacin da ya ke daukar hoton selfie.

Wannan lamari dai ya faru a Hyderabad, bayan da mutumin mai suna T Siva, ya yi watsi da gargadin da wani mutum da ke kusa da layin dogon ya yi masa da kuma hon din jirgin a lokacin da ya ke daukar hoton na selfie.

Mr Siva dai bai mutu ba, amma kuma ya samu raunuka a kansa, inji ‘yan sandan da ke aiki a tashar jirgin.

Yanzu haka dai ya samu sauki, har ma ya bayyana gaban kotu inda kuma aka ci shi tarar dala kusan takwas, saboda dokar da ya taka ta hana daukar hoton selfie a wuraren da aka hana.

Yadda mutane ke mutuwa wajen daukar kansu hoto a India

An kai karar Kim Kardashian saboda satar jakar selfie

Daukar hotuna a lokacin da jirgin kasa ke tahowa ya zamo wani abu na ya yi da ke da matukar hadari a India.

Ko a watan Oktoban da ya gabata, wani jirgin kasa ya bi takan wasu matasa uku a lokacin da suke kokarin daukar hoton selfie a jihar Karnataka, yayin da wasu matasan biyu ma a Delhi suka mutu a irin wannan yanayi.

Karancin suga ya janyo zanga-zanga a kasar Habasha


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Karancin suga a Habasha, ya sa jama’a da dama dai na cin abubuwan da ake hadawa da sugan kamar cincin da kek

Habasha na fuskantar matsanancin karancin sukari wanda ya haifar da zanga-zanga da mutuwar sama da mutum 10 zuwa yanzu.

Hukumar samar da sukari a kasar, ta dora alhakin wannan karanci a kan rashin kyawun yanayi wanda ya janyo raguwar sarrafa shi.

A yanzu gwamnati na cewa nan gaba kadan za ta karbi fiye da tan 200,000 na sukari daga Aljeriya da Thailand, don rage zafin wannan hali wanda hatta ‘yan kasuwa ke ci gaba da iyakance sugan da za su sayar a shaguna da manyan kantunan kasar.

Wakilin BBC a kasar, ya ce ba a fiye samun sugan ba ma sai anje manyan kantuna, kuma talaka da kananan ‘yan kasuwa ne suka fi jin jiki a wannan yanayi na karancin sugan da ake fama dashi a kasar.

Karancin sugan ya sanya farashinsa tashi inji wakilin na BBC.

Shin me ya sa muke san shan alawa?

Ko wayar salula na iya warkar da ciwon suga?

Wannan yanayi da ake ciki ya sa gwamnatin kasar bullo da wani shiri na kayyade sukarin da za a sayarwa duk wani magidanci a kasar a duk wata.

Wani mai shago a kasar, ya sahida wa BBC cewa, suna sayar wa magidanta sukari kilogram biyar a duk wata, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayar da umarni.

Wata mata da wakilin na BBC ya tattauna da ita, ta ce saboda karancin sukarin da ake fama da shi a kasar, yanzu ‘ya’yanta hudu sun dai na cin cincin da kek.

Cutar Lassa ta hallaka mutum 16 a Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ma’aikatan lafiya na cikin wadanda suka rasa rayukansu

Hukumomin lafiya a Nigeria sun ce mutane akalla sha shidda ne suka mutu ciki har da ma’aikatan lafiya uku a sakamakon zazzabin Lassa a kasar.

Akwai kuma wasu gwamman mutanen da ke kwance a asibitoci sakamakon kamuwa da cutar, wadda ake dauka daga beraye, kuma mutane ke yada wa juna.

Ma’aikatar lafiya ta Nigeria ta ce cutar ta watsu a jihohi goma, amma ta fi yaduwa ne a jihohin Ebonyi, da Ondo da kuma Edo.

Ta ce tana aiki tare da hukumar lafiya ta duniya da kuma cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka akan yadda zaa dakile yaduwar cutar.

Hukumomin kasar sun yi kira alummar kasar akan su tsabtacce muhalinsu.

Maganin karfin maza ya kusa kai wasu lahira


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Annobar ta tayar da hankali mutane sosai a kasar

An kwantar da wasu maza uku a asibiti sakamakon barkewa da amai da guduwa mai tsanani, bayan da suka sha magungunan kara karfin maza a Zambiya.

Daga farko dai an yi tsammanin sun kamu da kwalara ne sai daga baya aka gano cewa magungunan kara karfin mazan ne suka yi musu illa.

Tun a shekarar da ta gabata ne kasar Zambiya ke fama da matsananciyar annobar kwalara da ta yi sanadin kashe mutum 70, inda aka samu wadanda suka kamu da ita fiye da 3,000.

Amma akwai alamun cewa mutum ukun wadanda ‘yan yankin gabashin kasar ne, ba sa daga cikin masu fama da annobar.

A maimakon haka, sai aka gano cewa sun yi ta dirkar maganin karfin maza ne wanda ake kira da mvubwe.

Babban jami’in gwamnati na yankin Chanda Kasolo, ya shaidawa BBC cewa, nan da nan mutanen suka fara amai inda aka garzaya da su cibiyar masu kula da kwalara.

Bayan da aka yi musu gwaje-gwaje sai aka gano cewa maganin karfin maza da barasa da kuma abincin da suka ci ne suka hadu suka zame musu guba a ciki, har aka yi tsammanin kwalara ce.

Amma bayan da aka kara yin wasu gwaje-gwajen da yi musu tambayoyi, sai aka gano cewa magungunan karfin mazan ne suka fi yi musu illa.

Ya ce marasa lafiyar har yanzu suna cibiyar da ake kula da masu kwalarar, kuma sun fara farfadowa.

Mourinho ya tsawaita zamansa a United


Image caption

Kwantiragin da kocin ya saka wa hannu ta baya za ta kare ne a 2019.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa 2020.

Kwantiragin da kocin ya saka wa hannu ta baya za ta kare ne a 2019.

Mourinho ya ce,”Ina jin dadin yadda United ta gamsu cewa ni ne kocin da ya dace da horar da wannan babban kulob wajen samar masa da kyakkyawar makoma”.

A watan Mayun 2016 ne dan kasar Portugal din ya karbi aikin horarwar kungiyar daga hannun Louis Van Gaal, inda ya lashe kofin EFL da na Europa a kakarsa ta farko.

Yanzu dai United ce ta biyu a teburin Firimiya, inda take bin bayan ta farko a teburin Manchester City, kuma kungiyar na cikin gasar zakarun Turai da na FA.

“Muna kirkiro hanyoyin da za su kai kungiyar ga gaci, da kuma samar mata da kyakkyawar makoma. Ina son ‘yan wasana, kuma zan so mu kasance da su a kalla shekara uku masu zuwa, in ji kocin.

Gwamnatin Buhari ta umarci jami’an tsaro su sa ido a shafukan zumunta


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Gwamnati ta ce bai kamata a bar masu yada kiyayya ba

Gwamnatin Najeriya ta bukaci jami’an tsaron kasar su soma sanya ido sosai a kan masu amfani da shafukan sada zumunta.

Ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ne ya bayyana hakan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da manyan jami’an tsaron Najeriya ranar Alhamis.

A cewar ministan, “akwai bukatar jami’an tsaro su magance matsalar kalamai na kiyayya da cin zarafi da ake yada wa a shafukan zumunta cikin gaggawa, musamman wadannan wasu mutane da suka yi suna a Najeriya ke yi”.

Ministan ya ce yanzu haka sojojin kasar na hada gwiwa da sauran jami’an tsaron kasar wajen ganin an magance matsalar.

Wasu ‘yan kasar dai sun dade suna kira kan a sanya ido a shafukan na sada zumunta, ko da yake wasu sun yi fatali da kiran.

Hakan ne ma ya sa a watan Disambar shekarar 2015, lokacin da majalisar dattawan kasar ta so kawo dokar da za ta sanya ido kan masu amfani da shafukan, aka yi ta kai ruwa rana tsakanin masu fafutika da wasu ‘yan majalisar.

Sanchez ya bar kulob mai kayatarwa ya koma gagara-badau — Mourinho


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Litinin ne Sanchez ya kom a United

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce Alexis Sanchez ya bar kulob mai kayatarwa ya koma na gagara-badau, bayan da dan wasan ya bar Arsenal ya koma United.

Dan kasar Chilen ya koma Old Trafford a wata musaya da aka yi inda dan wasan tsakiya Henrikh Mkhitaryan ya koma Arsenal.

Mourinho ya ce “wannan yarjejeniya ta yi wa kowa dadi”.

Ya kuma tabbatar da cewa Sanchez na cikin tagawar da za su fafata a gasar FA a Yeovil ranar Juma’a.

Saura kiris Sanchez, mai shekara 29, ya koma Manchester City a bazara, ya saka hannu a kan kwantiragin shekara hudu da rabi a United a kan fam miliyan 14 a shekara bayan an cire haraji.

Ya ci kwallo sau 80 a Aresnal bayan da ya koma kungiyar daga Barcelona a watan Yulin 2014, a kan fam miliyan 30, kuma shi ne wanda ya fi cin kwallo a kakar bara inda ya ci kwallo 30 a dukkaan wasannin da ya fafata.

“Mun samu daya daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka iya kai hari a duniya, kuma yana da matukar muhimmanci a wurinmu saboda muna bukatar gwarazan ‘yan kwallo”, in ji Mourinho.

‘Yan kwallo mafi tsada a City


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Man City ta sayo Kevin de Bruyne daga Wolfsburg a kan kudi fam miliyan 55 a shekarar 2015.

Dan wasa mafi tsada a kungiyar Manchester City shi ne Kevin de Bruyne, wanda aka sayo daga Wolfsburg a kan kudi fam miliyan 55 a shekarar 2015.

Benjamin Mendy ne yake bi masa baya wanda aka sayo kan kudi fam miliyan 52 daga Monaco a shekarar 2017.

Sai kuma John Stones da aka dauko daga Everton a shekarar 2016 a kan kudi fam miliyan 47.5

Na hudunsu shi ne Kyle Walker wanda ya dawo kungiyar a kan kudi fam miliyan 45 a shekarar 2017.

Sai kuma na karshe Raheem Sterling wanda aka sayo daga Liverpool a shekarar 2015 akan kudi fam miliyan 44.

Yanzu kuma kungiyar na son daukar mai tsaron bayan Athletico Bilbao Aymeric Laporte a kan kudi fam miliyan 57 a matsayin dan kwallo mafi tsada a kulob din.

Nigeria: Za a yi wa mutum miliyan 25 riga-kafin shawara a 2018


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sauro ne ke haddasa cutar, kuma masana sun bayyana cewa alamominta sun hada da zazzabi mai zafi, tsananin ciwon kai, da amai, da jin sanyi, da kasala

Hukumomin Nigeria tare da hadin gwiwar hukumomi na kasa da kasa, ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, na kaddamar da aikin riga-kafin cutar shawara, wanda shi ne aikin riga-kafin cutar mafi girma a fadin kasar a tarihinta.

Ana sa ran za a yi wa mutum fiye da miliyan 25 riga-kafin a bana.

Aikin riga-kafin ga dimbin jama’a wani bangare ne na kokarin kawar da cutar ta shawara a duniya baki daya izuwa shekara ta 2026 kamar yadda hukumomin lafiya suka bayyana.

A ranar Alhamis ne ake soma aikin a jihohi uku da suka hada da Zamfara da ke arewa maso yamma da kuma Kogi da Kwara a arewa ta tsakiya.

Nan da ‘yan kwanaki kuma za a fadada zuwa jihar Borno, inda za a bai wa mutanen da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram, muhimmanci a aikin.

Cikin kwanakin da ke tafe, ana sa ran yi wa mutum miliyan 8.6 riga-kafin na shawara, yayin da a tsawon shekarar kuma ake son yi wa mutum fiye da miliyan 25 musamman a jihohin da suka fi fuskantar kasadar barkewar annobar cutar.

Bayanai na cewa za a yi rigakafin ne ga ‘yan shekara daya zuwa ‘yan shekara 30.

Wata sanarawa daga WHO, na cewa ita da UNICEF su na tallafawa wajen aikin, musamman ta fuskar horar da dubban ma’aikatan lafiya da za a tura wuraren aikin.

Wannan aiki na rigakafi dai na zuwa ne yayin da Najeriya ke fama da matsalar cutar, wadda hukumomi ke cewa ana kyautata zaton ta kama mutum fiye da 350 kana mutum 45 suka mutu tun lokacin da ta barke a watan Satumban da ya gabata a wani gari da ake kira Ifelodun a jihar Kwara.

Sauro ne dai ke haddasawa, kuma masana sun bayyana cewa alamominta sun hada da zazzabi mai zafi, tsananin ciwon kai, da amai, da jin sanyi, da kasala da dai sauransu.

Kuma ta kan yi sanadiyar hasarar rayuka, amma idan aka yi wa mutum rigakafi, to zai iya samun kariya daga kamuwa da cutar tsawon rayuwarsa.

City na son daukar Aymeric Laporte


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Aymeric Laporte na taka leda a Athletic Bilbao.

Manchester City na fatan kammala daukar mai tsaron bayan Athletic Bilbao Aymeric Laporte a kan kudi fam miliyan 57.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya nuna muradinsa a akan daukar dan kwallon mai shekara 23 kuma yana fatan kammala cinikin.

An fara cimma matsaya a kan yarjejeniyar, sai dai ana sa ran za a kammala cinikin kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan tamaulan ranar Laraba.

Yanzu dai Kevin de Bruyne ne dan wasa mafi tsada a kungiyar wanda aka saya a kan kudi fam miliyan 55 a 2015.

Copa del Rey: An yi waje da Madrid


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zidane ya ce yana fargabar makomarsa a kungiyar

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce yana jure matsin lambar da ya fuskanta a matsayinshi na mai horar da kungiyar, kuma zai mayar da hankali wajen samun kyakkyawar makoma da kuma yin nasara a gasar zakarun Turai.

Madrid na da tazarar maki 19 tsakaninta da ta daya a teburin La Liga Barcelona, kuma a daren jiya ne aka fitar da kungiyar a gasar Copa del Rey bayan ta sha kaye a hannun Leganes a karawar da suka yi daren jiya Laraba a Bernabeu.

“Lokacin da na fuskanci matsin lamba a matsayina na koci, ban yi nadamar komai a kan wasan ba, kodayake na dora alhakin akan abun da nayi,” in ji kocin.

Ya kara da cewa,”Ba muyi amfani da salon da ya dace ba a farkon wasan, kuma hakan ne ya ba ni haushi. Ban fahimci abin da yake faruwa ba”.

West Ham na daf da daukar Joao Mario


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Joao Mario na taka wa Inter Milan da Portugal leda

West Ham ta kusa kammala daukar aron dan wasan tsakiyar Inter Milan da Portugal Joao Mario.

Kocin kungiyar David Moyes na san kara ‘yan wasansa bayan da Manuel Lanzini da Marko Arnautovic suka tafi hutun jinya.

A watan Agustan 2016 ne kungiyar ta dau Mario daga Sporting Lisbon akan kudi fam miliyan 35.

Halin da kungiyar ta samu kanta ne ya yi sanadiyyar korar kocin kungiyar biyu a bara, aka kuma nada na uku a lokacin bazara, lokacin da Luciano Spaletti ya karbi aikin horarwar daga hannun Stefano Vecchi.

An kama ‘faston’ da ya halasta zina da shan giya a Tanzania


‘Yan sanda a Tanzaniya sun kama wani da ya kira kansa fasto bayan an gan shi a wani bidiyo inda yake rawa da kwalaben giya da kuma ikirarin cewa littafin baibil ya halatta shan giya da zina.

Gwajin lafiyar da aka yi wa mutumin mai suna Onesmo Machibya, mai shekara 44, wanda aka fi sani da suna Manzo Tito, ya nuna cewar yana da tabin hankali, in ji Gilles Muroto, kwamandan ‘yan sanda a babban birnin kasar, Dodoma.

Kawo yanzu dai Mista Machibya ko kuma wakilansa ba su yi magana ba.

Bidiyon da aka yi ta yayatawa a shafukan sada zumunta sun nuna mutumin da ke ikirarin cewa shi manzo ne yana rawa kuma yana sumbatar matarsa da wata matashiya, yana mai cewa babu matsala mutum ya yi jima’i da matar da ba tasa ba.

‘Yan sanda sun zarge shi da bayar da takardu a wuraren shakatawa da kuma wuraren sayar da barasa a Dodoma, da kuma yayata akidar da ta yi hannun riga da al’ada da dabi’un Tanzaniya.

An saki bidiyon yadda aka kashe sojojin Amurka a Niger


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An yi jana’izar sojojin da suka mutu a Amurka

Rundunar sojin Amurka ta ce tana kokarin tantance bidiyon da ake yayatawa a kafafan Intanet wanda ke ikirarin nuna gawarwakin sojojin Amurka bayan an kai musu hari a Nijar a shekarar da ta gabata, in ji kafar watsa labarai ta The Hill.

Wata sanarwar da rundunar sojin Amurka a Afirka (USAFRICOM) ta fitar ta ce: “Muna nazari a kan bidiyon kuma muna kokarin tantance gaskiyar sakon na Twitter da kuma ikirarin cewa bidiyo ne na kisa.”

Sanarwar ta kara da cewa, rundunar ba za ta kara cewa komai ba game da lamarin har sai an kammala bincike.

Ranar 4 ga watan Oktobar bara ne dai aka yi wa sojojin Amurka 12 da kuma sojojin Nijar 30 kwanton bauna a kauyen Tongo da ke kudu maso yammacin kasar, wurin da ke da tazarar kilomita 240 daga babban birnin kasar, Niamey.

Rahotanni sun ce kimanin masu kaifin kishin Islama 50 dauke da manyan bindigogi ne suka yi wa sojojin kwanton bauna.

Wani mai bincike ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, wata kungiya mai alaka da kungiyar IS ta fitar da wani bidiyo, kuma ya kara da cewa bidiyon ya nuna sojojin da suka ji ciwo da kuma gawarwakin sojojin Amurka.

Rahotanni dai sun ce sojojin sun je neman bayanai ne game da wani babban mai tayar da kayar baya a yankin.

Amurka tana da kimanin sojoji 800 a yankin, in ji kafar The Hill .

Sakin fim din Padmavati ya janyo zanga-zanga a India


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana zanga-zanga a India saboda sakin fim din Padmavati na Bollywood

Masu zanga-zanga a jihar Gujarat ta kasar India, sun toshe hanyoyi tare da dakatar da zirga zirgar motocin bas, bayan kotun kolin kasar ta bayar da umarnin sakin fim din nan na Bollywood da ke janyo ce ce-ku ce wato Padmavati a ranar Alhamis.

Masu tsattsauran ra’ayi na addinin Hindu, sun kona motocin bas da kuma kwasar ganima a wata sinima da ke yammacin jihar ta Gujarat.

Ce ce kucen ya samo asali ne bayan da wasu kungiyoyi na addinin Hindu wato ‘yan bangaren da sarauniyar ta fito, suka ce, a lokacin da aka fito da tallan fim din, an nuna wani wuri da aka bata sunan sarauniyar, inda aka nuna ta da wani sarki musulmi, Alaudin Kilji, suna soyayya.

Wannan dalili ya sa suka ce, an ci mutuncin sarauniyar, kuma hakan ya sosa musu rai, don haka sam ba za su amince da fim ba, ballantana a sake shi har duniya ta gani.

Kotu ta amince a saki fim din Padmavati

An ci zarafin jarumar fim din Dangal Zaira Wasim a cikin Jirgi

An dai ta kai ruwa rana game da haramcin fim da wadan da suka fito daga bangaren sarauniyar suka ce, domin har kotu aka je, daga karshe kuma kotun kolin kasar ta amince da a saki fim din, bayan ta umarci wanda ya shirya fim din, Sanjay Leela Bhansali, da ya cire duk wasu wuraren da basu kamata ba a cikin fim din.

Fim din na Padmavati, labarin fim din wata kyakkyawar sarauniya ce daga bangaren mabiya addinin Hindu wadda aka taba yi a karni na 14, tare da wani sarki musulmi.

Wannan dai ba shi ne fim na farko da aka taba yi wa zanga-zanga a India ba.

Gasar kyau ta rakuma ta bar baya da kura


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana gudanar da gasar kyau ta rakuma a duk shekara a Saudia

An hana rakuma 12 shiga gasar kyau ta rakuma da ake yi shekara-shekara a kasar Saudiyya, saboda masu su sun yi musu alluran ta da komada.

Alkalan sun duba siffofi daban-daban na rakuman wadan da suka hada da, yanayin tozonsu da kyan kunnuwansu, kai harma da girman labbansu ana duba wa.

Saudiyya ta kori raƙuman Qatar daga kasarta

Wasu sun yi liyafa da naman shanu a Indiya

Wannan dalili ya sa masu rakuman suka yi kokarin tayar musu da komada domin kara musu kyau sosai ta yadda za suyi nasara a gasar.

Dubban masu rakuma ne kan shiga gasar kyau ta rakuman, wadda ake yi a wajen birnin Riyadh, inda ake cin kyautar miliyoyin daloli.

EFCC ta kama Babachir Lawal


Hakkin mallakar hoto
The Guardian

Image caption

Kamen nasa na zuwa ne bayan kwana daya da tsohon shugaban kasa, Olusegun ya soki gwamnatin kasar kan yaki da cin hanci da rashawa

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nigeria watau EFCC ta ce ta kama tsohon sakataren gwamnatin kasar , Babachir Lawal.

Rahotanni sun ce a jiya Laraba ne jamian EFCC suka capke Mr Lawal.

A kwanakin baya da suka gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya kori Mr Lawal din.

Ya kuma dauki wannan matakin ne bayan kwamitin da ya kafa domin gudunar da bincike kan zargin karkatar da kudaden da aka ware ma ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita, ya same Babachir Lawal da laifi.

A baya ma ,Majalisar datawan kasar ta sameshi da laifi dangane da wannan batu.

Kamen nasa dai na zuwa ne bayan da tsohon shugaban kasar Nigeria, cif Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Buhari da rashin daukar mataki akan mutane da ke da kusanci da shi, wadanda ake zarginsu da almundahana.

Wadanne ‘kura-kurai’ Buhari ya tafka tun hawansa mulki?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce ‘yan Najeriya sun yi tururuwar zaben Shugaba Buhari ne a 2015 saboda gazawar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta bangarori da dama.

Sai dai ya ce har yanzu ana fama da matsalolin da aka yi fama da su lokacin mulkin Mista Jonathan din ba tare da samun sauyi ba.

Matsalolin kuwa da ya lissafa sun hada da rashin taka rawar gani a wajen gudanar da al’amuran gwamnati, da talauci, da rashin tsaro, da gazawa wajen kyautata tattalin arziki, da bai wa wasu na kusa da shi mukamai da sakaci wajen tafiyar da aiki.

Ya kara da cewa akwai kawar da kai yayin da ake aikata ba daidai ba da rashin hadin kan kasa da rashin tafiyar da siyasar cikin gida yadda ya dace da kuma karuwar bambance-bambance tsakanin masu hali da marasa galihu.

Sai dai Cif Obasanjo ya ce baya ga wadancan matsaloli, akwai wasu bangarori guda uku da gazawar Buhari ta fito fili ba kamar yadda aka zata ba.

“Ta farko ita ce bai wa na kusa da shi mukamai da ya yi daidai da mutum ya debo ‘yan kabilarsa ya damka musu komai. Wannan ya yi mummunan tasiri a kan tafiyar da sha’anin mulkinsa wanda haka bai haifar wa kasar alheri ba.

“Ya ya za a bayyana badakalar mayar da Abdulrashid Maina bakin aiki? Batutuwa irin wannan nawa aka boye aka ki bayyana wa al’umma?” a cewar Obasanjo.

Wasikar ta ci gaba da cewa gazawa ta biyu daga Buhari ita ce rashin iya tafiyar da siyasar cikin gida yadda ya dace.

“Wannan al’amari ne da ya sa aka kara samun rarrabuwar kawuna a kasar da kuma karuwar bambance-bambance tsakanin masu hali da marasa galihu. Hakan ya yi matukar tasiri ga tsaron kasar.”

“Gazawa ta uku ita ce yadda yake dora laifukan gazawarsa a kan wadansu. Alal misali, yadda yake zargin gwamnan babban bankin Najeriya da rage darajar naira da kashi 70 cikin 100, da kuma zargin gwamnatocin baya da hakan.

“Kar mu bari wani ya yaudare mu, tattalin arziki ya ta’allaka ne akan siyasa, saboda haka tun da siyasarmu ta shiga halin ni-‘yasu, dole tattalin arzikinmu ya shiga halin ha’ula’i.

“Idan da a ce komai yana tafiya yadda ya kamata to da ba za mu bukaci Shugaba Buhari ya shigo cikin tafiyar ba ma.”

Ba Cif Obasanjo ne kawai mutumin da ya taba fitowa karara ya bayyana gazawar Shugaba Buhari ba, ko a baya ma an taba samun mutanen da a baya na kusa da shi ne da suka soke shi kan mulkinsa.

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/TUNDE BAKARE

A baya-bayan nan ma mutumin da ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a shekarar 2011, Fasto Tunde Bakare, ya ce gwamnatin Buharin ta jefa Najeriya a halin ci baya maimakon ci gaba.

A cewarsa, “Wannan gwamnatin ta kafu ne a jigo uku, wadanda suka hada da magance matsalar tsaro da samar da ayyuka da yaki da cin hanci, amma idan ka duba babu abin da za ka gani sai alamomin ci gaba.

Haka shi ma Buba Galadima wanda yana daya daga cikin jigogin da aka kafa jam’iyyar APC da su, tare da kasancewa na gaba-gaba wajen fafutukar ganin Shugaba Buhari ya samu mulkin Najeriya, ya ce bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin ba.

A kwanakin baya ya shaida wa BBC cewa a yanayin salon jagorancin jam’iyyar da kuma mulkin da ake yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Buba Galadima ya ce Buhari ya yi watsi da jama’arsa na asali

Baya ga mutanen da a da suke marawa Shugaba Buhari baya ma, akwai mutanen da har a yanzu suke da kusanci da shi amma kuma suka fito fili suka fadi wasu kura-kurai da a cewar su in har bai gyara su ba to fa ba lallai ya samu nasarar zarcewa a mulkin ba a 2019.

Daya daga cikin wadannan mutane su ne matarsa Aisha Buhari, wadda a karshen shekarar 2016 a wata hira da BBC Hausa ta ce, wasu ‘yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, inda suke hana ruwa gudu.

Duk da cewa Aisha ba ta bayyana sunayen mutanen ba, sai dai ta ce ‘yan Nigeria sun sansu kuma “tana tsoron boren da za su iya yi.”

Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa shugaba Buharin ya yi watsi da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar APC wadanda suka sha wahala da mijin nata a lokacin gangamin yakin zabe.

Mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya Dokta Abubakar Kari ya ce daya daga cikin kuskuren shugaban shi ne “rashin nakaltar dimokradiyyar cikin gida saboda nada wadansu mutane na kut da kut misali gaba daya manyan jami’an tsaro ‘yan Arewa ne kuma Musulmi ne.”

Hakazalika ya ce “akwai mukamai da dama da aka bai wa wadansu da ake ganin suna da dangantaka ta jini ko auratayya misali Ministan albarkatun Ruwa na kasar Husseni Adamu.”

Masanin ya ce yawancin masu fada a ji na fadar shugaban kasa suna da alaka da shi,”amma a baya ba haka abin yake ba don za ka ga mutane ne daga sassan Najeriya daban-daban.”

Dangane da batun dorawa gwamnatocin baya laifi, Dokta Kari ya ce masu magana da yawunsa suna yawan dora laifi ga gwamnatocin da suka gabata.

Ya ce mutane suna kafa hujja da cewa saboda haka ne aka zabe shi wato saboda ana tunanin Buhari zai iya kawo gyara, masanin ya ce wannan ya sa jama’a kin gamsuwa da uzurin gwamnatinsa.

Dokta Kari ya kara da cewa shugaban ya nisanta kanta daga talakawa, “amma a lokacin neman zabe talakawa na da yakinin cewa shi nasu ne don zai share musu hawaye amma sai aka samu akasin hakan.”

Har ila yau masanin ya ce “cin hanci ya ragu a kasar amma kuma ba a daina ba.”

Ya kuma ce “ba a daina daukar ma’aikata ta bayan gida ba. Na kusa da shi na cin karen su ba babbaka kuma ba abin da ake yi, ko abin ya fito fili ba ya daukar wani mataki.”

“Hakan ce tasa wasu ke ganin Buharin ne kuwa?” in ji shi.

Tasiri a zaben 2019

Dokta Kari ya ce “gaskiya ni ina ga idan abubuwa suka ci gaba yadda suke a yanzu, to za su yi tasiri kan sake tsayarwarsa takara a zaben shekarar 2019.”

Daga nan ya ce “a baya irin wannan abuwane ne suka jawo aka ki sake zabar gwamnatin PDP.”

“Magoya bayan Buhari da dama a ciki da wajen kasar jikinsu ya yi sanyi. Idan ba a yi hankali ba da dama ba za su fito zabe ba, wadansu kuma za su iya zabar abokan adawarsa.”

Ko lokaci ya kure wa Buhari?

Sai dai masanin ya ce lokaci bai kure wa shugaban ba, “don zai iya yin gyara.”

“Zai iya gyarawa tun da akwai sauran kusan watanni 15, muddin ya yarda an yi kuskure, kuma aka dauki matakin gyara to zai iya yin nasara, amma idan dai aka ci gaba a yadda ake yanzu to zai iya shan kasa a 2019,” in ji shi.

Dan Nigeria Shehu Abdullahi ya koma Bursaspor


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shehu ya ci kwallo uku a wasa 48 da ya yi wa Anorthosis Famagusta

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeri, Shehu Abdullahi koma Bursaspor daga Anorthosis Famagusta kan yarjejeniyar shekara biyu da rabi.

Dan wasan mai shekara 24, ya shiga Anorthosis Famagusta daga União da Madeira a Satumbar 2016.

Abdullahi, wanda ya murza-leda a Kuwait da Portugal zai yi wasa a Busaspor tare da William Troost-Ekong da Mikel Agu da Paschal Okoli karkashin tsohon kocin Kamaru Paul Le Guen.

Dan wasan ya buga wa Nigeria gasar matasa ta duniya ta ‘yan shekara 23 a 2013 a Turkiya da gasar CHAN da aka yi a 2014 a Afirka ta Kudu.

2019: ‘Batun tazarce ba shi ne a gaban Buhari ba’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ministan ya ce hauhawan farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a watanni 11 a jere

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce maganar sake tsayawa takara ba shi ne a gaban Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba a wani martani da ya aike ga tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.

Jami’in gwamnatin ya ce wajibi ne a yaba wa Buhari kan abubuwa biyu cikin ukun da aka yi kamfe a kansu; wato yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki masu tada kayar baya.

Har ila yau, ministan ya ce tsohon shugaban ya ce gwamnatin Buhari ba ta samu nasara ba a fannin tattalin arziki saboda shi ne na uku cikin jerin alkawurran da aka yayin kamfe.

Daga nan ya ce yana ganin cewa aikace-aikacen Obasanjo ne ba su “ba shi sukunin fahimtar dimbin ayyukan ci gaban da gwamnatin Buhari take gudanarwa ba a halin yanzu musamman a fannin bunkasa tattalin arziki.”

Ministan ya kuma ce dukkan alkalumman da ake amfani da su wajen bayyana karfin tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya na samun ci gaba.

Hakazalika ya ce kasar ta fita da matsin tattalin arziki ne ta hanyar amfani da shawarwarin da wadansu ‘yan kasar suke ba ta.

Bugu da kari, ministan ya ce hauhawan farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a wata 11 a jere.

Ya ce fito tsarin amfani da asusu na bai daya wato (TSA) ya sa gwamnatinsu ta tara naira biliyan 108 kuma ya ce kasar tana adana fiye da naira biliyan 24 a kowane wata daga sabon tsarin.

Jami’in gwamnatin ya ce sun samu naira biliyan 120 bayan sallamar ma’aikatan bogi.

An kai wa kungiyar agaji ta Save the Children hari


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Harin ya sa bakin hayaki ya turnuke yankin baki daya

Maharan sun tayar da abubuwa masu fahsewar ne kafin daga bisani su shiga ofisoshin ma’aikatan agaji na kungiyar Save the Children a birnin Jalalabad na gabashin Afghanistan.

A kalla mutum biyu ne suka mutu, wasu 12 kuma suka jikkata in ji jami’ai. An yi amannar cewa kusan mutum 50 ne suke cikin ginin ofishin a lokacin faruwar abun.

Kungiyar IS ta ce uku daga cikin mayakanta ne suka kai harin.

A yanzu haka dai kungiyar Save the Children ta dakatar da ayyukanta a Afghanistan na wucin-gadi.

Ya ya harin ya faru?

Harin ya faru ne da karfe 9 na safiyar kasar a ranar Laraba, a yayin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wata mota a gaban mashigar ofishin Save the Children, kamar yadda wani mai magana da yawun gwamnan lardin Nangarhar Attaullah Khogyani, ya shaida wa BBC.

Wani ganau da ke cikin ginin lokacin da abun ya faru ya shaida wa kamfanin dillancin labarau na AFP cewa ya ga wani dan bindiga yana dukan kyauren shiga ginin da wata roka.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wata mota a gaban mashigar ofishin Save the Children,

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Jami’an tsaro sun sun yi wa yankin kawanya

Kwamandojin sojin Afghanistan sun hada kai da ‘yan sanda don kokarin kawo karshen harin.

Kusan mutum 45 aka ceto daga ginin da ke kasan ofishin, yayin da aka ci gaba da gwabza fada a saman bene.

Tun da fari dai AFP ta ruwaito cewa wani ma’aikaci ya aiko da sakon Whatsapp da ke cewa” Ina jin maganganun wasu mahara biyu…. Suna neman mu. Ku yi mana addu’a… Ku gayawa jami’an tsaro.’

Akwai wasu kungiyoyin agajin da dama a wannan yankin, da kuma ofisoshin gwamnati.

Pillars ta samu maki uku a kan Abia Warriors


Hakkin mallakar hoto
Pillars Twitter

Image caption

Kano Pillars ta hada maki bakwai a wasa hudu da ta buga

Kano Pillars ta doke Abia Warriors da ci 2-1 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na hudu da suka fafata a ranar Laraba.

Pillars ta fara cin kwallo ta hannun Nyima Nwagua a minti na 18 da fara tamaula, kuma da wannan sakamkon ake tafi hutu.

Bayan da aka dawo ne Abi ta farke ta hannun Ndifreke Effiong, sai dai mintu biyu tsakani Pillars ta kara na biyu ta hannun Lakosa.

Da wannan sakamakon Pillars ta hada maki bakwai a wasa hudu da ta buga a gasar.

Ga sakamakon wasannin mako na hudu da aka buga a ranar Laraba:

 • Plateau United 3-0 El-Kanemi
 • Rangers 1-0 Katsina
 • Kwara Utd 1-0 Wikki
 • MFM 2-1 FCIU
 • Sunshine 2-0 Rivers
 • Niger Tornadoes 1-2 Akwa United

Obasanjo bai isa ya gaya wa Buhari abun da zai yi ba – Dattijan Arewa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar Tuntubar Juna ta Dattawan Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF), ta mayar wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo martani kan budaddiyar wasikar da ya yi wa Shugaba Buhari cewa kar ya sake tsayawa takara a 2019.

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Muhammad Biu, ya fitar, ta ce Shugaba Buhari ne kawai yake da damar yanke shawarar sake tsayawa takararsa a zaben 2019.

Cif Obasanjo dai ya rubuta wasika ce a ranar Litinin inda yake shawartar Shugaba Buhari da cewa kamata ya yi ya je ya huta a 2019 saboda yawan shekarunsa da yanayin lafiyarsa.

Kungiyar ACF ta soki Obasanjo da cewa yana son sanya bakinsa a ko wanne al’amari har da wanda bai shafe shi ba.

Wasikar Cif Obasanjo dai ta jawo ce-ce-ku-ce a kasar tun daga ranar Litinin, al’amarin da yake nuna alamar cewa an bude hanyar fara musayar kalamai kan zaben 2019.

Mascherano ya koma China da taka-leda


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mascherano ya ci kwallo daya a shekara takwas da ya yi a Barcelona

Dan wasan tawagar Argentina, Javier Mascherano ya koma buga gasar China a kungiyar Hebei China Fortune, bayan shekara takwas da ya yi a Barcelona.

Dan wasan mai shekara 33, ya koma Barca daga Liverpool a 2010 kan fam miliyan 17, bayan da ya yi West Ham da Corinthians da River Plate, zai kuma bar Nou Camp a ranar 26 ga watan Janairu.

Mascherano ya lashe kofi 18 a Barcelona ciki har da na La Liga hudu da na Zakarun Turai biyu.

Tsohon kocin Manchester City, Manuel Pellegrini shi ne ke jan ragamar Hebei China Fortune tun daga Augustan 2016.

Kocin ya kai kungiyar mataki na hudu a gasar kwallon China a bara, kuma dan wasan Argentina, Ezequiel Lavezzi ya na kungiyar da ya koma can daga Paris St-Germain.

Fitattun ‘yan wasan da suka bar Wenger a Arsenal


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manyan ‘yan wasan da suka bar Arsenal karkashin Arsene Wenger

Alexis Sanchez shi ne dan wasa na baya-baya nan da ya bar Arsenal a lokacin da Arsene Wenger ke jan ragamar kungiyar.

Wenger wanda ya ci Premier uku da FA bakwai da Super Cup, bai hana wasu fitattun ‘yan wasan kungiyar barin Gunners ba a lokacin suna kan ganiyarsu.

Wasu daga cikinsu sun hada da Thiery Henry da Emmanuel Adebayor da Nicolas Anelka da Alex Oxlade-Chamberlain da Samir Nasri da kuma Robert Pires.

Ga jerin fitattun ‘yan wasa 11 da suka bar Arsenal

Jens Lehmann: Ya bar Arsenal a 2008 ya koma Stuttgart a 2008 lokacin da kwantiraginsa ta kare a kungiyar daga baya ya yi ritaya. Ya sake koma wa tamaula a 2011 daga nan ya sake shiga Arsenal.

Bacary Sagna: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Landa.

Kolo Toure: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Arsenal.

Thomas Vermaelen: A shekarar 2014 ya koma Barcelona.

Ashley Cole: Ya koma murza-leda a Stamford Bridge ita kuwa Chelsea ta bayar da William Gallas.

Patrick Vieira: Ya koma wasa ne a Juventus.

Cesc Fabregas: A shekarar 2003 ya koma murza-leda a Barcelona.

Marc Overmars: A shekarar 1997 ya koma Barcelona domin maye gurbin Luis Figo.

Alexis Sanchez: Ya komaOld Trafford, inda Manchester United ta bayar da Henrikh Mkhitaryan.

Robin van Persie: A shekarar 2012 ya koma murza-leda a Manchester United.

Thierry Henry: Ya koma buga tamaula a Barcelona a 2000.

Henry bai ce na bar Arsenal ba – Sanchez


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sanchez ya ci wa Arsenal kwallo 80 tun komawarsa can a 2014 daga Barcelona

Sabon dan wasan Manchester United, Alexis Sanchez ya ce Thierry Henry bai ce masa ya bar Arsenal ba, don radin kansa ya yanke shawarar barin kungiyar.

Bayan da dan kwallon tawagar Chile ya koma United ne Arsenal ta karbi Henrikh Mkhitaryan, sai Sanchez ya kawo misalin tattaunawar da ya taba yi da Henry.

A ranar Litinin ne Sanchez ya koma Old Trafford a kuma ranar ya yi rubutu a shafinsa na Instagram cewae ”Na tuna ranar da na tattauna da Henry, dan wasa mai hazaka wanda ya sauya kungiya saboda dalili iri daya da muke da shi”.

Wannan batun ya sa wasu magoya bayan Arsenal ke fassara cewar Henry ne silar tafiyar Sanchez , sai dan dan kwallon Faransa ya ce bai ta ba cewa dan wasan Chile ya bar Gunners ba.

Sanchez ya ce Henry wanda ya koma Barcelona a 2007 yana kaunar Arsenal, inda ya yi rubuta a Twitter da cewar ”Zai yi kyau wata rana na ganshi yana horar da Arsenal”.