China ta rage harajin shigar da fatar jaki kasar


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

China ta rage harajin shigar da fatar jaki kasar

China ta rage harajin shiga da fatar jaki kasar, wadda suke amfani da ita wajen hada maganin gargajiya, duk da tsorn da ake na rage yawan dabbobi a fadin duniya.

Daga ranar Litinin ne za a rage harajin daga kashi biyar cikin 100 zuwa kashi biyu cikin 100, don saukaka shiga da shi.

Maganin da ake yi da fatar jakin na da matukar tsada a kasar, kuma shi ne maganin da aka fi saye a shekarun baya-bayan nan.

Masu fafutuka sun ce hakan zai kawo rage yawan jakai a kasashen Afirka, inda aka fi yin amfani da su wajen daukar kaya da kuma tafiye-tafiye.

A yawancin kasashen Afirka, tuni aka samu karancin dabbobi sakamakon samun yawan bukatarsu.

A China kuwa ana amfani da fatar jakin ne wajen hada maganin gargajiya na gelatine, wanda yake maganin amosanin jini.

Har ila yau naman jaki shaharrren abinci ne a China, amma saboda karancinshi a kasar da kuma rashin yawan haihuwa akai-akai ya tilasta musu fita wasu kasashen nemo shi.

Ana amfani da dafaffiyar fatar jaki wajen hada magani Ejiao, inda suke sayer da shi kusan fam 300 duk kilo daya.

Tuni kasashen Afirka irinsu Uganda, daTanzania, da Botswana, da Niger, da Burkina Faso, da Mali, da kuma Senegal suka haramta fitar da jakai zuwa China.

Man City ta kasa cin Crystal Palace


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Manchester City tana nan a matakinta na daya a kan teburin Premier

Crystal Palace ta kawo karshen lashe wasa 18 a jere da Manchester City ta yi a jere a gasar Premier ta shekarar nan.

Manchester City da Crystal Palace sun tashi wasa babu ci a karawar mako na 21 da suka yi a ranar Lahadi.

Daf da za a tashi daga kwallo Palace ta samu bugun fenariti bayan da Raheem Sterling ya yi wa Wilfred Zaha keta a yadi na 18 din City.

Sai dai Palace din ba ta ci kwallon da Luka Milivojevic ya buga ba, inda mai tsaron ragar City, Ederson ya hana ta shiga gidan kifi.

Cikin wasa 21 da City ta buga a gasar Premier ta bana, ta ci wasa 19 inda 18 a jere ta yi nasara, sannan ta buga canjaras a fafatawa biyu a gasar.

Karim Benzema zai yi jinya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Benzema bai yi atisayen da Real Madrid ta fara a ranar Asabar ba

Dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema zai yi jinya, sakamakon raunin da ya ji a wasan hamayya da Barcelona wanda ake yi wa lakabi da El Clasico.

Real ba ta bayyana ranar da Benzema zai dawo fagen tamaula ba, bisa raunin da ya yi a kafarsa ta hagu ba.

Sai dai kuma ana rade-radin cewar dan kwallon ba zai buga wasan Copa del Rey da Real za ta yi da Numancia gida da waje da karawa da Celta Vigo a gasar La Liga da watakila fafatawa da Villarreal da kuma Deportivo La Coruna ba.

Benzema bai halarci atisayen da Madrid ta fara a ranar Asabar ba, sai da likitocin kungiyar sun duba girman raunin da ya yi a ranar 23 ga watan Disamba.

Real Madrid wadda ta ci kofi biyar a 2017, tana ta hudu a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu da Paris St Germain a gasar Zakarun Turai a watan Fabrairu.

Nike ya yi tallar rigar Barca dauke da sunan Coutinho


Hakkin mallakar hoto
Nike Website

Image caption

Liverpool ba ta sallama tayi biyu da Barcelona ta yi wa Coutinho a lokacin bazara ba

Kamfanin da yake yi wa Barcelona kayayyakin wasa, Nike ya yi tallar rigar kungiyar dauke da sunan dan kwallon Liverpool, Philippe Coutinho.

A jerin sunayen ‘yan kwallon da Nike ya rubuta a jikin rigar wadda ya wallafa a shafinsa na Intanet ya ce ”Philippe Coutinho ya shirya bayyana a Camp Nou”, sai dai kuma ya goge rubutun daga baya.

Coutinho dan kwallon Brazil, mai shekara 25, yana saka kayan wasa na kamfanin Nike, wanda ke daukar nauyin dan kwallon.

Coutinho ya bukaci koma wa Barcelona a lokacin bazara, kuma ana rade-radin cewar zai koma Camp Nou a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon ta Turai.

Liverpool taki sallama tayin da Barcelona ta yi wa dan kwallon kan fam miliyan 72 da fam miliyan 90 a lokacin bazarar.

BBC ta tuntubi kamfanin Nike da Barcelona don karin bayani.

Mutum 36 sun mutu a hatsarin mota a Kenya


Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty

Image caption

Adadin wadanda suka mutu ya karu daga 30 zuwa 36 bayan da shida daga cikin masu raunuka sun mutu a asibiti.

Fiye da mutum 36 suka mutu a wani mummunan hatsarin mota tsakanin wata motar fasinja da mai dakon man fetur.

Hatsarin ya auku ne da safiyar Lahadi a garin Salgaa dake kimanin kilomita 200 yamma da birnin Nairobi, inda fiye da mutum 12 suka jikkata.

A sanadiyyar wannan hatsarin, hukumar sufurin da kiyaye hatsurra ta Kenya ta dakatar da tafiye-tafiyen dare ga motocin sufuri masu dogon zango.

Hukumar kuma ta bayyana cewa hatsarin, wanda ya auku da misalin karfe 3 na dare, ya auku ne a sanadiyyar wani taho mu gama tsakanin wata motar fasinja mai daukar mutum 62 da wata tankar man fetur a wani wuri da yayi kaurin suna sabili da yawan hatsura.

Kungiyar Red Cross ta Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 36.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty

Image caption

Jami’ai sun ce 34 daga cikin matattun fasinjojin motar bas din ne kuma biyu na cikin babbar motar

Sauran wadanda suka sami raunuka an kai su babban asibitin garin Nakuru da wasu asibitocin dake garuruwan dake kusa.

A farkon watan Disamba, fiye da mutum fiye da 20 ne suka halaka a wani hatsarin mota a daidai wannan wurin.

Kuma hukumar sufuri da kiyaye hatsurra ta kasar ta ce ta damu da yadda ake asarar rayuka kimanin 3,000 a kowace shekara, ta a dalilin hatsurran mota a fadin kasar.

A bana kadai, mutum 2,883 ne suka halaka a a kan wannan hanyar, kuma mutum 300 a cikinsu sun mutu ne a watan nan na Disamba.

‘Sojin Najeriya sun fatattaki ‘yan boko haram daga Kanamma’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sojin Najeriya sun fatattaki ‘yan boko haram daga Kanamma

Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta fattaki mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da suka kai hari a wani barikin soja da ke garin Kanamma a jihar Yobe.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa maharan sun yi hakon wasu layuka a yankin wanda ake kusa da iyakar Nijeriya da Nijar.

To sai dai kwamandan rundunar dake yaki da Boko Haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Rogers ya shaida wa BBC cewa sojoji na sama da na kasa sun kori ‘yan Boko Haram din. Ya kara da cewa jami’an tsaro sun yi amfani da jirgin saman yaki a lokacin artabun wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana yinsa.

To amma ya ce kawo yanzu ba zai iya tabbatar da irin hasarar rayuka ko jikkata da aka yi a lamarin ba.

A halin da ake ciki kuma wasu rahotanni na cewa wasu mahara da ake jin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Maiwa dake kusa da Maiduguri babban birnin jihar Borno inda suka kashe akalla mutane hudu. Bayanai sun ce wadanda lamarin ya rutsa da su a jiya Asabar sun tafi daji ne domin nemo icen hura wuta.

Kwamandan rundunar ta yaki da Boko Haram ya nanata kira ga mayakan Boko Haram da cewa su tuba su a jiye makamansu. Ya ce duk wanda ya ajiye makaminsa kuma ya tuba, to rundunar soja ba zata yake shi ba.

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a shekarar 2017


Ga wasu zababbun hotuna da wasu abubuwa da suka faru a Afirka a shekarar 2017:

Hakkin mallakar hoto
Daniel Irungu/EPA

Image caption

A watan Janairu wasu yara masu rawar kudancin Amurka ta balleri suna shirin yin darasi kan rawar a wata makaranta ta Spurgeons Academy, wadda ke samar da ilimi kyauta ga marayu fiye da 425 da kuma yara marasa galihu da ke yankin Kibera a birnin Nairobi na kasar Kenya.

A group of young boys stretch their legs before playing a game of football on the beachHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A wannan watan ne dai kuma wasu ‘yan yara maza suke shirin yin tamaula a bakin gabar teku a yankin West Point da ke Monrovia, babban birnin Laberiya.

A cake for Zimbabwe's President Robert Mugabe with his portrait and the numbers 93 in Harare, Zimbabwe - Tuesday 21 February 201Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A watan Fabrairu ne wani ma’aikacin Shugaban Zimbabwe Ribert Mugabe ya yi masa wani babban kek mai hotonsa don taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

South Sudanese refugees queuing for food in Kuluba, Uganda - Friday 24 February 2017Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan gudun hijira sun yi layi a wajen karbar abinci na MDD a Kuluba a cikin wannan wata. MDD ta ce fiye da ‘yan Sudan Ta Kudu miliyan daya ne suke samun mafaka a Uganda tun fara yakin basasa a watan Disambar 2013, kuma a kalla wasu 100,000 ne suka shiga wajen a bana.

Somali model Halima Aden presents a creation for fashion house Max Mara during a fashion week in Milan, Italy - Thursday 23 February 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Halima Aden ce mace ta farko wacee sanye da hijabi da ta shiga yarjejeniya da kamfanin tallan kayan kawa. Halima ‘yar Somaliya tana tafiyar kwalisa a birnin Milan na Italiya a watan Fabrairu.

A group of sharply dressed young men in suits and ties pose togetherHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A watan Afrilu wasu magoya bayan shahararren mawakin nan na Congo Papa Wemba suka ci ado don nuna girmamawa ga mawakin bayan ya mutu.

A man sells roast mice to passing motorists near Salima, Malawi 15 May 2017. Mice is a delicacy for many Malawians and is popular as a source of income for many unemployed men in rural Malawi.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A watan Mayu ne wani mutum yake sayar da gasassun beraye a kan titi a garin Salima na kasar Malawi.

Olufunke Oshonaike of Nigeria competes during Women Single 1. Round at Table Tennis World Championship at Messe Duesseldorf on May 31, 2017 in Dusseldorf, Germany.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Olufunke Oshonaike ta Najeriya a lokacin da take gasar mata ta kwallon kwando a Jamus.

A South African freestyle motor cross rider performs during a carnival to mark 50 month-long celebrations on May 13, 2017 in Lagos. A carnival was held with captivating cultural displays, traditional costumes and folk music to showcase the state rich cultural tradition at the event.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A wannan watan ne kuma, wani mai wasa da babur dan kasar Afirka Ta Kudu ya bai wa ‘yan kallo mamaki a lokacin bikin cikar jihar Lagos shekara 50 da kafawa a Najeriya.

A woman sits next to murals as opposition parties march for the removal of President Jacob Zuma outside the Constitutional Court in Johannesburg, South Africa, May 15, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A Afirka Ta Kudu kuwa, wata mata tana kallon abun da ke faruwa a kusa da kotun tsarin mulki da ke birnin Johannesburg, inda ake maci don neman a tsige Shugaba Jacob Zuma.

Libyans fish from the shore in the eastern city of Benghazi on June 14, 2017Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Yuni, wasu masunta ‘yan Libya sun fito da sassafe don yin su a gabar tekun da ke kusa da birnin Benghazi.

Women after the colour runHakkin mallakar hoto
Mercy Juma/BBC

Image caption

Wasu ‘yan Kenya sun yi bikin ranar kaloli ta farko a kasar, wata al’ada da aka ara daga mabiya addinin Hindu, inda mutane ke jefawa juna hodar kaloli.

A man runs from sea spray as storms hit Cape Town, South Africa, June 7, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A birnin Cape Town na Afirka Ta Kudu a wannan watan, wani mai hoto ya kaucewa feshin tabo s lokacin da ake wata guguwa.

A mural shows spare parts for vehicles on a wall of a shop in Hodan district of Mogadishu, Somalia, July 24, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A watan Yuli, wani wajen gyaran motci a babban birnin Somaliya, ya jera wasu bangarorin motoci don sayarwa a jikin bango. Kasuwanci ya ci gaba da bunkasa a kasar tun bayan da dakarun Kungiyar Tarayyar Afirka ta fatattaki mayakan Al-Shabab daga birnin na Mogadishu.

One of the 51 best Ivorian students of the school year 2016-2017, seated in the place of Ivorian vice president Daniel Kablan Duncan during the first visit to the Cabinet room at the presidential palace in Abidjan.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An gayyaci daliban da suke fi hazaka a Ivory Coast zuwa fadar shugaban kasa a Abidjan babban birnin kasar, da suka hada da wannan yarinyar da aka dauki hotonta a kujerar mataimakin shugaban kasa. Tana daga cikin dalibai 51 da aka girmamasaboda samun sakamako mai daraja a jarrabawarsu.

Eva Msando, widow of Chris Msando at Requiem Mass in Nairobi on 17 August 2017.Hakkin mallakar hoto
Roderick MaCleod/BBC

Image caption

Matar shugaban hukumar zaben Kenya da aka kashe wato Chris Msando ta halarci taron addu’a na tunawa da mijinta, a kusa da ita karamin danta ne. An kashe Mr Msando kwanaki kadan kafin babban zaben kasar.

A mother who lost her son during the mudslide reacts near the entrance of Connaught Hospital in Freetown, Sierra Leone August 16, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wannan wata uwa ce da ta rasa danta a bala’in zaftarewar laka da ya faru a Saliyo, take kua a gaban wani asibitin jami’a a birnin Freetown a watan Agusta. Jami’ai sun ce mutum 400 ne suka rasa rayukansu, yayin da mutum 3,000 suka rasa muhallansu a wannan bala’i mafi muni da yake bukatar agajin gaggawa.

Luvo Manyonga mid-jumpHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A wannan watan ne dai kuma, wani dan wasan guje-guje na Afirka Ta Kudu Luvo Manyonga ya ja hankalin ‘yan kallo a wasannin da ya yi inda ya yi nasara a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje da aka yi a Landan. Shekara hudu da ta gabata, yana tu’ammali da wata kwaya da ake kira “tik”. A yanzu a matsayinsa na zakara a gasar tseren maza, yana burin ya zama zakara a duniya baki daya.

A palace guard stands in front of the Emir"s palace before the start of the Durbar festival, on the second day of Eid al-Adha celebration, in Nigeria"s northern city of Kano September 2, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani bafade yana tsaye a gaban fadar Sarkin Kano gabannin fara hawan babbar sallah a watan Satumba, a birnin da ke arewacin Najeriya.

Pope Tawardros II delivers morning Mass at St Mary ^ St Mina Cathedral on September 1, 2017 in Sydney, Australia. Pope Tawardros II is visiting Sydney, Canberra and Melbourne during his 10 day pastoral visit. Australia is home to the third largest Coptic community outside Egypt. Copts began arriving in Australia in 1969 and there are now over 100,000 who call Australia home. Sydney has some 70,000, and its Diocese now comprises 41 churches, 70 priests, three schools, two monasteries and two Theological Colleges.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwana guda bayan nan shugaban Cocin Kibdawa, Fafaroma Tawardros II, ya yi jawabi ga dumbin mahalarta taron adduo’i a mujami’ar St Mina Cathedral da ke Sydney, a kasar Australiya. Kasar ita ce ta uku a mafi yawan kirsitoci Kibdawa baya ga Masar. T

People manually remove water hyacinth weed from Lake Tana in Bahir Dar, Amhara region in northern Ethiopia, September 1, 2017. Picture taken September 1, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wasu maza na tsinke ganyen wiwi a tafkin Tana da ke arewacin Habasha. Wannan ganye dai yana barazana ga zamantakewar dumbin masunta a gabashin Afirka.

Undated handout photo issued by the Fairtrade Foundation of Fairtrade gold miners in Uganda. Mobile phones could use precious metal which supports better conditions for small-scale miners in Africa under a scheme to supply Fairtrade gold to technology supply chains. PRESS ASSOCIATION Photo. Issue date: Thursday September 21, 2017. See PA story ENVIRONMENT Gold.Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Wasu masu hakar zinare a Uganda suna bakin aiki a wannan ranar.

A supporter of The National Super Alliance (NASA) opposition coalition and its presidential candidate Raila Odinga sits on top of a street sign post that has been relabeled "Judge Maraga Street", referring to Chief Justice David Maraga, and "Orengo Street", referring to NASA"s lawyer James Orengo, in front of the Supreme Court in central Nairobi, Kenya, 01 September 2017. Kenya"s Supreme Court on 01 September overturned the re-election of President Uhuru Kenyatta and ordered a re-run of the election within 60 days, citing irregularities. Ecstatic opposition supporters marched through the city to celebrate "historic" court decision.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani dan kasar Kenya yana zaune a gaban kotun kolin kasar inda babban Mai Shari’a David Maraga ya yanke hukuncin da ya yi wa ‘yan adawa dadi kan korafin da suka shigar na soke zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Agusta saboda kura-kuran da aka tafka. Mutane sun bai wa titunan kusa da kotun sunan alkalin da kuma lauyan James Orengo, don nuna jinjinarsu gare su.

Maitre Gims pulls the beard of his wax look alike at the Musee Grevin wax museum in Paris, France - Monday 2 October 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani mawakin gambara dan kasar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, Maitre Gims, ya tsaya kusa da mutum-mutuminsa da aka kaddamar a Paris, babban birnin Faransa a watan Oktoba.

Chess players in Khartoum, Sudan - Friday 29 September 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A birnin Khartoum kuwa wasu masu yin gasar wasan dara sun dukufa don neman samun nasara a wasan dara da ake yi na kasa a Sudan, a wani bangare na shirin zuwa gasar Olympics.

A pupil prays inside a classroom ahead of the primary school final national examinations at Kiboro Primary school along Juja road in Nairobi, Kenya - 31 October 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wasu lokutan ka kan bukaci taimako. Wannan yaron na addu’a gabannin ya fara zana jarrabawarsa a wata makarantar firamare da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Moroccan children head to the Great Mosque of Sale to pray for rain on November 24, 2017 near the capital of Rabat. Parched Morocco which is heavily dependent on its agricultural sector is holding prayers for rain in mosques across the country under a royal decree. Like its Iberian neighbours to the north, Portugal and Spain, Morocco has suffered a severe shortage of rainfall since the end of the summer. Moroccan university studies show that temperatures have risen by up to 4 degrees Celsius since the 1960s and annual rainfall been on the decline.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu yara ‘yan kasar Morko suna tafiya zuwa Babban Masallacin Sale da ke kusa da babban birnin kasar, Rabat, don yin addu’ar samun ruwan sama. Sarkin Moroko ne ya bayar da umarni ga ‘yan kasar da su yi addu’a don a samu ruwan sama saboda a samu a fara noma don samun wadataccen abinci a kasar.

A picture taken on November 27, 2017 shows African migrants waiting outside in a courtyard at the Tariq Al-Matar detention centre on the outskirts of the Libyan capital Tripoli.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Haka kuma a watan Nuwamba, an dauki hoton ‘yan ci-ranin Afirka a wani waje da ake tsare su a birnin Tripoli na kasar Libya. A wannan watan ne aka samu wani bidiyo da ke nuna wata kasuwar sayar da bayi wadanda ‘yan ci-ranin Afirka ne da ke da muradin zuwa Turai, al’amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.

Anti-Mugabe protesters in Zimbabwe mass in Harare, one of whom holds a signs which reads 'leadership is not sexually transmitted'.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kafin ya yi murabus a watan Nuwamba, Shugaba Robert Mugabe ya fuskanci matsin lamba da barazanar tsigewa a kan tuhumarsa da ake, ciki har da batun barin matarsa da son maye gurbinsa, abun da wasu da dama ke ganin ‘hadama’ ce.

A South African diver dressed as Santa Claus feeds a stingray as he swims in an aquarium during a show before Christmas at Africa's largest marine theme park, uShaka Sea World, in Durban on December 19, 2017.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A watan Disamba, wani mai yin iyo yana ciyar da kifaye a yayin wani bikin nuni a birnin Durban da ke bakin gabar teku a Afirka Ta Kudu.

Hotuna daga AFP da EPA da PA, Reuters da kuma Getty Images

Nada matattu a gwamnatin Buhari rashin iya aiki ne – PDP


Hakkin mallakar hoto
PDP

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari game da nade-naden mutanen da tuni suka mutu a mukamai na hukumomin gwamnati.

Jam’iyyar PDP ta ce wannan ya zama babban abin kunya ga Najeriya a karkashin jagorancin jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya sanya wa hannu, PDP ta ce gwamnatin APC ta gaza.

“Gwamnatin APC ta rikice baki daya, ta yamutse, kuma a fili yake cewa ba zata iya tafiyar da mulkin kasar ba idan aka lura da irin rikon sakainar kashi da gwamnatin APC ke yi wa lamuran kasar.”

Amma kakakin gwamnatin Najeriya, Garba Shehu ya kare wannan lamarin, inda ya ce tsohon jadawali ne da ya dade yana jiran shugaban kasa ya amince da shi:

“Tun watan Oktobar shekarar 2016 aka rubuta sunayen wadanda aka nada. Amma sai aka ajiye shi domin sukar da wasu gwamnoni suka yi.”

Ya ce daga baya shugaba Buhari ya bada umarnin a saki sunayen cikin kurarren lokaci, wanda a ganinsa ya janyo wannan matsalar.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati zata sauya sunayen wadanda suka mutun da wasu wadanda suka cancanta.

A nata bangaren, jam’iyyar ta PDP ta ce wannan batu ya nuna dalilan da suka sa tattalin arzikin kasar ya kasa farfadowa.

“Yaya gwamnatin da bata iya shirya jadawalin ma’aikata ba zata iya fuskantar manyan ayyukan kasa kamar shirya kasafin kudin kasa, da tsare-tsaren ayyukan ci gaban kasa da batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da ilimi da noma da kuma sarrafa ma’aikatan gwamnati?”

Sanarwar ta PDP ta kara da cewa: “Gaskiyar magana ita ce kasarmu ta shiga hannayen wadanda basu san ina suka dosa ba a shekaru biyun da suka gabata.”

Ta ce tana tsoron makomar kasar, daga yanzu zuwa shekara ta 2019.

Kakakin gwamnati, Garba Shehu ya cigaba da kareta, kuma ce bai ga dalilin da za a hukunta wani jami’in gwamnati ba dangane da wannan lamarin.

An kama mahaifin da ya yi shekara 20 yana lalata da ‘yarsa


Image caption

Yarinyar ta ce babanta ne yake lalata da ita sama da shekara 20

An yanke wa wani dan kasar Ajantina mai ‘ya’ya takwas hukuncin shekara 12 a gidan yari.

Wata kotun kasar ta kama Domingo Bulacio mai shekara 57 da laifin yin lalata da ‘yar cikinsa har tsawon sama da shekara 20.

‘Yar tasa wacce hukuma ba ta bayyana sunanta ba, ta ce ya ajiyeta yana lalata da ita tun lokacin tana ‘yar shekara 11.

Al’amarin ya faru ne a garin Villa Balnearia da ke arewacin lardin Santiago del Estero a Ajantina.

Kafofin watsa labaran kasar sun bayar da rahoton cewa mahaifiyar yarinyar (matarsa) ba ta gidan, wata kila ko ta mutu ko kuma ta bar gidan tun lokacin ‘yar tana karama.

Gwajin kwayoyin halittar da aka yi ya tabbatar da cewa yarinyar ta haihu da mahaifin nata.

Ta kara da cewa tun daga lokacin da ta bayar da rahoton cin zarafion da mahaifinta yake mata take fuskantar barazanar mutuwa daga danginsu.

An gano lamarin ne a farkon shekarar 2016, lokacin da yarinyar ta je asibiti da daya daga cikin yaran da aka tambayeta tayi bayani game da mahaifinta.

A lokacin da aka kai rahoton wajen ‘yan sanda, Bulacio ya tsere inda aka shafe kwana 45 sannan ‘yan sanda suka kamo shi suka kuma tsare shi.

Wannan lamari ya yi dai-dai da na Josef Fritzl, wanda aka yanke wa hukunci a shekarar 2009 bisa laifin yin lalata da ‘yar cikinsa na sama da shekara 24, a lokacin da ta haifi ‘ya’ya bakwai tare da shi.

Wasu labaran Afirka da ba ku sani ba a 2017


Hakkin mallakar hoto
AFP

Abubuwa da dama sun faru a shekarar 2017, ciki har da muabus din Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da kuma wani sauyi makamancinsa da aka samu a Gambiya da Angola.

Ba kuma za a manta da soke zaben shugaban kasa da kotu ta yi ba a Kenya, wanda shi ne karo na farko da aka taba samun irin haka a Afirka.

Mun kuma kawo muku rahotanni a kan labaran tashin hankali da na kirkire-kirkire – amma a nan wasu sabbin labarai ne da watakila ba ku ji su ba a cikin shekarar 2017.

Dan ta-kifen da kafafen sada zumunta suka sa ya yi zarra a Kenya’

Wani dan Kenya yana cin githeri, wani nau’in abinci ne da ake ci sosai a kasar, wanda ake dafa masara da wake, yana da cika ciki, yana da gina jiki da kuma araha, a watan Agusta lokacin da ake zabe, mutumin ya yi suna sosai kawai saboda yadda ya dinga cin githeri a kan layin zabe.

Image caption

An yi ta tattauna batun mutumin wanda aka sanyawa sabon suna ‘Mai cin Githeri’ a kafafen sada zumunta na zamani

‘Yan kasar Kenya da dama sun kaunaci Martin Kamotho, saboda yanayin tsayuwarsa, da rigar da ya sa, da yadda ya dinga cika bakinsa da githeri, da kuma rike ledar da ya yi mai dauke da abincin, duk cikin saukin kai.

Yanayinsa ya wakilci abubuwa da yawa ga mutane daban-daban, amma mafi yawa sun dauke shi a matsayin wani tsageri, ko ‘dan-ta-kife’, ko dan ba-ruwana, ko kuma mai saukin kai.

A sakamakon haka a yanzu dai Mista Kamotho ya yi fice sosai da sunan ‘Mai cin Githeri’ kuma ya zama wani da ake yada shi sosai a shafukan sada zumunta a matsayin mai barkwanci:

Wannan fice da ya yi ya sa an yi ta hira da shi a wasu tasoshin talabijin na kasar.

Ficen da yake kara yi a kullum, ya sa kamfanoni da dama a Kenya suke ganin ya zama wata hanyar samun kudi da za su yi mu’amala da shi.

A sakamakon farin jinin da ya yi dai ya samu kyautar fili, an kuma dauki nauyin kai shi yawon bude ido wani shahararren gandun daji na Maasai a Kenya, da kuma kyautar wayoyin komai da ruwanka da aka ba shi shi da iyalansa.

Kuma Mista Kimontho ya kasance daga cikin ‘yan kasar 59 da suka sami jinjina daga shugaban kasa kan aikin da ya yi wa kasar a lokacin bukukuwan tunawa da ranar samun ‘yanci na Kenya.

A cewar jaridar Daily Nation, an bayar da lambar yabon ne don girmama mutanen da suka nuna “wasu dabi’u da za a iya koyi da su, ko cimma wasu nasarori na gwarzantaka ko kishin kasa ko kuma shugabanci.”

Wasu ‘yan kasar har yanzu suna mamakin wanne abu Mista Kimotho ya yi da har ya cancanci irin wannan lambar yabo da jinjina.

Jami’in FRSC a Najeriya ya ‘ci mutuncin mata’

A watan Afrilu, Hukumar Kiyaye Kare Afkuwar Hadurra ta Najeriya ta ladabtar da wani babban jami’inta bayan da aka dauki bidiyonsa yana horar da wasu jami’an hukumar mata hanyar yanke musu dogon kashin kansu.

Hotuna sun nuna yadda jami’in ya dauki almakashi ya dora a kan gashin matan, a yayin da suke wani fareti, al’amarin da ya janyo matukar ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta na kasar.

A bisa doka dai matan sun kaucewa ka’idar aikin hukumar ne na yadda mata za su gyara gashin kansu.

Hakkin mallakar hoto
FRSC Rivers State/Facebook

Image caption

Wata mataimakiya ga Shugaba Muhammadu Buhari ta yi Allah-wadai da abun da jami’in ya yi, tana mai cewa ‘hakan cin zarafin mata ne

Wani mai magana da yawun hukumar FRSC ya ce halayyar da babban jami’in ya nuna ta kaucewa ta hukumar.

Wata mataimakiya ga Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ta yi Allah-wadai da abun da jami’in ya yi a shafinta na Twitter, tana mai cewa ‘hakan cin zarafin mata ne.’

An dakatar da jami’in FRSC kan yi wa mata askin dole

‘Cocin da ke maraba da masu shan barasa’

Wata hudubar da aka saba ji daga shugabannin cocin darikar evangelical ga mabiyansu ita ce, su guji mu’amala da masu shan barasa da sigari.

Amma wani sabon coci a Afirka Ta Kudu yana kalubalantar wannan huduba, inda yake nuna cewa a yi mu’amala da masu shan barasa da sigari maimakon kaurace musu.

Cocin Gobola da ke birnin Johannesburg ya bude kofofinsa da kwalabansa ga masu tu’ammali da barasa, inda yake raba musu barasa a lokacin da ake addu’i’i, a cewar kafar yada labarai ta Afirka Ta Kudu ta eNCA.

Faston cocin Tsietsi Matiki ya ce, cocin waje ne da ya dace sosai da mashaya barasa da masu shan sigari.

Sai dai hukumar kula da coci-coci ta kasar ta ki amincewa da cocin, in ji eNCA.

Wani mabiyin cocin Gobola ya ce, a kan bayar da barasar ce ga wadanda suka kai shekara 20, wato wadanda suka wuce shekarun da dokar kasar ta yi umarnin shan barasa da shekara biyu.

Masu sanko na cikin barazana

A watan Yuni ne, ‘yan sanda a Mozambique suka gargadi masu sanko da yi taka tsan-tsan bayan samun rahotanni cewa matsafa na hakonsu don kashe su.

Kwamandan ‘yan sanda na tankin Zambezi da ke tsakiyar Mozambique ya yi gargadi cewa hare-haren suna da alaka da imanin da wasu suka yi cewa ana samun zinare a kawunan masu sanko.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu sun yi imanin cewa ana samun zinare a kawunan masu sanko

A kalla mutum uku aka kashe a yayin da muka hada wannan labari.

‘Yan sanda sun kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da kashe mutane don yin tsafi.

Karanta karin labari kan lamarin:

‘Yan majalisa sun bai wa hammata iska a Uganda

Wani kokari da ‘yan majalisar jam’iyya mai mulki a Uganda suka yi na yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don cire yawan shekarun tsayawa takarar shugaban kasa ya jawo an bai wa hammata iska a majalisar.

‘Yan majalisa daga jam’iyyar adawa sun ce yin hakan wata makarkashiya ce ta gyarawa Shugaba Yoweri Museveni mai shekara 73, hanya don yin takarar shugabancin kasar a zaben 2021.

A karkashin tsarin mulkin da kasar ke amfani da shi yanzu dai, ba a so duk wanda ke son tsayawa takarar shugaban kasa ya wuce shekara 75.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

An yi ta jifa da kujeru a yayin muhawarar a majalisar dokokin

A bangare guda kuwa, ‘yan majalisar dokokin Afirka Ta Kudu sun yi abun da ya fi na ‘yan majalisar dokokin Uganda kamari.

‘Yan majalisar jam’iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters, sun yi arangama da jami’an tsaro a watan Fabrairu, sakamakon kin bin umarnin da aka ba su na daina katse Shugaba Jacob Zuma a yayin da yake jawabi ga ‘yan kasar.

Fada ya kaure sosai a yayin da jami’an tsaro suka yi kokarin fitar da ‘yan majalisar daga zauren.

A karshe dai sun yi nasarar fitar da ‘yan majalisar amma fa an sha artabu:

An haramta sa wando a Sudan

‘Yan sanda a Sudan sun kai samame wajen da aka yi wata liyafa a babban birnin kasar Khartoum, a watan Disamba inda suka samu wasu mata sanye da wanduna.

An kama matan 24 aka kuma tuhume su da rashin kamun kai, amma daga bisani aka dakatar da tuhumar.

‘Yan sandan da ke kula da bangaren da ke tabbatar da cewa da’a ne suka kai samamen.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A al’adance dai mata a Sudan kan sanya dogayen riguna ne

Idan da a ce an gurfanar da matan, da za su iya fuskantar hukuncin bulala 40 da kuma tara, saboda sanya kayan ‘da ba su dace ba.’

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce an sha kama dubban mata tare da yi musu bulala ko wacce shekara, kuma sun ce za a iya sanya doka ba tare da tsawwala ba.

Sun kara da cewa wannan dokar a kasar da Musulmai suka fi yawa ta hana sanya dogon wando ko gajere ko kuma matsattsen siket, tamkar nuna wariya ce ga Kiristoci.

A al’adance dai mata a Sudan kan sanya dogayen riguna ne.

Wata mai fafutuka Amira Osman ta shaidawa wani gidan rediyon kasar Netherlands, Dabanga, cewa wannan doka ta take hakkin mata.

Ta ce: “An yi liyafar ne a wani rufaffen waje da ke cikin wani gini na El Mamoura a kudancin birnin Khartoum.”

“An kama ‘yan matan saboda sun sanya wando, duk da cewa sun samu izinin yin liyafar daga hukumomi,” in ji Amira.

Karanta karin labarai kan lamarin:

#WengerOut

An ci gaba da samun rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kan kocinta Arsene Wenger, a nahiyar Afirka da ma wasu wuraren.

A watan Nuwamba dai, a yayin da mafi yawan ‘yan Zimbabwe suke murnar kwace mulki da sojoji suka yi daga hannun Robert Mugabe har suka bazu kan tituna suna bukatarsa da ya yi murabus, a sannan ne wasu magoya bayan Arsenal su ma suka bazama tituna suna kiran Wenger da ya yi murabus.

Amma dai hakan ya zama tamkar wani take da aka yi yayi a shekarar nan. An yi irin hakan ma a yayin da ake wani wasa a Habasha a ranar 16 ga watan Afrilu, kwanaki kadan bayan da Crystal Palace ta ci Arsenal a wata fafatawa da suka yi:

Hatsari biyu, ganau daya

Wani dan kasar Kenya ya yi wani abu da ya kullewa mutane na tsawon kwanaki bayan da ya bayar da labarin wasu munanan hadurra biyu da suka faru a kan idonsa, a wasu sassan kasar biyu daban-daban.

An yi ta yada wasu hotuna da wani gidan talbijin ya nuna na mutumin a lokacin afkuwar hadurran, a shafukan sada zumunta.

Mutumin mai suna Dennis Muigai ya yi hira da gidan talbijin na Citizen bayan wani mummunan hatsarin helikwafta da aka yi ranar 21 ga watan Oktoba, inda a kalla mutum biyar suka mutu.

Ya kuma sake shaidar wani hatsarin a ranar 7 ga watan Nuwamba a yankin Murang’a, da ke tsakiyar Kenya, mai nisan kilomita 200 daga inda hatsarin farkon ya faru, inda har wani gwamna ya mutu.

Ya kuma sake shaida wa wani gidan talbijin na NTV cewa, yana cikin fasinjoji ne a wata motar ‘yan sanda a lokacin afkuwar hatsarin, ya kuma yi bayanin abun da ya gani.

A cewar kafar yada labarai ta Nairobi News, ya ce abun da ya fara yi bayan afkuwar hatsarin shi ne ya zare bindigar mai tsaron gwamnan da kuma kayayyakin mutanen cikin motar.

Sai dai wata kafar yada labarai ta kasar ta ruwaito cewa daga baya ne ‘yan sanda suka kama Mista Muigai saboda yin badda kama a matsayin dan sanda. Ba a dai kara sanin me ya faru da shi ba tun lokacin.

A duk hirar da aka yi da shi a gidajen talbijin din, ya manna bakin tabarau a idonsa wanda ke hade da wata na”urar sauraron sauti ta kunne, wanda hakan ya jawo aka yi ta tattauna yanayin shigar tasa a shafukan sada zumunta har ake zolayarsa, aka kuma kirkiri wani maudu’i mai taken #WitnessChallenge a shafin Twitter, inda har wasu suka yi ta kwaikwayon shigar tasa:

Salah ya ceci Liverpool a wajen Leicester


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salah ya ci kwallo 17 a gasar Premier ta shekarar nan

Liverpool ta yi nasarar doke Leicester City da ci 2-1 a wasan mako na 21 a gasar Premier da suka fafata a ranar Asabar a Anfield.

Tun farko Leicester City ce ta daga ragar Liverpool ta hannun Jamie Vardy, kuma haka aka je hutun rabin lokaci Leicester nada kwallo daya a raga.

Bayan da aka dawo ne Mohamed Salah ya farke ya kuma kara ta biyu a raga, kuma jumulla ya ci 17 a gasar ta Premier.

Wannan ne karon farko da Jurgen Klop ya yi nasarar doke Leicester City, bayan kashi da ya sha a wasa uku a baya.

Liverpool za ta jiyarci Burnley a wasan mako na 22 a gasar ta Premier, yayin da Leicester City za ta karbi bakuncin Huddersfield Town.

Chelsea ta zurara wa Stoke City kwallaye


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Chelsea za ta ziyarci Arsenal a wasan mako na 22 a gasar Premier ranar 3 ga watan Janairu

Kungiyar Chelsea ta doke Stoke City 5-0 a gasar cin kofin Premier wasan mako na 21 da suka fafata a Stamford Bridge a ranar Asabar.

Chelsea ta ci kwallayen ta hannun Antonio Rudiger da Danny Drinkwater da Pedro da Willian da kuma wadda Davide Zappacosta ya zura a raga.

Wannan ne karon farko da Chelsea ta zura kwallo biyar a raga a gasar Premier ta shekarar nan, sai dai ta ci FK Qarabag 6-0 a gasar cin Kofin Zakarun Turai da doke Nottingham Forest 5-1 a wasan Caraboa Cup.

Chelsea za ta ziyarci Arsenal a ranar 3 ga watan Janairu a gasar Premier wasan mako na 22, kuma tana ta biyu a kan teburi kafin Manchester United ta buga wasanta da Southampton.

Real Madrid ta koma atisayen tunkarar 2018


Hakkin mallakar hoto
Real Madrid

Image caption

Real Madrid ta lashe kofi biyar a 2017

A ranar Asabar Real Madrid ta koma atisaye a filinta na Valdebebas domin shirin tunkarar kalubalen 2018.

Real mai rike da kofin La Liga da na Zakarun nahiyoyin duniya, ta buga wasan karshe a 2017 da Barcelona, inda Barca ta yi nasara da ci 3-0.

Magoya bayan kungiyar sama da 5,000 ne suka sayi tikiti domin ganin atisayen Madrid wadda ta shirya baje kolin kofi biyar da ta lashe a 2017.

Real Madrid ta ci kofin La Liga da na Zakarun Turai da Uefa Super Cup da Spanish Super Cup da na Zakarun nahiyoyin duniya.

Real Madrid wadda ke mataki na hudu a kan teburin La Liga tana da maki 31 da kwantan wasa daya.

Real za ta buga wasan farko da Numancia a gasar Copa del Rey ranar 4 ga watan Janairun 2018, sannan ta ziyarci Celta Vigo a gasar La Liga a ranar 7 ga watan Janairun.

Sai a ranar 13 ga watan Fabrairu ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Paris St Germain a Santiago Bernabeu.

Kotu ta daure wani dan damfara shekara 13,275


Hakkin mallakar hoto
Paula Bronstein/Getty Images

Image caption

An yanke wa dan damfarar hukuncin shekara 13,275 a gidan yari

Wata kotun Thailand ta yanke wa wani dan damfara hukuncin daurin sama da shekara 13,000 a gidan yari.

Pudit Kittithradilok mai shekara 34 ya yarda cewa ya zambaci mutane ta hanyar shirya wata badakkala inda yayi wa masu zuba jari alkawuran bogi.

Masu shigar da kara sun shaida wa kotun cewa mutumin ya shirya wani taron karawa juna sani.

Ya karfafawa wadanda suka halarci taron kwarin gwiwa da cewa harkar kasuwanci na da alaka da kyau, da yin amfani da motoci da fitar da su.

Kusan mutum 40,000 suka zuba sama da dala miliyan 160 a kamfanoninsa.

An tsare Pudit a gidan yarin Bangkok Remand tun bayan da aka kama shi a watan Agusta, kuma a lokacin an hana bada belinsa.

Kotun ta ci tarar kamfanoninsa biyu wadanda ya yi dai-dai da dala miliyan 20 ga kowanne.

An kuma umarci Pudit da kamfanonin da su biya kimanin dala miliyan 17 ga mutane 2,653 da aka gano na wanda abun ya rutsa da su, da kuma kashi 7.5 cikin dari na ribar shekara zuwa shekara.

Wasu abubuwa da suka faru a fagen wasanni a 2017


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shekara ta 2017 sai san barka ga wasu ‘yan wasa da jami’ai da mahukunta, bayan da suka yi bajinta a fage da dama.

Haka kuma shekara ce da ta ci karo da kalubale a fanni da dama, ciki har da batun shan abubuwa masu kara kuzarin wasanni.

Wasu kuwa jami’ai da ‘yan wasa ba su kai ga karshen shekarar ta 2017 da muke ban kwana da ita ba.

Mohammed Abdu Mam’man Skeeper ya yi bitar wasu daga cikin mahimman abubuwa da suka faru a shekara ta 2017

10 JANUARY

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta kara yawan kasashen da za su buga gasar cin kofin duniya. A bisa sabon tsarin, rukuni 16 mai tawagogi uku ko wanne za a samar a matakin farko kafin a kai matakin kifa-daya-kwala inda tawagogin da suka kai labari 32 za su fafata idan aka fara amfani da sauyin a gasar shekara ta 2026.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta yi ittifaki wajen kada kuri’ar amincewa da kawo sauyin ne yayin wata ganawar da a ka yi a birnin Zurich ranar Talata.

12 JANUARY

Tsohon dan kwallon Ingila da Aston Villa wanda ya horar da Watford, Graham Taylor ya mutu sakamakon ciwon zuciya yana da shekara 72.

25 JANAIRU

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya kwace lambar zinariya ta Nesta Carter dan kasar Jamaica, sakamakon samunsa da laifin shan abubuwa masu kara kuzari.

Nesta ya wakilci Jamaica a tseren mita 100 ta ‘yan wasa hudu a gasar Olympic da aka yi a shekarar 2008, kuma kasar ce ta lashe tseren.

Sakamakon hakan ne yasa aka kwace lambar zinare guda hudun da ‘yan wasan Jamaica suka ci a tseren mita 100 da aka yi a Beijing, cikinsu har da ta Usain Bolt.

Hakan kuma na nufin Bolt din ba shi ne dan wasa na farko da ya lashe lambobin zinare uku a jere a wasannin kakar Olympic uku ba.

28 JANUARY

Serena Williams ta doke ‘yar uwarta Venus da ci 6-4 da 6-4 a wasan karshe a gasar kwallon tennis ta Australian Open, inda hakan ya sa ta lashe babbar gasa ta 23.

29 JANUARY

Carl Frampton ya rasa kambunsa na damben boksin na WBA ajin featherweight a hannun wanda ya karbi kambun Leo Santa Cruz, a dambatawar da suka yi karo na biyu a Las Vegas.

29 JANUARY

Roger Federer ya doke Rafael Nadal ya kuma lashe gasar kwallon tennis ta Australian Open kuma babbar gasa ta 18 da ya lashe.

5 FABRAIRU

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kasar Kamaru ta lashe gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka a karo na biyar bayan ta doke Masar da ci 2-1.

Vincent Aboubakar, wanda aka sako daga baya ne ya zura kwallon da ta ba su nasara minti biyu kafin a tashi daga wasan.

Tun da farko sai da dan wasan Kamaru Nicolas Nkoulou ya farke kwallon da Masar ta ci su, abin da ya bai wa ‘yan wasan kwarin gwiwa.

23 FEBRUARY

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Leicester City ta kori Claudio Ranieri kasa da shekara daya da kocin ya jagorancin kungiyar Lashe kofin Premier a karon farko a tarihi.

26 FEBRUARY

Zlatan Ibrahimovic ya taimakawa Manchester United ta lashe League Cup a Wembley, bayan da United ta doke Southampton 3-2.

08 MARCH

Barcelona ta kafa tarihin kungiyar tamaula ta farko da ta farke kwallo 4-0 a gasar cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League, bayan da ta ci Paris St Germain 6-1 a Camp Nou, inda Barcelona ta kai wasan zagaye na biyu da kwallaye 6-5.

28 MARIS

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta dakatar da Lionel Messi daga buga wa tawagar kwallon kafa ta Argentina wasa hudu.

Fifa ta hukunta dan wasan da ke taka-leda a Barcelona ne sakamakon samunsa da laifin yin kalaman cin mutunci ga mataimakin alkalin wasa a karawar da Argentina ta ci Chile 1-0.

Messi, wanda shi ne ya ci kwallo a fafatawar ta neman shiga gasar cin kofin duniya, ya yi fushi a lokacin da aka hura ya yi laifi, inda ya dinga yi wa mataimakin alkalin wasa surutai.

Haka kuma hukumar ta Fifa ta ci tarar Messi mai shekara 29 kudi fan 8,100.

29 MARIS

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Brazil, ta zama ta farko da ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Nasarar da Brazil ta doke Paraguay 3-0, da cin Argentina da Uruguay da aka yi ne, ya bai wa kasar damar ci gaba da zama ta daya a kan teburin Kudancin Amurka.

30 MARCH

Wanda ya kera butum-butumin Cristiano Ronaldo ya kalubalanci masu sukar aikin da ya yi, inda y ace Ronaldo ya amince da aikin da ya gabatar masa, yayin da ake cewar butum-butumin ya yi kama ne da Niall Quinn ba Ronaldo ba.

07 APRIL

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Kocin Celtic, Brendan Rodgers ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar bayan da ya ci wasa gasar kasar guda 10 a jere.

09 APRIL

Shekara biyar bayan da Sergio Garcia ya ce bai da kwarewar da ta dace ya ci babbar gasar kwallon golf, sai gashi ya yi Justin Rose a gasar kwarru ya kuma lashe ta.

11 APRIL

Aka kai wa motar Borussia Dortmund harin bam guda uku da ya raunata dan kwallonta mai tsaron baya, Marc Bartra, wanda hakan ya sa aka dage karawar da kungiyar ta yi niyyar yi da Monaco a gasar cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League.

29 APRIL

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Anthony Joshua ya dambace Wladimir Klitschko, ita kuwa Katie Taylor ta ci wasan dambe na biyar a jere tun sanda ta zama kwararriyar ‘yar wasa, inda ta doke Nina Meinke a fafatawar da suka yi Wembley.

‘Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar tsallen-baɗake, inda Joshua ɗan boksin ɗin Burtaniya, ya buge tsohon gwarzon duniyan a zagaye na biyar, kafin a kai shi ƙasa a zagaye na shida – karon farko a fafatawa 19 da ya yi.

01 MAY

Mark Selby ya kare kambunsa na zakaran wasan Snooker na duniya, bayan da ya yi nasara a kan John Higgins da ci 18.

12 MAY

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Chelsea ta lashe gasar Premier League a kakar farko da Antonio Conte ya fara jan ragamar kungiyar bayan da ta ci West Brom 1-0 duk da saura wasa biyu a kamala gasar

21 MAY

Celtic ta kammala gasar cin kofin Scottish Premiership ba tare da an doke ta ba, inda ta ci Hearts 2-0 a wasan karshe.

22 MAYU

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Juventus ta lashe kofin Serie A na Italia kuma na shida da ta dauka a jere, bayan da ta ci Crotone 3-0.

22 MAY

Tsohon zakaran tseren motoci ta MotoGP na duniya Nicky Hayden ya mutu yana da shekara 35, kwana biyar da wata mota ta buge shi a lokacin da yake tuka keke a Italiya.

24 MAY

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester United ta doke Ajax 2-0 a Stockholm ta kuma lashe kofin Zakarun Turai na Europa.

27 MAY

Arsenal ta hana Chelsea lashe kofi biyu bayan Premier da ta dauka, inda Gunners ta doke Chelsea 2-1 ta kuma lashe kofin FA Cup, kuma na 13 jumulla.

28 MAY

Dan wasan Roma, Francesco Totti ya yi ritaya yana da shekara 40, bayan shekara 24 da ya yi a kungiyar, wacce ya buga wa tamaula sau 786 ya kuma ci kwallo 307.

3 JUNE

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar zakarun Turai bayan ta doke Juventus da 4-1 a wasan karshen da suka buga a birnin Cardiff da ke Birtaniya. kuma kofi na 12 da ta lashe jumulla.

14 JUNE

Tsohon Zakaran damben boksin na duniya, Floyd Mayweather ya amince ya fafata da Conor McGregor, inda aka tsara wasan domin su kara a Las Vegas a ranar 26 ga watan Agusta.

16 JUNE

Brooks Koepka ya lashe gasar kwallon golt ta US Open, inda tsohon zakara Rory McIlroy ya kasa kai bantensa.

22 JUNE

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan kwallon Roma, Mohamed Salah ya je Liverpool domin a duba lafiyarsa, bayan da ya amince zai koma Anfield da murza-leda kan Euro miliyan 39.

26 JUNE

Tsohon dan wasan tawagar Holland, Frank De Boer ya zama kocin Crystal Palace kan yarjejeniyar shekara uku, sai dai wasa hudu kacal ya jagoranci kungiyar a gasar Premier.

10 JULY

Romelu Lukaku ya amince ya koma Manchester United daga Everton kan kudin da ake cewa zai iya kai wa fam miliyan 100. Shi kuwa Wayne Rooney ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Everton duk a cikin kunshin yarjejeniyar sayen Lukaku.

15 JULY

Garbine Muguruza ta lashe babbar gasar kwallon tennis a karo na biyu, bayan da ta doke Venus Williams da ci 7-5 6-0 a wasan a gasar Wimbledon Open.

17 JULY

Manchester United ta doke Real Madrid a bugun fanareti bayan sun tashi a wasan gabannin kakarsu da ci 1-1 a Santa Clara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Anthony Martial ne ya bai wa Jesse Lingard damar fara ci wa United kwallo daga gefen hagu.

Casemiro ya daukar wa Real Madrid fansa a bugun fenareti bayan sabon mai tsaron bayan United, Victor Lindelof, ya kayar da Theo Hernandez.

A bugun fanaretin da aka yi na raba gardama bayan an tashi wasan kunnen doki, an barar da fanareti 7 daga cikin 10 inda United ta doke Real Madrid da ci 2-1.

16 JULY

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan wasan tennis Roger Federer ya lashe kofin Wimbledon na bana bayan ya doke Marin Cilic.

Ya doke Cilic ne da ci 6-3 6-1 6-4, wanda rabon da ya lashe kofin tun a shekarar 2012.

Federer mai shekara 35 ya kafa tarihi na zama dan wasan tennis na farko a duniya da ya lashe kofin sau takwas.

Har ila yau, Federer wanda dan kasar Switzerland ne kuma shi ne dan wasa ma fi shekaru da ya lashe gasar Wimbledon tun bayan da aka sauya mata suna zuwa Open.

23 JULY

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Chris Froome ya ci gasar tseren keke ta Tour de France karo na hudu.

23 JULY

Jordan Spieth ya lashe gasar kwallon tennis da aka yi a Royal Birkdale, yana da shekara 23.

29 JULY

Aka soke damben Carl Frampton wanda ya so ya buga a karon farko bayan da ya rasa kambun WBA , bayan da abokin karawarsa Andres Gutierrez ya fadi a bandaki a Belfast inda ya ji rauni.

03 AGUSTA

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Paris St-Germain ta kammala daukar Neymar daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a matsayin dan kwallo mafi tsada a tarihi a duniya.

Cinikin dan wasan na tawagar Brazil mai shekara 25, ya haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a Agustan 2016 kan fam miliyan 89.

Neymar zai karbi albashin fam miliyan 40.7 a shekara, za a biya shi fam 782,000 a duk mako kafin a cire haraji, kan yarjejeniyar shekara biyar.

03 AUGUST

Tsohon zakaran damben boksin na duniya, Wladimir Klitschko ya sanar da yin ritaya, sannan ya karyata cewar ya bukaci ya sake dambatawa da Anthony Joshua.

6 AGUSTA

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Justin Gatlin ya burge duniya inda ya yi wa zakaran tseren duniya Usain Bolt fintinkau a gasar 100m, kuma ya lashe lambar zinare.

An bar Bolt da tagulla a ranar da ya yi tserensa na karshe kafin yayi ritaya, inda Ba’amurke Christian Coleman mai shekara 21 yayi na biyu.

11 AUGUST

Dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho ya nemi izinin barin Anfield, bayan da Barcelona ta ce tana son sayen dan Kwallon na Brazil.

27 AUGUST

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Floyd Mayweather ya lashe dambensa na 50, bayan da ya yi nasara a kan Conor McGregor a turmi na 10 a dambatawar da suka yi a Las Vegas.

31 AUGUST

Kylian Mbappe ya koma wasa Paris St Germain daga Monaco, tare da yarjejeniyar cewar PSG za ta iya sayen dan kwallon mai shekara 18 kan kudi Euro miliyan 180.

07 SEPTEMBER

Kungiyoyin Premier League suka amince a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon tamaula kwana daya kafin a fara kakar wasan 2018-19.

09 SEPTEMBER

Sloane Stephens ta lashe babbar gasar kwallon tennis a karon farko, inda ci gasar US Open, bayan da ta doke Madison Keys da ci 6-3 6-0.

9 SATUMBA

Hakkin mallakar hoto
LMCNPFL

Kungiyar Plateau United ta ci kofin Firimiyar Nigeria na bana, bayan da ta doke Enugu Rangers 2-0 a wasan mako na 38 a ranar Asabar.

Emeka Umeh ne ya fara ci wa Plateau kwallo tun kafin aje hutun rabin lokaci, kuma bayan da aka dawo ne Benjamin Turba ya kara na biyu.

Hakan ya sa Plateau United ta hada maki 66 a wasa 38 da ta yi a gasar bana da rarar kwallaye 24.

13 SEPTEMBER

Kwamitin wasannin Olympic ya bai wa birnin Paris da na Los Angeles izinin karbar bakuncin gasar da za a yi a 2024 da kuma wacce za a kara a 2028.

08 OKTOBA

Hakkin mallakar hoto
NFF

‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya suka samu tikitin zuwa wasan cin kofin duniya wanda za a yi a kasar Rasha 2018.

Nigeria ta yi nasarar cin Zambia 1-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.

23 OCTOBER

Kungiyar Everton ta kori Ronald Koeman, bayan da kungiyar ta kasa taka rawar gani a wasannin shekarar nan.

23 OKTOBA

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar dan kwallon kafa da babu kamarsa da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta karrama shi a 2017.

28 OKTOBA

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta yi nasarar lashe kofin matasa ‘yan kasa da shekara 17, bayan da ta casa Spaniya da ci 5-2.

Tun farko Spaniya ta ci kwallo biyu ta hannun dan wasan Barcelona Sergio Gomez, sai dak kafin hutu Ingila ta zare daya ta hannun Rhian Brewster kuma na takwas da ya ci a gasar.

Daga nan ne Ingila ta samu kwarin gwiwa ta farke ta hannun Morgan Gibbs Wwhite wasa ya koma 2-2.

Ingila ta kara cin kwallo biyu ta hannun Phil Fodaen, sannan Marc Guehi ya ci na biyar.

29 OKTOBA

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Lewis Hamilton ya lashe gasar tseren motoci ta Formula 1 ta Mexican Grand Prix duk da kammala wasan a mataki na tara, bayan da ya yi karo da motar Sebastian Vettel.

Hamilton shi ne dan wasan da babu kamarsa a Burtaniya a wasan tseren motoci, ya kuma yi kan-kan-kan da Sebastian Vettel da Alain Prost wajen lashe gasar sau hudu.

Juan Manuel Fangio yana da tarihin lashe gasar sau biyar, yayin da Michael Schumacher ya dauka sau bakwai.

02 NOVEMBER

Dan wasan Marseille, Patrice Evra ya yi wa wani magoyin bayan kungiyar kafa a lokacin da ‘yan wasa ke motsa jiki kafin karawa da Vitoria Guimaraes a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa.

04 NOVEMBER

Celtic ta karya tarihin da ta kafa shekara 100 da ta wuce, bayan da ta lashe wasa 63 ba tare da an doke ta ba, bayan da ta ci St Johnstone 4-0.

14 NUWAMBA

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafa ta Italiya, Gianluigi Buffon, yana zubar da hawaye ya nemi gafarar magoya bayan kasar, bayan da suka kasa samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Kyaftin din ya yi ritaya daga buga wa Italiya tamaula, bayan da kasar ta kasa yin nasara a kan Sweden a wasannin da suka buga gida da waje don neman tikitin shiga gasar ta duniya.

Italiya ta tashi wasa babu ci da Sweden a gida, bayan da a wasan farko ta sha kashi da 1-0, hakan ne ya sa a karo na farko tun 1958 ba za a ga kasar a gasar ba.

01 DECEMBER

Aka raba jadawalin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

7 DISAMBA

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ronaldo ya lashe Ballon d’or

11 DISAMBA

Dan wasan kasar Masar da kuma Liverpool, Mohamed Salah, ya ci kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta BBC ta shekarar 2017.

Bayan ya samu kuri’u masu tarin yawa, Muhamed Salah ya doke dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da dan kasar Guinea Naby Keita da dan Senegal Sadio Mane da kuma dan Najeriya, Victor Moses.

17 DECEMBER

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin hukumar FIFA na kungiyoyin kwallon kafa na duniya inda ta doke kungiyar Gremio da ke kasar Brazil.

An dai buga wasan ne a birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Asabar.

17 DISAMBA

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsohon dan wasan kungiyoyin AC Milan da Real Madrid, Kaka, ya yi ritaya daga taka leda.

Yana daya daga cikin ‘yan wasa takwas da suka lashe Kofin Zakarun Turai da Kofin Duniya da kuma kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d’Or.

Dan wasan ya yi fice ne a iya yanka da zura kwallo a raga kuma ya zura kwallaye 29 a raga a wasannni 92 da ya buga wa kasarsa Brazil.

Buhari ya nada matattu su shugabanci hukumomin gwamnatinsa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da sunayen mutanen da ta nada su shugabanci a wasu ma’aikatun gwamnati.

Amma abin mamaki sai kawai aka ga sunayen wasu matattun ‘yan Najeriya a cikin wadanda aka nadan.

Gwamnatin ta nada mutum 209 da mambobi fiye da 1,250 domin su jagoranci hukumomin.

Al’amarin ya zama baban abin mamaki ga ‘yan Najeriya, musamman a shafukan sada zumunta.

Amma Garba Shehu, wanda shi ne mataimaki na musamman mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ya kare gwamnati daga zargin rashin iya aiki.

Ya fada wa BBC cewa an shirya wannan jerin sunayen ne fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Ya kuma bayyana cewa, “Tun watan Oktobar shekarar 2016 aka rubuta sunayen. Amma sai aka ajiye shi domin sukar da wasu gwamnoni suka yi.”

Da alama babu wanda ya tantance jerin sunayen kafin aka wallafa shi ranar Jumma’a.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kakakin gwamnatin bai ga dalilin da za a dauki matakin ladabtarwa akan wadanda suka saki sunayen ba.

“Babu wani dalilin da za a dauki mataki akan wani jami’in gwamnati saboda wannan kuskuren,” inji shi.

A cikin sunayen akwai sunan sanata Francis Okpozo wanda ya mutu a watan Disambar 2016, amma sai ga sunansa a cikin nadaddun.

An nada shi ya shugabanci hukumar Nigeria Press Council.

Ban da shi akwai Donald Ugbaja, wani tsohon mataimakin sufeto-janar na ‘yan sandan Najeriya wanda ya mutu a farkon wannan shekarar, wanda aka nada shi domin ya shugabanci hukumar Consumer Protection Council.

Akwai kuma marigayi Rabran Christopher Utov, wanda sunansa ya fito a jerin sunayen mambobin hukumar Nigeria Institute of Social and Economic Research.

Garba Shehu ya ce za a sauya sunayen matattun mutanen da na wasu ‘yan kasar da suka cancanta.

Abin da na fada wa Buhari – Abdulmumini Jibrin


Hakkin mallakar hoto
A. Jibrin

Image caption

Dan majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin tare da shugaba Muhammadu Buhari a lokacin ganawarsu.

Wani dan majalisar wakilai da aka dakatar saboda badakalar cushe a kasafin kudin kasar na shekara ta 2016 ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Abdulmumini Jibrin shi ne dan majaisa mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta jihar Kano.

Jibrin ya gurfanar da shugabannin majalisar a gaban wata kotu bisa zargin dakatar da shi ba bisa ka’ida ba.

Ya shaida wa BBC cewa ganawar ta sa da Shugaba Buhari za ta zama sanadin warware matsalar da ta kai ga dakatar da shi daga majalisar.

Ya ce sun tattauna game da “Abubuwan da suka shafi harkokin siyasar kasa da kuma abubuwan da suka shafi dakatar da ni da mazabata a majalisa.”

Da aka tambaye abin da ya fada wa shugaba Buhari game da batun dakatar da shi da aka yi daga zaman majalisar wakilan, sai ya ce:

“Ka ga irin wannan zaman, daga ni sai shi, sai kuma Allah… Amma ina tabbatar maka da cewa zama ne aka yi mai kyau, kuma an sami kyakkyawar nasara kuma na fito cikin farin ciki”.

Majalisar wakilai ta ce ta dakatar da dan majalisar ne saboda ya fallasa lamarin cushen kasafin kudin Najeriya.

Batun cushe a kasafin kudin ya tayar da kura, ko da yake shugabannin majalisar karkashin jagorancin Yakubu Dogara sun sha musun aikata ba daidai ba.

Amma dan majalisa Jibrin ya dage da cewa dakatawar da aka yi masa ba bisa ka’ida take ba.

“Yau wata 16 muna kotu, duk da muna ganin girman kotu, amma abin in ka kalle shi ta wata fuska abin mamaki ne.”

Ya kara da cewa “Karar da muka shigar a kotu abu ne da ba ya daukar lokaci fiye da wata uku kotun ta yanke hukunci. To amma kararmu ta yi wajen wata 15 a kotu.”

Ya ce karar da ya shigar ta nemi kotu ta fayyace ko “Majalisar kasa tana da ikon ta dakatar da dan majalisa?”

Ya kuma nuna rashin gamsuwarsa da yadda majalisar wakilan ta dakatar da shi har na tsawon kwana 180 a karon farko.

“Kwana 180 din sun zo sun wuce, amma an ki a mayar da ni gidan. An ce kuma sai na bada hakuri.”

Da aka nemi ko ya bayar da hakurin, sai ya ce:

“Ba abin da gwamnatin Kano ba ta yi ba da Dogara, kuma ta bada hakuri. Sarkin Kano ya sa baki. Majalisar jihar Kano a dunkule sun bada hakuri.”

Ya tuhumi shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da kin mayar da shi bayan da ya bukaci dukkan ‘yan majalisar jihar ta Kano da shi kansa Abdulmumini Jibrin su rubuta takardar bada hakuri.

Ya ce sun cika dukkan sharuddan da Yakubu Dogaran ya nemi a cika domin warware matsalar, amma har yanzu bata sauya zani ba.

“Kaga wannan sai ya nuna cewa ba hakuri yake nema ba, akwai wani abin da ake nema.”

BBC ta yi kokarin jin ta bakin shugabancin majalisar wakilan Najeriya kan wannan batu, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.

Wakokin Hausa da suka fi shahara a shekarar 2017


Hakkin mallakar hoto
Ibrahim Sheme Facebook

Image caption

Ibrahim Sheme mutum ne mai sha’awar fina-finai da wakokin Hausa na da da na yanzu

Daga IBRAHIM SHEME

Allah mai zamani; a bana ma ba a samu wasu wakokin gargajiya na Hausa da su ka yi fice kamar na zamani da ake bugawa da fiyano ba.

Masu son Mamman Shata da Musa Dankwairo da sauran mawakanmu na gargajiya sun ci gaba da sauraren mawakan saboda sabo da kuma rike al’ada, to amma wakokin da aka fi saye ko aka fi saurare a kafafen yada bayanai da su ka hada da rediyo, talbijin da soshiyal midiya su ne wakokin da matasa ke yi da kayan kida na zamani.

Bayan tsananta bincike, mun zakulo wakokin Hausa guda 10 da jama’a su ka fi saurare a wannan shekarar ta 2010, daga cikin dimbin wakoki na mawaka daban-daban.

Wakokin sun shafi jigon soyayya ne da kuma siyasa da biki.

1. UMAR M. SHARIFF (tare da Murja Baba) – “Jirgin So” (daga fim din ‘Mansoor’)

Wakar “Jirgin So” fito ne a fim din ‘Mansoor’ na Ali Nuhu. Fitaccen mawaki Umar M. Shariff ne ya rera ta, tare da fitacciyar zabiya Murja Baba.

Haka kuma ‘Mansoor’ shi ne fim na farko da Umar ya fito a ciki a matsayin dan wasa. Hasali ma dai shi ne jarumin fim din, inda ya fito tare da sabuwar ‘yar wasa Maryam Yahya a matsayin jarumar shirin.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Jirgin So ta fim din Mansoor

Wakar ‘Mansoor’ ta yadu ne a dalilin ficen Ali Nuhu a industiri din fina-finan Hausa, da kuma kasancewar Umar M. Shariff daya daga cikin mawakan da su ka fi yin tashe a wannan lokaci.

“Jirgin So” wakar soyayya ce tsakanin saurayi da budurwa. A cikinta, gwanayen mawakan (Umar M. Shariff da Murja Baba) sun nuna kwarewa wajen karya murya da kuma zuba kalmomi na shauki.

An yi ittafaki da cewa babu wata wakar soyayya da ta yi fice kamar ta a bana. An yada ta sosai a kafofin sada zumunta na zamani a yunkurin tallata fim din. Hakan ya sa lokacin da fim din ya fito, matasa sun yi caa zuwa gidajen sinima domin su kalli yadda aka yi rawar wakar.

2. SADIQ ZAZZABI (tare da Maryam Fantimoti) – “Maza Bayan Ka”

Jigon wakar “Maza Bayan Ka” ta Sadiq Zazzabi dai shi ne zambo, ba kambawa ba kamar yadda wasu ke zato.

Duk da yake mawakin bai ambaci wanda ya ke yi wa zambon ba, masu lura da siyasar jihar Kano sun san takaddamar da ake yi tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da masu adawa da shi, musamman a jihar inda ya yi gwamna kafin zuwan sa Majalisar Tarayya.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Maza Bayanka ta Sadiq Zazzabi

Wakar na kunshe ne da kalamai na muzanta babban abokin adawar Kwankwaso.

Wani al’amari da ya sa wakar ta kara yin fice shi ne kama Sadiq Zazzabi tare da gurfanar da shi a gaban kotu da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi a bisa zargin ya saki wakar kafin hukumar ta ba shi takardar izinin fitar da ita.

3. ABDUL D. ONE (tare da Khairat Abdullah) – “Abin Da Ke Cikin Rai Na” (daga fim ]in ‘Mansoor’)

Wannan wakar ita ce ‘yar’uwar wakar “Jirgin So” ta Umar M. Shariff; dukkan su sun fito a fim din ‘Mansoor’ na Ali Nuhu.

Wakar soyayya ce. Abdul D. One, daya daga cikin yaran Umar M. Shariff, shi ne ya rera ta tare da mawakiya Khairat Abdullah. Wannan waka dai ta fito daga Kaduna, akasin yawancin wakokin zamani da ke fitowa daga Kano.

Abin da ya kara daga wakar shi ne kasancewar ta cikin fim din Ali Nuhu mai suna ‘Mansoor’ wanda ya na daga cikin manyan finafinan shekarar 2017.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Abin da ke raina na fim din Mansoor

Wannan fim ya sha talla a shafukan sada zumunta, da yake Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Kannywood, shi ne ya shirya fim din kuma ya ba da umarni, sannan jarumin shirin, wato Umar M. Shariff, mawaki ne mai dimbin masoya, wadanda ke so su ga yadda ya yi a fim din.

Masoyan Ali da na jaruman fim din sun taimaka wajen tallata wakar a Instagram ta hanyar yada bidiyon ta da kuma shirya nasu bidiyon na rawar wakar.

4. DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA) – “Buhari Ya Dawo”

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa lakabi da Rarara, ya fitar da wannan wakar ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga London, inda ya shafe watanni yana jinya.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Sannu da sauka Baba Buhari ta Rarara

Sanin kowa ne an yi ta shaci-fadi kan rashin lafiyar, saboda haka ‘yan Nijeriya da dama sun zaku su ga dawowar sa.

Don haka sakin wakar a daidai lokacin na da wuya sai ta karbu a wajen masu saurare.

Rarara ya yi waar ne a matsayin martani ga masu adawa da Buhari, musamman masu cewa rashin lafiyar zai hana shi ci gaba da mulki. Da ma can Rarara magoyin bayan Shugaba Buhari ne.

5. UMAR M. SHARIFF (tare da Khairat Abdullah) – “Rariya” (daga fim din ‘Rariya’)

Umar M. Shariff ya ci gaba da rike kambin sa na kasancewa daya daga cikin manyan mawakan wannan zamanin da wakar “Rariya” wadda ta fito a cikin fim din ‘Rariya’. Shi da Khairat Abdullah suka rera wakar.

Jigon wakar shi ne soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cewar saurayin, ya yi tankade da rairaya na soyayya da rariya ne, a karshe ya yi dacen samun budurwar tasa a matsayin “tsabar” da wannan tankaden ya samar.

Ya ce: “Tankade na yo na sa rariya, Ke ce ki ka zam tsaba, Zabi na a soyayya.” Ita ma ta mayar masa da wadannan kalmomin, tare da nuna masa cewa za ta yi masa sakayya da ba shi zuciyar ta.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Rariya ta fim din Rariya

Kalmomin soyayya da ake furtawa a wa}ar sun taba zukatan matasa matuka.

To amma ficen wakar ya samo asali ne daga kansancewar ta wakar da ta jagoranci fim din Rahama Sadau, fitacciyar jarumar da sunan ta ya kara yaduwa saboda korar ta daga Kannywood da kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta yi a shekarar da ta gabata.

Da yake ‘Rariya’ shi ne babban fim din da Rahama ta shirya a bana, masoyan jarumar sun yi mata kara wajen tallata wakar a shafukan su na Instagram.

Kwatankwacin dai yadda su ka yi wa wakokin fim din ‘Mansoor’ na Ali Nuhu, sun rika shirya bidiyo na rawar waka nasu na kan su, su na turawa.

Babu mamaki, lokacin da za a nuna fim din a gidajen sinima, matasa sun rika yin tururuwa zuwa wajen kallo, don su ga yadda aka yi rawar wakar.

6. ADO ISA GWANJA – “Ayyaraye Indosa, A Sha Ruwa”

An fi sanin Ado Isa Gwanja ne da wakar “Kujerar Tsakar Gida” wadda ta kasance waka mafi karbuwa ga matan biki a fadin arewacin Najeriya tun bayan da ya rera ta shekara biyu kenan.

Ba a daina jin “Kujerar Tsakar Gida” ba, sai kuma Gwanja ya so ya rike kambinsa na jagaba a wakokin gidan biki da wakar “Mata Mu kame kam”.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Indosa ta Ado Gwanja

To amma wakar da ta fi jan hankali a bana ita ce wakarsa mai taken “Indosa”.

Akasin sauran, ita ba wakar rawar cashewa ko girgiza jiki ba ce; waka ce ta saurare wadda kuma za a iya rausayawa.

A cikin ta, Gwanja na yabon kan sa ne saboda ficen da ya yi a matsayin mawakin gidan biki. Ya yi nuni da cewa yanzu ya zama gamji a cikin mawaka, wato ya gagara a sare shi.

Ya ce duk da yake wasu na cewa mata ya ke yi wa waka, to ya tabbatar in har ya doka wakar sa, har mazan ma sai sun taka.

7. NURA M. INUWA – “Ranar Aure Na”

Nura M. Inuwa ya rera wakar “Ranar Aure Na” ne sakamakon auren da ya yi a wannan shekarar a Jihar Katsina.

A wakar, ya yi godiya ga Allah da ya nuna masa ranar aurensa da kuma jama’ar da su ka je bikin auren, tare da bayyana farin ciki da wannan al’amari.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Ranar Aurena ta Nura M Inuwa

Haka kuma ya tabo masu adawa da shi a kan wannan aure, ya nuna cewa Allah ya yi ko da su ba su so. Ita ma amaryar, ya yi addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya.

Da yake Nura mawaki ne mai dimbin masoya saboda wakokinsa na soyayya, kuma an jima ana jiran ranar aurensa, wakar ta karbu sosai, musamman wajen matasa.

8. ASMA’U SADIQ – “Dolin-Dolin”

Asma’u Sadiq ta zama kallabi a tsakanin rawunna da wakarta ta “Dolin-Dolin”. Waka ce ta gada. Jigon wakar shi ne soyayyar samari da ‘yanmata, musamman a gargajiyance.

Wakar ta yi fice musamman saboda yawan saka ta da ake yi gidajen rediyo na FM a garuruwan Arewa.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Dolin-dolin ta Asma’u Sadeeq

Duk da yake an kira ta “Dolin-Dolin”, wannan waka ba amshi daya ba ne ta ke da shi; hade-hade ce ta wasu wakokin gada guda biyar, wato “Dolin-Dolin”, “Soriyalle Maigida Na”, “Kacalle-Kacalle Mu Yi Gada”, “Mai Zamani ‘Yanmata”, da “Warai-Warai”.

A karshen wakar, zabiyar ta kawo wani baiti da ya yi kama da na wakokin hip-hop.

9. MORELL – “Aure”

Wakar “Aure” ta Morell ce kan gaba a bana cikin rukunin wakokin hip-hop. Duk da yake tun bara ya saki wakar, amma dai ba a samu wadda ta doke ta a fagen ba.

Wakar ta rike matsayin ta ne bayan fitar bidiyo ]in ta da ya faru a cikin wannan shekara ta 2017, wanda Moe Musa ya ba da umarni. Akwai Ali Nuhu a bidiyon.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Aure ta Morell

Sunan Morell na asali dai shi ne Musa Jikan Musa, kuma ya yi wasu wakokin wadanda su ka hada da “Karota”, “Borno”, “Safay”, “Ganga Da Garaya” da kuma “Ba Wani Bugatti”.

Wakokin hip-hop na Hausa da su ka kara da wannan wakar sun hada da wadda marigayi Lil Ameer ya yi mai taken “Dance for Me – Ni Ameer Na Kowa Ne” da wakar “Arab Money” ta Nomiis Gee.

10. NAZIRU M. AHMAD – “Rawa, Rawa”

Naziru M. Ahmad ya yi fice wajen wa}o}in sarakuna da kidan gargajiya, musamman wajen yin amfani da tambura da tallaye da ganguna da algaitai.

Amma ya kan yi wakoki na soyayya ko na aure, da sauran su.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakar Rawa-Rawa ta Naziru M Ahmad

A bana, hazikin wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka, ya rike mukamin sa ta hanyar sakin wakar “Rawa, Rawa”.

Wakar biki ce wadda ya yi hikimar kawo ta da salon gargajiya, ana buga ganguna, sannan ga ‘yan amshi su ma su na sako kalmomi kwakwankwacin yadda su Musa Dankwairo ke yi.

Adikon Zamani: Me yake sa wasu mazan yawan auri-saki?


Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron shirin tare da Fatima Zahra Umar:

Yayin da wani lokaci zawarawa suka koma abin wasa da dariya, maza kuma da ke ‘auri saki’ ke yadda suka ga dama ba abin da ya shafe su.

Kusan dai saki ya zama ruwan dare ga maza a arewacin Najeriya, musamman yadda namiji zai yi aure kuma ya saki cikin lokaci kankani.

Irin wadannan mazajen yana da wahala su iya rayuwar aure da mace fiye da shekara daya.

Wasunsu kan saki matarsu bayan haihuwa daya. Suna auren mata su watsar da su yadda suka ga dama.

Ko me ya sa babu wani hukunci a kan irin wadannan mazajen da ke bata rayuwar mata?

Shirin Adikon Zamani na wannan makon ya ci karo da wani magidanci da ya auri mata 13 yana saki, kuma yanzu yake rayuwa da ta 14.

Ya ce bai taba fuskantar kalubale ba wajen neman aure.

Na yi mamakin yadda bai taba fuskantar tirjiya ba daga iyayen matan duk da sun san ya yi kaurin suna a wajen auri-saki.

Wai me ya sa muke barin ‘ya’yanmu suna auren irin wadannan mazajen da ke lalata rayuwar mata?

Kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta na BBC Hausa Facebook da BBC Hausa Twitter.

MDD ta taya sabon shugaban Liberia Murna


Image caption

Tun a shekarar 2005 ne Mista Weah ya fara tsayawa takarar shugaban kasar Liberia

Babban magatakardar MDD ya mika sakon taya murna ga sabon shugaban Liberia kuma tsohon fitaccen dan wasan kwallo George Weah kan nasarar da ya yi a zaben da aka gudanar a kasar.

Antonio Guterres ya kuma yabawa mataimakin shugaban kasa, kuma abokin takarar mista Weah wato Joseph Boakai da ya amince da shan kaye ba tare da wata hatsaniya ba.

Ya kara da cewa zaben da aka gudanar bisa gaskiya ta adalci ‘yar manuniya ce da ke nuna zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu zama a kasar.

Sai dai yace akwai kalubale da aiki Ja ga sabon shugaban na ciyar da Liberia gaba, dan haka ya ce hada kai tsakanin ‘yan kasar da ‘yan siyasa abu ne mai matukar muhimmanci dan ciyar da ita gaba.

Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.

Yakin neman zaben Mista Weah a karkashin hadakar jam’iyyun siyasa ta CDC – Coalition for Democratic Change – ya burge matasa sosai, amma abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Mista Boakai bai sami karbuwa sosai ba.

Kuma matar tsohon shugaba Charles Taylor, Jewel Taylor ce mataimakiyarsa, duk da cewa shi Charles Taylor din na tsare a wani gidan yari dake Burtaniya a sanadiyyar samunsa da laifukan yaki da aka yi a makwabciyar kasar Saliyo.

A watan Oktoba, Mista Weah ya lashe zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar, inda ya sami kashi 38.4 cikin dari, shi kuwa mai binsa a baya, Mista Boakai dan shekara 73 ya samu kashi 28.8 cikin dari.

Rashin samun wanda yayi nasara kai tsaye ne ya janyo aka gudanar da zaben a zagaye na biyu.

Hukumar zaben kasar ta Laberiya ta ce an kammala kidayar kashi 98.1 cikin dari na kuri’un da aka kada, kuma zuwa ranar yau Alhamis, Mista Weah ya lashe kashi 65.5 cikin dari na kuri’un.

Mista Boakai kuma na da kashi 38.5 cikin dari ne na dukkan kuri’un.

Chelsea ta samu kudin da ba ta taba samu ba a shekara kusan naira biliyan 2


Hakkin mallakar hoto
OTHERS

Image caption

Chelsea ta dauki kofin Premier a kakar da ta wuce, abin da ya ba ta damar dawowa gasar zakarun Turai

Mai rike da kofin Premier Chelsea, ta sanar da yin cinikin da ba ta taba yi ba na fam miliyan 361.3, kusan naira biliyan biyu a shekara nan ta 2017.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa ta ci ribar fam miliyan 15.3, wadda ta danganta da cinikin sayar da ‘yan wasa na fam miliyan 69.2.

A cikin wata ukun da ya wuce Manchester United ta samu kudin da ita ma ba ta taba samu ba fam miliyan 581, yayin da ita ma Manchester City ta sanar da nata cinikin na fam miliyan 473.4, amma ita City na tsawon wata 13 ne.

Shugaban Chelsea Bruce Buck ya ji dadi ganin cewa kungiyar ta yi nasara a wasanninta kamar yadda ta yi a fannin kasuwanci a shekarar.

Chelsea ta ce tana sa ran kudin da take samu ya karu a kakar da ake ciki ta 2017/18 saboda sun dawo gasar cin kofin zakarun Turai, tare kuma da sake kulla yarjejeniya da kamfanin yin kayan wasa na Nike.

Firaministan Mali Idrissa Maiga ya yi murabus


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Idrissa Maiga shi ne Firaminista na hudu a gwamnatin Keita

Firaministan Mali Idrissa Maiga ya yi murabus tare da gwamnatinsa, kamar yadda fadar gwamnatin kasar ta sanar.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Firaministan ya gabatar da takardar murabus din ne ga shugaba Ibrahim Boubakar Keita.

Kuma sanarwar ta ce Maiga ya yi murabus ne tare da gwamnatinsa.

A watan Afrilu ne aka nada Idrissa Maiga matsayin Firaminista.

Maiga shi ne Firaminista na hudu a gwamnatin Keita, bayan gwamnatin Omar Tatam Ly da Moussa Mara da Modibo Keita.

Murabus dinsa na zuwa ne a yayin da ya rage watanni bakwai a gudanar da zaben shugaban kasa wanda za a gudanar a watan Yulin 2018.

Maiga shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar RPM mai mulki a Mali, kuma ya taba zama daraktan yakin neman zaben Shugaba Keita a zaben 2013.

Sai dai kuma babu wani cikakken bayani a sanarwar da gwamnatin ta fitar game da dalilin murabus din Firaministan.

Tanzania za ta rufe coci-coci ma su sukar Magafuli


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

John Magufuliya musanta cewa yana mulkin kama-karya ne, duk da yadda yake dira kan masu sukar salon mulkinsa

Hukumoni a Tanzania sun yi gargadin cewa za su rufe dukkanin mujami’un kiristocin kasar da ke gauraya addini da siyasa, bayan da wani malamin addini ya soki shugaba John Magufuli a wani wa’azi na bikin kirsimeti.

Malamin addinin, Zachary Kakobe ya ce kasar na kan hanyar komawa wacce ake mulki a karkashin jam’iyya daya tilo.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce za a soke lasisin duk kungiyar addinin da ta yi sharhi na siyasa game da salon mulkin shugaban kasar.

Masu sukar gwamnatin kasar na cewa lamarinta ya fara wuce gona da iri, inda a baya ta rufe jaridu kuma ta hukunta mutane da dama kan abin da gwamnatin ta kira sun ci zarafin shugaban kasar a shafukan sada zumunta na intanet.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana kiran Magafuli “bulldozer” saboda salon mulkinsa

Tsarin mulkin Tanzaniya ya tabbatar wa kowa ‘yancin addini, duk da cewa ana bukatar kungiyoyin addinin su yi rajista a ma’aikatar cikin gida kafin su fara gudanar da ayyukansu.

Cairo: Dan bindiga ya kai wa Kiristoci Kibdawa hari a coci


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wani mutum na duba ramukan harbi a jikin cocin Mar Mina bayan harin da aka kai a gundumar Helwan na birnin Alka’ira.

Hukumomi a Masar sun ce mutum tara sun rasa rayukansu bayan da wani dan bindiga ya kai hari a wata coci da kuma wani shago mallakin mabiya kirista a Helwan da ke kudancin Alkahira babban birnin kasar.

Rahotannin farko na cewa jami’an tsaro sun kashe dan bindigan, amma ma’aikatar cikin gida ta ce yana hannu kuma rauni kawai ya samu.

Wannan harin ya zo ne dab da bukukuwan sabuwar shekara da kuma bikin kirsimetin kibdawa da za a yi ranar 7 ga watan Janairu.

A shekarar da ta gabata, an kashe fiye da kirista dari a hare-haren bam da na ‘yan bindiga a Masar, kuma reshen kungiyar IS a kasar ne suka dauki alhakin kai hare-haren.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Jami’an tsaro na sintiri a sassan babban birnin Alkahiira

Mutumin da ya ba ‘yan Rohingya mafaka a gidansa


Mofiz Uddin ya ba musulmi ‘yan Rohingya 130 da ke gudun hijira mafaka a gidansa, bayan da sojin Myanmar suka raba su da muhallansu.

“Sun zo nan da rauni a sanadin harbin da sojojin Myanmar suka yi musu da kuma sauran raunuka.”

Ya ce halin da ya same su a lokacin da suka isa Bangladesh ya sosa masa zuciya, har sai da ya yi kuka.

Ya ce: “Musulmi ne su, kuma mu ma musulmi ne.”

Mofiz Uddin dan kasar Bangladesh ne, kuma a sanadiyyar wahalar da ‘yan Rohingyar suke ciki ne ya ba 130 daga cikinsu muhallinsa.

Ya ba su mafaka a gidansa na tsawon wata hudu kawo yanzu, inda ya ce, “Ba su da komai a lokacin da suka iso nan.”

Su ne suka nemi ya ba su wani fili da ke kusa da gidansa, kuma ya yarda nan take.

Shahila Katun na cikin wadanda suka amfana da wannan karamcin na Mofiz Uddin.

Ta ce: “Sojojin Myanmar din sun rika harbi da yankan mutanenmu. Ya zama wajibi mu bar muhallanmu da kauyukanmu domin mu ceci rayukanmu.”

Ba ‘yan kabilar ta Rohingya mafaka da Mofiz ya ke yi laifi ne, domin gwamnatin Bangladesh ta haramta yin haka.

Amma ‘yan Bangladesh da dama na ganin cewa taimaka wa ‘yan gudun hijirar ya zama wajibi.

A sanadiyyar taimakon da suke ba su, wasu daga ‘yan Bangladesh din na fuskantar matsaloli.

“A da ina noma kayan gwari a filin, amma na daina domin ‘yan gudun hijirar sun gina muhallai na kwali a kai,” in ji Mofiz.

Allah ne kadai ya san ranar da za mu bar wannan wurin, yana iya kai wa shekara daya, ko biyu ko biyar,” in ji Hasina Begum wacce ta sami matsuguni a filin da Mofiz Uddin ya ba su ita da ‘ya’yanta.

Ta ce ba za su iya komawa gida ba har sai gwamnatin Myanmar ta ba tabbatar musu da cewa su ma cikakkun ‘yan kasar Myanmar ne kuma an basu kariya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hare-haren da aka rinka kai wa musulmi ‘yan Rohingya a matsayin “laifin kare dangi”.

Fiye da ‘yan Rohingya 650,000 sun tsere daga Myanmar zuwa Bangladesh bayan da sojojin Myanmar din suka rika kai musu hare-hare.

Ana zanga-zangar adawa da gwamnati a biranen Iran


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zanga-zangar ita ce mafi girma tun wacce aka taba gudanarwa a 2009

Zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran da aka soma a jiya yanzu ta bazu a manyan biranen kasar.

Mutane da dama ne aka ruwaito sun shiga zanga-zangar a Rasht a arewaci da Kermanshar a yammaci da kuma yankunan Shiraz da Isfahan da Hamadan na kasar.

Da farko an fara zanga-zangar ne domin adawa da tsadar rayuwa, yanzu kuma ta rikide ta koma ta adawa da gwamnati.

Rahotanni sun ce an cafke wasu daga cikin masu zanga-zangar a Tehran babban birnin kasar.

Kamfanin dillacin labaran Iran ya ruwaito mataimakin gwamnan Tehran na cewa gungun mutane 50 ne suka hada gangamin, a wani babban dandalin tsakiyar birnin.

Tun da farko mataimakin gwamnan ya ce ‘yan sanda za su tarwatsa gungun masu zanga-zangar.

Masu aiko da rahotanni sun ce zanga-zangar ta adawa da gwamnati ita ce mafi girma tun wacce aka taba gudanarwa a 2009 bayan babban zaben kasar mai cike da kalubale.

An ji masu zanga-zangar na cewa “Mutane na bara”.

A birnin Mashhad da ke arewa maso gabashi ne aka gudanar da babbar zanga-zanga, inda aka cafke mutane 52.

An kira zanga-zangar ne ta kafofin sadarwa na intanet, duk da gwamnati ta yi kashedin shirya duk wani gangamin da ya sabawa doka.

Wasu hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sadarwa na intanet sun nuna yadda masu zanga-zangar ke arangama da masu zanga-zanga.

Masu zanga-zangar na adawa ne da gazawar gwamnatin shugaba Hassan Rouhani kan magance matsalar hauhawan farashin kayayyakin masarufi.

Zanga-zangar ta rikide ta koma ta adawa da gwamnati tare da yin kiran a saki fursunonin siyasa da kawo karshen cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa jama’a.

Masharhanta a gabas ta tsakiya sun ce zanga-zangar ta zo wa gwamnatin Iran ba-zata, wacce ba a saba gani ba.

Wani sakamakon binciken BBC game da Iran ya nuna cewa kashi kusan 30 na ‘yan kasar na shiga hali na talauci a shekaru 10 da suka gabata.

Wasu na ganin kudaden ya kamata a ce an kashe domin inganta rayuwarsu, amma an koma ana hidimar yaki da kudaden a Syria da Yemen da Iraqi.

Sannan ana kashe makudan biliyoyi domin watsa farfagandar shi’a a sassan duniya

Shugaba Hassan Rouhani ya yi alkawalin cewa yarjejeniyar nukiliya da ya sanya wa hannu tsakanin Iran da manyan kasashen duniya za ta taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar idan har an cire ma ta takunkumai.

Tattalin arzikin kasar dai yanzu ya fara bunkasa kamar yadda aka samu sassauci a hauhawan farashin kayayyaki amma har yanzu kasar na fama da karancin masu saka jari yayin da alkalumman rashin aikin ya kai kashi 12.4.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban Iran Hassan Rouhani na ci gaba da fuskantar kalubalen matsalolin tattalin arziki

Lukaku na bukatar hutu amma ba zai samu ba- Mourinho


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lukaku tun zuwansa Manchester United ya buga wasannin Premier ba tare hutu ba

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ba zai iya ba Romelu Lukaku hutu ba duk da ya fahimci cewa dan wasan ya nuna “ya gaji”.

Lukaku tun zuwansa ya buga wasannin Premier ba tare hutu ba, saboda jinyar raunin da Zlatan Ibrahimovic ya yi.

Dan wasan wanda ya koma United a bana kan kudi fam miliyan 75 daga Everton ya ci ma ta kwallo 11 a wasa 10 da ya yi, amma yanzu kwallaye hudu ya ci a wasanni 19.

“Yaron ya gaji amma yana da kyau har yanzu, ba zan iya ajiye shi ba” a cewar Mourinho.

A makwannin da suka gabata Lukaku ya tafka kurakurai da suka haddasa kwallayen da Manchester City da Burnley suka doke Manchester United.

Dan wasan ya dade yana fuskantar kalubale amma ba tare da Mourinho ya soke shi ba.

Tazarar maki 15 Manchester City ta ba Manchester United a teburin Premier, kuma a ranar Asabar 30 ga watan Disemba United za ta karbi bakuncin Southampton a Old Trafford.

‘Yan Isra’ila sun yi addu’ar rokon ruwa saboda gudun fari


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ministan ya ce addu’a za ta taimaka wajen kawo karshen matsalar.

Ministan noman Isra’ila Uri Ariel ya jagoranci addu’ar rokon ruwa tare da shugabannin addinin kasar a wani mataki na amfani da girman addu’a domin kawo karshen matsalar fari.

Mista Ariel, ya jagoranci addu’o’in ne a bangon Yammacin Kudus da Yahudawa ke ibada.

Isra’ila na fuskantar matsalar karancin ruwa sakamakon tsananin fari a tsawon shekara hudu.

Wasu ‘yan kasar na ganin, kamata ya yi ministan ya dauki matakan yaki da matsalar a aikace.

Girman matsalar fari a Isra’ila dai ta yi tasiri matuka ga manoma.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mabiya addinin yahudanci sun yi taron rokon ruwa a Isra’ila

Ministan ya ce duk da sun dauki matakai amma addu’a ma za ta taimaka wajen kawo karshen matsalar.

Wata jaridar kasar Yedioth Ahronoth ta rubuta cewa, “Addu’a na da kyau, amma ya kamata a ce ministan ya dauki matakai da suka shafi rage matsalar sauyin yanayi.

Gobara ta hallaka mutane 12 a Amirka


Image caption

Jami’an kashe gobara sun shawo kan wutar

Mutane 12 ne suka mutu a lokacin da wata gobara ta tashi a gundumar Bronx da ke birnin New York din Amurka.

Magajin birnin Bill De Blasio ya ce an samu shawo kan gobarar, ya kuma ce wasu mutane 4 na kwance a asibiti saboda kunewar da suka yi.

Mista De Blasio ya ce wannan ce gobara mafi muni da birnin ya fuskanta cikin shekara 25.

Wani mutumin ya ga abin da ya faru, ya ce wutar ta na ci balbal ya yin da mutanen da ke cikin gidajen da ta shafa su ke gudun ceton rai.

Mutane sun yi ta fitowa daga gidajensu, wasu babu ko sutura wasu kuma sanye da kayan bacci.

A bangare guda kuma jami’an kashe gobara sun dukufa dan shawo kan ta, ya yin da aka garzaya da wadanda suka kone asibiti.

Hukumomi sun ce ya yi wuri a gano musabbabin tashin gobarar, amma su na gudanar da bincike.

Kamfanin Apple ya nemi afuwar abokan huldarsa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wayar salula samfurin iPhone na da farin jini musamman tsakanin matasa

Kamfanin Apple da ya yi fice wajen samar da wayoyin zamani na komai da ruwanka, ya nemi afuwar abokan huldarsa kan gwangen da ya yi kan wayar iPhone rage saurin wasu tsofaffin wayoyin da gangan.

Masu hulda da kamfanin sun dade suna zargin kamfanin Apple na ragewa tsofaffin wayoyin hannu sauri, musamman idan ya na gab da fitar da sabuwar wayar iPhone, domin a tilastawa musu amfanin wayar sayen sabuwar fitowa.

Kamfanin ya ce ya na shirin kara inganta wayoyin salular, da sanya matakan kare ta daga lalacewa baki daya.

Apple ya yi alkawarin zai rage farashin batirin wayar sanfurin iPhone 6 da wasu sabbin wayoyin idan ya fitar da su.

Haka kuma ya ce zai samar da wata Saftiwaya da za ta bai wa maso amfani da wayar damar samun bayanan sirri da suka shafi ingancin wayar.

A tsakiyar watan nan ne, Kamfanin Apple ya tabbatar wa masu wayoyin iPhone cewa yana rage saurin wasu tsofaffin wayoyin na iPhone da gangan.

Masu hulda da kamfanin sun dade suna tuhumar kamfanin Apple din da rage wa tsofaffin wayoyin hannu na iPhone sauri domin a tilasta musu sayen sababbin wayoyin da suka fito.

Kamfanin ya fito fili ya bayyana cewa lallai yana rage wa wasu wayoyin sauri domin karfin batirin wayoyin na raguwa bayan wasu shekaru.

Apple ya ce yana yin haka ne domin ya “tsawaita ran” na’urorin da yake kerawa.

Lamarin ya fara bayyana ne a lokacin da wani mai amfani da wayar Iphone ya wallafa rahoton wani gwaji da ya yi a shafin intanet na Reddit, a inda ya nuna cewa wayarsa samfurin iPhone 6S ta rage sauri matuka amma ta fara saurin sosai bayan da ya sauya tsohon batirin da sabo.

“Na yi amfani da wayar dan uwana samfurin iPhone 6 Plus, kuma na lura wayar tasa ta fi tawa sauri.

“A lokacin ne na tabbatar cewa akwai lauje cikin nadi,” inji mawallafin rahoton mai suna TeckFire.

Daga nan ne shafin fasahar yanar gizo, Geekbench ya binciki samfurin wayoyin iPhone masu amfani da manhajar iOS daban-daban, inda ya gano cewa lallai kuwa ana rage musu sauri da gangan.

Abubuwan mamaki takwas na kimiyya da suka faru a 2017


Shekara ce mai cike da abubuwa da suka faru a karon farko da kuma wasu abubuwa da suka kawo karshensu: kumbon samaniya na Kasini ya kammala aikinsa na shekara 13, yayin da wasu matattun taurari suka yi taho-mu-gama a sararin samaniya saboda yanayin kurar karfen taurarin.

BBC ta yi nazari kan takwas daga cikin labaran kimiyyar yanayi da suka fi ko wanne yin fice a shekarar 2017.

Hatsarin taurari

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Taswirar da wani mai zane ya yi game da yadda yake ganin taho-mu-gamar taurari biyun

A shekarar 2017, masana kimiyya sun gano motsin maganadisun kasa da Einstein ya yi hasashe daga wani wuri na daban – karon taurari biyu.

An sanar da gano wannan motsin na karon farko ne a shekarar 2016, a lokacin da dakin bincike na Advanced LIGO ya bayyana yamutsa sararin samaniya sanadiyyar hadewar bakaken ramuka biyu da ke da nisa da juna. An jinjina wa sakamakon a matsayin wani sabon reshe na ilimin taurari, amfani da motsin maganadisu domin tattara alkaluma game da abubuwan da ke faruwa daga nesa.

Na’urorin hangen nesa daga fadin duniya sun nada yadda taurarin biyu suka hade. Fashewar ta faru ne a wani wuri mai nisan kimanin kilomita dubu biliyan daya. Wasu daga cikin bayanai game da wannan gagagrumin abin suna da ban-mamaki. Alal misali, taurarin neutron suna da kauri ta yadda cikin cokali zai kai nauyin tan biliyan daya. Masanan sun tabbatar da cewa irin wannan karon ne ya samar da zinari da karfen platinum da ake da su a fadin duniya.

Kumbon Cassini ya karasa aikinsa

Hakkin mallakar hoto
NASA/JPL-CALTECH

Image caption

Tasiwra: Kumbon Cassini ya tafiya a wani tsukekken gibi tsakanin saman duniyar Saturn da kuma zobenta

Kumbon Cassini ya kai duniyar Saturn ne a shekarar 2004. A cikin shekaru 13 da kumbon ya yi aiki, ya sauya fahimtarmu game da duniyar mai zobe da watanninta. Ya gano mabubbugin ruwa mai fesa ruwan kankara da turiri zuwa sararin samaniya daga watan Enceladus mai kankara a lokacin da kumbon ke aiki.

Amma domin mai na karewa daga tankin man, sai hukumar binciken sararin samaniya ta NASA ta lalata kumbon a saman duniyar Saturn maimakon kumbon ya ci karo da wani abin da ake saka wa ido a binciken rayuwa, kaman watan Enceladus, ya kuma gurbata shi da kwayoyin halitta na sararin samaniya. Ranar 15 ga watan Satumba, Cassini ya shiga sararin samaniyar babbar duniyar kuma aka barke shi. Kuma ya iya mayar da bayanai duniyar mutane a daidai lokacin da yake fsukantar halaka.

Janyewa daga yarjejeniyarParis

Hakkin mallakar hoto
EPA

A lokacin da yake yakin neman zabe, Donald Trump ya ce zai soke yarjejeniyar Paris kan yanayi, kuma zai cire Amurka daga yarjejeniyar. Amman bayan ya lashe zaben Amurkaa watan Nuwamban wanna shekarar, yayi kalamai kadan a bainar jama’a kan lamarin sauyin yanayi. Rahotanni sun fito cewa kawunan masu bai wa Mista Trump shawara kan lamarin ya rabu, abin da ya sa wasu masu sharhi suka yi taunain cewa tayiwu shugaban ya gamsu da cigaba da yarjejeniyar.

Duk da haka, ranar daya ga watan Yuni, Shugaba Trump ya yi wani taron manema labarai a lambun Rose da ke fadar White House inda ya sanar da janyewar Amurka. Mista Trump ya ce : “Domin in cika alkawarin da na dauka na kare Amurka da ‘ya’yanta, Amurka za ta janye daga yarjejeniyar yanayi ta Paris … amma ta fara tattaunawa domin sake shiga yarjejeniyar Paris din ko kuma wata sabuwar yarjejeniyar ta daban kan sharrudan da za su dace da muradun Amurka.”

Kamar yadda ak yi tsammani, ‘yan jam’iyyar Demokrat da kuma shuagabannin duniya sun mayar da martani da yin Allah-Wadai da matakin shugaba Trump. Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama ya zargi gwamanatin Trump da yin watsi da makomar mutane masu zuwa, yayin da tsohon sakataren harkokin waje John Kerry ya bayyana matakin a matsayin tsagoran watsi da aikin shugabanci

Duniyoyi “masu yawa”

Hakkin mallakar hoto
Nature

Image caption

Taswira: wanan shi adadi mafi yawa na duniyoyi masu kama da duniyar mutane da suka kewaye tauraro daya

Daga cikin duniyoyi 3,500 da aka tabbatar da kasancewarsu nesa daga duniyar mutane da rana da wata, wasu na da matukar ba da mamaki. Ga wadanad ba su sani baakwai duniyar J1407b wadda take da zobe da ya fi zoben duniyar Saturn girma sau 200.

Amma a wannans shekarar, masu ilimin taurari sun gano wasu jerin taurari da ke da duniya bakwai da suka ka kai duniyarmu. Bugu da kari wadannan duniyoyin da alamar sun bin wani tsari ne yayin da suke kewaye tauraronsu. Kuma uku daga cikin duniyoyin suna wuararen da rayuwa zata iya kasancewa ne inda za a iya samun ruwa a sama. Kuma duk ida aakwai ruwa, akwi yiwuwar rayuwa.

Dangin kwanan nan

Hakkin mallakar hoto
Philipp Gunz/MPI EVA Leipzig

Image caption

Kwarangwal na mutanen yanzu da aka sake zanawa bisa hotunan kasusuwa da aka dauka

A watan Yuli, amsu bincike sun fitar da kasusuwa wasu mutanen farko da aka samu a arewacin Afirka wadanda suka nuna cewa mutanen yanzu – Homo sapiens -suka bayyana, akalla shekara 100,000 fiye da yadda ake hasashe da. Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen yanzu ba su fito daga zuri’a daya daga gabashin Afirka ba. Maimakon haka ta yiwu halittan mutanen yanzu ta dade tana juyawa a fadin nahiyar

Kuma akwai karin manyan labarai game da juyin halitta dan Adam a wannan shekarar. A lokacin da masana kimiyya suka fitar da wasu bangarori na kasusuwan mutane 15 na wata sabuwar halittar mutane, labarin ya yi suna a fadin duniya. A wanna lokacin masu bincike ba su iya tabbatar da iya shekarun mutanen da ake cewa Homo naledi ba, amma wasu halayyar da ba su gama cigaba ba, sun nuna cewa za us iya kai shekaru miliyan uku a duniya.

A wannan shekarar, shugaban masu binciken Lee Berger, ya fitar da sanarwar cewa kasusuwan shekaraunsu tsakanin 200,000 zuwa 300,000 ne. Sakamakon binciken ya nuna cewa, maimakon su kasance kakannin mutane yanzu, ta yiwu Homo naledi sun yi kicibis da mutanen yanzu- Homo sapiens.

Kusufin rana

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ranar 21 ga watan Augustan,wata babbar inuwar wata ta rufe Amurka, lamarin da ya janyo kusufin rana na farko tun lokacin da aka samar da kasar a shekarar 1776.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalla: yadda Amurka ta samu kalar zobe mai launin lu’u-lu’u

Kuma wani abu ne mai jna hankali. Da yake bayar da raho daga garin Madras, na jahar Oregon, wakilin BBC, Pallab Ghosh ya ce: “Za ku iya ganin cewa karfe 10 da minti 15 n asafe , amma ya yiu kaman dare ne. Saura dakika kadan rana ta kammala kusufi…ranar tana nan kamar wata fuska mai dariya a sama.”

Bayan kusufin ya wuce, a kara da cewa: “Na ji kamar ina mafarki ne.”

Bako daga wata duniya

Hakkin mallakar hoto
ESO/M. Kornmesser

Image caption

Taswira: ‘Oumuamua tana ficewa daga inda na’urar hangen nesa za ta iya ganinta

Duk da cewa masana kimiyya sun dade suna hasashen cewa wani dutse daga sararin samaniya zai ziyarci duniyarmu, shekarar 2017 ne karon farko da muka ga irin wann dutsen. Dutsen da wasu masana da suka yi mafani da wata babbar na’urar hangen nesa ta Hawaii a watan Oktoba, ba da jimawa ba ne suka gane cewa irin gudu da kuma hanyar da dutsen ke bi ya nuna cewa dutsen ya fito ne daga wata duniya ta daban. Anrda masa suna ‘Oumuamua da ke nufin “dan sako mai zuwa cikin gaggawa daga wuri mai nisa” a harshen Hawaii, dutsen ya zama wani abu da masu na’urar hangen nesa suka yi ta neman kallo a fadin duniya.

A bangarori daban-daban ya kasance kamar sauran ababen da ake samu a wuri mafi nisa a sararin samaniyar duniyarmu- wurin da a ke kira Kuiper Belt objects (KBOs) – kuma yana da wani ja a cikin launinsa lamarin da ya samu sakamakon hasken rana na miliyoyin shekarau. Daya daga cikin abubuwan ba a cika gani ba game dutsen da ke yawo a sararin samaniya da ba cika sani ba ita ce siffarta.Duk da cewa an cigaba da bincike game da dutsen, da alama tsawon ‘Oumuamua ya kai fadinta sau 10, lamarin da ya sa ta zama abar da ta fi komai tsawo a cikin duniya da taurarinmu.

Babbar kankara

Hakkin mallakar hoto
Copernicus Sentinel (2017) ESA/Andrew Flemming

Image caption

Tauraron dan Adan na Turai mai suna Sentinel-1 ta tabbatar daballewar dutsen kankarar

Daya daga cikin dutsen kankara mafi girma da aka taba gani a duniya ya balle a yankin Larsen C na Antartica cikin watan Yuli. Amma masana kimiyya sun dade suna bibiyar girman wani babban tsagu na kimanin shekarau 10. An yi kiyasin cewa katafaren kankaran ya yi fadin kimanin murabba’in kilomita 6,000 – kimanin kwatan fadin Wales.

Fina-finan Kannywood 12 da suka shahara a 2017


Hakkin mallakar hoto
Muhsin Facebook

Image caption

Muhsin Ibrahim, Malamin harshen Hausa ne a jami’ar Bonn da ke Jamus kuma Malamin Ingilishi a jami’ar Bayero ta Kano

Daga Muhsin Ibrahim

Duk da babban kalubalen matsalar satar fasaha da masana’antar finafinan Kannywood ke fuskanta, amma an fitar da fina-finai da dama a cikin shekarar 2017, da suka kunshi masu kayatarwa da marar kyau da matsakaita.

Kuma kafin shekarar ta kawo karshe ana sa ran fitowar wasu sabbin fina-finai, kamar Juyin Sarauta, Sabon Dan Tijara, Dan Sarkin Agadaz, Mu Zuba Mu Gani, Dan Kuka a Birni da dai sauransu.

Don haka daya ko biyu daga cikinsu na iya shiga sahun Fina-finan 2017.

1. There’s a Way

Ana ganin wannan ne Fim na Inglishi na farko a masana’antar Kannywood, wanda furodusansa shi ne babban malamin Ingilishi Kabiru Jammaje, sannan Falalu Dorayi a matsayin darakta.

Fim din ya bayar da labari ne akan gwagwarmaya tsakanin masu karamin karfi da attajirai.

Hakkin mallakar hoto
Falalu Dorayi Instagram

An fito da halayyar wasu ‘ya’yan attajirai a Jami’a da kuma rayuwar mata, wanda a haka aka tsara labarin.

Soyayya ce tsakanin Isham (Nuhu Abdullahi) Dan talaka amma hazikin dalibi da kuma Fadila (Hajara Jalingo) ‘yar wani babban hamshakin attajiri Alhaji Mahdi (Sani Mu’azu) wanda ba ya kaunar hada zuri’a da talaka inda ya bi duk hanyoyin da zai bi domin ganin ya raba su.

Ana sa ran This is the Way, zai fito kafin karshen shekara. Raunin Fim din shi ne karshensa da kuma amfani da salon harshe mai sarkakiya.

Amma tsarin fim din baki dayansa ya kayatar wanda hakan martani ne ga sukar da ake wa masu shirya finafinan Hausa cewa jahilai ne, da ba su iya da turanci ba.

2. Umar Sanda

Kamal S. Alkali ne Daraktan Fim din, labarin ya mayar da hankali ne a kan mai ra’ayin rikau Umar Sanda (Ali Nuhu) da iyalinsa.

Ko da yake ma’aikaci ne, kuma yana kokarin ganin iyalinsa na cikin wadata. Ana zaman lafiya har zuwa lokacin da ‘yarsa ta hadu da wani abokin karatunta Dan shugaban ‘Yan sanda da aka shagwaba, wanda kuma ta kashe shi a kokarin kare kanta.

Hakkin mallakar hoto
Kamal Alkali Instagram

Umar Sanda ne ya binne gawar a yayin da ‘yan sanda ke bincike mai tsauri.

Duk da cewa an kwaikwayi fim din ne daga wani fim na Indiya, amma yadda aka tsara shi zai iya kasancewa daya daga cikin mafi shahara a bana. Ya nuna girman gaskiya da hadin kai da dabi’u masu kyau.

3. Ankon Biki

Ali Gumzak ne daraktan Fim din, kuma Ankon Biki ya mayar da hankali ne a kan muhimmin batu da ake fuskanta a yanzu.

Mubarak (Adam Zango) da Fa’iza (Sadiya Bulala) suna shirin aure, sai Fa’iza ta kawo batun “Anko” da bukatar a hada wani babban bikin kasaita a wani wuri mai tsada.

Mubarak da abokansa sun yi iya kokarin ganin sun biya bukatar Amarya da kawayenta amma sun gagara, amma Amaryar ta dage a kan bukatar har ta bayar da kanta a madadin kudin kama wajen da za a yi bikin.

Hakkin mallakar hoto
MIA Enterprises

Ya fasa aurenta a ranar bikin bayan asirinta ya tonu, kuma a madadinta ya auri kawarta ta kud da kud. Fim din ya nuna girman nisan da wasu mata ke dauka don cimma bukatunsu.

Duk da yake wasu wuraren a fitowar fim din na da tsayi amma an yi amfani da Hausa mai kyau da salon magana.

Sauran taurarin fim din sun hada da Hafsar Idris da Umma Shehu da Al Amin Buhari da dai sauransu.

4.Rariya

Yaseen Auwal ne Daraktan Rariya, kuma fim na farko da Rahama Sadau ta dauki nauyin fitowarsa, wato matsayin furodusa.

Labarin Fim din ya danganta tasirin wayar salula ta zamani da ake kira “komi da ruwanka”. Fim din ya shafi yadda wasu ‘yan matan Jami’a ke amfani da wayar salula domin janyo hankalin maza.

Yadda aka hada fim din ya kayatar. Babban muhimmin abu shi ne yadda daya daga cikin ‘yan matan ta banbanta da saura inda har ta yi kokarin kammala karatunta.

Hakkin mallakar hoto
Rahama Sadau Instagram

Mutane da dama ba za su so haka ba, musamman iyaye da ke da’awar karatun ‘ya’ya mata. Amma duk da haka linzamin labarin ya shafi abin da ke faruwa kuma ke shafar jama’a.

Taurarin Fim din sun kunshi Ali Nuhu da Rabiu Rikadawa da Rahma Sadau da Fati Washa da Hafsar Idris da sauransu.

5.Mijin Yarinya

Ali Gumzak ne Darakta, kuma Mijin Yarinya ya shafi labarin wani Dattijo Attajiri Bashir Nayaya (Alhaji).

Wata rana ya ji matansa guda biyu da Allah bai ba su haihuwa ba suna ma shi addu’ar mutuwa domin gadon dukiyarsa kuma don su aure yara samari, su yi sabuwar rayuwa.

Saboda haka ne ya je ya auri budurwa Maryam Yahaya bayan ya saye imanin iyayenta da saurayinta da kudi.

Hakkin mallakar hoto
Falalu Dorayi Instagram

Wannan ne ya fusata manyan ‘ya’yansa Aminu Sharif da Sadiya Bulala, inda suka taya iyayensu mata kishi.

Bayan shafe lokaci ana makirci da takaddama, Alhaji ya yanke shawarar sakin dukkanin matansa, hadi da amaryarsa. Fim din na kunshe da darussa masu yawa a yadda aka tsara fim din.

Sabuwar ‘yar fim Maryam Yahya ta yi kokari a fim din mai kunshe da gwanaye. Ba tare da zuzutawa ba fim din na cike da ban dariya da ilmantarwa.

6.Kalan Dangi

Wannan ma wani fim ne na barkwanci da Ali Gumzak ya bada umurni wato a matsayin Darakta, Fim din ya nuna yadda talakawa ke neman arziki da kuma attajirai.

Yayin da kuma masu arzikin ke kaskanta Talakawa. Ali Nuhu da Aminu Sharif da Sadiq Sani Sadiq da Jamila Nagudu da Fati Washa da Aisha Tsamiya na rayuwa ne ta nuna arziki da karya da makirci da nuna karfin iko. Idan kana neman nishadantarwa, to ka nemi Kalan Dangi.

Hakkin mallakar hoto
Aisha Tsamiya Instagram

Sai dai an raba fim din biyu, na daya da na biyu. Amma an takaita labarin da kuma karshensa, wanda ake sa ran fitarwa a shekara mai zuwa.

Kamar taken fim din Karshen Kalan Dangi zai iya kawo karshen duk wani rikici.

7.Makaryaci

Kamar sauran shahararrun fina-finan barkwanci da aka fitar a 2017, Ali Gumzak ne daraktan Makaryaci.

Sadiq Sani Sadiq ne da Allah ya ba basirar wasan kwaikwayo, ya daukaka fim din a matsayin daya daga cikin fitattu a bana. Labarin Fim din ya shafi yadda kwadayinsa na dukiya ya kai shi ga samun kudi ba tare da ya sha wata wahala ba.

Yakan je ya yi hayar tufafi ya harde cikin babbar motar mai gidan Rabiu Daushe ana tuka shi zuwa wurare har zuwa cikin Jami’a. Yakan yi wa dalibai karyar cewa shi dan gidan minista ne ko ambasada.

Hakkin mallakar hoto
Sadiq Sani Instagram

A hakan ne ya fara soyayya da daya daga cikin daliban Hafsat Idris. Ba tare da bin umurnin kakanninsa ba, ya je ya kadar da dabbobinsa na gado, domin ya kashe wa budurwarsa kudi wacce daga baya ta gano asalinsa.

Taurarin Fim din sun kunshi Sulaiman Bosho da Mama Tambaya da Mustapha Nabaruska da Musa Maisana’a da sauransu.

8.Husna ko Huzna

Husna (Jamila Naguda da Abdul (Adam Zango) sun shirya yin aure, yayin da kuma Huzna (Fati Washa) ta yi kokarin hana auren saboda matukar son da ta ke wa Abdul.

A yayin da suke hamayya, wata rana Husna ta watsa wa Huzna guba a fuska, ba tare da sanin cewa ashe fatalwa ce. Washegari Huzna ta tafi gidansu ta mallaki Husna.

Wannan ya bude wani sabon babin hamayya tsakaninsu inda Huzna ta shiga jikin Husna kuma ta ci gaba da zama a gidanta. Yadda aka tsara fim din ya ja hankali.

Hakkin mallakar hoto
Falalu Dorayi Instagram

Amma duk da akwai matsaloli da aka samu, Fim din na iya zama daya daga cikin manyan fitattu finafinai a Kannywood.

Fim din dai bai kasance wani abin muni ga mata ba, kamar yadda aka tsara labarin fim din irin na ban tsoro, a rikicin rayuwar aure tsakanin mata don mallakar namiji.

Rawar da Washa ta taka ya kayatar. Falalu Dorayi ne Daraktan Fim din.

9.Burin Fatima

Wasu za su yi mamakin yadda wannan fim ya shigo sahun fitattu. Ya cancanta. Labari ne akan wata matar aure da ta fada tarkon shawarar kawarta.

Aisha Tsamiya tauraruwar fim din ita ce kuma ta dauki nauyin fitowarsa a matsayin furodusa.

Fim din ya ba da labarin wata mata (Tsamiya) da mijinta, Adam Zango a yayin da ta ke makaranta, wata kawarta ta ba ta shawarar ta zubar da juna biyu da take dauke shi don ta samu sukunin karatu.

Hakkin mallakar hoto
Ali Gumzak Instagram

Ta karbi shawarar kuma ta yi wa mijinta karya cewa cikin ya bare, ba tare da sanin cewa ba ta kara haihuwa ba. Ta fuskanci kalubale daga sarakuwarta kan rashin haihuwa inda ta tursasawa Zango ya kara aure.

Ali Gumzak ne ya bayar umurni a fim din da ba a kashewa kudi ba. Sannan bai samu karbuwa ba.

Amma ba don haka ba da zai kasance daya daga cikin finafinan da suka samu karbuwa ga jama’a. Wannan dai ci gaba ne ga Tsamiya, kasancewar fim dinta na farko a matsayin furodusa.

10.Mansoor

Fim din Mansoor na FKD yana cikin wadanda ake kururutawa a matsayin gwarzon shekara. Ali Nuhu ne Darakta.

An fara fim din ne da soyayyar wasu matasa daliban makaranta, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif.

Amma mahaifin Sharif ne ya kawo karshen abotar, saboda yana zargin Sharif ba ya da uba, wanda wannan ya ba shi kwarin guiwar gudanar da bincike domin gano asalin mahaifinsa, ba tare da sanin cewa ashe gwamnan jiha ba ne mahaifinsa.

Hakkin mallakar hoto
Maryam Yahaya Instagram

Labari ne ya mamaye fim din. Kuma ko shakka babu, fim din ya kasance kamar a zahiri. Baki dayan fim din ya shafi labarin matasan masoya tsakaninsu da iyayensu.

An aiwatar da fim din da kyau. Taurarin fim din sun hada da Ali Nuhu da Abba El Mustapha da Baballe Hayatu da Teema Yola da dai sauransu.

11. Dawo Dawo

Fim din Kabuwagawa ne wanda Ali Gumzak ya bayar da umurni.

Dawo-Dawo labari ne game da wasu da suka reni yaro (Adam Zango) tun kuriciya har girmansa inda suka kuma aurar ma shi da ‘yarsu (Maryam Gidado).

Amma daren farkon aurensu, amaryar ta yi karyar cewa tana da aljannu, ta tursasa ma shi ya sake ta. Nan take iyayen suka daura ma shi aure da kanwarta (Aisha Tsamiya).

Hakkin mallakar hoto
Ali Gumzak Instagram

Ita kuma (Gidado) ta koma ga tsohon saurayinta (Zahraddeen Sani) wanda saboda shi ta kulla makircin. Daga baya ya yi watsi da ita, inda ta shiga wani hali ta koma kamar mahaukaciya lokacin da ta fahimci cewa ta dauke da cikin Zaharaddeen.

Fim din na cike da makirci da rikici, kuma taurarin fim din Zango da Tsamiya da Gidado suna yi kokari sosai. Wannan ya sa fim din ya sha gaban takwarorinsa a bana.

12. Ta Faru ta Kare

Aminu Saira ne daraktan Ta Faru ta Kare, labarin fim din ya shafi rayuwar Hafsat Idris, gurguwa, makauniya amma ‘yar attajiri, da kuma Aminu Sharif (Momo) wanda ya aure ta kuma yake cin amanarta yana kawo ‘yan matansa a gidanta har zuwa lokacin da dubunsa ta cika.

Inda Adam Zango, abokin wasanta wanda Momo ya yi wa kanwarsa ciki ya yake shi har ya fitar da shi daga gidan.

Hakkin mallakar hoto
Umar Gombe Instagram

Fim din na tattare da nishadi. Hafsat Idris da ta fito mai nakasar jiki da kuma Momo sun yi kokari a rawar da suka taka a fim din.

Sauran taurarin fim din sun hada Hadiza Gabon da Hauwa Waraka da sauransu.

Arsene Wenger ya ce ba ya tsoron tafiyar Sanchez daga Arsenal duk da cin kwallon da yake yi


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Arsene Wenger ya yaba wa Alexis Sanchez kan kwallo biyun da ya ci suka doke Newcastle 3-2

Arsene Wenger ya ce ba shi da wata damuwa a kan rasa Alexis Sanchez a watan Janairu, duk da kwallo biyu da dan wasan na gaba ya ci wa kungiyar da ta doke Crystal Palace 3-2.

Kwantiragin dan wasan na Chile zai kare ne da Arsenal a karshen kakar da ake ciki, kuma ana danganta dan wasan mai shekara 29 da tafiya jagorar Premier Manchester City, wadda ta kasa sayensa a karshen kakar da ta gabata.

Wenger wanda ya kamo tarihin da Sir Alex Ferguson ya kafa a Premier na jagorantar wasa 810 a gasar, ya ce shi kam ba shi da wata damuwa, illa dai abu ne da ya shafi kwantiragin dan wasan.

A wasan nasu da Newcastle bayan Andros Townsend ya farke kwallon da Shkodran Mustafi ya ci wa Arsenal a kashin farko na wasan ne, Sanchez ya zura kwallo biyu a cikin minti hudu a ragar masu masaukin bakin.

Mustafi ya fara daga ragar ‘yan Newcastle a minti na 25 da wasa, amma Townsend ya farke a minti na 49, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ke nan.

Daga nan ne kuma sai Sánchez din ya ci wa Arsenal ta biyu a minti na 62, sannan ya kara daga ragar bayan minti hudu.

Ana shirin tashi ne daga wasan sai kuma Tomkins ya ci wa Newcastle ta biyu a minti na 89.

Nasarar ta sa Gunners din sun ci gaba da zama a matsayi na shida da yawan maki 37 daidai da ta biyar Tottenham, kuma maki daya tsakaninta da ta hudu Liverpool.

Ita kuwa Newcastle tana matsayi na 16 a teburin na Premier bayan wasa 20.

Wenger da Ferguson: Wa ya fi samun nasara a Premier?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wenger ya jagoranci Arsenal wasanni 810 a premier.

Arsene Wenger ya jagoranci Arsenal wasannin Premier 810 inda ya yanzu ya yi kafada da Sir Alex Ferguson tsohon kocin Manchester United.

Wenger ya kamo Ferguson ne a wasan da Arsneal ta samu sa’ar Crystal Palace 3-2 a Selhurst Park.

Arsene Wenger zai sha gaban Ferguson a matsayin kocin da ya fi jagorantar wasannin premier a wasan da Arsenal za ta fafata da West Brom a jajibirin farkon shekara.

Arsene Wenger mai shekaru 68, tun a 1996 ne yake jagorantar Arsenal, shekaru 21 da suka gabata.

Kafin 2004, Arsene Wenger ya lashe kofin premier guda uku, amma tun daga lokacin yake farautar kofin.

Wenger da Ferguson.

Duk da cewa Wenger ya kamo Ferguson da yawan jagorantar wasannin premier 810, amma akwai rata tsakaninsu ta fuskar nasorori.

Tazarar nasarar wasanni 60 ne Alex Ferguson ya ba Arsene Wenger.

Arsene Wenger ya lashe wasanni 467, Ferguson kuma ya samu nasara a wasanni 528.

Wenger ya sha kashi a wasanni 145, yayin da Ferguson ya sha kashi a wasanni 114.

An ci Wenger kwallaye 779 a Arsenal, Ferguson kuma 703.

Sannan Farguson ya fi cin kwallaye inda ya ci 1,627, Wenger kuma 1,521

Kofi 13 na lig Fergusaon ya lashe inda ya ba Wenger tazarar kofi 10, yayin shi kuma ya ci guda uku.

Mourinho ya ce kudaden da ya kashe a Manchester ba su isa ba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mourinho na bukatar kudi domin sayen ‘yan wasa.

Jose Mourinho ya bukaci Manchester United ta ware ma sa wasu karin kudade domin cefanen sabbin ‘yan wasa.

Mourinho ya ce kudaden da ya kashe sama da fam miliyan 300 tun zuwansa Manchester United a watanni 18 sun yi kadan.

Mourinho ya fadi haka ne bayan Burnley ta rike shi 2-2 a Old Trafford.

Kocin ya ce idan har United za ta sha gaban City, to dole sai ta kara kashe kudi a kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu.

Tazarar maki 15 yanzu Manchester City ta ba Manchester United a teburin Premier.

Mourinho ya ce yana iya datse yawan makin da City ta ba United idan har ya yi zubin sabbin ‘yan wasa.

Amma wasu magoya bayan Manchester United na ganin kudaden da Mourinho ya kashe sun isa ace ya gina kungiyar.

Kocin City Pep Guardiola ya fi Mourinho kashe kudi a kasuwar musayar ‘yan wasa da ta gabata.

Kuma yanzu nasarorin da Manchester City ke samu ne a bana suka shafe duk wani kokarin da Mourinho ke yi a United.

A kakar da ta gabata Mourinho ya lashe wa Manchester United kofuna biyu, kuma a bana yana matsayi na biyu a teburin premier.

George Weah ya lashe zaben Liberia


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mista Weah ne ya lashe zaben a zagayen farko da aka yi a watan Oktoba

Tsohon shahararren dan kwallon kafa George Weah ya lashe zaben shugaban kasar Liberia.

Bayan da aka kidaya kuri’u daga kusan dukkan mazabun kasar, kuma bayan zaben da aka yi a zagaye na biyu, George Weahn ya tserewa abokin karawarsa, Joseph Boakai nesa ba kusa ba.

Zai gaji Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko da aka taba zaba a matsayin shugabar kasa a Afirka, kuma a zaben demokradiyya na farko da zababbe zai mika wa wani zababben tun bayan yakin basasar kasar.

Mrs Sirleaf ta doke Mista Weah a zaben shugaba kasar da aka gudanar, shi ma a zagaye na biyu, a 2005 bayan yakin basasar kasar.

Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.

Trump ya amince da sayar wa Nigeria jiragen yaki


babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Marshall Sadik Baba Abubakar jakadan Amurka a Najeriya Stuart SymingtonHakkin mallakar hoto
NAF

Image caption

Babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Marshall Sadik Baba Abubakar (Tsakiya) da Jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington (biyu daga hagu)

Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen yakin guda 12 samfurin A29 Super Tucano a cikin wata wasika sa ta aikewa rundunar sojan samar kasar.

Da yake gabatar da wasikar, jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington ya bayyana kudurin gwamnatin kasarsa na taimakawa Najeriyar cin galaba kan mayakan kungiyar Boko Haram.

Ya kuma ce wannan ya hada da taimakawa Najeriya kawar da duk wani nau’in ta’addanci daga cikin iyakokinta.

Jakadan na Amurka ya ce ko baya ga sayar da jiragen, gwamnatin kasarsa a shirye ta ke ta taimakawa rundunar sojin saman ta Najeriya a kokarin da take yi na kara karfafa mayakanta ciki har da rika samar mata da kayayyakin gyara da kuma tattalin jiragen.

Hakkin mallakar hoto
NAF

Image caption

Gwamnatin ta Donald Trump kuma ta ce a shirye take ta mika wa Najeriya jiragen

Gwamnatin ta Donald Trump kuma ta ce a shirye take ta mika wa Najeriya wadannan jiragen tun da wuri amma sai ta biya kudinsu lakadan.

Babban hafsan sojan saman Najeriya Air Marshall Sadique Baba Abubakar, wanda ya karbi wannan wasikar a madadin rundunar ya yaba da wannan mataki na Amurka.

Ya kuma ce ba da bata lokaci ba zai bayar da sunayen matuka da kanikawan jiragen yakin rundunar domin a ba su horo a kasar ta Amurka kan yadda za su sarrafa wadannan jiragen.

A cikin wata sanarwa daga daraktan watsa labarai na rundunar sojan saman ta Najeriya Air Vice Marshall Olatokunbo Adesanya ta ce ana sa ran kammala sa hannu a kan yarjeniyoyin cinikin da kuma biyan kudin jiragen kafin ranar 20 ga watan Fabrairu na shekarar 2018.

Gwamnatin Donald Trump ta amince da bukatar sayar wa Najeriya wadannan jiragen yakin domin yakar kungiyar Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Tun a shekara ta 2014 ne Najeriya ta bukaci sayen jiragen daga kasar ta Amurka.

Amma a wancan lokacin gwamnatin tsohon shugaba Barrack Obama ta ki amincewa da hakan saboda damuwar da take da ita cewa mai yiwuwa a yi amfani da makaman wajen keta hakkin bil adama.

Swansea ta nada Carlos Carvalhal sabon kocinta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Carlos Carvalhal sabon kocin Swansea City

Swansea City da ke kasan teburin Premier ta nada tsohon mai horar da ‘yan wasan Sheffield Carlos Carvalhal a matsayin sabon kocinta.

Carvalhal dan kasar Portugal zai ci gaba da horar da Swansea ne har zuwa karshen kaka amma da nufin tsawaita kwantaraginsa idan kakar ta yi kyau.

Swansea ta dauki Carvalhal ne bayan Sheffield da ke Lig mataki na biyu a Ingila ta sallame shi a jajibirin Kirsimeti yayin da kungiyar ke matsayi na 15 a tebur.

Yanzu shi ne mai horar da ‘yan wasa na biyar da Swansea ta dauka a shekaru biyu bayan kungiyar ta kori Paul Clement.

A ranar Talata Liverpool ta lallasa Swansea 5-0 bayan kungiyar ta buga wasanni hudu tana shan kashi a premier.

Swansea City ce ta karshe a teburin premier, kuma babban kalubalen da ke gaban Carvalhal a yanzu shi ne farfado da kungiyar a teburin gasar.

Goodluck Jonathan ya jajanta wa Buhari kan Yusuf


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mista Jonathan yace shi da iyalinsa suna yi wa Yusuf addu’a

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya taya shugaban kasar Muhamadu Buhari jaje game da hatsarin da dansa Yusuf ya yi a kan wani babur na tsere.

Fadar shugaban kasar ta ce Yusuf “ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki” bayan hatsarin da ya yi a unguwar Gwarimpa da ke kwaryar birnin Abuja.

Sai dai ta musanta wani rahoto da ke cewa an kai asibitin kasashen waje domin kula da lafiyarsa.

A wata sanarwa da Goodluck Jonathan ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi addu’ar samun sauki ga Yusuf Buhari, yana mai cewa “Ina kasar Liberia inda nake sa ido kan zaben kasar sai kawai na ji wannan mummunan labari.

“Ni da iyalina muna yin addu’ar saurin samun sauki ga Yusuf Buhari. Ina matukar shaukin ganin wannan matashi wanda ke kan ganiyarsa ya rayu sannan ya cika alkawuran da Allah ya dora masa a matsayinsa na dan adam.”, in ji tsohon shugaban.

Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar da shugaban majalisar dattawan Najeriya sun jajanta wa Shugaba Buhari kan hatsarin da dansa ya yi.

An kai Yusuf Buhari asibitin kasar waje?


Hakkin mallakar hoto
TWITTER/YUSUF BUHARI

Image caption

Yusuf Buhari ya samu karaya ne da rauni a kai a wani mummunar hatsarin babur ranar Talata

Fadar Shugaban Najeriya ta karyata rahoton da ke cewa an fitar da dan Shugaban kasar, Yusuf Buhari kasar waje domin duba lafiyarsa bayan raunin da ya ji sakamakoni hatsarin babur.

Kakakin fadar Shugaban Garba Shehu ne ya shaida wa BBC hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoton da aka wallafa a wata jaridar da ake wallafawa a shafin intanet.

Rahoton dai ya ce an garzaya da Yusuf Buhari wani asibiti a kasar Jamus a wani jirgin daukar marasa lafiya da safiyar Alhamis.

Kazalika rahoton ya ce jirgin ya tashi ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja tare da na’urar da ke tallafawa mutum yin numfashi da wani likitan Najeriya.

Sai dai Mallam Garba Shehu ya ce rahoton ba gaskiya ba ne.

Da BBC ta nemi sanin ko akwai shirin fitar da dan shugaban kasar Najeriyar waje, mai magana da yawun shugaban na Najeriya ya ce iyayen matashin ne kawai za su iya yanke wannan shawarar.

Yusuf Buhari ya samu karaya ne da rauni a kai a hatsarin da ya yi a kan babur din tsere ranar Talata.

Nigeria: fursunoni 36 sun tsere daga gidan yari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hudu daga cikin fursunonin sun mutu

Akalla fursunoni 36 ne suka tsere daga gidan yarin garin Ikot Ekpene da ke jihar Akwa-Ibom a kudu maso kudancin Najeriya bayan sun fasa gidan.

Wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na rundunar gandirobobin jihar Ogbajie J. Ogbajie ya fitar ta ce fursunonin da suka fasa gidan yarin sun kwace gatari daga masu dafa abinci daga cikinsu suka yi amfani da shi wajen kai musu hari har suka ji musu ciwo a ka.

Sanarwar ta ce daga nan sai suka afka wa kofar baya ta gidan yarin da gatarin suna masu gumurzu da jami’an tsaron gidan da suka bi su.

Kazalika sanarwar ta ce bayan rikicin ya lafa dai hudu daga cikin fursunonin sun mutu daga raunukan da suka ji sakamakon harbin bindiga kuma an kamo bakwai daga cikinsu, yayin da 36 suka tsere.

Shugaban rundunar jami’an gidan yari na jihar, Alex Oditah, ya bayar da umarnin bincika yadda aka fasa gidan yarin.

Ana samun irin yanayin da fursuna ke fasa gidan yari a Najeriya inda ake samun cinkoso da yawa, yayin da mafi yawa daga cikin mutane da ke gidan yarin suna jiran shari’a ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana yawan samun cinkoso a gidajen yarin Najeriya

Aikin agaji ya fara kai wa ga yara a Syria


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Yara sun kasance wadanda yakin Syria ya fi jefa wa cikin mawuyacin hali

Ma’aikatan sa-kai na agaji a Syria sun kwashe kashin farko na yaran da ke cikin wani mummunan hali na rashin lafiya daga yankin da ‘yan tawaye ke iko da shi a kusa da Damascus.

Kungiyoyin bayar da agaji sun bukaci Shugaba Assad da ya bayar da dama a samu a shiga a yi wa tarin yaran da ke cikin matukar bakutar taimako, ciki har da wasu yara bakwai da ke fama da cutar daji.

Yanayin lafiyar da mazauna yankin gabashin Ghouta ya shiga wani mataki na kaka-ni-kayi ne bayan shekara hudu da yankin yake rike a hannun mayaka masu tayar da kayar baya.

An ga yara da dama sanye da tufafin da ke musu maganin tsananin sanyin da ke addabarsu, iyayensu mata na sanya su cikin motocin daukar marassa lafiya ana tafiya da su asibitoci a Damascus.

Yaran marassa lafiya na daga tarin wadanda ke cikin mawuyacin hali wadanda aka mika jerin sunayensu ga majalisar dinkin duniya tun wata biyu da ya gabata.

Mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross a Geneva, Anastasia Isyuk ta ce, tana fatan za su samu damar ci gaba da wannan aiki na kwashe yaran marassa lafiya, tare da fatan bangarorin biyu da ke yaki za su taimaka wa aikin.

Kuma ana matukar maraba da duk wani aiki na bayar da agaji.

Takwarar kungiyar agajin ta Red Cross, wato Red Cresent ta ki bayar da bayanin yadda aka cimma wannan yarjejeniya ta kwasar yaran, illa dai ta ce an cimma matsaya ne bayan doguwar tattaunawa da hukumomin Syria.

Hakkin mallakar hoto
SARC

Image caption

Tawagar motocin agaji na kungiyar Red Cresent

‘yan wasu kalilan din likitoci ne kawai suke aikin kula da lafiyar mutane kusan dubu 400 a yankin na Gabashin Ghouta.

Yankin dai na daga cikin wadanda aka lasafta na wadanda aka daina bude wuta a cikinsa, amma kuma rahotanni na cewa dakarun gwamnatin Syria na ci gaba da ruwan bama-bamai a cikinsa a ‘yan makonnin nan.

Yayin da ake cikin wannan yanayi, ita kuwa Rasha ta ce an kawo karshen babbar fafatawar da ake yi a Syrian ta neman murkushe kungiyar IS ta masu ikirarin jihadi.

Sai dai ta ce muhimmin abin da aka sanya a gaba yanzu shi ne na ganin an kawar da kungiyar Nusra Front wadda ke da alaka da al-Qaeda.

Ministan harkokin waje na Rashar Sergei Lavrov, ya ce wasu daga cikin mayakan ‘yan tawaye da suka tsere daga filin daga, suna kokarin kara haduwa a cikin Syria ko kuma suna neman tserewa daga kasar.

A wasu kalaman na daban babban hafsan hafsoshin Rasha Janar Valery Gerasimov, ya yi zargin cewa Amurka na horar da tsoffin mayakan kungiyar IS a Syria a sansanin soji na Tanf wanda ke kan iyakar Syria da Iraq.

Sai dai wannan zargi ne da daman Amurka ta sha musawa tana cewa ita har yanzu tana goyon bayan kawar da kungiyar IS.

‘Matan Nigeria na kauracewa Facebook saboda cin zarafi’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau’i na tauye ‘yancin mata

Wani bincike ya nuna cewa mata da dama a arewacin Najeriya su na kaurace wa intanet sakamakon barazana da cin zarafin da suke fuskanta daga ma’abota shafukan sada zumunta, musamman ma Facebook.

Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau’i na tauye ‘yancin mata, wanda ke bukatar mahukunta su dauki matakan yaki da shi.

Wannan lamari ne ya sa Cibiyar Sasahar Sadarwa da ci gaban al’umma da ke Kano ta shirya wani taro don nazarin rahoton tare da duba hanyoyin magance matsalar.

Ibrahim Isa ya tattauna da Mallam Muhammad Awwal Garba daga hukumar Hisbah ta jihar Kano da Maryam Ado Haruna, jami’a a wannan cibiya ta fasahar sadarwa da aka fi sani da CITAD, inda suka yi masa bayanin yadda girman matsalar take.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron cikakkiyar hirar tasu:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da jami’an Hisbah da CITAD

Kun san sirrin garayar zinari ta Afirka Ta Kudu?


Image caption

Wannan kayan kidin ya taba kasancewa wani abu mai sheki kan muhimman dandamali a Afirka ta Kudu

A shekarar 1962 Igor Stravinsky, mai kirkirar wakar gargajiya ta Turai dan asalin Rasha, wanda yana kuma jagorantar wake-wake, ya ziyarci hukumar talabijin ta Afirka ta Kudu domin ya jagoranci wasu jerin wakoki da za a yi.

Lokacin da ake tsaka da mulkin wariyar launin fata, gwamnatin ta yi imanin cewar wakar gargajiya ta Turai ta fararen fata ne kawai.

Wakiliyar BBC, Sophie Ribstein, ta yi waiwaye domin ta yi nazari akan ko an yi amfani da wata babbar garaya ta zinari a taron wakokin.

Bincikenta tamkar komawa lokacin da can ne. An lullulbe bangwayen da darduma mai ruwan kasa.

Da na shiga zauren hedikwatar hukumar talabijin din Afirka ta Kudu, SABC, tamkar ina tafiya ne a shekarun 1970s, a lokacin da gwamnatin wariyar launin fata take iko da ginin tare da mamaye rediyo da talabijin din kasar.

SABC ta taba kasancewa muhimmiyar kafar watsa farfaganda ta gwamnatin wariyar launin fata.

Sannan na yi wata kwana, na tura wani get, sannan na shiga dakin adana wakoki… kuma komai ya sauya.

Na zo ne domin in ga wani abin tarihi na wancan lokacin – wata garayar zinari ta wancan lokacin, wadda fitaccen mai hada garaya na Amurka Lyon and Healy ya sassaka.

Wannan kayan kidin ya taba kasancewa kan mumman dandamali a kasar.

Image caption

Sautin garayar tana nan yadda take a da

A wancan lokacin babban mai kada garaya na gidan kade-kade na hukumar SABC shi ne yake kada garayar tarukan wakar gargajiya ta Turai – wadda a wancan lokacin fararen fata ne kawai ake kyalewa su halarci taron.

A halin yanzu kasaitattciyar garayar, ta yi shiru, karkashin wani lullubin kare datti a gefen wani daki na lokacin da.

Ni ma kaina ina kada garaya, kuma na ji labarin wannan kayan kidan daga mutumin da ya hada mini garayata a Faransa.

Na cire lullubin garayar a hankali, kuma na zauna sannan na rungumeta da kafadata ta dama.

Zuciyata ta kara sauri. Da na fara kadata, yatsuna suka motsa daga waya zuwa waya, sautin da ya fito tatacce ne kuma mai cike da ma’ana, na ji dadi tare da gamsuwa.

Har yanzu sautinta na nan kamar yadda yake a da can.

Image caption

garayar mai matukar tsawo tana nan cikin nagarta

A lokacin da mulkin wariyar launin fata ya zo karshe a shekarun 1990, an rufe gidan wakar farare na SABC, kuma an adana abubuwan gidan wakar a cikin dakin adana abubuwa.

Tare da kayayyakin waka akwai daruruwan da kuma dubban rubutattun wakoki, wadanda yawancinsu aka rubuta su da hannu cikin wasu abubuwan tarihi na wannan lokacin.

A kan bangon, na ga wasu hotuna marasa kala …. na Igor Stravinsky a Afirka ta Kudu.

Na yi tunanin me ya sa wannan fitaccen mai kirkirar waka dan asalin Rasha ya zo nan?

A shekarar 1962 ne ya ziyarci kasar wadda take cikin tashin hankali a wancan lokacin saboda gwamnatin wariyar launin fata da ke danne hakkin tofa albarkacin baki.

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

An gayyaci Stravinsky domin ya yi wasa wa farare kadai, amman ya hakikance akan cewa zai yi wasa a gaban bakake ‘yan Afirka ta Kudu ma

Daga baya na gano cewa, an gayyaci Stravinsky domin ya gudanar da wakar gidan kade-kade na hukumar SABC, amma abin da ya fi jan hankali dangane da ziyararsa, shi ne ya dage cewa dole sai ya yi wasa gaban bakake.

Hukumomi sun ba shi damar yin hakan a KwaThema, wani garin bakake da ke da nisan kilomita 40 daga birnin Johannesburg.

“Ina son in yi waka a gaban ‘yan Adam ne kawai ,” in ji mawakin.

“Na so in san yadda bakaken da suka kalli wakar suka ji dadinta.

Ta yaya ma suka ji labarinsa a daidai lokacin da gwamantin take ganin irin wannan wakar ta fararen fata ne kawai?

Yarima Thethe zai iya tunawa da wakar da ya yi.

“Na hadu da mawakin mai tsayi kuma mai shakara 82 a cikin katafaren dakin taro mai suna KwaThema, inda Stravinsky ya yi waka.

Sai mutum ya ji yana ko ina.

“Wancan lokacin ne karon farko da na tsaya kusa da gidan kade-kade! Na kasa yarda da cewa da gaske hakan na faruwa!

A daidai lokacin da hannayen Stravinsky suka yi sama, wakar kuma ta kayatar da masu kallo matuka,” kamar yadda ya shaida mini yana mai zakuwa kamar wanda zai hau kan dandamali domin ya kwaikwayi kwararren mawakin.

“Ana guda, ana fito! Amma da zarar an fara wakar, ko ina ya yi tsit ta yadda idan allura ta fadi za ka ji.”

A lokacin mulkin wariyar launin fata, ya ce, shiga shagon sayar da faya-feyin waka ya kasance haramtaccen abu.

Na zayyana wurin da abin ya faru a kaina: dubban mutane sun hallara a wannan dakin taron, suna jin ko wnne sauti, suna kallon ko wanne motsi da mawakan suka yi da kuma dan Rasha gajere da ke jagorantar makadan.

A bayan dakin taron, shin jitar zinaren ta kasance a wurin ne?

A lokacin da wani abokin aikina na BBC ya yi kicibis da wakar makadan da aka nada a fai-fai a wurin adana kayan tarihi na hukumar gidan talabijin ta Afirka ta Kudu (SABC), mun saurarri wakoki daga The Fireworks Suite da kuma kadan daga cikin wakokin Pulcinella da Petrushka a hankali.

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Wakar da Stravinsky ya yi a gaban bakake ta karya dokar mulkin wariyar launin fata

Ta yiwu ba a saurari faifayin wakar ba cikin shekara 55. Wannan ya sosa mana rai.

Amman babu alamar garayar cikin wakar da aka nada. Abu ne mai jan hankali, amman wani sirri ne da ba a gano bakin zarensa ba.

Kuma yayin da nake tunanin wannan tarihin, wata rana na zauna a bayan kayan kidana a gida kuma na saka wata gajeruwar waka wadda Igor Stravinsky ya yi a karshen ziyararsa.

Ya gina wakarsa ne bisa sautin “S, A, B, C” – S wanda ke daidai da E mai shimfida – domin ya gode wa gidan kade-kaden doa gayyatar da ta yi masa.

Kalli hotunan abubuwan da suka faru a duniya a 2017


Hotunan wasu labaran da suka fi jan hankali da muka zabo dominku daga sassa daban-daban na duniya a shekarar da ke karewa ta 2017.

Hakkin mallakar hoto
ABIR SULTAN/ EPA

Image caption

A nan ana yi wa wata mai bin addinin kirista daga Eritriya a Qasr El-Yahud da ke bangaren Yamma da Kogin Jordan. Wannan ne wurin da kirista suka yi imanin cewa Annabi Yahaya ya yi wa Isa Al-Masihu baftisma. Sabili da yanayin rikice-rikicen addini a wurin ne aka kulla wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Isra’ila da hukumar Falasdinawa tare da wasu dariku bakwai domin masu ziyara su sami damar zuwa wurin.

Kandy Freeman participates in a Black Lives Matter protest in front of Trump Tower in New York City, on 14 January 2017.Hakkin mallakar hoto
Stephanie Keith/REUTERS

Image caption

Ita kuma Kandy Freeman ta shiga wata zanga-zanga ta “Black Lives Matter” a gaban ginin Trump Tower da ke birnin New York. An shirya wannan zanga-zangar ce a Amurka domin mayar da martani saboda kisan bakaken fata da ‘yan sanda ke yi.

A moth lands on the nose of Rafael Nadal.Hakkin mallakar hoto
LUKAS COCH/ EPA

Image caption

Wani kwaro ya sauka a kan hancin Rafael Nadal na Spaniya a yayin da yake fafatawa da Milos Raonic na kasar Canada a gasar wasan tennis da aka yi a Ostreliya.

President Donald Trump takes the oath of office from Supreme Court Chief Justice John Roberts on the West Front of the U.S. Capitol on 20 January 2017 in Washington, DC. In today's inauguration ceremony Donald J Trump becomes the 45th president of the United States.Hakkin mallakar hoto
Alex Wong/Getty Images

Image caption

Ranar 20 ga watan Janairu ne aka rantsar da Donald J Trump a matsayin shugaban Amurka na 45 a birnin Washington, yayin da matarsa Malania ke kallon bikin. A jawabinsa bayan an rantsar da shi, ya sha alwashin tsaya wa Amurkawan da aka “manta da su”, kuma ya ce “kasarmu za ta sake samun daukaka”.

Khalil Hymore Quasha and his daughter Norah Quasha participate in the Women's March on Washington.Hakkin mallakar hoto
Lucy Nicholson/ Reuters

Image caption

An gudanar da fiye da maci 600 a sassan duniya daban-daban a ranar farko ta mulkin shugaba Trump na Amurka. A birnin Washington DC, Khalil Quasha ya dauki ‘yarsa mai shekara shida a bisa kafadunsa.

A golden eagle grabs a flying drone.Hakkin mallakar hoto
Regis Duvignau/ Reuters

Image caption

A yankin kudu maso yammacin Faransa, wani maiki mai ruwan zinari ya kama wani karamin jirgi mai sarrafa kansa a yayin da ake wani atisayen soji a sansanin Mont-de-Marsan na sojin sama.

Children dressed as Charlie Chaplin pose for a group photo.Hakkin mallakar hoto
LAURENT GILLIERON/ EPA

Image caption

Fiye da mutum 600 sun halarci wani bikin tunawa da shahararren mai wasan barkwancin nan, Vharlie Chaplin, inda suka yi shiga irin tasa a Corsier-sur-Vevey. Chaplin ya mutu ne a wannan garin bayan da ya shafe shekara 24 a garin.

Italy's Mount Etna, Europe's tallest and most active volcano, spewed lava as it erupted on the southern island of Sicily, Italy on 28 February 2017.Hakkin mallakar hoto
Antonio Parrinello/REUTERS

Image caption

Dutse mai amon wuta na Mount Etna da ke Italiya ya amayar da narkakken dutse da wuta a tsibirin Sisili da ke kudancin kasar a watan Fabrairu.

Aibhin Kenneally aged 13 from the Flynn-O'Kane dance group warms up backstage.Hakkin mallakar hoto
Clodagh Kilcoyne/ Reuters

Image caption

Yarinya ‘yar shekara 13 da haihuwa, Aibhin Kenneally na motsa jiki gabanin gasar rawar ‘yan Irish ta duniya da aka yi a birnin Dublin.

The sun reappears behind the moon during a full eclipse in Sisters Oregon, USA.Hakkin mallakar hoto
MONICA M. DAVEY/ EPA

Image caption

Ranar 21 ga watan Agusta, fiye da mutum miliyan bakwai a fadin Amurka suka kalli kusufin ranar da ya ratsa kasar daga tekun gabas zuwa tekun yamma, a karon farko tun 1918. A garin Sisters na jihar Oregon, ranar ta leko kadan bayan wata. An dai gargadi jama’a game da hatsarin kallon kusufin da idanunsu kai tsaye.

Photographers help a Rohingya Muslim to come out of Naf River.Hakkin mallakar hoto
Hannah McKay/ Reuters

Image caption

A wannan hoton ana iya ganin masu daukar hoto na taimaka wa wata musulma ‘yar Rohingya don ta sami ficewa daga kogin Naf a hanyarta ta zuwa Bangladash daga Myanmar. ‘Yan Rohingya Musulmai ne da ba su da kasa tasu ta kansu da aka dade ana muzguna musu a Myanmar. Fiye da mutum 647,000 sun tsere zuwa kasar Bangladesh tun da rikici ya barke a watan Agusta.

Caleb Amisi Luyai, an opposition politician, reacts after a gas canister fired by policemen hits his car.Hakkin mallakar hoto
Baz Ratner/ Reuters

Image caption

Rikici ya barke a birnin Nairobi na kasar Kenya a yayin da ake kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka yi. Ana iya ganin wani dan majalisa kuma dan adawa, Caleb Amisi Luyai, yana kokarin fito da kansa waje bayan da hayaki mai sa hawaye ya turnuke motarsa bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin dakile macin da ‘yan adawar ke yi a babban birnin kasar.

North Korean leader Kim Jong Un watches the launch of a Hwasong-12 missile.Hakkin mallakar hoto
KCNA/ Reuters

Image caption

A Satumba, shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ya kalli yadda kasarsa ta harba rokar Hwasong-12. Kasar ta yi gwaje-gwajen rokoki masu linzami a yayin da kasashen duniya ke nuna damuwarsu.

Fire fighters rest during a wildfire at Penela, Coimbra.Hakkin mallakar hoto
PATRICIA DE MELO MOREIRA/AFP

Image caption

Masu kashe gobara na hutawa a lokacin da suke kokarin kashe gobarar daji a Panela na yankin tsakiyar Portugal. An sami irin wannan gobarar dajin a yankunan arewaci da tsakiyar kasar da suka zama sanadin mutuwar fiye da mutum 30 kuma gomman mutane suka sami raunuka bayan wani yanayi na zafin da rashin ruwan sama da ya shafi yankunan.

Spanish Civil Guard officers remove demonstrators outside a polling station for the banned independence referendum.Hakkin mallakar hoto
Susana Vera/ Reuters

Image caption

‘Yan sandan Spaniya na kokarin kawar da masu zanga-zanga a wata cibiyar zabe da ke birnin Barcelona a ranar da aka gudanar da zaben raba gardamar zaman yankin Kataloniya a kasar ta Spaniya. Daga baya gwamnatin Spaniya ta mayar da yankin karkashin mulkinta kai tsaye.

Ushers throw their hats in the air as they pose for photographers at the Tiananmen Square.Hakkin mallakar hoto
Thomas Peter/ Reuters

Image caption

A Beijing, babban taron kasa na jam’iyyar gurguzu ta kasar Sin ya duba batun wanda zai jagoranci kasar a wa’adin mulki da ke gaba. Shugaba mai ci Xi Jinping ya cigaba da jagorantar jam’iyyar na wa’adin shekara biyar masu zuwa, a babban taron jam’iyyar na gaba.

Bonskot Chaisuwan cries as she joins everyone in singing the Royal anthem.Hakkin mallakar hoto
Paula Bronstein/ Getty Images

Image caption

Bayan shekara guda, an kammala zaman makokin tsohon Sarkin Thailand Bhumibol Adulyadej wanda ya mutu a bara. Shi ne sarki wanda yafi dadewa a bisa karagar mulki a duniya, bayan da ya shafe shekara 70 yana mulki. Ya rasu yana da shekara 88 da haihuwa.

A migrant arrives at a naval base.Hakkin mallakar hoto
Ahmed Jadallah/ Reuters

Image caption

Wani dan ci-rani a tashar sojin ruwa a Triopli, bayan da sojin ruwa na Libya suka ceto shi daga Bahar Rum. Dubban daruruwan ‘yan ci-rani daga yankin Afirka Ta Yamma sun rika ratsa hamadar Sahara da Bahar Rum a kokarin isa Turai.

A young woman walks between tombstones.Hakkin mallakar hoto
LIANNE MILTON/ PANOS

Image caption

A kasar Guatemala, wata budurwa ke tafiya tsakanin kaburbura a yayin da ake gudanar da bikin ranar matattu a wata makabarta da ke garin. An rika yin wasanni da jiragen leda irin wadanda yara kan hada domin wai su kore muggan aljanu, ko matattun sa sami damar karbar kyaututtukan da suka kai musu.

Actor Rose McGowan raises her fist at a podium.Hakkin mallakar hoto
Rebecca Cook/ Reuters

Image caption

‘Yar fim Rose MvGowan ta dunkule hannunta kuma ta daga shi sama bayan ta gabatar da jawabi a wajen wani taro na mata a birnin Detroit, na jihar Michigan. Fitowarta ta farko kenan bayan da ta zargi babban furodusan fina-finai Harvey Weinstein da yi mata fyade. Ms McGowan na cikin mata masu yawa da suka zargi Mr Weinstein da yi musu fyade. Ya musanta dukkan zarge-zargen, inda ya ce ya kwanta da matan ne a bisa yardarsu da amincewarsu.

Shoppers reach out for television sets as they compete to purchase retail items on Black Friday.Hakkin mallakar hoto
Paulo Whitaker/ Reuters

Image caption

A wani shago da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil, mutane na rububin sayen talabijin a ranar da ake karyar da farashin kayayyaki, wacce aka fi sani da Black Friday. Wannan al’ada ta fara ne a Amurka inda a ko wacce shekara ake rage farashin kaya dab da lokacin bukukuwan kirsimeti.

Zimbabweans celebrate after President Robert Mugabe resigns in Harare, Zimbabwe, 21 November 2017.Hakkin mallakar hoto
Mike Hutchings/REUTERS

Image caption

‘Yan Zimbabwe na murnar saukar Shugaba Robert Mugabe, lamarin da ya kawo karshen mulkinsa na shekara 37. Emmerson Mnangagwa ya gaje shi bayan da aka shafe mako guda cur ana takardama game da saukarsa daga mulki, bayan kuma sojojin kasar sun kwace mulki.

A man holds a baby at the border wall between Mexico and United States, during the "Keep our dream alive" event, in Ciudad Juarez, Chihuahua state, Mexico on 10 December 2017.Hakkin mallakar hoto
HERIKA MARTINEZ/AFP

Image caption

Wani mutum ya rike ‘yarsa a jikin shingen da ke iyakar Mexico da Amurka. A ranar ‘Yanci ta Duniya, a kan kyale iyalan da iyakar ta raba su gana na minti uku a iyakar da ke Ciudad Juarez Park a Mexico da Sunland na jihar New Mexico a Amurka.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka

Manchester City ta kara fintinkau da maki 15 bayan doke Newcastle 1-0


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rabon da Manchester City ta kasa cin wasanta a Premier tun lokacin da ta yi kunnen doki 1-1 da Everton a watan Agusta

Manchester City ta kara fintinkau da maki 15 a saman teburin Premier bayan da Raheem Sterling ya ci mata kwallo daya tilo da suka doke Newcastle.

Dan wasan gaban na gefe na Ingila ya zura kwallon ne a raga a minti na 31 bayan da Kevin de Bruyne ya zura masa ita, hakan ya kawo yawan bal din da ya ci wa City a kakar nan zuwa 17.

Tun kafin sannan sai da Sergio Aguero ya kusa ci bal din tana dukan karfen raga har sau biyu.

City ta ci gaba da kafa tarihin yawan nasara a gasar ta Premier ba tare da an doke ta ba, har zuwa wasanni 18 a jere, tare da jan ragaramar teburin gasar.

Rashin nasarar ga masu masaukin bakin shi ne na biyar a jere a gida, kuma hakan ya sa maki daya ne tsakaninsu da rukunin faduwa daga Premier.

Yadda wata ‘yar Indiya ke amfani da tsiraici don nema wa mata ‘yanci


Hakkin mallakar hoto
Claudia Pajewski

Image caption

A wurin Malika Taneja, jiki makami ne babba.

Yaya zaka dauki wata mace mai kananan shekaru da ta fara wasa na kwaikwayo tsirara. A kasar kamar Indiya mai halin ‘yan mazan jiya, da wuya ka sami irin haka. Amma ga marubuciyar wasannin kwaikwayo kuma ‘yar wasan na kwaikwayo, jikinta shi ne makami babba da take amfani da shi wajen samar wa mata ‘yanci. Ta fada wa Ayeshea Perera ta BBC abin da ke bata karfin gwuiwa.

“A lokacin da na fara yin wasa tsirara a bainar jama’a …na ji dadina.

“Akwai wani mai daukan hoto a wurin, kuma idan kika kalli bidiyonsa zaki ga wani wuri a ciki inda hoton yayi tsalle bayan da aka kunna hasken lantarki saboda faduwa da baya yayi a sanadiyyar gani na tsirara. Kuma can sai wani dan kallo ya ce ‘Aiyo!’,” inji Malika Taneja, tana dariya.

Duk da yake wannan ne abin da mutane suka fi yin magana akai, amma ‘yar shekara 33 da haihuwar ta ce ba shi ne dalilin yin wasan da take yi ba.

Wasan me suna Thoda Dhyan Se (wato A dan yi a hankali) wasa ne da take so ya sosa zukatan mutane game da ko irin kayan da mata ke saka wa na da nasaba da harin da ake kai musu.

Hakkin mallakar hoto
Claudia Pajewski

Image caption

Wasanninta na neman sanin ko sanya kaya na da nasaba da kai wa mata hari

“Yaya ake watsa taron mutane? Bijirewar mutum guda kawai ake bukata”.

Ta ce, “Mutum guda na iya shiga tsakiyar jama’a ya kuma dakatar da ita.”

A wani wasa da ta shirya – inda ta fito tsirara tana kallon ‘yan kallonta na tsawon minti takwas – misali ne na yiwuwar hakan.

A kowane wasa da ta shirya a shekaru hudu da suka gabata, ta ce masu kallo kan yi tsit a mintunan farko, shirun da “kan cika dakin.”

A wannan lokacin da Ms Taneja ke kallon da masu kallonta, ta kan lura duk da cewa an fi ta yawa, amma ta fi su karfi a lokacin.

Amma yin wasa tsirara na damunta sosai. Ba ta barin a shiga da wayoyin hannu ko wani abin daukar hoto cikin wurin da take wasa. Kuma a shekaru hudun da ta dauka tana wasa, ba a taba samun hoto ko bidiyo daya da ya nuna tsiraicinta ba.

Bayan da wasan ya cigaba, Ms Taneja kan saka wasu kaya a jikinta, har ma ta kan saka hular kwano, inda ta ke sanar da masu kallonta cewa a matsayinta na mace, dole ta “yi taka tsantsan”.

Hakkin mallakar hoto
Claudia Pajewski

Image caption

Maza masu yawa sun bayyana wasannin Ms Taneja abin bude idanu

Ta kara da cewa: “Mata sun fahimci dalilin wannan wasan nawa, amma yana da muhimmanci da maza suka ce ya bude musu ido.”

Dalilanta na yin wannan wasa ita kadai sun hada da irin rayuwar da ta ke yi ne. Ms Taneja ba ta da miji, ita kadai take zaune a gidanta, kuma bata aiki irin na yau da kullum – wato irin wanda ake farawa daga karfe 9 na safe zuwa karfe 5 na yamma.

Ta yarda cewa nasarar da ta samu, da kuma kudaden da take da su sun taimaka wajen bata karfin zuciyar ci gaba da yin wasannin.

“Babu wanda ya taba sukar yadda nake tafiyar da rayuwata – ko babana, ko ‘yan uwana,” inji ta.

Hakkin mallakar hoto
Claudia Pajewski

Image caption

Ms Taneja bata da aiki irin na yau da kullum, kuma ita kadai take zama a gidanta

Idan mace ta ce a’a ko sau daya ne, to lallai ta bada gudummuwarta wajen samun daidaito tsakanin jinsuna.

In 2012, India saw that happen. The horrific Delhi gang rape prompted hundreds of thousands of women to come out on to the streets, shouting that they had put up with enough. India’s tough new rape laws and a complete change in the way rape was reported and talked about, were direct consequences of that anger.

A 2012 kasar Indiya ta shaida haka. Wani lamari na fyade da aka yi wa wata mata ya zaburad da dubban mata, inda suka fito suna cewa sun gaji da wannan halayya. Bayan wannan fitowar ce aka sami sauyi wajen sabbin dokoki da kasar ta kaddamar domin maganin lamarin.

Hakkin mallakar hoto
Claudia Pajewski

Image caption

Ms Taneja na gudanar da kamfe domin kare wadanda aka yi wa fyade.

Amma wasu mata na ganin ba zata iya wadannan wasannin ba ma sam-sam da tana da kiba.

Sai ta ce “Ban san amsar wannan maganar ba. Wannan jikin shi ne nawa. Amma zan gaya musu cewa ‘Ina fata’.

Wannan labarin na daga cikin jerin labarai game da matan Indiya masu yakin kawo daidaito tsakanin jinsuna.

Virgil van Dijk: Liverpool ta sayi dan wasan Southampton akan £75m


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Liverpool ta sayi Virgil Van Dijk daga Southampton

Dan wasan Southamton Virgil van Dijk zai koma Liverpool ranar 1 ga Janairu da zarar an bude kasuwar cinikin ‘yan wasa a kan fam miliyan 75.

Tun bara ake sa ran dan wasan dan asalin Holland zai koma Liverpool bayan da shi da kansa ya nemi a sayar da shi.

Amma hakan bai yiwu ba saboda an tuhumi Liverpool da zawarcin dan wasan ba tare da sanin kungiyar shi ba.

Kudin da za a biya Southampton ya fi na kowane dan wasan baya da aka taba saya a duniya.

Benjamin Mendy da Manchester City ta biya Monaco fam miliyan 52 a watan Yuli shi ne dan wasan baya mafi tsada kafin cinikin Dijk.

Van Dijk ya ce yana alfaharin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallo a duniya.

A wata sanarwa da ya fitar, Van Dijk ya bayyana farin cikin komawa Liverpool.

“Ina matukar farin cikin komawa Liverpool a matsayin dan wasa. Yau rana ce ta alfahari a gare ni da iyalina a yayin da na ke shirin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya.”

“Na zaku da in saka jar rigar wasan Liverpool da ta shahara a karon farko a filin wasan Kop, kuma na yi alkawarin sadaukar da kai na wajen taimakawa wannan kungiyar cimma burinta a shekaru masu zuwa.”

‘Mutum miliyan 30 na fuskantar barazana a yankin Tafkin Chadi’


Hukumomi na kasashen yankin Tafkin Chadi na ci gaba da nuna damuwa kan yadda tafkin ke ci gaba da kankancewa cikin shekarun baya-bayan nan inda suka ce adadin ruwan ya ragu da kamar kashi 90 cikin 100 duk da muhimmancin da ya ke da shi ga miliyoyin mutane.

Don haka ne kasashen yankin su shida tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanar da wani taro a Nijeriya, irinsa na farko a tarihi, cikin watan Faburairu da ke tafe da nufin nemo hanyoyin hana tafkin bacewa baki daya.

Ishaq Khalid ya tuntubi Alhaji Sanusi Imrana Abdullahi, shi ne Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Yankin Tafkin Chadi domin jin karin bayani kan halin da tafkin ke ciki.

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin jin hira da Alhaji Sanusi Imrana Abdullahi:

Dan Shugaba Buhari ya karye a hatsarin babur


Hakkin mallakar hoto
Twitter/yusuf buhari

Image caption

Yusuf shi ne da namiji kadai da Aisha Buhari ta haifa

Yusuf Buhari, dan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi mummunan hatsarin babur din tsere a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin ranar Talata da daddare.

A cewar Garba Shehu, “Ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki”.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari da mai dakinsa Aisha suna godiya ga ‘yan Najeriya bisa addua’ar da suke yi wa dan nasu.

Mbappe ya ce ya tattauna da Real Madrid


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mbappe shi ne na bakwai a kyautar Ballon d’Or wacce Ronaldo ya lashe

Dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe ya ce ya tattauna da wakilan Real Madrid kan batun zuwa can da murza-leda kafin ya koma Paris Saint-Germain a bana.

An bayar da rahoton cewar Real Madrid ta yi zawarcin Mbappe, bayan da ya jagoranci Monaco ta ci French Lik, bayan shekara 17 rabonta da kofin, amma ya amince da zuwa PSG aro a watan Agusta.

Mbappe ya ce ”Anyi ta rade-radin zuwa na Real Madrid, kuma gaskiya ne na tattauna da wakilan kungiyar, amma yanzu batun ya wuce babu maganar komawa Spaniya”.

A hirar da Marca ta yi da dan kwallon a ranar Laraba ya ce ”Ni dan wasan PSG ne yanzu haka, zan kuma ci gaba da kare martabar kungiyar dari bisa dari”.

Mbappe wanda ya cika shekara 19 da haihuwa a makon jiya ya kara da cewar ya amince ya buga wa PSG tamaula ne saboda Paris garin shi ne.

Yaya Toure ya yi amai ya lashe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Toure ne kyaftin din tawagar Ivory Coast a lokacin da ta lashe kofin nahiyar Afirka a 2015

Dan wasan Manchester City, Yaya, Toure zai koma buga wa tawagar kwallon kafa ta Ivory Coast tamaula.

Dan kwallon mai shekara 34, ya yi ritaya daga buga wa kasar kwallon kafa a Satumbar 2016, bayan da ya yi mata wasa 100, sannan ya lashe kofin nahiyar Afirka a 2015 a tawagar.

Toure ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na Twitteer cewar ”Ina kyaunar kasata kuma a shirye nake na buga mata tamaula”.

”Ina son na taimakawa matasa da irin kwarewar da nake da ita, ta yadda Ivory Coast za ta yi alfahari da hakan”.

Toure, wanda ya koma Manchester City daga Barcelona a 2010, ya buga wa kungiyar da ke murza-leda a Ettihad wasa uku a gasar Premier a bana.

Ivory Coast ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 ba, amma tana shirin fara buga wasannin kai wa gasar kofin nahiyar Afirka a watan Maris.

Obama ya yi gargadi kan amfani da shafukan zumunta


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Barack Obama ya bayyana yadda ya ji game da shirin Donald Trump na korar baki

Tsohonshugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi gargadi a kan amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ta yadda ya dace ba, a wata hira da ba safai yakan yi ba tunda ya sauka daga mulki a watan Janairu.

Ya ce yin amfani da shafukan ba yadda ya dace ba yana gurbata tunanin mutane kan al’amura masu sarkakiya, da kuma yada labaran karairayi.

Mutumin da ya gaje shi, Donald Trump, ya shahara wurin yin amfani da Twitter, ko da yake Mr Obama bai ambaci sunansa a hirar ba.

Yarima Harry ne ya yi hira da tsohon shugaban kasar a madadin shirin Radio 4 na BBC.

Yariman, wanda shi ne na biyar a cikin jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniya, na cikin masu gudanar da shirye-shirye a shirin Radio 4 tsawon lokacin bukuwan Kirsimeti.

Tsohon shugaban kasar ya kuma bukaci masu rike da madafun iko su rika yin takatsantsan kan irin sakonnin da suke wallafawa a shafukan zumunta, yana mai cewa shafukan na kawo matsala game da rayuwar jama’a.

Mr Obama ya bayyana taiakcinsa kan yadda ake maye gurbin labarai na gaskiya da labaran kanzon-kurege, da kuma yadda mutane ke karanta ko saurarar abin da kawai zai gamsar da ra’ayinsu ba tare da tantance sahihancinsa ba.

Matar da aka nemi ta biya $284bn a matsayin kudin wutar lantarki


Takardar biyan kudin amfani da wutar lantarkin da ta kai $284bn da aka aike wa wata mata a jihar Pennsylvania ta ba ta matukar mamaki… har sai da ta gano kuskure aka yi sannan hankalinta ya kwanta.

Mary Horomanski ta ce takardar ta nuna cewa dole ta biya kudin kafin karshen watan Nuwambar shekarar 2018.

“Lamarin ya firgita ni sosai,” in ji matar, a hirar da ta yi da jaridar Erie Times-News. “Mun kunna wutar lantarki ta bikin Kirsimeti kuma mun yi zaton mun kunna ne bisa kuskure.”

Daga bisani kamfanin samar da hasken wutar lantarkin ya ce $284.46. ne hakikanin kudin da ya kamata matar ta biya.

Kakakin kamfanin ya ce bai san yadda aka tafka wancan kuskuren ba, yana mai cewa ba don an gano kuskuren ba da sai Ms Horomanski ta $284,460,000,000 inda za ta soma biyan $28,176 a matsayin kashin farko a watan nan na Disamba.

” Ban taba ganin an aike wa wani ko wata takardar kudin wuta da ta kai ta dala biliyan daya ba,” in ji Mark Durbin a tattaunawarsa da Erie Times-News.

“Mun ji dadin yadda matar ta tuntube mu bayan ta ga takardar da aka aike mata bisa kuskure.”

Ivory Coast: An yanke wa tsohon minista zaman sarka na shekara 22


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hubert Oulaye tsohon na hannun daman Laurent Gbagbo ne

An yanke wa tsohon ministan Ivory Coast Hubert Oulaye hukuncin shekara 22 a gidan Kaso, bayan samunsa da hannu a kisan mutane 18 ciki har da dakarun wanzar da zaman lafiya 7 na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2012.

Babban lauyan gwamnatin kasar ya ce Mista Oulaye wanda shi ne ministan yada labarai na lokacin mulkin Shugaba Laurent Gbagbo, ya samar da wata kungiyar ‘yan tawaye tare da ba ta kudade a yammacin kasar.

Sai dai tsohon ministan ya musanta tuhumar da cewa an yi ta ne kawai domin kawai a bata masa suna, sannan lauyansa ya ce za su daukaka kara a kan hukuncin.

Harin na shekarar 2012 ya faru ne a daidai lokacin da Ivory Coast ke kokarin farfadowa daga tashin hankalin da aka yi bayan zaben Shugaba Gbagbo ya ki amincewa da shan kaye bayan sanar da Alassane Ouattara a matsayin sabon shugaban kasa.

Syria: ‘Za a kai marasa lafiya asibiti a Damascus’


Image caption

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta wallafa hoton motar daukar marasa lafiya na jiran daukar yaran zuwa asibiti, a shafukan sada zumunta na internet

Jami’an agaji da ma’aikatan sa kai na Syria sun fara kwashe marasa lafiyar da ke cikin mawuyacin hali daga wani yanki da ‘yan tawaye ke iko da shi a kusa da birnin Damascus.

Ma’aikatan agaji na kasashen waje sun roki shugaba Basharul-Assad na Syria ya taimaka dan a kwashe wasu yara bakwai da ke cikin mawuyacin hali da kuma su ke dauke da cutar Cancer.

Kungiyar agaji ta kasashen larabawa wato Red Crescent ta wallafa wasu hotuna a shafin tweeter na wasu yara da iyayensu cikin yanayi na rai kwa-kwai mutu kwa-kwai, su na jiran a kwashe su zuwa asibiti a birnin Damascus.

Mai magana da yawun kungiyar Red Cross a Geneva, Anastasia Isyuk ta ce babu wasu bayanai da aka yi na karin haske kan lamarin.

Sai dai ta ce tabbas an cimma matsaya tsakanin wadanda ke rikici da juna, kuma halin da marasa lafiya ke ciki a yankunan da ‘yan tawaye suke iko da shi ya munana.

Babu isasshen abinci, ko ruwan sha ko magani a asibitocin da ke yankin Ghouta. Tun a farkon wannan shekara ne ‘yan tawaye da ke yaki da shugaba Assad suka karbe iko da garin wanda ke kusa da birnin Damascus.

Sama da shekara 5 kenan da fara yakin na Syria, bayan guguwar juyin-juya hali ta kada a kasashen gabas ta tsakiya inda ta kawo karshen mulkin wasu daga cikin shugabannin kasashen yankin wasu kuma aka hallaka su, kamar Mu’ammar Gaddafi na Libya, da Saddam Hussain na Iraqi.

An kakabawa jami’an Koriya ta Arewa takunkumi


Image caption

Amurka ta ce manyan jami’an biyu, su na taka mhummiyar rawa a shirin shugaba Kim Jong-un na tada zaune tsaye kan gwajin makamai masu linzamin da wasu kasashen duniya ke kallon tsokanar fada ce.

Gwamnatin Amurka ta kara sanyawa wasu manyan jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu su biyu takunkumi, saboda rawar da suka taka a shirin samar da makami mai linzami a kasar.

A makon da ya gabata ne dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da sunayen jami’an, a lokacin da ta Majalisar ke zama na musamman.

Rahotanni sun ce Kim Jong-Sik ya taka rawa wajen samar da makami mai linzami wanda ke aiki da sinadarai masu karfi kamar dutse ba ta hanyar amfani da sinadari masu ruwa ba.

Shi kuwa Ri Pyong-chol an same shi da bai wa kasar kwarin gwiwar samar da wasu makamai masu linzami manya da kanana ne fita a jikinsu ya yin da aka harba shi.

A nata bangaren Rasha ta gargadi Amurka da ta guji matsawa Koriya ta Arewa lamba, dan kaucewa wani rikicin, ya yin da ta maimakon takalar fada kamata ya yi a sanya lokacin tattaunawa dan magance rikici tsakanin kasashen biyu.

Tun da fari, Shugaban Amurka Donald Trump ya jinjina wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri.

A wani sako da ya rubuta a shafinsa na twitter, Mr Trump ya ce hakan ya jaddada cewa duniya na bukatar zaman lafiya ne ba kashe-kashe ba.

A cewar Amurka, Koriya ta Arewa ta shigar da gangar tattacen man fetur miliyan 4 da rabi a shekarar 2016.

Barayin PDP ne suka kafa gwamnatin APC – Sule Lamido


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Duk masu cewa ‘yan PDP barayi ne, to ai ga shi nan ai barayin ne suka je suka yi cikin wannan gwamnatin har aka samar da ‘yar barauniya, in ji Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba ya fargabar dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar jam’iyyar PDP, za ta kawo cikas a burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2019.

Sule Lamido ya fadi hakan ne a wata hira da suka yi da Haruna Tangaza na BBC, inda ya ce yana maraba da dawowar Atiku PDP don dama can jam’iyyar ce ta haife shi.

“Abun da aka yi wa Atiku Abubakar na daukaka da karamci a PDP ai ba a yi masa irinsu a APC ba, don haka mene ne laifi don ya dawo gida?” In ji Suke Lamido.

Da yake Sule Lamido ya jima da bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takara a inuwar jam’iyyar PDP, sai Haruna Shehu Tangaza ya tambaye shi shin ko dawowar Atikun ba ta dagula masa lissafi ba?

“Babban burinmu PDP ta tsayar da dan takara nagari wanda ‘yan Najeriya ke so, don haka babu wani abun damuwa, a takaice ma so nake duk ‘yan PDP da suka fice to su dawo, tun da dai Atiku ya dawo,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “So nake duk su Wamakko su Kwankwaso su AbdulFatah su Saraki su Abdullahi Adamu, kuma na tabbata duk za su dawo. Ya kamata a gane cewa su wadannan mutanen duk sun samu sunansu da kwarjininsu a PDP ne.

“Komawarsu APC cin mutuncinsu ne, wulakantasu ne kuma cin mutuncin tarihinsu ne”.

‘Atiku Abubakar zai kawo rigima a PDP’

PDP ba za ta bai wa Atiku takara ba sai…

Mutum miliyan uku sun rasa aiki a lokacin Buhari — Atiku

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Abun da aka yi wa Atiku Abubakar na daukaka da karamci a PDP ai ba a yi masa irinsu a APC ba, in ji Sule Lamido

Sule Lamido ya kuma mayar wa jam’iyyar APC martani a kan yadda take cewa duk ‘yan PDP masu cin hanci da rashawa ne, inda ya ce duk barayi da kazaman jam’iyyarsa ta PDP ne suka kafa gwamnatin jam’iyyar APC.

“An shafe shekaru jam’iyyar APC na takara a kasar amma ba ta samu nasara ba sai da “wadannan barayi kazaman ‘yan PDP suka koma suka yi wa APC ciki, sannan aka haifi gwamnatin APC ta yanzu.”

“Duk masu cewa ‘yan PDP barayi ne, to ai ga shi nan ai barayin ne suka je suka yi cikin wannan gwamnatin har aka samar da ‘yar barauniya. Don haka don da ya zagi uwarsa mene ne laifi?” a cewar Sule Lamido.

Ya kara da cewa yana mamakin yadda don kawai a baya mutum yana jam’iyyar PDP sai ya koma APC sai a dinga ganin kamar ya zama wani waliyyi.

“Ga misali lokacin da Atiku yake APC duk an yi shiru, amma yanzu da ya dawo PDP sai aka aka fara zaginsa.

“A tsarin ‘yan APC babu siyasa sai fushi da gilla da cin mutunci babu maganar sanin kasa.”

Dawowar Atiku Abubakar jam’iyyar PDP dai a baya-bayan nan, ta sa masu sharhi na ganin za a kai ruwa rana tsakaninsa da Sule Lamido don a bayyane take cewa Atikun ya koma jam’iyyar ne domin neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019.

Harry Kane ya wuce Messi da Alan Shearer bayan da Tottenham ta casa Southampton 5-2


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Harry Kane ya zama dan kwallon da ya fi cin bal a Turai a shekarar 2017

Harry Kane ya zura kwallo uku rigis, ya kuma kawar da tarihin bajintar cin kwallo mafi yawa a Premier a cikin shekara bayan da Tottenham ta caskara Southampton a Wembley 5-2.

Dan wasan na gaba na Tottenham da Ingila ya ci bal dinsa ta 37 a Premier a wannan shekara ta 2017 a minti 22 da wasa, ya wuce bajintar da Alan Shearer ya yi, lokacin yana Blackburn a 1995.

Daga nan ne kuma Kane din ya kara biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci a minti na 39 sannan kuma bayan an dawo ya ci ta uku a minti na 67, abin da ya kawo jumullar yawan kwallon da ya ci wa kungiyarsa da kasarsa a shekarar nan zuwa 56, inda ya zarta dan wasan gaba na Barcelona da Argentina Lionel Messi da kwallo biyu.

Kafin kane ya ci bal ta uku Dele Alli shi ne ya ci wadda ta sa wasan ya zama 3-0 a minti na 49.

Minti biyu bayan wannan ne kuma sai ya ba wa Son Heung-min wanda shi ma ya kwarara tasa a raga a minti na 51.

Southampton, wadda ta kasance ba tare da gwanin ci mata kwallo ba Charlie Austin, ta farfado lokacin da Sofiane Boufal ya ci mata daya a minti na 64.

Sannan kuma Dusan Tadic ya kara ci mata ta biyu ana minti 82 da wasa bayan da dan wasan ya sheko bal din da ta wuce golan Tottenham Hugo Lloris.

Daga nan kuma bakin ba su kara daga raga ba, abin da ya sa yanzu suka kai wata daya ba tare da sun ci wasansu ba a gasar ta Premier.

Yanzu Tottenham ta tsaya a ta biyar a tebur bayan da Liverpool wadda ta jaddada zamanta a matsayi na hudu bayan da ta lallasa bakinta ‘yan Swansea 5-0 a wasan na Talata.

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Roberto Firmino ya ci biyu daga cikin bal biyar din da Liverpool ta zura a ragar Swansea

Sakamakon sauran wasannin Premier na Talata:

Bournemout 3-3 West Ham

Chelsea 2-0 Brighton

Huddersfield 1-1 Stoke

Man Utd 2-2 Burnley

Watford2-1 Leicester

West Brom 0-0 Everton

A ranar Laraba 27 ga watan nan na Disamba Newcastle United za ta karbi bakuncin jagora a gasar ta Premier Manchester City, inda za su fara karawar da misalin karfe 8:45 agogon Najeriya.

Saudiyya ta hana ‘yan Isra’ila iznin shiga kasarta yin gasar dara


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An fara gasar wasan dara ta duniya ta Rapid and Blitz Chess a Riyadh da ce-ce-ku-ce

An fara gasar wasan dara ta duniya a Saudiyya da ce-ce-ku-ce, bayan da kasar ta hana ‘yan wasan Isra’ila izinin zuwa.

Wani jami’in Saudiyya ya ce ba za a iya bai wa ‘yan Isra’ila izinin shiga kasar ba saboda babu wata alakar diflomasiyya tsakanin masarautar kasar da Isra’ila.

Hukumar Wasan Dara ta Isra’ila ta ce za ta nemi a biya ta diyyar kudi.

Ana ganin karbar bakuncin wannan gasa da Saudiyya ta yi a matsayin budewa kanta wata hanya ta yin mu’amala da sauran kasashen duniya sosai.

Amma ‘yar wasan da ke rike da kambun gwarzuwa ta duniya ta ce ba za ta je gasar ba saboda ba ta son sanya abaya, wato riga mai tsawo da mata ke sawa kafin su fita bainar jama’a a Saudiyya.

Anna Muzychuk mai shekara 27 wadda ke yi wa kasar Ukraine wasa ta ce, “duk da irin makudan kudin da za a bai wa wanda ya yi nasara, ni ba zan je Riyadh wannan wasa ba,” ko da hakan na nufin ta rasa kambunta biyu da take rike da su.

Gasar Dara ta kungiyar Sarki Salman ta Rapid and Blitz Chess, ta sanya kyautar dala 750,000 a wasan bude gasar, da kuma dala 250,000 a gasar mata.

Ta yi rubuta a shafinta na Facebook inda take ba da misali da wata gasa ta duniya da aka yi a Tehran babban birnin Iran a farkon shekarar 2017, kamar haka: “Na yi ta sa rayuwata a hadari ina sanya abaya ko yaushe? Komai yana da makura, dankwalin da na sanya a Iran ma ya ishe ni.”

A wani rubutun kuma da ta yi a ranar 23 ga watan Disamna cewa ta yi duk da cewa za ta ji bacin ran rasa kambunta, hakan ba zai hana ta tsayawa a kan ka’idojinta ba.

Ms Muzychuk ta nuna wannan kin amincewar ne a lokacin da ake samun karuwar mayar da hankali kan ‘takurar’ da mata ke fuskanta kan ‘yancinsu a Saudiyya.

A yayin da aka dage dokar haramtawa mata tukin mota daga tsakiyar shekara mai kamawa, masu fafutuka sun ce kasar na da sauran aiki a gabanta wajen inganta daidaton jinsi da hakkin dan adam.

Mai rike da kambun wasan dara na uku a duniya dan kasar Amurka Hikaru Nakamaru, ya ce yanke shawarar yin wannan gasa a Saudiyya ‘abun tsoro ne.’

A yayin da ‘yan wasa bakwai daga Isra’ila ba za su samu damar halartar wasan ba bayan hana su izinin shiga kasar da hukumomin Saudiyya suka yi, ‘yan wasan Qatar da Iran za su samu damar zuwa bayan da aka ba su izinin shiga a kurarren lokaci, duk kuwa da irin lalacewar da dangantaka ta yi tsakanin kasashensu da masarautar Saudiyyar.

Hukumar Dara ta Isra’ila ta ce da fari ta yi amannar cewa za a bar ‘yan wasanta su shiga, duk da cewa babu dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Ta soki Saudiyya da yi wa Hukumar Dara ta Duniya rufa-rufa don ta samu damar karbar bakuncin gasar.

An kafa dokar takaita zirga-zirga a Bwarin Abuja


Image caption

Wutar da aka cinna wa kasuwar Bwarin dai ta kone dukkan shagunan da ke cikin kasuwar

An kafa dokar takaita zirga-zirga a garin Bwari da ke babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, kwana daya bayan wani rikici mai nasaba da kabilanci ya haddasa salwantar rayuka da kadarori.

An kafa dokar takaita zirga-zirgar ne daga karfe shida zuwa shida yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum uku a hukumance sakamakon rikicin.

Duk da cewa hukumomi ba su fayyace iya abin da aka rasa a kasuwar garin da aka cinna wa wuta ba, abokin aikinmu Abdulwasiu Hassan da ya ziyarci garin na Bwari, ya ce an kone kasuwar garin da kuma wasu shaguna ciki har da shagunan da ke gefen reshen bankin Zenith na garin.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci kasuwar garin, ya tarar da masu shaguna suna neman dan abin da za su iya samu daga cikin shagunansu wadanda galibinsu sun kone kurmus.

Mallam Ibrahim Saidu ya shada wa BBC cewa, yana kokarin tsamo buhunhunan shinkafar da ba su gama konewa daga shagon dan uwansa ne.

Hakkin mallakar hoto
Abdulwasiu Hassan

Image caption

Masu shaguna da sauran mutane sun fito domin ganin abin da ya faru a garin Bwari da safiyar Talata

Mallam Ibrahim ya ce dan uwansa mai shagon ya rasa shagunan sayar da kayan abinci da wuta ta kone a kasuwar.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da shagonsa ya kone, Godwin Onah, ya ce ya rasa naira miliyan biyar a shagonsa.

Godwin ya ce: “Ina cikin gida ina shan bukin Kirstimeti, sai wani ya kira ni a waya ya ce kasuwar Bwari na ci da wuta.

“Da muka isa wajen wancan gidan man, sai aka ce an toshe hanya. An hana mutane isa ga kasuwar.

“Da safiyar yau Talata da na zo na ga komai ya kone. Ban samu komai ba. Ban tsira da ko allura ba daga shagona, ko allura daga cikin kayayyakin nake sayarwa.

“Kayayyakin da na rasa a cikin shagon tare da cinikin da na yi na lokacin Kirsimeti ya kai naira miliyan biyar,” in ji Onah.

A lokacin da ake hada wannan rahoton dai sojoji da ‘yan sanda na ci gaba da sintiri a garin na Bwari.

Image caption

Masu shaguna da dama sun yi ta kokarin neman abin da za su iya samu daga tarkacen shagunansu

Hotunan yadda ake lullube giwaye da bargo don maganin sanyi


Ana zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Liberia


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ofishin hukumar zabe ta Liberiya a birnin Monrovia

A yau Talata ne ne ake zaben shugaban kasa a Liberia zagaye na biyu.

‘Yan takara biyu ne dai za su fafata a zaben wanda shi ne karon farko da kasar ke shirya zabe don mika mulki daga wata sabuwar gwamnati zuwa wata tun bayan yakin ba-sa-sar kasar.

Mataimakin shugaban kasar mai ci Joseph Boakai da kuma shahararren tsohon dan wasan kwallon kafan nan George Weah sune ke fafata wa.

Wasu dai na ganin hukumar zaben Liberia ta yi gaggawar sake shirya zaben zagaye na biyu kafin shekarar ta kare.

Sai dai a hira da BBC, tsohon shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce hukumar zaben ba ta yi gaggawar shirye zaben ba.

Mr Jonathan wanda ke jagorantar tawagar masu sa ido daga cibiyar bukansa demukradiyya ta National Democratic Institute, ya ce Liberia tana da kalubale da dama na yadda shugaban kasa mai ci za ta mika mulki ga zababben shugaba.

Ya kara da cewa hakan zai nuna wa duniya cewa mulkin demukradiya a ya kafu sosai a Liberia kuma abun daya rage shi ne a bunkasa tattalin arzikin kasar.

Nigeria: Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN ARMY

Image caption

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile wani hari da ‘yan kungiyar BokoHaram su ka yi yunkurin kai wa a birnin Maiduguri a ranar Kirsimeti.

Kwamandan rundunar sojojin ta Lafiya Dole a yankin arewa maso gabashin kasar Major Janar Nicholas Rogers shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa.

Ya ce dakarun sojin sun yi bata kashi da masu tayar da kayar bayan da suka farma wani wurin binciken ababen hawa na sojoji da ke wajen birnin a cikin motocin a kori kura.

Janar Nicholas Rogers ya ce an kwashe sama da awa guda ana artabu tsakanin mayakan da sojoji.

Sanarwar ta ce babu asarar rayuka sai dai a lokacin da maharan ke tserewa sun kona wasu motoci biyu da wasu gidaje da ke kusa.

Hukumomi a birnin Maiduguri sun ce an kara tsaurara matakan tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

‘Yan Kannywood sun zama dankali sha kushe’


Hakkin mallakar hoto
Instagram/HADIZAN SAIMA

Image caption

Hadiza ta fito a fim sama da dari uku

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun zama abin nan da Hausawa ke cewa dankali sha kushe.

“Allah yana kallon abin da muke yi; idan muna yi don mu bata ko mu gyara mu fadakar, Allah ya sani.

“A cikin fina-finan da muke yi ana yin karatun Al-Qur’ani, ana jan baki a fassara, ana ce wa ‘Allah ya ce, Annabi ya ce’. Shi ma duk wannan koya rashin tarbiyya ne?”, in ji Hadiza, lokacin da take amsa tambayar da BBC ta yi mata kan zargin bata tarbiya da ake yi wa ‘yan fim.

Ta kara da cewa: “Ka san mu dankali ne sha kushe, ana sonmu ana kushe mu. Amma haka za mu yi ta tafiya tun da haka Allah ya yo mu.

“Haka za a yi ta hakuri da mu, mu ma muna hakuri da masu kushe mu kuma a hankali za su fahimce mu. Na san wasu ma sun fahimta yanzu.”

Jarumar, wacce akasari ta fi fitowa a matsayin uwa, ta kara da cewa ta soma sha’awar fina-finai ne tun lokacin da take da aure.

A cewarta, “Karance-karancen littafai da kallon fina-finan tarihi ne suka sa na soma sha’awar shiga fim.

“Na kalli fim din ‘Ki Yarda Da Ni’ a lokacin ina gidan mijina, kuma da aurena ya zo karshe sai na ji sha’awar shiga fim. Na soma fim ne sama da shekara 16 da suka wuce kuma na fito a fim fiye da 300.”

“Wani darakta ne marigayi Tijjani Ibrahim ya tambaye ni irin rawar da na fi so na taka a fim, ni kuma na ce masa na fi son fitowa a matsayin uwa.

“Shi ya sa tun daga wancan lokaci nake fitowa a matsayin uwa, tun ma ina da kuriciya ake yi min kwalliya irin ta uwa domin na taka irin wannan rawar.”

Hakkin mallakar hoto
INSTAGRAM/HADIZAN SAIMA

Image caption

Hadiza (ta farko daga dama) ta shaku sosai da Saima (ta tsakiya)

Yawan marasa aiki ya karu a Nigeria – Rahoto


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masana tattalin arziki sun yi imani cewa, karancin hada-hadar kasuwanci da kuma rasa ayyuka na nufin iyalai da dama na fafutukar yadda za su rayu

Wani sabon rahoto ya ce yanayin rashin aikin yi ya kara tabarbarewa a Najeriya, inda marasa aiki suka kai miliyan 17 a bana daga miliyan 13 a 2016.

Rahoton, wanda Hukumar Kididdiga ta kasar NBS ta fitar, ya bayyana cewa tabarbarewar tattalin arziki da aka yi fama da ita zai iya zama babban abun da ya munana lamarin, kuma za a iya shafe shekara daya kafin yanayin ya sauya.

Ya kuma kara da cewa rashin aikin yi ya karu da kashi biyar cikin 100.

Rahoton ya yi hasashen cewa za a dauki tsawon wata hudu zuwa takwas ba tare da an samu sauyi ba, kafin tattalin arzikin kasar ya kara farfadowa.

Sharhi dags wakilin BBC Chris Eworkor

Ga alama wannan rahoto na bayyana abun da yake a zahiri ne.

Faduwar farashin man fetur da kuma rashin samun kudin shiga sun sa gwamnati na fafutukar ci gaba da biyan ma’aikatanta.

A yayin da ake samun sabbin wadanda suka kammala karatu masu neman aiki, a wannan lokaci ne kuma kamfanoni masu zaman kansu da masana’antu suke rage yawan ma’aikatansu.

Masana tattalin arziki sun yi imani cewa, karancin hada-hadar kasuwanci da kuma rasa ayyuka na nufin iyalai da dama na fafutukar yadda za su rayu.

An gano gawar wani alkali da aka sace a Saudiyya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alkalin, dan shi’a ne tsiraru da ke Awamiya a kasar Saudiyya da ke korafin cewa ‘yan sunna masu rinjaye sun mayar da su saniyar ware.

‘Yan sandan Saudiyya sun ce sun gano gawar wani alkalin da aka sace shekara daya da ta wuce.

An gano gawar Sheikh Mohammed al-Jirani ne bayan wani artabu a makon da ya wuce tare da wasu da ake zargin ‘yan gwagwarmaya ne a wata gona a gabashin kasar.

Alkalin, dan shi’a ne tsiraru da ke birnin Awamiya a kasar Saudiyya da ke korafin cewa ‘yan sunna masu rinjaye sun mayar da su saniyar ware.

Sheikh Jirani dai ya sha sukar zanga-zangar da ‘yan shi’a ke yi, kuma ya zargi manyan malamai a cikin al’ummar shi’a din da kasancewa kut-da-kut da Iran.

A watan Disambar 2016 ne aka sace Sheikh Mohammed al-Jirani a gaban gidansa da ke birnin Awamiya.

A wancan lokacin hukumomi sun ce sun kama mutum uku da ake zargi da hannu a sace shin.

Kafofin yada labaran kasar sun ce dama an sha hakon alkalin a wasu hare-hare da aka sha kai wa kafin daga bisani a sace shi.

Labaran da suka fi burge masu daukar hoto a Afirka a 2017


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Ya ya za ku ji idan ku ka dauki hotunan wasu lokuta da manyan labarai suka faru a Afirka a shekarar 2017?

Wasu masu daukar hoto hudu sun gayawa BBC wani abu kan hotunan da suka fi so wadanda suka dauka a wannan shekarar.

Fitar farin dango (Hoton da ke sama)

Mike Hutchings shi ne babban mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Reuters a Kudancin Afirka. Mazaunin birnin Cape Town na Afirka Ta Kudu ne, ya yi bulaguro zuwa Zimbabwe a watan Nuwamba don yin labari a kan kwace mulkin da sojoji suka yi daga hannun Shugaba Robert Mugabe.

Tun safiyar ranar Mista Hutchings ya yi ta daukar hotuna a wajen majalisar dokokin kasar yayin da ‘yan majalisar ke tattauna batun tsige Shugaba Mugabe.

Bayan ya gama daukar hotunan, sai ya yanke shawarar yin dan tattaki a wajen ginin majalisar a karo na karshe.

Yana tsayawa don neman tasi ne sai wani abokin aikinsa ya yi masa waya ya shaida masa cewa Shugaba Mugabe ya yi murabus.

Nan da nan sai Hutchings ya ruga kan titin da kamararsa inda ya ji ihun mutane, wadanda suka yi fitar farin dango don nuna murnarsu, shi kuwa sai ya dauki hotonsu.

Ya bayyana cewa: “Ina son yadda mutanen suka nuna karfinsu a hoton. Na ji dadin kasancewa a wajen a wannan lokacin har na shaidi abun da ya faru.”

Presentational grey line

Yin kwalliya don zuwa makaranta

Babbar mai daukar hoto ta kamfanin dillanci labarai na Reuters a arewa maso yammacin Afirka Zohra Bensemra, ta yi bulaguro zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira na wucin-gadi a Dallow da ke Somaliya, inda ta hadu da Zeinab.

Kamar sauran takwarorinta ‘yan mata a duniya, Zeinab kan yi kwalliyarta a tsanake duk safiya kafin ta tafi makaranta.

Sai dai duk da cewa ba kamar miliyoyin sa’anninta ba, ita Zeinab ‘yar shekara 14 tuni an yi mata aure, amma tursasata aka yi.

Iyeyen Zeinab na daga cikin kusan ‘yan Somaliya 900,000 da suka tsere daga gidajensu, ba saboda yaki ba, sai dai saboda fari da hadarin fadawa cikin kuncin yunwa.

Sai dai tserewa zuwa sansanin na bukatar dumbin kudi, shi ya sa iyayenta suka bayar da aurenta kan sadakin dala 1,000, wanda zai ishe su su yi bulaguron.

Zeinab applies make up before schoolHakkin mallakar hoto
Reuters

Sai dai Zeinab ta ki yarda. Ta gudu ta buya a cikin daji, amma a karshe aka dawo da ita gida, aka kulle ta a daki aka kuma tilasta mata auren mutumin da ya girmeta da kusan shekara 40.

Iyayenta da ita kanta da kuma sabon mijin nata sun samu isa sansanin na Dallow.

Sai dai bayan kwana uku kacal da yin auren, Zeinab ba ta bata lokaci ba ta nemi saki, shi kuwa ya bukaci a biya shi kudinsa.

Tafiya tamkar tauraruwa

Bensemra ta fara ganin Zeinab ne a matsuguninta a wata safiya, inda hasken rana zai ba da damar daukar hoton yadda wannan matashiya ke gudanar da rayuwarta.

Wata kungiyar agaji ta Italiya ce ta ceto ta bayan kungiyar ta yi alkawarin biyan kudin.

A yanzu tana da ‘yanci kamar sauran ‘yan mata takwarorinta, har ma mai daukar hoton ta samu damar daukarta a yayin da take kwalliya don shirin tafiya makaranta.

Bensemra ta tambaye ta: “Me ya sa ki ke kwalliya idan za ki je makaranta?”

Sai Zeinab ta amsa da cewa: “Ina so na kasance kyakkyawa a ko yaushe.”

Amma ba wannan ne ya fi jan hankalin Bensemra dangane da Zeinab ba. A maimakon haka, ta fi sha’awarta kasancewar ta wata matashiya mai tafiya makaranta dauke da litattafanta, tana tafiya tamkar tauraruwa.”

“Ba ta mallaki komai ba amma tana son yin karatu – Na yi farin cikin haduwa da ita.”

Presentational grey line

Sabon tabo

Wani mai daukar hoto dan Najeriya Akintunde Akinleye ya je Maiduguri, a arewa maso gabashin kasar, ya hadu da mutanen da ke yakar ‘yan kungiyar Boko Haram.

A matsayinsa na dan Najeriyar da ke zaune a kasar Canada, mutane na yawan tambayar Akinleye ko yaki ake a fadin Najeriya baki daya.

“Wani bangare na kasar ne kawai,” in ji shi. Da yawan ‘yan Najeriya ba su ma san me yake faruwa a can ba, amma ya shafi kowa da ke kasar. Gagarumar matsala ce.”

Amma Akinleye ya kagara sosai don son nuna wani bangare daban na yakin – bangaren da ya dauka kuwa na wannan hoton ne na wani dan shekara 38 mai suna Dala Aisami Angwalla, daya daga cikin ‘yan kato da gora 30,000.

A volunteer vigilante sits outside his house after a fight against Boko HaramHakkin mallakar hoto
Akintunde Akinleye

Angwalla ya ji rauni a wani kwanton bauna da aka kai musu, amma Akinleye ba ya so mu fi mayar da hankali a can.

A maimakon haka, ya saita kamararsa kan mutumin amma ba a matsayin wanda ya ji rauni ba, sai dai a matsayin kamar wanda yake yi wa al’ummar duniya wata tambaya.

Mai daukar hoton ya ce: “Mutane na tunanin cewa duk wanda ke rayuwa a arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma matasa, to ‘yan kungiyar Boko Haram ne.”

Amma Angwalla ya ce babu wani muhimmanci a gare shi ya tsaya cewa hakan ba gaskiya ba ne: Abun da ya fi muhimmanci shi ne ya kare gidansa da al’ummarsa daga kungiyar Boko Haram.

Abu ne mai wahala. Angwalla ya ce mayakan Boko Haram na zaune a cikin al’ummar tare da ‘yan kato da garo.

“Mutanen da ke yakarsu sun san su, sun san dukkan mutanen da ke jawo matsaloli,” in ji Akinleye.

Presentational grey line

Dankwali

Mai daukar hoto na Afirka Ta Kudu John Wessels ya yi bulaguro zuwa yankin Kasai a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo a watan Agusta tare da kungiyar agaji ta Oxfam.

“Akwai wani yanayi na yin shiru, da tunani a wannan hoton,” a cewar Wessels, yana mai nuna hoton Anny Mafutani, mai shekara 30.

Matashiyar, wadda tana daya daga cikin dubbai da suke tsere daga kauyenta don gujewa yaki, tana zagaye da duk wasu tarkace da ta samu tserewa da su, a wani coci da ake ajiye mutanen da ke neman mafaka.

A woman in the Kasai region, Democratic Republic of CongoHakkin mallakar hoto
John Wessels/Oxfam

Labarinta na son tsira da rayuwa na nan tas a kwakwalwar Wessels: Tun tuni aka hada wadannan kayan waje daya, tun kafin mayakan sa kan su kai musu farmaki.

Hakan na nufin a yayin da suka ji amsa kuwwar harbin bindiga, Mafutani da ‘ya’yanta biyar sun shirya don tserewa daji.

Sai dai mijinta bai yi sa’a ba – an kashe shi a lokacin da yake kokarin tsira. Ba ta iya tsayawa don taimakonsa ba.

Mafutani da yaranta biyar sun shafe wata biyar a cikin daji. Babu isasshen abinci a cikin shirgin da suka kwasa, don haka sai ta kai su wannan cocin.

Amma duk da haka a lokacin da za a dauke ta hoto kokari take ta ga ta yi kyau sosai a hoton. Wannan ne ya sa ta bar Wessels cikin matukar mamaki.

“Ta iya daukar mutum biyar ta rayu da su a cikin daji, amma duk da haka tana son ta dauki dankwali ta daura don kawai ta yi kyau a hoto,” in ji Wesells.

Presentational grey line

Dukkan masu daukar hoto hudun an yi hira da su ne a wani shiri na BBC World Service Focus on Africa, suna magana a kan ayyukansu don bayyana kadan daga cikin hotunan da suka zamo manyan labaran Afirka a wannan shekarar ta 2017.

Nigeria: Rikicin kabilanci ya barke a Bwari ta Abuja


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a garin Bwari da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Rikicin dai ya barke ne bayan wasu da aka ce ‘yan kungiyar asiri ne suka kai wani hari ranar Lahadi da daddare.

Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa harin ya yi sanadin mutuwar wani mutum.

Duk da cewar rikicin ya yi kamar ya kwanta daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin, amma ya sake dawowa a ranar Litinin din inda aka yi ta afka wa juna tsakanin ‘yan kabilar Gbagi (Gwarii) da Hausawa.

Wani mazaunin Bwari ya shaida wa BBC cewa an kona kusan rabin kasuwar Bwari.

Kasuwar kamar wata matattara ce inda kabilu daban-daban mafi yawa Hausawa da Igbo ke kasuwanci.

Rundunar ‘yan sanda a birnin Abuja ta tabbatarwa da BBC cewa tuni ta baza jami’anta a garin na Bwari domin kwantar da rikicin.

Sai dai kakakin rundunar, Anjuguri Jesse Manzah, bai yi karin haske a kan adadin rayuka da kadarori da suka salwanta ba, yana mai cewa rundunar ta fi mayar hankali ne kan kokarin tabbatar da doka da oda kafin ta fara kididdigar abubuwan da aka rasa.

Kawo yanzu dai ba a san ainihin dalilin da yawo barkerwar wannan rikici ba, wanda kafin barkewar rikicin, mazauna yankin ke cewa ana zaune lafiya tsakanin kabilun da ke rayuwa a garin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce tana kokarin tabbatar da doka da oda a garin na Bwari

‘Wahalar rayuwa ta hana kiristoci ziyara lokacin kirsimeti’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A daidai wannan lokaci na kirsimeti da sabuwar shekara mabiya addinin kirista kan bar wuraren da suke domin komawa mafari, wato garuruwansu na asali, akasari domin sada zumunta

Lokacin kirsimeti da sabuwar shekara lokaci ne da mabiya addinin kirista ke yin tafiye-tafiye, wanda wasu shugabannin addinin kirista suka ce tafiye-tafiyen na da asali a ekilisiyya.

Wasu mabiya na kokarin sada zumunci a wannan lokaci, amma wasu na ganin a yadda al’amuran rayuwa suke tafiya, tafiye-tafiye ba su zama dole ba.

A daidai wannan lokaci na kirsimeti da sabuwar shekara mabiya addinin kirista kan bar wuraren da suke domin komawa mafari, wato garuruwansu na asali, akasari domin sada zumunta.

Reverend John Joseph Hyab, wani malamin addinin kirista a Najeriya ya ce tafiye-tafiyen mabiya addinin kirista na da asali ne a ekilisiyya.

“Duk wanda ya san littafi mai tsarki wato labarin haihuwar Yesu to ya san cewa haihuwar Yesun ta hada da tafiye-tafiye, tun lokacin da Mala’ika ya bayyana gaban Maryamu ya ba ta busharar za ta haihu a lokacin ya kuma shaida mata cewa Elizabeth mahaifiyar Yohanna na da juna biyu, to sai Maryamu ta ziyarce ta don taya ta murna,” in ji Reverend Hyab.

Sai dai mabiya addinin suna korafin cewa a wannan lokaci da yawa ba su da halin yin tafiye-tafiyen saboda halin matsin rayuwar da ake ciki.

Mista Adamu Marshall ya ce wani lokaci dole ne wasu sai sun yi kaura daga birane zuwa garuruwan da aka haife su.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana ci gaba da wahalar man fetur a Najeriya a lokacin bikin kirsimeti

“Eh tafiya na da amfani don akwai wadanda ke zaune a birane kuma iyayensu na kauye, kuma wannan ne kawai lokacin da akan samu damar zuwa a gaida iyaye. Shi ya sa ake amfani da damar don yin ziyara.

“Kuma tafiya ta yi wahala ne a wannan zamanin saboda tsadar rayuwa wanda ina ganin laifin gwamnati ne, ai a wasu kasashe a irin wannan lokacin komai sauki yake kara yi ba wahala ba, amma a Najeriya komai kara tsawwala yake,” in ji Adamu Marshal.

Yayin da Adamu Marshall ke nuna alfanun irin wannan bulaguro, shi Mista Modekai Ibrahim na ganin in dai ba da wani uzuri ba, shi ya gwammace ya yi zamansa a inda yake.

“Yanzu idan na ce zan je gida sai na sha mai rabin tanki, to ka ga da wannan kuwa ai gara na saya wa iyalina kaji su ci.

“Masu sayar da mai da gangan suke bullo da wanann wahalar, tun da sun san cewa a wannan lokaci na kirsimeti ana yawan yin tafiye-tafiye. Haka ba kyau gaskiya., in ji Mista Marshall.

Da yawan Jama’ar Igbo daga kudu maso gabashin Najeriya da ke zaune a arewa, kan bar arewa don komawa yankinsu tun kafin Kirsimeti, wasun su kuma su zauna a gida har sabuwar shekara.

Chief Dominic Uzu ya ce nauyin sarauta ne ke sanya shi tafiya gida, ba don haka ba lokacin sabuwar shekara da kirsimeti ba lokaci ne na tafiye-tafiye a halin da ke kasar ke ciki yanzu.

Hausawa dai kan ce zumunci a kafa yake ,kuma kowa ya bar gida gida ya bar shi kila laakari da haka ne kan sa mabiya addinin kirista lekawa gida a lokacin kirsimeti da sabuwar shekara .end

Talakawa na matukar kauna ta- Buhari


Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Buhari ya ce a duk lokacin da ya yi Sallah ya kan godewa Allah daya sa talakawa ke matukar kaunar sa

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce goyon bayan da ‘yan Nigeria ke nuna masa shi ne babban garkuwan sa.

Ya bayyana haka ne a wani shirin talbijin da fadar shugaban kasar ta dauki nauyi da aka watsa rana Lahadi.

Shugaba Buhari ya ce a duk lokacin da ya yi Sallah ya kan godewa Allah daya sa talakawa ke matukar kaunar sa kuma suka yarda da shi.

Shirin dai ya tattauna ne da shugaban kasar tare da jin ra’ayoyin wasu fitattun ‘yan Nigeria.

Daga cikin su har da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da wasu ministocin gwamnatin wadanda suka yi tsokaci kan halayyar shugaban kasar da kuma salon mulkin sa.

Sai dai wasu masu sharhi a shafukan sada zumunta sun soki shirin da aka watsa ta gidan talbijin.

Wani dan Jarida mai suna Ja’afar Ja’afar ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa;

“…..na kwashe sa’a guda ina bata lokaci wajen kallon shirin da babu komai a ciki illa shirme ..Ban yahewa wallah!

Shi kuwa Idris Mohammed ya rubuta a shafin sa na Facebook cewa;

”Kasancewar mutane miliyan 12 ne suka zabi shugaba Buhari har yanzu suna goyon bayan sa fiye da shekaru goma, babu wani dan siyasa da ya kama kafar sa.. Ko yau aka yi zabe shine zabi na.”

Sai dai wani mai suna Yakubu Lere cewa ya yi;

”Na fara kallon shirin a matsayina na kwararren ma’aikacin watsa labarai fiye da shekaru 30, amma na ji takaici har sai da na kashe akwatin talbijin di na”…..

Wasu masu lura da al’amura a Najeriyar dai na ganin wannan shiri tamkar sharar fage ne kan shirye shiryen shugaba Buhari na sake tsaya wa takarar 2019.

Sai dai kawo yanzu shugaba Buhari bai fito fili ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara ba a shekarar 2019.

Mu tuna da ‘yan gudun hijira a lokacin Kirsimeti- Fafaroma


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGE

Image caption

Fafaroma ya yi takaicin yadda aka tilastawa miliyoyin mutane tserewa daga muhallan su

Fafaroma Francis ya yi kira ga mabiya darikar katolika a fadin duniya da kada su yi watsi da halin da ‘yan gudun hijirar da suka bar garuruwansu a dalilin tashin hankali ke ciki.

A wani taron jajibirin Kirsimeti a cocin Saint Peter’s a birnin Vatican, shugaban ya kwatanta hakan da labarin Maryam da Yusuf wadanda su ka rasa wajen zama a Bethlehem a lokacin da Maryam ke nakudar haihuwar Annabi Isa (AS).

Fafaroma Francis ya ce akwai darasi kan labarin Yusuf da Maryamu, mun ga yadda aka tilastawa iyalai watsewa mun ga yadda aka tilastawa wasu miliyoyin mutane tserewa daga muhallan su.

A Bethlehem din yanzu an samu raguwar masu zuwa ziyara saboda karuwar tashin hankali tsakanin Falastinawa da sojojin Isra’ila.

Hakan ta faru ne tun bayan da Shugaba Trump ya ayyana Jarusalem a matsayin babban birnin Isra’ila.

Guatemala za ta mayar da ofishin jakadancinta birnin Kudus.


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Trump na Amurka ne ya fara sanar da yunkurin sa na mayar da ofishin jakadancin Amurkar zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv

Shugaban kasar Guatemala Jimmy Morales ya ce yana shirin mayar da ofishin jakadancin kasar da ke Israila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus.

Kasar Guatemala na cikin kasashe bakwai da suka kada kuri’ar goyon bayan Amurka da Israila kan kudirin da MDD ta zartar.

Kudirin ya nemi Amurka ta sauya matsayin da ta dauka na ayyana birnin a matsayin babban birnin Israila.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin shugaba Trump ta yi barazanar katse agajin da ta ke ba kasashen da suka bijire wajen kin goyon bayan ta.

Wasu na ganin mai yiwuwa wannan shi ne babban dalilin kasar na yin hakan.

Sai da shugaba Morales ya ce dama can Guatemala ta dade tana kawance da Israila.

Tunisiya ta hana jiragen Emirate sauka a kasar ta saboda dalilan tsaro


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

Matakin da Hadaddiyar Daular Larabawar ta dauka akan matan Tunisiya ya janyo cece kuce

Kasar Tunisiya ta sanar da haramta saukar duk wani jirgin sama a kasar daya fito daga Hadaddiyar Daular Larabawa saboda dalilan tsaro.

Sanarwar na zuwa ne kwana biyu bayan jami’an gwamnatin Tunisiya sun yi zargin cewa Hadaddiyar Daular Larabawar ta haramtawa matan Tunisiya tafiye-tafiye ta jirgin sama zuwa kasar ko kuma yada zango a cikin kasar ta.

Wasu matan Tunisiyar da suka yi balaguro zuwa kasar sun yi korafin cewa, an jinkirta tafiyarsu a jirgin Emirates, inda wasun su suka ce sai da aka sake tantance takardunsu na Visa.

Ma’aikatar kula da harkokin sufuri a Tunisiyar ta ce haramcin saukar jiragen saman zai ci gaba har sai an dauki matakan da suka kamata.

Kawo yanzu dai ba bu wani martani daga Hadaddiyar Daular Larabawar.

Bahagon Musa ya buge Shagon Shagon Mada


Kimanin wasa 10 aka fafata a safiyar Lahadi a gidan dambe na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigera.

Mohammed Abdu ne ya hada mana wannan rahoton

Wasannin da aka kisa shi ne wanda Dogon Bahagon Sico daga Kudu ya buge Shagon Zakka daga Arewa da wanda Shagon Cinnaka daga Arewa ya doke Dogon Aleka daga Kudu.

Da wanda Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa ya yi nasara a kan Shagon Shagon Mada daga Kudu.

Wasannin da aka yi canjaras kuwa:

Shagon Dan Aminu daga Arewa da Bahagon Ibola daga Kudu

Bahagon Ibola daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa

Shagon Abata Mai karami daga Kudu da Shagon Gidan Sani Dankande daga Arewa

Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Dan Matawallen Kwarkwada daga Kudu

Shagon Abata Mai Karami daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau karami daga Arewa

Dan Asuba Shagon Autan Sikido daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusaudaga Arewa

Dan Ali Shagon Bata Isarka daga Kudu da Aminun Mahaukaci Teacher daga Arewa

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan 18-22 Disamba


Zababbun hotunan wasu abubuwan da suka wakana a kasashen Afirka a makon nan.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani mai daka tsari da ya yi shiga irin ta Santa Claus yana bai wa kifi abinci a lokacin bikin shiga ruwa ranar Talata a birnin Durban na Afirka ta Kudu.

Egyptian Handicapped Mohamed Azeema (C) in action during the first disabled soccer match in Cairo, Egypt, 16 December 2017Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Kungiyar kwallon kafar mutanen da aka yanke wa kafafu mai suna, The Medicals, ta kasar Masar ta yi gasa a karon farko a birnin Alkahira ranar Asabar, inda take fata wata ran za ta fafata a gasar cin kofin kwallon mutanen da aka yanke wa kada ta duniya.

A young man from Kenya's Maasai ethnic group poses after coming out of the bush on Wednesday after a month-long circumcision ceremony, which serves as a rite of passage to adulthood.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani matashi dan kabilar Maasai ta kasar Kenya ya fito daga daji ranar Laraba bayan an yi bikin yin kaciya na zamansa saurayi…

Circumcised Maasai young men wearing a ritual costume covered with hunted birds, come out from the bush to receive blessing from ceremony masters near Kilgoris, KenyaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A lokaci guda kuma, wasu matasan sanye da ‘tufafin’ gargajiya na tafiya inda suka nufi wurin da manyan baki suke zaune domin su sanya musu albarka.

Chadian model Brigitte Tanegue is pictured during the 8th African Model Exhibition Awards on December 15, 2017, in Abidjan.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A nan kuma ‘yar kasar Chadi ce mai sanya kayan kawa mai suna Brigitte Tanegue ta yi kwalliya irin ta fure a wurin bikin nunin kaya ranar Juma’a da aka yi a Abidjan, babban birnin Ivory Coast ranar Juma’a

Georgian actors perform during "The Three Sisters" by Konstantin Purtseladze at the 19th session of Carthage Theater Days in Municipal Theater in Tunis, Tunisia, 15 December 2017.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A wannan ranar ce kuma dai wasu taurarin fim na Georgia suka yi wani wasa a Tunis, babban birnin Tunisiya.

A ranar Talata wasu 'yan mata suka yi wasan kwallon shinge a wani sansanin 'yan gudun hijira a yankin da 'yan Somaliya ke zama a Habasha.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Talata wasu ‘yan mata suka yi wasan kwallon shinge a wani sansanin ‘yan gudun hijira a yankin da ‘yan Somaliya ke zama a Habasha.

Daliban makarantar sojoji na Libya suna atisaye a ranar da ake yaye su daga makarantar sojojin ranar Litinin a makarantar da ke birnin Benghazi na gabashin kasar.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Daliban makarantar sojoji na Libya suna atisaye a ranar da ake yaye su daga makarantar sojojin ranar Litinin a makarantar da ke birnin Benghazi na gabashin kasar.

A farm worker at a tobacco field at Herne Farm, 66 km south of Harare, Zimbabwe, 18 December 2017. The tobacco selling season is to start in March 2018. Zimbabwe is the biggest grower of tobacco in in Africa and sixth in the world.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A wannan rana kuma a Zimbabwe, wani ma’aikaci yana shanya ganyen taba don ya bushe bayan ya tsinko.

South African President and former President of the ANC Jacob Zuma departs following the closing ceremony on the final day of the 54th ANC conference at the NASREC Expo Centre in Johannesburg.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Laraba, Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu yana waka a wani taron jam’iyyarsa ta ANC bayan ya sauka daga shugabancinta.

Christmas decorations light up the streets of Lagos on December 18, 2017.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tun a ranar Litinin kuwa aka fara kawata birnin Lagos na NAjeriya da kwalliyar bikin kirsimeti.

Hotuna daga AFP da EPA da kuma Reuters

An ci kwallo 504 a gasar Premier Ingila


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester City ce ke mataki na daya a kan teburin Premier bana

Bayan da aka kammala wasannin mako na 19 a ranar Asabar a gasar cin kofin Premier ta bana, an ci kwallo 504.

Gasar wacce aka fara a ranar 11 ga watan Agustan 2017, wacce kungiyoyi 20 ke fafatawa sun buga wasanni 190 kawo yanzu.

‘Yan wasa biyu ne ke kan gaba a yawan cin kwallo a raga, inda Harry Kane na Tottenham da Mohamed Salah na Liverpool kowannensu ya ci kwallo 15.

Wasan da aka fi cin kwallaye a gida shi ne wanda Manchester City 5-0 Liverpool, Manchester City 5-0 Crystal Palace, Manchester City 7-2 Stoke City da na Arsenal 5-0 Huddersfield Town.

Manchester City wacce ke mataki na daya a kan teburi ta ci wasa 17 a jere, ta kuma yi 19 ba a doke ta ba.

Ita kuwa West Bromwich Albion wacce take ta 19 a kasan teburi ta yi wasa 17 ba tare da ta yi nasara ba a kakar ta bana.

Za a shiga wasannin mako na 20 a ranar Talata 26 ga watan Disamba:

  • Chelsea da Brighton & Hove Albion
  • Manchester United da Burnley
  • West Bromwich Albion da Everton
  • Watfordda Leicester City
  • Huddersfield Town da Stoke City
  • Bournemouth da West Ham United
  • Liverpool da Swansea City
  • Tottenham da Southampton

Muna ba ku hakuri kan man fetir – Buhari


Hakkin mallakar hoto
LEON NEAL

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna jimaminsa dangane da wahalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta na karanci man fetur.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna jimaminsa dangane da wahalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta na karanci man fetur.

“Ina jinjina wa ‘yan Najeriya game da wahalar rashin man fetur da kuma yadda suke jure wa wahalhalun bin dogayen layuka domin neman man,” inji shugaban a cikin wani jawabi da BBC ta samu.

“Ana sanar da da ni halin da ake ciki musamman irin kokarin da kamfanin mai na kasa, NNPC ke yi domin samar da isasshen man fetur a wannan lokacin da kuma nan gaba.”

Shugaban ya kara da cewa “Kamfanin na NNPC ya tabbatar min cewa za a sami saukin yanayin a cikin kwanaki masu zuwa.”

Ya sanar da ‘yan Najeriya cewa ana sa ran shigowar man fetur daga lkasashen waje, kuma za a raba man zuwa dukkan sassa na kasar.

Shugaban ya kuma ce ya umarci hukumomin da lamarin ya shafa da su “dada kaimi wajen dakile masu boyar da man fetur da kuma ‘yan kasuwa masu kara kudin man.”

Messi ya ci kwallo 22 a kakar bana


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga kuma Argentina za ta buga kofin duniya a 2018

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Argentina da Barcelona, Lionel Messi ya ci kwallo 22 a kakar 2017/18.

Messi ya fara zura kwallo ne a bana a karawar da Real Madrid ta doke Barcelona 3-1 a gasar Spanish Super Cup da suka kara a Nou Camp a ranar 13 ga watan Agustan 2017.

Daga nan ne dan wasan na Argentina ya ci biyu a fafatawar da Barcelona ta ci Alaves a ranar 26 ga watan Agustaa gasar La Liga.

Jumulla kwallo 22 Messi ya ci a kakar bana, 15 a gasar La Liga ya ci wa Barceloa, da hudu da ya zura a raga a gasar cin kofin Zakarun Turai da ukun da ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Argentina.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai, sannan Argentina za ta je gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Gasar Hikayata: Saurari Labarin ‘Garin Neman Gira’


A ci gaba da kawo muku karatun labaran da suka yi nasarar lashe gasar Hikayata ta bana, a wannan mako za mu fara kawo muku labarai goma sha biyun da alkalan gasar suka ce sun cancanci yabo.

Za kuma mu fara ne da labarin Garin Neman Gira na Na Rabi Ishaq Usman Dawakin Dakata, birnin Kano, Najeriya, wanda Badariyya Tijjani Kalarawi ta karanta.

Dilan wiwi ya afka motar ‘yan sanda ya dauka motar tasi ce


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Police said the man was carrying about 1,000 joints

Wani wanda ake tuhuma da dillancin tabar wiwi yayi wani abin takaici, bayan da fada cikin wata mota cikin hanzari dauke da daurin tabar ta wiwi 1,000 a tare da shi, kafin ya fahimci cewa motar ta ‘yan sanda ce.

Jami’an ‘yan sanda a Denmark sun ce mutumin na sauri ne ya isa gidansa a lokacin da yayi wannan batar basirar.

Wannan lamarin ya auku ne a Christiana, wani yankin babbban birnim kasar da akak kafa shi a shekarun 1970, kuma sanannen cibiyar cinikin haramtattun kwayoyi ne a kasar.

‘Yan sandan sun ce zasu gurfanar da shi a gaban alkali, inda zai iya fuskantar dauri a gidan yari idan aka same shi da laifin cinikin tabar wiwi.

Ga yadda rahoton na ‘yan sandan ya bayyan lamarin: “A jiya, wani dilan tabar wiwi daga Christiana wanda ke cikin saurin domin komawa gidansa ya fada bayan wata motar tasi. Amma ya sha mamaki bayan da ya fahimci cewa motar ‘yan sanda ce ya shiga.”

“Jami’an ‘yan sanda dake cikin motar sun yi murna da ganinsa, tun da yan dauke da daurin tabar ta wiwi kimanin guda 1,000.”

Dauka da dillancin tabar wiwi laifi ne a kasar ta Denmark.

Jami’an ‘yan sanda sun yi ta kai samame cikin unguwar Christiana a watannin da suka gabata, domin neman zakulo dillalan haramtattun kwayoyi da tabar wiwi.

Kun san gidan yarin da fursunoni ke iyo cikin fitsari?


Hakkin mallakar hoto
HMIP

Image caption

Masu sa ido a gidan yarin na Liverpool sun ga yadda ake rayuwa cikin kazanta kamar ban-dakin da ba a iya wanke wa

Fursunoni a gidan yarin Liverpool na rayuwa a yanayi mafi muni da wata tawagar masu sa ido ba su taba gani ba a duniya, a cewar wani rahoto da BBC ta gani.

Beraye da kyankyasai ne cike a gidan yarin, kamar yadda wani bangare ke cike da kazanta da ba a iya tsabtacewa.

Takardun binciken da aka bankado sun ce wasu fursunonin na rayuwa a kurkukun da ya kamata a ce ma an daina amfani da shi, saboda lalacewarsa musamman ban-daki.

Ma’aikatar shari’a ba ta ce komi ba a kan bayanan ba da aka bankado.

Tawagar masu sa ido a gidajen yari sun kai ziyarar ba-zata ne a gidan yarin na Liverpool a watan Satumba bayan sun samu labarin halin da ya ke ciki.

Abubuwan da suka gano, a cewar rahoton, babbar matsala ce ga samar da tsabtataccen muhalli.

Hakkin mallakar hoto
HMIP

Image caption

Babu wani tsari da aka yi tanadi na kawo karshen matsalar Beraye da kyankyasai a cewar rahoton

Tawagar kwararrun sun ce ba za su taba iya tuna wani gidan yari mafi muni kamar na Liverpool ba.

A lokacin da yake ba da labarin abin da ya gani a gidan yarin, babban sufeton gidajen yari Peter Clarke, ya kasa boye bacin ransa.

“Na sami wani fursuna da ke cikin wani hali na rashin lafiya kuma yake matukar bukatar kulawa wanda ake tsare da shi a wani dakin da babu ko kujera balle gado,” a cewarsa.

“Tagogi da kayan ban-dakin da ake tsare da shi duka sun karye, sannan ban-dakin kamar ya cika ko kuma ya toshe, yana diga kuma yana rayuwa ne a duhu”.

“Musamman ma wannan mutumin ana tsare da shi a cikin wannan yanayin a tsawon makwanni.”

Hakkin mallakar hoto
HMIP

Image caption

Masu sa ido sun ga yadda tagogi suka lalace a gidan yarin

Babban abin da ya kawo wadannan matsalolin a cewar rahoton, shi ne gazawa ce ta shugabanci tun daga karamar hukuma har zuwa matakin kasa.

Rikici a ko wane nau’in ya karu, sakamakon tu’amulli da kwayoyi, kamar yadda yawancin fursunonin ke shaidawa masu sa idon cewa samun kwaya abu ne mai sauki.

Haka kuma masu binciken sun gano wani zargin da ake wa jami’an gidan yarin kan yadda suke amfani da karfi, kuma ba wani kwakkwaran bincike da shugabannin gidan yarin suka gudanar.

Wasu jami’an gidan yarin na gallazawa fursunoni ta hanyoyin da suka saba wa dokokin gidan yarin kamar haramta ma su wanka a rana.

Akwai ayyukan kula da gidan yarin sama da 2,000, da ya kamata a ce an dauka amma shawarwari 22 daga cikin 89 ne kawai aka gabatar bayan rahoton 2015 da aka aiwatar.

Gazawar gwamnati

“Yana da wahala a iya fahimtar yadda shugabancin gidan yarin ya bari har matsalolin suka kai wannan matsayin,” kamar yadda babban jami’in masu binciken ke kalubalar ma’aikatar shari’a.

“Mun samu kwararan hujjoji da suka tabbatar da jami’an gidan yarin sun nemi taimako daga hukumomi a matakin yanki har zuwa na kasa game da matsalolin da suka tabbatar da cewa ba za a lamunce ba kafin ziyararmu amma ba abin aka yi.”

Rahoton ya kammala da cewa: “babu wani yunkuri da muka gani a kasa na tunkarar matsalolin.”

Image caption

Rahoton ya dora alhakin matsalolin ga shugabanni a matakin kananan hukumomi da yanki da ma kasa baki daya.

“Rahoto ne mafi muni da na taba gani,” a cewar Lord Ramsbotham, tsohon babban sufeton gidan yari.

“Amma… ta yaya mutum zai zo daga hedikwata ya je Liverpool kuma ba zai ji kunya akai ba?”

“Ta yaya shugabannin gidajen yari suka bari har gidan yarin ya shiga irin wannan yanayin?”

An tambaye shi a kan rahoton, cewa Liverpool na iya zama gidan yari mafi muni a Ingila, Lord Ramsbotham ya amsa da cewa: “Ba zan karyata ba.”

‘Iyo cikin fitsari’

Wani fursuna da aka saki ya shaidawa BBC cewa: “Batun matsalar fama da kyankyasai abu ne mafi muni” za ka ji suna bibiyar ka da dare.”

Sannan wani kuma ya ce yadda bututun ban-daki ya fashe, “Za ka ji kana iyo a cikin fitsari.”

Image caption

Darren Harley, daya daga cikin wadanda suka yi rayuwa a gidan yarin Liverpool

A lokacin bazara ne aka saki Darren Harley, bayan ya kwashe watanni 27 a gidan yarin kan laifin da ya shafi tu’ammuli da kwayoyi, ya danganta kuncin rayuwar da ya fuskanta a gidan yarin.

“Idan ka ajiye kare a wuri irin wannan, mutane za su zo su tafi da kai su rufe ka kan ka kuntatawa dabba.”

“Mu mutane ne, don haka ya kamata a kula da mu da kyau.”

Duk da ana danganta gidan yarin Liverpool a matsayin mafi muni, amma gidajen yari da dama a Ingila da Wales na fuskantar matsin lamba.

A karkashin gwamnatin hadaka, sakataren harakokin shari’a a lokacin, Chris Grayling ya datse yawan kasafin kudin gidajen yari da ma’aikata.

Tun datsewar, an samu karuwar kisan kai, da rikici da hare-hare a gidajen yarin.

Amincewa da gazawarta, ma’aikatar shari’a tana shirin daukar ma’aikata 2,500 a badi.

Cikin kwanaki kalilan an tube gwamnan gidan yarin Peter Francis bayan ziyarar, kuma a makon da ya gabata aka nada wani tsohon jami’in gidan yarin Pia Sinha a madadinsa.

A martanin da ta mayar kan gidan yarin Liverpool, Ma’aikatar shari’a ta ce: “Ba za mu yi magana kan wani rahoto da aka bankado ba”

Motar bas ta rikito daga kan gada


Image caption

Hukumomi sun ce yawancin wadanda abun ya rutsa da su mata ne da kuma kanannan yara.

‘Yan sanda sun ce wata motar bas mai dauke da mutum 50 ta rikito daga kan gada a arewacin Indiya, a kalla mutum 32 suka mutu.

Rahotannin sun ce wani dan shekara 16 ne yake tuka motar inda bayan da ta kwace masa ta afka cikin ruwa sa’annan ta gangara cikin kogin Banas.

Rahotanni daga kasar sun ce motar na dauke da fasinjoji daga Rajasthan zuwa Ramdevji Hindu temple, wani wurin bautar Hindu da ke gundumar Sawai Madhopur.

An samu yawancin gawarwakin mutanen an kuma garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitoticin kasar.

Image caption

Hukumomi sun ce yawancin wadanda abun ya rutsa da su mata ne da kuma kanannan yara.

Hukumomi sun ce yawancin wadanda abun ya rutsa da su mata ne da kuma kanannan yara.

Jaridar Hindustan Times ta rawaito ‘yan sanda na cewa direban motar na cikin wadanda suka mutu.

Man City ta ci wasan Premier 17 a jere


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallo na 100 da Sergio Aguero ya ci a filin wasa na Ettihad

Manchester City ta yi nasarar cin Bournemouth 4-0 a wasan mako na 19 a gasar Premier da suka fafata a ranar Asabar a Ettihad.

City ta ci kwallayen ne ta hannun Sergio Aguero wanda ya ci biyu a fafatawar da wacce Raheem Sterling ya ci da kuma Danilo wanda ya zura ta hudu a raga.

Wannan ne karo na 17 a jere da Manchester City ta ci wasan Premier, tana kuma matakinta na daya a kan teburi da maki 55.

Pep Guardiola ya jagoranci Barcelona cin wasa 16 a jere a shekarar 2010-11, ya kuma yi nasarar cin wasa 19 a jere a Bayern Munich a shekarar 2013-13.

Manchester City za ta ziyarci Newcastle United a wasan mako na 20 a ranar Laraba.

Kun san yadda wani ya kirkiri injin bayar da wutar lantarki?


Image caption

Mutanen kauyensu na kiransa da suna “mai cike da buri”

Wani dan kasar Tanzaniya John Mwafute ya kirkiro wani injin bayar da wutar lantarki a kauyensu.

John ya kirkiro injin din ne a kauyensu da ke kudancin Tanzaniya, inda ya ke ba wa gidaje sama da 250 wutar lantarki.

Kuma yana amfani ne da ruwan da yake kwararowa daga saman wani dutse da ke kusa da kauyen.

John ya yi aikin goge-goge bayan da ya daina zuwa makaranta. Amma kuma ba a son ransa yake aikin ba.

Sai dai yanzu injin samar da wutar da ya kirkiro na samar da wutar lantarki mai karfin 28kilowatts a kowacce rana.

Mutanen kauyensu na kiransa da suna “mai cike da buri”.

Hamsik ya buge tarihin Maradona


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Marek Hamsik ya koma Napoli daga Brescia shekara 10 da ta wuce

Marek Hamsik ya buge tarihin da Diego Maradona tsohon dan wasan Argentina ya kafa na wanda yafi cin kwallaye a Napoli.

Napoli ta yi nasarar doke Sampdoria 3-2 a ranar Asabar a wasan mako na 18 a gasar cin kofin Serie A karawar mako na 18, kuma hakan ya sa ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi.

Kyaftin din Napoli, Marek Hamsik shi ne ya ci kwallo na uku tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma na 116 da ya ci wa kungiyar a wasa 465 da ya buga mata.

Tun a makon jiya ya yi kan-kan-kan da Maradona a yawan cin kwallaye a fafatawar da Napoli ta doke Torino 3-1, bayan ya buga wasa 13 bai ci kwallo ba a kungiyar.

Napoli ita ce ta daya a kan teburin Serie da maki 45, bayan wasa 18 da ta yi.

Guguwa ta hallaka sama da mutum 100


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Irin barnar da ta biyo bayan guguwar Tembin

Fiye da mutum 100 ne aka ba da rahoton guguwa ta hallakasu a yankin kudancin kasar Phippines, kuma ba a san inda gomman mutane suke ba.

Guguwar da aka saka wa sunan Tembin ta janyo ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a wasu sassa na tsibirin Mindanao.

Garuruwa biyu da abin ya fi shafa sune Tubod da Piagapo, inda zaftarewar kasa ta danne wasu gidaje.

Kasar Philippines na fuskantar guguwa mai karfin gaske akai-akai, amma abin lura shi ne bai cika shafan tsibirin Mindanao ba.

Guguwar Tembin, wacce aka fi saninta da sunan Vinta a Philippines ta fara karfi ne a Mindanao ranar Juma’a kuma hukumomi sun ayyana yanayin-ta-baci a wasu yankunana kasar.

Image caption

Taswirar yankin da guguwar Tembin tafi shafa zuwa karfe 1 na ranar Asabar

Jami’ai masu aikin gaggawa sun ce an sami mace-mace akalla 62 a Lanao del Norte, 46 kuma a Zamboanga del Norte, inda aka sami akalla 18 a Lanao del Sur.

Shi ma wani jami’in dan sanda a garin Tubod, Gerry Parami ya fada wa AFP cewa akalla mutum 19 ne suka mutu a garin dake yankin Lanao del Norte.

Ya ce “Ruwan kogi ne yayi ambaliya har ya tafi da yawancin gidajen. Babu kauyen gaba dayansa.”

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Masu aikin ceto na taimakawa mazauna Davao a tsibirin Mandanao

Matsalar rashin wutar lantarki da ta sadarwa tana dakile kokarin ceto mutane a yankin.

A makon jiya gomman mutane. suka rasa rayukansu a yayin da guguwar Kai-Tak ta auka wa yankin tsakiyar Philippines.

Wannan yankin bai gama farfadowa daga wata mahaukaciyar guguwa mai suna Haiyan ba, wacce ta kashe mutum fiye da 5,000, ta kuma tarwatsa miliyoyin jama’a daga muhallansu a 2013.

Everton ta rike Chelsea canjaras a Premier


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Chelsea mai rike da kofin Premier tana matakinta na uku a kan teburin bana

Everton da Chelsea sun tashi wasa babu ci a gasar Premier wasan mako na 19 da suka kara a Goodison Park a ranare Asabar.

Everton ta ci gaba da buga wasanni ba tare da an doke ta ba tun lokacin da Sam Allardyce ya maye gurbin Ronald Koeman.

Everton wacce ke mataki na tara a kan teburin Premier ta yi wasa tara ba a yi nasara a kanta ba, kuma biyar daga ciki Allardyce ne ya jagoranta.

Chelsea wacce ke rike da kofin Premier kuma mai mataki na uku a kan teburin bana ta buga karawar ba tare da Alvaro Morata ba, sakamakon katin gargadi biyar da ya karba a bana.

Chelsea za ta buga wasan mako na 20 a ranar Talata da Brighton, ita kuwa Everton za ta ziyarci West Brom ne.

Barca ta bai wa Real tazarar maki 14


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Barcelona wacce ke ta daya a kan teburi ta bai wa Real Madrid wacce ke mataki na hudu tazarar maki 14

Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-0 a wasan mako na 17 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu da suka kara a ranar Asabar.

Barcelona ta ci kwallo ta hannun Luis Suarez da Lionel Messi da kuma ta uku da Aleix Vidal ya ci daf da za a tashi daga karawar.

Lionel Messi shi ne yafi cin kwallo a tarihin karawar El Clasico, bayan da ya ci kwallo na 25, guda 15 a Bernabeu kuma 17 a gasar La Liga ta bana.

Real ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dani Carvajal jan kati sakamakon taba kwallo da hannu a cikin da’ira ta 18 din Madrid

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga da maki 45, ita kuwa Real Madrid mai rike da kofin tana ta hudu da maki 31.

Barcelona za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na 18 a ranar 7 ga watan Janairun 2018, a kuma ranar ce Real Madrid mai kwantan wasa daya za ta ziyarci Celta Vigo.

An gano ana fataucin kananan ‘yan mata daga Nigeria


Mahukunta a Najeriya sun bayyana damuwarsu dangane da wani sabon salon fataucin ‘yan mata wadanda shekarunsu basu wuce 15 ba da ake yi zuwa kasashen larabawa.

Wannan ya biyi bayan batun garkuwa da mutane da ya bayyana inda aka gano ana sayar da daruruwan ‘yan Najeriya a matsayin bayi a Libya.

Wata jami’a a ofishin shugaban kasa a Abuja ta ce an gano cewa wasu likitoci ne da wasu ejan masu samar wa matafiya izinin shiga kasashen waje ne ke aikata wannan kazamin laifin.

Ba a san dalilan da yasa ake fita da wadannan ‘yan matan ba.

Mrs Abike Dabiri ita ce mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan batutuwan da suka shafi ‘yan kasar dake zaune a kasashen ketare, ta ce akan samar wa wadannan ‘yan matan da shekarunsu suka kama daga 13 zuwa 15 takardun izinin shiga kasashen larabawan na ainihi domin a shigar da su kasashen Saudiyya da Maroko da Masar.

Jami’ar ta yi kira ga hukumar hana fasa kwaurin mutane da ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya da su dauki kwakkwaran mataki tun kafin abin ya zama abin da ba za a iya shawo kansa ba.

A makwanni biyun da suka gabata ne aka fara kwashe ‘yan Najeriya kimanin 6,000 da suka makale a Libya.

Yadda za a yi aiki tare da mata-maza


Hakkin mallakar hoto
(Credit: Elizabeth S. Cameron/Quinn Nelson)

Image caption

Abokan aikin Quinn Nelson suna cike da tababar abin da ya kamata su yi lokacin da suka kasance a wajen aiki su ba a bangaren kowane jinsi suke ba.

Daga Jessica Holland

30 ga Agustan 2017

Kokarin tabbatar da kimar mutuntakar mutanen da ba sa cikin jinsin mata ko maza ba, al’amari ne da ke bukatar sauya alkiblar fahimtar kimar mutuntaka da kalmomin da muke amfani da su, musamman a wajen aiki.

“Ina da tabbacin cewa akwai murtanen ba sa kaunar kasancewa haka ko samun kansu a yanayin,” a cewar Quinn Nelson. “Kawai a birkice suke tattare da rudani.”

Dalibar nazarin halayyar dan Adam a Jami’ar Calgary da ke Canada mai shekara 24 ta kwatanta yadda mutum zai kasance a cikin abokan aikinsa in ya kasance ba a daya daga cikin jinsi mace ko namiji ba – a shekaru kadan da suka gabata, kuma a hakan ake ta kokarin bayyana cewa jinsi ba zabi ba ne na alamun da ake bari a takardun neman bayanai a wajen aiki na guraben da ake yi wa alama da zanen akwatunan.

Abokan aikin Quinn Nelson suna cike da tababar abin da ya kamata su yi lokacin da suka kasance a wajen aiki su ba a bangaren kowane jinsi suke ba.

“Wadanda ba a kimanta su tsakanin jinsuna biyu – marasa jinsi” lakabi ne da ake yi wa mutane don fahimtar jinsinsu a matsayin mata-maza, wadanda babu su, ko ba su kasance a tsakanin jinsunan ba, sannan ba su da kimar jinsi takamaimai. Nelson, tamkar dimbiun mutane a rukuni daban-daban sun fi son a yi musu amfani da lakabi mara nuni da jinsi., kamar “su,” sabanin “shi” ko “ita.”

Daga 2 zuwa 58 zuwa karshen kirga

Shekaru kadan da suka wuce, ana ta fafutikar kimanta mutuntakar mutane da ba su kasance a rukunin jinsunan da al’ada ta fayyace ba, Facebook ya fadada jerin jinsuna da ake da zabi daga 2 Zuwa 58 a shekarar 2014 kafin bayar da dama ga masu ta’ammmali da shafin su yi amfani da siffar kimanta mutuntaka bisa al’adarsu a shekarar da ta biyo baya..

Kasashe da dama sun fara kimanta mutumtakar mutanen da ba sa cikin rukunin jinsuna.

Duk da cewa akwai dimbin bayanai kan yawan al’umma, yawan mutanen Birtaniya da suka cikee guraben akwatunan alamun rashin jinmsi ya kasance 0.4 cikin 100 a daukacin kidayar jama’a da aka gudanar a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2011.

Birataniya a halin yanzu ta fara bin Kadin ko nazarin yadda za ta tattara bayanan rukunin marasa jinsi a kidayar jama’a ta shekarar 2021.

Sun ji cewa akwai abin da suke bukatar yi, amma ba su da tabbaci kan ko mene ne.

Duk da fadakarwar da ake yi game da rukunin marasa jinsi – kashi 50 cikin 100 na matasan karni na 21 suna da tabbacin cewa jinsi alama ce da nuni da rukunin mutane biyu, kamar yadda sakamakon wani bincikeen jin ra’ayin jama’ ya nuna na Fusion a 2015, al’amarin da har yanzu yake tayar da hankali mutane irrin su Nelson su kasa samun natsuwa a wajen aiki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

“Wadanda babu su a rukunin jinsuna biyu” ana kwatanta su a matsayin mutanen da suka tattare jinsuna biyu, wato mata-maza, ta yadda su ba sa cikin rukunin jinsuna ko sun tokare a tsakani, haka kuma ana iya daukarsu marasa jinsi ko wadanda jinsinsu ya kwaranye.

“Na ji cewa [abokin aikina] na da tunanin yin wani abu, amma ba su da tabbaci kan ko mene ne,” in ji Nelson. Nima ban san ko mene ne ba.”

Wani bincike da mujallar da ake wallafawa a shafin intanet ta gudanar mai taken lamarin da ya sha gaban jinsuna biyu (Beyond the Binary) a Maris din 2017 ya yi nuni da cewa kashi 1 cikin 100 daga mata-maza 225 na mutanen da ke jin cewa “suna da cikakkiyar kariya” dokar daidaito a wajen aiki da ake da ita a halin yanzu a wajen aiki, kuma kashi 42 cikin 100 na fama da matsalar halin da suka samu kansu a ciki bisa la’akari da kimar mutuntakar jinsin su a wajen aiki.

Misalan wadannan munanan al’amuran sun hada da zolaya, kimanta rashin jinsi, hana su amfani da bandakunan wajen aiki, akan kwace ayyukan yi da a ka ba su.

“Al’amarin ya tayar mini da hankali,” a cewar J Fernandez, editan mujalla. “Idan ka ji cewa ba ka da natsuwa a mafi yawan kwanakinka, wannan na nufi karara lafiyar kwakwalwarka ta yi matukar tabuwa.

Samun natsuwa

Fernandez yana amfani da da daukacin nau’ukan wakilan sunan da ke nuni da mutane biyu ko fiye a Ingilishi, wato “they/their” kuma a halin yanzu ba shi ne alamar nunin jinsi ga abokan aiki a kan aikinsu ba.

Wannan ba wani abu ba ne bambarakwai (da za a ce ba a saba da shi ba), a cewar binciken jinsin mata-maza na 2016 Scottish Trans Alliance (Kungiyar Hadin gwiwar mata-maza a Scitland)), wanda ya gano cewa kashi 4 cikin 100 na mata-maza suna jin dadi a kodayausshe su bayyana kimar jinsin su a lokacin aiki, kuma kashi 90 cikin 100 suna da damuwar kada a wulakanta su.

“Ina tsoron bayyana kaina a matsayin mata-maza a wajeen aiki,” in ji. “Ina ganin rashin bayyanawa karara wajen tafiya da mutanen da ba su da jinsi (mata-maza) shi ke firgita ni fiye da yadda ya kamata.

Samar da tsari karara da ke nuni da cewa mata-maza mutane ne da ake maraba da su, wadannan su ne matakan da muke dauka,’ ta yadda za su rage wa mutane firgici.”

Idan ka ji baka da natsuwa a mafi yawan lokutan rana, ta bayyana karara lafiyar kwakwalwarka ta dan tabu.

Irin wadannan al’amuran ban tsoro ba za a ce ba su da tushe ba.

Wani marubuci da ke zaune Landan, mai kwanaren shigar mata da gabatar da shirin rediyo na Ray Filar ya gano wannan lamari ne bayanan da ya aike da saqon imail ga abokan aikinsa da ke aiki a wata mujalla a lokacin, kan su bayyana jinsinsu, sannan wane juyin harshe (sarrafa kalmomi) ya kamata a yi amfani da shi yayin da ake nuni a kansu.

“Ba na jin cewa nau’ukan wakilin ssuna ne karshen lamari wajen damawa ko tafiya tare da mata-maza (marasa ggurbi a tsakanin jinsunan mace da namiji),” inji filar. “Sai dai su ne muhimman takun tarairayar kyautatawa.”

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Alamy).

Jarumin nahiyar Asiya mata-maza Kate Dillon (a dama) wanda ake kira Taylor Mason sai mashahurin mai koyon aikin talabijin da asusun saka jari na hedge ya dauki nauyinsa a shirin Biliyoyi.

Duk da haka, filar ya gnao cewa kadan daga cikin abokan aikinsa sun yi watsi da nusarwar da aka yi musu ko “kawai sun yi watsi ko kin tuna abin da na bukace su da shiga.”

Baya ga kasancewa “marar jinsi da ake ta maimaitawa tsawon shekara biyu,” Filar ya ajiye aikinsa. Bisa la’akari da al’amuran da ya samu kansa a ciki, filar ya bukaci wuraren aiki da su aiwatar da tsare-tsaren da za su sshawo kan kyarar wariyar bambanci da ke nuna wa mata-maza (marasa gurbin jinsi a tsakanin maza da mata).

“A yi ta maimaita muhimmiyar horarwa da ilimantarwa a matsayin wani yanki na aiki,” Filar ya bayar da shawara, “sannan ma’aikata mata-maza da masu aikin wucin gadi ta yadda za a ba su damar shawo kan matsalarsu don kada ta sake dirar musu in an yi amfani da ita.

Dangane da masu daukar aiki (kamfanoni ko ofishsoshi ko ma’aikatu) da ba su da masaniyar ta inda za su fara aiwatar da wadannan tsare-tsaren, Fernandez ya bayar da shawarar tunkarar kungiyar mata-maza don bayar da shawara, kamar kungiyoyin da suka hada da Gendered Intelligence (masu bin Kadin jinsi) da Scottish Trans Alliance (hadin gwiwar mata-maza a Scotland)..

“Lamarin ba shi da wani babban tashin hankali,” a cewar Fernandez.

“Idan kana wani mata-maza a jerin ma’aikata, kawai ka tattauna da su kan abin da zai kawo musu saukin jin dadin rayuwa (ta aiki). Lamarin na da matukar sauki ta hanyar ba su tabbacin cewa babu wata matsala don an sanya tufafi na daban ko suna mabambanci.

Abokan iki na da gudunmuwar da za su bayar wajeen samar da kyakkyawan muhalin tarairayar mata-maza, a cewar Fernandez.

“Abin da ya taimaka mini shi ne yadda mutane suka kula, wajen karrama ni, suna amfani da wakilin sunan da ya dace, kuma su nemi afuwa idan sun yi kwaba, amma ba wani babbban abin damuwa ba ne, kawai a san yadda za a zauna a halin da ake ciki.

“Mafi yawan mutane na dari-darin bijiro da tambaya kan kowane ne mata-maza (mara gurbi a jinsuna biyu – mata da maza), ‘Wane nau’in wakilin suna kafi ganin dacewarsa?’

“Amma kawai lamari mafi kyau wajen karrrama mutum, tamfar yadda za ka tambayi sunan mutum idan ba ka sani ba.”

Matakan da za a dauka

Idan masu daukar aiki sun yi matukar kokari wajen tarairayar daukacin jinsuna da nunin furuci, kyakkyawan tasirin lamarin zai kasura ya bayyana karara.

Quinn Nelson ta koma aiki a matsayin mai karbar kudi da bayar da canjin ciniki a karamin kamfani sayar da kayan abinci, kuma a wannnan karon, sabanin fitowarta bayan da ta fara aiki, Nelson karara take bayyana alamun jinsin su a lokacin tattaunawa, kuma sun samu kyakkyawan yanayin da ya bayar da damar yin hakan.

Wannan bayana nufin a ce ko da yaushe lamarin na da sauki ba.

Daya daga cikin abokan ciniki ya fada wa Nelson za su kasance “sarauniyar masu kwanaren sanya tufafin mata” wani kuwa korafi ya yi ga hukumar gudanarwar kamfanin game da “mazan da ke sanya suturar mata.”

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Ray Filar)

Nau’ukan wkailin sun aba su ba ne jigon tafiya da kowa-da-kowa, amma kyakkyawar hulda ce, a cewar marubuci mazaunin Landan, mai kwanaren shigar mata da gabatar da shirin rediyo na Ray Filar.

Akwai kyakkyawan yanayi game da lamuran. Da zarar abokin hulda ya kalli bajen da ke makale a jikin Nelson dauke da wakilin suna, sai ya ce lalllai zai sanar da abokansa su mallaki guda.

Wani namiji ya sanya yaro ya Makala jan farce, sai ya cika annnashuwa ganin nelson ta lailaye shafen farcenta da shi. Na ce: “Nakan yi kuka lokacin da nike magana kan lamarin, kuma ina yin kuka da zarar hakan ya faru.”

Wannan lokaci na kulla alaka zai iya faruwa ne kawai, a cewar Nelson, saboda sun samu cikakkiyar natsuwa a wajen aiki.

“Zan yi matukar kaunar samun aiki a wurin da tsarin gudanarwarsa tuni ya saba tafiya tare da mata-maza,” in ji Nelson.

“Ko akwai wajen wanka da aka kebe wa mutanen da babu su a jerin jinsuna (na mace da namiji), ta yadda ban a bukatar ilimantar da mutane, sannan in ji dadin yin aiki a wajen.

“Lamarin na da ban takaici ganin cewa akwai Karin aiki a gabanka da zarar an dauke ka aiki.”