Sam Allardyce ya kulla yarjejeniyar koci da Everton zuwa 2019


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An dauki hoton Sam Allardyce (a tsakiya) tare da mai kungiyar Everton Farhad Moshiri a filinsu na Goodison Park ranar Laraba

Sabon kocin Everton Sam Allardyce ya ce yana matukar shauki da jin dadin dawowa aikin horarwa tare da kungiyar Everton.

Tsohon kocin na tawagar Ingila mai shekara 63 ya kulla yarjejeniya da kungiyar har zuwa watan Yuni na 2019, ta zama magajin Ronald Koeman, wanda aka kora a watan Oktoba, kungiyar tana matsayin ta 18 a teburin Premier.

Allardyce ba shi da aiki tun lokacin da ya bar Crystal palace a watan Mayu.

Yanzu dai Everton tana matsayi na 13 a gasar kuma za ta kara da Huddersfield a ranar Asabar.

Everton ta zama kungiyar Premier ta bakwai da Allardyce ya jagoranta, fiye da kowa ne koci, in banda Harry Redknapp wanda ya horar da kungiyoyi biyar.

Kocin bai taba faduwa da wata kungiya daga Premier ba, amma kuma sabanin haka ya kai Bolton da West Ham gasar da Championship.

An tuhumi kocin Chelsea Antonio Conte da rashin da’a


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Antonio Conte ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata, amma ya yi abin ne saboda yana wahala lokacin wasansu

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi kocin Chelsea Antonio Conte da laifin rashin da’a sakamakon korarsa da alkalin wasa ya yi lokacin karawarsu da Swansea City, saboda kin yarda da hukuncin lafirin.

A minti na 43 da wasan ne lafirin ya kore shi zuwa cikin ‘yan kallo a fafatawar Premier da kungiyarsa ta yi nasara 1-0 a ranar Laraba.

Conte ya ci gaba da kallon wasan gaba daya ne na bayan hutun rabin lokaci a talabijin din dakin sanya tufafi na ‘yan wasa, sakamakon korar saboda ya nuna rashin amincewa da hukuncin alkalin wasan na kin ba kungiyarsa bugun gefe lokacin ana canjaras a wasan.

Yana da wa’adin har zuwa ranar talata karfe shida na yamma agogon Najeriya, ya bayar da bahasi ga tuhumar in ji hukumar ta kwallon kafar ta Ingila.

Bayan wasan kocin dan kasar Italiya ya nuna nadama tare da bayar da hakuri a kan abin da ya yi.

Kun san yadda za a fitar da jadawalin gasar Kofin Duniya?


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Za a yi bikin fitar da jadawalin gasar kofin duniyar ta 2018 a zauren kade-kade na fadar gwamnatin Rasha ranar Juma’a 1 ga Disamba

Nan da kasa da sa’a 24 ne za a hada jadawalin gasar cin kofin duniya ta shekara mai kamawa a Rasha, inda jami’ai da manyan baki suka fara sauka a birnin Moscow domin halarta.

Najeriya tana tukunya ta karshe, wanda hakan ke nufin za a hada ta wasa da manyan kasashe a rukuninta, to amma kocinta dan Jamus Gernot Rohr ba shi da wata fargaba. Hasali ma ya ce zai so a hada tawagarsa ta Najeriya da kasarsa Jamus.

Daga bangaren Turai, akwai Rasha mai masaukin baki, da kasashen da suka zama na daya a rukunansu na sharar fage, wadanda suka kunshi Belgium da Ingila da Faransa da Jamus da Iceland da Poland da Serbia da Spaniya.

Akwai kuma kasashen Turan da suka samu tikitinsu na gasar bayan sun yi wasan raba gardama, wadanda su kuma sun hada da Crotia da Denmark da Sweden da kuma Switzerland.

Wakilan Afirka guda biyar a gasar ta kofin duniya kuwa su ne Najeriya da Senegal da Masar da Tunisia da kuma Moroccoa.

Daga Amurka ta Arewa da ta Tsakiya da kuma yankin Karebiyan, Costa Rica ce da Mexico da kuma Panama.

Ita kuwa Latin Amurka tana da Brazil da Argentina da Colombia da Peru da Uruguay, yayin da Asia take da Saudi Arabia da Iran da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Australia.

Za a yi zaman fitar da jadawalin na gasar ta cin kofin duniyar ne a zauren kade-kade na fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, gobe Juma’a 1 ga watan Disamba da karfe hudu na yamma agogon Najeriya.

Za a raba kungiyoyin kasashen ne bisa jerin sunayen gwanayen wasan na kwallon kafa da Fifa ta fitar na watan Oktoba na wannan shekara ta 2017.

Akwai tukwane guda hudu, a gaba daya, wadanda kowacce take dauke da tawagar kasashe takwas.

Za a sanya Rasha a tukunya ta farko tare da gwanayen kasashen da ke gaba guda bakwai, sai kuma guda takwas da ke bin baya a tukunya ta biyu.

Daga nan kuma sai gwanaye takwas na gaba a tukunya ta uku, yayin da su kuma takwas din karshe za a sa su a tukunya ta hudu.

Babu kasashen da suke daga nahiya daya in ban da na Turai (uefa) da za a hada su a rukuni daya. Kasashe mafi yawa da za a iya hada wa a kowane rukuni daga Turai, su ne biyu.

Tsohon dan wasan gaba na Ingila kuma mai gabatar da sharhin wasan kwallon kafa na BBC Gary Linker tare da ‘yar jaridar harkokin wasanni ta Rasha Maria Komandnaya, su ne za su jagoranci taron.

Manyan bakin da za su halarci bikin za su hada da wakilai daga kowacce daga cikin kasashe takwas da suka taba cin kofin na duniya kamar haka;

Laurent Blanc (Faransa), da Gordon Banks (Ingila ), da Cafu (Brazil), da Fabio Cannavaro (Italiya), da Diego Forlan (Uruguay).

Sai kuma Diego Maradona (Argentina), da Carles Puyol (Spaniya) da kuma Miroslav Klose (Jamus).

‘Yan Nigeria sun yi zanga-zanga kan ‘sayar da bayi’ a Libya


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Saurari yadda ‘yan Nigeria suka yi zanga-zanga kan ‘cinikin bayi’ a Libya

Wasu ‘yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Libya da ke birnin Abuja domin nuna bacin ransu game da tozartawar da ake yi wa bakaken fata ciki har da ‘yan Najeriya a kasar Libya.

‘Yan Najeriyar da suka hallara a gaban ofishin jakadancin kasar dai sun ce abin takaici ne a ce ana cinikin ‘yan Najeriya kan dala 400, kudin da bai kai naira 150,000 ba.

Sun nemi gwamnatin Libya da ta Najeriya su kawo karshen cin zarafin ‘yan Najeriya a kasar Libya.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Deji Adeyanju, ya ce ba a san Najeriya da wulakanta baki ba, saboda haka bai kyautu a ce ana musguna wa ‘yan Najeriya a wata kasar Afirka kamar Libya ba.

Ya ce: “Abun mamaki ne a ce kudi kalilan ne ake sayan dan-Adam. Dan Adam guda wai azo a ce za a saye shi dala 400. Dala 400 nawa ne a kudin Najeriya?”

Hakkin mallakar hoto
Deji Adeyanju

Image caption

Masu zanga-zangar sun nemi a kwaso ‘yan Najeriyar da suka makale a Libya

Deji ya ce nuna rashin amincewa da yadda gwamnatin Najeriya take tinkarar lamarin inda ya ce idan aka yi wa dan Amurka irin wannan cinzarafin, Amurka za ta yaki kasar ne.

Masu zanga-zangar dai sun ce jami’an ofishin jakadancin kasar sun yi watsi da su.

Sai dai kuma BBC ta nemi jin ta bakin sakatariyar ofishin jakadancin kasar, Rose Diovu, kan zargin cewa ofishin jakadancin ya yi watsi da masu zanga-zangar, sai ta ce jami’an ofishin suna hutun maulidi ne shi ya sa babu masu tarbar masu zanga-zangar a ofishin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai ya bayar da umarnin cewa a kwaso ‘yan Najeriyar da suka makale a kasar Libya bayan wasu ‘yan Najeriya 242 suka dawo daga kasar a wannan makon.

Burin masu fafatika dai shi ne a dawo da dukkan ‘yan kasar da suka rage a can tare da samar musu ayyukan yi.

Aikin Koci: Ana nuna wa bakake da tsirarun jinsi wariya a Ingila


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Satumba aka nada Jimmy Floyd Hasselbaink a matsayin kocin Northampton Town

Koci-koci bakaken fata da kuma wadanda suka fito daga tsirarun jinsi har yanzu suna fuskantar matsalar nuna bambanci a wasan kwallon kafa na Ingila, kamar yadda wani rahoto na masana wasanni ya nuna.

Rahoton na shekara-shekara na kungiyar masana harkokin wasannin (SPTT), ya ce cigaban da aka samu na kawar da wannan matsala tun shekara ta 2014 kadan ne.

Binciken ya nuna cewa daga cikin manyan koci-koci 482, na manyan gasar kwallon kafa hudu na Ingila, 22 ne kawai bakaken fata da wadanda suka fito daga tsirarun jinsi.

Masu binciken suna son a bulla da tsarin da ake kira ‘Rooney Rule’, wanda aka yi wa lakabin da sunan tsohon mai kungiyar American Football, Dan Rooney, wanda hukumar kwallon zari ruga ta Amurka ta bullo da shi a 2003, wanda ya tanadi cewa dole ne a tantance akalla koci daya bakar fata ko wanda ya fito daga tsirarun jinsi a duk wani matsayi na babban koci da za a dauka.

An fitar da alkaluman ne bisa abin da ake da shi a farkon watan Satumba, wato kafin nadin Jimmy Floyd Hasselbaink a matsayin kocin Northampton da kuma Jack Lester a kungiyar Chesterfield.

Nadin nasu ya kawo yawan koci-koci bakaken fata ko ‘yan tsirarun jinsi zuwa biyar a kungiyoyin 92.

An ‘sassara’ wasu yara ‘yan Firamare uku a Borno


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Maharin ya abka cikin ajin ‘yan nazare ne ya kashe yara biyu da kuma wata yarinya

Wani mutum dauke da adda ya abka wata makarantar Firamare a jihar Borno inda ya sassara wasu ‘yan makaranta uku suka mutu, tare da wata malama.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar Alhamis a makarantar Firamaren gwamnati ta Jafi da ke kauyen Kwaya-Kusar a kudancin jihar Borno.

Wani mazaunin yankin da ya je makarantar bayan abkuwar lamarin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa maharin ya abka cikin ajin ‘yan kananan yara ne ya kuma dabawa kananan yara biyu da kuma wata yarinya wuka inda ya kashe su nan take.

Shugaban kungiyar malamai a karamar hukumar Biu, Malam Habu Sulaiman, wanda ya tabbatar wa da BBC abkuwar lamarin ya ce tuni aka mika mutumin ga jami’an tsaro.

Tuni dai aka kai gawar yaran babban asibitin garin Gombe da ke makwabtaka da Kwaya-Kusar.

Wasu rahotanni dai na cewa ana zargin mutumin da ya aikata wannan abu mahaukaci ne.

Rahotannin sun kara da cewa a sakamakon wannan hari dai matasan yankin sun far wa maharin, inda suka yi masa jina-jina har ta kai an mika shi asibiti.

A yanzu dai kwamishinan ‘yan sanda na Borno Cp Damian A. Chukwu ya bai wa hukumar ‘yan sanda ta Kwaya-Kusar umarni mika maharin ga Hukumar Binciken masu laifuka ta jihar, da su binciki mutumin sosai don a gane halin da lafiyar kwakwalwarsa ke ciki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A 2014 gwamnatin jihar Borno ta rufe dukkan makarantu a jihar sakamakon hare-haren Boko Haram

A bangare guda kuma wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai hari inda suka kashe mutum biyu a jihar Adamawa.

An dai kai wannan hari ne da yammacin ranar Laraba a kauyen Wanu kusa da garin Gulak a jihar.

Wannan na faruwa ne kwasa da makwanni bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a garin Mubi na jihar daya hallaka akalla mutum 50.

Gasar gudun Landan: Eliud Kipchoge zai tashi tsaye kan Mo Farah


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Eliud Kipchoge gwanin dan tseren kewaya fili ne kafin ya koma na titi

Zakaran gasar Olympic Eliud Kipchoge ya ce zai dauki kalubalan Mo Farah na shiga gasar gudun yada-kanin-wani na Landan da matukar muhimmanci.

Kipchoge, mai shekara 33, shi ne ya cinye gasar ta London Marathon, a shekara ta 2015 da ta 2016, kuma zai sake shiga gasar a shekara mai zuwa ta 2018.

Farah dan Birtaniya, dan asalin Somalia, ya shiga gasar gudun ta Landan sau biyu, amma wannan da za a yi a watan Afrilu na shekara mai kamawa za ta kasance ta farko, tun bayan da ya sauya wasa daga gasar gudun famfalaki na cikin fili, wadda ya ci lambar gwal ta Olympic hudu da kuma shida ta duniya a gudun mita 5,000 da mita 10,000, ya koma gasar gudu a titi.

Kipchoge ya ce Farah gwanin dan tsere ne wanda ake mutuntawa, wanda kuma zai iya samun nasara ba tare da wani jinkiri ba, saboda haka ba zai yi sake da shi ba.

Farah mai shekara 34, kamar yadda aka tsara ya fice daga gasar ta gun-yada-kanin wani ta Landan a rabin nisan da za a kai a shekara ta 2013.

Sanna kuma a shekara ta 2014 ya kammala gasar a matsayi na takwas a cikin sa’a biyu, da minti takwas da dakika 21.

Majalisar Dinkin Duniya ‘ta yi wa dan Nigeria coge’


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Korafin Zanna Mustafa kan MDD

Wani Lauya dan Najeriya da ya lashe lambar yabo mafi girma da Majalisar Dinkin Duniya ke bayar wa kan ayukkan jin kai, ya nuna damuwa kan jan kafar da ya ce hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar (UNHCR) ke yi wajen ba shi kudaden da ke tare da lambar yabon kimanin dala 150,000.

Zanna Mustafa dai ya samu lambar yabon ne kan kafa wata makaranta a jihar Borno da ya yi, inda ake bai wa yaran da rikicin Boko Haram ya mayar marayu ilimi da abinci kyauta.

Kuna iya latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron korafin da Zanna Mustafa ya yi.

Ku karanta karin wasu labarai:

David Silva ya tsawaita zamansa a Manchester City


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Yanzu David Silva wanda ya yi wa City kyaftin a wasanta na zakarun Turai da Napoli a watan Oktoba, zai zauna a kungiyar har shekara 10 kenan,

David Silva ya sanya hannu a yarjejeniyar kara zamansa a Manchester City da shekara daya, ta yadda zai ci gaba da taka leda a kungiyar har zuwa shekara ta 2020.

Dan wasan mai shekara 31, na Spaniya ya koma City ne daga Valencia a kan kudi fam miliyan 24 a shekara ta 2010.

Dan wasan na tsakiya ya dauki kofin Premier biyu, da na FA daya da kuma na Lig guda biyu a zamansa a Man City.

Kungiyar ta Pep Guardiola ta bayar da tazarar maki takwas bayan nasara 12 a jere a gasar ta Premier.

Nasara ta baya bayan nan da ta yi ita ce wadda ta ci Southampton ana dakika 30 ta karshe a tashi daga wasansu ranar Laraba, bayan kara minti biyar na cikon bata lokaci, inda suka yi 2-1.

Silva wanda ya bayar da kwallo har sau takwas aka ci a kakar bana ya kasance na daya, domin ba wanda ya yi wannan kokarin zuwa yanzu a gasar ta Premier, kuma ya ce burinsa shi ne kara cin kofuna a Etihad.

Dan wasan ya yi wa City wasa 234 a gasar Premier tun lokacin da ya koma kungiyar daga Valencia a 2010, inda ya ci kwallo 40.

An yi barazanar kai wa Saudiyya hari


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

‘Yan tawayen Houthi sun batawa Saudiyya rai

‘Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun yi barazanar kai hari tsakiyar kasar Saudiyya saboda ci gaban da take yi na hana shiga da kayan masarufi kasar.

Shugaban ‘yan tawayen Abdulmalik al-Houthi ya ce dakarunsa sun san yadda za su kai harin da zai yi mummunar barna a Saudiyya.

Kwanakin baya ne mayakan ‘yan tawayen Houthi suka harba makami mai linzamin da ya doshi birnin Riyadh.

Lamarin ya yi matukar bata ran Saudiyya abin da ya sa ta tsaurara matakin hana shugaba arewacin Yemen da ke hannun ‘yan tawaye.

Sai dai an dan sassauta matakin.

Miliyoyin ‘yan kasar Yemen ke fuskantar masifar yunwa kuma kasashen duniya na ci gaba da matsa lamba kan Saudiyya ta janye matsin da take yi wa Yemen.

Bosnia: Praljak ya sha guba a gaban kotun duniya


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Slobodan Praljak ya sha guba bayan kotu ta tabbatar da daurin da aka yi masa

Hukumomi a kasar Netherlands sun fara bincike game da yadda wani mai laifi dan Kuroshiyawan Bosniya ya shigar da guba cikin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague, kuma ya kashe kansa a zaman daukaka karar da aka nuna kai tsaye a talbijin.

Slobodan Praljak, mai shekara 72, ya mutu a asibiti ranar Laraba jim kadan bayan ya shanye wani abu a cikin kwalba bayan ya yi shelar cewa shi ba shi da laifi.

Wannan ya faru ne jim kadan bayan kotu ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 20 da aka yi masa kan laifukan yaki.

Wasu Kuroshiyawa ‘yan Bosniya sun yi tsayuwar dare domin tunawa da mutumin da suke yi wa kallon gwarzo.

Firai ministan Kuroshiya, Andrej Plenkovic, ya yi kakkausar suka ga kotun ta musamman ta kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka ta tsohuwar kasar Yugoslabiya wadda ta yi masa shari’a.

Shari’ar tabbatar da daurin da aka yi wa Praljak da wasu mutum biyar, ta kawo karshen shari’ar da ake yi a kotun sama da shekara 20.

Ta yaya ya mutu?

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

An ga wata motar daukar mara lafiya a wajen kotun ranar Laraba

Wasu dakiku bayan ya ji cewa karar bai yi nasara a karar da ya daukaka ba, tsohon Janar din ya ce, “Slobodan Praljak ba mai laifin yaki ba ne. Zan yi watsi da hukuncin kotun.”

Sannan ya sha guba daga wata kwalba mai ruwan kasa kuma ya yi shelar cewa, “Na sha guba.”

Alkalin da yake jagorantar zaman kotun ya dage zaman nata kuma aka garzaya da Praljak asibiti.

Ya yi fama da ‘yar gajeriyar rashin lafiya kuma ya mutu a asibitin, in ji mai magana da yawun kotun ICC Nenad Golcevski.

Ya kara da cewa shi ba zai iya tabbatar da abin da ke cikin kwalbar ba.

Mene ne binciken zai mayar da hankali a kai?

A wata takaitacciyar sanarwa, masu gabatar da kara na kasar Netherlands sun ce binciken zai mayar da hankali kan “taimakawa wajen kisan kai da kuma saba wa dokar magani”.

Masu bincike za su yi nazari kan wanda ya ba shi magani mai kisa, abin da yake ciki da kuma yadda ya iya shigar da shi dakin shari’ar mai tsananin tsaro, kamar yadda wakiliyar BBC Anna Holligan ta ruwaito daga birnin Hague.

Praljak ba shi ne mutumin da ya fara kashe kansa dangane da wata sharia’a da aka yi a Hague ba.

An taba samun wani dan Kuroshiyawan Sabiya da ake zargi da laifukan yaki Slavko Dokmanovic, ya rataye kansa a shekarar 1998, da kuma Milan Babic wanda shi ma ya kashe kansa a shekarar 2006.

An kama bakon da ya sace talbijin 120 a otal a India


Hakkin mallakar hoto
Bangalore police

Image caption

‘Yan sandan Bangalore tare da Vasudev Nanaiah da wadansu daga cikin talbijin din da ake zargin ya sata

An kama wani mutum da ake zarginsa da shafe wata hudu yana satar talbijin har guda 120 daga otal daban-daban a kudancin Indiya.

Wani babban jami’in ‘yan sanda ya shaida wa wakilin BBC Hindi Imran Qureshi cewa, ma’aikatan otal din ba su taba zargin Vasudev Nanaiah ba, kasancewarsa bakon da ke cike da nutsuwa da kamala.

‘Yan sanda sun ce a duk lokacin da Mr Nanaiah zai kwana a wani otal ya kan je ne da wani babban akwati da ake tsammanin kayansa ne a ciki.

A watan Oktoba ne aka kama shi yana satar talbijin a wani otal, amma an bayar da belinsa kafin daga bisani a sake kama shi kuma.

‘Yan sanda sun ce ya sake komawa ruwa wajen yin satar kwanaki kadan bayan da ya fito daga gidan yari.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Chetan Singh Rathor ya ce, idan Mr Nanaiah ya fahimci cewa akwatin da ya je da shi ya yi karami, sai ya auna girman talbijin din da ke dakin ya koma ya nemo wani akwatin da ya fi wannan girma.

Mista Rathor ya ce: “Ya kan shiga otal din ya fita a lokuta da dama ta yadda ma’aikatan otal din ba za su fahimci cewa ya fita da talbijin ba.”

An kama Mr Nanaiah ne bayan da mutumin da ya yi niyyar sayar wa da talbijin din ya tona masa asiri a wajen ‘yan sanda.

‘Yan sandan Bangalore sun same shi da laifuka 21 na sata, kuma suna fatan zai yi zaman gidan yari na tsawon lokaci.

Wata kotu za ta yanke hukuncin ko yana bukatar a binciki lafiyar kwakwalwarsa.

Manoman alkama sun ce gwiwarsu ta yi sanyi da gwamnatin Buhari


Image caption

Gonar alkama

Manoman alkama a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, sun fara yanke-kauna game da shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman alkama.

Manoman sun ce ba su taba samun tallafi daga hukumomin tarayya ba, duk da ikirarin gwamnatin Buhari na wadata kasa da abinci.

Masu noman na cewa, sai manomi ya je kasuwa da buhu 10 amma sai ya shafe sati guda bai sayar da ko buhu daya ba.

Bayan gwamnati ta yi kira ga manoman alkama su fadada noman, shugaban manoman alkama na jihar Kano, Alhaji Faruk Rabi’u Mudi ya ce daga manoma 800 har sai da aka samu 7, 000 da suka yi rijista.

A bara kawai sai da manoman alkama suka kai sama da dubu 30 a fadin jihar Kano, in ji shi.

Saboda matsaloli daban -daban da manoman alkamar ke fuskanta a jihar ta Kano a bana yawan wadanda za su noma alkama ya yi matukar raguwa zuwa kasa da dubu bakwai

A yanzu dai ana sayar da kwanon alkama daya a kan naira dari hudu, wanda a bara ana sayar da kwano daya ne a kan kimanin naira dubu daya.

Manoman sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shigo cikin wannan lamari na noman alkama.

Cacar baki ta kaure tsakanin Trump da Theresa May


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Donald Trump da Theresa May a fadar White House a watan Janairu

Shugaba Trump ya ce kamata ya yi fira ministar Burtaniya Theresa May ta mayar da hankali kan abin da ya kira akidojin musulmi na ta’addanci masu mummunar illar da ke faruwa a kasarta maimakon sukarsa.

A sakon tiwitarsa na baya-bayan nan, Mista Trump ya ce bai kamata Theresa May ta yi haushin kaza huce a kan dami ba don kuwa abin da ya yi daidai ne in ji shi.

Shugaban Amurkan ya sake yada hotunan bidiyon tunzura jama’a guda uku da wata kungiyar masu tsananin kishin kasa a Burtaniya ta wallafa.

Sakon tiwitar ya zo ne bayan wani mai magana da yawun fira ministar ya ce ba daidai ba ne Shugaba Trump ya ci gaba da yada bidiyon nuna kiyayya ga musulmi.

Hotunan bidiyon da wata jagorar kungiya mai suna Burtaniya ce Farko na kokarin nuna Musulmai suna ruguza wani mutum-mutumi na kirista da kuma kashe wani yaro gami da far wa wani nakassashe.

Bidiyon wanda Mista Trump mai mabiya sama da miliyan 40 ya sake yada hotunan da Jayda Fransen, mataimakiyar shugabar kungiyar Britain First.

An tuhumi misis Fransen, ‘yar shekara 31, a Burtaniya da amfani da “barazana da cin zarafi da zage-zage ko dabi’ar cin zarafi” kan jawaban da ta yi a wani gangami da aka yi a birnin Belfast.

Mijin wata ‘yar majalisar dokokin Burtaniya da aka yi wa kisan gilla a baya, Brendan Cox ya fada wa cewa Trump na son “halasta nuna kiyayya” ne

A cewarsa: “Idan wani shugaba ya sake yada bayanan irin wadannan mutane ko ya ba su lasifika ko ya nuna alamun goyon bayansu, abin da hakan ke nufi shi ne halasta ba kawai bayanansu ba har ma da daukacin abubuwan da suka biyo baya.”

Amurka da Burtaniya aminan juna ne kuma sau da yawa ana cewa suna da alaka ta musammam da juna. Fira minista Theresa May ce shugabar wata kasa daga ketare da ta fara ziyartar Donald Trump a fadar White House.

Kalaman Buhari na Abidjan sun isa ‘yankan shakku’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mai fashin bakin ya ce gwamnoni na riga malam masallaci ne kan takarar Buhari saboda za ta taimaka musu

Wasu masu fashin bakin siyasa sun ce kalaman da shugaban Najeriya ya yi a Abidjan babban birnin kasar Kwatdebuwa alama ce karara ta bukatar sake tsayawa takara a karo na biyu.

“Idan ma akwai masu wasi-wasi a kan zai yi takara ko ba zai yi takara ba, to kalaman na birnin Abidjan za su yanke shakku,” in ji mai fashin baki.

Dr. Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa ya ce kusan ya nuna ga alkiblarsa cewa zai yi takara.

Muhammadu Buhari yayin wani takaitaccen jawabi a gaban ‘yan Najeriya mazauna Abidjan na kasar Kwatdebuwa ranar Laraba ya bukaci su yi masa uzuri saboda ya tsaya jiran wasu gwamnoni ne don su je tare, dalilin kuma da ya sanya shi makara kenan.

Ya ce yana son jera kafada da gwamnonin ne saboda idan ‘yan Najeriya suka zo gida za su shaida wa mutanensu cewa Buhari ya ziyarce su tare da gwamnonin jihohinsu abin da in ji Buhari zai sa ya samu kuri’a nan gaba.

Dr. Abubakar Kari ya ce tun kafin ya yi wadannan kalamai, mutane da dama sun dauka cewa zai sake tsayawa takara saboda take-take da faruce-furucen magoya bayansa.

A cewarsa ko da yake, har yanzu shugaban har yanzu nuku-nuku yake yi don kuwa bai fito fili ya furta ba amma dai “za a iya ba da wannan fassara.”

“Kuma ni dama ina ganin haka halin ‘yan siyasa ne, ba kullum ne za su fito fili su ce ga abin da za su yi. To amma daga furuce-furucensu da kalamansu da take-takensu da kuma irin abin da suke yi ko kuma suka ki yi, zai nuna ga alkiblar da za su bi.”

‘Likitoci’ 400 sun fadi jarrabawa a Nigeria


Image caption

Likitocin da suka yi karatu a jami’o’in kasashen wajen sun ce sun sami koyarwar a makarantunsu fiye da irin wanda ake samu a jami’o’in Najeriya

Sama da mutum 400 daga cikin kimanin ‘yan Najeriya 680 da suka karanta aikin likita a jami’o’in kasashen waje ne suka fadi jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.

Sai dai kuma wadanda suka fadi jarrabawar sun ce babu adalci a jarrabarwar suna masu zargin cewa kyashin karantun da suka yi a kasashen wajen ne ya sa aka kayar da su.

Daliban da suka yi karatun likitanci a jami’o’in kasashen wajen dai tare da wasu daga cikin iyayensu sun garzaya zauren majalisar dattawa domin su nemi ‘yan majalisar su bi musu kadi kan zargin da suke yi cewa an kayar da su ne a jarrabawar tantance likitoci ta Najeriya.

Image caption

‘Likitocin’ dai sun garzaya majalisar dattawan Najeriya ne don gabatar da korafin su

Daliban sun dauki lokaci suna muhawara a tsakaninsu game da yadda ya kamata su bullo wa matsalar domin samun nasara.

Ko yaya wasu iyayen daliban da suka yi karatun likita a jami’o’in kasashen waje ke ji game da faduwar ‘ya’yansu a jarrabawar?

Malam Muhammad Bala Jibrin yana da ‘ya’ya biyu a cikin likitocin da suka fadi jarabarar tantancewar.

Ya ce ”na taba yin aikin kwamishina ilimi a jihar Bauchi kuma kafin gwamnatin jihar ta kai yara karatu a kasar wajen, sai da suka dauki shugaban hukumar MDCN mai tantance likitoci na wancan lokacin zuwa kasar Misira domin ya amince da yadda ake koyar da aikin likitanci a jami’o’in da za su kai daliban.”

Ya kara da cewa hukumar MDCN ta amince da yadda ake koyar da aikin likitanci a jami’o’in tare da amincewa yadda za a yi aikin likitocin kasar Misira.

Daya daga cikin daliban da suka fadi jarabawar, Dr Bashir Isa, ya yi zargin cewa an kayar da su ne ba bisa ka’ida ba.

Ya ce: “Ai wannan fadar magana ce kawai. Ta yaya za a ce mutum kusan 700 sun rubuta jarrabawa, kuma wajen mutum 400 da wani abu su suka fadi jarrabawar? Ya kamata a yi tambaya.”

Image caption

Likitocin da suka fadi jarrabawar dai sun yi zargin cewa ana aikata ba daidai ba a jarrabawar tantance likitocin

“Na farko dai ka sani wannan jarrabawar tana da sauki ta yadda duk wannan saukin nata kuma aka zo aka ce mun fadi.”

“Sannan inda suke cewa mun fadin shi ya fi ko wane bangare sauki a koyarwar likitanci, shi ne kazo ka yi abu a fili a gani sabanin wani in kace ka tambaye shi ilimi a kwakwalwarsa zai sha wuya kafin ya gaya ma.”

Wakilin BBC ya nemi jin ta bakin hukumar MDCN mai tantance likitoci a Najeriya, amma hakar sa ba ta cimma ruwa ba domin jami’ar hulda jama’ar hukumar ta ce ba za ta iya magana kan lamarin ba, kuma bai sami shugaban hukumar, Tajudeen Sanusi, a waya ba.

Rashin tabbatar da kwarewar sama da likitoci 400 dai na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke fama da karancin likitoci.

‘Yan fashi sun sa wasu mutane tsere wa kauyukansu a Zamfara


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya-bayan nan sai da gwamnatin tarayya ta ce za ta tura dakarun soja zuwa jihar ta Zamfara don shawo kan rikicin da ke karuwa

Mazauna kauyukan Batoli da Kuka 9 da Tafkin Dawaki da kuma Gidan Sarauta a cikin jihar Zamfara sun tsere zuwa daji sakamakon wani wa’adi da wasu da ake zargin ‘yan fashin shanu ne suka ba su don su fanshi kansu.

An dai ba wa mazauna kauyukan zuwa ranar Juma’a don su biya naira miliyan biyu ko kuma su fuskanci farmaki.

Haka zalika an shaida wa BBC cewa su ma mutanen kauyukan Gidan Rana da Babu Dole da Gidan Saleh a cikin karamar hukumar Isan jihar Sokoto sun shiga irin wannan tsaka mai wuya bayan an ba su wa’adin zuwa ranar Litinin da ta gabata.

Wasu mutanen kauyukan da suka tsere sun fada wa wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza ta wayar tarho daga mafakarsu cewa suna cikin mawuyacin hali don kuwa ko abin da za su ci ma wahala yake yi musu ballantana su iya tara naira miliyan biyu a matsayinsu na talakawa.

Daya daga cikin mutanen wanda ba a ambaci sunansa ba ya ce: “Sunka ce ko mu ba su miliyan biyu zuwa Juma’a, ko su zaka su kakkashe mu, su kone muna gari.”

“To shi ne ga yanzu muna bakin daji, duka garin mun watce, ba kowa. Abincin ma da za mu ci babu, ba kowa garin namu.”

Shi ma abokin gudun tsiransa ya ce: “Abubawan da ke damunmu dai a halin yanzu shi ne, matsala ta barayin shanun nan.”

“Sabadda ka ga sun nuna sai mun ba su kudi, naira kusan miliyan biyu, to mu kuma alhali abincin da za mu ci ma, ya mana wahala. To shi ne gabaki daya suka ba mu notis zuwa Juma’a.”

Mutanen ba su dai fayyace ko sun fito ne daga kauye daya ne ko kuma kauyukansu daban-daban ne ba.

Rikicin barayin shanu dai ya addabi yankunan jihar Zamfara, inda ko a ranar 19 ga wannan wata na Nuwamba wasu da ake zargin barayin shanu ne sun kashe fiye da mutum 50 a hare-hare mabambanta da aka kai kauyukan Faro da Kubi da Shinkafi a jihar.

Mazauna yankunan sun ce, ana zaman dar-dar saboda maharan sun auka wa kauyukansu inda suka far wa mutane, abin da ya sa wasu da dama suka gudu don tsira da rayukansu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara dai ta ce ba ta da masaniya game da halin da mazauna kauyukan suke ciki.

Sai dai, mahukunta a nasu bangare cikin jihar Sokoto sun ce tuni sun dauki matakan tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ke fama da wannan al’amari.

Shugaban karamar hukumar Isa, Kanal Garba Moyi (Murabus) ya ce sun fada wa jami’an tsaro kuma sun kara musu man fetur a motoci, inda ya ba da tabbacin cewa yanzu haka suna kauyukan da aka tura su.

Sakamakon Premier: Man City ta sha da kyar 2-1 da Southampton


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Cin shi ne na tara da Raheem Sterling ya yi a Premier bana

Raheem Sterling ya ceci Manchester City bayan da ya ci mata bal a cikin dakika talatin ta karshen wasansu da Southampton, aka tashi 2-1, inda nasarar ta zamar musu ta 12 a jere a Premier.

Tun da farko De Bruyne ne ya ci wa Manchester United kwallo a minti na 47 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kafin kuma Romeu ya rama wa bakin a minti na 75.

Bayan minti 90 ana fafatawa 1-1, alkalin wasa ya kara minti biyar na lokacin da aka bata, wanda a cikin dakika 30 ta karshen lokacin ne Sterling ya sheko kwallon a murde ba ta tsaya ko ina ba sai a ragar Southampton, fili ya rude da sowa.

Yanzu Manchester City ta kara tazarar da ke tsakaninta da Manchester United ta biyu a tebur zuwa maki takwas, yayin da ita Southampton ta zama ta 11 da maki 16 a tebur.

Sakamakon sauran wasannin Premier na Laraba;

Arsenal 5-0 Huddersfierd ; Arsenal tana matsayi na 4 da maki 28, yayin da Huddersfield take ta 14 da maki 15.

Bournemouth 1-2 Burnley ; Bournemouth tana ta 15 da maki 14, yayin da Burnley take ta 6 da maki 25.

Chelsea 1-0 Swansea ; Chelsea tana ta 3 da maki 29, Swansea tana matsayi na 19 da maki 9.

Everton 4-0 West Ham ; Everton ta zama ta 13 da maki 15, West Ham na matsayi na 18 da maki 10.

Stoke City 0-3 Liverpool ; Stoke na matsayi na 16 da maki 13, ita kuwa Liverpool na matsayi na biyar da maki 26.

Copa del Rey: Barcelona ta caskara Real Murcia 5-0


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

A minti na 56 ne Piqué ya zi wa Barcelona ta biyu

Barcelona cikin sauki ta kai matakin wasan kungiyoyi 16 na sili-daya-kwale a gasar Copa del Rey bayan da a gidanta ta doke Real Murcia 5-0 ranar Laraba.

A karon farko da suka yi a gidan bakin nasu, sun yi galaba a kansu da ci 3-0, wanda yanzu sakamakon ya kasance 8-0, a karawa biyu gida da waje.

A minti 16 da shiga fili Paco Alcácer ya fara ci wa Barca, sai Piqué a minti na 56 ya ci ta biyu, sannan Aleix Vidal ya ci ta uku a minti na 60.

Bayan minti 14 kuma sai Denis Suárez ya kara ta hudu, kafin kuma José Arnáiz 79 ya zura ta biyar kuma ta karshe.

Sauran kungiyoyin da suka yi nasarar zuwa matakin na gaba, bayan wasan na jiya sun hada da Sevilla wadda ta fitar da FC Cartagena 4-0, a jiya hadi da wasan farko 7-0 jumulla.

Sai Lleida Esportiu wadda ta ci Real Sociedad 3-2, jumulla karawa biyu sakamakon ya kasance 3-3, amma albarkacin kwallon da ta zura a gidan Sociedad ta yi galaba.

Abubuwan kara kuzari: Fifa ta wanke Rasha


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Madam Fatma Samoura ta maye gurbin tsohon sakatare janar na Fifa Jerome Valcke, wanda aka haramta wa shiga harkar kwallon kafa tsawon shekara 12

Babbar Sakatariyar hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Fatma Samoura ta sheda wa BBC cewa babu badakalar amfani da abubuwan kara kuzari a harkar wasan kwallon kafa a Rasha.

Madam Samoura, wadda ta je birnin Moscow domin halartar zaman shirya jadawalin wasannin gasar kofin duniya da za a yi ranar Juma’a, ta kuma kare damar Rasha ta karbar bakuncin gasar ta kofin duniya.

Ta yi hakan ne duk da kwace lambobin bajinta na gasar Olympics na ‘yan wasan Rashar saboda samunsu da laifin amfani da abubuwan kara kuzari, da kuma hadarin da take fuskanta na hana ta halartar gasar Olympic ta lokacin hutura a birnin PyeongChang, na Koriya ta Kudu.

Babbar Sakatariyar ta ce daga samfurin da aka dauka na jini da fitsari sama da 800 na ‘yan wasan kwallon kafar babu wanda aka samu da yin amfani da abubuwan kara kuzari.

Amma ta ce da sun ga wani abu mai muhimmanci a gwaje-gwajen da ake yi nan da nan za su dauki mataki a kai.

An daure wasu sojojin Kamaru kan amfani da Facebook


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An bai wa sojojin zuwa ranar 9 ga watan Disamba domin daukaka kara

Wata kotun soji ta daure wasu dakarun Majalisar Dinkin Duniya biyu masu aikin tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka saboda amfani da Facebook.

An same su da laifin kulla zumunta da wata mata a shafin Facebook inda suka yi ta tura wa wata mata hotunan bidiyo, ita kuma ta sanya hotunan a Facebook tare da rubuta bayanan batanci game da sojoji.

Hakan ya sa an tuhumi dakarun da saba wa dokar aiki da nuna rashin ladabi.

Bayan aikin tabbatar da tsaro na tsawon kusan shekaru biyu da dakarun MDD din ‘yan asalin Kamaru suka yi a Jamhuriyar tsakiyar Afrika, a yanzu kuma za su yi zaman gidan yari na soji a birnin Yaounde.

Daya daga cikin dakarun ya bayar da tabbacin cewa a watan Agusta na shekarar 2013 a lokacin da yake aikin tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, ya samu gayyatar wata mata a shafinsa na Facebook inda ta neme shi da su kulla abota.

Daga bisani dai sai ya amince mata.

Amma bayan haka sai ya aika mata da wasikar gayyata don ganawa da ita ke-ke-da-ke-ke inda ita kuma ba ta amsa bukatar ba.

Daga baya ne sai matar ta fara wallafa wasu hotuna da kuma bayanai masu barazanar tayar da hankali a kan tawagar dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Watanni biyu bayan dawowarsa daga wannan aiki, kawai sai aka aika masa sammaci domin ya bayar da wasu bayanai game da tuhumarsa da ake yi da kulla hulda da wata mata game da sakon hotunan bidiyon da ya dinga aika mata.

Sojan dai ya amsa cewa sun dinga yin musayar hotunan bidiyo a tsakaninsu tare da takwaran aikinsa da suke tsare a yanzu haka.

Amma kuma ya yi mamaki da kuma nuna shakku game da mutumin da ya sanya hotunan bidiyon da suka jefa shi a cikin wani hali.

Babban lauyan Gwamnati kuma ya ce takwaran aikin soja na farko da aka tsare su tare yana da shafukan Facebook hudu daban-daban, inda kuma yake amfani da sunaye daban-daban.

Sai dai sojan ya musanta zargin.

Babban lauyan na gwamnati ya ce haka ne ya kai ga yanke wa mutumin hukunci mai tsanani.

An bai wa sojojin zuwa ranar 9 ga watan Disamba domin daukaka kara.

Dambe: ‘Da wuya kudi su bar McGregor ya dawo fage’


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Conor McGregor da Dana White a watan Yuli na 2017

Shugaban hukumar damben hannu da kafa ta duniya, UFC, Dana White ya ce hukumar na kokarin kulla wata sabuwar yarjejeniya da zakaran damben, dan Ireland Conor McGregor, amma kuma ya ce kila shagon ba zai sake dawowa fageba.

McGregor bai yi dambe ba a karkashin hukumar tun bayan da ya yi wa Eddie Alvarez dukan kawo-wuka a watan Nuwamba na 2016.

Shugaban yana ganin tun da McGregor yanzu ya zama daya daga cikin attajiran ‘yan wasa a duniya bayan damben boksin din da ya yi da Floyd Mayweather Jr a farkon shekaran nan, akwai yuwuwar ba zai sake dambe ba a karkashin hukumar.

Da yake jawabi a hedikwatar hukumar a Las Vegas White ya ce, kila Conor ba zai sake damben ba, saboda ya mallaki dala miliyan 100, ”domin ina da mutanen da suka samu kudin da bai kai haka ba, wadanda lauyoyi ne, kuma duk tsawon rayuwarsu makaranta suka sani, amma yanzu sun bar aiki.”

Saudiyya ta saki Yerima Miteb bayan ya amince ya biya $1bn


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yerima Miteb na daya daga cikin fitattun Yerimomi a masarautar da aka tsare a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa

Hukumomi a kasar Saudiyya sun saki Yarima Miteb bin Abdullah bayan ya kwashe makonni uku a tsare bisa zargin cin hanci da rashawa.

Yarima Miteb na cikin mutum 200 da suka hada da yarimomi da ministoci da kuma manyan ‘yan kasuwa da aka kama a kasar a ranar 4 ga watan Nuwamba, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Ya kuma amince ya biya fiye da dala biliyan daya ga hukumomin kasar.

Jami’ai sun ce akwai wasu mutum uku da suka amince su biya gwamnati makuden kudade domin a sake su.

Kawo yanzu dai Yarima Miteb, wanda ake kallo a matsayin daya daga cikin yarimomi da za su gaji saurautar kasar bai ce komai ba kan al’amarin.

Babu tabbaci a kan ko ya na da ‘yancin yin walwala ko kuma har yanzu yana zaman daurin talala ne.

Yarima Miteb bin Abdullah mai shekaru 65 na daga cikin fitattun Yarimomi da kwamitin yaki da cin hanci da rashawa ya tsare karkashin jagorancin dan uwansa, Yarima Mohammed bin Salman mai shekaru 32.

Haka kuma Yarima Miteb shi ne tsohon ministan tsaron cikin gida mai kula da dakarun tsaro su kimanin 100,000.

Daga cikin ayyukansa na ministan tsaron cikin gida shi ne samar da tsaro ga manyan sarakuna, sai dai an sauke shi daga kan mukaminsa ‘yan sa’o’i kafin a tsare shi.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli bidiyon otel din da Saudiyya ta mayar gidan yari

Wani jami’i cikin masu binciken ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, an cimma yarjejeniya da Yarima Miteb bayan ya amince akwai hannunsa a wata badakala ta cin hanci.

Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana sunayen sauran mutane 208 da babban mai shigar da kara ya ce ana yi musu tambayoyi ba.

Haka kuma ba a bayyana tuhume-tuhumen da suke fuskanta ba, kuma ana kyautata zaton ba a ba su damar ganawa da lauyoyinsu ba.

Rahotanni sun ce an tsare Yarima Miteb ne a Otel din Ritz-Carlton da ke Riyadh tare da dan uwansa, Yerima Turki bin Abdullah tsohon gwamnan Riyadh.

Sauran wadanda aka tsare dasu sun hada da attajirin nan mai zuba jari Yarima Alwaleed bin Talal da Yarima Alwalid al-Ibrahim mai gidan talbijin na MBC.

Akwai kuma Amr al-Dabbagh, tsohon shugaban hukumar kula da harkokin kasuwanci da kuma Khalid al-Tuwaijri, tsohon shugaban kotu.

A wata hira da jaridar New York Times, Yarima Mohammed bin Salman ya ce: ”Kashi 95 cikin 100 na wadanda ake tsare da su sun amince su mikawa gwamnati kudade da kadarori bayan mun nuna musu takardun da muke da su.”

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Yerima Mohammed bin Salman ya ce gwamnati na fatan kwato kimanin dala biliyan $100bn

Wasu ‘yan kasar Saudiyya dai sun yi marhabin da matakin yaki da cin hanci da rashawa da aka kaddamar.

Kuma da yawa daga cikin ‘yan kasar na fatan cewa gwamnati za ta yi amfani da kudaden da aka kwato don yin ayyukan da za su amfani al’umma.

West Brom ta dauki Alan Pardew koci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nadin Alan Pardew ( na dama) na nufin shi da Tony Pulis dukkaninsu sun yi kocin West Brom da Crystal Palace a gasar Premier

West Brom ta dauki tsohon kocin Newcastle da Crystal Palace Alan Pardew a matsayin sabon mai horad da ‘yan wasanta har zuwa karshen kakar 2019-20.

Kungiyar ta kori Tony Pulis a ranar 20 ga watan nan na Nuwamba bayan wasanni goma na Premier da ya jagorance ta ba tare da nasara ba, kuma take maki daya tsakaninta da rukunin faduwa daga gasar.

Pardew mai shekara 56 ba shi da aiki tun bayan da Crystal Palace ta kore shi a watan Disamba na 2016.

Kocin zai jagoranci kungiyar a wasansa na farko a gida da Palace a gasar Premier ranar Asabar biyu ga watan Disamba (15:00 GMT).

Bayan nan ne kuma Albion din za ta je gidan Liverpool da kuma Swansea kafin ta karbi bakuncin Manchester United.

Pardew wanda ya yi kocin Reading da West Ham da Charlton da kuma Southampton a tsawon shekara 18 na aikinsa, sau biyu yana rashin nasara a wasan karshe na kofin FA.

Kocin ya yi fama da takaddama iri daban-daban, kamar lokacin da yake West Ham a 2006, ya yi fito-na-fito da kocin Arsenal, Arsene Wenger.

Sannan kuma a watan Janairu na 2014 lokacin yana Newcastle, ya zagi kocin Manchester City na lokacin Manuel Pellegrini.

Wata biyu bayan wannan an ci tararsa fam 100,000, sannan kuma aka yi masa gargadi a kan karo da ya yi wa dan wasan tsakiya na Hull City David Meyler.

Sam Allardayce na dab da zama kocin Everton


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sam Allardyce ya ce ba shi da wani buri na sake zama kociya bayan da ya bar Crystal Palace

Sam Allardyce zai kammala kulla yarjejeniyar zama kocin kungiyar Everton ta Premier a ranar Larabar nan, sakamakon fafutukar da take yi ta fita daga halin katabus da take ciki.

Tsohon kocin na Ingila mai shekara 63 zai zama magajin Ronald Koeman, wanda aka kora a watan Oktoba yayin da kungiyar ke matsayi na 18 a tebur.

David Unsworth wanda ke zaman kocin kungiyar na rikon kwarya shi ne zai jagorance ta a wasan da za ta je gidan West Ham, wato Goodison Park da karfe 8:00 na dare agogon GMT, a Larabar nan.

Ba wani aiki da Allardyce yake yi tun lokacin da ya ajiye aiki da Crystal Palace a watan Mayu.

Ya sauka ne bayan wata biyar kawai a kai, wanda shi ne aikinsa na farko tun bayan wasa daya da ya jagoranci Ingila, bayan da ya jagoranci kungiyar ta yi nasara a wasa takwas a cikin 21, ta kammala a matsayi na 14 a tebur.

Yanzu Everton tana ta 17 a tebur, kuma ta yi nasara a wasa daya ne kawai a cikin bakwai da ta yi na kowace gasa a karkashin jagorancin Unsworth, wanda shi ne kocin matasan kungiyar ‘yan kasa da shekara 23.

Koeman dan Holland ya kai Everton matsayi na bakwai a tebur a kakarsa ta farko a kungiyar a bara, amma an kore shi kwana daya bayan da a gida Arsenal ta doke su da ci 5-2 a ranar 22 ga watan Oktoba.

Kungiyar ta kashe sama da fam miliyan 130 wajen sayen sabbin ‘yan wasa, amma tana fama a yanzu ba tare da Romelu Lukaku ba, wanda ya fi ci mata kwallo a kakar da ta gabata, wanda Manchester United ta saya fam miliyan 75 a watan Yuli.

An kara kashe sojojin Kamaru


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A halin yanzu an kashe sojojin Kamaru takwas a yankin cikin wata guda

Hukumomi a Jamhuriyyar Kamaru sun ce an kashe sojojin kasar hudu a yankin da ake amfani da harshen Ingilashi dake kudu maso yammacin kasar.

Wasu majiyoyin a rundunar soji sun ce an kashe jami’an sojojin ne da sanyin safiyar Laraba a yankin Mamfe.

Hakan ya kara yawan sojojin kasar da aka kashe a yankin zuwa takwas cikin wata guda.

An dai shafe watanni ana tashe-tashen hankula sakamakon zargin nuna wariya daga bangaren da ake amfani da harshen Faransanci da suka fi rinjaye.

An kuma kashe wasu masu zanga-zanga yayin da aka tsare wasu mutane da dama.

Tashe-tashen hankula da ake fama da shi a yankin kan zargin nuna wariya ya haddasa zaman dar-dar, lamarin da ya janyo wasu neman ballewar yankin daga Jamhuriyar Kamaru.

Sai dai shugaba Paul Biya ya yi kakkausar suka akan masu neman ballewar, inda ya sanya dokar takaita zirga-zirga tare da tsaurara matakan tsaro a yankin.

Za a dawo da ‘yan ci-rani gida — Buhari


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An kai gawawwakin mutane sansanin sojin ruwa na Libya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a koma da dukkan ‘yan Najeriya ‘yan ci-rani da suka makale a Libya gida.

Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata da daddare a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.

Shugaban na Najeriya, wanda ke yin jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, ya sha alwashin rage yawan ‘yan kasar da ke yin ruguguwa wajen zuwa Turai.

Buhari na magana a daidai lokacin da rahotanni suka nuna yadda ake sayar da bakaken fata – cikinsu har da ‘yan Najeriya a kasar Libya – a matsayin bayi a kan kudin da bai wuce $400 ba (N144,000).

Lamarin da ya ya tayar da hankulan sassa daban-daban na duniya, musamman nahiyar Afirka.

“Abin takaici ne yadda ake sayar da ‘yan Najeriya a matsayin bayi tamkar wasu akuyoyi a kan daloli kalilan”, in ji Shugaba Buhari.

Shugaban ya musanta yawan ‘yan Najeriyar da aka ba da rahoton mutuwarsu a lokacin da suke bi ta Bahar Rum domin zuwa Turai a kwanakin bayan.

“An ce ‘yan Najeriya 26 ne suka mutu a Bahar Rum; amma an binne su ba tare da an tantance su ba.

“Sai dai shaidun da mai ba ni shawara kan harkokin kasashe waje Mrs. Abike Dabiri-Erewa ta kawo min su nuna cewa mutum uku ne kawai ‘yan Najeriya,” in ji shugaba Buhari.

Hukumar kaura ta duniya dai ta ce ko da a ranar Talata sai da aka koma da ‘yan Najeriya 140 gida daga Libya, cikin wadanda suka makale a can.

Yadda aka ’tilasta wa’ namiji fito da matar aure


Hakkin mallakar hoto
FALALU DORAYI

Image caption

Fim din “Na Manga” na cike da ban dariya

Fitaccen daraktan fina-finan Kannywood Falalu A. Dorayi ya ce ya hada fim din “Auren Manga” ne saboda ya bai wa mutane dariya da sanya nishadi a zukatan masu kallo.

A tattaunawarsa da Nasidi Adamu Yahaya, Baba Falalu, kamar yadda aka fi saninsa a Kannywood, ya ce ya gina maudu’in fim din ne domin ya sha bamban da sauran fina-finan barkwanci.

A cewarsa, “Na rubuta fim din “Auren Manga” ne sama da shekara biyar da suka wuce da zummar marigayi Rabilu Musa Dan Ibro ya zama babban jaruminsa, amma sai Allah ya yi masa rasuwa.

“Don haka ne na yi gyare-gyare a cikinsa kuma ni da kaina na zama babban jarumin cikin fim din”.

“Babban abin da yake koyarwa shi ne yadda ake tilasta wa namiji, wato Manga ya fito da matar da zai aura. Ka ga hakan ya bambanta da yadda aka saba.”

Falalu A. Dorayi ya ce mai daukar nauyin shirin Yakub Usman, ya kashe sama da naira miliyan biyu wurin hada fim din.

Fim din ya hada manyan jarumai irinsu Adam A Zango da Hadiza Gabon da Sulaiman Yahaya (Bosho) da Baban Chinedu da kuma Falalu Dorayi.

‘Za mu iya harba sabon makami mai linzami kan Amurka gaba daya’


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Koriya ta sha yin gwajin makami mai linzami a wannan shekarar har da ma wannan da ta kaddamar a watan Yuli

Koriya Ta Arewa ta ce ta samu nasarar yin gwajin wani sabon makami mai linzami (ICBM) wanda zai iya kai wa ga baki dayan kasar Amurka idan aka harba shi.

Gidan talbijin na kasar ya ce a yanzu Koriya Ta Arewa ta cimma burinta na zama mamallakiyar makami mai linzami.

An kaddamar da makami mai linzamin ne samfurin Hwasong-15, wanda aka bayyana shi da mafi karfi a ranar Laraba da sassafe.

Ya sauka a tekun Japan amma ya yi tafiya mafi tsawo da duk wani makami mai linzami da Koriya Ta Arewa ta taba gwajin harba shi a baya.

Gwajin, wanda ya bijirewa takunkumin kasa da kasa da aka kakabawa shirin makaman Koriya Ta Arewan, ya sha suka daga kasashen duniya, inda har Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa.

Koriya Ta Kudu ta mayar da martani ta hanyar yin atisayen harbe-harbe, inda ta kaddamar da daya daga cikin makamai masu linzaminta ita ma.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Koriya ta Kudu ma ta kaddamar da makami mai linzami samfurin Hyunmoo-2 a matsayin mayar da martani a ranar Laraba

Mene ne ainihin abin da Koriya Ta Arewa ke cewa?

An sanar da labarin kaddamar da harin ne a gidan talbijin na kasar da tsakar rana, da kuma a wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na kasar KCNA ya fitar.

Koriya Ta Arewa ta ce makami mai linzamin ya kai nisan kilomita 4,475 a sararin samaniya, ya kuma yi tafiyar kilomita 950 cikin minti 53, kamar dai yadda rundunar sojin Korita Ta Kudu ta kiyasta.

Sai dai a wannan karon makamin da aka harbadin bai bi ta sararin samaniyar Japan ba kamar yadda aka sha yi a baya, ya kuma sauka ne a nisan kilomita 250 daga gabar tekun kasar, a cewar jami’an kasar Japan.

Koriya Ta Arewa dai ta sha cewa makaminta zai iya kai wa Amurka, amma wannan ne karo na farko da ta ce za ta iya yin hakan da wani sabon samfurin makami mai linzami da ta kaddamar.

Kamfanin dillancin labaran kasar KCNA, ya kara da cewa shugaban kasar Kim Jong-un wanda shi ne ya sanya hannu don kaddamar da makamin, ya ayyana cike da alfahari cewa: ‘a yanzu mun kai ga cimma gagarumar nasara wajen kafa tarihi na zama kasa mamallakiyar makami mai linzami.”

Rahoton ya ce: ‘a matsayinta na mamallakiyar makami mai linzami kuma kasa mai son zaman lafiya, Koriya Ta Arewa za ta yi duk wani kokari don kare da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya.”

Rahoton KCNA din ya kara da cewa, kasar na kera makamai masu linzami ne saboda kare kanta daga ‘mulkin danniyar Amurka’ da kuma bata mata suna da shirinta na makami mai linzami.

Shin makamin na iya kai wa Amurka da gaske?

Wani bincike da wata kungiyar masana kimiyya ta Amurka ta yi ya nuna cewa makami mai linzamin na iya tafiyar fiye da kilomita 13,000, ta yadda hakan zai sa ya iya kai wa ga illahirin kasar Amurka.

Sai dai duk da haka binciken ya kara da cewa, makami mai linzamin ba zai iya daukar makamai da yawa a kansa har ya yi tafiya mai nisan zango irin haka ba.

Amma Koriya Ta Arewa ta ce sabon makamin samfurin Hwasong-15 zai iya kai wa ko ina a Amurka dauke da wasu tarin makaman a kansa.


Yaya duniya ta ji da wannan gwaji?

Kafin Koriya Ta Arewa ta fitar da sanarwa, sakataren tsaro na Amurka James Mattis ya ce gwajin makamin ya fi duk wanda aka taba yi a baya muni, ya kuma ce wannan barazana ce ga duniya baki daya.

Wanann gwaji dai shi ne na baya-bayan nan a gwaje-gwajen makamai da Koriya ke yi wanda ya jawo fargaba sosai, ganin yadda Koriyar take biris da sukar da take sha, take kuma ci gaba da shirinta na makami mai linzami.

A watan Satumba ne Koriya Ta Arewa ta kaddamar da wani gwajin makami mai linzami, kuma a cikin watan ne ta kaddamar da irin wannan gwaji har sau shida.

Buhari na halartar taron hadin guiwa na AU/EU


Hakkin mallakar hoto
PRESIDENCY

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari zai jaddada kudirin Najeriya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika da tarayyar turai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Abidjan na kasar Côte d’Ivoire don halartar taron hadin guiwa tsakanin kungiyar tarayyar Afrika da tarayyar turai.

Ana saran shugabannin kasashen Afrika 55 dana tarayyar turai 28 ne za su halarci taron hadin guiwar karo na biyar.

Wata sanarwa daga kakakin shugaban kasar Femi Adesina ta ce ba ya ga shugabannin kasashen, ana saran wakilai daga kasashe mambobin kungiyar da wasu kungiyoyi na kasa da kasa za su halarci taron.

Sanarwar ta kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi amfani da taron na kwanaki biyu don jaddada kudirin Najeriya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika da tarayyar turai.

Hakkin mallakar hoto
PRESIDENCY

Image caption

Ana saran shugabannin kasashen Afrika 55 dana tarayyar turai 28 ne zasu halarci taron hadin guiwar karo na biyar.

Gwamnonin jihohin Akwa Ibom da Bauchi da wasu ministoci tare da jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ne ke cikin tawagar shugaban kasar.

An halasta allurar kashe maras lafiya a Australia


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Magoya bayan allurar taimaka wa maras lafiya mutuwa sun rungumi juna a zauren majalisar dokokin Victoria makon gobe

Wata jiha a kasar Australia ta halasta taimaka wa marasa lafiya don a kashe shi da allurar mutuwa.

Majalisar dokokin Victoria ta kada kuri’ar amince wa marasa lafiyan da ke fama da cutar ajali, damar su bukaci allurar da za ta karasa su daga watan Yunin 2019.

Yankin Northern Territory mai jama’a nan da can a Australia ne cikin 1995, ya fara ba da hurumi a duniya don marasa lafiya su kashe kansu da taimakon likitoci.

Sai dai majalisar dokokin tarayyar kasar ta kifar da dokar bayan shekara biyu.

Amma a wannan karo, ba ta da ikon sauke dokokin Victoria, jiha ta biyu mafi girma a kasar.

An amince da muhimmiyar dokar ce bayan tafka muhawara tsawon sama da sa’a 100, ciki har da zaman da aka shafe tsawon dare har karo biyu.

Dokar na da nufin ba wa marasa lafiyan da ke fama da cutar da ajali a jiha ta biyu mafi yawan jama’a a Australia, ‘yancin gabatar da bukatar a yi musu allurar mutuwa daga tsakiyar 2019.

Ta yi tanadin cewa jazaman ne sai maras lafiya ya kai akalla shekara 18 kuma idan ya rage musu bai fi wata shida da rayuwa a duniya ba.

Firimiyan jihar Victoria Daniel Andrews ya ce “Ina alfahari a yau cewa mun sanya tausayawa cikin tsakiyar harkar dokoki da mulkinmu.”

“Siyasa kenan mafi inganci, ita Victoria ke yi wato yin abin da ya dace – jagorantar kasarmu.”

Kariya daga azabtarwa

An tsara dokar ce don marasa lafiyan da ke cikin matsanancin ciwo. Tana da matakan kariya guda 68, ciki har da:

Sai maras lafiya ya gabatar da bukata uku ga musammam kwararrun likitoci don su dauki ransa

Sai wani kwamiti na musammam ya yi bitar duk bukatun

Azabtar da maras lafiya yayin daukar ransa zai kasance aikata laifi

Bugu da kari, sai maras lafiya ya zauna a Victoria tsawon akalla wata 12 kuma sai ya kasance yana cikin hankalinsa.

Gwamnati ta ba ‘yar shekara 7 izinin shan wiwi


Hakkin mallakar hoto
VERA TWOMEY

Image caption

Ava na fama da wata matsananciyar cutar farfadiya ce da ake kira larurar Dravet

Ministan lafiyan Jamhuriyar Ireland ya ba da izini ga wata yarinya ‘yar shekara bakwai daga yankin County Cork ta rika samun tabar wiwi don maganin larurar da take fama da ita.

Ava Barry na fama da wata matsananciyar farfadiya da ake kira larurar Dravet.

A ranar Talata ce, Simon Harris ya fada wa majalisar dokokin Ireland wato Dáil cewa ko da yake ba zai iya bayani a kan daidaikun mutane ba, amma ya sa hannu kan bukatar ba da lasisi a karo na uku.

A cikin wani sakon bidiyo mahaifiyarta Vera Twomey na cewa ta ji “labari mai dadi”.

“An ba wa Ava lasisin shan wiwi don magani kuma muna nan zuwa gida. Za mu zo gida don bikin kirsimeti, ita kuma tana samun sauki.”

Jagoran jam’iyyar Fianna Fáil, Micheál Martin ya fada wa zauren majalisar dokokin cewa a yanzu Ava tana samun kulawa a karkashin wani shiri ta hanyar wani likitan jijiya.

Ya kuma nemi bijiro da wani tallafi don samar da kafa cikin sauri ga kananan yaran da ke fama da farfadiyar da ba ta jin magani.

Ava na fama da farfadiyar da kan shafe tsawon kama daga minti biyu har zuwa sa’o’i kuma zafinta idan ta tashi yakan bambanta.

Gwaje-gwajen da aka yi sun nuna cewa larurar Dravet takan lafa idan an yi amfani da wani nau’in tabar wiwi.

A baya, Misis Twomey ta bukaci majalisar dokokin Jamhuriyar Ireland ta halasta amfani da wiwi a matsayin magani.

A cikin watan Nuwamban 2016, ta fara wani tattaki daga gidanta da ke kauyen Aghabullogue mai tazara zuwa ginin majalisar dokoki a Dublin don bayyana alfanun wannan batu.

Yayin tattakin na tsawon mil 150, ta roki ministan lafiyan Ireland ta ji kukanta a wani sako da ta wallafa ta shafin Facebook.

Ministan Simon Harris ya tuntube ta daga bisani kuma ya sanar da shirin yi wa manufar gwamnati kan amfani da wiwi garambawul.

Gwamnatin Kaduna ta kori ma’aikata fiye da 4,000


Hakkin mallakar hoto
KADUNA STATE GOVERNMENT

Image caption

A baya ma jihar Kaduna ta sanar da korar malaman firamare sama da 20,000 saboda a fadarta rashin kwarewarsu.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana sallamar ma’aikatan kananan hukumominta fiye da 4,000 don rage kudaden da take kashewa a matsayin albashi da kuma bunkasa kudaden gudanar da ayyukan raya kasa.

Gwamnatin wadda ta tabbatar da haka a wani taron manema labarai a Kaduna, ta ce matakin ya zama dole don kuwa akasarin ma’aikatan na karbar albashi ne ba tare da aikin komai ba.

Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Ja’afaru Sani ya ce gwamnati ta yi wa ma’aikata 3,159 ritaya, yayin da kuma ta kori wasu 8,083 daga aiki.

Ya ce su kuma za su samu albashin wata daya kuma a ba su garatuti amma ba za a biya su fensho ba.

A cewarsa matakin zai ba wa kananan hukumomin jihar Kaduna damar gudanar da ayyukan raya kasa da kuma biyan albashi ba tare da an tallafa musu ba.

Wakilin BBC a Kaduna Nura Muhammad Ringim ya ce matakin ka iya haifar da irin ce-ce-ku-cen da aka yi a baya sakamakon sanarwar sallamar malaman makarantun firamare sama da 20,000 saboda gaza samun maki 75 a wata jarrabawar ‘yan aji hudu da ta yi musu.

Duk da bayanan da gwamnati ta sha yi kan fa’idar matakin amma wasu na ganin hakan a matsayin bi-ta-da-kulli ga jama’a kawai, in ji shi.

Alhaji Ja’afaru Sani ya ce idan martabar kananan hukumomi ta dawo kuma talaka ya san cewa karamar hukuma tana yi masa aikin da ya dace, shi kansa yadda zai rika hulda da ita zai sauya.

Premier: Leicester ta yi wa Tottenham bazata da 2-1


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Cin da Jamie Vardy ya yi shi ne na 100 a gasarsa ta lig

Tottenham ta kasa amfani da tarin damar da ta samu a wasan da mai masaukinta Leicester ta doke ta da ci 2-1, har ta dago zuwa tsakiyar tebur, a matsayin ta 9 da maki 17.

Jamie Vardy ne ya fara ci wa Leicester kwallo a minti na 13, kafin kuma Riyad Mahrez ya ci ta biyu ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Saura minti 12 a tashi daga wasa ne sai dodon-ragar ‘yan Tottenham harry kane ya farke kwallo daya, bayan da Christian Eriksen ya barar da wata dama.

Yayin da bakin suka tashi tsaye wajen rama ta biyu kafin alkalin wasa Anthony Taylor ya tashi Fernando Llorente shi ma ya barar da wata damar.

Yanzu Tottenham ta koma ta biyar a tebur da maki 24, bayan wasa 14 na gasar ta Premier

Copa del Rey: Real Madrid ta tsallake siradi 2-2 da Fuenlbrada


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gareth Bale ya ceci Real Madrid bayan dawowarsa daga jinya

Gareth Bale ya ceci Real Madrid a hannun ‘yar karamar kungiya ta gasar mataki na uku ta Spaniya Fuenlbrada inda ya yi sanadin cin kwallo biyu bayan dawowarsa daga jinya, a gasar Copa del Rey.

Dan wasan gaban na Wales mai shekara, 28, wanda ya shafe wata biyu yana jinyar guiwa da cinya, ya shigo wasan ne daga baya, ya samar da kwallo biyu da Borja Mayoral ya ci suka yi canjaras a wasan na karawa ta biyu.

Luis Milla ne ya fara daga ragar kungiyar ta Zinedine Zidane 1-0 a minti na 25 a wasan na Santiago Bernabeu, kafin a sako Gareth Bale, wanda shigowarsa ya sauya lissafin a minti na 63, inda ya dauko wa Mayoral kwallo ta gefe ya farke da ka.

kafin daga bisani ana shirin tashi a minti na 89 Alvaro Portilla ya farke wa bakin matasan.

Kusan minti bakwai tsakani ne kuma sai Bale din ya sake kai wani hari, wanda mai tsaron ragar bakin ya amayar da kwallon, Mayoral bai yi wata-wata ba ya mayar da ita raga.

Haka aka tunkari lokacin karshen wasan kafin minti na 89 Alvaro Portilla ya farke wa bakin matasan.

Nasarar da Real ta yi 2-0 a haduwarsu ta farko ta ba wa zakarun kofin na Copa del Rey sau 19, damar wucewa zuwa matakin kungiyoyi 16, na sili-daya-kwale.

Premier: Manchester United ta doke watford 4-2


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ashley Young ya ci kwallo biyu a Premier a karon farko tun watan Maris na 2012

Ashley Young ya zura kwallo biyu a ragar tsohuwar kungiyarsa a wasan da Manchester United ta doke Watford 4-2 a wasan Premier na mako na 14.

United ta jure wa matsin masu masaukin nasu a kusan karshen wasan, wanda suka ci kwallo uku a cikin minti 13 a kashin farko na wasan, inda ta rage ratar da ke tsakaninta da ta daya a tebur Manchester City zuwa maki biyar.

Ko da yake kungiyar ta Pep Guardiola za ta iya sake ba su wannan tazara ta maki takwas, idan ta hadu da Southampton ranar Laraba.

Young ya afara cin ta farko ne minti 19 da shiga fili, bayan minti shida kuma ya kara ta biyu.

Bayan minti bakwai kuma sai Martial ya ci tasa wadda ita ce ta uku da manchester United din ta zura.

Can an nitsa zuwa minti 77 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ‘yan Watford sun matsa wa United, sai suka samu fanareti wadda Troy Deeney ya kadar da De Gea ya jefa ta a raga.

Daga nan ne kuma suka kara samun karfin guiwa suka kai wata kora da Abdoulaye Doucoure ya kara ci musu ta biyu a minti na 84.

Sai dai kuma minti biyu tsakani ne sai Lingard ya yi musu ta’annati ya ci wa United ta hudu wadda ta sanyaya jikin ‘yan Watford din.

A ranar Asabar Watford ta takwas da maki 21, za ta kara karbar bakuncin Tottenham (lokaci15:00 GMT) yayin da Manchester United za ta je gidan Arsenal a wannan rana (lokaci 17:30 GMT).

Tsohon matashin dan wasan Man United John Cofie ya koma Derry City


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

John Cofie ya ci wa Manchester United kwallo a gasar Milk Cup a 2010

Wani dan wasa da Manchester United ta taba saye fam miliyan daya lokacin yana shekara 14, zai taka leda a kungiyar Derry City da ke gasar lig din Ireland a kaka mai zuwa.

Dan wasan na Ingila haifaffe kuma dan asalin Ghana, John Cofie, wanda yanzu yake shekara 24, na daya daga cikin ‘yan wasa biyar da kungiyar ta Ireland ta saya ranar Talata.

A shekara ta 2007 Manchester United ta kasa abokan hamayyarta a Premier, Liverpool da Chelsea a zawarcin matashin dan wasan wanda a lokacin yana Burnley.

Manchester United ta saye shi, sannan ya tafi Royal Antwerp, da Barnsley da kum Southport, in ji kocin Derry Kenny Shiels, wanda ya kara da cewa wannan wata dama ce ga dan wasan da zai farfado da sana’arsa.

Za a fara amfani da fasahar tantance shigar kwallo raga a Afirka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fifa za ta yi amfani da fasahar ta bidiyo (VAR) a gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha

Za a yi amfani da fasahar tantance shigar kwallo raga (VAR) a karon farko a wata gasa ta Afirka, a lokacin wasan cin kofin Afirka na ‘yan wasan da ke taka leda a gida (CHAN) a Morocco.

Kwamitin alkalan wasa na hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf), shi ne ya amince da fara amfani da fasahar, ta amfani da hoton bidiyo a lokacin taronsa ranar 27 ga watan Nuwamba a birnin Alkahira na Masar.

Za a fara gwajin fasahar ne a matakin wasan dab da na kusa da karshe na gasar wadda za a fara ranar 13 ga watan Janairu.

Kowanne daga cikin birane hudu na kasar ta Moroccon, wato Casablanca da Marrakech da Tangiers da kuma Agadir wadanda za a gudanar da gasar a cikinsa za a yi wasan dab da na kusa da karshe daya a can.

Alkalan wasan da aka zaba za su yi alkalancin wasanni a gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi a Rasha, da kuma wadanda aka ba wa horo a kan fasahar, su za su yi alkalancin wasa a gasar, ta ‘yan wasan da suke taka leda a lig-lig dinsu na gida.

An fara amfani da fasahar ta tantance shigar kwallo raga ne a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi na kasashe ta 2017 da aka yi a Rasha, inda aka samu ra’ayoyi daban-daban kan amfani da ita.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa tana son yin amfani da fasahar a gasar cin kofin duniya da za a yi mai zuwa.

Abubuwan kara kuzari: Rasha ta dora alhaki kan jami’inta


Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Mista Rodchenkov ya tsere zuwa Amurka bayan da kotu a Moscow ta bayar da sammacin kama shi

Hukumomin Rasha sun zargi mutumin da ya kwarmata zargin da ake yi wa kasar na kokarin boye maganar amfani da abubuwan kara kuzari da ‘yan wasanta suka yi a gasar Olympics ta Sochi ta 2014, da cewa shi ne ya samar da kwayoyin.

Sashen bincike na rasha ya ce ‘yan wasan ba su san cewa Grigory Rodchenkov na ba su abubuwan kara kuzarin ba.

Shi dai Rodchenkov shi ne darektan dakin binciken kimiyya na hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasa ta kasar.

Wannan zargin ya zo ne sati daya kafin Rasha ta san matsayinta kan ko za a dage mata hukuncin da aka yi mata na hana ta shiga wasanni, saboda hannun da take da shi wajen ba wa ‘yan wasanta abubuwan kara kuzari, kafin gasar wasannin da za a yi ta Pyeongchang a 2018.

A wata sanarwa da kwamitin bincike na kasar ya fitar, hukumomin sun ce an gano cewa Rodchenkov ne da kansa ya ba wa ‘yan wasan da masu horar da su magunguna wadanda ba su san abubuwan da suke dauke da su ba, wadanda daga baya aka ce suna dauke da sinadaran kara kuzari

A baya hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasa ta duniya ta zargi Rodchenkov da nema da kuma karbar cin hanci, ya batar da sheda 1,400 da jini da kuma fitsari.

A watan Janairu na 2016 ya gudu zuwa Amurka bayan kotu a Moscow ta bayar da sammacin kama shi.

Ya kamata a hukunta Lukaku – Ian Wright


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallo daya kawai Romelu Lukaku ya ci wa Manchester United a wasansa 10 na baya bayan nan

Ya kamata a ce an haramta wa dan wasan gaba na manchester United Romelu Lukaku buga wasanni saboda dukan da ya yi wa dan bayan Brighton Gaetan Bong in ji mai yi wa BBC fashin baki Ian Wright.

Lamarin ya faru ne a wasan Premier wanda Manchester United ta doke Brighton 1-0, ranar Asabar, amma kuma alkalin wasa Neil Swarbrick, bai gani ba a lokacin.

Bayan da wani kwamitin bincike na hukumar kwallon kafa ta Ingial ya yi nazari a kai ya ce babu bukatar yin wani hukunci.

Ian Wright, tsohon dan wasan Arsenal da Ingila ya ce, yana ganin abin a lokacin ya yi tunanin cewa kila za a yi nazari a kai. Sai ka yi tunanin me ya sa ba a hukunta shi ba?

Tsohon dan wasan ya ce akwai cikakkiyar sheda da ya kamata a hukunta shi, domin ya haure shi har sau biyu, amma bai san dalilin da ya sa aka kyale shi ba.

Ba zan bi Atiku Abubakar ba — Bindow


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Atiku ya ce APC ta gaza

Gwamnan jihar Adamawa da ke Najeriya Umar Jibrilla Bindow, ya ce ba zai bi sahun tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar wurin ficewa daga jan’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin kasar ba.

A makon jiya ne Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar, yana mai zarginta da rashin cika alkawuran da ta yi wa ‘yan kasar da kuma tabbatar da dimokradiyyar cikin gida.

Sai dai gwamnan jihar Adamawa, mahaifar Atiku Abubakar ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa ba shi da niyyar yin biyayya ga Atiku Abubakar ta fice daga APC.

Ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ranar Talata.

Gwamna Bindow ya ce zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC har tsawon rayuwarsa.

A cewarsa, “Ina daya daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar APC. A lokacin da nake dan majalisar dattawa tare da shugaban majalisa na yanzu wanda ya yi bakin kokarinsa wurin ganin dukkan mambobin majalisa da dama sun bi sahu domin kafa APC. Don haka ban ga dalilin da zai sa na fice daga gidan da na gina ba”.

“Saboda haka ni dan jam’iyyar APC ne har tsawon rayuwata,” in ji shi.

A wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya fitar tun da fari, ya ce ya bar jam’iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya na kawo sauyin halin da kasar take ciki.

Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman-zamansa jagororin jam’iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam’iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam’iyyarsa ta PDP.

Atiku ya kara da cewa an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba.

“A kan wannan dalili ne mambobin jam’iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin bin kundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci.”

“A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam’iyyar a watan Fabrairun 2014, don a lokacin ba ni da jam’iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Duk jam’iyyar da ba za ta kula da al’amuran matasa ba to matacciyar jam’iyya ce. Makomar kasar nan tana hannun matasa ne.”

A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauye-sauyen jam’iyya daga waccar zuwa wata.

Gidan tsohon shugaban Boko Haram zai zama gidan kayan tarihi


Image caption

A shekarar 2009 ne aka kashe Mohammed Yusuf, mutumin da ya assasa kungiyar Boko Haram

Gwamnati jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya tana son ta mayar da gidan tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, Mohammed Yusuf, gidan ajiye kayan tarihi.

Yusuf, shi ne mutumin da ya assasa kungiyar Boko Haram, amma an kashe shi a lokacin da yake hannun ‘yan sanda a shekarar 2009, kuma kungiyarsa na ci gaba da kai hare-hare a jihar Borno da ma wasu jihohi a arewa maso gabashin Najeriyar.

Kwamishinan ayyukan cikin gida da watsa labarai da kuma al’adu na jihar Borno, Dr Mohammed Bulama, ya ce gidan ajiye kayan tarihin zai taimaka wajen tattara bayanai game dakungiyar Boko Haram.

Bulama ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, gidan ajiye kayan tarihin zai kawo masu yawon bude ido tare da zama mai amfani ga al’ummar da ke zuwa nan gaba.

Amma mutane da dama suna fargabar cewa yin hakan zai iya raya sunan Muhammad Yusuf har abada.

Daya daga cikin masu wannan fargabar shi ne wani lauya mai fafitikar kare hakkin bil’Adama Anthony Agholahon.

Ya shaida wa BBC cewa wannan ba abu ne mai kyau ba.

“Ya kamata su yi amfani da kwalejin ‘yan sandan da kungiyar ta lalata, ba wai kawai su yi amfani da gidan mutumin da ya kashe mutane ba.”

Wanne suna za a bai wa gidan ajiye kayan tarihin?

Hakkin mallakar hoto
FLORIAN PLAUCHEUR

Image caption

Kungiyar Boko Haram, wadda sunanta na ainihi shi ne Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad, ta lalata wurare da dama a Najeriya tun lokacin da ta fara ayyukanta

Kwamishinan ya bayyana wannan matakin ne a lokacin da ya halarci zaman majalisar raya al’adun gargajiya da yawon bude ido da kuma wayar da kan jama’a a garin Dutse, da ke jihar Jigawa.

Dr Bulama ya ce: “Za a sanya wa wurin suna Markaz. Muna son mu gina gidan ajiye kayan tarihi a wurin in da za a tattara bayanan dukkan abubuwan da suka faru game da yakin kungiyar Boko Haram.”

Mohammed Bulama ya kara da cewa: “A lokacin da kura ta lafa, muna shirin mayar da dajin Sambisa wurin da zai ja hankalin masu yawon bude ido domin nuna wa duniya abin da ya faru a dajin Sambisa.”

Alexis Sanchez da Mesut Ozil ba za su tafi a watan Janairu ba – Wenger


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Alexis Sanchez da Mesut Ozil sun ci wa Arsenal kwallaye 149

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, yana tsammanin dan wasan gaba Alexis Sanchez da kuma dan wasan tsakiya Mesut Ozil za su tsaya a kulob din a lokacin kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu.

Yarjejeniyoyin ‘yan wasan biyu za su kare ne a karshen wannan kakar.

Da aka tambaye shi cewa ko yana tunanin ‘yan wasan biyu za su tsaya a kulob din, Wenger ya ce : “E, kwarai.”

Dan Faransan ya kuma ce dan wasan tsakiyar Ingila, Jack Wilshere yana bukatar ya cigaba da zama a Gunners.

Wenger ya kara da cewa: “Zan yi kokarin ganin ya zauna a nan domin shi wani kwararren dan wasa ne.”

Dan wasan tsakiyar Ingilan ,mai shekara 25, yana fama da raunuka tun lokacin da ya fara taka wa Gunners leda a shekarar 2008, kuma ya je buga wasan aro a Bournemouth a kakar 2016/2017.

An tsaurara tsaro a bikin rantsar da shugaban kasar Kenya


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Sojoji sun rika atiseye gabannin bikin rantsar da shugaban kasar Kenya

Shugaba Uhuru Kenyyata zai sha rantsuwar fara aiki a karo na biyu kuma a wa’adi na karshe ya yinda abokan hammayarsa ke gudanar da zanga zanga.

Hadin gwiwar jamiyun adawa da ake kira NASA sun kuduri anniyar ganin cewa sun yi zanga zanga a birnin Nairobi ya yinda ake bikin ranstar da shugaban kasa a wani bangare na birnin.

Masu zanga zangar sun ce sun shirya zanga zangar ce domin su nuna alhinininsu ga magoyan bayansu da aka kashe a arrangamar da suka yi da ‘yan sanda a cikin makwani biyu da suka gabata.

Sai dai yan sanda sun musanta zargin kuma sun gargadi gammayar jam’iyuun adawa kasar a kan kada su kuskura su gudanar da taron ganganmin.

Yan hammaya dai sun sauya faffitukar da suke yi zuwa wata kungiya da ke nuna tirjiya kan abubuwa da suke faruwa a kasar, bayan da sun janye daga zaben da aka sake yi a watan daya gabata.

Ana dai sa ran cewa shugabannin kasashe duniya fiye da 20 ne zasu halarci bikin ciki har da fira ministan Israila Benjamin Netanyahu.

Ma’aikatan Nigeria sun kusa samun karin albashi


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN GOVERNMENT

Shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari, ya rantsar da kwamitin da zai bayar shawara kan karin albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.

Wata sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin kasar ta ambato Shugaba Buhari yana cewa za ta kara albashin bayan shawara da wani kwamiti da aka kafa a shekarar 2016 ya bayar domin gano yadda za a rage radadin tasirin karin kudin mai kan talakawa.

Shugaba Buhari ya ce yana fatan kwamitin, da ya hada da gwamnoni da shugabannin ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki, zai cimma matsaya kan albashi mafi karanci da ya kamata a biya ma’akaci a Najeriya.

Ana sa ran kwamitin dai zai mika matsayar da ya cimma nan ba da dadewa ba.

A shekara 2016 ne dai aka kara kudin litar mai daga naira 86 zuwa 145 yayin da mafi karancin kudin da ake biyan ma’aikaci a Najeriya ya tsaya akan naira 18,000 kamar yadda yake a da can.

Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN GOVERNMENT

Image caption

Shugaban Najeriyar ya yi kira ga gwamnonin kasar da su biya ma’aikatansu kafin a yi bikin Kiristimeti

Karin kudin mai ya sa kayayyaki sun kara tsada a kasuwa, kuma kudin shiga na ma’aikata kuma bai karu ba.

‘Ana zolayar gwamnatin Buhari kan yaki da cin hanci’


Hakkin mallakar hoto
MINISTRY OF INFORMATION

Image caption

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce ta kwato makuden kudaden da aka sace

Gwamnatin Najeriya ta koka kan yadda wasu kafofin watsa labarai ke mummunar fassara game da yaki da cin hanci da rashawa da shugaban kasar ke aiwatarwa.

Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce kafofin watsa labarai na da ‘yancin sukar gwamnati amma bai kamata su rika yi wa gwamnatin shagube ba.

Mr Lai Muhammed ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a babban taron kungiyar gidajen rediyo da talbijin na kasar a Abuja.

Ministan ya ce a ‘yan kwanakin nan wasu jaridun kasar sun karkata wajen buga kanun labarai dake zolayar yaki da cin hanci da rashawa na gwamnati.

Ya bukaci kafofin watsa labarai da su taimakawa gwamnati wajen yaki da cin hanci da rashawa maimakon su koma gefe a matsayin ‘yan kallo.

Alhaji Lai Mohammed ya ce yaki da cin hanci ba zai yiwuwa ba matukar kafofin watsa labarai ba su shigo ciki ba.

Ministan ya ce kuma yi zargin cewa maida hankali ga kura-kuran gwamnati kan yaki da cin hanci da wasu kafofin watsa labarai ke yi tamkar nuna goyon baya ne ga masu satar kudaden gwamnati.

Ya kara da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta kwato makuden kudaden da aka sace karkashin shirinta na bada tukaici ga duk wanda ya fallasa masu satar kudaden gwamnati.

Tsohon Darektan Chelsea Emenalo ya koma Monaco


Hakkin mallakar hoto
MONACO

Image caption

Michael Emenalo tare damataimakin shugaban kungiyar Monaco Vadim Vasilyev

An nada tsohon darektan wasanni na Chelsea Micheal Emenalo a matsayin darektan wasanni na kungiyar Monaco ta Faransa.

A sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce Emenalo mai shekara 52 wanda ya taka wa Najeriya leda a gasar kofin duniya ta 1994, zai tafiyar da dukkanin harkokin wasanni na kungiyar ta Ligue 1.

Emenalo ya je Chelsea ne a 2007, kuma ya yi aiki a kungiyar ta Ingila a fannin nema mata ‘yan wasa da kuma horarwa, kafin ya zama darektanta na wasa a 2011.

Tsohon dan wasan ya ce ya yi amanna wannan sauyin aiki da ya yi daga Chelsea zuwa Monaco abu ne da ya dace.

Emenalo wanda tsohon dan wasan baya ne a lokacin yana taka leda ya yi wasa a gasar Amurka a shekarun 1990, sannan kuma ya yi kungiyar Notts County a Ingila.

A lokacin aikinsa a Stamford Bridge, Chelsea ta ci kofin zakarun Turai a 2012 da Premier uku, da FA uku da na lig da kuma na Europa.

Haka kuma kungiyar ta sayo manyan ‘yan wasa irin su Eden Hazard da Thibaut Courtois da kuma N’Golo Kante.

Monaco tana matsayi na uku ne a teburin gasar Ligue 1 ta Faransa, maki tara tsakaninta da ta daya Paris St-Germain.

Chairman ya musanta marin wata kansila a Kebbi


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

“Sau biyu yana gaura min mari”

Shugaban karamar hukumar Fakai a jihar Kebbi a Najeriya ya musanta zargin da wata kansila ta yi masa na marinta

Kansilar mai sunan Rakiyya Musa Birnin Tudu ta ce Alhaji Musa Rabi’u Jarma ya mare ta har sau biyu saboda ta ba shi shawarar ya rika tafiya tare da kansilolinsa kuma ya biya ma’akatan karamar hukumar albashin watanni hudu da suke binsa.

Rakiya Musa Birnin Tudu, wadda kansila ce mai wakiltar mazabar Birnin Tudu a karamar hukumar, ta ce sau biyu Alhaji Musa Rabi’u Jarma yana marinta.

Sai dai shugaban ya shaida wa BBC cewa kansilar “karya take, ban mare ta ba”, yana mai cewa nan gaba gaskiya za ta fito fili.

Da muka so mu dauki muryarsa sai ya ce “ba zan yi jayyaya da ita ba a kan batun”.

Na ba da shara kan ya yi gyara

Rakiyya Musa ta shaida wa BBC cewa shugaban ya mare ta ne a lokacin da suke gudanar da taron majalisar zartawar na karamar hukumar.

Kansilar ta ce: “Na ba da shawara cewa ya kamata a yi gyara a yanayin tafiyar da mulkinmu, saboda zabe na karatowa, don haka idan har ba a gyara ba yanzu, har sai yaushe?”

Rakiya ta ce daga cikin korafin da jama’ar karamar hukumar ke yi akwai batun albashi, inda ake kwashe watanni ba a biya wasu albashinsu ba, wasu kuwa ba gaira ba dalili aka rage musu albashi.

Hakkin mallakar hoto
Hamza Galadima

Image caption

Alhaji Musa Rabi’u Jarma ya ce ba zai yi jayayya da ita ba

Don haka ne ta bayar da shawarar cewa ya kamata a gyara, saboda su kansiloli su suka fi kusanci da jama’a, su ake yi wa korafin.

“Bayan na gama bayanina ne, sai shugaban hukumar ya harzuka, wai don na ce ya rungumi komai shi kadai baya sanya kowa a harkokin tafiyar da karamar hukumar, hakan ya sa ma’aikata da dama ba sa zuwa ma aiki ciki har da daraktoci,” in ji ta.

Kansilar ta ci gaba da cewa bayan ya harzukan ne, sai ya tashi daga kujerarsa ita kuma kanta na duke, ba ta yi aune ba kawai sai ta ji an wanka mata mari har sau biyu.

Rakiya ta kara da cewa, “Sai shugaban karamar hukumar ya ka da baki ya ce mini ba a taba marin kansila ba a tarihin karamar hukumar, to yau shi ya mara kuma ya mari banza, don haka duk wanda zan fadawa na je na fada sai kawai ya fice daga wajen taron”.

A cewarta, bayan ya mare ta sai ta zabura ta tashi ta tambaye shi “me na yi maka daga fadin gaskiya don a yi gyara?”

A yanzu haka dai wannan batu yana hannun gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC mai mulki, inda mutane ke sa ido don ganin matakin da za su dauka.

Gareth Bale zai yi wasa ranar Talata – Zidane


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Gareth Bale ya dauki kofin zakarun Turai uku da Real Madrid

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale zai taka leda ranar Talata a karon farko a cikin wata biyu in ji kociyan kungiyar ta Spaniya Zinedine Zidane.

Da farko Bale ya ji rauni ne a guiwarsa kafin kuma daga baya ya kara jin wani ciwon a cinya, amma yanzu tun da ya warke zai buga wasan da za su yi da kungiyar Fuenlebrada ta rukuni na uku a kasar a gasar Copa del Rey.

Dan wasan gaban na Wales mai shekara, 28, bai taka leda ba tun lokacin da Real Madrid ta bi Borussia Dortmund har gida ta doke ta 3-1 ranar 26 ga watan Satumba.

Bale, wanda bai samu damar buga wasannin karshe na neman zuwa gasar kofin duniya na Wales ba, takitin da suka rasa, bai yi wani wasa ko daya tare da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema a wata fafatawa ta Real Madrid ba, saboda ko dai wani ya ji rauni ko kuma hukuncin hana buga wasa na kan wani daga cikinsu.

Zidane ya ce yana matukar sha’awar ya ga ‘yan wasan uku, Gareth da Cristiano da Karim, suna taka leda tare.

Bale ya ci kwallo 70 a wasa 159 da ya yi wa Real, inda ya ci kofin zakarun Turai uku da kuma kofin La Liga na bara.

Everton za ta koma zawarcin Sam Allardayce


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Aikin kociya da Allardyce ya yi na baya bayan nan shi ne na Crystal Palace – ya yi murabus a watan Mayu

Everton ta sake karkatawa wajen duba yuwuwar daukar Sam Allardyce a matsayin kociyanta sakamakon hakin kaka-ni-ka-yi da ta shiga.

Kungiyar ta Premier ta sake bijirowa da bukatar samo sabon kociya ne cikin gaggawa bayan kashin da ta sha a gidan Southampton ranar Lahadi da ci 4-1.

Allardyce ne mutum na farko da aka yi tsammani zai gaji Ronald Koeman, wanda aka kora ranar 23 ga watan Oktoba, amma ya fito fili ya ce ya janye bayan da Everton ta yi jinkirin nemansa.

Everton wadda zawarcin da ta yi na neman kociyan Watford Marco Silva ya ci tura, ta yi rashin nasara a wasa biyar cikin bakwai tun lokacin da Koeman ya bar ta.

Allardayce mai shekara 63 ba ya rike da wani matsayi ko yin wata harka a wata kungiyar wasan kwallon kafa tun lokacin da ya bar Crystal Palace a karshen kakar da ta wuce.

Kociyan ya ceto Palace daga faduwa daga gasar Premier, bayan da ya bar aikin horad da tawagar Ingila a watan Satumba na 2016 bayan wasa daya kawai.

Everton ta sallami Koeman dan kasar Holland daga aiki bayan da kungiyar ta koma ta 18 a gasar Premier, sakamkon cin da Arsenal ta bi ta har gida ta yi mata 5-2.

Kociyan kungiyar na matasa ‘yan kasa da shekara 23 David Unsworth, wanda ya taka leda a kungiyar a matsayin dan wasan baya, shi ne ke jagorantarta a matsayin na riko tun bayan korar Koeman.

Ya yi nasarar dago Everton din zuwa matsayi na 16, bayan da ta samu maki hudu a wasa hudu na Premier

Bukatar babban mai hannun jari a kungiyar Farhad Moshiri da shugabanta Bill Kenwright ta daukar sabon kociya ta kara kamari ne bayan casa su da Atalanta ta yi a gidanta 5-1 a gasar kofin Turai ta Europa ranar Alhamis, kuma bayan wannan suka je gidan Southampton ta lallasa su 4-1 ranar Lahadi.

AC Milan ta kori kociyanta Montella, ta nada Gattuso


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Yuni na 2016 Vincenzo Montella ya fara aikin kociyan AC Milan

AC Milan ta kori kociyanta Vincenzo Montella sannan ta maye gurbinsa da Gennaro Gattuso bayan ya kasa tabuka abin-a-zo-a-gani a kungiyar.

Kungiyar tana matsayi na bakwai ne a teburin Serie A da maki 20, 18 tsakaninta da ta daya Napoli, bayan nasara biyu kawai a wasa tara na gasar.

A ranar Lahadi ne ta yi canjaras 0-0 da Torino a gida, kuma ta yi rashin nasara a shida daga cikin manyan wasanninta 14 a kakar bana.

Shi dai kociyan na yanzu, Gattuso wanda tsohon dan wasan kungiyar ta AC Milan ne an ciyar da shi gaba ne daga matsayin kociyan karamar kungiyar.

Kociyan mai shekara 39, dan Italiya ya yi wa Milan wasa tsakanin 1999 da 2013, inda ya dauki kocin gasar Serie A da na zakarun Turai sau bibbiyu.

A ranar Talata ne zai bayyana a wani taron manema labarai a filin atisayen kungiyar, Milanello.

Bayan korar tasa Montella ya sanya wata sanarwa a shafukan sada zumunta da muhawara, wadda a ciki yake nuna godiya da cewa ba karamar martaba ba ce kasancewarsa kociyan kungiyar.

AC Milan wadda ta dauki kofin Serie a sau 18 kuma ta dauki kofin zakarun Turai sau bakwai, ba ta samu shiga cikin manyan kungiyoyi uku ba na gasar tun 2013.

Kungiyar ta kashe fam miliyan 205 wurin sayen sabbin ‘yan wasa tun lokacin da attajiri dan kasuwar China Li Yonghong ya sayi kungiyar a watan Afrilu na shekarar da ta wuce.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna godiyarta ga tsohon kociyan Mista Montella tare da dukkanin jami’ansa.

Chairman ya mari wata kansila a Nigeria


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

“Sau biyu yana gaura min mari”

Shugaban karamar hukumar Fakai da ke jihar Kebbi ta Najeriya ya gaura wa wata kansila mari.

Rakiya Musa Birnin Tudu, kansila mai wakiltar mazabar Birnin Tudu a karamar hukumar ta Fakai.

Ta shaida wa manema labarai cewa sun kira shugaban karamar hukumar tasu domin su gudanar da taron majalisar zartawar na karamar hukumar.

Sai dai ana cikin taron ne, inda kowa ke fadin korafinsa game da yanayin mulkin karamar hukumar, kuma ita ma Honourable Rakiya ta fadi korafinta a kan matsalolin da jama’ar karamar hukumar suke fadi a kan yanayin mulkin.

Kansilar ta ce: “Na ba da shawara cewa ya kamata a yi gyara a yanayin tafiyar da mulkinmu, saboda zabe na karatowa, don haka idan har ba a gyara ba yanzu, har sai yaushe?”

Rakiya ta ce daga cikin korafin da jama’ar karamar hukumar ke yi akwai batun albashi, inda ake kwashe watanni ba a biya wasu albashinsu ba, wasu kuwa ba gaira ba dalili aka rage musu albashi.

Don haka ne ta bayar da shawarar cewa ya kamata a gyara, saboda su kansiloli su suka fi kusanci da jama’a, su ake yi wa korafin.

“Bayan na gama bayanina ne, sai shugaban hukumar ya harzuka, wai don na ce ya rungumi komai shi kadai baya sanya kowa a harkokin tafiyar da karamar hukumar, hakan ya sa ma’aikata da dama ba sa zuwa ma aiki ciki har da daraktoci,” in ji ta.

Kansilar ta ci gaba da cewa bayan ya harzukan ne, sai ya tashi daga kujerarsa ita kuma kanta na duke, ba ta yi aune ba kawai sai ta ji an wanka mata mari har sau biyu.

Rakiya ta kara da cewa, “Sai shugaban karamar hukumar ya ka da baki ya ce mini ba a taba marin kansila ba a tarihin karamar hukumar, to yau shi ya mara kuma ya mari banza, don haka duk wanda zan fadawa na je na fada sai kawai ya fice daga wajen taron”.

A cewarta, bayan ya mare ta sai ta zabura ta tashi ta tambaye shi “me na yi maka daga fadin gaskiya don a yi gyara?”

BBC ta tuntubi shugaban karamar hukumar ta Fakai, Alhaji Musa Rabi’u Jarma, ta wayar tarho don jin martaninsa, amma bai dauki wayar ba, haka an aika masa da sakon text nan ma ba bu amsa.

A yanzu haka dai wannan batu yana hannun gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC mai mulki, inda mutane ke sa ido don ganin matakin da za su dauka.

Fafaroma Francis na ziyarar Musulman Rohingya a Myanmar


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Za a sa ido sosai kan duk wani tsokaci da Fafaroma ya yi a tafiyarsa ta Myanmar

Fafaroma Francis ya isa Myanmar domin ziyara ta farko da wani Fafaroma ya taba yi a kasar da ke shan suka a wannan shekarar kan kisan kare dangi ga Musulman Rohingya.

Tafiyar tasa za ta iya mayar da hankali kan ko zai yi amfani da kalmar “Rohingya” wajen siffanta tsirarun musulman kasar, wadanda suka ce ana musguna musu.

Jami’an Myanmar sun yi watsi da kalmar, lamarin da ya kara yiwuwar barkewar rikici daga masu addinin Bhudda masu rinjaye idan ya yi hakan.

Fafaroma zai gana da shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi, da kuma shugaban rundunar sojin kasar.

Daga nan zai wuce Bangladesh inda zai gana da kadan daga cikin ‘yan gudun hijirar Rohingya a wani mataki na nuna damuwarsa kan halin da suka samu kansu ciki.

Fafaroman mai shekara 80 ya yi fice wajen zama mai matsakaicin ra’ayi da kuma yin tir da rashin adalci a duniya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Dubban mutane ne suka taru a Yangon domin ziyarar farko ta Fafaroma a kasar da mabiya addinin Budha suka fi rinjaye

Sama da Musulmai ‘yan kabilar Rohingya 600,000 sun tsere daga Myanmar (wadda ake kira Burma) zuwa kasar Bangladesh mai makwabataka tun watan Agusta, a lokacin da hare-hare kan shingen ‘yan sanda da masu ta da kayar baya na Rohingya suka kaddamar ya sa sojoji suka far wa ‘yan kabilar a jihar Rakhine.

Kafin ya fara ziyarar Fafaroma ya yi amfani da kalaman “‘yan uwanmu maza da mata na Rohingya” a lokacin da yake tir da rikicin.

Amma shugaban darikar katolika da ya kai matakin kadinal a kasar ya bukaci Fafaroma kar ya yi amfani da kalmar a lokacin da ya fara ziyarar, domin kauce wa bata wa mutanen kasar rai.

Mai magana da yawun fadar Batikan Greg Burke, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin cewa Fafaroma Francis yana mutunta shawara da aka ba shi kwarai.

Jami’an Myanmar ba sa amfani da kalmar Rohingya, maimakon hakan suna kiransu ‘yan “Bengal” ne, kuma sun ce bakin haure ne daga Bangladesh, saboda haka bai kamata a lissafa su cikin kabilun kasar ba.

Bangladesh ta musanta cewa ‘yan kabilar Rohingya al’ummar kasarta ne.

Myanmar ta ce matakin sojan da ta dauka a Rakhine ta dauka ne domin kawar da masu tayar da kayar baya daga wurin.

Amma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tashin hankalin a matsayin wani kisan kare dangi irin wanda aka bayyana a littattafai – ra’ayin da masu suka na kasa-da-kasa suka goya wa baya.

A makon jiya Myanmar da Banladesh sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta mayar da dubban wadanda suka tsere ta bakin iyaka, amman kungiyoyin ba da agaji sun nuna damuwa kan mayar da kowa da karfin tuwo sai dai in har za a iya tabbatar da tsaronsu.

Masu taimaka wa Fafaroma sun ce zai yi amfani da tafiyar ta kwana shida domin bayar da kwarin gwiwar tattaunawa da sasantawa bayan yarjejeniyar wucin-gadi ta makon jiya.

Daruruwan mutane sun fito bakin titunan Yangon, babban birnin kasar, domin ganin fafaroman da ayarin motocinsa a lokacin da yake wucewa ranar Litinin.

“Mun zo nan domin mu ga fadan mai tsarki . Hakan na faruwa ne a lokaci daya cikin daruruwan shekaru,” in ji Win Min Set, wanda ya kawo wasu ‘yan darikar katolika 1,800 birnin kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Daruruwan mutane ne suka yi wa ayarin motocin Fafaroman maraba a lokacin da yake ratsawa ta tsakiyar birnin Yangon

Ya kara da cewa: “Yana da ilimi sosai a fagen siyasa. Zai yi amfani da hikima wajen tinkarar lamarin.”

An shirya wannan ne kafin rikicin, a lokacin da Fafaroma ya gana da Mis Suu Kyi a fadar Batikan a watan Mayu.

Shugabar wadda ta taba cin lambar yabo ta Nobel ta fuskanci suka mai tsanani kan gazawa wajen matsa kaimi domin warware rikicin.

‘Yan darikar katolika kashi daya cikin 100 ne na al’ummar kasar Myanmar da suka kai miliyan 53, inda ake tsammanin da yawa daga cikinsu za su halarci taron ibada a birnin Yangon ranar Laraba.

Sa’annan zai zama fafaroma na farko da zai ziyarci Bangladesh, inda Muslmai suke da rinjaye, tun shekarar 1986.

Watakila a dakatar da Lukaku buga wasa uku


Image caption

Romelu Lukaku ya ci kwallo daya a wasanshi goma na karshe da ya buga wa Manchester United

Dan kwallon Manchester United Romelu Lukaku na jiran hukunci game da binciken da ake yi domin a gano ko yana da laifi a kan zargin da ake na ture Gaetan Bong a wasansu da Brighton.

Al’amarin ya faru ne a wasan da United ta doke kungiyar da ci 1-0 ranar Asabar, amma kuma alkalin wasa Neil Swarbrick bai dauki mataki ba.

Hukumar kwallon kafa ta Inglia za ta yi bincike a kan rahoton da Swarbrick ya gabatar a kan wasan.

Lukaku na iya fuskantar hukuncin dakatar da shi buga wasa uku a gida bisa laifin yin fada da ‘yan wasa, idan aka same shi da laifi, hukuncin zai iya jawo masa rashin shiga wasan da kungiyarsa za ta kara da Manchester City a gida ranar 10 ga watan Disamba.

Har ila yau zai iya rasa wasan da za su kara da Watford da Arsenal a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Nigeria: ‘Dabi’un iyaye na iya tasiri a gidan auren ‘ya’yansu’


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Baya ga matsalar mace-macen aure, matsalar fada tsakanin ma’aurata na cikin batutuwa da ke jan hankalin mutane a Najeriya

Dole iyaye su kaurace wa fada ko daukar makami a gaban ‘ya’yansu domin gudun kada ‘ya’yan su kwaikwayi ko kuma aiwatar da abin da suka gani bayan sun yi aure.

Wannan shawarar ta fito ne daga wani masanin ilimin zamantakewa a Jami’ar Bayero ta kano, Dr Abdullahi MaiKano Madaki.

A hirar da ya yi da BBC, Abdullahi MaiKano Madaki ya ce: ‘Shi dan’Adam an halicce shi da dabi’un kallo da sauraro da kuma kwaikwayo. In ya gani zai iya dauka. Idan ya ji, zai iya dauka.’

Ya kara da cewa: ‘Iyaye su zauna kan gaskiya bayan an gina aure kan gaskiya, kuma su kasance masu gaya wa kansu gaskiya.

“Abu na biyu da zan dora a kan wannan shi ne idan mutane suka haifi ‘ya’ya, to ya kamata a ce duk lokacin da suka samu wani sabani a tsakaninsu, ba a gaban ‘ya’yansu za su yi sa-in-sa ko ce-ce-ku-ce ba, balle har a kai ga matakin zage-zage ko doke-doke ko cin mutuncin juna ko ma daukar makami don a illata juna.”

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An bukaci ma’aurata da su guje wa aikata abin da za su yi nadama a kai

Malamin ya kara da cewa: ‘Idan ku ka bari suna yi za su dauka cewa wannan dabi’a ce mai kyau ko da sun ga kuna yi cikin fushi. Domin akwai matakin da ba za su iya tantance mene ne abu mai kyau kuma mene ne abu mara kyau ba.

“Saboda haka yi a gabansu illa ne. Yi a gabansu na iya sa wa su dauki wani abu wanda ku ba za ku iya sanin sun dauka ba.”

Dr Madaki ya ce a gaba idan yaran suka tsinci kansu cikin irin wannan yanayin za su yi kokarin aiwatar da abin da suka gani ba tare da sanin irin illar da za ta haifar musu ba.

Sai dai kuma masanin ilimin zamantakewar ya bukaci ma’aurata su kai zuciya nesa a lokacin da suka yi fushi, kuma su yi tunanin abin da matakin da suke son su dauka ka iya haifar wa domin gujewa nadama.

Latsa alamar lasifikr da ke kasa domin jin yadda hirar da kasance:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Dole iyaye su kauce wa fada a idon ‘ya’ya’

An ware ranar tuna haihuwar Mugabe a matsayin hutu a Zimbabwe


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mista Mugabe ya mulki Zimbabwe tun lokacin da ta samu ‘yancin kai a shekarar 1980

Gwamnatin Zimbabwe ta ayyana ranar tunawa da haihuwar hambararren shugaban kasar Robet Mugabe, a matsayin ranar hutu a ko wcace shekara, don nuna girmamawa gare shi na gudunmuwar da bayar wajen gina kasar.

Jaridar Herald ta kasar ta ruwaito cewa, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a ranar Juma’a bayan da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya sha rantsuwar kama mulki.

An dai ware ranar 21 ga watan Fabrairun ko wacce shekara ce a matsayin ranar hutu don girmama Mista Mugabe.

A watan Agustar da ya gabata ne gwamnatin Mista Mugabe ta yanke shawarar ware ranar tunawa da haihuwarsa a matsayin ranar hutu a kasar, sakamakon yawan kamun kafa da kungiyar matasa ta jam’iyyar Zanu-PF mai mulki ta dinga yi.

A makon da ya gabata ne sojojin kasar da kuma jam’iyyarsa ta Zanu-PF suka tursasawa Mista Mugabe sauka daga mulki.

Tarihin rayuwar Robert Mugabe a takaice

 • 1924: Shekarar da aka haife shi
 • An horar da shi a matsayin malami
 • 1964: Gwamnatin Rhodesia ta daure shi
 • 1980: Ya lashe zaben da aka yi bayan ‘yancin kai
 • 1996: Ya auri Grace Marufu
 • 2000: Bai yi nasara ba a zaben raba-gardamr da aka yi ba na karfin ikon shugaban kasa da kuma hana Turawa mallakar gonaki
 • 2008: Ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da suka fafata da Tsvangirai, wanda ya janye saboda harin da aka kai kan magoya bayansa
 • 2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin firai minista a lokacin da ake fuskantar durkushewar tattalin arziki a kasar
 • 2016: An gabatar da takardun lamuni a yayin da karancin takardun kudya yi tsanani
 • 2017: Ya kori mataimakinsa da ya dade suna aiki tare wato Emmerson Mnangagwa

Tafkin Victoria na fuskantar barazana


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tafkin Victoria shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrik, mai iyaka da kasashen Uganda da Kenya da Tanzani

Masana kimiyya na gargadin cewa tafkin Victoria ,wanda shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika , na fuskantar barazanar gurbacewa.

Tafkin Victoria shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika, mai iyaka da kasashen Uganda da Kenya da Tanzania

Sun ce yawan kamun kifi da ya zarce kima tare da gurbatar muhalli ya kassara adadin kifayen da ake samu a cikinsa, abinda ke barazana ga rayuwar miliyoyin masuntan da suka dogara da tafkin.

Masanan sun ce gurbataccen ruwan dake kwarara cikin tafkin na haddasa dafi a cikinsa, yayinda takin da ke gangarowa daga gonaki ke kashe tsirran da ke rayuwa a cikin ruwan.

Kuwesi Edi na daya daga cikin masuntan da ke kamun kifi a tafkin kuma ya ce kifin da suke kamawa ya yi karancin kwarai.

Ya baya wuce kilo goma kuma a da su kan kama kifi kilo dari zuwa dari biyar.

Kuwesi ya ce yana matukar fargabar abinda zai faru nan gaba.

Yadda kate ke hada kan ‘yan Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An bukaci masu yin kate akan su hada kate din da ya nuna muhiman abubuwan da suka faru a Nigeria

An gudanar da taron baje kolin kate domin murnar zagayowar ranar samun yancin Nigeria a birnin Abuja.

An nemi masu gasa kate a kan su hada kate din da zasu nuna muhiman abubuwan da suka faru a kasar a shekarun baya.

Wadanda suka shirya taron, sun kuma nemi a ayi kate da zasu yi hasashe game da makomar kasar nan gaba.

Daya daga cikin mutane da suka shiga gasar ,ya hada kate mai bangarori 4 inda wani bangare an yi masa zanen ganga ya yin da dayan ya yi kamada kwallon kafa.

Wadanda suka shirya taron baje kolin sun ce anniyarsu ita ce su nuna al’adun gargajiya na kasar tare kuma da karfafa gwiwar matasa da kuma hadin kai tsakanin alumomi daban daban ta hanyar hada kate.

Ban taba ambaton Sheikh Dahiru Bauchi a wa’azina ba — Kabiru Gombe


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Sheikh Dahiru ne ma yake ambatata sunana a wa’azinsa’

Babban sakataren kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta cewa yana yawan ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin wa’azinsa.

Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa BBC a ofishinmu da ke Landan a makon daya gabata, inda ya ce shi a tarihin rayuwarsa bai taba ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba a cikin wa’azinsa.

Malamin addinin ya ce, “idan akwai wanda ke da wani kaset na wa’azinsa da ya ambaci sunan malamin, to kofa a bude take ya fiddo da shi ya yada wa duniya.”

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

“Hasali ma shi shaihin shi ke ma ambatarmu a cikin wa’azinsa, domin ya kira sunana dana mahaifina ba sau daya ba, ya kuma kira shugaban kungiyarmu da sunansa karara, har ma ya kan siffantashi da munanan siffofi wanda shi shugaban bai taba mayar masa da martani a kan hakan ba,” in ji shi.

Jagoran Izalan ya ce “ita da’awa ta ahlul sunnah ba da’awa ce ta kiran sunaye ba.”

Karanta wadansu karin labarai

Premier: Manchester City ta doke Huddersfield da 2-1.


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Raheem Sterling lokacin da yake cin kwallo ta biyu, ta 8 a Premier kuma ta 12 a kakar bana

Jagorar Premier Manchester City ta farfado daga baya ta doke Huddersfield Town 2-1, nasarar da ta kasance mata ta 11 a jere a gasar, da maki 37.

Masu masaukin ne suka fara daga ragar City a minti na 45 lokacin da Nicolas Otamendi ya ci kansu, a wasan da kungiyar ta Pep Guardiola ta kai daidai da irin bajintar da ta yi a shekarar 2015.

Dawowa daga hutun rabin lokaci ke da wuya cikin minti biyu sai City ta samu fanareti bayan da aka ture Raheem Sterling, inda Sergio Aguero ya buga ya ci, kuma bayan nan ne ana saura minti shida lokaci ya cika Sterling din ya ci ta biyu.

Wannan shi ne karon farko da da Manchester City ta farfado a hutun rabin lokaci bayan an ci ta, ta yi nasara a wani wasan Premier na waje tun watan Afrilu na 1995.

Bayan an tashi daga wasan an samu sabani inda Rajiv van la Parra na Huddersfield ya bangaje Leroy Sane, abin da ya sa alkalin wasa ya ba shi jan kati, na kora, duk da cewa an tashi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Rajiv van La Parra lokacin da ya bangaje Leroy Sane

Da wannan nasara Man City ta kara yi wa abokiyar hamayyarta kuma ta biyu a tebur, Manchester United ratar maki takwas.

Rashin nasarar shi ne na biyu da Huddersfield ta hadu da shi a gida a karonta na farko na zuwa gasar Premier, abin da ya sa ta zama ta 11 a tebur da maki 15.

Arsenal ta farfado a wasan waje, da nasara kan Burnley 1-0


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Dan wasan baya na Burnley James Tarkowski lokacin da ya ture Aaron Ramsey alkalin wasa Lee Mason ya ba wa Arsenal fanareti

Arsenal ta ci gaba da yin manyan wasanninta har zuwa goma ba tare da an doke ta ba, inda ta buge Burnley da ci 1-0 a wasan Premier na 13, da nasara a 7, da canjaras a 3.

Wasan ya kasance kamar maimaici na haduwarsu ta bara a gidan Arsenal, Emirates, lokacin da Alexis Sanchez ya ci fanaretin da suka samu a minti na 98.

Haka kuma wannan shi ne karo na uku a jere wanda Arsenal take cin kwallon da ta ba ta nasara a kan Burnley a daidai lokacin tashi.

A yanzu Burnley ta yi rashin nasara a wasanninta na Premier uku a gida da Arsenal 1-0.

Kafin wasan Arsenal ta samu maki hudu ne kawai a waje a bana, kuma rashin kokarinsu a wasan wajen kamar zai ci gaba kafin Sanchez ya ceto su.

Da wannan cin Sanchez ya ci kwallo hudu a wasa biyar da ya buga na Premier da Burnley, ya ci Sunderland 6 Hull kuma 7.

Yanzu Arsenal ta hau mataki na hudu a tebur da maki 25, a gaban abokiyar hamayyarta ta Landan, Tottenham mai maki 24, wadda ta yi kunnen doki 1-1 da West Brom ranar Asabar, yayin da Burnley take matsayi na 7 da maki 22.

A wasan gaba Arsenal za ta karbi bakuncin Huddersfield, ita kuwa Burnley za ta je gidan Bournemouth ranar Laraba (dukkaninsu da karfe 19:54 GMT).

Mata sun fi maza bukatar wa’azi — Sheikh Kabiru Gombe


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Mata sun fi maza bukatar wa’azi – Kabir Gombe
 • Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon bidiyon hirar

Babban sakataren kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS),Sheikh Kabiru Haruna Gombe, ya shaida wa BBC dalilin da ya sa ya ke yawan yin wa’azi a kan mata.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa BBC a ofishinmu da ke Landan ranar Alhamis.

Ya ce ya fuskanci cewa an bar iyaye mata a baya kuma ba a cika mayar da hankali a kan wa’azin mata ba, a cewarsa.

Ya ce “ko da an yi wa’azi a kan matan, yawanci bai wuce a ce an rataye wata a wuta ba ko kuma malamancin haka, maimakon a tsaya a koyar da su koyarwar addinin Musulunci da kuma yadda za su bauta wa Allah Ubangiji Madaukakin Sarki.”

Sheikh Kabiru Gombe ya ce wa’azantar da mace ko ilmantar da ita ya fi muhimmanci a kan na namiji, “domin ita mace makaranta ce guda saboda ita uwa ce kuma ita ce mai tarbiyantar da yara.”

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

Jirgi ya bar ‘yan Chelsea a tasha


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Magoya bayan Chelsean sun rasa ta yi a tasha har zuwa karfe 12 na dare bayan wasan da Liverpool

Chelsea ta bayar da hakuri ta kuma yi hayar motocin safa suka dauki magoya bayanta da suka je kallon wasanta da Liverpool saboda jirgin kasa da ta yi haya musamman domin jigilarsu ya yi latti, har suka rasa ta yi a tasha.

Bayan an tashi daga wasan na ranar Asabar, magoya bayan Chelsean sun yi curko-curko a tashar jirgin kasa har zuwa karfe 12 na dare kafin a turo wata motar safa ta dauke su suka koma Landan.

Jirgin wanda mai tafiyar da harkar zirga-zirgar Chelsea Thomas Cook, ya yi shata ya tashi a kan lokaci, domin ya je ya dauko magoya bayan, bayan an tashi daga wasan da Liverpool, a Anfield amma sakamakon cunkoson da ba a yi tsammani ba, sai ya yi jinkiri.

A wata sanarwa da kungiyar ta Chelsea ta fitar, ta ba wa ‘yan kallon nata hakuri kuma ta ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin.

A shekara ta 2007, tsohon shugaban Sunderland Niall Quinn ya yi hayar motocin tasi a kan fam 8,000 domin jigilar magoya bayan kungiyar kusan 80 wadanda aka ba ri ba tayi a filin jirgin sama na Bristol lokacin da jirgin da zai dauke su ya lalace.

Premier: Southampton ta caskara Everton 4-1


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Southampton ta koma ta 10 damaki 16 a tebur bayan casa Everton wadda ita kuma ta zama ta 16 da maki 12

Everton ta ci gaba da shiga tsaka-mai-wuya a karkashin kociyan rikon-kwarya David Unsworth bayan da ta sha kashi 4-1 a gidan Southampton a wasan Premier na mako na 13.

Dusan Tadic ne ya fara ci wa masu masaukin bakin a minti na 18, amma ana dab da tafiya hutun rabin lokaci sai Sigurdsson ya farke wa Everton, wadda a yanzu wasa daya kawai ta ci a cikin bakwai a karkashin jagorancin Unsworth.

Bayan an dawo ne sai dan wasan gaba na Southampton Charlie Austin ya zura kwalllo biyu a minti na 52 da kuma minti na 58, kafin kuma can ana dab da tashi a minti na 87 Steven Davis ya ci ta karshe.

Wannan rashin nasara ya zo wa Everton ne kwana uku bayan casa ta 5-1 da Atalanta ta yi a gasar kofin zakarun Turai ta Europa, lamarin da ya sa tsohon dan wasan kungiyar Gary Lineker ya bayyana ta da shirme.

A yanzu an zura wa Everton kwallo 28 bayan wasa 13 a gasar Premier ta bana, abin da ba a taba yi musu ba tun kakar 1958-59.

Nasara daya kacal da suka yi a karkashin jagorancin Unsworth ita ce ta ranar biyar ga watan Nuwamba a kan Watford, wadda Everton din ke neman daukar kociyanta Marco Silva.

Da gaske ne kungiyar Izala ta karbi ‘kudin makamai’?


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Izala ba ta karbi kudin makamai ba – Sheikh Kabiru Gombe
 • Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon bidiyon hirar

Daya daga cikin jagororin Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta zargin da ake wa kungiyar na karbar “kudin makamai”.

Ana zargin gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da raba wa jama’a da kungiyoyi da kuma kamfanoni a kasar kudin da aka ware don sayo wadansu makamai.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau wanda shi ne shugaban kungiyar JIBWIS.

“Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai. Wannan abu ne da kungiyar Izala ba ta taba shiga cikin shi ba,” in ji Sheikh Kabiru Gombe.

Gwamnatin Najeriya tana ci gaba da tsare tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki ne bisa zargin yana da hannu a badakalar kudin sayo makamai da suka kai dala biliyan biyu.

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

Hotunan abin da ya faru a Afirka a makon jiya


Wasu zababbun fitattun hotunan Afirka a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Wannan matar mai suna Lilian Ericaah Maraule sanye da shigar al’adar kasar Tanzaniya, inda za ta wakilci kasar a bikin nunin kayayyakin al’ada da za a yi a birnin Las Vegas ranar Asabar.

Staff of Kajiado county government prepare their Maasai tribe costumes for their cultural performance before Kajiado half Marathon calling for peace and cohesion in Kajiado, Kenya, on November 18, 2017.Hakkin mallakar hoto
AFP

A dai wannan ranar a Kenya, wasu mata daga kabilar Maasai sanye da tufafinsu na gargajiya, a wani shiri na bunkasa hadin kan al’umun kasar a yankin Rift Valley.

Girls pose with their chalkboards as they attend a class at a school in Abidjan, Ivory Coast, 17 November 2017Hakkin mallakar hoto
EPA

Wadanan kananan yara manufarsu ita ce ilimi, yayin da suke halartar makaranta da allunansu a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast ranar Juma’a

An weaver works on a loom at the opening of the fourth International Exhibition of Agriculture and Animal Resources (SARA 2017) in Abidjan on November 17, 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

A wani wuri kuma a birnin, inda wata mata ke saka a masaka.

Visitors look at a display of cotton at the opening of the fourth International Exhibition of Agriculture and Animal Resources (SARA 2017) in Abidjan on November 17, 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Yayin da wasu kuma baki ke kallon Auduga a bikin baje-kolin kayayyakin noma da albarkatun dabbobi. Kasar Ivory Coast dai ita ce ke kan gaba wajen samar da Auduga a duniya.

An exhibitor poses with Malian rams at the opening of the fourth International Exhibition of Agriculture and Animal Resources (SARA 2017) in Abidjan on November 17, 2017.Hakkin mallakar hoto
AFP

Ga kuma raguna daga makociyar kasar wato Mali, inda ake nuna su a bikin baje-kolin, wanda aka shirya da nufin inganta harkokin noma da habaka kasuwanci.

An Egyptian man carries a wood rack full of bread near a traditional bakery in Al Sayeda Zainab district, Cairo, Egypt, 22 November 2017Hakkin mallakar hoto
EPA

Ranar Laraba ke nan, yayin da wani matukin keke dauke da kwandon biredi a kansa yayin da yake rarraba biredin a birnin Al-Khahira na kasar Masar.

Workers sew clothes inside the Indochine Apparel PLC textile factory in Hawassa Industrial Park in Southern Nations, Nationalities and Peoples region, Ethiopia November 17, 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Ma’aikata ke nan a kamfanin sarrafa tufafi ke dinki a kasar Habasha ranar Juma’a. Tufafin na wasu manyan kamfanonin kayan kawa ne na duniya.

A supporter holds a banner bearing a picture of President Uhuru Kenyatta as they celebrate on November 20, 2017 in Nairobi after Kenya"s Supreme Court dismissed two petitions to overturn the country"s October 26 presidential election re-run, validating the poll victory of Kenyatta.Hakkin mallakar hoto
AFP

Ranar Litinin a birnin Nairobi, wani matashi dauke da hoton Shugaba Uhuru Kenyatta bayan da ya samu nasara a karar da aka shigar game da zaben watan da ya gabata, abin da kuma ya share masa hanya wajen rantsar da shi a matsayin shugaban kasar karo na biyu.

A Zimbabwean Defence Force soldier poses for selfie-pictures with two women as they take part in a march in the streets of Harare, on November 18, 2017 to demand to the 93 year-old Zimbabwe"s president to step down. Zimbabwe"s president clings to office, the military is in power and the much-feared ZANU-PF party still rules - but Zimbabweans put such issues aside on November 18, 2017 to happily embrace what they hope is a new era for the country.Hakkin mallakar hoto
AFP

Ranar Asabar kuma a birnin Harare, wadansu mata ke daukar hoto tare da da sojoji a wani bangare na nuna murna game da matakin da sojojin suka dauka na yunkurin kawar da Shugaba Mugabe, mai shekara 93, inda kuma suka yi masa daurin talala abin da kuma ya haddasa masa yin murabus.

People wave national flags as they celebrate outside the parliament in Harare, after the resignation of Zimbabwe's president Robert Mugabe on November 21, 2017.Hakkin mallakar hoto
AFP

Ranar Talata ke nan yayin da dandazon mutane suka yi dafifi a kofar ginin majalisar dokokin kasar don nuna goyon bayansu ga ‘yan majalisar da suka nuna sha’awar tsige Mista Mugabe.

Zimbabweans living in South Africa celebrate by burning a banner with Robert Mugabe's image after President Robert Mugabe resigns, in Johannesburg, South Africa November 21, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Sa’o’i kalilan bayan sanar da yin murabus dinsa, ‘yan kasar ta Zimbabwe da dama sun fara nuna farin ckikinsu a ko’ina a fadin duniya, ciki har da kasar Afirka ta Kudu, inda suka yi ta kona allunan da ke dauke da hotunansa.

Supporters of Zimbabwe's former vice president Emmerson Mnangagwa await his arrival in Harare, Zimbabwe, November 22, 2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Kwana daya bayan ayyana murabus dinsa, wanna mutumin dauke da hoton kada domin yin maraba da sabon Shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa, wanda ake yi wa lakabi da “kada” saboda yadda aka sanshi da kwarewa ta fuskar siyasa.

Mourners attend the funeral of the late Tunisian fashion designer Azzedine Alaia, who died this month aged 77, in the Sidi Bou Said cemetary in the capital Tunis on November 20, 2017.Hakkin mallakar hoto
AFP

Tunisiya kuma, ana cikin yanayin jimami ranar Talata, inda mutane da dama suka halarci bikin jana’izar wani mai kera kayan kwalliya Azzedine Alaia wanda ya mutu yana da shekara 77.

Tunisian President Beji Caid Essebsi prays during the funeral of the late Tunisian fashion designer Azzedine Alaia, who died this month aged 77, in the Sidi Bou Said cemetary in the capital Tunis on November 20, 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Shugaban kasar Tunisiya yana daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar, inda kuma ya yi wa mamacin addu’a a lokacin da aka binne shi a makabartar birnin Tunis.

Bees fly amongst a lavender bush in Cape Town, South Africa, 18 November 2017. Bee colonies are under stress recovering from an American foulbrood disease outbreak in 2015 which killed off forty percent of all bees in the Western Cape.Hakkin mallakar hoto
EPA

A birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu ranar Asabar, yayin da kudan zuma ke kaura zuwa dajin Lavendar. Kudan zuma dai na fuskantar matsi a kasar bayan da wata cuta da ta bulla a shekarar 2015, inda kuma ta kashe a kalla kashi 40 na kudan zumar da ke yammacin yankin Cape.

Hotuna daga AFP, EPA, PA da kuma Reuters

Boko Haram sun kwace Magumeri da ke jihar Borno


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wata majiya a rundunar sojin Nigeria ta tabbatar da harin amma ba ta yi karin haske ba

Rahotanni daga arewa maso gabacin Nigeria na cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun karbe iko da garin Magumeri da ke arewa maso yammacin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutanen garin Magumeri sun shaida masa ta wayar salula cewa sun arce zuwa wani daji da ke kusa da su.

Wata majiyar soji ta tabbatar da cewa an kai hari garin, amma ba ta yi bayani game da ko maharan sun kwace garin ba.

A farkon watan da mu ke ciki ne,aka kashe mutun 6 tare da kone gidaje masu yawa a harin da aka kai a cikin gari .

Mayakan Boko Haram sun kara zafafa hare haren da suke kai wa tun bayan daukewar ruwan sama a watan Satumba.

Wannan shi ne hari na baya bayanan tun bayan harin kurnar bakin wake da aka kai a wani masallaci a jihar Adamwa inda mutum 50 suka hallaka.

Harin na cikin hare hare mafi ya muni da aka kai tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a shekarar 2015, inda ya yi alkawarin kawo karshen masu tada kayar baya.

‘Yan cirani 31 sun nutse a cikin tekun Libya


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An kai gawawwakin mutane sansanin sojin ruwa na Libya

‘Yan cirani 31 ne suka nutse a cikin teku bayan da jirgin ruwan da suke ciki, ya kife a gabar tekun Libya a ranar Asabar.

Mutanen na kokarin ketarawa ne zuwa turai daga tekun baharum.

Yara kanana na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

A kuma ceto mutane 60 daga cikin ruwa kuma daga bisani an ceto 140 daga cikin wani jirgin ruwa.

Kyawon yanayi ya sa an samu karuwa a yawan yan cirani da ke tafiya zuwa turai daga Libya a kwanakin baya bayanan.

Masu gadi a bakin teku a Libya sun ceto mutum 250 a ranar Alhamis.

Ha ka kuma masu gadi a tekun Italiya sun ce sun ceto mutane 1’100 a ranar Talata.

Kwale-kwalen ya yi karo ne a gabar birnin Garaboulli, mai nisan kilomita 60 daga birnin Tripoli.

Liverpool da Chelsea sun raba maki


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon dan wasan Chelsea Mohamed Salah ne ya fara zura kwallo a minti na 65

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi kunnen doki da Chelsea a gida, wato 1-1.

Mohamed Salah ne ya fara daga ragar bakin bayan dawowa daga hutun rabin lokaci wato a min na 65.

Sai dai ana cinkin minti na 85 ne dan wasan Chelsea Willian ya farke kwallon.

Wannan ce kwallo ta 10 da tsohon dan wasan Chelsea Mohamed Salah ya ci a wasa 13 da ya buga a kakar bana.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga ranar Asabar su ne:

 • Crystal Palace 2-1 Stoke City
 • Man Utd 1- 0 Brighton
 • Newscastle 0-3 Watford
 • Swansea 0-0 Bournemouth
 • Tottenham 1-1 West Brom

Karanta wadansu karin labarai

Ko kaciyar mata tana da wata illa a likitance?


 • Latsa alamar lasikifa da ke sama don sauraron cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zahra Umar game da batun

Na hadu da Hajiya Ladidi, wanda ba shi ne sunanta na gaskiya ba.

Shekararta 39 kuma ga dukkan alamu tana cikin matukar damuwa.

Ta shaida mini cewa an mata kaciya a lokacin tana da shekara 13 da haihuwa, aka kuma yi mata aure tana da shekara 15.

Mutumin da ta aura ya girmeta da shekara 30, a lokacin da aka mata aure, bata iya biya masa bukata ma’ana saduwar aure saboda zafin da take ji a duk lokacin da ya kusance ta.

Sun kasance a haka har shekara guda, wannan dalili ya sa mijin nata ya sake ta.

Wannan dai ya faru ne shekaru da dama da suka gabata.

Yanzu Hajiya Ladidi tana kan aurenta na uku ne, kuma bata canja zani ba, domin har yanzu tana fama da wannan matsalar ta rashin yarda da miji ya kusanceta.

Ta shaida mini cewa har yanzu tana cikin fargabar kaciyar da aka yi mata shi ya sa bata yarda da mijinta.A wannan karon mijinta mai fahimta ne, hakan ya sa yakan fita ya nemi mata a waje don ya biya bukatarsa.Ta ce bata jin dadi kuma tana gani kamar ana cutar ta.

A cikin shirin Adikon Zamani na wannan makon, na tattauna da wata matashiya da itama ka yiu mata kaciyar domin na fahimci yama ake yinta.Itama labarinta kamar na Hajiya Ladidi ne, ma’ana bayan anyi mata kaciyar aka yi mata aure kuma ga mijin da bata so.

Sun fara fuskantar matsala ne tun bayan da ta ki amincewa mijin nata ya kusance ta, hakan ya sa itama ya mayar da ita gidansu.

Na tattauna da wasu wanzamai wadanda suka hakikance cewa, mace ba ta zama cikakkiya idan ba a yi mata kaciya ba.

Abind a suka yi imani da shi shi ne namiji baya jin dadin matarsa matukar ba a yi mata kaciya ba.

Sannan kuma sun ce kaciyar tana ragewa mata sha’awa kuma tana sa su su kame.

A takaice ma dai daya daga cikin wanzaman ya shaida mini cewa matan da ba a yiwa kaciya ba ba za su taba zama masu kame kansu ba.

Likitoci da kungiyoyi masu zaman kansu na daga kan gaba gaba wajen watsi da wannan al’ada ta kaciyar mata saboda matsalolin da ake samu sakamakon kaciyar kamar kamuwa da cutar HIV da ragewa mata ni’ima da dai sauransu.

To amma babban abin shi ne damuwar da matan kan shiga bayan an yu musu kaciyar.

Daya daga cikin batutuwan shi ne matan da ba a yiwa kaciyar ba ba za su taba jin dadin zaman aurensu ba, wanda hakan kuma ba karamin rashin adalci bane.

Don haka a cikin shirin Adikon Zamani na wannan makon mun tambaya shin ko kaciyar mata nada wani alfanu?

Dr Zainab Datti ta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta ce ana yawan samun karuwar matan da ake musu aiki saboda kaciyar da aka yi musu.

Ta kuma tabbatar mini da cewa irin wadannan matan na bukatar shawarwari masu kyau da kuma ta yadda zamu samu nutsuwa a rayuwar aurensu.

A kwanan baya an samu rahoton wata yarinya wadda aka ji mata ciwo sosai saboda kaciyar da aka yi mata.

Mahaifin yarinyar dai ya yi imanin cewa kin yarda da mijinta ya kusanceta da ta yi saboda ba a yi mata kaciyar bane kafin ta yi aure.

Ko da ya ke mahukunta sun shiga maganar inda suka ceto yarinyar har kuma ta warke daga raunin da ta ji.To bayan jin irin wadannan labarai, abin tambayar anan shi ne, shin ko kaciyar mata ta zama dole?

Sai ku sanar da mu abinda kuke ganin.

Abin da ya kai mu wajen Buhari – Sheikh Bala Lau


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Har ayoyin Al-Kur’ani sai da na jawo wa Buhari – Bala Lau
 • Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon bidiyon hirar

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa BBC dalilin da ya kai su fadar shugaban Najeriya.

A farkon watan nan ne wadansu malaman addinin Musulunci a kasar suka kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Sheikh Bala Lau ya ce dalilin zuwansu fadar bai wuce batun cewa shugaban ya kwashe lokaci mai tsawo bai sadu da malaman addinin ba, tun gabanin ya fara jinya a farkon shekarar nan.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Kabiru Gombe.

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

A farkon watan ne wane wadansu malaman addinin Musulunci suka kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja

“Ba kawai malunma na addinin Musulunci shugaban ya gani ba. A’a har da ma malaman addinin Kirista ya gana da su a lokacin,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “Babu shakka mun shaida masa halin da talakawa suke ciki har ayoyin Al’kur’ani sai da na karanta masa.”

Har ila yau malamin ya ce sun bukaci shugaban da ya rika kawo sauki a cikin shugabancinsa.

Kuma ya ce shugaban ya ba su tabbacin aiki da shawarwarin da suka ba shi.

Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.

BBC ta karrama matan da suka lashe gasar Hikayata ta 2017


Gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai na shekarar 2017.

An gudanar da bikin karrawar ne a otel din Sheraton da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ranar Juma’a.

Maimuna Idris Sani Beli ta zama gwarzuwar gasar a bana, inda aka ba ta lambar yabo da kuma $2000.

Maimuna, wacce ta fito daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labarinta ne mai suna “”Bai Kai Zuci Ba”.

“Fasalin bayar da labarin”, a cewar jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi, “da yadda ya ginu, da yadda aka fita daga duniyar da muke ciki aka koma lahira; daga lahirar aka dawo Najeriya, a cikin Najeriyar kuma aka bi wurare daban-daban aka gina labarin.”

Image caption

Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu

Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu, da labarinta mai suna “Zawarcina“, yayin da Habiba Abubakar da Hindatu Sama’ila Nabame Argungu ne suka yi na uku a labarin hadin gwiwa da suka shigar, mai suna “Sana’a Sa’a”.

An zabi labaran ne bayan fafatawar da matan da suka shiga gasar suka yi, kana alkalai kan gasar suka tantance labarai uku da suka dace da ka’idojin da aka shimfida.

Image caption

Habiba Abubakar da kuma Hindatu Sama’ila Nabame Argungu (daga dama) wadanda suka yi na uku

Da take karbar lambar yabonta, Maimuna ta yi godiya ga Sashen Hausa na BBC bisa wannan gasa da ya kirkiro ta mata zalla.

Wannan ne karo na biyu da BBC ta sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla.

Editan Sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, ya ce: “Mun gamsu da irin yadda aka nuna sha’awar shiga gasar da kuma irin labaran da aka turo, muna kuma farin ciki ganin cewa mun bai wa mata damar fadar labaransu. Fatanmu shi ne mata iyayenmu sun rungumi harkar rubutu na kagaggun labarai.”

Karanta wadansu karin labarai

Ayatollah Khamenei na Iran ‘Hitler’ ne – Yariman Saudiyya


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko Saudiyya za ta yi yaki da Iran?

Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman, ya bayyana jagoran addinin Iran a matsayin sabon Hitler na Gabas ta Tsakiya.

Yariman ya yi wadannan kalamai ne a yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin kasashen biyu.

Da yake gugar zana, Muhammad bin Salman ya ce yana da matukar muhimmanci a guji maimaita irin abun da ya faru a nahiyar Turai, a Gabas Ta Tsakiya.

Saudiyya da Iran dai manyan abokan fada ne, kuma a baya-bayan nan ana samun ci gaba da nuna yatsa tsakaninsu.

Zuwa yanzu dai Iran ba ta ce komai ba dangane da kalaman yariman Saudiyyar.

Yarima mai jiran gadon ya shaidawa jaridar New York Times cewa, “Ba ma son a sake samun sabon Hitler a Iran kamar yadda ya taba faruwa a Turai,” ya fada yana mai alakanta hakan da Ayatollah Ali Khamenei.

Yarima Muhammad ya kuma yi tsokaci kan yaki da cin hanci da yake a kasarsa, inda ya ce yakin da yake yi da cin hanci ba wai yanayi ba ne don neman mukami, tun da yawancin wadanda ake zargi da aka kama sun masa mubaya’a.

Yariman ya ce kiyasin kadarorin da aka bankado zai kai kusan dala biliyan 100.

Yarima mai jiran gadon ya kuma yi bayani a kan irin manufofinsa na sassauta dokokin addinin musulunci wanda ya ce Manzon Allah SAW ma yafi son haka.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Abubuwa biyar kan Yarima mai jiran gadon Saudiyya

Tun shekara biyu da suka gabata dai, Mohammed bin Salman, mai jiran gado, ya sake jan layi tsakanin mu’amalar kasarsa da Iran.

A farkon watan nan ne, ya zargi Iran da son jawo yaki a kasarsa, inda ya ce ita ce ta sa ‘yan tawayen Yemen suka kai harin makami mai linzami babban birnin kasar, Riyadh.

Amma Iran ta yi watsi da zargin.

Saudiyya dai kasa ce da mafi yawan mabiyanta Musulmai ne ‘yan Sunni, yayin da mafi yawan ‘yan Iran ‘yan Shi’a ne.

Saudiyya na zargin Iran da taimakawa mayakan sa kai na Houthi masu bin tafarkin Shi’a a Yemen, inda Saudiyyar ke jagorantar wata gamayyar kawance, da ke ta tafka yaki tun shekarar 2015.

Iran dai da mayakan Houthi sun yi watsi da wannan tuhuma.

An yi ta zargin Saudiyya da damalmala rikicin da ke faruwa a Yemen, inda mutane ke cikin halin ha’ula’i, da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da mafi muni da aka taba samu a duniya.

Saudiyya ta kuma yi gargadi kan yadda Iran ke shiga cikin al’amuran Iraki, inda mayakan sa kai ke fafatawa da mayakan IS, da kuma Syria, inda sojojin Iran din ke taimakon Shugaba Bashar al-Assad don ya samu nasara a yakin basasar kasar.

Dukkan kasashen biyu suna zargin juna da son kawo rashin zaman lafiya a Lebanon, inda Firai ministan da Saudiyya ke goyon baya ya jagoranci wata gamayyar kawance da ta hada da kungiyar Hezbolla da Iran ke goyon baya.

A baya-bayan nan ne Firai minista, Saad Hariri ya sanar da cewa ya dakatar da janyewarsa, inda yake zargin Iran da Hezbollah jawo sabani, yayin da Iran kuma ke zargin Saudiyya da rura wutar rikicin.

Ficewar Atiku Abubakar ba ta bamu mamaki ba -Elrufai


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

El rufai ya ce da ma suna da sane da shirinsa na barin jami’yyara watan gobe

Daya daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki ya ce ba za su rasa bacci ko na dakika guda ba don tsohon Mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar.

Gwamna Nasiru Elrufa’i na jihar Kaduna ya ce da ma suna sane da shirinsa na barin jam’iyyar a watan gobe.

Ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, ya dauki wannan mataki bayan taron da wasu gwamnoni da suka fito daga yankin arewa suka yi a kwaakin baya baya nan.

Gwamnanonin sun yi kira ga shugaba Muhammdu Buhari akan ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.

Shugaban kungiyoyin da ke goyon bayan Atiku Abubakar ya tabbatarwa da BBC wannan labari, sai dai bai bayyana jam’iyyar da yake son komawa ba zuwa yanzu.

A wata sanarwa da Atikun ya fitar tun da fari, ya ce ya bar jam’iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya na kawo sauyin halin da kasar take ciki.

Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman-zamansa jagororin jam’iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam’iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam’iyyarsa ta PDP.

Atiku ya kara da cewa an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba.

“A kan wannan dalili ne mambobin jam’iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin binkundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci.”

“A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam’iyyar a watan Fabrairun 2014, don a lokacin ba ni da jam’iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Duk jam’iyyar da ba za ta kula da al’amuran matasa ba to matacciyar jam’iyya ce. Makomar kasar nan tana hannun matasa ne.”

A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauye-sauyen jam’iyya daga waccar zuwa wata.

An ceto mutum 500 daga hannun masu fataucin mutane


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An yi kamen ne a kasashen Chadi da Niger da kuma Mauritania

Hukumar yan sanda ta kasa da kasa ta ce samamen hadin giwa da suka kai da yan sanda a wasu kasashen Afrika 5 ya sa sun kubatar da mutane 500 rabi daga cikinsu yara kanana ne.

Hukumar ta Interpol ta kuma ce jamianta sun capke mutum 40 wadanda ake zargin masu fataucin ne.

Ta ce samamen da ta kai ya sa jamianta sun kama mutanen a kasashen Chadi da Mali da Mauritania da jamhuriyar Niger da kuma Senegal.

Ta ce akwai lamarin da ya sahafi wata yar Niger mai shekara 16 da aka tilastawa shiga karuwanci a Mali domin ta iya biyan bashin take bin wadanda suka dauki nauyin tafiyarta.

Wasu kuma an turasu ne domin su dinga yin bara kan tituna.

Yan sanda daga Faransa tare da hadin gwiwar takwarorinsu da ke Code d voire da kuma Kamaru suka kai samamen.

Hukumar ta interpol ta ce zaa gurfanar da mutane a gaban kotu a kasashen da aka kamasu kan tuhumar da ake yi masu da suka hada da safarar mutane da da aikin tilas da kuma da kuma ci da gumin yara.

A cikin mutane 500 da aka kubutar ,236 daga cikinsu yara ne kuma hukumar kula da masu kaura ta duniya tace zata taimaka mu su kan akan yadda zaa maidasu gida .

Ra’ayi: Ko wanne darasi za a koya daga dambarwar siyasar Zimbabwe?


A wannan makon ne Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 a kan karagar mulki ya yi murabus. To shin hanyar da Mr Mugabe ya sauka za ta iya kasancewa wata sabuwar hanya ta kawar da Shugaban da ya kwashe shekaru ya na mulki a Afrika? Wane darasi ne kuma ya kamata sauran shugabannin nahiyar za su dauka game da abinda ya faru a Zimbabwe? Batutuwan da muka tattauna a filinmu na Ra’ayi Riga kenan.

Yau ake karrama wadanda suka lashe Gasar Hikiyata


Hakkin mallakar hoto
Maimuna Beli

Image caption

Maimuna Idris Beli wadda ta lashe Gasar Hikayata ta bana

Daga Jimeh Saleh, Editan Sashen Hausa na BBC

Wannan wani abin tarihi ne ga BBC Hausa, da kuma miliyoyin masu sauraronmu inda ake karrama wadanda suka lashe gasar gajeren kagaggen labari karo na biyu.

A bara ne aka fara gabatar da gasar don bayar da kwarin gwiwar rubuta a tsakanin mata da kuma ba su damar bayyana labarinsu.

Muna da yakinin cewa mata na da labarai masu kayatarwa, kuma mun tabbatar da hakane ta hanyar labaran da muke samu kodayaushe.

Shahararriyar hirar da muka yi da Nawal Alhawsawy a bara, (wato wata mace mai tukin jirgin saman Saudiyya ta farko ‘yar asalin Najeriya), na cikin labaran da suka yi fice wajen karantasu da kuma yada labaran a shafinmu.

Har ila yau tattaunawarmu da matar shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari, ta zama ruwan dare game duniya.

Kwanaki kadan da suka gabata ne muka tattauna da Had wacce take sanye da hijabi.

Ita ma labarinta ya karade duniya da kuma an yada shi a shafikan sada zumunta na zamani dabam-dabam.

Mun san cewa kowanne lokaci idan mata suna magana mutane suna saurarensu.

Kuma sun fi mayar da hankali idan suna rubutu.

A lokacin da muka bijiro da gasar a bara, mun yi shawarar fara wanannn gasa ne daga matan da suka yi nasara da shirye-shiryen da muka gabatar a kan littattafan soyayya na Hausa a Kano, wanda yawancin mata suka rubuta.

Mata suna yin rubutu a kan burikansu, da abun da yake damunsu da kuma abubuwan da suke faruwa a zahiri na yau da kullum.

Muna son kai wannan aiki mai cike da basira zuwa wani mataki, saboda haka ne muka kirkiri wannan gasa ta Hikayata.

Wacce ta lashe gasar ta bara ita ce Aisha Sabiu, wacce take da ‘ya’ya uku ‘yar asalin jihar Katsina.

Labarinta da ta rubuta Sansanin ‘yan gudun hijira, ya yi bayani ne a kan ziyarar da ta kai sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar Adamawa a Najeriya, inda ta yi ido biyu da wadanda suka shiga rikicin Boko Haram.

Gajeren labari ne amma kuma a zahiri dogo ne, mai cike da sosa zuciya wacce ta gina labarin a kanta wato Falmata ta fada cikin rikici da kuma azabar Boko Haram, inda mayakan suka kashe iyayenta da kuma dan’uwanta.

Daga baya kuma mayakan suka sace ta suka yi mata fyade.

Daga karshe Falmata ta samu nutsuwa da samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira, inda take aikin sa- kai a matsayin mai taimaka wa sauran mutanen da rikicin ya shafa.

A take wadanda suka samu nasarar lashe gasar suka zama taurari, kuma na tuna lokacin da Aisha ta kasa cewa komai tana zub da hawaye, a lokacin da aka bukaci ta yi jawabi.

Har aka tashi daga bikin karramawar ba ta daina zubar da hawayen farin ciki ba.

Nasarar da muka samu a bara ne, ta ba mu kwarin gwiwar yanke shawarar mayar da gasar duk shekara, kuma mun kara kudin kyautar daga dala 500 zuwa dala 2,000.

Hakika ba kawai batu ne akan kudi ba kamar yadda yawancin marubutan suka sani, sai dai karramawar da marubuci zai samu ta kuma zaboshi da (alkalai suka yi) a matsayin fitacce daga cikin daruruwan wadanda suka shiga gasar abin alfahari ne.

Image caption

Aisha Sabitu wadda ta lashe Gasar Hikiyata ta bara

Aisha Sabitu ta samu nasarar lashe gasar ne saboda alkalan ma sun yi tsammanin kwararriyar marubuciya ce.

Kuma salon ya yi kama da na wacce ta lashe gasar bana Maimuna Sani Beli, wadanda dukakninsu sun yi aure tun suna yara.

Labarin Maimuna, Bai kai zuci ba, labari ne da yake magana a akan wata mace da take da makon ‘ya’yanta, kuma take yawan yin mafarki a kan abin da zai iya faruwa idan ta mutu.

Inda ta fada wa mijinta cewa idan ta mutu ya auri aminiyarta wacce take son yara saboda za ta afi kula da ‘ya’yanta.

Kodayaushe tana yin mafarki ta mutu kuma ta yi fatalwa inda take zuwa wurin ‘ya’yanta.

Alkalan sun bayyana salon rubutun Maimuna a matsayin sassaukan salo da kuma kirkira, inda labarin yake yawo da mai karatu daga duniya zuwa lahira.

Shugaban alkalan Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce “ba kowa ne marubuci ba ne yake iya gina labari rayuwa bayan mutuwa ba.

Nan gaba kadan kuma sanar da wadanda suka lashe gasar da kuma sauran labaran da alkalan suka zaba.

Kuma na tabbata da zarar mun saka labaran a shafinkanmu na sa da zumunta tambayoyin da aka yi a baya za su sake biyo baya, me ya sa gasar ta mata ce zalla?

Me ya sa ba za a ba wa maza marubuta dama ba?

Maza ma za su iya shiga sahun masu gasar?

Irin tambayoyin da ake yi ke nan.

Na sha amsa wasu daga cikin irin wadanann tambayoyin a lokuta da dama tun daga lokacin da aka fara gabatar da gasar a bara, amma har yanzu mutane suna damuwa a kan me ya sa gasar ta mata zalla ce?

Dalilinmu kuwa mai sauki ne.

Zama da kishiya, mutuwar aure, auren wuri, lalata mata da yi musu fyade na cikin matsalolin da mata suke fuskanta musamman a al’ummar Hausawa.

Matsalar na da alaka da talauci waye ya cancanci ya yi rubutu a kan wadannan matsalolin a zahiri da kuma tabbacin shi ne ya shiga irin wannan halin?

Wacce ta lashe gasar ta bana kammala makarantar sakandare ba aka yi mata aure a lokacin ta na da shekara 14.

Sai dai kuma wani abin sha’awa Maimuna ta ci gaba da karatunta a makarantar matan aure bayan da ta haifi danta na biyu.

Wani dalilin kuma da ya sa gasar ta mata zalla ce shi ne, tarihi ya nuna cewa, mata ne suke a sahun gaba a adabin al’ummar Hausawa.

Har yanzu duniya tana alfahari da gudunmawar da Nana Asma’u ta bayar, ‘yar Usman Dan Fodio wanda ya jaddada addinin Musulunci a karni na 19.

Har yanzu ana nazarin wakokinta a jami’o’i a fadin duniya.

Wanann al’ada ta bunkasa adabi ne mata suke ci gaba da yi a yau.

Daya daga cikin alakalan gasar ta bana, Balaraba Ramat Yakubu, ta zama abar buga misali a fagen mata masu rubuce-rubuce.

Daya daga cikin littattafanta shi ne Alhaki Kuykuyo Ne, inda aka juya shi zuwa harshen Turanci kuma ana iya samun shi a kasuwa.

Irin wannan rubutu na bayyana ra’ayi na mata musamman ga Hausawa da suke sasssan duniya, muna alfahari da nasarar da muke samu da tarihin da muka kafa na Hikayata.

Yanzu kuma muna aiki akan buga labaran da suka yi nasara, muna sa ran nan gaba kadan kuma za mu iya amfani da wadansu labaran a bangaren talabijin.

Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauye-sauyen jam’iyya daga waccar zuwa wata

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC.

Shugaban kungiyoyin da ke goyon bayan Atiku Abubakar ya tabbatarwa da BBC wannan labari, sai dai bai bayyana jam’iyyar da yake son komawa ba zuwa yanzu.

A wata sanarwa da Atikun ya fitar tun da fari, ya ce ya bar jam’iyyar APC ne saboda gazawarta wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya na kawo sauyin halin da kasar take ciki.

Ya kara da cewa a shekarar 2013 yana zaman-zamansa jagororin jam’iyyar APC suka same shi da gayyatar ya shiga jam’iyyarsu bayan da aka samu rarrabuwar kai a jam’iyyarsa ta PDP.

Atiku ya kara da cewa an zauna an cimma yarjejeniya kan yadda abubuwa za su kasance don APC ta samu nasara a zaben 2015, amma kuma ba a cika sharuddan ba.

“A kan wannan dalili ne mambobin jam’iyyar APC suka roke ni, da alkawarin kawo gyara a duk wasu abubuwa marasa kyau na rashin adalci, da kuma rashin binkundin tsarin mulki da PDP ke yi a wancan lokaci.”

Buhari ya yi watsi da wadanda suka taimake shi — Atiku

Atiku ya kalubalanci masu cewa ya yi sata su ba da hujja

Atiku ‘na so talakawa su karbi mulki’

“A kan wannan dalili ne da kuma alkawura ya sa na shiga jam’iyyar a watan Fabrairun 2014, don a lokacin ba ni da jam’iyya, saboda tabbacin da APC ta ba ni,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Duk jam’iyyar da ba za ta kula da al’amuran matasa ba to matacciyar jam’iyya ce. Makomar kasar nan tana hannun matasa ne.”

A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauye-sauyen jam’iyya daga waccar zuwa wata.

An kashe mutum 184 a masallacin Juma’a a Masar


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

An kai harin ne a wani masallaci kusa da garin al-Arish

An kai wani harin bam a wani masallacin Juma’a da ke yankin arewacin Sinai na kasar Masar, inda ya kashe akalla mutane 184, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ta bayyana.

Wadansu ganau sun ce an kai harin ne a masallacin al-Rawda wanda yake garin Bir al-Arish yayin da ake sallar Juma’a.

‘Yan sanda sun ce wadansu mutane hudu ne da ke kan wani abin hawa suka bude wa masallatan wuta.

Kasar Masar tana fama da rikice-rikice masu nasaba da ‘yan gwagwarmaya a yankin Sinai tun a shekarar 2013.

An sha fuskantar hare-hare ‘yan gwagwarmaya a yankin Sinai, amma wannan ne hari mafi a yankin.

Wadansu hotuna da suka fito daga masallacin sun nuna mutanen da abin da ya rutsa cikin jini.

Akwai akalla mutane 125 da suka ji raunuka, a cewar wani rahoto.

Wani rahoto ya ce an nufi harin ne a kan wadansu mutane da suke goyon bayan jami’an tsaro kasar wadanda suke salla a masallacin.

Wadansu mutane sun ce mabiya darikar Sufaye suna yawan halartar masallacin Juma’a.

Kungioyin ‘yan gwagwarya ciki har da kungiyar IS suna yi Sufaye kallonsu a matsayin wadanda akidarsu ta sha bamban da sauran Musulmi.

Sai dai har yanzu babu wadda ya dauki alhakin harin.

Karanta wadansu karin labarai

Wadda ake zargi da kashe mijinta ta bayyana a kotu rike da Kur’ani


Image caption

Maryam a gaban kotu

Matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, ta bayyana a gaban wata babbar kotu da ke Abuja ranar Juma’a.

Lauya mai shigar da kara ya ce suna so su sauya tuhume-tuhume saboda sabbin hujjoji da aka samu sakamakon bincken da ake yi mata.

Maryam ta shiga kotun ne tana rungume da jaririyarta da kuma Al-Kur’ani a hannunta, inda ta lullube fuskarta ba a iya gani.

An karanta mata tuhume-tuhume da ake mata.

Ana tuhumurta da dabawa mijinta fasasshiyar kwalba a kirji wanda ya yi sanadin mutuwarsa, ‘amma ta musanta hakan tana mai zubar da hawaye,’ in ji wakilin BBC da ke wajen.

Tuhuma ta biyu an ce ta ji masa ciwo da kwalba a kirji wanda ya yi sanadin mutuwarsa, a nan ma Maryam ta ki amsa laifinta.

Lauya mai kare wadda ake kara ya ce ba sa sukar dage zaman shari’ar sai dai suna so a ba da wadda ake zargi beli.

Kotun dai ta bayar da umarni a atsare ta a gidan yari na Suleja.

An kuma dage zaman shari’ar zuwa 7 ga watan Disamba

Ana zargin ta ne da kashe mai gidanta, Bilyaminu Bello, bayan ta daba nasa wuka a sassan jikinsa.

Al’amarin ya faru ne a gidan ma’auratan da ke unguwar Maitama a Abuja.

An rantsar da Emmerson Mnangagwa sabon shugaban Zimbabwe


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yada aka rantsar da Emmerson Mnangagwa

An rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasr Zimbabwe, a wani biki da dumbin jama’a suka taru makil a filin wasa na Harare, babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan yin murabus da Shugaba Robert Mugabe ya yi ne, bayan shekara 37 da ya shafe yana mulkin ‘kama-karya.’

Korar da Mista Mugabe ya yi wa mataimakin nasa a farkon watan nan ce ta jawo jam’iyya mai mulki ta Zanu-PF da kuma sojoji suka tursasawa Mugabe yin murabus.

Mr Mnangagwa, wanda a baya ya bar kasar, ya koma Zimbabwe daga Afirka Ta Kudu inda ya je neman mafaka.

Jam’iyyar adawa ta nemi Mista Mnangagwa, wanda ya zamto daya daga cikin masu fada a ji a mulkin kasar, da ya kawo karshen al’adar cin-hanci da rashawa da ta addabi kasar.

Yaya ranstuwar shan mulkin ta gudana?

An gabatar da bikin rantsuwar ne a Filin Wasanni na Kasar, kuma masu shirya bikin sun yi kira ga al’ummar Zimbabwe da su fito kwansu da kwarkwatarsu don shaidar wannan rana mai dumbin tarihi.

Mr Mnangagwa ya je wajen ne karkashin rakiyar matarsa Auxilia.

Manyan baki da suka hada da shugabanni daga kasashen Afirka daban-daban sun je bikin rantsuwar.

Babban mai shari’a na kasar Justice Luke Malaba ne ya rantsar da Mr Mnangagwa.

Daga bisani kuma an yi ta harba bindiga a matsayin gaisuwar ban girma, sannan kuma sabon shugaban zai gabatar da jawabi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An zargi Mista Mugabe da son dora matarsa a matasyin shugabar kasa bayan ya sauka

Hanyar warkar da gane-ganen mutanen ɓoye


Hakkin mallakar hoto
KING’S COLLEGE LONDON

Image caption

Mutum-mutumin kwamfyuta uku da aka yi amfani da su wannan gwaji na tsawon makwanni

Wasu masu bincike sun ce mutanen da ke fama da ɗimuwar kwakwalwa, na iya amfana daga wata sabuwar hanyar warkarwa.

Hanyar dai za ta ba su damar yin gaba da gaba da wata surar mutumin kwamfyuta da ke shirbicen da akasari suke ji a kwakwalensu.

An gudanar gwajin ne a London kuma sakamakon ya nuna cewa hanyar warkarwar surar mutumin kwamfyutar, ta fi tasiri wajen rage gane-ganen mutanen boye a kan ta hanyar amfani da kwantar da hankali da lallami.

Masu binciken sun ce bakwai a cikin mutum 75 da suka shiga gwajin na tsawon wata uku sun daina jin irin wadannan muryoyin sumbatu.

Masu larurar da suka samu wannan magani na ci gaba da samun karancin gigita sun kuma rage jin muryoyin sumbatu, idan an kwatanta da mutanen da ake kwantar wa hankali da lallaminsu.

Kwararru sun ce hanyar warkarwar ka iya samar da karin wata muhimmiyar damar magani ga masu larurorin gane-ganen mutanen boye sakamakon ɗimuwar kwakwalwa.

An wallafa gwajin wanda aka yi wa mutum 150 a mujallar nazarin larurorin kwakwalwa ta The Lancet Psychiatry.

Bayan wani kwarya-kwaryan nazari na zakaran gwajin dafi a shekara ta 2013.

Ganin mutanen boye abu ne ruwan dare ga masu larurar dimuwa wadda ka iya zama barazana.

Daya daga cikin maras lafiya hudu na ci gaba da faman jin amon muryoyin sumbatun duk da magunguna da kuma jinyar amfani da hujjojin zahiri da aka yi musu.

A wannan nazari da King’s College ta London da Jami’ar College London suka gudanar, marasa lafiya guda 75 da suka ci gaba da jin amon muryoyi a kwakwalensu sama da tsawon shekara guda, an kula da su ta hanyar amfani da surar mutumin kwamfyuta tsawon mako shida, yayin da wasu 75 kuma aka yi musu jinyar kwantar da hankali da lallami.

Gwajin ya ba marasa lafiya damar kirkiro wata sura a kwamfyuta wadda za ta wakilci amon muryar da suke ji kuma suke son dakilewa, ciki har da yadda ake jinta da kuma yadda mai yiwuwa siffarta take.

Hakkin mallakar hoto
KING’S COLLEGE LONDON

Image caption

Farfesa Tom Craig na aiki matsayin mai shiga tsakanin maras lafiya da surar mutumin kwamfyutar a wannan gwaji

Masu ba da jinyar daga nan sukan sanya surar yin magana a lokacin da su ma suke tsoma baki a wani salon hira tsakanin mutum uku don taimaka wa mai larurar ya fi zakewa.

Farfesa Tom Craig, daga King’s College ta London, ya ce koya wa mai larurar yadda zai fuskanci surar kwamfyutar an gano na da aminci da kuma saukin yi haka zalika na da tasiri ninki biyu a kan amfani da hanyar kwantar da hankali da lallami wajen rage jin muryoyin shirbice.

“Bayan mako 12 an samu gagarumin ci gaba idan an kwatanta da sauran hanyar warkarwa,” in ji shi.

“Ta hanyar amfani da muryar sambotsai, masu larurar suna koyon yadda za su tunkari surar kuma su ji amsa daga gare ta.

Ana karfafa gwiwar masu larurar su yi magana da surar kwamfyutar har ma su fi ta zakewa ta hanyar fadar kalamai irinsu, “Ni ba fa zan ci gaba da biye maka ba.”

BBC ta ziyarci Ritz Calton otel wanda Saudiyya ta mayar gidan yari


A farkon watan nan ne hukumomin Saudiyya suka tsare wadansu ‘yan gidan sarautar kasar ciki har da ministoci hudu a birnin Riyadh.

Ritz Calton otel ne da shugabannin kasashe da firaministoci ke sauka, domin masauki ne na hamshakan attajirai, sai dai yanzu ya koma wani gidan yarin kasaita ga yarimomin gidan sarautar.

A wannan otel din ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sauka lokacin da ya kai ziyararsa ta farko kasar a watan Mayun da ya gabata.

‘Yan Zimbabwe na tururuwa don rantsar da Mnangagwa


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Dumbin ‘yan kasar ne suka fita kan tituna suna murnar sauka daga mulkin Mugabe

Dubban ‘yan Zimbabwe ne ke tururuwa zuwa filin wasa na Harare, babban birnin kasar don shaida rantsuwar tsohon ministan tsaron kasar mai shekara 75, Emmerson Mnangagwa da ake yi wa lakabi da “Kada”.

Emmerson Mnangagwa na maye gurbin Robert Mugabe wanda ya shafe tsawon shekara 37 a kan karagar mulkin kasar Zimbabwe.

Ba lallai ne tsohon shugaban kasar ya halarci bikin rantsar da magajin nasa ba, wanda tun bayan saukarsa mulki sakamakon matsin lamba daga sojoji ba a gan shi a bainar jama’a ba, .

Sojojin kasar sun dauki matakin goya wa Mnangagwa baya ne lokacin da aka kore shi daga mukamin mataimakin shugaban kasa yayin wata gwagwarmayar iko da tsagin da ke biyayya ga Grace, matar Robert Mugabe.

Mista Mugabe da Mnangagwa sun yi aiki kafada da kafada tun lokacin gwagwarmayar kwatar ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekarun 1970.

Kungiyar Raya Kasashen Kudancin Afirka ta ce a shirye take ta yi aiki kut-da-kut da sabon jagoran Zimbabwe.

Wadanne kalubale ne a gaban sabon shugaba Mnangagwa?


Image caption

Emmerson Mnangagwa

A yau jumma’a ne da musalin karfe 11 na rana gogon Najeriya wato 12 na rana agogon Zimbabwe ake sa ran rantsar da Emmerson Mnangagwa.

Za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe da zai maye kujerar Robert Mugabe.

Tun dai da musalin karfe 6 da muti 30 na safe agogon kasar ne aka bude kofofin babban filin kwalo na Harare.

Wurin da zai kasance dandalin da shugulgullan rantsar da sabon shugaban za su gudana.

Kafin dai a rantsar da sabon shugaban,ya fara kiraye-kiraye ga al’ummar kasar.

Ana dakon rantsar da sabon Shugaban Zimbabwe

Karanta tarihin Shugaba Mugabe na Zimbabwe

Dakarun soja sun kwace iko a Zimbabwe

Image caption

Tsoho da Sabon sarkin Zimbabwe

Mnangagwa ya yi kira ga ‘yan kasar da su yi watsa da lamura irin na ramuwar gaya .

Haka ma kuma da su guji gudanar da siyasa irin ta fifita kai .

A yau din daga bakin karfe 11 da rabi agogon Zimbabwe, Sabon shugaban zai sha rantsuwar kama aiki.

Wannan zai gudana a gaban alkalin alkailai na kasar, Honourable Justice Luke Malabo kafin kuma ya kama aiki gadan-gadan.

Daga cikin manyan kalubalen da ke gaban sabon shugaban, har da maganar bunkasa tattalin arzikin kasar da ya sukwykwyce .

Wasu kuma sun hada da maido wa kudin kasar dajarar su da samar da ayyukan yi ga dinbin matasan kasar da dai sauren su.

Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Najeriya


Image caption

Dumbin mata da kananan yara ne ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a ciki da wajen Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram

An fara kwaso yaran da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, bayan sun tsere zuwa Jamhuriyar Kamaru, da nufin hada su da iyayensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu daga cikin yaran dai marayu ne yayin da wasu kuma har yanzu iyayensu na nan da rai kuma an kwaso su ne cikin jirgin sama, wasu daga sansanin ‘yan gudun hijira na Minaoa.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ce ta dauki gabarar wannan aiki na sada irin wadannan yara da iyaye ko danginsu.

Wakilin BBC, Usman Minjibir ya yi kicibis da yaran da kungiyar ta kwaso a filin jirgin sama na Abuja, bayan sun ci zango a kan hanyar zuwa Maiduguri.

Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN ARMY

Image caption

Wasu daga cikin yara da iyayensu kenan a sansanin ‘yan gudun hijira na Rann da sojojin Najeriya suka kwato

Daya daga cikin yaran wanda ya ce shi dan asalin Bama ne a jihar Borno ya tsere ne sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram, inda ya rabu da iyayensa da su kuma suka nufi Maiduguri a lokacin.

Ya ce ya shafe kimanin shekara biyar rabonsa da ya ga mahaifansa don haka ba shi da tabbacin halin da suke ciki.

A cewarsa ya hada da jami’an kungiyar Red Cross ne a sansanin Minaoa da ke tattara bayanan yara wadanda ba sa tare da iyayensu a can.

Don haka sai shi ma ya bukaci su hada shi da iyayensa wadanda yake da yakini har yanzu suna birnin Maiduguri.

“Ina farin ciki bayan shekara kusan biyar ga shi muna hanyar zuwa Maiduguri. Ina farin ciki,” in ji shi.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin duniya ta fitar a shekara ta 2015 ya ce rikicin Boko Haram ya raba kananan yara kimanin miliyan daya da rabi daga gidajen iyayensu.

Boko Haram ba kawai raba kananan yara da iyayensu ta yi, tana ma kuma shigar yaran cikin kungiyar, inda ake sanya su kai hare-hare ciki har da na kunar-bakin-wake.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross International ta lashi takobin sake sada irin wadannan yara da mahaifansu. kuma a jiya Alhamis ta debo guda takwas.

Ta ce kuma ce za ta ci gaba da wannan aiki har sai ta tabbatar da ganin ta hada fuskokin dukkan wadannan yara da suka tsere suka bar Najeriya.

Gwanayen Fifa: Jamus ta daya a duniya, Senegal a Afirka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Senegal ba ta taba samun cigaba ba a jerin sunayen na Fifa kamar na yanzu, inda ta tashi daga ta 32 zuwa ta 23

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta fitar da jerin sunayen wannan watan na kasashen da suka yi fice a wasan a duniya, inda Jamus ke zaman ta daya, Brazil na bi mata baya, yayin da Senegal ta 23 ke zaman ta daya a Afirka.

Wannan cigaba na Kungiyar ta Teranga Lions ta Senegal ya kasance ne sakamakon nasarar da ta yi sau biyu a kan Afrika ta Kudu a watan Nuwamba, abin da ya ba ta damar zuwa gasar kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa a Rasha

Ga jerin sunayen;

1. Germany 2. Brazil 3. Portugal 4. Argentina 5. Belgium 6. Spain 7. Poland 8. Switzerland 9. France 10. Chile 11. Peru 12.Denmark 13. Colombia 14. Italy 15. Englang

Duk da cewa Italiya ba ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa ba a Rasha, ta wuce Ingila.

Tunisia ce ta 27 a duniya yayin da take ta biyu a Afirka, sai Masar ta uku a Afirka amma ta 31 a duniya. Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo tana ta hudu a Afirka kuma ta 36 a duniya.

Sai Morocco tana matsayi na biyar a Afirka amma ta 40 a duniya, Burkina Faso na bi mata baya a Afirka amma ta 44 a duniya.

Kasar kamaru ta kasance ta bakwai a nahiyar Afirka yayin da take ta 45 a gaba daya. Sai kuma Najeriya wadda ke matsayi na takwas a Afirka, kuma ta 50 a duniya, wadda kuma ta kasance mafi koma baya a cikin kasashen Afirka da za su je gasar kofin duniya a Rasha.

Fyade: An yanke wa Robinho hukuncin zaman yari na shekara 9


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Robinho mai shekara 33 wanda bai je kotun ba ya musanta zargin

Wata kotu a Italiya ta samu tsohon dan wasan Brazil Robinho da laifin fyade,kuma ta yanke masa zaman gidan yari na shekara tara.

Kotun ta ce lamarin ya faru ne shekara hudu da ta wuce, lokacin da Robinho din yake wasa a kungiyar AC Milan. Matar da abin ya faru a kanta wata ‘yar Albaniya ce mai shekara 22, wadda Robinho din da wasu maza biyar suka far mata a wani gidan rawa.

Bisa tsarin shari’a na kasar ta Italiya ba za a aiwatar da hukuncin ba har sai an yi ta daukaka kara, zuwa matakin karshe.

Robinhon wanda ya musanta zargin, bayan AC Milan din ya kuma yi wasa a Real Madrid da Manchester City sannan ya tafi China, kafin kuma ya koma wasa a Brazil.

Fifa za ta dakatar da kasar Gambia


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dokar Fifa ta hana wata hukuma ta daban ta tsoma baki kan harkokin kwallon kafar wata kasa

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta ce dole ne hukumar wasanni ta kasar Gambia, ta soke hukuncinta na dakatar da shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasar nan da ranar Litinin 27 ga watan nan na Nuwamba.

A wasikar da Fifa ta aika wa hukumar ta yi gargadin cewa idan har ba a yi hakan ba zuwa wa’adin, ta ce za ta dauki mataki wanda zai iya hadawa da hana shigar kasar ta gambia harkokin wasannin kwalllon kafa na duniya.

Har zuwa yanzu dai hukumar wasannin ta Gambia ba ta ce komai ba game da wa’adin na hukumar kwallon kafar ta duniya.

A ranar 10 ga watan nan na Nuwamba ne hukumar wasannin ta kasar ta dakatar da shugabancin hukumar kwallon kafar ta Gambia a kan zargin aikata almundahana.

Hukumar ta ce ta dakatar da shugabannin ne domin a samu damar gudanar da bincike kan zargin ba tare da sun yi katsalandan a ciki ba.

Idan dai har Fifa ta dakatar da kasar, to hakan zai hana kungiyoyinta shiga wasannin nahiyar Afirka, kuma ba wata tawagar wasan kasar da za ta shiga wata gasa da Fifa ta amince da ita.

Haka kuma hukuncin zai iya hana zuwan alkalin wasa Papa Gassama, wanda shi ne ke samun lambar gwarzon lafiri na Afirka karo uku, gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi a Rasha.

Abubuwan kara kuzari: Ministan Rasha ya zargi hukumomin duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rahoton McLaren ya gano cewa an yi matukar amfani da abubuwan kara kuzari a wasa a Rasha

Ministan wasanni na Rasha ya ce bai kamata a dora alhakin matsalar shan abubuwan kara kuzari a wasa ba, wadda ta dabaibaye gasar Olympic ta huturu ta 2014 da aka yi a Sochi, Rasha.

Vitaly Mutko wanda ya ce an yi hakan ne kawai domin bata sunan kasar, ya ce kamata ya yi a dora alhakin a kan hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta duniya da kuma kwamitin shirya wasan Olympic na duniya.

Ya ce wadannan hukumomi biyu su ne suka gaza a aikinsu, na tabbatar da bin ka’idoji a wasannin na Sochi.

Ministan ya ce an rudi mutane da cewa Rasaha ce da laifi kan badakalar amfani da abubuwan kara kuzarin a wasa, har ma ba wanda yake tunanin irin nauyin da ya rataya a wuyan kwamitin shirya wasan Olympic din na duniya da kuma hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasa ta duniya.

Mista Mutko ya ce me suke yi a can? Suna barci ne?

A watan satumba, hukumomin hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasa na kasashe 17 suka bukaci a haramta wa Rasha shiga gasar da za a yi daga ranar 9-25 ga watan Fabrairu a Pyeonchang, suna masu bayar da shedar almundahana a wasannin Sochi na 2014, da kuma gazawar Rasha ta tsaftace harkar wasa.

Hukumar shirya wasan Olympic din ta duniya za ta yanke hukunci kan ko za a bar Rasha ta shiga gasar wasan Olympic ta huturu ta 2018, a taronta na gaba wanda za a yi daga ranar 5-7 ga wata na Disamba.

An ki daukar matasa aikin asibiti saboda shan kwaya a Kano


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana yawan kama muggan kwayoyi a sassan Najeriya

Ta leko ta koma ga wasu mutane kimanin 30 wadanda aka dauka aiki a asibitin kashi na Dala da ke birnin Kanoa arewacin Najeriya.

An dai janye matakin ba su aikin ne bayan da aka yi masu gwaje-gwajen shan miyagun kwayoyi kuma aka gano suna shan muggan kwayoyin.

Suna dai cikin mutum kimanin 150 da aka dauka aikin jinya a asibitin, daga cikin dubban mutane da suka nemi aikin.

Gwajin shan muggan kwayoyi dai ba wajibi ba ne ga masu neman aiki a fadin Najeriya.

Sai dai kuma daraktan watsa labarai na asibitin kashin na Dala Tijjani Musa Muhammad, ya shaida wa BBC cewa, asibitin ya dauki matakin gwajin shan kwayar ne a daukar aiki na baya-bayan nan, saboda a tabbatar an dauki ma’aikatan jinya masu cikakkiyar lafiyar kwakwalwa, saboda yadda aikin likita ke bukatar taka tsan-tsan da kuma nutsuwa.

“Yanzu idan aka ce an dauki mai tu’ammali da shan kwaya, ai ka ga akwai hadari ga su kansu marasa lafiyar.,” in ji shi.

Ya ce ba zai iya tabbatar da adadin sabbin ma’aikata da ba a ba su aikin ba, saboda samun su da shan kwaya.

Amma dai wasu majiyoyi a asibitin sun ce sabbin ma’aikatan da al’amarin ya shafa sun kai 30.

Kawo yanzu dai hukumomin ba su bayyana irin kwayoyin da aka gano mutanen suna tu’ammali da su ba.

Rahotanni sun ce sabbin ma’aikatan wadanda galibinsu matasa ne da suka kammala karatun jami’a sun fusata da aka shaida musu cewa ta-leko-ta-koma, saboda suna shan miyagun kwayoyi.

Asibitin kashi na Dalan ya ce a halin yanzu ma yana fama da wasu ma’aikatan biyar, wadanda aka dauka aiki a can baya, kuma suke fama da tabin hankali, ga alama sanadiyyar shan muggan kwayoyi.

Jihar Kano, wadda ita ce jiha mafi yawan jama’a a Najeriya ce kan gaba wajen shan muggan kwayoyi a kasar, a cewar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutum 30 ne aka samu da alamun shan kwaya cikin wadanda aka dauka aikin

An shigar da karar wadda ake zargi da kashe mijinta a Abuja


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rundunar ‘yan sandan Abuja dai ta ce za ta yi iya kokarinta wajen tabbatar da cewa doka ta yi aikinta

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Najeriya Abuja ta shigar da karar da Maryam Sanda da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka, a gaban kotu.

A wata sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar, ta ce ta shigar da karar Maryam Sanda ne gaban kotu ta 32 ta birnin tarayyar Najeriya, bisa tuhumar ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru.

A cikin sanarwar, rundunar ta ce abun da ake tuhumar Maryam Sanda da shi laifi ne a karkashin dokar kundin hukunta laifuka na Najeriya sashe na 221.

Sanarwar, wadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan birnin Abuja, Anjuguri Jesse Manzah, ya sanya wa hannu, ta ce rundunar ‘yan sandan ta samu damar ajiye Maryam Sanda na mako biyu domin ta samu ta kammala bincike game da kisan kan.

Har ila yau rundunar ‘yan sandan Abujan ta ce ta nemi damar rike Maryam Sanda ne domin tana da jaririya ‘yar wata shida, lamarin da zai sa ya yi mata wuya ta zauna a gidan yari, har zuwa lokacin da za a saurari karar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu damar rike Maryam Sanda na mako biyu domin ta kammala bincike

Sanarwar ta ce sai an kammala binciken ne sannan za a gano cewa ko za a iya sauya tuhumar da ake mata ko kuma za a tuhumi wasu mutanen daban da ake zargin tare suka aikata laifin da Maryam.

An kashe Bilyaminu Bello Halliru ne ranar 19 ga watan Nuwamba, kuma mutuwarsa na jan hankalin mutane da dama shafukan sada zumunta a Najeriya.