Kwanan nan zan yi sabbin nade-nade – Buhari


Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Buhari ya bayyana takaicin jinkirin nadin kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnati

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce nan ba da jimawa ba zai yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa domin amfanar jama’ar kasar.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a taron koli na jam’iyyar APC mai mulki da aka gudanar ranar Talata a Abuja.

Ya ce “za a fadada Majalisar zartarwa ta hanyar nadin magoya baya da za su kawo sabbin dabaru kan yadda ake tafiyar da gwamnati.”

Shugaba Buhari ya kuma bayyana takaicinsa kan jinkirin da aka samu wajen nadin mambobin kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya.

Ya danganta jinkirin ga wasu kwamitoci daya kafa don tabbatar da cewa an zabo mutane daga kowane bangare na kasar a kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin.

” Ya ce na san cewa magoya bayan mu sun kosa su ga an yi nade-naden, amma nan ba da jimawa ba za’a sanar musamman ganin yadda tattalin arzikin kasar ya inganta”.

Tun bayan daya dawo jinya daga Birtaniya a watan Agusta ne ake ta kiraye-kirayen shugaban ya sauke wasu daga cikin ministocinsa.

Sai dai Shugaba Buhari bai yi karin bayani ba a taron koli na jam’iyyar APC akan ko zai sauke wasu ministocinsa.

Masu lura da al’amaru dai na ganin babu kyakkawar dangantaka tsakanin shugaban kasar da wasu ministocinsa, musamman yadda wasu ministocin ba sa iya ganin shugaban kasar a duk lokacin da suke so.

A kwanakin baya ne aka tseguntawa manema labarai wata wasika da ministan mai Dokta Ibe Kachikwu ya aikewa shugaban kasar.

A cikin wasikar dai ministan ya nuna damuwa kan kokarinsa na ganawa da shugaban kasar a lokuta daban-daban amma bai samu dama ba.

Super Eagles ta gayyaci Ahmed Musa da ‘yan wasa 23


Hakkin mallakar hoto
The NFF

Image caption

Nigeria ce ta farko da ta fara samun tikitin zuwa Rasha domin buga gasar kofin duniya a 2018

Kocin tawagar kwallon kafar Nigeria, Gernot Rohr ya gayyaci ‘yan wasa 24 domin karawa da Algeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya da wasan sada zumunta da Argentina.

Super Eagles wacce tuni ta fara samun tikitin shiga gasar kofin duniya daga Afirka, za ta buga wasan karshe na cikin rukuni da Algeria a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Haka kuma kwana hudu tsakani wato ranar 14 ga watan Nuwamba, Nigeria za ta buga wasan sada zumunta da Argentina wanda za su kece raini a birnin Krasnodar na Rasha.

Super Eagles ta gayyaci sabbin ‘yan wasa da suka hada da Francis Uzoha da ke wasa a Deportivo La Coruna da tsohon dan wasan matasa ‘yan 17, Chidiebere Nwakali.

Shi kuwa Brian Idowu zai yi jiran ko ta kwana a wasan sada zumunta da Argentina.

An bukaci dukkan ‘yan wasan da aka gayyata da su iya sansanin horo a Morocco a ranar 6 ga watan Nuwamba, daga nan su iya Algeria a ranar 9 ga watan na Nuwamba.

Ga jerin ‘yan wasan da Super Eagles ta gayyata:

Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi (Chippa United, South Africa); Ikechukwu Ezenwa (FC IfeanyiUbah); Francis Uzoho (Deportivo La Coruna, Spain)

Masu tsaron baya: William Ekong (Bursaspor FC, Turkey); Abdullahi Shehu (Anorthosis Famagusta, Cyprus); Tyronne Ebuehi (ADO Den Haag, The Netherlands); Leon Balogun (FSV Mainz 05, Germany); Uche Agbo (Standard Liege, Belgium); Chidozie Awaziem (Nantes FC, France); Olaoluwa Aina (Hull City, England)

Masu wasan tsakiya: Mikel John Obi (Tianjin Teda, China); Ogenyi Onazi (Trabzonspor FC, Turkey); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Oghenekaro Etebo (CD Feirense, Portugal); John Ogu (Hapoel Be’er Sheva, Israel); Mikel Agu (Bursaspor FC, Turkey); Chidiebere Nwakali (Sogndal FC, Norway)

Masu cin kwallo: Ahmed Musa (Leicester City, England); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Alex Iwobi (Arsenal FC, England); Odion Ighalo (Chang Chun-Yatai, China); Henry Onyekuru (RSC Anderlecht, Belgium); Anthony Nwakaeme (Hapoel Be’er Sheva, Israel)

Masu jiran ko ta kwana: Kenneth Omeruo (Kasimpasa FC, Turkey); Alhassan Ibrahim (FK Austria Wien, Austria); Brian Idowu (FC Amkar Perm, Russia)

‘Yan Madrid da za su kara da Tottenham


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid da Tottenham suna da maki bakwai-bakwai a rukuni na takwas

Tun a sanyin safiyar Talata Real Madrid ta sauka a Ingila domin shirin karawa da Tottenham a wasa na biyu na cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai da za suyi a ranar Laraba.

Wasan farko da suka kara a Bernabeu kungiyoyin biyu sun tashi ne kunnen doki daya da daya.

Kuma Real Madrid da Tottenham suna kan teburin rukuni na takwas da maki bakwai-bakwai kuma duk wacce ta yi nasara za ta kai wasan zagaye na biyu.

Tuni kocin Madrid, Zinedine Zidane ya isa Ingila da ‘yan wasa 19 da yake sa ran fuskantar Tootenham da su.

Ga jerin ‘yan wasan da Real Madrid

Masu tsaron raga: Casilla da kuma Moha.

Masu tsaron baya: Vallejo, Sergio Ramos, Nacho, Marcelo, Theo da kuma Achraf.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, M. Llorente, Asensio, Isco da kuma Ceballos.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo, Benzema, Lucas Vázquez da kuma Mayoral.

Watakila Kane ya buga wasa da Madrid — Pochetino


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Kane ya ci kwallo biyar a wasa uku da ya buga a gasar cin kofin Zakarun Turai

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino yana da tabbacin cewar Harry Kane zai murmure domin buga gasar Zakarun Turai da za su kara da Real Madrid a ranar Laraba.

Kane ya ci wa Tottenham kwallo 13 a wasa 12 da ya buga wa kungiyar a bana, amma bai buga karawar da Manchester United ta doke su daya mai ban haushi a ranar Asabar a Premier ba.

Dan wasan ya buga atisaye a ranar Talata ana kuma sa ran zai iya fuskantar Real Madrid wacce suka tashi 1-1 a fafatawar da suka yi a Bernabeu.

Pochettino ya ce da sunan Kane a cikin wadanda za su kara da Madrid, kuma zai iya buga wasan amma ba shi da tabbaci dari bisa dari cewar zai saka shi a gumurzun.

Tottenham da Real Madrid suna mataki na daya da maki shida, sai Borussia Dortmund da Apoel Nicosia da suke biye da su.

Rasha za ta gina tashar wutar lantarkin Nukiliya a Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a gina sabbin tashoshin ne a jihohin Kogi da kuma Akwa Ibom

Kasar Rasha ta kulla yarjejeniyar ginawa da tafiyar da sabuwar tashar makamashin Nukiliya a Najeriya, kasar da take fama da matsalar karancin hasken wutar lantarki.

Wani kamfanin kasar Rasha, mai suna Rosatom, shi ne zai yi aikin gina tashar, wadda a zangon farko za ta samar da Megawatt 1000.

Wani jami’i a hukumar kula da makamashin Nukiliyar ta Najeriya wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa BBC batun gina sabuwar tashar.

“Za a samar da tashohi guda biyu ne a jihohin Kogi da kuma Akwa Ibom kuma kasar Rasha ce za ta fi zuba kudi a aikin, amma za a fara gina guda daya ne saboda yadda gina tashar yake tsada,” kamar yadda ya ce.

Ya ce ana fatan fara gina tashar a tsakanin “shekara daya zuwa biyu da ke tafe amma ba a sanya ranar farawa ba tukuna.”

A shekarar 2015 ne kasar ta fara tattaunawa da kamfanin Rosatom don samar da tashohin wutar lantarki hudu a lokacin a kan kudi dala biliyan 20.

Megawatta 4,500 na wutar lantarki Najeriya take samarwa a halin yanzu.

Karanta wadansu karin labarai

An kashe mutum 10 a cikin tasi a Afirka ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A kalla mutum 10 ne suka mutu a Afirka ta Kudu bayan da aka yi wa motar da suke ciki kwanton bauna a yankin KwaZulu Natal da ke bakin gabar teku.

Shugaban kungiyar ‘yan tasi na yin balaguro ne tare da dogaransa, lokacin da aka budewa motocinsu biyu wuta a garin Ladysmith.

Dukkan mutane biyar da ke cikin motocin sun mutu, kuma motar tasu ta yi taho mu gama da wata motar safa ta daukar fasinja inda wasu mutum biyar da ke ciki su ma suka mutu.

An sha samun matsalar tare motocin haya a hanyoyin yankin KwaZulu Natal.

“Ga dukkan alamu wannan hari na da halaka ne da wani rishin jituwa tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan tasi guda biyu,” a cewar ‘yan sanda.

Sai dai ‘yan sanda sun ce duk da cewa babu wani karin haske game da lamarin, za a ci gaba da bincike.

Nigeria za ta biya diyyar naira biliyan 88 na yakin Biafra


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fiye da mutum miliyan daya ne suka rasa rayukansu a yakin Biafra

Gwamnatin Najeriya ta amince za ta biya wadanda yakin Biafra ya shafa diyya da kuma kwashe ragowar abubuwan fashewar da suka a rage a yankin da aka yi yakin basasar a karshen shekarun 1960.

Kasar za ta dauki matakin ne bayan an cimma wata yarjejeniya da kotun Raya Tattalin Arzikin Kasashen yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta jagoranta.

Takardun kotun sun ce akwai fiye da bama-bamai 17,000 da aka gano a yankin.

Najeriya za ta biya naira biliyan 88 (kimanin dala miliyan 245) a matsayin diyyar ga wadanda yakin ya shafa, shekara 47 bayan kawo karshensa.

Za a biya naira biliyan 50 ne ga wadanda yakin ya shafa a jihohi 11 a yankin kudu maso gabashi, da kuma yankin arewa maso tsakiya wuraren da yakin ya fi shafa.

Ragowar kudin za a yi amfani da su ne wajen kwancewa da share nakiyoyin da suka rage a yankin, da kuma wajen gina makarantu da kotuna da coci-coci da kuma masallatai a yankunan.

Fiye da mutum miliyan daya ne suka rasa rayukansu sanadiyyar yakin, galibinsu saboda yunwa da kuma cututtuka a yakin da aka yi tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970.

An fara yakin ne biyo bayan ayyana ballewa da yankin Biafra daga Najeriya, wadanda galibi ‘yan kabilar Ibo ne suka jagoranta.

A ‘yan shekarun nan, jagoran kungiyar da ke fafutikar kafa kasar (IPOB) Nnamdi Kanu yana kafa hujja da rashin biyan diyyar wajen sake farfado da fafutikar ballewar yankin daga Najeriya.

Karanta karin labarai

Ruwan sama ya hallaka mutum shida a wasu kasashen Turai


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Bishiyoyi sun fado a kan motoci

Ruwa da iska mai karfin gaske sun yi kaca-kaca da wasu bangarori na yankin tsakiya da na arewacin Turai, inda har ya jawo mutuwar a kalla mutum shida a Jamus da Poland da kuma Jamhuriyar Czech.

Cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da wani dan shekara 63 da ya yi sansani ya yada zango a bakin gabar teku a Jamus, da kuma wasu ‘yan yawon bude ido biyu.

Karfin gudun iskar ya kai kilomita 180 a sa’a daya inda har ta kai nisan tsauni mafi tsawo a kasar Czech.

Daruruwan ‘yan kasar Poland da Czech sun kasance har yanzu babu wutar lantarki, yayin da aka samu ambaliyar ruwa a yankin tsakiyar birnin Hamburg na Jamus.

An dakatar da sufuri ta hanyoyin jirgin kasa a wasu yankunan na Jamus saboda lalacewar hanyoyi.

An sanar da yankewar layukan dogo da kuma hanyoyi a cikin kasar Czech.

Faduwar bishiyoyi saboda karfin iskar a Jamus da Czech da kuma Poland ya yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama.

A Jamus, rahotanni sun ce wata mata ‘yar shekara 48 da kuma wani namiji mai shekara 56 sun mutu bayan da jirgin ruwa ya tuntsure da su a jihar Mecklenburg-Vorpommern, da ke arewacin kasar.

Amma har a ranar Litinin ana ci gaba da neman mutum na uku da ya bace.

Ambaliyar ta zagaye wata kasuwar sayar da kifi a Hamburg.

Da akwai fargaba game da yanayin da wajen ajiyar man fetur na Jamus ya ke ciki a Glory Amsterdam da ke arewacin tekun kasar.

Hukumomi na sa ido don gane alamun yoyo da ma’ajiyar man ka iya yi, mai yawan tan 1,800.

Ana kokarin kai dauki ga wani gungun masu aikin jirage su 22 da ba su ji rauni ba domin ceto su, to sai dai karfin igiyar ruwan na kawo cikas ga kokarin da ake yi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tsikiyar birnin Hamburg na Jamus ya yi ambaliya

Ko Facebook na satar jin hirarrakinmu?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutane da dama sun ce suna jin Facebook na satar hirarrakinsu ta waya

Ko da yaushe Facebook yana musanta amfani da ‘yan kananan lasifikokin wayoyin zamani wajen tattara muryoyi daga hirarrakin jama’a daga nan sai ya yi amfani da irin wadannan bayanai don aika musu tallace-tallace.

Makon jiya mataimakin shugaban Facebook mai kula da harkokin talla, Rob Goldman, ya fada a sakon Twitter cewa katafaren kamfanin fasahar ba ya yi kuma bai taba yi ba.

“Kawai ba gaskiya ne ba,” ya fada a Tiwita.

Bisa la’akari da adadin tallace-tallacen intanet da mutane ke gani a kullum, akwai wata gagarumar mujadala, cewa tsagwaron arashi ne – watakila an sanya tallace-tallacen tun tuni, ba kuma tare da an lura da su ba, sai yanzu kawai hankali ya zo kansu.

Sai dai, akwai mutanen da sun yi yakinin cewa hakan ta faru a kansu. Ga irin labaran da wasu suka bayyana wa BBC.

Mun ga tallar bukukuwan aure kafin mu bayyana batun sa ranarmu

“Ni da wadda aka yi mana baiko sun samu tallace-tallace kan bukukuwan aure kwana guda bayan mun tsaida rana, tun kafin mu kai ga fada wa kowa,” a cewar Nate, daga Springfield, a Amurka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mun sayi zoben baiko bayan ganin tallarsa a intanet

“Cikin garaje muka sayi zoben sa rana ba tare da mun yi la’akari da wani abu mai alaka da haka ba.

“Duk da yake mako biyu a baya ni da ita mun je gidan wani abokinmu, muka sha barasa, wadda ba mu taba saya ko yin maganarta ba a wayar tarho, amma kwatsam da safe tallanta ne ya fara bayyana lokacin da ta bude shafinta na Facebook.”

Na’urar taimaka wa jina tana sadarwa da wayata

“A shekara ta 2016, Kunnena na dama ya daina ji. Sai aka ba ni wata ‘yar na’urar taimaka wa ji wadda ake hada ta da iPhone,” Jon a Amurka ya ce.

“Hakan ta sa ina iya amsa waya, na saurari kida da sauransu ta hanyar wannan sabuwar na’ura.

“Duk lokacin da na hada wayata da na’urar kara jin, nakan ji wani canji, kamar wata ‘yar kara dil, saboda za ta sauya karakainar da take yi daga duniyar da ke zagaye da ni zuwa sautin da take ji daga na’urar nan.

“A manhajar Facebook Masinja da ma shafina Facebook duka, ina jin irin wannan ‘yar karar, wato wayar ta sauya akalarta daga na’urar kara jina, an yi haka lokaci ya fi a kirga, kai ko da na kashe muryar wadannan manhajojin.”

Na samu wani talla kan aikin da na ambata cikin raha

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Cikin raha na ambata samun aiki a kamfanin sarrafa kofi

“Kawai makon jiya na bar aikina kuma na zauna da kawata muna hira a kan abin da zan yi nan gaba,” Lindsey daga Lincoln ta bayyana.

“Sai na ce, ‘Ai ko ina son shan kofi, Mai yiwuwa na tsinci kaina a kamfanin Starbucks, yadda zan rika shan kofi sosai.’

“Karo na gaba da na leka shafina na Facebook a kan wayata, [Sai na ga] wani tallan kamfanin sarrafa kofi na Starbucks, inda suke wani taro a London don neman sabbin ma’aikata.”

Kwatsam mun ga rumfar ajiye kwanduna shara bayan hirar

“Kwanan nan na samu wani talla da ake tura wa mutum da ya ba sa ni cikin mamaki matuka har na kasa nutsuwa, kai abin ya fi karfin arashi, bayan na yi waya ta manhajar WhatsApp,” a cewar Olivia, daga Austin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akwatin ajiye kwanduna zuba shara

“Ina cikin tafiya da kawata wadda ke zaune a London inda take fada min wani labari kan yadda sabon mai gidan hayarsu ya sayo wata rumfa da ake kafawa a waje don ajiye kwandunan shara.”

“Muka yi ta dariya a kan haka, har nake bayyana mata yadda ni ma nake bukatar irin wannan abu a nan Texas.

“Washe gari kawai ina bibiyar labaran Facebook dina, ba sai na ga wani talla daga kamfanin Wayfair mai sayar da kayan amfanin gida ana nuna mini wata rumfa ta ajiye kwandunan zuba shara, abin nan ya yi matukar ba ni mamaki.

“Kafin mu yi waccan hira, ban taba sanin da irin wannan rumfa ba a duniya.”

Cikin minti biyar sai ga talla biyu na katifa

“Muna ta muhawara kan wannan abu ni da wasu abokaina a gidan barasa… don gano gaskiya kuma a raba musu, sai muka shiga tattauna batun sabuwar katifa,” in ji Justin, a Atlanta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mun shiga hirar katifa don gano gaskiyar wannan batu

“Tun da yake ban taba saya ko neman saya, kai ko na yi tunani a kan gado, na shafe shekaru da dama, don haka ba ma zan iya tuna wani lokaci da na ga tallar katifa da na taba gani a intanet ba.

Muka fara hira a kan gadaje da katifu muna ambaton kalmomi, irinsu birgima a kan wani gado da ake kira ‘California king’ da ‘sayen katifa ta intanet’ a hirar, a lokacin da muke bibiyar shafukanmu na facebook.

“A cikin minti biyar sai ga talla biyu na katifu. Ba mu taba ganinsu ba kafin hirar.”

Talla cikin harshen Sifaniyanci ya bayyana

“Ina aiki a masana’antar wayoyin salula kuma na lura da yadda hakan ke faruwa sau da dama a cikin ‘yan shekarun nan,” Michael, daga Grimsby ya rubuta.

“Don in tabbatar, sai na fara koyon harshen Sifaniyanci, kuma cikin kwana daya sai ga tallace-tallacen kayayyaki cikin harshen Sifaniyanci! Wallahi hankali ba zai dauka ba.”

An yi mini talla kan kyamarorin tsaron gida

“Na kai wa wata kawata da ke kafa kyamarorin tsaro ziyara a gidanta,” Melissa, daga Australia, ta rubuta.

“Ban taba amfani da intanet don neman wani abu mai alaka da tsaron gida daga nesa ba, amma kasa da sa’a daya bayan hirarmu kan yadda ake kafa kyamarorin, sai na samu tallar kyamarorin tsaron gida a Facebook.

“Duk tsawon lokacin hirarmu wayata tana cikin aljihuna.”

Na samu tallace-tallace kan aikin ido duk da yake idanuna garau

“Wata rana, wani abokina ya fada min bukatar da yake da ita ta a yi masa tiyata a ido,” in ji Austin, daga Tigard, a Oregon.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Daga zancen aikin ido sai ga tallar ta bayyana a Facebook

“Kawai bayan nan, Ina bincika Facebook dina sai na ga tallar irin wannan tiyata da ake kira Lasik.

“Ni idona garau yake, ban taba neman bayani a kan tiyatar Lasik ba.”

Sai na ga bindigar kashe kuda da ban taba gani ba

“Na ga wani abu a makaranta da ake kira bindigar gishiri, wadda ake amfani da ita wajen kashe kudaje,” a cewar Peter, “ban taba ganinta ba sai lokaci, kuma ban taba bincika irin wadannan abubuwa ba.

“Muna hira da matata sai zancen bindigar ya fado, nake bayyana mata wadda na gani.

“Washe gari da safe, ina bude Facebook dina sai ga talla daga kamfanin Amazon na irin wannan bindiga a cikin jerin ‘abubuwan da mai yiwuwa kake da sha’awa’.”

Ta faru da ni ba sau daya ba

“Hakan ya faru da ni, karo da dama ina ganin tallace-tallace masu alaka da wata hira da na yi ko na gama yi kenana,” Faris, daga Alkahira ya ce.

“Mun yi hira a kan abokin dan’uwana da ya mutu, kuma ba da dadewa ba sai daya daga cikinmu ya ga tallace-tallace a kan masu shirya gawa.

Zafi na haifar da karancin abinci mai gina jiki


Image caption

Yanayin zafi kan gigita bil adama

Wani sabon rahoto kan sauyin yanayi ya ce karuwar zafi na matukar cutar da lafiyar dan’adam.

Rahoton wanda rukunin wasu jami’o’i da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka fitar, ya ce karuwar zafi na illa ga karin mutane kuma yana haifar da karancin abinci mai gina jiki da yaduwar cuta.

Masu binciken wanda aka buga a mujallar Lancet, sun ce karancin abinci mai gina jiki sakamakon gazawar amfanin gona na da babban tasiri ga lafiya a wannan karni.

Sun kuma nunar da karuwar kusan kashi 10 cikin 100 ta bazuwar zazzabin Denge wanda sauro ke yadawa tun cikin 1950.

Korar su Babachir ba ta isa ba – Rafsanjani


Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Wannan ne karon farko da shugaban ya kori wani babban jami’i da ke gwamnatinsa

A ranar Litinin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami Sakataren Gwamnatin kasar Babachir Lawal, inda ya maye gurbinsa da Boss Mustapha.

Hakazalika shugaban ya kori shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasar (NIA) Ambassador Ayo Oke.

Wannan ne karon farko da shugaban ya sallami wani babban jami’i a gwamnatinsa kan zargin almundahana.

Sai dai jim kadan bayan sanarwar dakatarwar ne jama’a a kasar suka rika bayyana ra’ayoyinsu musamman a kafofin sada zumunta

Ade Banqie wani dan kasar ne wanda ya ce sun “zuba idanu su ga ko shugaban zai mika Babachir Lawal ga hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar tu’annati (EFCC).”

“Muna neman karin haske. Don kora ba ta wadatar ba,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/ Banky

‘Dole a hukunta su Babachir’

Akwai manyan jami’an tsohuwar gwamnatin kasar da har yanzu hukumar EFCC take rike da su kamar Olisa Metuh da Kanar Sambo Dasuki da Diezani Alison-Madueke da sauransu, bisa zargin almundahana.

Auwal Musa Rafsanjani, wakili a kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transperancy International ya shaida wa BBC cewa:

“Korar da akai musu ba za ta gamsar da mu ba, lalle duk wanda aka kama da laifi ya kamata ne a hukunta shi. Don ya zama darasi”

Ya kara da cewa: “Idan kawai aka tsaya a kora, to sauran mutane za su rika korafi suna cewa to damme ga wadansu mutane ana musu shari’a, amma wadannan fa?”

“Dole ne idan ana so a yi yaki da cin hanci da gaske sai an hukunta wadannan mutane,” in ji shi.

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ce ba zai iya cewa “eh ko kuma a’a ba” game da batun gurfanar da mutanen da ake zargi da almundahanar.

“Ai hukunci doka ba magana ce ta shugaban kasa ba. Idan sai an jira sai shugaban kasa ya ce a kama wancan, ko a saki wancan to ai ba za a bi doka ba ke nan,” in ji shi.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Buhari ba ya yin rufa-rufa – Garba Shehu

Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron cikakkiyar ganawar da BBC ta yi da shi ta manhajar Skype.

Sai dai Malam Kabiru Lawanti wanda ke koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya ce batun ba haka yake ba.

Ya ce abin da kakakin shugaban kasar ke ikirari zai yiwu ne kawai idan a ce hukumomin gwamnati suna aikinsu yadda ya dace.

Lawanti ya ce “Garba Shehu ya yi kokarin kare bangaren shugaban kasa ne kawai. Idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a kwanakin baya.”

“Yawancin mutanen da ake zargi da babakere a kan dukiyar al’umma hukumar EFCC tana musu dirar mikiya ne a gidajensu. Su kamu su, san nan su fara bincike.”

“Abu biyu ‘yan Najeriya suke son ganin a wannan lokaci,” kamar yadda ya ce.

“Na farko ya kamata hukumar EFCC ko ICPC ta kama su. Kuma ta kwace kadarorinsu, daga nan sai a ci gaba da bincike kan al’amarin.”

Ya ce abu na biyu “idan duka wadannan ba su samu ba, to dole ne hukuma ta gurfanar da su a gaban kotu tun da akwai sakamakon binciken da aka yi a kansu. Idan an same su da laifi sai a hukunta su.”

“Wannan shi ne abin da duk wani dan Najeriya mai son ci gabanta zai so a yi, amma ba maganganun siyasa ba,” in ji Lawanti.

Nigeria: Ana baje koli kan illolin bauta ta zamani


Image caption

Yawanci matasa sun fi tafiya turai domin neman aiki

Ana gudanar da bikin nune-nunen tarihi kan bauta irin ta zamani a gidan adana kayan tarihi na bauta da ke birnin Kalabar babban birnin jihar Kuros Riba a Najeriya.

Duk da yake dai an kwashe shekaru da dama da dakatar da cinikin bayi, a zamanin yau, an bullo da wasu hanyoyi na bautar da mutane, inda ake zargin ana yaudarar matasa daga yankin Afirka ta yamma ana kai su kasashen Turai da sauransu.

Darakatan hukumar gidajen adana kayan tarihi ta Najeriya, Alhaji Yusuf Abdallah Usman, ya shaida wa BBC cewa, duk da an soke bauta a kusan kowacce kasa ta duniya, yanzu akwai wani salo na bauta da ke faruwa a kusan kasashen daban-daban na duniya.

Don haka ne aka shirya wannan biki domin a fito da ire-iren abubuwan da suka shafi nau’in bauta ta zamani da kuma yadda za a yi maganinsa ta yadda zai zama darasi ga matasa da ma sauran mutane.

Alhaji Yusuf Abdallah Usman, ya ce yanayin bauta ta zamani ya sha bam-bam da na da, saboda ada ta karfin tsiya ake daukar bayi a kai wasu kasashe don bautar da su, to amma a yanzu mutane ake yaudara don su tafi turai da zimmar suje suyi aiki daga nan sai buge da zama bayi.

Saboda idan suka je can din, a kan kwace musu takardunsu na tafiya kamar fasfo, ta yadda ba damar su koma kasashensu.

Darakatan ya ce, irin wadannan mutanen ana bautar da su gami da azabtar da su, inda a wani lokacin ma, a kan sa mata suyi karuwanci.

Alhaji Yusuf Abdallah Usman, ya ce to duk irin wadannan abubuwan ne za a nusar da mutane musamman masu son tafiya turai domin suyi aiki, ta yadda za su guji fadawa tarkon irin mutanen da ake azabtarwa.

Lukaku shafaffe da mai ne — Mourinho


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lukaku ya ci wa Manchester United kwallo 11 a wasa 10 da ya buga, amma ya yi wasa biyar bai ci kwallo ba a yanzu

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce ya kamata Romelu Lukaku ya zama shafaffe da mai a wajen magoya bayan kungiyar ba wai sukarsa ba.

Lukaku wanda ya koma United a bana kan kudi fam miliyan 75 daga Everton ya ci mata kwallo 11 a wasa 10 da ya yi, amma yanzu ya buga wasa biyar bai ci kwallo ba.

Mourinho ya ce dan wasan yana yi wa kungiyar kokari, kuma ba wai kawai cin kwallo ne aikinsa ba.

Kocin ya kara da cewar Lukaku shafaffe da mai ne a wajensa ya kamata ya zama hakan a wajen magoya baya, ya kuma kamata su dunga martaba shi.

United za ta karbi bakuncin Benfica a ranar Talata a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Za a fadada rijiyar Zam-zam a masallacin Makkah


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An yi amannar cewa rijiyar Zamzam da ke kusa da Ka’aba ita ce rijiyar data fi kowace dadewa a duniya

Kasar Saudiyya na yin wani gagarumin aikin gyara rijiyar Zamzam a babban Masallacin Haram da ke birnin Makkah.

Babban mai kula da Masallatan Makkah da Madinah, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais wanda ya sanar da fara aikin, ya ce za a fadada girman rijiyar tare da tsabtace kewayanta.

Miliyoyin mahajjata ne ke amfani da ruwan Zamzam a Masallacin Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad SAW da ke Madina.

Musulmi na dibar ruwan a ko wanne lokaci zuwa kasashensu.

Musulmai sun yi amannar cewa rijiyar samuwarta daga Allah ne, wacce ta samar da ruwa don kashe kishirwa lokacin da Annabi Ibrahim AS ya bar matarsa da dansa a cikin Sahara.

Sarki Salman ne ya amince da aikin gyara rijiyar da za a kwashe watanni bakwai ana yi.

Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya ce ana sa ran kammala gyaran kafin watan Ramadan mai zuwa.

An dai yi amannar cewa rijiyar Zamzam da ke kusa da Ka’aba, ita ce rijiyar da ta fi ko wacce dadewa a duniya.

Uhuru Kenyatta ya lashe zaben Kenya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Uhuru Kenyatta ya lashe zaben ne bayan an ki yin zabe a yankunan da ‘yan adawa suke da rinjaye a kasar

An ayyana Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar mai cike da ce-ce-ku-ce.

Ya lashe kashi 98 cikin 100 na kuri’un da aka kada yayin da masu kada kuri’u kasa da kashi 39 cikin 100 suka fito- kasa da rabin wadanda suka kada kuri’a a zaben watan Agusta, in ji hukumar zaben kasar.

Jagoran ‘yan adawa, Raila Odinga, ya janye daga zaben da aka sake yi kuma ya bukaci mabiyansa su kaurace wa zaben.

Ko a zaben da aka yi watan Agusta ma, an ayyana Mista Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben wanda aka soke bisa dalilai na magudi.

Kuma an dakatar da zaben a mazabu 25 domin fargabar rashin tsaro.

Hukumar ta ce sakamakon wadannan mazabun ba zai shafi sakamakon zaben ba, don haka ne ta bayyana sakamakon zaben.

Shugaban hukumar zaben, Wafula Chebukati, ya bayyana zaben na baya-bayan nan a matsayin sahihin zabe.

Bangaren adawa na Kenya dai yana da kwanaki bakwai don kalubalantar zaben, kuma Mista Odinga ya ce zai yi wata sanarwa a ranar Talata.

Boss Mustapha: Wane ne sabon sakataren gwamnatin Nigeria?


Hakkin mallakar hoto
NIWA Website

Image caption

Kwarewarsa a harkar shari’a ta hada da sayar da hannayen jarin kamfanonin gwamnati

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabon sakataren gwamnatin kasar, bayan da ya kori Mista Babachir Lawal bisa zargin cin hanci da rashawa.

Wane ne Boss Gida Mustapha?

Mr Boss Gida Mustapha lauya ne, dan siyasa kuma dan kasuwa. Kafin a ba shi wannan mukami na sakataren gwamnatin Najeriya, shi ne shugaban Hukumar Kula da Rafuffukan Najeriya, (NIWA).

Mista Mustapha ya kware sosai a fannin aikin gwamnati da na kamfanoni.

Haifaffen jihar Adamawa ne kuma ya yi karatunsa na sakandare a garin Hong, ya yi kwalejin kimiyya ta Maiduguri, ya yi karatun digirinsa a fannin shari’a a jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya kuma tafi makarantar koyon aikin shari’a a shekarar 1980 zuwa 1981.

Bayan kammala bautar kasarsa a hedikwatar rundunar sojin Najeriya, sai ya fara aiki da wani kamfanin kasar Italiya da ke Najeriya, Sotesa Nigeria Limited.

A shekarar 1983 kuma ya koma aiki da kamfanin lauyoyi na Onagoruwa & Co da ke Lagos.

Daga bisani kuma ya bude kamfaninsa na kashin kansa na aikin lauya mai suna Messrs Mustapha & Associates.

Kwarewarsa a harkar shari’a ta hada da sayar da hannayen jarin kamfanonin gwamnati.

Mista Mustapha ya taba zaman mamba na wani kwamitin gudanarwa na wucin-gadi a hukumar Tara Rarar Kudaden Man Fetur ta Najeriya, PTF, daga shekarar 2000 zuwa ta 2007.

Haka kuma ya taka rawa a shugabancin kungiyar lauyoyin Najeriya NBA, a matsayin shugaban kungiyar reshen jihar Yola.

Bayan ya bar PTF ne ya zama daya daga cikin manyan masu hannun jari na kamfanin Adroit Lex, ya kuma zama mamba na majalisar dokoki karkashin mulkin soja daga shekarar 1988-1989.

Ya shugabanci jam’iyyar PSP ta jihar Gongola a wancan lokaci a shekarar 1989-1990, da shugabancin jam’iyyar SDP daga shekarar 1990-1991.

Ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a shekarar 1991. Ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar ACN ta kasa daga shekarar 2010 zuwa ta 2013.

A shekarar 2007 kuma ya zama mataimakin shugaban kungiyar yakin neman zabe ta dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ACN.

Shi ne kuma sakataren kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a shekarar 2015, kuma mamba ne na kwamitin amintattu na APC.

Bayanai: Daga Hukumar Kula da Rafuffukan Najeriya, NIWA

Matar Danjuma Goje, Hajiya Yalwa ta rasu


Hakkin mallakar hoto
Goje Twitter

Allah ya yi wa matar tsohon gwamnan Gombe, Hajiya Yalwa Danjuma Goje rasuwa bayan fama da rashin lafiya da ta yi.

Hajiya Yalwa ta rasu ne a ranar Litinin da safe a kasar Amurka bayan ta sha fama da doguwar jinya da ba a bayyana ba.

Wata majiya mai karfi daga makunsantan marigayiyar ta tabbatar wa BBC cewa marigayiyar ta fara jinya ne a Indiya kafin daga bisani a mayar da ita Amurka inda ta rasu.

Hajiya Yalwa ta mutu ne tana da shekara 55, ta kuma bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

Hajiya Yalwa dai ita ce uwargidan tsohon gwamnan Gomben wanda a yanzu sanata ne a majalisar dattawa ta Najeriya.

Man United za ta karbi bakuncin Benfica


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester United tana da maki tara a wasa uku da ta buga a gasar cin kofin Zakarun Turai a wasan rukunin farko

Manchester United za ta kara da Benfica a gasar cin Kofin Zakarun Turai wasan cikin rukunin farko da za su kece raini a ranar Talata a Old Trafford.

A makon jiya ne United ta ci Benfica daya mai ban haushi a Portugal kuma Marcus Rashford ne ya ci kwallo bayan da aka koma zagaye na biyu a karawar.

Kuma Manchester United da Benfica sun kara a gasar cin kofin Zakarun Turai sau 10, inda United ta ci wasa bakwai, suka yi canjaras biyu, Benfica ta ci wasa daya.

Daya wasan rukunin farkon za a yi ne tsakanin FC Basel da CSKA Moscow a Switzerland.

United ce ke mataki na daya a rukunin farko da maki tara sai Basel mai maki shida, yayin da CSKA Moscow keda maki uku, ita kuwa Benfica ba ta da maki ko daya.

Barcelona ta gagara a gasar La Liga ta bana


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona tana ta daya a kan teburi da maki 28, bayan da ta yi wasa 10

Kungiyar Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Ligar Spaniya, bayan da ta kammala wasannin mako na 10 a karshen sati.

Barcelona ta ci wasa tara ta yi canjaras a karawa da ta tashi kunnen doki 1-1 a gidan Atletico Madrid a ranar 14 ga watan Oktoba.

Hakan ya sa kungiyar ta hada maki 28 kuma kwallo 28 ta ci inda Lionel Messi ya ci 12 daga ciki, sannan aka zura mata uku a ragarta tun fara kakar La Ligar shekarar nan.

Barcelona za ta buga wasan mako na 11 a ranar 4 ga watan Nuwamba, inda za ta karbi bakuncin Sevilla a Nou Camp.

Sai dai kafin nan kungiyar za ta buga gasar cin kofin Zakarun Turai da inda za ta ziyarci Olympiacos a wasan cikin rukuni, kuma Barcelona ce ke kan gaba a rukuni na hudun da maki tara.

Wadanne tambayoyi ku ke da su kan Daniel Amokachi?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Me kuke son sani game da Daniel Amokachi ne?

Daniel Amokachi daya ne daga cikin tsaffin fitattaun ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya.

Me kuke son sani game da shi? Ku tambayi duk abin da ku ke son sani dangane da rayuwar wannan gwarzo, BBC za ta samar muku da amsoshi ga tambayoyin da ku ka yi ta kuma wallafa muku su nan ba da jimawa ba.

An yi walkiya sau 176,000 a dare daya a Australia


Hakkin mallakar hoto
Alex Gregg

Gagarumin hadari ya jawo ruwan sama mai yawa da kuma walkiya mai ban mamaki ba kakkautawa a birnin Queensland da ke kasar Australiya.

A lokacin da hadarin ya hadu an shafe sa’o’i da dama ana ta walkiya mai karfi ba kakkautawa a sararin samaniya, inda aka shafe tsawon dare ana yin walkiyar har sai da aka yi ta sau sama da 176,000.

Kuma ana sa ran za a sake wasu jerin walkiyar a ranar Litanin.

Ofishin hukumar kula da yanayi a birnin Queensland, ya yi gargadin cewa da akwai hadari mai dauke da tsawa mai tsanani da iska mai karfi da zai yi barna har da ruwa da kankara.

Ruwa mai tafe da iska da walkiyar ya barnata gidaje tare da barin daruruwan muhallai babu wutar lantarki.

Da akwai hotunan iskar hadarin mai karfi ta yadda ta mamaye samaniya, wadanda aka dauka da suka nuna yadda walkiyar ta wakana.

Hakkin mallakar hoto
Steph Doyle

”Sararin samaniya ya murtuke na tsawo sa’o’i ba kamar yadda aka saba gani ba a lokacin haduwar hadari,” in ji mai daukar hoto a Brisbane, Steph Doyle, kamar yadda ya shaida wa BBC.

“Hadarin na taruwa ya narke abun da ke jawo walkiya ba kakkautawa baki daya a sararin samaniya,” a cewarsa.

Hakkin mallakar hoto
Alex Gregg

Hakkin mallakar hoto
Alex Gregg

Hukumar kula da samar da wutar lantarki a birnin wato Energexx, ta sanar da cewa sama da gidaje 4,000 ne suka kasance ba su da wutar lantarki sanadiyyar wannan gagarumin hadari.

Hakkin mallakar hoto
Mark Jessop

A garin Brisbane an shafe tsawon sa’a uku ana yin walkiya a ranar Lahadi, inda hadarin ya sake haduwa sosai da sassafe.

Hukumomi sun yi gargadin cewa ga dukan alamu hadarin zai ci gaba da haduwa ganga-ganga a kudu masu gabashin Queensland tare da yin barna mai yawa.

An killace mutum 60 a Kano saboda kyandar biri


Hakkin mallakar hoto
EPA

Hukumomin lafiya a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun ce an killace mutum 60 bayan da suka yi mu’amala da wani mara lafiya da ake zargin ya kamu da cutar kyandar biri.

A karshen makon nan ne kwamishinan lafiya na jihar, Dr Kabir Getso, ya ce: “an gano alamun cutar ne a tare da mara lafiyar, sai dai muna zargin cewa tasa cutar ta fi kama da farankama maimakon kyandar biri.”

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya yi watsi da zargin da ake masa cewa bai dauki halin da mara lafiyar ke ciki da muhimmanci ba.

Ya ce ba za mu tabbatar da cewa yana dauke da cutar ba har sai an dawo da sakamakon jini da aka kai babban birnin tarayyar kasar Abuja.

Dr Getso ya ce an samu bullar cutar kyadar biri a jihohi 11 daga cikin 36 na kasar, kuma mutum 94 ne ake zargin sun kamu da ita, sai dai shida daga cikinsu ne kawai aka tabbatar sun kamu.

A farkon wannan watan ne wani jami’in lafiya a jihar Bayelsa da ke kudancin kasar ya ce ana samun cutar ne daga jikin birrai da sauran dabbobin daji kamar bera da kurege da barewa.

Hukumomin lafiya a Najeriya sun yi ta gargadin jama’a da su guji cin naman biri da sauran naman daji.

Ministan lafiyar kasar Isaac Adewole, a wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, ya ce duk da cewa ba a san maganin cutar ba, to babu wani abun daga hankali don ba mai yin muguwar illa ba ce.

Sai dai ya shawarci al’umma da su dauki matakan kariya kamar gujewa shiga cunkoson jama’a.

Ya ce cutar na cikin rukunin cututtuka da suka hada da farankama da agana da ciwon ‘yan rani.

Sanata Wamakko ya tsallake rijiya da baya bayan ruftawar gidansa


Hakkin mallakar hoto
SA Media Wamakko

Image caption

Al’amarin ya faru ne ranar Lahadi da daddare

Wani dan Majalisar dattawan Najeriya daga jihar Sakkwato a arewa maso yammacin kasar ya tsallake rijiya da baya ranar Lahadi da daddare, bayan wani sashe na gidansa ya rufta.

Mai magana da yawun Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Bashir Mani, ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni.

Ya ce lamarin ya faru ne jim kadan da ficewar Sanata Wamakko daga gidan wanda ke a unguwar masu-hannu-da-shuni ta Gawon-nama; bayan kammala wata ganawa da ‘yan siyasa da ya yi a gidan.

Sai dai wata majiya daga iyalan Sanata Wamakkon ta ce yana cikin gidan lokacin da abun ya faru, sai dai ba a sashen da yake ba ne ruftawar ginin ta afku.

“Hakan ne ya sa ba a fi minti goma ba sai ga Gwamna Aminu Tambuwal ya iso gidan da sauri saboda yadda labari ya bazu cewa ginin ya rufta da shi a ciki,” in ji wani makusancin tsohon gwamnan na jihar Sakkwato.

Alhaji Bashir Mani ya ce babu kowa a sashen ginin da ya rufta din lokacin da lamarin ya faru domin ana gyaran sashen ne.

Hakkin mallakar hoto
SA Media Wamakko

Hakkin mallakar hoto
SA Media Wamakko

‘Yadda na sauya rayuwar abokina na kuruciya da ke shaye-shaye’


Hakkin mallakar hoto
Wanja Mwaura

Wata mata ta taimakawa wani tsohon abokinta, inda yanzu ya daina shan miyagun kwayoyi bayan ya kwashe shekara yana gararanba a kan titi.

Al’amarin ya faru ne a farkon watan Oktoba. Wanja Mwaura mai shekara 32 tana kan hanyarta ta zuwa kasuwa a unguwar Lower Kabaete, wadda ba ta da nisa daga birnin Nairobi.

Sai ta ji wani ya kwala mata kira. Da ta waiyawa sai ta ga wani dogon mutum mai kwala-kwalan idanuwa sanye da bakaken tufafu da hula, yana zaune jefan hanya. Sai dai ita ba ta gane shi ba.

Amma da Patrick wanda ake kira Hinga ya gabatar da kansa, sai Wanja ta kidime.

Mutumin da ke gabanta wani tsohon abokinta ne lokacin da take da shekara bakwai a duniya.

“Patrick ko Hinga kamar yadda muke kiran shi, na hadu da shi ne lokacin da nake makarantar firamare a shekarar 1992,” in ji Wanja wanda ma’aikaciyar jinya ce daga yankin Kiambu, wanda yake wajen babban birnin Kenya.

“Hinga ya kasance gwani wajen kwallon kafa yayin da muke makaranta. Mun rada masa suna ‘Pele’.”

Hakkin mallakar hoto
Wanja Mwaura

Hinga ba ya tare da iyayensa, sai dai yana zaune ne wurin kakarsa a wani dan karamin daki.

Ya daina zuwa makaranta ne saboda yadda ya gaza biyan kudin makaranta.

A karshe kuma ma an tashe su daga dakin da suke zaune.

Amma duk da haka Hinga ya ci jarabawarsa, har sai bayan da kakarsa ta rasu – daga nan ne sai ya daina zuwa makaranta kuma sai rayuwarsa ta fara tabarbarewa.

Hinga ya fara shan miyagun kwayoyi, kodayake da farko ya fara ne da shan wiwi.

Yakan kwashe lokaci mai tsawo yana tone shara don neman abin da tsinta ya sayar.

Hinga da Wanja ba su kara jin duriyar junansu ba.

Hakkin mallakar hoto
Wanja Mwaura

Sai bayan fiye da shekara 15 ne suka sake haduwa, Hinga yana kwana ne a kan titi fiye shekara 10.

Babu wata alama da za ka ganni a jikinsa wadda za ta nuna cewa yaron nan ne da ake kira Pele.

Ganin yadda Wanja ta fusata, sai Hinga ya ce ya yi mata magana ne kawai don ya gaishe ta.

Ta tambaye shi ko ta saya masa abinci.

Daga nan ne sai ta sayo masa nau’in abincin da ya fi kaunar ci lokacin da yake yaro – wato kashin awazan alade da damamman dankali.

Ta ce daga nan ne sai ya rude, ya kasa magana.

“Na ba shi lambar wayata kuma na shaida masa cewa ya kira ni idan yana bukatar wani abu,” in ji Wanja.

Bayan wasu kwanaki, Hinga ya karbi aron waya wanda da ita yake kiran Wanja lokaci zuwa lokaci, musamman ma don ya ji muryarta.

Ya shaida mata cewa a shirye yake ya daina tu’ammali da miyagun kwayoyi.

“Akwai wani abu da ya kamata a yi don taimakon shi,” in ji Wanja.

Hakkin mallakar hoto
Wanja Mwaura

Ta hanyar amfani da shafinta na sada zumunta, Wanja ta bukaci abokanta da su taimaka da kudin da za a taimaka wajen dawo da Hanga cikin al’umma.

“Kai mutum cibiyoyin kintsa masu shaye-shaye tana da tsada sosai kuma ba ni da kudin da zan iya biya ni kaina,” in ji ta.

“Mun kafa wani shafi, amma daga farko mun iya samun shilling din Kenya 41,000 (fam 300) ne kawai.”

Kodayake ana biyan shillings 100,000 ne a tsawon kwana tara idan aka kai mutum cibiyar Chiromo Lane Medical Center da ke Nairobi.

“Ba mu san inda za mu samo cikin kudin ba.”

Amma kuma Wanja ta dauki alkawarin taimaka wa Hinga, don haka sai muka kai shi cibiyar ba tare da sanin abin da zai faru a karshe ba.

Hakkin mallakar hoto
Wanja Mwaura

Wani mai magana da yawun cibiyar ya ce Hinga wani mutum ne da ya dukufa kan tarbiyyar da aka dora shi a kai a tsawon kwana taran da ya yi a wurinsu.

Cikin ‘yan kwanaki Hinga ya fara murmurewa, ya fara jiki kuma natsuwarsa ta dawo.

Daga nan ne sai Wanja ta ce shafin Facebook don ta ba da labarin yadda Hinga ya murmure cikin dan kankanin lokaci.

“A mako guda da ya wuce idan ina magana da Hinga sai na rika sa hannu ina tallabar kansa saboda na tattara hankalinsa wuri guda. A yau za mu iya yin magana yana kallona ina kallonsa,” kamar yadda Wanja ta wallafa a shafin Facebook.

Wani dan kasuwa daga birnin Mombasa, Fauz Khalid, ya ga wannan sako a Facebook inda ya ce zai yada sakon don sauran jama’a su gani.

Ya wallafa hotunan a shafinsa na Twitter kuma a yanzu fiye da mutum 50,000 sun yada hotunan ga duniya.

Bayan haka ne kafafen yada labaran Kenya suka fara yada labarin kuma daga nan cibiyar Chiromo Lane Medical Center ta ce ta yafe kudin maganin da ta yi wa Hinga.

Wanja ta ce wannan “abin alheri ne”, amma ta ce ta damu sosai ga Hanga don ganin ya murmure gaba daya kuma yanzu ta fara neman masa taimakon kudi, inda zai yi kwana 90 a cibiyar Retreat Rehabilitation, wurin da yake a halin yanzu.

Akwai ‘yan Kenya tsakanin 20,000 zuwa 50,000 wanda suke shan tabar ibilis ta Heroin, amma kuma kasar ba ta da cibiyar kintsa masu shan miyagun kwayoyi ko guda.

Hakkin mallakar hoto
Wanja Mwaura

“Sai dai har yanzu ana kyamar masu shan miyagun kwayoyi a Kenya,” in ji Wanja.

Kuma wannan yana iya zama daya daga cikin dalilan da suka sa gwamnati ta ki samar da magunguna kyauta a cibiyoyin kintsa masu shan miyagun kwayoyi.

“Cibiyoyin suna da tsada kuma yawancin mutane ba za su iya kai kansu can ba, ba kawai a Kenya ba amma har sauran sassan nahiyar Afirka. Na dukufa wajen ganin al’umma ta taimake ni don na taimaki abokina,” in ji Wanja.

“Wanja wata mutuniyar kirki ce wadda Allah Ya aiko ta. Ba zan iya biyanta ba, ko da zan sadaukar da raina ne. Ta min taimakon da ya fi wanda ‘yan uwana za su yi min,” kamar yadda Hinga ya shaida wa BBC.

Haka aka rika yayata wannan kalaman da Hanga ya yi a shafukan sada zumunta.

Wani masani kan harkokin hada-hadar kudi, Abraham Wilbourne, wanda yake zaune a Nairobi ya ce “Wanja tana da gida a aljannah!”

Yawancin mutane suna kiranta da sunan “mashujaa,” wato ana nufin gwarzuwa a harshen Swahili.

“Mutane suna cewa na sauya rayuwar Hinga, amma shi ma ya sauya tawa rayuwar.” in ji Wanja.

“Yanzu na gane cewa karamar tattaunawa za ta iya sauya rayuwar wani.”

‘Har Cuba na je neman magani ban dace ba’


Image caption

Wasu lokuta masu fama da cutar mele kan fuskanci tsangwama

Wata mai fama da cutar mele a Najeriya ta bayyana damuwa saboda rashin maganin cutar, wadda ta ce ta kai ta har zuwa kasar Cuba amma ba ta dace ba.

Matar wadda ba a bayyana sunanta ba, ta ce tun cikin shekarar 1995 ta fara amfani da wani magani Melaganina da likitoci suka ba ta, da ya yi aiki.

A cewarta ya kamata ta sake komawa ganin likita bayan shekara guda amma ba ta samu zarafin yin haka ba, sai bayan shekara biyar ta koma.

“Sun kara ba ni wani magani sai abin kamar ma yana karuwa” maimakon raguwa, don haka “sai na zo na daina magani ma, don gaji.”

Hakkin mallakar hoto
CBS

Image caption

Cutar mele dai kusan takan fito a kowanne sashe na fatar jiki

Cutar mele dai tana dade wa mutum wani sashen jiki, inda wajen zai yi dau kamar kuna.

A cewar shafin intanet na Gidauniyar kula da cutukan fata ta Burtaniya (British Skin Foundation) mele cuta ce ruwan dare da ke shafar kimanin kashi 1 cikin 100 na al’ummar duniya.

“… masu fama da cutar mele sun fi sauran mutane yiwuwar kamuwa da wasu cutukan, da ake samu ta irin wannan hanya, da kuma sauran sassan jiki irinsu makwallato.”

Mai fama da wannan cutar ta fada wa BBC cewa melen ba ya yi mata ciwo, amma dai takan fuskanci tsangwama musammam lokacin tana yarinya.

Ta ce ko da yake akan haifi wasu, da wannan cuta amma ita ta kamu da ita ne sakamakon wata allura da ta gama aiki.

“Ina ‘yar shekara shida (lokacin) aka ban allurar a hannu kuma daga nan sai cutar ta fara bayyana,” in ji ta.

Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

Mai sana’ar tallata tufafi Winnie Harlow ‘yar kasar Kanada na daga cikin fitattun mutanen da ke fama da wannan cuta a duniya

Gidauniyar tallafa wa masu cutukan fata ta Burtaniya ta ce cutar mele wani lokaci tana warkewa da kanta, kuma akan samu wasu magunguna da ke rage karuwarta a jiki.

“Ko da yake, babu wani tabbaci na samun maganin da ke warkar da ita.”

Matan Saudia za su fara shiga filayen kallon kwallo


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matan Saudia sun samu ‘yancin shiga filayen wasanni don kallon wasan kwallon kafa da sauransu

A karon farko kasar Saudia za ta fara barin mata zuwa filayen wasa domin kallon wasannin da ake yi.

Wannan dai wani karin yunkuri ne na ba wa mata ‘yanci a kasar.

Kamfannin dillancin labaran kasar ne ya sanar da cewa daga yanzu za a rinka barin iyalan mutum da suka hada da mata da yara su rinka halartar filayen wasanni da ke manyan biranen kasar uku, wato na Riyadh da Jedda da kuma Dammam.

Wannan sabon mataki dai zai fara aiki ne daga farkon shekara mai zuwa.

Hakan dai wata ‘yar dama ce a masauratar da ake killace mata a gidaje, domin a kara fito da su don shiga a dama da su a cikin al’umma.

Kazalika wannan mataki, wani bangare ne na yunkurin da matashin yarima mai jiran gado, Mohammad bin Salman, ke da shi na kara habaka tattalin arziki kasar ta hanyar samar da damammaki da kuma harkokin nishadantarwa ga daukacin ‘yan kasar.

Kasar Saudia dai ita kadai ce a duniya da ta hana mata tuka mota a baya.

Tun bayan sanarwar damar tuka mota ga matan kasar,hankula suka kwanta musamman a fannin masu wannan fafutuka ta neman bayar da izinin tuka mota ga mata, to sai dai kuma wasu na ganin wannan dama wata hanyace ta bude kofar neman wasu ‘yancin na mata da sauransu.

Kungiyoyin kare ‘yancin dan Adam, sun shafe shekaru suna kiraye-kirayen ba mata damar tuki da kansu a kasar.

Kuma hukumomi sun sha tsare matan da suka karya dokar haramcin tukin mota.

Nigeria ce kan gaba a yaran da ba a yi wa riga-kafin kyanda ba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yara na mutuwa saboda kamuwa da cutar kyanda

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ta ce Najeriya ce kan gaba a yawan yaran da ba a yi wa riga-kafin kyanda ba a duniya.

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin wani rahoto da ta fitar da ke nuna an samu raguwar mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar wadda ba a taba ganin irinta ba.

Rahoton ya ce, a bara mutum dubu 90 ne suka mutu sakamakon cutar ta kyanda a duniya, wanda hakan ya nuna cewa, an samu raguwarta da kaso 84 cikin 100, idan aka kwatanta da mutum 550 da cutar ta hallaka a shekarar ta 2000.

WHO ta ce, har yanzu ba a yi ko kusa da cimma muradin kawar da cutar ba a duniya.

Hukumar ta ce, hakan ba ya rasa nasaba da rashin yi wa yaran allurar riga-kafin cutar ta kyanda, domin a yanzu haka akwai yara miliyan 20 da dubu 800 da ba a yi wa riga-kafin cutar ta farko bayan haihuwa ba a duniya.

Kuma fiye da adadin wadannan yaran na zaune ne a kasashe shida kawai, da suka hada Najeriya wadda ita tafi yawan yaran da ba yi wa riga-kafin ba.

Sai India da Pakistan da Indonesia da Habasha da kuma Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Rahoton hukumar ya yi gargadin cewa tunda cutar mai yaduwa ce, za a iya ci gaba da samun barkewarta a sassan daban-daban na wadannan kasashen har ma ta bazu zuwa wasu kasashe.

Hukumar ta ce, bazuwar cutar ta kyanda, za ta iya jefa yara cikin hadarin kamuwa da cutukan da suka hada da amai da gudawa da limoniya da kuma makanta.

Cutar kyanda na daga cikin manyan cutuka biyar da ke kan gaba wajen kisan yara a kasashe masu tasowa.

An kai harin kunar bakin wake Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mako guda ke nan da kai wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 14

Wata ‘yar kunar bakin wake ta kai hari a kusa da ofishin hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka ce.

Sai dai a cewar shugaban hukumar Injiniya Satomi Ahmad, ‘yar kunar bakin waken ce kawai ta rasa ranta a lamarin wanda ya faru da yammacin Asabar.

Mutum 14 ne suka mutu a makon jiya baya ga ‘yan kunar-bakin-wake uku sanadiyyar wani harin da aka kai Muna Garage a wajen birnin Maiduguri.

Karanta wadansu karin labarai

Girona ta ga barakar Real Madrid a La Liga


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mai rike da kofin La Liga na Spaniya, Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Girona da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka kara a ranar Lahadi.

Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Isco a minti na 12 da fara tamaula, kuma haka aka je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne Girona ta farke kwallo ta hannun Cristhian Stuani daga baya kuma Portu ya kara ta biyu, tun farko dan wasan da Pablo Maffeo sun buga kwallo ta bugi turke.

Wannan ne karo na biyu da aka ci Real Madrid a La Liga, bayan da ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Real Betis a Barnebeu a ranar 20 ga watan Satumbar 2017.

Da wannan sakamakon Madrid tana ta uku a kan teburi da maki 20, inda Barcelona wacce take ta daya ta ba ta tazarar maki takwas.

Na kunyata masu sukata — Wenger


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal tana mataki na biyar a kan teburin Premier bayan wasa 10 da ta buga

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce ya rufe bakin masu sukarsa karo biyu a jere da ake fara cinsu a wasa daga baya su farke su yi nasara.

Arsenal ta yi nasarar doke Swansea City da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka yi a ranar Asabar, kuma Swansea ce ta fara cin kwallo.

Wenger ya ce Arsenal ta saka kwazo bayan da aka zura mata kwallo ta farke ta kuma yi nasara a karawa da Swansea da kuma Everton a Premier da Norwich a gasar kofin Caraboa.

Kocin wanda ya ja ragamar Arsenal wasa na 800 a ranar Asabar ya kuma ce sun nuna kwarewar lashe wasa, musamman ace kai aka fara ci ka farke sannan kayi galaba.

Wenger ya kara da cewar ya kunyata masu sukarsu tun a wasan Everton da Norwich da kuma wanda suka yi da Swansea.

Turawan Ingila sun fi kowa rashin iya isar da sako


Hakkin mallakar hoto
University of Southampton

Image caption

“Asalin masu magana da Ingilishi sun fi sanin harshe guda, kuma ba za su iya sauyawa wajen amfani da wani harshe daban,” in ji Farfesa Jennifer Jenkins

A karshen shekara, hedkwatar BBC za ta dawo muku da wasu daga cikin labaran da kuka fi sha’awarsu daga shekarar 2016.

Kalma guda kacal ce a sakon i-mail, amma ta haifar da dimbin asarar kudi ga babban kamfani.

Sakon da aka rubuta cikin Ingilishi, asalin mai magana da harshen ne ya rubuta zuwa ga abokin aikinsa, wanda ya kasance Ingilishi harshe ne na biyu a gareshi.

Bisa rashin tabbaci game da kalmar, wanda ya samu sakon ya samu ma’anoni biyu da suka ci karo da juna a kamus dinsa.

Ya kuma yi aiki bisa la’akari da ma’anar da ba ta dace ba.

Tsawon watanni daga bisani babban jami’in gudanarwa ya binciki dalilin da ya sa aikin da ake yi ya wargaje har ya lakume daruruwan dubban dala.

“Duk an gano asalin aukuwar al’amarin daga kalma guda,” a cewar Chia Suan Chong, wani kamfanin kwararru a harkar sadarwa na Birtaniya da ke bayar da horo bisa la’akari da hadakar al’adu, wanda bai bayyana wannan kalma mai rikitarwa ba, ssboda ta fi alaka da masana’anta kuma ta yiwu a ganota.

“An kasa shawo kan lamarin saboda daukacin wadanda lamarin ya shafa alkiblar tunaninsa ta sha bamban.”

Kwatsam sai Ba’Amurke ko dan Birtaniya ya shigo cikin dakin, kuma babu wanda ya fahimce su – a cewar Chia Suan Chong.

Lokacin da irin wannan rashin fahimtar ya auku, kawai sai a dora alhakin al’amarin kan masu magana da harshen na asali.

Abin mamakin shi ne su suka fi kowa rashin iya isar da sako in an kwatanta da mutane da suka koyi Ingilishi a matsayin harshen a biyu ko na uku, a cewar Chong.

Dimbin asalin masu magana da ingilishi suna farin cikin cewa Ingilishi ya zama ahrshen duniya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Asalin masu magana da Ingilishi sun fi sanin harshe guda’

Suna jin cewa basa bukatar bata lokacin koyon wani harshen,” in ji Chong.

“Sai dai akai-akai idan akwai dakin taron cike da mutanen da suka fito daga kasashe daban-daban da ke magana cikin Ingilishi, kuma kowa na fahimtar kowa, kwatsam sai Ba’Amurke ko dan Birtaniya ya shigo cikin dakin kuma babu wanda ya fahimce su.”

“Asalin masu magana da Ingilishi sun fi sanin harshe guda, kuma ba za su iya sauyawa wajen amfani da wani harshe daban,” in ji Farfesa Jennifer Jenkins.

Wadanda ba asalin masu amgana da harshen ba ne, za su iya sauya harshe, inda sukan yi magana mai ma’ana a tsanake, musamman mutumin da ke magana da harshen a biyu ko na uku.

A wani yanayin masu magana da Ingilishi suna da saurin magana don saura su kwaikwaye su, suna amfani da barrkwanci da kalallame kalami da doka misalan da suka ta’allaka ga al’adarsu, a cewar Chong.

A sakon i-mail suna amfani da rikirkitattun curin haruffa (bakake) a magana kamar ‘OOO- (out of office)’, maimakon kawai su ce za mu fita daga ofis.

“Asali mai magana da iIngilishi… shi ne wanda ta yiwu ya fi jin ba ya bukatar janwo wasu a jika,” in ji ta.

Dangantaka da masu saurarenka

Inda aka samu dimbin wwadanda ba asalin Turawan Ingilishi ba ne a daukacin fadin duniya, masu magana da Ingilishi na bukatar kara kaimi

A ko da yaushe asalin masu Magana da ingilishi kan kane wurin taruka da kashi 90 cikin 100 na lokuta a cewar Michael Blatter

Asalion masu magana da harshen na samun matsala a inda ake amfani da shi a matsayin harshen mu’amalar harkokin kasa,” inda Ingilishi ya kasance jigo mu’amala, a cewar Jennifer Jenkins, Farfesan harsunan Ingilishi a duniya a Jami’ar Birtaniya ta Southampton. “”Wadanda harshensu na asali Ingilishi ne su ke samun matsala wajen fahimta da za su sanya a fahimce su.”

Wadanda ba asalin harshensu Ingilishi ba ne a mafi yawan lokuta ba su cika amfani da manyan kalmomi ba, sun ma fi yin amfani da saukakan kalamai, ba tare da kawata harshee ko kalallame kalamai ba.

Saboda haka, suna fahimtar juna kai ytsaye. Jenkins ta gano cewa, alal misali daliban kasashen waje da ke karatu a jami’ar Birtaniya sun fahimci juna da kyau a cikin harshen Ingilishi, ta yadda cikin sauri za su iya taimako wanda bai kware ba a rukuninsu.

‘Wai me ake nufi ETA?’

Michael Blattner wanda ke Zurrich, asalin harshensa Jamusancin Switzerland, amma a amtsayinsa na kwararre yana hulda da mutane ne cikin harshen Ingilishi.

“Na sha ji daga abokan aikina wadanda ba asalin harshensu ke nan cewa sun fi fahimta ta da kyau in suna saurarena fiye da asalin masu harshen,” a cewar shugaban sashen bayar da horo da tsare-tsare na runkunin kamfanin inshorar IP Operation da ke birnin Zurich.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: Jean-Paul Nerriere).

Image caption

Jean-Paul Nerriere ya bullo da harshen Ingilishi duniya da ya yi wa lakabi da Globish

Jean-Paul Nerriere ya bullo da harshen Ingilishi duniya da ya yi wa lakabi da Globish, wani salon Ingilishi da ke takaita isar da sakonni da kalmomi 1,500, masu sauki amma da managarcin nahawu (ka’idar sarrafa harshe) a matsayin makami.

Daya daga cikin abin damuwa shi ne cura daidaikun haruffa

“Karon farko da na fara aiki a kasasheen duniya na ji wani ya furta ‘Eta 1653’ sai na yi tunani ‘wai mene ne ma ETA?” inji Blattner.

“Karin rudanin ma shi ne wasu daga jerin curarrran haruffa a Ingilishin Birtaniya sun sha bamban da Ingilishin Amurka.”

Sannan akwai salon al’ada, a cewar Blattner. Yayin da dan Birrtaniya ke mayar da martini kan tsarin da aka bijiro masa da cewa, “Abin na da ban sha’awa” wani takwaransa dan Birtnaiya zai iya dauka abin da rashin kima don aganinsa, “Wannan shirme ne.”

Sai dai mutanen da suka fito daga kasashe daban-daban za su iya iya daukar kalmar “interesting – kayatarwa ko ban sha’awa” da kimar daraja, a cewarsa.

Kalmomin da aka saba da su, furta su cikin saurin magana bai cika yin wani tasiri ba, don a cewarsa, musamman idan kullin sadarwar alakar tarho ko bidiyo ba shi da kyau. “Sai ka fara kaucewa kana yin wani abu daban, saboda babu wata damar samun fahimta,” in ji shi.

A wajen taruka, ya kara da cewa, “mafi yawan asalin Turawan Ingilishi sukan kankane batutuwan wurin da kashi 90 cikin 100 na tsawon lokacin. Amma fa sauran mutanen da aka gayyato an gayyato su ne bisa wani dalili.

Masu magana da harshen Ingilishi kadai a mafi yawan lokuta ba su da wayewar yadda za su yi magana game da duniya dungurungum – a cewar Dele Coulter.

Dale Coulter, shugaban sashen koyar da Ingilishi a cibiyar TLC international House da ke Biden a kasar Switzerland, ya yarda cewa: “Masu magana da harshen Ingilishi kadai a mafi yawan lokuta ba su da wayewar yadda za su yi magana game da duniya dungurungum.

A Berlin, Coulter ya ga ma’aikaci Bajamushe da ke aiki a Kamfanin Fortune 500 ana yi masa bayani ta shafin sadarwar bidiyo a intanet daga Hedkwatar kamfaninj da ke California.

Duk da gogewarsa a Magana da Ingilishi, Bajamushen ya tattara bayanai ne kan muhimmin al’amarin da jagoransa wajen aiwatar da ayyuka xan Amurka ya furta.

Don haka a tsakaninsu suka fito da wani tsari da suka amince da shi, wanda ta yiwu ko yaki yiwuwa kan abin da ma’aikacin kamfanin da ke California ke nufi.

“Ana rikirkitar da ma’anonin dimbin bayanai,” in ji Coulter.

Saukakawa ce mafi kyawun lamari

Asalin mai magana da harshen a tattare da hadarin yin asarar cimma matsayar yarjejeniyar kasuwanci, kamar yadda wani Bafaranshe, Jean-Paul Nerriere, wanda tsohon babban Jami’in kasuwanci na duniya ne a kamfanin Kwamfuta na IBM ya yi gargadi.

“Dimbin wadanda ba sa magana da Ingilishi, musammman ‘yan nahiyar Asiya da Faransawa, suna da matukar damuwar “asarar fahimtar abin da ake tattaunawa a kai’ – sai su rika gyada kai da ke nunin amincewarsu, alhali ba su fahimci sakon ba dungurungum,” in ji shi.

Don haka ne Nerriere ya bullo da tsarin tatattacen Ingilishin duniya da ya yi wa lakabi da ‘Globish’ inda ya takaita yawan kalmomin da ake amfani da su zuwa 1,500 cikin sauki, amma bisa managarcin tsarin sarrafa harshe (nahawu).

“Ba maganar harshe ba ne, makamin aiki ne,” in ji shi. Tun sa’adda aka kaddamar da tsarin sarrafa Ingilishin duniya na ‘Globish’ a shekarar 2004 ya sayar da litattafai fiye da 200,000 (da aka fassara) cikin harsuna 18.

“Idan za ka iya isar da sako da kyau a takaice cikin sauki ka tattala lokacinka, ka kauce wa gurguwar fasssara, kuma ba za ka samu kurakurai a harkar sadarwa ba,” in ji Nerriere.

Akwai bukatar ka takaita, da bayyanawa karar da bayani kaitsaye, sannnan akwai bukatar yin al’amura cikin sauki – a cewar Rob Steggles.

A matsayinsa na Baturen Ingilishi wanda ya yi aiki tukurru wwajen koyon Faransanci, Rob Steggles Babban daraktan Kasuwanci na Turai a hamshakin kamfanin sadarwana NTT, ya shawarci Turawan Ingilishi.

Kasancewar yana zaune a birnin Paris, Steggles ya ce, “akwai bukatar takaitawa da bayani karara, kuma kai tsaye, don haka akwai bukatar a saukaka al’amura. Amma akwai kyakkyawar iyaka tsakanin yin hakan da samun karbuwa.

“Gudanarwar na da matukar wahala,” a cewarsa.

Bai wa saura dama

A lokacin da ake kokarin isar da sako a harshen Ingilishi tare da rukunin mutane wadanda kwarrewarsu ta bambanta, yana da muhimmanci a yi kyakkyawar hulda da saukaka al’amura, tare da baje kunnuwanka wajen sauraren mabambantan salon amfani da harshen Ingilishi, a cewar Jenkins.

Mutanen da suka koyi wasu harsunan suna iya yin hakan da kyau, amma asalin masu magana da harshen Ingilishi akasarinsu da ahrshe guda sukee amgana, kuma ba za su iya sauyawa su yi magana da wani ahrshe na daban ba.,” in ji ta.

A taruka, masu magana da harshen Ingilishi suna da hanzari da kazar-kazar kana bin da suka duaka daidai ne, sannan su yi hanzarin cike gibi a wajen tatttaunawa, a cewar Steggles.

“Ta yiwu wadanda ba asalin masu magana da harshen ba su yi kokarin kirkira jimla,” in ji shi.

“Sai ka jira bugun zuciya daon ba su dama. Ko kuma bayan ttaron su zo su ce, “daukacin al’amuran da aka tattauna me suke nufi?

Ko su tafi kawai, sannan babu abin da zai faru saboda ba su fahimta ba.”

Ya bayar da shawarar a rika gudanar da al’amura iri guda a hanyoyi mabambanta, ta yadda za a samu fahimta da daukar mataki da martani.

“Idan babu wadanda ake harka da su,’ Steggle ya yi gargadin cewa, “ba za ka san cewa an fahimceka ko ba fahimce ka ba.”

Aminu Langa-Langa ya buge na Abata Mai


Image caption

A turmin farko Aminun Langa-Langa ya buge Shagon Abata Mai

An dambata da dama a fafatawar da aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Daga cikin wasannin da aka yi har da wanda Aminu Shagon Langa-Langa daga Arewa ya buge Shagon Abata Mai daga Kudu a turmi farko.

Sai dai kuma Bahagon Aleka ne daga Kudu ya fara doke Sani Mai Kifi daga Arewa a turmin farko a wasan da aka fara a safiyar Lahadin.

Damben Autan Horo daga Arewa da Autan Dogon Aleka daga Kudu canjaras aka yi, haka ma wasa tsakanin Usha daga Arewa da Shagon Abata Mai daga Kudu babu wanda ya fadi.

Karawar da aka yi turmi uku tsakanin Bahagon Balan Gada daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu babu kisa alkalin wasa Tirabula ya raba su.

Sai aka dambata a wasan da Shagon Sama’ila daga Kudu ya yi nasara a kan Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa a turmin farko.

Damben Shagon Fanteka daga Kudu da Shagon Bala Dan Zuru daga Arewa babu kisa, haka ma wasa tsakanin Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Dan Abata Mai babu kisa.

Wasan daf da karshe da aka dambata kuwa Shagon Nuran Dogon Sani ne daga Arewa ya buge Shagon Autan Faya daga Kudu a turmi na biyu.

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya


Wasu zababbun hotuna daga nahiyar Afirka da kuma na ‘yan nahiyar a wasu sassan duniya.

Hakkin mallakar hoto
AFP

An haska filin wasanni na Mohamed VI a birnin Casablanca da wuta mai launin ja a ranar Asabar a yayin da magoya bayan kungiyar kwallon kafar Morocco mai suna Wydad Casablanca suka doke kungiyar kwallon kafar Algeria mai suna USM Algerm inda suka kai matakin karshe a wasan zakarun Afirka.

Models display creations by Amede at the Lagos Fashion and Design Week in Lagos 25/10/2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Kayan wata ‘yar Najeriya Amede, mai dinka kayan kawa sun kayatar ranar Laraba a bikin baje kolin kayan kawan a jihar Legas, wanda zai taimaka wajen tallafawa da kuma inganta masana’antun kayan kawa a Najeriya da ma Afirka.

Two men take a selfie during Kenya's Mashujaa Day (Heroes' Day) celebrations at Uhuru park in Nairobi 20/10/2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Zaman lafiya a Kenya, shi ne jigo ga wadannan maza da suke daukar hoto a lokacin bikin ranar jarumai ta kasar a babban birnin Nairobi ranar Juma’ar da ta gabata wacce ta kasance ranar hutu ce.

A man holds a burning stick as opposition supporters demonstrate at a burning barricade in Kibera, Nairobi, 25/10/2017Hakkin mallakar hoto
AFP

Sai dai kuma banga da tashin hankali sun gabaci maimaicin zaben shugaban kasar- a wannan hoton, wani mutum ne rike da sandar da take ci da wuta inda magoya bayan ‘yan adawa suka yi zanga-zanga a wajen shingaye masu ci da wuta a wani yankin marasa galihu na Kibera a birnin Nairobi ranar Laraba.

A man watches as protesters clash with riot police attempting to disperse supporters of Kenyan opposition leader Raila Odinga in Kibera slums of Nairobi. 26/10/2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Ranar Alhamis, wadda ta kasance ranar zaben, tashin hankalin ya ci gaba: A wannan hoton, wani mutum ne yake hangen arangamar da ake yi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a garin Kibera.

Members of the Legio Maria Church react while being affected by tear gas during clashes between the police and opposition supporters in Mathare, Nairobi, Kenya - Thursday 26 October 2017Hakkin mallakar hoto
AFP

A yayin da su kuma wadannan mabiya cocin Kenya na Legio Maria suka shiga matsi lokacin da aka harba hayaki mai sa hawaye lokacin arangama a unguwar Mathare a Nairobi ranar zabe.

African migrants sit on the side of a road as they wait for work in Misrata, Libya 22/10/2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

‘Yan ci rani sun zauna a jere ranar Asabar yayin da suke jiran samun aiki a birnin Misrata na Libya.

A South Sudanese refugee girl is seen at the Nguenyyiel refugee camp during a visit by US Ambassador to the UN Nikki Haley (not pictured) to the Gambella Region, Ethiopia October 24, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Wata yarinya ‘yar gudun hijira daga Sudan ta Kudu a sansanin ‘yan gudun hijira a Nguenyyiel ranar Talata, a lokacin da Jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya ya kai ziyara yankin Gambella a Kasar Ethiopia.

Graca Machel, ex UN Secretary-General Kofi Annan (R) and ex Chile President Ricardo Lagos (C) take part in a Mandela Walk Together event in Westminster, Central London, Britain, 23/10/2017.Hakkin mallakar hoto
EPA

Wani taron tunawa da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela mai taken ‘Mandela Walk Together’ a Westminster birnin London ranar Litinin wanda ya samu halartar matar marigayin, Grace Machel, da tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan da ma wasu sanannun mutane a duniya.

Tom Morgan, from Bristol-based company The Adventurists, flies in a chair with large party balloons tied to it near Johannesburg, South Africa 20/10/2017Hakkin mallakar hoto
Reuters

Wani dan kasar Birtaniya Tom Morgan ya gwada wani abu da ba a taba ganin irinsa ba inda ya tashi sama tsawon kilomita 25 da taimakon balan-balan guda 100 da ya daura a jikin kujerar da yake zaune a kai.

South African surfer Mike Schlebach surfing, Cape Town, South Africa - Monday 23 October 2017Hakkin mallakar hoto
EPA

Wani dan kasar Afirka ta Kudu Mike Schlebach ya taka rawa a gasar zamiyar cikin ruwa a birnin Cape Town ranar Litinin.

Hotuna daga AFP da EPA da PA da kuma Reuters

Yadda mata ke shiga matsala sakamakon zubar da ciki


Image caption

Yawancin mata ba sa kaunar yin magana game da zubar da ciki

Daya a cikin mata uku za ta zubar da ciki a tsawon rayuwarta, amma abu ne da ba a cika yin maganarsa ba.

Ga wasu, yanke hukuncin zubar da cikin na da tsananin tashin hankali kuma yana iya zama a zuciyar mutum har abada. Ga wasu kuwa, yana karfafa masu gwiwa, kuma yasauya masu rayuwa.

Kuna ta ba mu labarin zubar da cikinku shekaru hamsin bayan da a ka sanya dokar zubar da cikin a shekarar 1967.

‘Na samu sassauci, na ji farin ciki kuma na ji dadi’

Louise a Landan: “Lokacin da na ke da shekara 23 na gane ina da ciki. Ban taba yin da-na-sanin zubar da ciki ba. Ya taimaka wajen tabbatar min da cewa lallai ba na so in haihu”.

“Daga farko da ban ga al’adata ba, sai na yi tunanin ko saboda ina cikin damuwa ne. Na ji kamar ina da lalurar rashin lafiyar da mata ke yi kafin zuwan al’adarsu.

“Sai wata rana a wajen aikina, sai da na kwanta a tantagaryar kasa saboda tsananin gajiya. Na shiga tunanin abun da ya same ni, sai kawai abun ya fado min a rai.

“Na yi gwaji domin duba juna biyu lokacin hutun cin abincin rana a wajen aiki. Ina ganin gwajin ya nuna cewa ina da juna biyu, sai na fara jijjiga da karfi. Na so in yi dariya da kuka duk a lokaci daya.

“Wata abokiyar aikina wacce ta dade tana neman haihuwa ta fara murna da na gaya mata cewa ina da juna biyu. Amma ko da na gaya mata ni a wurina ba abun farin ciki ba ne ta fahimce ni. Sai kawai ta rungume ni”.

“Mijina ya kyale ni na dau shawarar ni kadai. Ba mu taba tattaunawa a game da zubar da cikin ba. Kawayena na kusa-kusa sun bani goyon baya”.

“Likitana kuwa ya nuna halin ko in kula. Na tattauna sau biyu da wasu malaman asibiti kafin a ka zubar da cikin.

“Ba su taba tambayata ko abun da na ke yi daidai ne ba. Na tabbata. Aikin zubar da cikin na da matukar zafi saboda na zabi a yi min aikin ba tare da an yi min allurar kashe zafi ba, amma ba a dade ana yin aikin ba”.

“Da a ka yi aikin, damuwar da na shiga kafin a yi aikin ta tafi. Na samu sassauci, na ji farin ciki kuma na ji dadi.”

Ya jefa ni halin bakin ciki’

Beth (ba sunanta na gaskiya ba)na zaune a Ingila:

“Shekaruna 17 lokacin da na samu juna biyu, kuma na zubar da shi a watan Fabrairu”.

“A yanzu haka ina da ciki kuma wannan karon ba zan zubar ba, ina farin ciki da shi.”

“Lokacin wani bikin kirisimeti ne, kowa na ta annashuwa, ni kuwa ina ta rashin lafiya. Na yi tunanin saboda mu na ta shan barasa ne, sai wani ya zolaye ni ya ce ko dai juna biyu ne da ni. Sai ko na gano juna biyun ne da ni.”

“Saurayina bai ce komai ba dangane da juna biyun, kuma ya kyale ni na dauki matakin da na so. Mahaifiyata kuwa ta natsu, kuma ta ce in yi abun da nake so in yi.”

“Amma mutane da dama sun ta gaya min cewa na yi yarinta kuma ban shirya haihuwa ba. Na fuskanci matsin lamba dangane da zubar da ciki. Ya jefa ni cikin halin bakin ciki.”

“Na fuskanci tsananin damuwa bayan da na zubar da cikin saboda raina ya baci sosai. Na ji kamar na dauki matakin da bai dace ba kuma babu abun da zan iya yi dangane da hakan.

“Likitan ya bani magunguna da shawarwari. Dama can ina da ciwon damuwa da rashin kwanciyar hankali sai hakan ya sa ciwon nawa ya kara tsanani.

“Yanzu da nake dauke da wannan cikin, mahaifiyata da saurayina su na ganin in yanke hukunci da kaina.”

“A watan Afrilu zan haihu, kuma na kagu lokacin ya yi.”

Hakkin mallakar hoto
Science Photo Library

Image caption

Na shiga damuwa kan yanke hukuncin da ya dace

Ya kamata a rika ilmantar da mutane cewa zubar da ciki ba laifi bane”

Harriet a Kudu Maso Gabashin Ingila:

“Abu ne da ba shi da dadi amma kana koyar darasi daga wadannan abubuwan.”

“Shekarata 20 lokacin da na zubar da ciki.”

“Idan na ga ‘ya’yan kawayena ko kuma ‘ya’yan ‘yan’uwana sai na rika tunanin da yanzu ni ma ina da jariri dan wata uku.”

“Da na fara gane cewa ina da ciki na yi murna kuma na nuna kulawa- na yi tunanin wannan jaririna ne kuma babu wanda zai iya karbe shi.”

“Mahaifiyar kawata ta taimaka min kuma ta ce ni ma danginta ce amma ni na sa nawa iyalin, ko kuma makamancin hakan.”

“Ba ni da wani zabi. Mahaifina ya ce zabina ne amma ba zai iya tallafa min da kudi ba. Da gaske ne, gaskiya ya gaya min. Na yi tunanin zan zamo mai son zuciya idan na ce zan haihu. Ya kamata a ce da ya samu kulawa daidai gwargwado.”

“Uban dan ba ya son cikin. Na ji haushinsa saboda matsayin da ya sani a ciki. Sai ya zamo kamar an takura ni a sako, kuma ba zan iya haihuwar dan ba saboda bani da halin kula da shi.”

“Abu ne mai matukar ban takaici farfadowa daga allurar baccin. Cikin ya wuce wata uku don haka sai da aka yi min tiyata.

“Abu ne marar dadi. Na farka da zummar sanin abun da ya faru da jikina, da kuma rashin son sanin abun da ya faru.”

“A ko yaushe na kasance cikin kuka kuma yanzu ina tunanin wannan shi ne abun da na yi wa dana na fari.”

“Hukumar Kula da Lafiya ta Kasar (NHS) ta bani tallafi sosai kuma ta bani damar sauya ra’ayina. Ya kamata a rika ilimantar da mutane a kan cewa zubar da ciki ba laifi ba ne kuma zabin mace ne amma dole a ba ta tallafi sosai.”

“Akwai kyama sosai da a ke alakantawa da zubar da ciki.”

Aure ka iya hana samun cutar mantuwa – Bincike


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bincike ya nanata muhimmanci shiga jama’a da kuma samun aminattun abokai a rayuwa

Aure da yin abokai ko kawaye na kukut ka iya taimakawa wajen hana kamuwa da cutar mantuwa a cewar masu bincike na Jami’ar Loughborough a Ingila.

Binciken wanda aka wallafa a Mujallar kimiyyar nazarin tsufa, ya bibiyi rayuwar manyan mutane guda 6,677 tsawon kimanin shekara bakwai.

Dankon zumuncin da ke tsakaninn rukunin abokan mutum na kukut ga alama ya fi muhimmanci a kan yawan abokai, a cewar ayarin masu bincike.

Gidauniyar Alzheimer’s Society mai tallafa wa masu cutar shiriricewa ta ce abu ne mai matukar muhimmanci taimaka wa marasa lafiya su samu “mu’amaloli masu ma’ana da jama’a”.

Babu wani cikin mutanen da aka bibiyi rayuwarsu da ke da cutar matsananciyar mantuwa a farkon gwaji, sai dai a tsawon lokacin da ake ci gaba da gwaje-gwajen an gano mutum 220 na da ita.

Rukunin masu binciken ya kwatanta halayyar mutanen da suke da cutar matsananciyar mantuwa da wadanda ba su da ita da nufin gano alamomi kan yadda huldarsu da jama’a ke da nasaba da hatsarin kamuwa da ita.

Wani bincike ya ce idan ana batu kan abin da ya danganci abota, to dankon zumunci ya fi tasiri a kan yawan abokai.

Farfesa Eef Hogervorst ta ce: “Mutane na iya kasancewa a kusa da kai, amma adadin aminai na kukut ne ke da alaka da raguwar hatsarin kamuwa da cutar mantuwa… ba wai yawan abokai ba.”

Ta ce tana jin samun abokai na kukut ka iya kasancewa “shamaki” daga matsalar nuƙurƙusar jiki, wadda ke da alaƙa da raunin lafiya.

Sabubba tara da ke janyo hatsarin cutar mantuwa

Kurumcewa a shekarun manyanta – na sanadin kashi 9% na hatsarin kamuwa

Gaza kammala karatun gaba da sakandare – 8%

Shan taba sigari – 5%

Gaza neman maganin sirewar rayuwa tun wuri – 4%

Rashin katabus – 3%

Ware kai daga jama’a – 2%

Hauhawar jini mai tsanani – 2%

Taiba – 1%

Ciwon suga rukuni na 2 – 1%

Wadannan sabubba – da aka bayyana, na cikin jerin wadanda ake iya sauyawa – sukan hadu su kasance kashi 35 cikin 100.

Ana jin ba a iya sauya sauran sabubban da ke haddasa cutar mantuwa wadanda su ne da ke da kashi 65 cikin 100.

Nazarin kuma ya nuna cewa mutanen da ke rayuwar gwaurontaka na da ninki biyu na hatsarin kamuwa da cutar mantuwa a lokacin binciken idan an kwatanta su da masu aure.

Ana da masaniyar cewa cutar mantuwa na fara shafar kwakwalwa ne shekaru gommai kafin a gano ta, ta hanyar gwaje-gwaje kuma wasu daga cikin sauye-sauyen farko da mai cutar ke samu na hana mutum mu’amala da jama’a.

Ko ma dai yaya abin yake, daraktan bincike a gidauniyar tallafa wa masu cutar kuncewar tunani, Dr Dough Brown na cewa kadaici wani gagarumin abu ne wajen haddasa cutar mantuwa.

Mutane na mutuwa saboda yunwa a Congo


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yunwa na hallaka mutane musamman yara a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan uku ne ke cikin hatsarin yunwa a lardin Kasai mai fama da rikici na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Shugaban shirin samar da abinci na Duniya, David Beasley, ya fada wa BBC cewa tuni kananan yara da dama suka riga mu gidan gaskiya saboda yunwa.

Ya kuma ce ana bukatar tallafi cikin gaggawa don kare karin wasu dubban daruruwan mutane daga mutuwa a watanni masu zuwa.

Rikici tsakanin dakarun gwamnati da abokan kawancensu a hannu guda kuma da sojojin sa-kai ne ya ta’azzara farin da ake fama da shi a yankin.

Ana zargin duka bangarorin biyu da far wa fararen hula.

Nigeria: ‘Muna kamo macizai ne don ceton rayuka’


Hakkin mallakar hoto
AFP/GETTY IMAGES

Image caption

Mesa da kububuwa na daga cikin macizan da suka fi addabar mutane a Kaltungo

Wani mai kama macizai a Najeriya ya ce dabara suke amfani da ita wajen kama maciji amma ba dogaro da jikon magani ba.

Malam Ali Garba wanda a yayin zantawa da wakilinmu Ishaq Khalid yake tare da macizai kimanin bakwai da ya kamo ciki har da kububuwa da gamsheka da kasa ya ce ya fara sana’ar kama macizai ne tun shekarar 1999 don ceton rayukan jama’a.

Akasarai dai sai an kamo macijin da ya yi sara kafin a san kowanne iri ne, idan za a yi wa mutum magani.

A cewar Ali Garba ana amfani da basira ne wajen kama maciji. Kuma sukan kamo su da yawa, su kai asibitin Kaltungo a jihar Gombe.

“Za ka ga an kawo mutum ba yadda yake, to kuma idan ba an kamo macijin ba, ba za a samu asalin maganin macijin ba, ko kuma yadda za a cire dafinsa a yi maganin ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa sukan shiga daji su kamo su, idan suka kamo su kuma sai a tara macizan kafin a kai su inda za a cire dafin.

Shi ma wani mai kama macijin Dala Usaini ya ce sun sani cewa sana’arsu tana cike da hatsari, don kuwa “da ya sare ka a wurin, idan babu mai taimakonka to ka gamu da nakasa”.

“In ba mutum a kusa da kai kafin ka dawo gida, in ba Allah yai maka nisan kwana ba, za ka bar duniya a take,” in ji shi.

Ya ce suna neman taimako don tsare jiki, sai dai duk da haka macijin ya taba saransa.

Dala Usaini ya ce maciji kan sare su amma saboda sun sha magani, abin ba ya nakasa su kamar wanda bai taba amfani da magani ba.

Shi ma Ali Garba ya ce maciji ya sare shi lokacin da ya je kamo shi, don ya kai a yi magani, inda ya yi ta zuba masa dafi a hannu.

“Lokacin da ake neman maciji, ba magani a nan (asibitin Kaltungo) ni kuma aka nemi a kamo macijin don a yi magani.

Na sa hannu na kamo shi, sai ya sa hakori kuma maimakon ya sa dafi kadan amma sai ya yi ta zubawa kafin na bude akwati na sa shi wurin ya riga ya zama baki. Na ji kamar an dora min dutse a kai.”

Ali Garba ya ce daga baya sai da aka yanke yatsan don gudun kada ya shafi hannun gaba daya kuma dole a yanke shi.

Ya koka kan yadda mutane kan tsaya amfani da magungunan gargajiya a gida bayan maciji ya sari mutum har sai dafin ya ratsa jiki, abin da ke da matukar hatsari.

“Gaskiya akwai magani amma akwai wasu masu yaudarar mutane a kan magani, za ka ga wasu suna tallan maciji…amma yawanci suna cire hakoran ne su zo suna wannan abu a kasuwa.”

Dala Usaini ya ce a yankin Gombe sun fi kama kububuwa, wanda kuma hatsabibin macijin ne da ba ya tsoron mutum.

Ana bincike kan ko cutar kyandar birrai ta je Kano


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Cutar kyandar birrai dai ta bulla a wasu jihohin Najeriya ciki har da Abuja babba birnin tarayyar kasar

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta musanta jita-jitar da ake yadawa kan bullar cutar kyandar birrai a jihar.

A ranar Alhamis ne dai aka fara rade-radin an samu wani mutum da ya kamu da cutar, bayan mutum na farko da gwamnati ta ce ba cutar ce ta kama shi ba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Kabir Abubakar Getso, ya shaida wa BBC cewa, an samu mutum guda da ake zargin ya kamu da cutar a karamar hukumar Bebeji, to amma tuni aka dauke shi aka kai shi cibiyar da aka ware domin kula da wadanda suka kamu da irin wannan cuta ko makamanciyarta don kula da shi.

Dr Kabir Abubakar Getso, ya ce yanzu haka an fara yi wa wannan mutum gwaje-gwaje da kuma gudanar da cikakken bincike, don gano kowacce irin cuta ce.

Ya ce, ya zuwa yanzu ba a tabbatar da ko cutar kyandar birrai ba ce, sai abinda bincike ya gano tukunna.

Kwamishinan ya ce, ko a makon da ya gabata, an kawo musu wani da ake zargi ya kamu da cutar saboda kurajen da suka fito a jikinsa sun yi kama da na wanda ya kamu da cutar kyandar birran, to amma ko da a gwada sai aka gano ba ita bace.

Do haka ya ce yanzu bincike ne kadai zai tabbatar da cutar ce ko ba ita bace.

Ita wannan cutar dai ta samo asali ne daga jikin biri da sauran dabbobi kamar su bera da kurege da kuma barewa.

Somalia: An sake kai harin bam a Mogadishu


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wurin da aka kai harin

Bama-bamai biyu sun fashe a babban birnin Somalia Mogadishu, mako biyu bayan mummunan harin bam din da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 350.

Harin farko ya faru ne bayan da aka shigar da wata mota cikin wani otel. Daga nan ne sai wadansu mahara suka yi wa ginin dirar mikiya.

Hari na biyu ya faru ne kusa da tsohon ginin majalisar dokokin kasar.

Sai dai ba san adadin wadanda harin ya rutsa da su ba tukuna.

Kungiyar al-Shabab wadda aka zarga da kai harin makon jiya – ta ce ita ta kai harin.

Jami’in dan sanda Mohamed Hussein ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa:

“Akalla mutum bakwai ne ciki har da wani soja da fararen hula ne suka mutu”.

Masu aikin asibiti sun ce mun 15 ne suka jikkata, kuma “mutane da dama ne suka mutu.”

Ingila ta ci kofin duniya na matasa ‘yan 17


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Karon farko da Ingila ta lashe kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekara 17

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta yi nasarar lashe kofin matasa ‘yan kasa da shekara 17, bayan da ta casa Spaniya da ci 5-2.

Tun farko Spaniya ta ci kwallo biyu ta hannun dan wasan Barcelona Sergio Gomez, sai dak kafin hutu Ingila ta zare daya ta hannun Rhian Brewster kuma na takwas da ya ci a gasar.

Daga nan ne Ingila ta samu kwarin gwiwa ta farke ta hannun Morgan Gibbs Wwhite wasa ya koma 2-2.

Ingila ta kara cin kwallo biyu ta hannun Phil Fodaen, sannan Marc Guehi ya ci na biyar.

Tawagar kwallon kafar Ingila ce ta lashe kofin duniya na matasa ‘yan 20 da aka yi a watan Yuni.

Arsenal ta koma ta hudu a kan teburin Premier


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ramsey ya ci kwallo a karawar da Arsenal ta doke Everton 5-2

Arsenal ta koma ta hudu a kan teburin Premier, bayan da ta doke Swansea City da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka kara a ranar Asabar a Emirates.

Swansea ce ta fara cin kwallo ta hannun Sam Clucas, bayan da aka dawo ne Arsenal ta farke ta hannun Sead Kolasinac daga baya Aaron Ramsey ya kara ta biyu.

Wasan wanda shi ne na 800 da Arsene Wenger ya ja ragamar Arsenal ya sa ta samu maki uku a ranar Asabar, sannan 19 jumulla a wasa 10 da ta buga ta kuma koma ta hudu a teburi.

Sai dai kuma Chelsea wacce take ta biyar da maki 16 za ta ziyarci Bournemouth a karawar mako na 10.

World Cup U-17: Brazil ta yi ta uku bayan da ta ci Mali


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Brazil ce ta uku sai Mali ta hudu a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan 17 a India

Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta yi nasarar doke ta Mali 2-0 ta kuma zama ta uku a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan 17 da suka kara a India.

Brazil wacce ta yi rashin nasara a hannun Ingila a wasan daf da karshe ta ci Mali ne ta hannun Alan fortuitous da kuma Yuri Alberto a fafatawar da suka yi a Kolkata a ranar Asabar.

Mali wacce ta yi rashin nasara a wasan daf da karshe a hannun Spaniya ta zama ta hudu a gasar ta matasa ta duniya, duk da cewar ita ce zakara a nahiyar Afirka.

Za a buga wasan karshe tsakanin Ingila da Spaniya.

‘Yan PDP ne rabin gwamnatin Buhari – Hameed Ali


Hakkin mallakar hoto
Facebook/Nigeria Customs

Image caption

Hameed Ali yana daya daga cikin na kusa da Shugaba Buhari

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya Kanar Hameed Ali ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa cika alkawurran da ta yi wa al’ummar kasar na kawo sauyi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi lokacin kaddamar da wani sabon ofishin kungiyar goyon bayan Shugaba Buhari wato (Buhari Support Organisation BSO) a Abuja ranar Juma’a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Kungiyar BSO ita ce babbar kungiyar da ta kunshi sauran kungiyoyi da suka shige wa shugaban gaban wajen yakin neman zaben shekarar 2015.

Hameed Ali ya ce kalubalen da za a fuskanta a zaben shekarar 2019 sai ya fi wanda aka gani a shekarar 2015.

“A yanzu, zan iya cewa muna da ‘ya’yan jam’iyyar PDP kaso 50 cikin 100 a cikin gwamnatinmu. Ta yaya za a ci gaba da wannan nauyin a kanmu? Ta yaya za mu iya cimma abin da muke fata da wannan nauyin,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “A yanzu ‘yan PDP ne suke ba da umarnin abin da za a yi. Wannan ne abin da ya kamata mu yaka. Za mu yi yaki don kwato hakkinmu da kuma kyawawan manufofin gwamnatinmu.”

Hakazalika ya ce lokaci ya yi da za su farka daga bacci don samar wa kasar makoma ta gari.

Sai dai ya ce “Shugaba Buhari ba shi da wata matsala don yana abin da ya dace ne.”

Adikon Zamani: Yadda mata ke shan tasku a sansanin ‘yan gudun hijira a Abuja


Kuna iya latsa alamar lasifikar nan ta sama don sauraron cikakkiyar tattaunawar da Halima Umar Saleh ta yi da matan a shirin Adikon Zamani.

A duk lokacin da aka ambaci lamarin mata, to babban abun da ke fara zuwa ran yawancin mutane shi ne matsalar da suke fuskanta ta bangarori daban-daban na rayuwa.

Tun bayan da rikicin Boko Haram ya yi kamari mutane da dama suka tsere daga garuruwansu don neman mafaka a inda suke tunanin ya fi musu kwanciyar hankali.

Sai dai duk yawancin ‘yan gudun hijirar kan fake ne a sansanoni da ko dai gwamnati ce ta gina ko kuma kungiyoyi masu zaman kansu, a matsayin sabon muhalli.

A irin wannan yanayi na zaman gudun hijira dai mata ne suka fi shan wahalar rayuwa a sansanonin saboda irin lalurorin da aka fi sanin mata na fama da su ko da kuwa zaman jin dadi suke yi a gidajensu.

Lalurorin sun hada da na goyon ciki da haihuwa da raino da tsaro da ma batun jinin al’ada.

An kiyasta cewa mata ne suka fi yawa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke yankuna daban-daban na Najeriya da ma makwabtan kasashe irin su Nijar da Kamaru.

Da yawansu kuma mazajensu sun mutu sun bar su da yara, yayin da wadanda nasu mazajen ma ke raye ba su tsira daga wahalhalun rayuwa ba a sansanonin.

A shirin Adikon Zamani na wannan makon BBC Hausa ta kai ziyara wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda Halima Umar Saleh ta tattauna da wasu mata kan irin matsalolin da suke fuskanta kamar na goyon ciki da haihuwa da ma batun jinin al’ada.

Sun kuma shaida mata cewa, suna cikin tasku ba kadan ba, dangane da samun kayayyakin kawar da lalurorinsu wadanda mata ke yawan fama da su.

Matan aure da ‘yan mata da ke rayuwa a wannan sansani dai duk suna zaman tsammanin warabbuka ne, na jiran kayayyakin taimako da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma bayin Allah da ke kai musu don tare matsalolin nasu.

Baya ga wannan batu kuma, akwai batun rashin ingantaccen tsarin bandaki don zagayawarsu, inda a dole suke tafiya jeji su kawar da lalurarsu.

Sai dai wata budurwa ta shaida min cewa, duk da dai bandakin ba shi da tsafta kuma ana iya daukar wasu cututtuka ma, to ta gwammace ta shige shi hakan nan maimakon ta je jeji.

“Wata rana na je jeji na tsugunna kenan sai ga maciji, shi yasa na daina zuwa gara dai na je bandakin duk da cewa a can na kwaso wata cuta ta kaikayin al’aura da kuraje, saboda rashin tsaftarsa,” a cewar Patience.

To ko ma dai mene ne yawan matsalolin da matan ke fuskanta, sun gwammace zama a wannan waje a takure maimakon su koma garuruwansu da suka baro sakamakon rikicin Boko Haram.

An daure mutumin da ya sa wa mata 30 HIV


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Lauyoyin da ke kare Velentino Talluto sun ce ba gangan ya aikata wannan ta’asa ba

An daure wani dan kasar Italiya mai cutar kanjamau tsawon shekara 24 a gidan yari bayan samunsa da laifin yad’a cutar da gangan ga mata har talatin ta hanyar jima’i ba tare da kariya ba.

An zargi mutumin wanda akanta ne dan shekara 33, Valentino Talluto da yada cutar ga ‘yan matan da yake gamuwa da su ta shafukan samartaka na intanet tsawon shekara goma bayan ya kwan da sanin yana da kwayoyin cutar.

Masu bincike sun ce akwai maza guda uku samarin irin wadannan mata da su ma suka harbu, baya ga wani jariri na hudu.

Lauyoyi masu kare mutumin sun ce ayyukan Talluto rashin kiyayewa ne amma ba ganganci ba.

Mahaifiyar Valentino wadda ‘yar shaye-shaye ce, ita kanta ta kamu da cutar ta HIV , inda kuma ta mutu a lokacin yana da shekara hudu da haihuwa.

Matsalar tabin hankali na sa asarar naira triliyan 47


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Shin ana iya kokari wajen taimaka wa maus tabin hankali a wajen aiki?

Wani bincike ya nemi a kara matsa kaimi wajen dakile matsalolin tabin hankali a wajen aiki.

Rahoton wajen aiki mai nagarta ya ce mutane 300,000 da suka dade da larurar tabin hankali yana zama musu tilas su bar aikinsu a ko wacce shekara.

Kuma wannan yana sa Birtaniya tana rasa fam biliyan 97 kimanin naira triliyan 47 a ko wacce shekara.

Mutum uku sun bayyana wa BBC yadda suka hadu da matsalarsu ta tabin hankali a wajen aiki.

Stephanie da Landan ta ce ya kamata a samar da gagarumin sauyi kan yadda ake tunkarar matsalar tabin hakali a wurin aiki.

“A matsayina na wacce take fama da bakin ciki da fargaba, ba zan iya tattauna matsalar tabin hankalina da wadanda suka dauke ni aiki ba.

“Akwai wata al’ada – musamman a cikin ofisoshi – wadda ke ganin wannan a matsayin wata alama ta rauni ko kuma rashin iya tafiyar da aikinsu.”

Stephanie ta daura laifin ne kan al’adar dadewa ana aiki kullum, inda manajoji ke sa ma’aikata su ji sun yi laifi idan suka dauki hutun lokacin cin abinci.

“Akwai bukatar gagarumin sauyi kan yadda ake tunkarar lafiyar hankali,” wadda ta ce, “ba za a iya magance ta da horaswa kadan a wajen aiki ba.”

Hakkin mallakar hoto
Daisy

Image caption

Daisy ta ce ta yi sa’ar samun wajen aiki mai agazawa

Daisy daga Taunton ta fuskanci yanayi biyu na tunkarar matsalar lafiyar hankali a wajen aiki.

Daisy ta yi aiki tare da wata hukuma, amman ta ce: “Ina ganin suna neman uzurin da za su yi amfani da shi domin su kore ni.

“Na bar aiki domin ban gamsu da wurin aikin da kuma rashin tallafi ba.”

“Sauya wurin aiki daga ma’aikatar gwamnati zuwa ta masu zaman kansu ya bude mini ido.

“Na gaya wa masu sabon wurin aikina gaskiya game da matsalolin da nake da su game da lafiyar hankalina, kuma martanin da suka fara mayarwa shi ne, ‘ba matsala ba ce’.

“Martanin da suka mayar din wata halayya ce wadda ta ba ni matukar mamaki.”

A lokacin da ta samu koma baya a lafiyar hankalinta, ta samu tallafi a kan lokaci: “Wadanda suka dauke ni aiki sun ba ni damar ganawa da wani likitan hankali mai zaman kansa domin ya taimaka musu wajen kara fahimtar halin da nake ciki da kuma samun wani bincike mai zaman kansa.

“Daga baya aka gane cewa ina fama da matsalar saurin sauya halayya da yadda nake ganin kaina da kuma yadda nake aiki wadda ake ce wa Borderline Personality Disorder a Ingilishi, tare da matsalar damuwar bayan shan wahala da nake da ita da damuwa mai tsanani da kuma fargaba.

“Taimakon da wadanda suka dauke ni aiki suka ba ni ya ceci rayuwata”.

Hakkin mallakar hoto
Lorna

Image caption

Lorna ta gane cewa tsayawa tsayin daka ka iya taimakawa

Lorna daga Ballymena ta bar aikinta sabida matsalolin lafiyar hankali bayan haihuwarta ta uku a shekarar 2006.

Ta gano cewa tsayawa tsayin daka shi ne mataki na farko na warkewa daga matsalar.

“Tsarin kiwon lafiyan ya taimaka mini,” in ji ta. “Na yi sa’a sosai na samun taimako cikin gaggawa game da halayya kuma likitana ya lura da cigaban da nake samu a warkewa.

“Amman ni ne na yi tambaya kan ko zan iya daina karbar magani a karkashin kulawa”.

Lorna ta kuma koma aikin ‘yan wasu lokuta, lamarin da ya rage iya matsin da take samu.

A yanzu haka tana aikin kwana biyar ne kuma tana amfani da kayayyakin aiki tare da mayar da hankali da wani nau’in magani da kuma rubutu wa mujalla domin tattabar da lafiyar hankalinta.

“Har yanzu ina da ranaku da nake jin dadi da kuma ranakun da ba na jin dadi, amman a yanzu na san yadda zan gane yadda nake ji.

“In akwai wani abu da zan iya sauyawa, zan dauki mataki. In kuma ba haka ba – zan rungumi kaddara, warware matsalar sannan in cigaba da rayuwa”.

‘Don me Buhari ke gum in makusantansa sun yi laifi?’


Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

An gudanar da taron ne mai taken #BuhariMeter don kimanta nasarorin gwamnatin Buhari

Manazarta a Najeriya sun nuna cewa daga cikin abubuwan da suka fi damun mutane ya zuwa yanzu a mulkin Muhammadu Buhari, sun hadar da gaza inganta tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

“Domin haka, shirin da suka fito da shi sai aka ga ba wani abu takamaimai da zai tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar zai habaka.”

Haka zalika, ana ta diban bashi, wanda kuma a cewa manazartan ka iya gagarar Najeriya biya, don kuwa a cewarsu kudin shigar kasar ba wani karuwa ya yi ba.

Taron ya ce: “Gwamnati kamar wata dabara suke yi, suna cewa idan aka duba girman tattalin arzikin, bashin da ake ciyowa ba zai iya fin karfin kasar ba.

Amma idan ka duba kudin da suke shigowa nan ne za ka ga ba shakka akwai matsala, don kuwa duk wata kasa wadda yawancin kudin shigarta, ana amfani da su wajen biyan bashi. Shi kenan babu abin da za a yi wa mutane aiki?”

Wadannan na daga cikin batutuwan da masana gami da masu ruwa da tsaki suka bijiro da su a wani taron kimanta nasarorin gwamnatin Muhammadu Buhari da ta shafe kusan shekara uku a mulki.

Akasarin ra’ayin mahalarta taron wanda cibiyar wanzar da ci gaba da kuma dimokradiyya a Najeriya ta shirya, shi ne babu wani ci gaban a-zo-a-gani da ‘yan kasar suka shaida tun bayan kafa gwamnati.

Da yake shaida wa BBC sakamakon da taron ya cimma, wani wakili a cibiyar, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce karuwar garkuwa da mutane a kasar ta dusashe nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu ta fuskar tsaro.

“A kan tsaro, an dan samu zaman lafiya, amma har yanzu ana kashe-kashe. Mutane a yankin arewa maso gabas har yanzu samun matsalar Boko Haram.

Batun garkuwa da mutane kuma a fadin kasar ya zama ruwan dare, har ta kai mutane ma na tsoron tafiye-tafiye.”

A cewar taron, idan aka duba an samu gyara ta wani fanni, ta wani fannin kuma sai a ga abubuwa ma na kara lalacewa ne.

Game da batun cin hanci da rashawa kuma, Farfesa Jibrin Ibrahim mutane sun yi tambayar cewa me ya sa idan makusantan Buhari sun yi laifi sai ya yi shiru?

“Mutane da yawa sun yi magana a kan tsohon Sakataren Gwamnati, Babachir wanda fiye da wata shida kenan aka yi bincike kansu, kuma aka ba shi rahoto kuma ya yi tsit a kan abin.”

Farfesa Jibrin ya ce tambayar da mutane ke yi ita ce me ya sa idan abokansa ne ko aminansa, suka yi laifi wato kenan su doka ba za ta shafe su ba kenan?

Tashin farashin man fetur ya sa kasashen OPEC darawa


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

OPEC ta ce farashin man fetur ya tashi ne saboda karin bukatar man a kasuwannin duniya

Farashin danyen man fetur ya yi tashin da bai taba yi ba cikin ‘yan shekarun nan a duniya, inda ya kai dala sittin a kan kowacce ganga.

Faduwar da farashin man ya yi a baya ya haddasa koma-bayan tattalin arzikin kasashe masu arzikinsa irinsu Najeriya, lamarin da ya jefa al’ummarsu cikin kunci.

Babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya wato OPEC, Alhaji Muhammadu Sanusi Barkindo, ya shaida wa BBC cewa, kasuwa na kara bunkasa a hankali, su kuma suna kara damara da tattaunawa a tsakanin kasashen da ba sa karkashin kungiyar kamar Rasha a kan lallai su tabbata cewa an tsaya a kan yarjejeniyar da aka cimma.

Sannan ya ce abinda ya sa farashin man fetur din ya tashi shi ne yadda aka yi amfani da yarjejeniyar da aka cimma da kasashen kungiyar da ma wadanda ba sa cikinta na rage samar da ganga miliyan daya da dubu dari takwas, sannan kuma a watanni shida da suka wuce an samu karuwar bukatar man a kasuwannin duniya.

Alhaji Muhammadu Sanusi Barkindo, ya ce wani karin dalilin kuma shi ne, shugabannin kasashen kungiyar OPEC din da na Rasha, na kara gargadin cewa lallai a guji sake faruwar abinda ya faru a shekarun da suka wuce.

Harry Kane ba zai buga wasan Man Utd ba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kane ya ji rauni ne a wasansu da Liverpool ranar Lahadi a filin wasa na Wembley

Dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Manchester United ba ranar Asabar saboda raunin da ya ji a kafarsa.

Kane ya ci kwallaye biyu lokacin da Tottenham ta lallasa Liverpool da ci 4-1 ranar Lahadi, kafin a sauya shi a minti na 88.

Dan kwallon shi ne wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar firimiyar bana, inda yake da kwallo takwas.

“Likitoci ne suka bukaci dan wasan ya huta,” in ji kocin Tottenham Mauricio Pochettino.

A wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na kungiyar, ya ce “karamin rauni dan wasan ya samu a kafarsa ta dama.”

Kane ya ci kwallaye 13 a wasanni 12 da ya buga wa Tottenham a kakar bana – kungiyarce take mataki na uku a gasar firimiyar bana.

Manchester United ce ta biyu a teburin, kuma makin su daya da Tottenham.

Nigeria: IS ta dau alhakin harin da aka kai Yobe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sojin Najeriya dai ba ta bayyana adadin wadanda suka mutu a harin ba

Kungiyar IS mai ikirarin jihadi ta dauki alhakin kai hari wani kauye a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya inda ta ce ta kashe akalla soji takwas. Ko da yake ba za a iya tantace iya mutum nawa suka mutu a harin ba.

A wata sanarwar da ta fitar ta Intanet da harshen larabci, kungiyar IS ta ce mayakanta sun far wa wani sansanin sojin Najeriya a jihar Yobe kuma sun yi awon gaba da makamai da kuma motocin soji hudu.

Rundunar sojin Najeriya dai ta tabbatar da cewa an kai harin kuma an samu mace-mace a bangarorin biyu, amman ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu ba.

A baya dai, bangaren kungiyar Boko Haram da ke da alaka da kungiyar IS ya yi ikirarin cewa yana hakon jami’an tsaron Najeriya.

Boko Haram ta shafe kusan shekara goma tana kaddamar da hare-hare a arewacin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya dai na ikirarin cewa ta kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa inda suka fi karfi a da.

Amman mayakan kungiyar suna ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake tare kai hare-hare kan jami’a tsaro da fararen hula, musamman ma a arewa maso gabashin Najeriyar.

Yankin Catalonia ya balle daga Spain


Majalisar dokokin yankin Catalonia na Spaniya ta kada kuri’ar ballewa daga kasar baki daya domin kafa kasarsu.

Matakin ya samu goyon bayan ‘yan majalisa 70 daga cikin 80 yayin da ‘yan adawa suka kauracewa zaman.

Tun da farko Fira Ministan Spaniya Mariano Rajoy ya shaida wa ‘yan majalisar dattawa cewa ana bukatar kawar da kwarya-kwaryar ‘yancin da yankin yake da shi domin dawo da “doka, da demokuradiyya da kuma zaman lafiya” a Catalonia.

Wannan rikici ya barke ne lokacin da jama’ar yankin suka kada kuri’a mai cike da rudani a farkon watan nan, inda suka amince da kafa kasarsu mai cin gashin kanta.

Turawa za su sha dauri kan tura wani baki cikin akwatin gawa


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Willem Oosthuizen da Theo Martins Jackson sun ce su ba su yi wani laifi ba

An yanke wa wasu Turawa biyu hukuncin daurin fiye da shekara 10 a gidan yari a Afirka Ta Kudu, sakamakon tursasa wani bakin fata da suka yi ya shiga cikin akwatin gawa.

An kama Theo Martins Jackson da Willem Oosthuizen da laifin ne a watan Agusta bisa tuhmar laifin kisan kai da satar mutum.

Sun zargi mutumin mai suna Victor Mlotshwa da kutsawa cikin gonarsu ba tare da izini ba, suka lakada masa duka, suka kuma tursasa masa shiga akwatin gawa tare da barazanar kona shi da ransa.

Mista Oosthuizen mai shekara 29 zai yi zaman gidan kaso na shekara 11 shi kuma Mista Jacksonmai shekara 30 zai yi zaman kasaon shekara 14.

Daga cikin dalilan da suka sa aka yanke musu hukunci har da cin zarafin shaida kwaya daya tal inda suka yi kokarin hana shi fadar gaskiyar abun da ya faru.

Wakiliyar BBC da ta halarci zaman kotun Pumza Fihlani, ta ce wannan lamari dai ya jawo tashin-tashina a Afirka Ta Kudu, musamman kan batun nuna wariyar fata a wasu yankunan manoma.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon yadda aka sa shi a akwatin gawa

Mista Mlotshwa dai ya kai rahoton abin da ya faru ne kawai bayan da wani bidiyo na yadda aka ci zarafin nasa ya bayyana a shafin Youtube bayan faruwar lamarin da watanni.

A wata takardar rantsuwa da suka rubutawa kotu, Jackson da Oosthuizen sun ce ba su yi hakan da niyyar zaluntar Mista Mlotshwa ba a lokacin faruwar lamarin a watan Agustar 2016, kawai dai sun so su ‘koya masa hankali ne.’

Mista Mlotshwa dai ya musanta cewa ya yi musu kutse ne a gonarsu, ya ce ya bi hanya mafi kusa ne da za ta kai shi wajen wasu shaguna da mahaifiyarsa ta aike shi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mista Mlotshwa ya ce ya bi hanya mafi kusa ne da za ta kai shi wajen wasu shaguna da mahaifiyarsa ta aike shi ba gonarsu ya shiga ba

Mai shari’ar da ta yanke hukuncin Sheila Mphahlele, ta ce ta yi hakan ne saboda yadda hujjoji suka nuna cewa wadannan Turawa sun yi hakan ne don nuna wariyar launin fata.

Kuma mai shari’ar ta ce za su karasa dukkan sauran rayuwarsu a Afirka Ta Kudu.

Ta ce ta yi hakan ne don aike sakon gargadi ga dukkan mutanen da har yanzu suke nuna wariyar launin fata.

Sai dai Turawan sun ce za su daukaka kara.

Shugaba Buhari ya nemi gafarar ‘yan majalisa kan hana su ganinsa


Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Daga bisani Saraki da Dogara sun hakura sun shiga fadar bayan an ba su hakuri

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi afuwar shugabannin majalisar dokokin Najeriya bisa hana su shiga fadarsa da jami’an tsaro suka yi a ranar Alhamis da daddare.

Jami’an tsaron fadar sun hana shugabannin majalisar shiga ne bisa dalilin cewa ba a ba su izinin barin su ba, suka kuma bukaci sai sun sauko daga motar safa da ta kai su don a bincike su daya bayan daya.

Wannan dalili ne ya sa shugabannin majalisar suka yi zuciya suka koma ba tare da shiga fadar ba.

Daga bisani bayan tafiyar shugabannin majalisar ne sai Shugaba Buhari ya tura shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa Ita Enang, domin su ba su hakuri su kuma shigar da su fadar.

Sai dai wasu daga cikin shugabannin majalisar sun yi zuciya suka ki komawa, sai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ne kawai suka koma.

BBC ta yi kokarin tuntubar bangaren fadar shugaban kasar amma ba ta samu jin ta bakinsu ba kawo yanzu, sai dai wata kwakkwarar majiya daga majalisar dokokin ta tabbatar mana faruwar lamarin, ta kuma ce tuni Shugaba Buharin ya bai wa ‘yan majalisar hakuri kan abun da ya farun.

Tun farko dai Shugaba Buharin ne ya rubuta wasikar gayyatar shugabannin majalisar zuwa fadarsa don tattaunawa ta musamman da cin abincin dare.

Shugabannin majalisar da suka kai su 20 sun hada da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai da mataimakansu da shugabannin masu rinjaye da na marasa rinjaye na majalisun biyu.

Wasu rahotanni sun ce bayan komawar shugabannin majalisar Shugaba Buharin ya kara ba su hakuri, ya kuma tabbatar musu cewa za a ba su takardar izinin shiga fadar a ko wanne lokaci suka so ba tare da shamaki ba.

A yanzu dai Shugaba Buharin ya sanya ranar Talata a matsayin sabuwar ranar da dukkan shugabannin majalisar za su koma fadar tasa don ganawa ta musamman din.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Presidency

Image caption

Bayan kammala cin abincin ne shugabannin suka dan taba raha

‘Yan majalisa sun mayar da cin hancin $8,000


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Shugaban Yuganda Yoweri Museveni ya shafe shekara 31 yana mulkin Yuganda

‘Yan majalisar kasar Uganda sun mayar da dala 8,000 kimanin fam 6,000 da aka ba kowannensu domin tsawaita mulkin shugaba Yoweri Museveni.

Shugaba Museveni ya shafe shekara 31 yana mulkin Uganda.

‘Yan majalisun su takwas sun mayar da fam 8,000 da kak bai wa kowannensu domin su tuntubi al’umominsu game da wani kuduri mai cike da takardama na tsawaita wa’adin shugaban kasa.

‘Yan adawa a kasar sun soki wannan lamarin, suna cewa “cin hanci da rashawa” ne, saboda ‘yan majalisar sun riga sun ziyarci mazabunsu.

Ana kallon wannan a matsayin wani yunkuri na zawarcin ‘yan majalisar domin su cire wani sashe na dokar kasar da ya hana duk wanda shekarunsa suka wuce 75 daga takarar shugabancin kasar.

‘Yan adawar na ganin jam’iyyar shugaban kasa Museveni na neman tsawaita mulinsa ne a fakaice. Shekarun shugaba Yoweri Museveni na da shekara 73 da haihuwa ne a halin yanzu.

Za a gudanar da zaben shugaban kasar Yugandan ne dai a shekarar 2021, kuma wa’adin shugabancin kasar ta Uganda shekara 6 ne.

Jam’an majalisar sun bayyana cewa an ware dala miliyan 3.5 domin ‘yan majalisar kasar su tuntubi jama’arsu dangane da wannan kudurin dokar.

Ko wane dan majalisa zai karbi dala 8,000 domin aiwatar da wannan aikin cikin mako biyu masu zuwa.

Matsalar fyade a Ghana – BBC Hausa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana ci gaba da nuna damuwa a kan yadda matsalar fyade ta yi kamari a Afrika

Wata yarinya mai shekara 4 na kwance a asibiti a Ghana cikin halin rai kwa-kwai, mutu kwa-kwai, bayan cin zarafinta da aka yi ta hanyar Fyade.

Mahaifiyar yarinyar ta ce sun shaida wa Mai-unguwar yankin sunan wanda suke zargi da wannan ta’asa.

Amma abin mamaki sai ya ce babu abin da za a iya yi wa mutumin, saboda abin bautar su, ya ayyana mutumin a matsayin mai gaskiya.

Wannan lamari dai ya janwo muhawara a shafukan sada zumunta da gidajen Rediyon kasar.

Matsalar fyade dai tayi kamari a wasu kasashen Afrika, ciki har da Nigeria, inda ake samun batutuwan da suka shafi yi wa yara mata kanana fyade.

Matata da ‘ya’yana 5 na hannun Boko Haram


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Editan BBC na Abuja, Naziru Mikailu ya yi kicibis da wani mutumin garin Bama dake jihar Borno, wanda yanzu yake Abuja, kuma wanda mayakan Boko Haram suka sace matarsa da ‘ya’yansa biyar, a cikin shekaru 4 da suka gabata.

Ya dai nemi sakaya sunansa saboda matsalar tsaro.

Ya fara da bayyana makasudin dalilin barin gidansa da garinsa a lokacin da rikicin Boko Haram ya isa garin na Bama:

“A da muna cikin garin Bama ne. To, da abin ya dau wuta, sai muka gudun hijira zuwa Kamaru ni da iyalina biyu da ‘ya’yana goma”.

Ya ce daga baya ya dawo gida daga Kamaru, kuma ya aika wa iyalan nasa kudi domin su dawo.

“Daya ta sami fitowa daga Kamarun zuwa Bama, amma dayar an riketa da ‘ya’yanta biyar”, inji mutumin.

Yace: “zai kai shekara uku zuwa hudu da faruwar wannan abun. Sam ban sake jin labarinsu ba, kuma ban san inda suke ba”.

Ya ce saboda matsalar ta yaki da Boko Haram, ya kasa komawa ya nemo iyalin nasa a wancan lokacin.

“Ina da niyyar in tafi in duba su, amma ba halin tafiya. Ba hanyam babu halin tafiya”.

“Ni da kaina ina kwana biyu ko uku bana iya barci saboda zulumi. kuma idan na tuna da su ma ba na iya cin abinci ma”.

Ya ce har yanzu bai sanar da sauran ‘ya’yansa halin da ‘yan uwan nasu dake hannun mayakan Boko Haram gaskiyar al’amarin ba:

“Ina gaya musu ‘yan uwansu basu sami tahowa ba, suna can a Kamaru. Idan na sami kudi zan aika musu domin su dawo”.

Ya sanar da BBC cewa duk da halin da yake ciki, bai sanar da hukumomi cewa mayakan Boko Haram na rike da matrsa daya tare da ‘ya’ya biyar ba, amma yana da karfin zuciyar cewa iyalinsa suna nan raye, kuma wata rana zasu hadu.

Mata 100: Me ya sa ba a biyan ‘yan wasa mata sosai kamar maza?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A jerin masu wasan motsa jiki da aka fi biya, mace daya ce take cikinsu – wato shahararriyar ‘yar kwallan tennis Serena Williams.

Serena tana mataki na 51 kuma kudin da take samu ya gaza na Cristiano Ronaldo, dan wasan da ya fi samun kudi a duniya a cewar mujallar Forbes.

Tawagar mata ‘yan kwallon kafa ta kasar Amurka ta samu kyautar dala miliyan biyu bayan ta ci gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2015.

Har ila yau, gasar kwallon kafa ta duniya ta maza kuma ta samar wa wadanda suka lashe kyautar dala miliyan 35 a shekarar 2014.

Wadannan ‘yan misalai ne kawai da ke nuna gagarumin gibin biya a duniyar wasanni da ya dade da zama al’ada.

Sai dai kuma, bincike na baya-bayan nan, ya nuna cewa bambanci wajen samun kudin shiga tsakanin ‘yan wasa mata da ‘yan wasa maza ya ragu sosai a ‘yan shekaraun da suka wuce.

Hakkin mallakar hoto
Harry How/GETTY IMAGES

Image caption

Kwallon kafar mata ta fi farinjini a Amurka a kan ta maza – duk da haka tawagar kwallon mata ta kasar ba ta samun kudin da ya kai ta tawagar maza

Jumullar kashi 83 cikin 100 na wasanni a duniya yanzu suna biyan maza da mata kudi bai daya, in ji wani bincike kan fannoni 68 da sashen wasanni na BBC ya wallafa a watan Yunin da ya gabata.

Kudin da ake biyan mata yana karuwa ne tun shekara uku da suka wuce, kuma 35 daga cikin wasanni 44 da suka bayar da kyautar kudi suna biya bai daya ne.

Wannan ya yi kama da labari mai kyau, musammann idan aka kwatanata da shekarun da suka gabata – a shekarar 2014 kashi 70 cikin 100 na wasanni ne kawai suka samu suka cike gibin kudin biya,

Kuma a shekarar 1973 babu wani wasan da ya biya maza da mata bai daya.

“Mata sun fi fitowa a wasanni yanzu fiye da ko wane lokaci a tarihi,” in ji wata sanar daga Hukumar Kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya.

Duk da haka sauyi na tafiyar hawainiya ta yadda za a dauki dogon lokaci kafin a kai ga samun biya bai daya a mataki na sama, in ji masana.

“Muna samun ci gaba, amman yana faruwa ne kamar tafiyar hawainiya,” in ji Fiona Hathorn, darakatar kungiyar Women on Boards da ke fafatukar ganin mata suna shugabanci.

“Har yanzu duniyar wasanni ta kasance cike da maza a kan mata, kuma bambanci tsakanin maza da mata a wasu wasanni na da tayar da hankali sosai.”

Hakkin mallakar hoto
Shaun Botterill/ GETTY IMAGES

Image caption

An bar mata masu buga kwallon Kriket baya idan ana maganar biya bai daya

Kriket da Golf da kuma kwallon kafa suna cikin wadanda suka fi sabawa biya bai daya tare da snuka da sauransu.

Kasuwancin wasanni na duniya – da ya kai dala biliyan 145.3 , in ji kiyasin PwC- bai kai ga samar da daidaito tsakanin jinsin maza da mata ba.

“Ba zan iya tunanin wani fannin da yake da irin wannan gibin ba. Ya danganci irin halin da ake ciki a kasa da kuma wasa, na miji ka iya zaman biloniya kuma mace (wadda take irin wasan) ba za ta iya samun albashi mafi karanci ba,” in ji Beatrice Frey, manajar hadin gwiwa na wasanni a hukumar da ke kula da mata ta Majalisa Dinkin Duniya.

Wadanda suka fi laifi

Bambance-bambance suna fitowa karara a wane mataki na harkar kwallon kafa mai biloyoyin kudade.

Hakkin mallakar hoto
David Ramos/GETTY IMAGES

Image caption

Real Madrid ta samu kyautar dala miliyan 18 domin ta ci kofin gasar zakaarun Turai a kakar bara, yayin da wadanda suka lashe gasar ta mata, Lyon, suka samu kasa da dala 300,000

Wani bincike na kwanan nan da kungiyar Women on Boards ta fitar ya nuna cewa maza masu taka leda sukan samun abin da ya rubanya na mata sau hudu duk da cewa matan sun fi su kokari.

Gibin zai kara girma idan aka yi la’akari da jumullar kudin da aka biya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ce take yanke iya kyautar da za a bayar a dukkan gasa biyun.

Ita ce ta ba da dala miliyan 15 ga wadanda suka lashe gasar kwallon kafa ta duniya ta mata, kuma ta ba da dala miliyana 576 ga wadanda suka lashe gasar kwallon kafa ta maza.

Kuma a daidai lokacin da kyaftin din Ingila, Wayne Rooney, yake samun kudi dala 400,000 a ko wane mako, albashin takwararsa mace, Steph Houghton, bai taka kara ya karya ba idan aka yi la’akari da nashi – kimanin dala 1,600 a ko wane mako, in ji kafar Ladbrokes Sports.

Ana iya ganin irin wadannan gibin biya a wasu wasannin.

A wasan Golf, maza a gasar US Open suna neman samun kyuatar kusan dala miliyan $1.5 ne, kudin da ya rubanya kyautar da mata za su samu a gasar.

Ka dubi labarin Lydia Ko, daga kasar New Zealand, wadda ta zama mai karamar shekaru irin nata cikin ko wane jinsi da ta fara zama cikakkiyar ‘yar wasan Golf a shekarar 2015.

A wanna shekarar ta samu kudin da ya gaza na dan wasan golf da ke matsayi na 25 a jerin sunayen gwanaye cikin maza na gasar PGA Tour, kamar yadda Newsweek ta bayyana.

Har ila yau, a gasar Kriket wata tawagar maza da ta lashe gasar cin kofin duniya za ta iya rubanya abin da mata za su samu fiye da sau bakwai.

Kuma ana maimaita gibin albashin a gasar kwallon kwando ta maza da ta mata da ta fi daraja duniya – NBA da WNBA.

“‘Yar wasan da ta fi samun kudi a gasar kwallon kwando ta WNBA tana samun kashi daya cikin biyar na abin da dan wasan kwallon kwandon da yake karbar kudi mafi karanci a gasar maza NBA,” in ji mujallar NBA .

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

LeBron James ne dan wasa na biyu da ya fi arziki a tsakanin ‘yan wasan motsa jiki na duniya in ji Forbes

Kulob din yara

Domin a samu daidaito, masana sun ce, bayar da kyaututtuka ba tare da la’akari da jinsi ba bai zai isa ba wajen kawar da matsalar sai an hada da daukar nauyi da talla da kuma sharuddan yarjejeniya.

Alal misali a fagen tennis, muhimman gasar da ake yi a ko wace shekara sun kaddamar da biya bai daya ga mata da maza tun shekarar 2007, duk da haka fitattun ‘yan wasa maza sun fi mata samun kudi a ko wace shekara domin yarjejeniyoyi na daukar nauyi domin talla.

Shi ya sa Serena Williams ta kasance ita kadai a jerin sunayen ‘yan wasa 100 da suka fi kudi ta mujallar Forbes.

“‘Jerin ‘yan wasa 100 da ke kan gaba ya fi zama na maza fiye da yadda aka saba”, in ji wakilin mujallar Forbes kan wasanni Kurt Badenhausen a lokacin da aka fitar jerin sunayena watan Yuni.

“Maria Sharapova ta kasa shiga cikin jerin sunayen bayan an rage kudaden yarjejeniyoyin tallan da take da su.”

Hakkin mallakar hoto
Lintao Zhang/GETTY IMAGES

Image caption

An soke kwantiragin tallan ‘yar Rasha Maria Sharapova bayan an dakatar da ita na tsawon wata 15 sakamakon faduwar da ta yi a gwajin kwaya

Ronaldo ya samu dala miliyan 58 na alabashi da kyaututa, amman ya kara da dala miliyan 35m daga masu talla da masu daukar nauyi domin talla da kuma kudaden fitowa.

Ga kuma dan wasan golf Tigers Woods da kuma tauraron wasan tsere Usain Bolt, daukar nauyi domin talla ya kai kashi 90 cikin 100 na kudaden shigansu.

“Nuna wariyar jinsi ya zama ruwan dare gama duniya a fagen wasanni,” in ji Frey.

“A matakin farko zai iya kasancewa domin mata ba sa iya wasannin da a al’adance ba na mata ba ne, lamarin da yake janyo wariya a tun suna kanana wanda zai bi su har zuwa lokacin da suka zama matasa zuwa gwanayen wasa.”

Sannan, ta ce, yana nufin za a samu rashin daidaito a damarmaki a daukar nauyi da talla, har ya kai ga yawancin ‘yan wasa mata a fadin duniya ba sa iya ciyar da kansu daga sana’o’insu na wasanni.

Hakkin mallakar hoto
Thos Robinson/GETTY IMAGES

Image caption

Taurariyar kwallon kafa ta Amurka mai murabus Abby Wambach ta buga wani littafin tarihinta kuma tana samun gayyata na halartan tarurruka – amman mata ‘yan wasa da yawa ba sa samun irin wadannan damarmakin bayan sun yi murabus

Kuma yanayin na ta ci gaba.

“Ga mata ‘yan wasa da suka yi murabus lamarin na tare da matsaloli. Bawai ba su samu kudi mai yawa ba ne kawai,ta yiwu ba su fansho ko gida ko kuma tsaro ba,” in ji Hathorn.

“Kuma wannan wata matsala ce ga burin ‘yan mata: me ya sa za su so zama ‘yan wasa in har haka makomarsu za ta kasance?”

Yadda za a gane gibin

Za a iya ga ni tushen wannan gibin shi ne daga asalin wasannin zamani da kansu.

Al’ummomi daban-daban suna ganin atisaye a matsayin wani aiki da ke da alaka da namiji mai karfi, wanda yake da bambanci da mace mai rauni.

Hakkin mallakar hoto
Hulton Archive

Image caption

‘Yar Birtaniya, Charlotte Cooper Sterry, ta zama mace ta farko da fara zama zakarar wasan Olympics a shekarar 1900

Wanda za a iya cewa baban gasar Olympics na zamani, Pierre de Coubertin, ya bayyana wasannin mata a matsayin wani abin da ba shi da dadin gani kuma yana ganin shigan mata zai sa gasar ta rasa armashinta duk da cewa an bawasu mata kadan su shiga gasar Olympics a shekarar 1900.

A wancen lokacin mata suna shiga gasar tseren mita 1,500 domin ana ganin ba su shirya wa tseren da ya fi haka tsawo ba.

Ta fannin wakilci, sai gasar Olympics da aka gudanar a birnin Landan a shekarar 2012 ne ko wace kasa ta saka akalla mace daya a cikin ‘yan wasanta na zuwa gasar.

Saboda haka za a iya alakanta gibin biya ga rashin daidaito na cikin jama’a – wanda ya fa rawar da mata suke takawa a wasanni yake kasa da na maza a kullum.

“Takarawar wata matsala ce wadda take farawa tun a shekarun da matan suke makaranta: a wanna lokacin ne yake farawa,” in ji Ruth Holdaway, shugabar kungiyar Women in Sport da ke fafutukar kare ‘yancin mata a wasanni.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kusan rabin matan sukan barin wasanni a lokacin da suka balaga, in ji wani bincike a Birtaniya

Lamarin na da alaka ne da yadda suke ganin jikinsu da yadda ake ganinsu da kuma irinwariyar da suke fuskanta, in ji Holdaway.

Alkaluma daha hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa kashi 49 cikin 100 na ‘yan mata suna barin wasanni a lokacin da suka balaga, kuma wannan yana da tasiri a kan yawan wadanda za su zama kwararrun ‘yan wasa daga cikinsu a gaba

Kunna talabijin

An yarda cewa yawan gibin biya na jinsi yana da nasaba da kasuwancin da ake yi da wasannin, inda sayan ‘yancin watsa wasa yake taka muhimmiyar rawa.

Wani binciken da jami’ar cibiyar bincike kan ‘yan mata da matan da ke wasanni ta Tucker Centre da ke jami’ar Minnesota ta gano cewa a shekara 2014 kashi hudu daga cikin 100 ne gurbin da wasannin mata suka samu a kafafan watsa labarai duk da cewa kashi 40 cikin 100 na masu wasan mata ne.

Hakkin mallakar hoto
Doug Pensinger/GETTY IMAGES

Image caption

Yawancin muhimman ‘yancin wasa na taimakawa wajen biyan ‘yan wasa

Kuma cikin dan lokacin da suka samu akwai yiwuwar cewa za a nuna wariyar jinsi a wajen watsa wasannin mata, ta hanyar nuna ‘yan wasa a wajen fili da kuma cikin kayan gida inda ake mayar da hankali kan yadda suke da kyau a jiki maimakon iya wasansu”, in ji daraktan Tucker Centre, Mary Jo Kane.

Sabaoda haka, mutane da yawa za su ce matana ba sa samun kudi kaman maza saboda haka kasuwar take so saboda wasanni mata ba su da farin jini irin na maza, kuma ssaboda haka wasannin suna samun kudin shiga wanada bai kai na maza ba.

Mene ne shirin Mata 100?

Shirin Mata 100 yana bayyana sunayen mata 100 wadanda suka yi zarra da tasiri a fadin duniya kowace shekara.

A shekarar 2017, muna bukatarsu da su magance wadansu manyan batuwa guda hudu da suke jawo wa mata cikas a yanzu – cimma wani babban mataki da batun ilimi da batun cin zarafi da kuma nuna wariya musamman a fannin wasanni.

Da taimakonmu, za su lalubo hanyoyin magance matsalolin kuma muna so su ba da gudunmuwa da shawarwari.

Za a iya tuntubar mu a shafukanmu na Facebook da Instagram da Twitter da kuma ta hanyar amfani da maudu’in #100Mata


Wadansu daga cikin mutanen da ke cikin jerin Mata 100 za su yi aiki ne daga birane hudu a tsawon mako hudu na watan Oktoban bana, inda za su samar da hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin.

Sauran za su ba da gudunmuwarsu daga sauran sassan duniya.

Za a bayyana ragowar sunayen mata 40, yayin da mata ke ci gaba da shiga shirin da kuma ba da gudunmuwarsu da kwarewarsu.

Burundi ta fice daga kotun ICC


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yan Majalisar dokokin Burundi sun kada kuriar ficewa daga Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya

Burundi ta kasance kasar ta farko a nahiyar Afirka da ta fice daga Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Tun a bara ne dai kasar ta sanar da Majalisar dinkin duniya cewa za ta fice daga kotun.

Ha kuma wannan lamari ya tabbata a yanzu.

A yanzu dai ana yi wa wannan batu kallon zakaran gwajin dafi ga yunkurin samar da adalci ko shari’a a tsakanin kasa da kasa.

Batun dai ya ba mutane da dama mamaki.

kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun sha nuna adawarsu ga yunkurin wasu kasashen Afirka na ficewa daga kotun.

Kasashen dai na cewa kotun ba ta yi musu adalci, domin kuwa ba ta tuhumar sauran shugabannin kasashen duniya.

Sai dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce matakin da Burundi ta dauka,wani yunkuri ne,na hana dama ga wadanda aka ci zarafinsu a rikicin siyasar da ya faru a 2015, inda aka kashe mutane da dama.

Buhari ya kammala tsara kasafin kudin 2018


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A bana Najeriya ta yi kasafin Naira tiriliyon 7.44

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2018 a wajen taron mako-mako na majalisar da aka yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasa a Abuja.

Majalisar zartarwar ta ce nan ba da jimawa ba ne za a gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokoki ta kasar.

Ministan Ayyuka, Wutar Lantarki da Gidaje Babatunde Fashola, ya ce aikin shugaban kasar ne ya mika wa majalisar kasafin kudi kuma ya yi bayanin kan yadda za a kashe kudin.

Har ila yau ministan ya ce suna tattaunawa da bangaren majalisa don tsayar da ranar da shugaban kasar zai je ya mika mata daftarin kasafin kudin.

“A baya muna mika wa majalisar daftarin kasafin kudin ne a watan Disamba, amma a bana za mu ba su a wannan watan na Oktoba ne, akwai bambanci kan yadda aka saba gani,” in ji shi.

Ministar Kudi Kemi Adeosun, ta ce an kashe naira biliyan 450 wadanda za a gudanar da ayyukan raya kasa da su a kasafin kudin shekarar 2017.

Bugu da kari, majalisar zartarwar ta karbi bukatar samar da wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki a jihar Edo a zaman da ta yi na ranar Alhamis.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Leicester ta nada Puel a matsayin kocinta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Puel ya horar da Lyon da Monaco da Southampton

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta sanar da na Claude Puel a matsayin sabon kocinta, ya kuma sa hannu kan yarjejeniyar shekara uku.

Kocin mai shekara 54, zai fara jan ragamar kungiyar a wasan da za ta fafata da Everton a gasar Premier wasan mako na 10 a filin wasa na King Power a ranar Lahadi.

Puel tsohon kocin Monaco da Lyon da Southampton zai yi aiki da Michael Appleton a matsayin mataimakinsa.

A ranar Juma’a ne Leicester za ta gabatar da Puel wanda zai maye gurbin Craig Shakespeare wanda ta kora a makon jiya.

Leicester City tana ta 14 a kan teburin Premier da maki tara, bayan wasa tara da ta fafata a gasar.

Arsenal za ta auna kwazon Arsene Wenger


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

masu hannun jari a Arsenal sun tafa wa Wenger bayan da ya kammala jawabi

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce shugabannin kungiyar za su auna kokarinsa a matsayin koci a karshen kakar bana.

A farkon kakar bana Wenger ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu domin ci gaba da jan ragamar kungiyar, zai kuma yi kaka 21 a Gunners kenan.

Wenger ya ce zai so jin abinda shugabannin Arsenal za su ce kan aikin da yake gudanarwa a Emirates.

Arsenal ta kammala a mataki na biyar a gasar Premier da ta wuce, kuma karon farko kenan da kungiyar ta kasa shiga gasar cin kofin Zakarun Turai tun bayan shekara 20 a jere tana zuwa.

Arsenal tana matsayi na biyar a kan teburin Premier bana da maki 16 bayan wasa tara da ta buga a gasar.

Za a kona gawar Sarkin Thailand shekara guda bayan rasuwarsa


Hakkin mallakar hoto
AFP

Dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Bangkok don martaba gawar Sarkin Bhumibol Adulyade.

Sarkin ya mutu ne a watan Oktobar shekarar 2016, yana da shekara 88.

An fara bukuwan binne marigayin ne a ranar Laraba kamar yadda tanadin addinin Buddha ya shinfida.

Galibin gidajen da ke birnin an lullube su da kyallaye masu ruwan dorawa, yayin da jama’a suka sanya bakaken tufafi.

A ranar Alhamis ne za a kona gawar sarkin, bayan dansa ya cinnna mata wuta a fadarsa.

Ana hasashen cewa taron jana’izar ya samu halartar kimanin mutum 250,000.

Shekara daya ke nan yanzu da aka fara ayyana zaman makoki a kasar tun bayan rasuwarsa a ranar 13 ga watan Oktoban bara.

Kenya: An fara zaben cikin yanayi na tsatssaurar matakan tsaro


An fara zabe a Kenya cikin wani yanayi na tsattsaurar matakan tsaro a zaben shugaban kasa da ake sakewa, wanda madugun ‘yan adawa ya kaurace wa.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Magoya bayan Shugaba Uhuru Kenyatta sun yi murna bayan yunkurin jinkirta zaben ya ci tura.

‘Yan sanda sun yi arangama da magoya bayan ‘yan adawa inda wasu daga cikinsu suke kokarin hana mutane zuwa rumfunan zabe.

An ayyana Shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe wani zaben da aka yi a watan Agusta, amman ana sake zaben ne domin “magudi”.

Wakilin BBC, Alastair Leithead dake Nairobi ya ce da alama fitowar mutane domin kada kuri’a bai kai na zaben da aka yi a karon farko ba.

Mista Kenyatta yana neman wa’adi na biyu. Jagoran ‘yan Adawa Raila Odinga ya janye daga takarar.

An fara zaben ne ranar Alhamis da misalin karfe 06:00 (karfe kenan a agogon 03:00 GMT) inda aka tura dubban ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin su kare maus zabe da rumfunana zabe.

Masu sa ido na kasa da kasa sun rage yawonsu saboda dalilan tsaro.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce ‘yan sanda yi harbi cikin iska domin tarwatse magoya bayan ‘yan adawa a birnin Kisumu da ke yammacin kasar da kuma unguwar Kibera dake birnin Nairobi.

An kuma yi mafani da hayaki mai sa hawaye.

Wani jami’in zabe a Kisumu- garin jagoran ‘yan adawa Raila Odinga – ya shaida wa BBC cewa biyu daga cikin jami’an rumfar zaben ne suka fito.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘yan sanda sun yi kokarin tarwatsa magoya bayan Odinga a unguwar marasa galihu na Kibera dake birnin Nairobi

Wani mai zabe a unguwar marasa galihu ta Mathare dake Nairobi, kuma dan tasi David Njeru, mai shekara 26, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa : “Nauyin kada kuri’a ya rata a wuyata ne. A wancan lokacin layin masu zaben yayi tsawon gaske kuma na yijiran sa’o’i shida domin yi zabe, amman yanzu mutane ba su da yawa.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

‘Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga hayaki mai sa hawaye a birnin Kisumu

An kashe kimanin mutum 70 a tashe-tashen hankula tun lokacin da aka ayyana Mista Kenyatta a matsayin wanda ya lashen zaben watan Agusta.

Mista Odinga ya so a jinkirta zaben, amman yunkurin ya ci tura bayan alkalai biyu suka halarci zaman kotun kolin kasar ranar Laraba cikin alkalai bakwai.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Raila Odinga ya shaida wa magoya bayansa cewa: “Za mu ci yakin”

Ba bu wani aibu a auren wuri


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Auren wuri ba shi da aibu a cewar wasu iyaye

Ya yinda a jiya ne aka kamala taron da ake akan yadda zaa kawo karshen auren wuri a yammacin Afrika ta tsakiyar Afrika wasu iyaye a Nigeria sun ce ba bu wani aibu tattare da auren wuri.

Sun ce auren wuri nada alfanu sosai saboda yana hana matasa aikata dabiar da bata dace ba.

Malam Muhammad Sadisu Rajab mahaifin yayata mata ne a Nigeria kuma acewarsa barin auren wuri na kawo matsaloli da suka fi yoyon fitsari illa.

Taron da aka yi a Dakar babban birnin kasar Senegal ya samu halatar shugabannin kungiyoyin agaji, da jami’an gwamnati da shugabannin addinai da na al’umma da kuma hukumomin majalisar dinkin duniya .

Mahalatan taron na son su hana aurar da yaran mata kafin su kai shekaru 18

Yadda wani nau’in abinci ya jawo annobar mummunar cuta a Amurka


Daga Veronique Greenwood

28 ga Yunin 2017

Cikin Disambar 2015 aka rika samun tsilli-sillin matsaloli a sassan Amurka. Ba su da yawa a lokacin, amma suna faruwa akai-akai, inda wadanda suka jikkata alamun cutarsu ke nuni da amai da zawayi mai jini, kuma gwajin da aka yi musu ya tabbatar suna dauke da kwayar cutar E. coli.

Kuma wadannan majinyata akwai su kusan ko’ina, inda aka samu aukuwar cututttuka a jihohi 20 daidai lokacin da cibiyoyin shawo kan cututtuka suka bayyana barkewar annobar, daidai lokacin da aka kai mutum 10 asibiti.

An fahimci cewa kwayar cutar E.coli na damfare ne a abin da suka ci, kuma cibiyoyin tarairayar cututtukan na CDC, da ke aiki tare da kananan hukumomin kula da lafiya da na jihohi, suka sanya masu bincike su shawo kan al’amuran.

Yayin da mutane da yawa ba su san cewa guba kadan a cikin abinci na iya yin mummunar illa, kuma ba a al’amari da yake a kebe ba. A mafi munin lamuran har kisa take yi.

Don gano tushen asalin yaduwar cutar sai aka bi kadin gubar baibaye da mahauta ko kazantar da ta baibaye tsirrai, ta yadda in an bi misali sai a fahimci cewa ita ce kariyarmu nan gaba.

Labarin barkewar annobar cutar E.cooli ya samu asali ne a hunturun 2015 wadda ta bude kafar barazana ga rayuka; akwakun dakin girkinka, domin aikin dubagari ya ta’allaka ne wajen tabbatar da kariyar lafiyar al’ummma, al’amarin da ke farawa daga halartar wurin da matsala ta auku nan take, tare yin tambayoyi kan lamarin.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Masu bincike su kan yi kokarin shawo kan annobar amma ba abinci ba, amma a wani nau’in kwadago da aka saka a akwakun gilashi da ke gida

Ko mene majinyata suka ci har suka kamu da rashin lafiya? Ko za su iya tuna abin da suka sawo daga shagon sayar da kayan masarufi a wannan makon da suka kamu rashin lafiya?

Ko sun yi matukar karakaina a shaguna sayar da kayayyaki da amfani da katin sayayya, masu bincike za su gano shagon da suka yi sayayya?

A kan ko wanne majiyaci, jami’in duba garin lafiya kan shafe mintuna 30 zuwa 40 don cike takardun tambayoyi, kamar yadda Ian Williams, shugaban reshen kawo daukin gaugawa lokacin barkewar annoba da shawo kanta na CDC ya bayyana.

Manufar dai a gano nau’ukan abincin da ke da alaka da marasa lafiyar.

A wasu lokutan sukan ci gyada da makwalashen burodi mai kakide. Ko daukacinsu sun ci kwadon ganyen salat. Saqi dai a irin wannan yanayin, cewa ya yi, “yadda managarcin tsarin bin kadin al’amaurta ta hanyar cike takardun tambayoyi bai haifar da komai ba.”

Sannan akwai wasu matsalolin da ke tattare da barkewar annobar. Kimanin kashi 80 cikin 100 na marasa lafiyar mata ne.

Cigbiyar shawo kan cututtuka ta CDC ta tattara bayanan kwayoyin halittar majiyatan da suka kamu da cutar E. coli, wani kyakkyawan tsarin bin kadin al’amura da suka fito da shi, tattare da tattara bayanan kwayoyin halittar dangwala yatsu da suka kasance iri guda, ko suka kusa yin kama da dama.

Wannan na nufin cewa matsala guda ce ta haifar da daukacin cututtukan. Amma ko mene ne? A dalilin haka cututtukan suka yi ta faruwa. “Mun rika samun uku, hudu ko biyar na wadanda suka kamu da cutar daga mako zuwa mako, mako bnayan mako,” in ji Williams.

Wannan bakon al’amari ne. Suna ta yawan bazuwa cikin kankanen lokaci, tamkar daukacin abin da amrasa lafiyar suka ci na haifar da matsala da ta ki ci, ta ki cinye tsawon lokaci, ko kuma sun yi ta ci akai-akai.

Tashin hankalin shi ne barkewar annobar asalinta ba daga abinci ba ne, amma an ganota a jikin kwado.

Masu binciken suna ganin masu fama da cututtukan a akwatin talabijin din na’urarsu lokacin da asibiti ko dakunan bincike suka tattara bayanai, inda aka yi gwajin burrbusshin cututttukan majiyatan kan kwayar cutar backteria.

Sannan aka dorata a shafukan sadarwar dakin bincikeen da ake kira PulseNet PulseNet nan ne inda cibiyar shawo kan cututtuka ta CDC take gane cewa an samu barkewar annoba, kuma ta sanar da su cewa annonbar na ci gaba da yaduwa. Sai dai har yanzu abin da ya haifar da ita na da rikitarwa (ko ba a gano shi ba).

Sai dai a irin wannan hali masu bincike sai sun yi amfani da basira ta musamman. Alal misali, lokacin da aka samu barkewar annobar cutar gubar salmonella (ta zazzabin typhod) shekara shida da ta wuce ta fi addabar kananan yara.

Kasancewar takardar tambayoyi ba ta haifar da wani sakamako mai alfanu ba, sai masu bincike suka sake sabon salo. Sai suka gano cewa mafi yawan marasa lafiyar suna da akwakwun gilashi.

Tashin hankalin shi ne barkewar annobar asalinta ba daga abinci ba ne, amma an ganota a jikin kwado; wadan kwadon Afirka, wanda marasa lafiya suka ajiye a gida don sha’awa.

Da aka ja hankali kamfani da ke kiwata dabbar sai aka gudanar da binciken da ya kawo karshen barkewar annobar.

Wannan lamari ya haifar da kyakkyawan sakamako. Alal misali fda aka samu barkewar annobar gubar salmonella shekara shida da ta wuce sai ta kasance ta fi addabar kananan yara.

Takardun tambayoyi ba su yi wani tasiri mai kyau ba, don haka masu bincike suka sake salo. Daga nan suka gano cewa mafi yawan majiyatan suna da akwakun gilashi (na saka halittun ruwa).

Abin damuwa game da annobar ba a ganota a cikijn abinci ba, amma sai a jikin kwado; nau’in wadan Afirka, wanda marasa lafiyar suka ajiye a gidajensu ddonb sha’awa.

Da aka ja hankalin kamfano nin da ke kiwata irin wannan dabbar sai aka yi binciken da ya kawo karshen annobar.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

An danganta daya daga mummunar annobar da garin alkama ‘fulawa a Amurka

Dangane da barkewar annobar kwayar cutar E.coli, an gano cewa dabi’un marasa lafiyar ya taimaka wajen bin kadin lamarin.

Jami’in binciken sirri kan barkewar annnoba da aka dora wa alhakin bin kadin lamarin ya fahimci cewa tashin farko mutanen da suka kamu da cutar mfi yawansu mata ne kuma suna yawan aikin kwaba garin fulawa.

Abin damuwar an ga burrbushin kwayar cutar E.coli a jikin ganyayyaki da naman da ba a sarrafa ba, amma shin ko su ne musababbi, ko a ce, fulawar na iya haifarwa?

Rikicin shi ne mutane kan zuba fulawarsu a wani mazubi sannan su yi watsi da jakar, don haka yana da wuya a tantance nau’in aboin da suke amfani da shi.

Duk da haka masu binciken suka yi kokarin gano jakunkuna biyu nau’in Gold Medal na fulawar da majiyatan ke amfani da su a gidjensu a jihohi daban-daban.

An yi su ne a masana’anta guda da ke birnin Kansas da Misssouri, inda kwana guda ne tsakaninsu.

Daga bisani “abin ya haifar da barkewar annobar a garemu,” a cewar William, “shi ne akwai yara uku wadanda suka ci abinci a wurare uku daban-daban na gidan sayar da abincin al’adun Mexico,” a irin wannan alakar, yayin da iyalai ke jiran abincinsu, ma’aikacin gidan abincin ya kan bai wa yara kwababben curin makwalashen da ba sarrafa ba (ball of tortilla dough) su yi wasa da shi.

“Shin daga ina fulawar da aka cura kwabin tortilla ta fito? in ji Williams. “Hakikanin gaskiya sai aka koma masana’antar birnin Kansas, da ta samar da kayan a lokaci guda.”

Ba za ka taba zaton burbushin fulawa da ya watsu a dakin girki zai zama matsala ba.

Daga nan sai hukumomin lafiya suka tuntubi General Mills, kamfanin fulawar gold Medal, inda daga bisani suka janye kanyan daga kasuwa, inda suka shawarci masu masu sayen kayan da su yi watsi da irin wadannan kayayyakin da aka yi a daidai wannan lokacin da ake zargi (cewa sun haifar da annobar).

Daidai lokacin da aka kammala binciken barkewar annoba, an tabbatar da bazuwar kwayar cutar E. coli a fulawar da dimbin majiyatan suka yi amfani d aita, inda mutum 63 suka kamu da rashin lafiya, kodayake an yi sa’a babu wanda yam utu.

Daga nan aka fara tattaunawa kan fulawar, a cewar Williams.

Don haka sai aka yanke cewa a rika dafa fulawa kafin a ci. Kuma kada a dauka cewa burbudin fulawa a dakin girki ba zai iya haifar da cuta ba.

Sai dai kayan amfanin gona da ba a sarrrafa (dafa) ba, a karshe, wadanda aka debo daga gona ko nau’in dabbbobi (wadanda za su iya yada kwayar cutar E.coli).

Da zarar an sarrrafa tsirrai, inda alkama da ta fito daga wurare daban-daban a lokaci guda, ta yadda gubar wata gona na da tasirin yaduwa da yawa.

Barkewar annoba tunatarwa ce kan cewa a daina cin abincin da ba a sarrafa ba( kamar kwababbiyar fulawa ko curin kayan makwalashe da za a soya).

Wannan na nuni da cewa kamfanonin ko masana’antun za su fahimci cewa mutane za su iya kamuwa da rashin lafiya daga sinadarin kwaba fulawa.

Sai aka rika dauka lamarin na tattare da hadari, inda ake lura da guba, sai suka bullo da dabarrun shawo kan lamarin, tun daga kan alkamar da ke tsaye a gona (ba a girbe ba) zuwa ga masana’antar da ake sarrrafata, inda ake ganin yiwuwar ceton rayukanan gaba.

Daukacin wannan aikin rana guda ne, na duba-garin da suka gano gubar da ke gurbata abinci.

Matar da ke aikin fasa dutse don neman na abinci a Abuja


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sana’ar fasa duwatsu ta zame wa wasu mata da dama hanyar samun abinci a Abuja

A yawancin lokuta, matan da mazansu suka mutu na tagayyara kuma sukan fuskanci talauci. Wannan lamarin haka yake a Afirka inda mafi yawan irin wadannan matan basu da ilimin zamani da zai taimake su wajen lura da kansu ballantana yaransu. Amma duk da haka, wasu matan marasa ilimin zamani suna ayyukan da ba kasafai mata keyi ba domin kula da yaran nasu. Usman Minjibir na Sashen Hausa na BBC ya ziyarci wani wuri a Abuja babban birnin Najeriya inda wasu mata da mazansu suka mutu ke ayyukan fasa dutse domin biya wa ‘ya’yansu kudin makaranta.

Patience Tanimu na cikin masu aikin fasa dutse a kauyen Gudaba dake kusa da birnin Abuja. Ta nade hannayenta kuma ta yi daurin dankwali da ake kira “ture ni kaga tsiya”.

Ta kuke tana fasa dutse da wata katuwar guduma da ake amfani da ita wajen gine-gine, kuma tan zufa babu kakkautawa duk da yake tana karkashin wata lema.

Uwargida Tanimu na rera waka domin rage zafin aikin fasa dutsen da take yi.

“A gaskiya jikina ya kan yi min ciwo da dare. Amma na kan sha wasu kwayoyi domin in samu barci. Dole ne in zage damtse kamar namiji idan ina son yin wannan aikin”.

Mijin Patience ya mutu a wani hatsarin mota kimanin shekara shida da suka gabata. Amma har yanzu tana tuna irin yadda waccan rayuwar ta kasance tare da maigidan nata.

“Tun mijina na da rai nake wannan aikin na fasa dutse. Ya so ya hana ni aikin kafin mutuwarsa, amma hakan bai yiwu ba”.

Babban kalubale dake gaban wannan matar da ‘ya’yanta shi ne na biya wa yaran kudin makaranta. Kuma gashi Patience bata da ‘yan uwan da zasu taimaka mata.

“Bani da iyaye ko ‘yan uwa. A halin yanzu nine komai ga yaran nan. Ni ke ciyar da su, na tufatar da su kuma nine ke ilmantar da su. Ina iya kokarina. Daya daga cikin ‘ya’yana na son zama dan kasuwa. Wan kuma y ce yana son zama likita ne. Sauran yaran ma na da nasu burin”.

Amma fasa dutse baya kawo isassun kudade duk da yake wannan sana’a ita ce take rike gidan na tsawon shekaru shida da suka gabata.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A wasu kasashen Afirka ma ba manyan mata kadai ke aikin fasa duwatsu ba har da kananan yara mata

“Muna godiya ga Ubangiji. Duk da yake ana samu a sana’ar, amma ina fatar samun wacce ta fi wannan. Dalilin shi ne na kan fara aiki da karfe 6:00 na safe kuma in tashi da karfe 6:30 na yamma. Wasu lokutan na kan koma gida babu ko kwabo a hannu na. Amma wata rana kuma na kan samu abin da baya kasa fam biyar na Amurka”.

A halin yanzu Patience na amfani da kudin da take samu domin biyan kudin makarantar ‘ya’yanta. Ko lamarin zai dore sai Allah kadai ya sani. Wasu kuma na ganin kamata yayi masu hannu da shuni da ma gwamnati su taimaka wa iyalai irin na Patience, domin al’amarinta irin na sauran iyalai ne dake sassan Najeriya.

Ivory Coast: Tsoffin mayaka na neman hakkinsu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tsoffafin mayaka a Ivory Coast suna shirin gudanar da wasu jerin zanga-zanga a fadin kasar yau.

Sun ce shugaban kasar Alassane Ouattarra ya kasa biyan kowannensu dala dubu ladan yakin da suka yi na tabbatar da shugaban ya dare karagar mulkin kasar.

Ba wannan ne karon farko a bana da wannan gwamantin ke fama da batun zanga-zanga da tsoffin mayaka ke gudanarwa ba na neman a biya su kudi.

A watan Mayu, fiye da sojoji dubu takwas rike da makamai suka dakatar da komai a kasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban Ivory Coast Alassane Dramane Ouattara

Yawancinsu tsoffin mayaka ne da aka shigar da su cikin sojin kasar, kuma suna ikirarin kowannen su na bin gwamnatin shugaba Alassan Ouattarra bashin fiye da dala 20,000 na shekarun da suka shafe suna kokarin dora shugaban a kan mulki.

A wancan lokacin, gwamnatin ta amince ta biya su, amma wannan lamarin ya janyo wata sabuwar matsala – akwai wasu tsoffin mayakan 6,000 da basu sami aikin soji ba dake neman a biya su kudade su ma.

Sun ce zanga-zangar ta yau domin iyalan wadanda suka mutu a cikinsu ne a yayin da ake yakin basasar kasar da kuma wadanda suka sami raunuka, kuma gwamnati ta manta dasu gaba daya.

Sun ce kuma suna da makamai, amma zasu gudanar da zanga-zangar cikin lumana – har sai an biya su kudadesu.

A nata bangaren, gwamnatin kasar ta ce tana tattaunawa da tsoffin mayakan.

Zaben shugaban kasar kenya – BBC Hausa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zanga zanga kan zaben shugaban kasar Kenya

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya yi kira ga mutane a kan su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kuma su kada kuria a zaben shugaban kasa da za a sake yi a yau .

Mista Kenyatta ya ce an tura da jamian tsaro zuwa sasan kasar daban-daban kuma ya yi gargadin cewa ba zai amince da tashe tashen hankula ba.

Jagoran ‘yan hammaya, Raila Odinga , ya nemi magoya bayansa a kan su kauracema zaben , saboda ya yi ammanar cewa ba sahihin zabe bane.

Zaben zai gudana ne bayan da kotun koli ta kasa saurarar karar da wasu suka shigar a gabanta, inda suka nemi a dage zaben.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jagoran ‘yan hammaya Raila Odinga

An yi taho-mu-gama tsakanin ‘yan sanda da magoya bayan Mista Odinga a lardin Kisumu.

Gwamnatin kasar ta bada hutu a jiya Laraba domin mutane su samu damar yin tafiya zuwa wuraren da aka yi mu su rajista.

Zaman doya da manya da ake yi tsakanin ‘yan siyasa na janyo fargaba kan barkewar tashe tashen hankula.

Mutum fiye da 1’600 ne suka mutu ya yinda dubai sun rasa matsugunansu a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi a 2007.

Kalli yadda ‘yan shi’a suka gudanar da zanga-zangar neman a sako Zakzaky


Daruruwan ‘yan kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Sheikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja domin neman gwamnati ta saki malamin.

Baya ga haka ‘yan kungiyar sun nuna adawa da yunkurin gwamnatin kasar na sa kwamitin da zai binciki abin da ya faru tsakanin jami’an tsaro da ‘yan kungiyar a garin Zariya a shekarar 2015 yayi zama a asirce.

Rikicin dai ya haddasa asarar rayuka da dama, kuma tun lokacin ne ake tsare da malamin duk kuwa da umarnin kotu na a sake shi.

Sojin Nigeria sun ‘kashe’ matar Shekau a luguden wuta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rundunar sojin saman Najeriya ta sha kai hare-hare yankuna da dama a jihar Borno

Wasu bayanan sirri na rundunar sojin saman Najeriya sun nuna cewa an kashe matar shugaban kungiyar Boko Haram, Malama Firdausi Shekau, a wasu hare-haren sama da aka kai yankunan Durwawa a wajen garin Urga da ke kusa da Konduga a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojin sama ta aikewa manema labarai a ranar Laraba, wadda mai magana da yawunta Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya sanyawa hannu.

Sai dai babu wata majiya mai karfi zuwa yanzu da ta tabbatar da ikirarin nasu.

Ko a baya ma rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa ta kashe manyan kwamandojin Boko Haram har ma da shugabansu Abubakar Shekau, sai dai daga baya kungiyar ta musanta.

Rundunar ta ce rahotanni sun nuna cewa Malama Firdausi na wakiltar mijinta ne a jan ragamar wani taro da sauran mayakan kungiyar ke halarta a wajen da aka kai hare-haren saman.

A ranar 19 ga watan Oktobar 2017 ma rundunar sojin kasar ta ce ta samu nasara a wani hari da ta kai kan wasu wurare da suka kasance maboyar mayakan Boko Haram din a Durwawa.

Rahoton da aka tattara na ta’adin da aka yi a lokacin ya nuna cewa harin saman da aka kai ya sa wuta ta tashi, abin da ya lalata wasu gine-gine na mayakan Boko Haram inda da dama suka mutu, ya kuma tilasta wa kadan daga cikin su tserewa.

Dama dai rundunar sojin kasan ta fitar da sanarwar cewa ta fara wani aiki na kai wa mayakan Boko Haram hare-hare ta sama, da ta yi wa lakabi da Operation Ruwan Wuta.

An fara aikin Operation Ruwan Wuta ne a ranar Litinin 23 ga watan Oktobar 2017, don yin ruwan wuta a maboyar mayakan Boko Haram.

A ranar farko ta fara aikin, rundunar sojin saman ta yi ruwan wuta sosai a wasu yankuna da ke garin Garin Maloma.

An yi amfani da jiragen yaki biyu masu dauke da bama-bamai da rokoki inda aka dinga luguden wuta, aka kuma kwashe wasu mayakan masu kokarin tserewa.

Hakkin mallakar hoto
NAF

Rahama Sadau ta nemi gafarar Ganduje da Sarki Sanusi II


Image caption

Wannan waka ce ta jawo aka dakatar da Rahama Sadu daga Kannywood

Shahararriyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana “rungumar” wani mawaki.

Wannan batu ne ya jawo kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa reshen jihar Kano, MOPPAN, ta koreta daga masana’antar a watan Oktoban bara.

A wata wasikar da ta aike wa MOPPAN, wacce BBC Hausa ta samu kwafi, Rahama ta nemi afuwa kan abin da ta yi, tana mai cewa “kuskure ne,” kuma za ta “kiyaye gaba”.

Jarumar, wacce korar tata ta sa ta koma fitowa a fina-finan Nollywood, ta kuma tabbatarwa da Nasidi Adamu Yahaya cewa hakika ta nefmi gafara” kan rungumar mawaki Classiq da ta yi.

Sai dai wannan wasika da Rahama ta rubuta tamkar ta yi amai ta lashe ne, saboda ko a watan Yulin da ya gabata ta shaida wa BBC cewa babu wanda ya dakatar da ita daga Kannywood.

Shugaban MOPPAN Kabiru Maikaba ya shaida wa BBC cewa kungiyar za ta sanar da matsayin da ta dauka a kan afuwar da jarumar ta nema bayan sun tattauna a hukumance.

Amma ya ce kungiyar za ta yi kokarin kwatanta adalci ga Rahama kan duk wani mataki da za su dauka.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba wanda ya dakatar da ni- Rahama Sadau

Abin da wasikar ta kunsa

Ta rubuta cewa: “An kai shekara daya kenan tun faruwar wannan lamari, na yi iyakar kokarina don na nutsu sosai ta yadda ba za a bai wa kalamaina wata ma’ana ta daban ba kamar yadda kafofin yada labarai da wasu mutane suka dinga yi a baya.”

“Ni ‘yar adam ce wacce ba ta kubuta daga aikata kuskure ba, kuma ni ‘ya ce wadda za a iya yi wa gyara, ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu shirya fina-finai, da dukkan al’ummar arewacin Najeriya da ma dukkan masu kallo da su gafarce ni,” in ji Rahama.

Kazalika, jarumar ta yi magana a wasu gidajen rediyo na jihar Kano, inda ta jaddada neman gafarar musamman ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da kuma gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A karshen wasikar dai Rahama ta yi alkawarin bin dokokin da kungiyar ta shimfida.

Karanta wasikar neman gafarar da Rahama Sadau ta rubuta

Hakkin mallakar hoto
Rahama Sadau/Moppan

Image caption

Rahama Sadau ta yi alkawarin bin doka da oda a nan gaba

Hakkin mallakar hoto
TWITTER

Image caption

Wannan batu na Rahama Sadau ya jawo ce-ce-kuce sosai a Kannywood

Fifa ta wanke Juventus kan batun Pogba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tun a watan Yuni hukumar kwallon kafa ta duniya ta wanke United

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta wanke Juventus kan cinikin Paul Pogba da ta sayar wa Manchester United kan kudi fam miliyan 89.3 a bara.

Tun a watan Yuni Fifa ta ce United ba ta laifi kan sayan dan kwallon da ta yi, amma ta zargi Juventus da laifin hada baki da wakilin Pogba, Mino Railo wajen karya ka’idar hukumar.

Amma yanzu hukumar ta ce babu wani hukuncin da za ta dauka kan Juventus bayan da kwamitin ladabtarwa ya kammala bincikensa, bai kuma sameta da laifi ba.

Kwamitin ya ce bai samu kwakkwarar shaida cewar kungiyar ta karya dokar cinikin Pogba da ta yi zuwa United ba.

Copa del Rey: Madrid da Fuenlabrada


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Madrid ta ci Copa del Rey sau 19 a tarihi

Real Madrid za ta ziyarci Fuenlabrada domin karawa da ita a gasar Copa del Rey a ranar Alhamis.

Madrid wacce ke ta uku a kan teburin La Liga za ta buga wasan kungiyoyi 32 da suke buga gasar.

Wasu wasannin da za a yi a ranar ta Alhamis Lleida Esportiu da Real Sociedad, Deportivo La Coruna da Las Palmas, Girona da Levante da karawa tsakanin CD Tenerife da Espanyol.

Real Madrid tana da Copa del Rey 19, sai dai Barcelona wacce ta dauki kofin sau 29 ita ce ke kare kambunta.

World Cup U:17 Ingila ta ci Brazil ta kai wasan karshe


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ingila ta kai wasan karshe bayan da Brewster ya ci kwallo uku a karawar da suka yi 3-1

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 da India ke karbar bakunci.

Ingila ta kai wasan karshen ne bayan da ta doke Brazil da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a ranar Laraba a filin wasa na Kolkata da ke India.

Kuma Ingila ta ci dukkan kwallayen ne ta hannun Rhian Brewster, inda ya fara cin guda biyu tun kafin aje hutu ya kara ta uku bayan da aka koma wasan zagaye na biyu.

Brazil wacce za ta buga wasan neman mataki na uku a gasar ta zare kwallo daya ta hannun Wesley tun kafin aje hutu.

Da wannan sakamakon Ingila za ta buga wasan karshe a ranar Asabar da wacce ta yi nasara tsakanin Mali ko kuma Spaniya.

Zan kakkabe tsattsauran ra’ayin addini a Saudiyya – Yarima


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Yariman ya sha alwashin kakkabe duk wani abu da ke da alaka da tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci nan ba da jimawa ba

Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya ce dawo da sassaukan ra’ayin addinin musulunci na daga cikin shirye-shiryensa na zamanantar da kasar.

Ya shaida wa manema labarai cewa kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar ‘yan kasa da shekara 30 ne, kuma sun fi son rayuwa irin wacce “addinin musulunci ya bayyana yadda za a zauna da juna lafiya”.

Yariman ya sha alwashin kakkabe duk wani abu da ke da alaka da tsattsauran ra’ayin addinin musulunci nan ba da jimawa ba.

Sai dai Yariman bai yi wani karin bayani kan abin da yake nufi da ‘tsattsauran ra’ayin addinin musuluncin’ da ya ke son kawar wa ba.

Wadannan kalaman nasa ka iya bude sabon babi a muhawar da ake yi na irin salon da kasar ke son dauka a nan gaba.

Ya yi wadannan kalamai ne bayan da ya sanar da zuba jarin dala biliyan 500 don gina wani sabon birni a kasar.

Birnin mai suna NEOM zai kasance ne a yankin arewa maso yammacin gabar kogin maliya, kusa da iyakar Masar da kuma ta Jordan. Girman wajen kuma zai kai mita 26,500.

A Saudiyya dai yana daga cikin dokar kasar a tabbatar da cewa mutane sun yi shiga ta kamala kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A shekarar da ta gabata ne Yarima Mohammed ya kaddamar da wani faffadan shiri na samar da sauye-sauye a zamantakewa da tattalin arziki a kasar wanda aka yi wa lakabi da “Vision 2030”.

A bangaren wadannan shirye-shirye dai, yariman mai shekara 32 ya gabatar da bukatar sayar da wani bangare na kamfanin man fetur na kasar, Saudi Aramco, da kuma kirkirar asusun ajiyar rarar kudi na kasa saboda bacin rana mafi girma a duniya.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ya yi wadannan kalamai ne bayan da ya sanar da zuba jarin dala biliyan 500 don gina wani sabon birni a kasar

A watan Satumba ne kuma mahaifinsa Sarki Salman, ya sanar da janye dokar da ta haramta wa mata tukin mota daga shekara mai zuwa, duk kuwa da kin goyon bayan hakan da wasu malaman kasar suka yi.

Gwamnatin tana kuma son zuba jari a bangaren shakatawa.

A yanzu haka ana sa ran nan ba da jimawa ba za a sake bude gidajen rawa da gidajen kallo na sinima a kasar.

Yarima Mohammed ya kare wadannan sauye-sauye a wani taron tattalin arziki da aka yi a Riyadh ranar Talata, wanda aka yi da masu zuba jari da manyan mutane.

“Muna dab da komawa yadda muke a baya – kasar da ke bin matsakaicin ra’ayin addinin musulunci mai kyawun mu’amala da ko wanne addini, da al’adu da mutane a duk fadin duniya,” a cewarsa.

Ya kara da cewa: “Muna son mu yi rayuwa kamar kowa. Rayuwa wacce addininmu ya bayar da damar yin kyakkyawar mu’amala da kowa.”

“Kashi 70 cikin 100 na al’ummar Saudiyya ‘yan kasa da shekara 30 ne, kuma maganar gaskiya ba za mu bata shekara 30 masu zuwa wajen fama da akidun da za su rusa mu ba. Za mu ruguza su a yau kawai.”

Yariman ya kuma jadda cewa Saudiyya ba haka take ba a shekarar 1979, lokacin da aka yi juyin-juya hali na musulunci a Iran, kuma mayakan sa kai suka mamaye Masallacin Harami na Makka.

Bayan wannan lokaci ne aka haramta duk wani abu da ya danganci nishadi a Saudiyya, kuma aka bai wa malamai damar kula da abubuwa kan rayuwar al’umma.

Nigeria: Fursunoni za su yi zabe a 2019


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A watan Fabrairun 2019 ne za’a gudanar da babban zabe a Najeriya.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce tana duba yiwuwar kirkiro sabbin mazabu a gidajen yari da ke kasar.

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida wa wasu kungiyoyin farar hula a Abuja cewa, akwai wasu rukunoni na ‘yan fursuna da za’a ba su damar kada kuri’a a zaben 2019.

Sai dai Farfesa Yakubu bai bayyana rukunonin fursunonin ba.

Akwai fiye da fursunoni dubu 68,000 da ake tsare da su a gidajen yari daban-dabam a fadin kasar.

Galibin fursunonin dai suna jira ne a yi musu shari’a.

Kungiyoyi da sauran masu fafutika a Najeriya sun dade suna matsin lamba ga hukumomi don su bi wa ‘yan fursuna damar kada kuri’a.

A cewar kungiyoyin, rashin bai wa fursunoni damar yin zabe tamkar tauye hakkokinsu ne.

A watan Fabrairun 2019 ne za a gudanar da babban zabe a Najeriya.

Rashin alkalai ya hana yanke hukunci kan zaben Kenya


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

David Maraga ya nemi afuwa kan kasa sauraran karar

Babban jojin Kenya ya ce kotun kolin kasar ba ta iya saurarar karar dake neman a soke zaben shugaban kasar da aka shirya yi ranar Alhamis ba.

David Maraga ya ce ba a samu isassun alkalai daga cikin alkalai bakwai na kotun da za su iya saurarar karar ba.

‘Yan bindiga sun harbi dogarin mataimakiyar babban jojin kasar ranar Talata.

Mista Maraga ya ce Philomena Mwilu “bata iya ta samu halartar zaman kotun ba”.

Dogarinta yana jinya a wani aisbiti a babban birnin kasar, Nairobi.

Wakilin BBC’s Alastair Leithead a Nairobi ya ce a yanzu ana sa ran a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Kotun kolin ta soke zaben farko da aka gudanar a watan Agusta, tana mai cewa an samu “kurare da sabawa doka”.

Jagoran ‘yan adawa Raila Odinga yana kauracewa zagaye na biyu na zaben, inda ya ce babu wani abu da ya sauya.

Ana sa bangaren Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ke neman wa’adi na biyu, ya ce dole ne a gudanar da zaben.

Zaben Kenya na cike da takardama


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kotun koli ta Kenya na fuskantar jan aiki a gabanta. An shigar da wata kara a gaban alkalan kotun domin su fayyace ko ya kamata a cigaba da zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa gobe.

Alkalan kuma sun amince su duba wani koke na gaggawa mai neman a jingine zaben ko ma a dakatar da shi gaba daya.

Shugaban gamayyar jam’iyyun adawa ta NASA, Raila Odinga ya fasa tsayawa a zaben, amma a daya bangaren shugaban kasar na cewa sai an gudanar da zaben ba tare da jinkiri ba.

Masu shigar da kara zasu iso kotun kolin nan ba da jimawa ba, domin su nemi ta dakatar da wannan zaben.

Zasu kuma nemi a gudanar da wani sabon zaben, wanda zai iya daukar watanni kafin a shirya shi, kuma yana iya jefa kasar cikin rudanin tsarin mulki.

Harun Ndubi shi ne lauyan babban kotu da zai kawo wannan karar a kotun kolin.

“A madadin masu kara, mn shigar da koke a gaban kotun koli inda muke neman ta soke sabon zaben da aka shirya na 26 ga wata”.

Ya kara da cewa: “Wadanda nake wakilta na cewa kamata yayi a gudanar da zaben mai inganci, wanda za a kamanta adalci, kuma wanda ya yi daidai da abin da dokar kasa ta tanada”.

Mista Ndubi ya ce kamata yayi a soke zaben na gobe, idan babu adalci a cikinsa:

“Amma idan haka ba zai samu ba, to kamata yayi mu fasa gudanar da shi babu jinkiri, domin mu sami zabe wanda zai gamsar da dukkan ‘yan Kenya su goyi bayan wanda yayi nasara a zaben”.

Abin damuwa shi ne wannan yanayin ya zame tamkar taken dukkan zabubbuka a Kenya.

Rikice-rikce sai karuwa suke a biranen Nairobi da Kisumu – inda ‘yan adawa suke da goyon baya a yammacin kasar, inda kuma ake ta kamfe ga mutanen yankin su kauracewa zaben.

Raila Odinga na da jerin dalilai da suka sa ya fice daga zaben: “Ba a samar da isassun sauye-sauyen da zasu tabbatar da zabe mai inganci ba”.

Kotun kolin Kenyar zata yanke hukunci game da ko hukumar zabe zata iya cigab da gudanar da zaben.

An dai kawo kuri’u, kuma wani kamfanin Faransa da ke da alhakin bayyana sakamakon zaben ya ce ya shirya tsaf.

Abin mamaki na baya-bayan nana shi ne cewa a makon jiya shi kansa shugaban hukumar zaben, Wafula Chebukati ya nuna shakku game da zaben.

“A irin wannan yanayin, da wuya a iya tabbatar da zabe mai inganci”, inji shi.

Rudanin bai tsaya anan ba, domin daya daga cikin kwamishinoninsa ta tsere zuwa Amurka.

Roselyne Akombe ta ce tana tsoron abin da zai iya faruwa a gareta, kuma tana da shakku game da zaben…

Kwatsam sai shima shugaban hukumar zaben yace zai tafi hutu, kuma ya janye kansa daga gudanar da zaben.

Da alama dai rarrabuwar kawuna da rigingimu ba zasu sa mutane su amince da hukumar zaben ba.

Ana kusa da daina gangamin neman kuri’u, sai shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa dole ne a gudanar da wannan zaben ba tare da jinkiri ba.

Shugaba Kenyatta ya ce: “Tattalin arzikin kasarmu na bukatar bunkasa, kuma dole ne mu kawar da wannan yanayi na rashin tabbas da muke ciki”.

Shugaban ya kara da cewa: “Ina kira ga dukkan ‘yan Kenya da fito ranar 26 ga watan Oktoba domin zaben dan takarar da suke ra’ayinsa”.

A nasu bangaren, jakadun kasashen Turai sun ja hankalinsa da ya tyi taka tsantsan…sun yi kira ga ‘yan siyasar kasar da su hau teburin tattaunawa.

Jakadan Amurka, Bob Godec ya bayyana matsayin kasashen duniya.

Ya kamata ‘yan Kenya, musamman ‘yan siyasar kasar su yi taka-tsatsan, kada su ruguza abin da aka shafe shekaru masu yawa wajen ginawa”.

Ana sauran kwana daya a fara zaben, har yanzu ‘yan kasar basu da tabbacin ko za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Kuma idan anyi zaben, ko jerin kararraki a gaban kotuna da zasu biyo bayan zasu sa a karbe shi da hannu bibiyu. Tambaya anan ita ce: Shin, tsarin demokradiyyar Kenya zai iaya jure wa abin da zai biyo baya kuwa?

Ko me ya sa kasar Zimbabwe ta nada Ministan WhatsApp?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan Zimbabwe sun rika raha suna bayyana sabon ministan tsaro a harkar Internet a matsayin “Ministan WhatsApp”

An yi ta watsa sanarwar gwamnati a shafukan sada zumunta jim kadan bayan da shugaba Robert Mugabe ya sanar da kafa wata ma’aikata da za ta maida hankali wajen samar da tsaro a harkar Internet.

Al’ummar Zimbabwe dai sun yi ta raha kan wasikar wacce ke dauke da sa hannu da kuma adireshi na boge na sabon ofishin ministan samar da tsaro a harkar Internet, Mr Patrick Chinamasa wanda ke umurtar duk masu amfani da WhatsApp a matsayin dandali da su yi rijista a ma’aikatar nan da watan Nuwamba.

Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Wasikar dake umurtar masu amfani da WhatsApp a matsayin dandali su yi rijista

Sai dai yanzu an rage yawan raha da ake yi kuma ‘yan kasar Zimbabwe sun maida hankali wajen nazarin tasirin sabuwar ma’aikatar musamman kan batun da ya shafi ‘yancin fadin albarkacin baki.

Barazana ga Kasa

Gwamnatin Zimbabwe dai na dari-dari da yadda ake amfani da shafukan sada zumunta tun bayan da a shekarar data gabata, wani Fasto Evan Mawararire ya jagoranci wani gangami da aka rika amfani da maudu’in #ThisFlag movement.

Ta hanyar shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook an shirya gangami na zama a gida, gangamin da shi ne mafi girma na kin jinin gwamnati da aka taba shirya wa a ‘yan shekarun nan.

Kakakin shugaban kasar Mr George Charamba, ya ce shugaba Mugabe ya yanke shawarar kafa ma’aikatar ce don shawo kan sabuwar barazanar da kasa ke fuskanta wanda ya ce ”ana tsara wa da kuma daukar nauyi don aikata ayyukan da ba su kamata ba”.

Da alamu dai shafukan sada zumunta su ne hanyoyin farko da al’ummar Zimbabwe ke amfani wajen mu’amala tare da samun labarai.

Wannan hanya dai ta na cigaba da bunkasa duk kuwa da dokokin takaita fadin albarkacin baki.

A cikin shekaru 16 da suka gabata, amfani da Internet a kasar ya karu daga kashi 0.3% zuwa kashi 46%, kamar yadda kididdiga daga hukumar sadarwa ta nuna.

Gidajen talbijin da kuma jaridu na Internet har da wadanda suke aiki daga wasu kasashen waje na amfani da Internet don watsa labarai da gwamnati ba ta da iko akai.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

#ThisFlag- Maudu’in da masu zanga zanga suka yi amfani da shi kenan bara suka sa komai ya tsaya cak a Harare

A lokacin da gidajen sayar da man fetur suka rasa mai a watan daya gabata, an yi ta ganin dogayen layukan a manyan shagunan Zimbabwe inda ‘yan kasar ke rige-rigen sayen abinci don kaucewa karancin sa.

Gwamnati dai ta yi zargin cewa an yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yada sakonnin karya da suka firgita jama’a.

Kokarin hana fadin ra’ayi’

Sai dai wasu na ganin cewa matsayin gwamnati kan wannan batu tamkar barazana ce ga ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma walwala.

Wata kungiya kan yancin sadarwa a Zimbabwe ta reshen cibiyar yan jaridu a ynkin kudancin Afrika a wata sanarwa, ta ce wannan sabon bincike kan kafafen sada zumunta ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma yancin fadin albarkacin baki.

Sanarwar ta kara da cewa, ”abun takaici barazanar da ake yi ta janyo mutane na takaita yadda suka tattauna al’amurran da suka shafi kasa.”

Kungiyar ta kuma suko takunkumi da ake sanya wa kafafen yada labarai a Zimbabwe saboda kawai suna ba jama’a damar fadin ra’ayin su a shafukan Internet kan rahotanni da kafafen suka gabatar.

A nata bangaren, gamayyar jam’iyyun adawa a Zimbabwe, Movement for Democratic Change (MDC) ta ce sabuwar ma’aikatar tsaro a harkar Internet da gwmanati ta kafa, wata hanya ce ta rika yi wa jama’a leken asiri.

Jagoran gamayyar jam’iyyun adawar Morgan Tsvangirai ya yi amannar cewa an kafa ma’aikatar ce don takaita ‘yancin fadin albarkacin baki yayin zabubbukan 2018.

Ya ce “Shugaba Mugabe… zai yi duk abun da zai iya yi don dakile shafukan sada zumunta saboda ya hana tasirin korafin da jama’a ke yi kan gwamnatin sa,”.

“Koda yake a cewar sa, babu yadda gwamnati zata yi don dakile shafukan sada zumunta.”

Za’a tsare mutane nan gaba?

Yayin da wa su kasashen duniya da dama su ke da hukumomi wadanda ke yaki da masu aikata laifuffuka ta shafin Internet, Zimbabwe ce kasa ta farko a duniya da ta kafa ma’aikata sukutum da guda don kula da hakan.

A yanzu dai ana cigaba da yada sakonni na gargadi a shafukan sada zumunta.

Misalin irin wadannan sakonni shi ne daga wani mutum mai suna “Mr Chaipa”, wanda ya bukaci ‘yan Zimbabwe da suka rika yada labaran da za su iya kare kansu a gaban kotun ne kadai a shakukan sada zumunta.

Mr Chaipa ya ce yana da sauki gwamnati ta sa ido kan sakonni da ake watsawa inda ya lissafa jerin ayyuka ta Internet da za’a iya dangantawa a matsayin manyan laifuffuka.

”Nan da wa su watanni ma su zuwa za’a kame mutane da dama don su zama abun misali da za su sa mutane suk guji wuce makadi da rawa a lokacin da su ke amfani da shafukan sada zumunta gabannin zabe,” in ji shi. “

Twitter ya bullo da sabbin kaidojin talla


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sabbin kaidojin yin tala na shafin Twitter

Shafin sada zumunta na twitter zai kaddamar da wasu sabbin kaidoji kan tallace tallacen da ake yi a lokacin zabe.

Twitter ya ce ya dauki wannnan mataki ne domin maida martani kan sukar da aka rika yi ,game da kutsen da ake zargin Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na Amurka a shekarar 2016.

An dai gano wasu shafuka 200 masu alaka da gwamnatin Rasha .

Mata sun yi kira da a kauracewa shafin Twitter

Sanatocin Amurka sun soki Twitter

Amurka ta yi barazanar daukar mataki a kan rashin gaskiya a kudaden da ‘yan siyasa suke kashewa a shafukan sada zumunta.

A yanzu shafin Twitter zai dinga bada bayani a kan wanda ya biya kudin talla da ya walafa da yawan kudin da aka kashe da kuma masu amfani da shafin da ake son a ja hankalinsu.

Sabuwar allurar rigakafi kan cutar taifod


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Taifod ta fi yaduwa a ruwan da ba shi da tsafta

Hukumar lafiya ta duniya ta bayar da shawarar amfani da wata sabuwar allurar riga-kafin zazzabin taifod, wadda za a rika amfani da ita.

Kwararru sun yi amanna cewa, idan har allurar riga-kafin ta yi matukar tasiri, za ta taimaka wajen kawar da cutar baki daya.

Sabanin sauran alluran riga-kafin, sabon maganin yana amfani ga yara kanana, wadanda ke matukar fuskantar hadarin kamuwa da cutar.

An yi kiyasin zazzabin na taifod yana halaka mutane fiye da dubu dari biyu a sassan duniya a duk shekara.

Kwayar cutar Salmonella Typhi ce ke haddasa zazzabin taifod .

Alamun cutar sun hada da

1 Zazzabi da zafin jiki

2 Ciwon kai

3 Amai gudawa

4 Rashin cin abinci.

Kwayar cutar na saurin yaduwa a gurbattaccen ruwan sha ko kuma abinci.

Cutar ta fi kamari a kasashen da ba su da tsafattacen muhali da kuma ruwan sha musaman a Asiya da kuma yankin kudu da sahara na Afrika.

United ta kai daf da na kusa da na karshe a League Cup


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

United ce ke rike da League Cup wanda ta lashe a bara

Mai rike da kofin League Cup, Manchester United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe bayan da ta ci Swansea City a karawar da suka yi a ranar Talata.

United wadda ta lashe kofin bara ta ci kwallonta biyu ne ta hannun Jesse Lingard daya kafin aje hutu, dayar kuwa bayan da aka dawo daga hutu.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Arsenal ta doke Norwich City 2-1, Bournmouth ta ci Middlesbrough 3-1 da wasan da Bristol City ta doke Crystal Palace 4-1 da fafatawar da Leicester City ta ci Leeds United 3-1.

Sai a ranar Laraba ne Chelsea za ta kara da Everton da wasan da Tottenham za ta karbi bakuncin West Ham United.

Tottenham za ta tsugawa Kane kudi — Perez


Image caption

Madrid da Tottenham sun buga 1-1 a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka kara a Spaniya

Shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Perez ya ce Tottenham za ta saka kudi mai tsada ga duk kungiyar da ke son sayen Harry Kane.

Da aka tambayi Perez ko ya tattauna da shugaban Tottenham, Daniel Levy kan nawa za a sayar masa da dan wasan sai ya ce bai yi ba, amma za a ce ya biya fam miliyan 223.

Sai dai kuma shugaban na Real Madrid ya ce bai taba tunanin kawo Kane Santiago Bernebeau domin ya taka-leda ba.

Kocin Madrid, Zinedine Zidane ya ce Kane cikakken dan kwallo ne tun kafin su fafata a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka tashi 1-1 a Spaniya.

Kane ya ci wa Tottenham da tawagar Ingila kwallo 15 tun fara kakar bana, ya kuma ci 45 jumulla a shekarar 2017.

A bana ne Paris St Germain ta sayi Neymar daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya

Super Eagles za ta kara da Argentina


Hakkin mallakar hoto
The NFF

Image caption

Super Eagles za ta buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2017

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta buga wasan sada zumunta da ta Argentina a birin Krasnodor na Rasha.

Kasashen biyu za su fafata ne a ranar 14 ga watan Nuwambar 2017, idan har hukumar kwallon kafa ta duniya ta amince da kammala tsare-tsaren jirgin da zai kai ‘yan wasa.

Super Eagles za ta buga karawar ce, kwana hudu bayan ta fafata da Algeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya, wacce tuni Nigeria ta zama ta farko da ta samu tikitin kai wa Rasha.

Sakatare janar na hukumar kwallon kafar Nigeria, Dakta Muhammadu Sunusi ya ce kasashe kamar su Iran da Saudi Arabia da Morocco duk sun nemi su buga wasan sada zumunta da Nigeria, amma ta zabi ta fuskanci Argentina.

Nigeria da Arhgentina sun kara a wasan sada zumunta a 2011, inda wasan farko a Abuja Super Eagles ta ci 4-1 a watan Yuni, karawa ta biyu kuwa Argentina ce ta yi nasara da ci 3-1 a Bangladesh a watan Satumba.

Nigeria: Majalisa za ta binciki batun Maina


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan majalisun dokokin sun bayyana takaicin yadda shugaban kasar ke shelar yaki da cin hanci da rashawa sabanin wasu mukarrabansa

‘Yan Majalisar dattawan Najeriya da ta wakilai za su gudanar da bincike kan yadda aka dawo da tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar, AbdulRasheed Maina bakin aiki.

‘Yan Majalisun dokokin dai sun zartar da kudirin ne sakamakon ce-ce-kucen da ya barke a kasar bayan mayar da Maina bakin aiki a matsayin darekta a ma’aikatar cikin gida.

Da suke tafka muhawara ranar Talata, wasu ‘yan Majalisar dattawa sun bayyana takaicinsu kan yadda shugaban kasar ke shelar yaki da cin hanci da rashawa sabanin haka a tsakanin wasu mukarrabansa.

Majalisar dattawa ta umurci kwamitocinta da suka hada da na harkokin cikin gida da kwamitin shari’a da kuma kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Su ma ‘yan Majalisar wakilai sun kafa wani kwamiti na musamman don binciken yadda aka yi AbdulRasheed Maina ya koma bakin aiki.

Majalisar wakilan ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ta gaggauta kama AbdulRasheed Maina domin ya fuskanci shari’a.

‘Yan Majalisar wakilan sun kuma sha alwashin ba da shawarar hukunta duk wani da aka samu da hannu a lamarin.

A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori AbdulRasheed Maina, daga sabon mukamin mukaddashin darakta a ma’aikatar harkokin cikin gida.

‘Yan BH na jin takaicin ana cewa suna lalata da mu – ‘Yar Chibok


Daya daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sako a watan Mayu ta shaida wa ‘yar jarida Adaobi Tricia Nwaubani yadda ba za ta manta da abubuwan da suka faru da ita a cikin shekara uku da ta shafe a hannun mayakan Boko Haram ba.

Naomi Adamu na daya daga cikin wadanda suka fi yawan shekaru a ajinsu kuma tana da shekara 24 a lokacin da ‘yan Boko Haram suka sace su, suka boye su a dajin Sambisa da ke arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2014.

A lokacin da suke hannun mayakan, sun ba su littattafan rubutu da suke zuwa da su aji a lokacin da suke koyon karatun Kur’ani.

Sai dai wasu daga cikin yaran na amfani da wadannan littattafan rubutu ne wajen rubuta abin da ya faru da kuma sirrikansu. A lokacin da mayakan suka gano haka ne suka tilasta musu kona littattafan.

Sai dai Naomi da kawarta wacce ko da yaushe suna tare wato Sarah Samuel, mai shekara 20 sun yi kokarin boye nasu littafin, da wasu ‘yan mata uku wadanda su ma suka yi amfani da littatfin wajen adana labarinsu da kuma halin da suka shiga.

Image caption

Littattafan biyu ne masu shafi 40 wadanda ‘yan matan suka adana don rubuta labarin halin da suka shiga

An yi rubutun cikin littafin ne a harshen Turanci da kuma Hausar da ba ta nuna, sai dai ba a rubuta kwanan wata a jiki ba, amma ana ganin an yi rubutun ne tun a watannin farko na kama ‘yan matan.

Ga goma daga cikin abubuwan da suka rubuta. Sai dai an dan yi gyare-gyare a wasu wuraren don a fahimta sosai:

1. Ba da niyyar sace ‘yan matan Chibok aka je ba

Mayakan da suka kai hari makarantar Chibok a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, sun je da niyyar sace “injin da ake buga bulo ne” kamar yadda ‘yan matan suka rubuta a littafin.

Sai dai ba a san takamaimai injin da suke nema ba, saboda an yi aikin gine-gine a makarantar na wasu ‘yan makonni, amma wata kila injin da ake yin bulon siminti suke nema wanda kuma ana amfani da shi a wajen kera makamai.

Sai dai da ba su samu ba ne, sai suka fara shawarar ya za su yi da daliban da suka taru kungiya-kungiya. Bayan da suka dauki lokaci suna wannan mahawara ne sai suka yanke shawarar tafiya da yaran.

“Sun fara mahawarar ne a tsakaninsu. Sai wani karami daga cikinsu ya ce a kona mu duka kawai, sai suka ce a’a ba haka za a yi ba, mu tafi da su dajin Sambisa.

“Sai wani kuma ya ce, ‘a’a kar mu yi haka, mu kai su gidan iyayensu. Suna cikin wannan mahawarar ne sai daya daga cikinsu ya ce, gaskiya ba zai yiwu na zo da mota ba komai cikinta sannan kuma na koma da ita fanko ba, idan muka kai su wajen shugabanmu (Abubakar Shekau) zai san yadda za a yi.”

2. Labarin yadda aka kange su daga tserewa

An zuba wasu daga cikin yaran cikin motar da mayakan suka zo da ita makarantar, da dama kuma aka sa su suka fara tattaki da kafarsu ana binsu da bindigogi inda suka yi doguwar tafiya, har sai da aka kawo wasu motocin da suka dauki sauran ‘yan matan.

Wa ya rubuta labarin?

Ainihin wadanda suka rubutawa: Naomi Adamu da Sarah Samuel

Rhoda Peter da Saratu Ayuba da Margaret Yama sun ba da ‘yar gudunmowa wajen rubutun

An sako hudu daga cikinsu a watan Mayun 2017

Sarah Samuel ta yarda ta auri daya daga cikin mayakan a bara kuma har yanzu tana wajen su.

Image caption

Wannan shi ne littafin da Naomi ta dinga rubuta abin da ke faruwa

A kan hanyarsu ta zuwa dajin da aka boyesu, sai wasu daga cikin daliban suka fara tsalle suna dira daga motar suna tserewa, amma sai daya daga cikin su ta sanarwa da mayakan.

Wata kila ta yi hakan ne don tana jin tsoron kar a tafi a bar ta ita kadai, ko kuma don yin biyayya ga dokar da aka ba su.

“Sai daya daga cikin ‘yan matan ta ce, Direba wasu yaran suna tsalle suna tserewa. Sai direban ya bude kofar motar ya fara nemansu amma bai samu ko daya ba. Sai suka ce musu su zauna wuri daya, kuma idan suka samu wata ta kara tsalle ta fita sai sun harbeta.

3.Mugayen dabaru

Mayakan sun yi amfani da mugayen dabaru a kan ‘yan matan da suka sace, da suka hada da barazanar cewa tuni mayakan suka sace iyayensu.

A wani lokacin kuma suna ware Kirista dabam Musulmai dabam, har ma su ce duk wanda bai Musulunta ba za su konashi da fetir.

“Sanann sai suka zo wurinmu suka ce mana, Musulmai su fito lokacin sallah ya yi. Bayan da suka idar da sallah sai suka ce, Musulmai su ware Kirista ma su ware gefe daya”.

“Sai muka ga wasu jarkoki a mota sai muka yi tsammanin fetir ne. Sai suka ce mana, Su waye zasu Musulunta a cikinku. Da yawa daga cikinmu suka tashi tsaye suka shiga ciki saboda tsoro, sai suka ce, ku sauran kuna so ku mutu kenan tunda ba kwa son ku Musulunta ko?

“To zamu kona ku, sai suka ba mu wadanann jarkokin da muka yi tsammanin fetir ne ashe ruwa ne a ciki.”

4. Mayakan na jin takaci a kan zargin da ake yi a kansu cewa suna lalata da ‘yan matan

Wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da aka tattauna da su sun bayyana cewa ba a yi lalata da su ko tilasta musu aure ba, ko da yake wani lokacin sun nuna bukatar aurensu.

Wasu ‘yan matan kuma ana daukarsu a matsayin kwarkwara.

Image caption

‘Yan matan sun boye litatfin da suka yi rubutun a karkashin kasa

Rubutun ya nuna cewa mayakan suna jin haushin abin da kafafen yada labarai ke yada wa cewa suna lalata da ‘yan matan.

Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya sha fadar haka a lokuta da dama, na farko a wani sakon da aka nada da aka kunana wa ‘yan matan.

“Sannan da dare kuma, suna taramu suyi mana wa’azi kuma su kunna mana kaset.

Sun ce kaset din daga wurin shugabansu yake Abubakar Shekau, inda ya ce ba don wani abu aka daukoku ba sai don a koya musu addini da bin hanyar Allah, amma iyayenku da gwamnati da shugaban makarantarku suna yin kuka suna cewa muna yin lalata da ku, muna yi muku abubuwa marasa kyau, to mu mun kawoku ne don mu koyar da ku hanyar Allah.

5. Saka hijabi don gujewa rudin shedan

The militants pleaded with the girls to not lead them into temptation, encouraging them to always keep their bodies covered in a hijab.

Mayakan na fadakar da ‘yan matan muhimmancin saka hijabi a ko yaushe don kar su jefa su a rudin shaidan su yi sha’awar jikinsu.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Boko Haram

“Ya bude Kur’ani ya fara karantawa, sannan ya karanta wani wuri da ya fassara da cewa duk wanda aka sace a jihadi, to naku ne kuma kana da damar da zaku yi abin da ku ke so da shi, saboda haka ne sai suka ba mu hijabi saboda ba sa so suna ganin jikinmu, saboda kar su aikata sabo kuma su yi abin da bai dace ba”.

6. Gabatar musu da bukatarsu ta neman aure

Mayakan boko haram suna yawan tilasta wa ‘yan matan da maganar aure.

“Wata yarinya tana so ta shiga daki ta dauki wani abu, sai wani daga cikin mayakan (Malam Ahmad) ya shiga ya sameta ya yi mata magana a kan aure. Sai ta ce masa, a’a, sai ya tambayeta, mece ce shawararki game da auren?

“Sai ta ce a’a, sun sato ta daga makarantar GGSS Chibok sun kawota Sambisa sannan kuma yanzu suyi mata maganar aure.Ta yaya za ta yi aure bayan mahaifiyarta da mahaifinta da sauran ‘yan uwanta ba su sani ba.

“Sannan sai ta tambayeshi idan ta ce a’a ba za ta yi auren ba, kawai za ta tsaya ta yi wa ubangijinta biyayya kawai, ta yi laifi? sai ya ce a’a, ba laifi”.

Wasu kuwa an matsa musu lamba don su sauya ra’ayinsu.

“Mun ga mutane suna fitowa daga mota kirar (Hilux). Sai suka tambayemu su waye suke son yin aure. Kuma suka ce mana duk wanda ya Musulunta to dole ne ya yi aure matukar ya rungumi addinin hannu bibbiyu.

Sai suka ba mu minti 30 mu ba su amsa amma sai muka yi shiru. Mun shafe sa’a daya ba wanda ya ce musu uffan”.

Naomi Adamu ta shaida min cewa duk wadanda suka ki amincewa su yi aure ana daukarsu a matsayin bayi, kullum sai an dake su.

Suna fada mana cewa mu yi aure idan ba haka ba za su dakemu. Mu yi wanki, mu debo ruwa, mu zamu yi wa matansu komai, mu kuma bayi ne”.

7. Mazauna wani kauye sun dawo da wadanda suka tsere

Duk da fafatukar da aka yi ta yi a duniya don ganin an dawo da yaran nan, inda har shahararrun mutane da dama a duniya suka tsoma baki, wasu mutanen kuwa ba sa so su zama wani bangare na wannan fafutuka don da suka tsinci ‘yan matan da suka yi koarin tserewa sai suka dawo da su hannun mayakan.

Hakkin mallakar hoto
AFP

“Akwai wata rana da wasu yaran suka gudu. Suna kokarin su tsere amma sun kasa. Sai wadanan mutane suka kamasu. Yadda aka yi suka kama su kuwa shi ne, sun shiga wani shago suka ce a taimaka musu a basu ruwa da biskit.

Sai mutanen suka tambayesu, su waye ku kuma daga ina kuke? Sai yaran suka ce, mu ne wadanda kungiyar Boko Haram ta sace daga GGSS Chibok. Sai daya daga cikin mutanen suka ce ku ba ‘ya’yan Shekau ba ne?”

“Sai suka ba su abinci mai kyau suka ci suka ba su wurin kwana, washe gari kuma suka dawo da su wurinmu, … Bayan sun dawo da su dajin Sambisa da daddare, sai aka zane su kuma zasu kaisu a yanke musu wuya.”

8. Tilastawa a kan su Musulunta

An shaida wa ‘yan matan cewa za a bar su su koma gida wurin iyayensu ne kawai idan dukkansu suka amince za su Musulunta. Wadanda ba su amince ba kuma za su ci gaba da rikesu.

“Sai suka ce wadanda ba su musulunta ba tamkar tumaki da shanu da akuyoyi ne …. za su kashe su

“Sai daya daga cikinsu da ake kira, Malam Abba ya ce duk wadanda ba su musulunta ba su ware gefe daya kar su shiga cikin wadanda suka musulunta. Sai ya ce mu tsaya gefe daya, don za su ware musu wani wuri dabam.

Sai wani mutumin daban yace a’a mu tsaya waje daya. Bayan an yi haka da mako guda, sai sauran ‘yan uwanmu suka ce mu da muka ki zama musulmai, mu ke jawo manat tsaiko wajen komawarmu gida wajen iyayenmu.”

9. Yadda ake daukar bidiyo

Boko haram ta saki bidiyo da dama game da ‘yan matan Chibok. Ga yadda suke shirya daya daga cikin bidiyon:

Hakkin mallakar hoto
AFP/Boko Haram

Image caption

We have blurred the girls’ faces as some former Boko Haram captives and “wives” have been stigmatised after their release

“Sannan kuma akwai wata rana kafin nan, da suka zo suka dauki bidiyon kusan ‘yan mata10 da suka tara su a karkashin bishiyar tsamiya.

Suna kiransu daya bayan daya suna tambayarsu sunansu da sunan iyayensu, sannan sai suka ce juyo wurinmu suka ce, ‘Mun taba cutar da ku? Muka ce a’a. Sai suka ce mana mu fada wa iyayenmu da gwamnati abin da suke mana. Gwamnati da iyayenmu suna cewa suna lalata da mu da kuma gallaza mana”.

“Sai suka kira daya daga cikinmu suka tambayeta, tun daga lokacin da muka daukoku wannan wurin kin taba kwana da wani ko an yi lalata da ke?

“Sai ta ce a’a, suka kara ce mata, ina so ki nunawa iyayenki da gwamnati abin da muke muku da kuma yadda muke kula da ku”.

10. Mayakan Boko Haram na sauraran labarai sosai

Wani lokaci ana shirya bidiyon ne da zarar mayakan sun gama sauraron labarai.

Akwai lokacin da bayan sun gama sauraron BBC Hausa, sai suka kira mu daya bayan daya. Sai suka ce wasu su tsaya wasu su durkusa wasu kuma su zauna, sauka dauki bidiyonmu muna karatun Kur’ani.

Me ya faru da wadanda suka rubuta labarin?

Naomi Adamu da wasu mutum uku da suka rubuta labarin da suka hada da Rhoda Peter, da Saratu Ayuba da kuma Margaret Yama duk an sako a watan Mayu.

A watan Satumba ne, gwamnati ta tura su karatu jami’ar Amurka ta Yola a arewa maso gabashin Najeriya.

Naomi Adamu wacce ita ce ta biyu a gidansu ta ce, ta adana labarin da ta rubuta a lokacin da take cike da kawa-zucin iyayenta.

“Na rubuta abubuwan da suka farun ne don ya zama tarihi,” in ji ta.

“Don ‘yan uwana da iyayena su gani.”

Image caption

Mahaifiyar Naomi Adamu ba ta iya karatu ba amma ta kagu ta san abin da rubutun ya kunsa

Mahaifinta Samuel Yaga ya shaida min cewa bai yi mamaki yadda aka yi ‘yarsa ta yi rubutun a lokacin da suke tsare ba.

“Ko da yaushe a cikin karatu take. Wani lokacin ma littafinta yana kan cinyarta bacci zai dauketa,” in ji shi.

A shafin karshe na littafin ne ta rubuta sunan kannenta biyar, ta kuma rubuta sunan mahaifinta Samuel da mahaifiyarta Rebecca.

Phil Neville na son karbar aikin kocin Everton


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Phil Neville ya taka-leda sau 303 a Everton bayan da ya koma can daga Manchester United a 2005

BBC ta fahimci cewa tsohon dan wasan Everton Phil Neville na son karbar aikin kocin kulob din.

Kulob din Everton ya kori Ronald Koeman ranar Litinin bayan da Arsenal ta doke su a gasar Firimiya.

Rashin nasarar ya jefa kungiyar sahun kulob uku da ka iya faduwa a gasar idan suka kare a haka.

Tsohon dan wasan na Ingila Naville, mai shekara 40, ya taka-leda fiye da sau 250 a Everton a shekara takwas da ya shafe a kulob din.

A baya ya taba zamowa mataimakin koci a kungiyar Valencia ta La Ligar kasar Spaniya.

A ranar Talata ne Everton ta tabbatar da cewa kocin tawagar ‘yan kasa da shekara 23 David Unsworth zai ci gaba da jan ragamar kulob din a matsayin riko.

Zai kuma fara jan ragamar kulob din a wasan da za su yi ranar Laraba a gasar cin kofin Carabou da Chelsea.

Rahotanni sun nuna cewa Ryan Giggs ma ya nuna sha’awarsa kan aikin, hakazalika ana kuma alakanta kocin Burnley Sean Dyche da tsohon manajan Bayern Munich Carlo Ancelotti da aikin na Everton.

Ba bambanci tsakanin gwamnatin Buhari da ta Jonathan – Rafsanjani


Wasu masu fafutika a Najeriya sun soki kamun ludayin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari kan yadda yake tunkarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar, suna cewa idan ana batun yaki da cin hanci da rashawa, babu bambanci tsakanin gwamnatinsa da ta tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Masu sukar lamarin shugaban kasar dai na kafa hujja da wasu bincike da aka gudanar na zargin wasu jami’an gwamnati da aikata almundahana, amma shugaban kasar ya kauda da kansa.

Har ila yau sun ba da misali da rashin daukar matakai bayan ya karbi rahoton binciken sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar Mista Babachir David Lawal.

Da da kuma batun daraktan hukumar leken asiri ta kasar NIA, Ayo Oke tare da wasu jami’an gwamnatin kasar da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Auwal Musa Rafsanjani, wakili a kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transperancy International ya shaida wa BBC damuwarsu:

Latsa alamar lasifika da ke hoton sama don sauraron cikakkiyar hirar da Rafsanjani ya yi da BBC

Yadda mutum-mutumi zai kwace ayyukan da muke yi


Hakkin mallakar hoto
Wang He

Image caption

Matan Tibet na amfani da wayar hannu a wani kauye kusa da tafkin Yamdok a kasar

Kusan akai-akai labaran fasahar kere-kere iri guda ne daga lokaci zuwa lokaci; taken labaran manyan na’urorin Silicon Valley (katafariyar cibiyar hada-hadar kayan sadarwa, musamman na’ura mai kwakwalwa da wayoyin salula na alfarma).

Da dimbin bayanai ba kakkautawa game manyan wayoyin alfarma; mummuna hasashen yadda mutum-mutumin Robot zai kwace ayyukan da muke yi don neman abin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Sai dai a daukacin fadin duniya, ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasahar kere-kere kai-tsaye suke shafar al’ummomin da ba a cika bayar da labaransu ba, kan yadda rayuwarsu ta sauya da aikinsu da kuma yadda suke hulda da juna.

Fasahar kere-kere na haifar da wargajewar tarayya al’umma akai-akai, don haka yake da muhimmanci a gano inda lamarin ke aukuwa.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya muka kaddamar da shirin Duniya ta Daban.

Wato wani sabon sashe a makalun BBC da zai rika bayyana labaran ban mamaki na mutane da ke kowane sako na duniya, wadanda ke amfani da fasahae kere-kere don inganata rayuwarsu – ko kuma suke fafutikar shawo kan matsaloli da kalubalen da fasahar t ahaifar musu.

A yau shirin Duniya ta Daban, mun tattara labarai daga dadaddun al’amuran kundin tarihinmu, kuma a watanni masu zuwa za mu fara wallafa su, kamar yadda aka ruwaito su daga sassan duniya.

Ga wadanda suke sabon shiga, za mu mayar da hankali ne kacokam kan rukunin mata kwararru da ake yin wasannin bidyo a kasar China don shawo kan kyara da bambancin da ake nuna wa jinsin mata a harkar hada-hadar wasannin kwamfuta da ake hada-hadar biliyoyin Dala.

Daga nan za mu tura a bibiyi Kadin al’amuran rayuwa tun daga kasar Somaliya zuwa kwarya-kwaryar saharar yankin Gabashin Afirka.

Al’amarin da zai zamo share fage mai ban mamaki kan yadda ake biyan kudin kasuwanci ta shafukan intanet, har ta kai ga yankin na hankoron zama al’umma adoron kasa da ba sa mu’amala da kudi.

Daga bisani, za mu yi nazarin kamfanin Indiya guda da ke cusda wasannin al’adar Japanawa na Karaoke a fina-finan talabiji na Bollywood da fina-finai don yada ilimin manya.

A wannan zamani da fasahar kere-kere ke kara kaimin wargaza tarayyar al’umma akai-akai, yana da matukar muhimmanci a san inda al’amarin ke faruwa – kuma wadanne mutane suka tasirantu da faruwar lamarin.

Ku biyo mu tafi tare don kutsawa cikin duniya tare da rukunin wakilanmu, wadanda za su kawo muku makaloli da hotunan bidiyo da za su kusanta ku da mutane na hakika, wadanda fasahar kere-kere ta sauya rayuwarsu.

Duniyar nan na da girma. Don haka za mu tabbatar da cewa a rika bayar da muhimman labarai.

Ban manta sunan sojan America ba – Trump


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Uwargidan sojan Amurkan da aka kashe a wani harin kwantan bauna a Nijar ta ce shugaba Donald Trump ya kasa tuna sunan mijin nata a yayin da yake mata ta’aziyya ta wayar tarho.

Amma nan take shugaba Trump ya wallafa rashin yardarsa da wannan furucin na matar a shafinsa na Twitter.

Shugaba Trump ya kira matar mai suna Myeshia Johnson, wanda mijin nata, Saje La David Johnson na cikin sojojin Amurka hudu da ‘yan wata kungiya mai alaka da kungiyar IS suka kashe ranar 4 ga watan Oktoba.

Matar ta fito a wani shirin gidan talabijin na ABC mai suna Good Morning America, inda ta ce “Lallai shugaban ya ce ai mijina ya san makomarsa da ya shiga aikin soji.

Wannan ne karo na farko da ta bayyana halin da take ciki a bainar jama’a dangane da mutuwar mijin nata mai shekara 25 da haihuwa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Uwargida Myeshia Johnson da ‘ya’yan marigayi sojan Amurka – Ah’leeysa mai shekara 6, da La David Jr. mai shekara 2

Ta kara da cewa “Yadda ya bayyana lamarin da salon maganarsa sun fusata ni, kuma sai da nayi kuka.”

Uwargida Myeshia Johnson wacce a halin yanzu take dauke da cikin dansu na uku ta bayyana cewa, “na ji shi yana kame-kame domin ya manta sunan mijina, kuma wannan abu ne da ya kona min rai fiye da komai.”

Shi kuwa shugaba Trump, maida martani yayi a shafinsa na Twitter, inda ya ce: “Na tattauna cikin mutunci da matar marigayi Saje La David Johnson, kuma na fadi sunansa daga fari babu wata inda-inda!”

Wata ‘yar majalisa ce, Frederica Wilson daga jihar Florida kuma ‘yar jam’iyyar Demokrat ta fallasa bayanan tattaunawar da shugaba Trump yayi da matar marigayin, inda ta tuhume shi da rashin tausayawa matar.

Wannan batun ya janyo kace-na-ce tsakanin jami’an gwamnatin shugaba Trump da ‘yar majalisa Wilson, kuma da alama tsugune bata kare ba.

Uwargida Myeshia Johnson ta fada wa tashar ABC cewa bayanan ‘yar majalisa Wilson yayai daidai da ainihin abin da ya faru, wanda ke nuna cewa fadar shugaban Amurka tayi karya kenana game da batun.

Ta ce ‘yar majalisar na tare da ita a lokacin da shugaba Trump ya yi mata wayar ta’aziyyar, kuma ta saurari tattaunawar daga farkonta har kashe.