Rikita-Rikita: Hatsabibi Nnamdi Kanu Fa Ya Bace Bat Inji Yan Sandan Jihar AbiaA wata hira da suka yi da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Alphonsus Okoroigwe, Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Abia, Mr Anthony Okwueze, ya bayyana cewa basu da masaniya akan inda Nnamdi kanu yake.

Labaran duniya.com  ta samu dai cewa jami’in ya bayyana cewa da suna da masaniya da sun fahimtar da shi akan tunani mai armashi, dan haka ya kara da cewa idan manema labarai na da masaniya, akwai bukatar su shaidawa jami’an domin tafiya tare wajan shawo kan lamarin.

Lamarin batan dabon da madugun kungiyar ya yi ya haifar da musayar ra’ayoyi a tsakanin jama’ar jihar, Mr Moses Okoye, wani dan kasuwa ne kuma ya bayyana cewa tana iya yiwuya Nnamdi Kanu na raye ko kuma baya raye ganin yadda sojoji suka kai hari a fadar mahaifinsa, dan haka idan yana raye a taimaka a sake shi.

Yan Kungiyar IPOB Yan Ta’Adda Ne Yayinda Fulani Makiyaya Suka Kasance Masu Laifi Lawai – Lai Mohammed​Lai Mohammed, ministan labarai, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya bata nada Fulani makiyaya a matsayin yan ta’adda ba saboda ayyukansu na masu laifi ne babu dangantaka da ta’addanci. Mohammed ya bayyana ra’ayinsa ne a wata shirin BBC dake mayar da hankali kan Afrika.

NAIJ.com ta lura cewa ministan yayi wannan jawabin ne a madadin ra’ayinsa kan zargi da ake yi wa shawarar gwamnatin tarayya na nadi da tayi wa kungiyar IPOB a matsayin Kungiyar ta’adda, da kuma rashin nada hari da Makiyaya ke aikatawa ba a matsayin ta’addanci.

Yan kungiyar IPOB yan ta’adda ne yayinda Fulani makiyaya suka kasance masu laifi kawai – Lai Mohammed

Yace Gwamnatin Tarayyar Najeriya bata yarda da matsayin Amurka ba kan zancen. 

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba wata kotun majistare dake zaune a karamar hukumar Arewacin Aba a jihar Abia karkashin jagorancin Ogbonna Adiele, ta gurfanar da mambobin kungiyar masu fafutukar Biyafara (IPOB) a gidan yarin tarayya dake Aba.

Ranar Ashura: Yan Shi’A Sun Gamu Da Babban Cikas A ArewaKwamishinan na jihar ya bayyana hakan a lokacin da ya gudanar da taron ga manema labarai a Sokoto, bayan wani zama da shugabannin jami’an tsaro na jihar Sokoto don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

NAIJ.com ta samu cewa Kwamishinan ya ce “Akwai wasu shirye-shiryen taruka da mabiya Darikar Shi’a (IMN) suke yi yanzu haka a jihar Sokoto wanda ake hasashen za su iya tada zaune tsaye a jihar Sokoto, wanda idan ba a dauki mataki ba wadannan shiriruwa da ‘yan Darikar Shi’a za su gudanar za su iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar Sokoto”.

Daga karshe Shugaban ‘yan sanda na jihar Sokoto, Muhammad Abdulkadir ya yi kira ga ‘yan Darikar Shi’a da su guji kowane abu da zai iya haifar da tashin hankali a jihar Sokoto tare da janye zaman lafiya da aka san Sakkwatawa da shi.

Oktoba 1: Yan Igbo Su Bar Arewa, Su Dawo Gida – Lauyoyin Igbo


 


Wasu Lauyoyi masu kula a Onitsha, jihar Anambra sun shawarci yan Igbo mazauna Arewa da su dawo gida yankin arewa maso gabas yayinda ranar 1 ga watan Oktoba da matasan Arewa suka ba yan Igbo ke gabatowa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Lauyoyin, Samuel Chukwukelu, Ben Okoko da kuma Maurice Efobi sun yi sharhin nasu ne yayinda suke magana da manema labarai a Onitsha a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.

NAIJ.com ta ttaro cewa lauyoyin sun shawarci yan Igbo da su bar arewa, imma za’a gudanar da barazanar ko a’a, duk da cewan matasan arewa sun janye wa’adin barin garin da suka sanya.

Yayinda suke shawartan yan Igbo da karda su bari a sake masu abun da akayi masu a 1966, lauyoyin sun bayyana cewa maimakon su sanya ransu cikin hatsari a wata kasa, yan Igbo su dawo kudu maso gabas wanda ya kasance gida a gare su.

Man City ta doke Chelsea har gida


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A minti na 67 ne De Bruyne ya samu nasarar jefa kwallo a gasar Chelsea

Manchester City ta doke Chelsea da ci 1-0 a gasar firimiya da suka yi ranar Asabar a filin wasa na Stamford Bridge.

Ita ma takwararta Manchester United ta samu nasara a kan Crystal Palace da ci 4-0.

Yanzu United da City suna kankankan a gasar, sai dai City ce take saman tebur da bambancin kwallaye, yayin da United take biye mata.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka fafata a gasar kamar haka:

 • Huddersfield 0-4 Tottenham
 • Bournemouth 0-0 Leicester
 • Man Utd 4 -0 Crystal Palace
 • Stoke City 2-1 Southampton

Pogba zai yi doguwar jinya – Mourinho

Aguero ya karya kashin hakarkari

Adikon Zamani: Me ya sa mata ke amfani da tsumma yayin jinin al'ada?


 • Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da Halima Umar Saleh ta yi game da wannan batu, idan kuka latsa alamar lasifika da ke hoton sama.

Batun al’adar da mata ke yi na jinin haila duk wata, wani al’amari da ba a faye tattaunawa a kansa ba, musamman a kasashen da ke girmama al’adu kamar Najeriya.

Hakan ce ta sa mata ke shiga wani yanayi na rashin sanin ainihin abin da ya kamata su yi ta fuskar kula da kansu don gudun kamuwa da wasu cututtuka a sakamakon rashin tsafta.

Wasu alkaluma da kungiyar WaterAid mai fafutukar ganin an samar da tsaftataccen ruwan sha da yanayi mai tsafta a rayuwar bil-Adama ta fitar a watan Mayun bana, sun nuna cewa a kullum mata kusan miliyan dari takwas ne ke al’ada; sai dai galibinsu sukan rika boye-boye da kuma fuskanci muzgunawa a wannan lokaci.

A cewar kungiyar an yi watsi da bukatun mata da ‘yan mata game da al’ada, lamarin da ke haifar da asara iri-iri ga al’umma, kama daga asarar damar zuwa makaranta zuwa ga ta tattalin arziki.

Shin wadanne bukatu mata ke da su a lokacin al’ada?

Me ya kamata su yi? Wanne taimako ya kamata al’umma ta ba su?

Kungiyar ta ce mace daya cikin mata uku a ko ina a fadin duniya ba sa samun damar amfani da tsaftataccen ban daki a yayin da suke al’ada, wanda hakan yana nufin zai yi matukar wahala su samu walwala a lokacin da suke al’adar.

Da yawan mata musamman wadanda ke zaune a karkara ko wadanda ba su da hali sosai na amfani da kyalle ko tsumma a yayin da suke al’ada.

Sai dai wani bincike ya gano cewa, amfani da tsumma ko kyalle da mata ke yi wajen yin kunzugu a lokacin da suke jinin al’ada, na janyo kamuwa da cutuka da dama.

Dokta Yalwa likitar mata ce a asibitin Maitama da ke birnin Abuja, ta shaida wa BBC cewa, daga cikin cutukan da ake kamuwa da su sakamakon amfani da tsumma musamman marar tsafta a matsayin kunzugu, akwai kuraje da kaikayi, wani lokacin ma har da fitar da ruwa mai wari daga al’aurar mata.

Hyeladzira Shalangwa, jami’a a kungiyar WaterAid ta ce duk da cewa dalilai na rashin sukuni ke sa mata amfani da kyalle ko tsumma maimakon audugar mata ta zamani, hakan ba zai zama dalilin da zai hana su tsaftace shi ba ta hanyoyin da suka dace don magance kamuwa da cututtuka.

Dokta Yalwa ta ce: “Yana da kyau matan da ke amfani da kyalle su dinga sauya shi kamar sau uku a rana, su kuma dinga wanke shi da ruwan zafi da gishiri a kuma goge shi ko da da dutsen dugar gargajiya ne na gawayi, domin hakan zai taimaka wajen kashe kwayoyin cutar da suke kai.”

Mutane da dama dai na ganin tun da ba za a iya shawo kan wannan matsala ba saboda ganin cewa tana da alaka da wadatar mutum, to yana da kyau masana a harkar lafiya su dinga wayar da kai da ba da shawarwari ga mata kan yadda za su dinga tsaftace kyallayen da suke amfani da su.

Zan Kasance a Majalisar Dattawa Har Abada – Bukar Ibrahim


A jiya Alhamis, 28 ga watan Satumba, dan majalisa mai wakiltan jihar Yobe ta gabas kuma tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya bayyana cewa zai dawwama a majalisar dattawa har abada.

Sanata Bukar ya taba rike mukamin gwamnan jihar Yobe har sau uku kafin a zabe shi zuwa majalisar dattawa a shekarar 2007 ya koma a 2011, aka kuma sake zabensa a 2015.

A yanzu haka dai, Sanatan na rike da matsayi na shugaban kwamitin majalisar dattawa akan sauyin yanayi.

Haka kuma, uwargidan Sanata Bukar, wato Hajiya Khadija Bukar Ibrahim ta kasance a majalisar wakilan Najeriya har sau uku kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada ta a matsayin ministar harkokin waje a shekara ta 2015.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Sanata Bukar Abba ya fadi cewa shi ne Sanatan da zai kasance a majalisar dattijai na har sai ya yi halinsa a lokacin da yake bada tasa gudunmawar a zauren majalisa a lokacin da ake fafatawa akan batun yadda za a gudanar da shagalin cikar Najeriya shekaru 57 da samun ‘yancin kai.

“Muna godiya ga Allah SWT kuma muna godewa ‘yan Najeriya. Mai girma shugaban majalisa, ina mai matukar farin cikin sanar da wannan majalisa cewa ni da wannan majalisar mutu ka raba,” inji Sanata Bukar.

Ya kara da cewa, zan cika shekaru 68 a ranar Lahadi mai zuwa, a wannan rana kuma Najeriya zata cika shekaru 57 da samun ‘yancinta. Na samu nasara a harkokina tun ina karami a matsayin dan makarantar firamare, sakandire, dalibin jami’a, sannan a harkokin siyasa ta a matsayin kwamishina, a matsayin zababben gwamna da kuma a matsayin sanata

Shugaban majalisar dattijan, Sanata Abubakar Bukola Saraki a lokacin da yake tsokaci kan jawabin Sanata Bukar Abba Ibrahim, ya fada cikin raha ga ragowar sanotocin jihar Yobe biyu cewa ” Sanata Ahmad Lawal da Sanata Muhammad Hassan, sai ku kiyaye fa, Sanata Bukar mutuwa ce za ta raba shi da majalisar nan”

Shanun Najeriya Ne Ke Samar Da Madara Mafi Karanci A Duniya – Audu Ogbeh– Minitsan harkokin noma da raya karkara ya ce shanun Najeriya basu samar da madara kamar yadda shanun wasu kasashe ke samarwa

– Ya ce shanun kasashe irin su Amurka na iya samar da lita 100 na madara a kowace rana alhali shanu Najeriya na samar da kasa da lita 1 kacal

Minitsan harkan noma da raya karkara, Audu Ogbeh, ya ce shanu ‘yan gida Najeriya su ne mafi lalacewa wurin samar da madara a duniya.

Minitsan ya fadi haka ne a wurin bikin cika shekaru 79 da kafuwar kulob din Ikoyi. Ogbeh ya ce ko wace saniya na wasu kasashe na iya samar da lita 100 madara a ko wace rana alhali saniya ‘yar Najeria kasa da lita 1 kacal ta ke samarwa.

Shanun Najeriya ne ke samar da madara mafi karanci a duniya – Audu Ogbeh 

Minitsan ya yi nuni ga yadda karancin ruwan sha ke kawo karancin samar da madaran. A cewar sa ko wace saniya a kasar Amurka ta kan sha ruwa lita 100 a ko wace rana alhali ita saniyar Najeria da kyar ta ke samun shan lita 2 a kowani mako.

Don haka ya dora laifin karancin madaran akan rashin mayar da hankali wurin kiwon dabbobin. Ya bada shawaran a killece dabbobin yadda za’a samu ba su kyakkyawar kulawar da suke bukata.

Abokan Amaechi Sun Bashi Laifin Faduwar APC A Zaben Gwamna, Da Na Kananan Hukumomi A RibasJam’iyyar APC reshen jihar Rivas ta na fuskanatar kalubale game dan takarar, da za ta tsayar na zaben gwamna a 2019.

Shugabanin APC na kananan hukumomin jihar Rivas 23 sunce idan jam’iyyar su ta na son ta samu nasara a zaben 2019, dole ta tsyar da dan takarar da mutane suke so.

Senata Magnus Abe, kuma jigo a Jam’iyyar APC ya bayyana takaicin akan rashin kokarin jam’iyyar su a zaben 2015 da yagabata a wani taro da kungiyan magoya bayan sa suka halarci shi.

Abokan Amaechi sun bashi laifin faduwar APC a zaben gwamna, da na kananan hukumomi a Rivas

Kungiyan sun ba Minista sufuri, Rotimi Amaechi laifi, saboda tsayar da daraektan NIMASA, Dakuku Peterside a matsayin dan takarar gwamnan jihar Rivas a zaben 2015.

Sun ce Peterside bai da farin jinin da zai iya kada Nyesome Wike a zaben.

Jigajigan jam’iyyar APC na jihar Rivas sun ba Amaechi laifin daura ma jam’iyyar su yan takaran da ba su da karfin cin zabe a jihar a Rivas.

Biyafara: Jigo A Jam’Iyyar PDP Onuesoke Ya Caccaki Shehu Sani Game Da Al’Amarin IPOB Da Nnamdi Kanu

 

Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon dan takarar gwamanan jihar Delta, Sunny Onuesoke, ya caccaki senata Shehu Sani, akan maganar da yayi na cewa kasar Amurka ba ta da izinin fada ma Najeriya kungiyar da za ta ayyana a matsayin kungiyan yan ta’adda.

Bayan gwamanatin Najeriya ta ayyana kungiyan IPOB a matsayin kungiyan yan ta’ada, kasar Amurka ta ce ba ta amince da hukunci ba.

Shehu Sani ya fito yay watsi da maganar Amurka da cewa ba ta da hurumin bane fada ma Najeriya abun da za ta yi.

Biyafara : Jigo a jam’iyyar PDP Onuesoke ya caccaki Shehu Sani game da al’amarin IPOB da Nnamdi Kanu

Onuesoke wanda ya bayyana ra’ayin sa ta mai magana da yawun sa, Stanley Efe ya ce martanin Sani akan kin amincewa da hukunci ta’adanci ga kungiya IPOB da kasar Amurka ta yi kabilanci ne kawai.

Onuesoke yana mamakin haramta kungiyan IPOB da gwamantin tarayya ta yi, kuma an bar makiyayan Fulani suna ta kashe kashe da yi wa mata fyade amma babu wanda ke magana.

Duk irin munafurcin da za ayi a kasar nan, duniya da kasar Amurka sun san yan Kungiyan IPOB ba yan ta’adda bane.

Sai Abdulmuminu Ya Bada Hakuri Zai Dawo Majalisa, Inji ‘Yan Majalisa

Majalisar wakilai a ranar alhamis ta ce tsohon ciyaman na kwamiti da aka dakatar daga aiki, Abdulmuminu Jibrin sai ya bada hakuri kafin a dawo da shi cikin majalisa. Ciyaman din kwamitin a harkar yada labarai, Abdulrazaq Namdas ya sanar da hakan a taron da suka yi a Abuja dalilin da yasa Jibrin bai dawo majalisa ba bayan shafe shekara daya da yayi tun san da aka dakatar da shi.

Ciyaman din ya sanar da cewa Jibrin bai cika kwanakin shi 180 da aka zartar zai yi ba, sannan ya ce dole Jibrin sai ya shaidawa majalisar in har ya gama kwanakin da aka yanke masa a rubuce.

Sai ya cika wasu ka’idoji da majalisar ta gindaya masa sannan kuma ya cika kwananki 180 din na dakatar da shi da aka yi. Har da sharadin sai ya rubuto wasikar bada hakuri kafin a dawo da shi cikin majalisa.

A shafin Jibrin kuwa na Tuwita, ya rubuta cewa ‘shekara daya kenan da aka dakatar da shi a aikin sa na mazabar sa a majalisa a cikin shekara hudu ta tsarin mulkin majalisa da cewar a Najeriya ne kadai za a yi irin wannan.’

Jibrin kuwa ya dau alwashin cewa zai iya kokarin sa wajen yin aiki mai kyau a majalisa da Najeriya ma baki daya saboda in za a tuno shi a tuno shi a mutum adili.

Ya bayyana maganar da ciyaman din kwamitin yayi a matsayin cin fuska ga mutanen mazabar sa. Tuni ‘yan mazabarsa ta kiru da bebeji sun fito a kan kin amicewar su ta dakatar da shi da aka yi.

Me zai faru idan aka fara yaki da Koriya ta Arewa?


Wadansu masana harkokin tsaron Amurka da Koriya ta Arewa sun yi wa BBC karin bayani game da abin da zai faru a makonni farko na fara yaki tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

“Kimanin mutum miliyan biyu za su rasa rayukansu a makonni farko na fara yaki tsakanin kasashen biyu,” kamar yadda tsohon sojan Amurka, David Maxwell ya yi hasashe.

Har ila yau, masanin ya ce yakin zai jawo a tafka mummunar asara tsakanin kasashen biyu musamman idan Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya yi amfani da makamin Nukiliyarsa.

Dalilin Da Yasa Ba Zan Yi Murabus Ba – Mugabe


 


Mugabe ya alakanta wannan yaudara da wata hikaya ta cikin littafin addininsu, inda ya kwatanta wannan ‘yan jam’iyyar ta su ta ZANU-PF da yaudara da kuma cin amana, sanadiyar yunkurinsu na ganin cewa shugaban ya yi murabus daga shugabancin kasar.

Naij. com ta ruwaito cewa, shugaban kasar na Zimbabwe mai shekaru 93 a duniya ya karbi shugabancin kasar tun lokacin da kasar ta samu ‘yan cin kai a shekarar 1980.

Shugaban ya bayar da sanarwar ba zai sauka daga kujerar mulkin kasar ba a yayin wata ziyarar jaje da yakai sanadiyar rashin wani mamba na jam’iyyar ta su da rai ya yi halinsa, inda kuma ya tuhumci wasu mambobin jam’iyyarsu da goyon bayansa a don anin idanu da kuma yi masa zagon kasa a bayansa.

Shugaban kasar ya cigaba da kawo hikayoyi da kuma kissoshi daga cikin littafin na su tare da alakanta mambobin jam’iyyar da wannan hikayoyi. Ya kuma ce, “mulkin kasar nan ba karba ko kwacensa ya yi ba, zaben sa aka yi, saboda haka kujerar da yake kai a yanzu ta al’ummar kasar ce”.

“Idan lokaci na ya yi zan ajiye mulkin, kuma na yiwa ‘yan uwana na kasar Zimbabwe godiya, sa’annan na baiwa wani damar gajiyar kujera ta. Amma a yanzu ni ke da ta cewa”.

Sarkin Katsina Ya Nemi Buhari Ya Amince Da Dokar Kafa Dogarawan Tsaro

 


Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, ya nuna goyon bayan sa dari-bisa dari ga kudirin da aka zartas a majalisar tarayya domin amincewa da kafa dokar kafa Dogarawan Tsaro.

Kudirin dai zai amince da sauya Dogarawan Tsaro daga masu zaman kan su zuwa wani fannin jami’an tsaro na gwamnati.

Wadanda ke goyon bayan wannan sabon tsari na ganin mayar dasu karkashin gwamnati zai samar wa matasa da dama aikin yi.

Dalili kenan su ke cewa matsalar biyan su albashi ma kan sa ko an fara aiwatar da shirin, to ba zai iya dorewa ba.

Haka nan kuma wannan kudiri ya na kan shan suka daga hukumomin tsaron Najeriya, musamman ganin cewa shugaban rundunar Dogarawan Tsaron, Dikson Akoh na a gaban alkali ana tuhumar sa da harkalla, dakasharama da kudade da kuma uwa-uba damfara.

Sai dai kuma baya ga mambobin majalisar tarayya da ke goyon bayan kudirin, shi ma ministan harkokin matasa da al’adu, Solomon Dalung yana goyon bayan sa, kuma ya yi roko ga Shugaba Buhari da ya amince da kudirin.

Shi ma Mai Martaba Sarkin Katsina, ya bi sahun masu goyon bayan tsarin, kuma ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya amince da tsarin, ya na mai cewa dogarawan kiyaye zaman lafiya su na da matukar amfani kuma za su kara jaddada hanyoyin wanzar da zaman lafiya a cikin kasa.

Abuja: Kotun Daukaka Kara Ta Umarci Dasuki Ya Bayyana A Shari’Ar Olisa Metuh

 

Kotun daukaka kara shiyar birnin Abuja ta umarci tsohon mai ba da shawara a kan tsaron kasa, Sambo Dasuki, da ya bayyana a gaban kotun a shari’a na tsohon kakakin jam’iyyar adawa ta PDP, Olisa Metuh.

Lokacin da aka ba da umurni, kotun ta yanke hukunci wanda ta saba da hukuncin babban kotun tarayya, wanda ta ki amincewa da bayyanar Dasuki.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, lauyoyin Mista Metuh sun bukaci Mista Dasuki ya kasance shaida a kotu tun da daga ofishinsa ne kudin da ake zargin Metuh ya fito.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Satumba cewa, hukuncin babban kotun tarayya shiyar Abuja wanda Okon Abang ke shugabanci, ba daidai ba ne, cewa Dasuki ba zai iya ba da shaida a wannan al’amarin ba.

Kotun ta kuma umurci ‘yan sandan farin kaya, wanda Mista Dasuki ke hannun su fiye da shekara daya, don su gabatar da shi a ranar shari’ar.

Zahra Buhari-Indimi Tayi Korafi Game Da Rashin Kyan Asibitin Aso RockGa dukkan alamu Zahra na da matsala da yanayin asibitin Aso Rock, har ta kasa boye bacin ranta a kan haka.

A rubutun da ta yada a shafin ta na Instagram, diyar shugaban ta nuna bacin ranta bisa yanayin asibitin inda ta bayyana cewa asibitin na cikin mumunar yanayi tunda babu kayan aiki.

A rubutun nata ta yi tambaya kan abinda yasa marasa lafiya da ma’aikatan asibitin suke siyan kayan aiki bayan an ware kudi kimanin naira biliyan 3 don amfanin asibitin.

Zahra Buhari-Indimi tayi korafi game da rashin kyan asibitin Aso Rock

Abin da ya sa nake damuwa da Nigeria – Bill Gates


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Arewacin Najeriya yana fuskantar babban kalubalen kiwon lafiya’

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu.

Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan al’umma a nahiyar Afirka.

“Wannan ne ya sa gidauniyarta ta Bill & Melinda Gates Foundation take ci gaba da aikace-aikacenta a can,” kamar yadda ya bayyana.

Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin kiwon lafiya a yankin arewacin kasar.

“Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun ‘yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da Borno a kokarinmu na ganin mun magance kalubalen kiwon lafiya a yankin,” in ji shi.

Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan raya a fadin kasar.

Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote.

Saraki Ya Koka A Kan Kara Tsamari Da Matsalar Shaye-Shaye Ke Kara Yi A Tsakanin Matasan ArewaShugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya nuna damuwarsa a kan muguwar dabi’ar nan ta shan miyagun kwayoyi dake kara kamari tsakanin matasan arewa.

Saraki ya koka a kan kara kamari da matsalar shaye-shaye ke kara yi a tsakanin matasan arewa

Saraki ya ci alwashin shawo kan matsalar ta hanyar yin dokoki a majalisa da zasu magance matsalar tare da kiran ‘yan Najeriya musamman matasa da suyi watsi da shan kwayoyi domin hakan ma na dakile Najeriya.

Saraki ya bayyana hakan ne a jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na kafar yada labarai ta tuwita.

A ranar alhamis ne dai ‘yan majalisar dattijai suka sahalewa kudirin daurin rai-da-rai ga masu aikata laifin garkuwa da mutane wucewa karatu na biyu. Kudirin ya haramta garkuwa da mutane, tsare mutum domin karbar kudi, tare da ayyana hukuncin daurin shekara 30 ga duk wanda ya hada baki da masu aika irin wadannan laifuka.

Me ya sa Nigeria ke son cire shingayen 'yan sanda a tituna?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hukumar ‘yan sanda ta ce ta dauki matakin ne domin a rage yawan lokacin da ake batawa a shingayen hanya da kuma saukaka yadda ake gudanar da aiki.

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ba da umarnin cire dukkan shingayen binciken ‘yan sanda a fadin kasar da gaggawa.

‘Yan Najeriya da yawa za su yi maraba da wannan labarin domin galibi shingayen tamkar hanyar damar karbar na goro ne daga matafiya da kuma masu jigilar kayayyaki.

Amman sanarwar ‘yan sandan ta ce an dauki matakin ne domin a rage lokacin da ake batawa a shigayen binciken da kuma saukaka yadda ake gudanar da kasuwanci.

Me nene ke faruwa a shingayen bincike?

Haduwa da dan sanda a hanya ka iya gajiyar da mutum.

Bindigar Ak47 da suke sabewa a kafada ba ta iya kwantar wa mutum hankali cewa yana cikin tsaro yadda yadda ya kamata.

Yawanci ‘yan sanda maza ne, kuma za su bukaci mutum ya bayyana kansa ya kuma fitar da lasisin tukinsa.

Sannan za su nemi su dubi wajen duba kayan mutum.

Daga nan za su tabbatar da cewar kana da dukkan abin da doka ta tanada – na’u’rar kashe wuta a ko wacce mota, da wata alamar da ake sakawa a hanya idan mota ta baci, da inshora, da takardar cancantar mota a kan hanya da kuma sauran takardu.

Duk abin da aka rasa ka iya sa a bai wa mutum zabi tsakanin bin dan sandan zuwa caji ofis ko kuma ba da na goro domin ya taimaka a kashe wutar matsalar nan take.

Ko kana da cikakkun abubuwan da ake bukata, wannan ba ya nufin za ka iya ci gaba da tafiyarka.

Jami’in ‘yan sandan zai tambaya in kana da ‘abin da za ka bai wa yaran’, ko kuma ya nuna maka irin zafin da ake yi (saboda haka yana bukatar kudin shan ruwa).

Wannan ba wani abun da ke faruwa jifa-jifa ba ne, ya zama ruwan dare ta yadda har ‘yan barkwancin Najeriya sun sha yin shaguben yadda ‘yan sanda ke neman na goro.

Me ya kamata a gujewa a shingen bincike?

Amsa waya a wurin shingen bincike ka iya janyo karin bata lokaci.

Jami’an tsaro ba sa jin dadi su ga mutane suna waya a gabansu.

Lamarin ka iya kamari idan ka nemi ka dauki bidiyon abin da ke faruwa a wurin.

Ba sa lamuntar a dauke su a bidiyo.

A shekarar 2013 an kori Sajen Chris Omeleze bayan wani mutum ya dauki hoton bidiyonsa yana kokarin karbar na goro a filin saukar jirgi na Legas.

Mutumin ya wallafa bidiyon a Intanet.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

An kalli bidiyon sosai a shafukan sada zumunta kamar yadda Tomi Oladipo ya ruwaito

Ta yaya za ki gane shingen da aka kafa bisa doka?

Babu wata takamammiyar hanya ta bambanta tsakanin shingen gaske da kuma hanyar kwace wa mutane kudi.

Za ki iya ganin durom da launin ‘yan sandan Najeriya – shudi da dorawa da kuma kore- a tsakiyar hanya.

Da daddare hasken tocila ne kawai zai nuna maka cewar akwai shingen bincike a wurin.

Idan ka yi rashin sa’a kuma, zai iya kasancewa ‘yan fashi ne.

Yayin da aka gindaya wasu shingayen domin kama masu laifi, sauran shingayen hanyoyi ne na samun kudi daga ‘yan sanda masu karbar na goro.

Yawanci wadannan na tasowa ne da dare da karshen mako.

Shugaban ‘yan sandan ya ba da umarnin cewar ‘yan sanda su saka kayan aikin da ke dauke da sunayensu da lambobin aikinsu.

Saboda haka bincike a shafin ‘yan sandan zai iya taiamaka wa wajen gano ‘yan sandan domin a kai kararsu.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wa yake kiyaye tsaron Najeriya?

Adadin cin hanci?

Alkalluman hukumar kididdiga ta Najeriya kan cin hnaci da rashawa na shekarar 2017, sun ce kashi 32 cikin 100 na ‘yan Najeriya da suka mallaki hankalinsu wadanda suka yi mu’amala da ma’aikatan gwamnati sun ce an tamabaye su na goro.

Hukumar kididdiga ta kasar NBS, ta ce an biya jumullar naira miliyan 82 naira ga jami’an gwamnatin Najeriya a wata 12 da suka wuce.

Wannan na daidai da cin hanci daya ga mutum daya a ko wacce shekara.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Direbobin manyan motoci da tasi su ne neman na goro ya fi shafa

Cin hancin da ake nema daga direbobi ya kan kai naira 20.

Direbobin manyan motoci da tasi su ne aka fi karbar na goto a wajensu.

Ba kasafai irin wadannan mutanen ke kalubalantar hukumomi ba kuma suna ba su da lokaci, saboda haka sun gwammaci su biya cin hanci.

Rahoton kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa na shekarar 2013 ya ce kashi 92 cikin 100 suna ganin ‘yan sanda sun yi dumu-dumu cikin cin hanci da rashawa.

Shin hana kafa shingen binciken zai yi nasara?

Wannan ba shi ne yunkurin farko na hana kafa shingen bincike a Najeriya ba.

A shekarar 2012, shugaban ‘yan sandan lokacin Mohammed Dahiru Abubakar, ya ba da irin wannan umarnin, kuma an dauke shigayen bincike 3,500.

Duk da haka, shingayen sun koma inda aka cire su.

Wannan sabon umarnin wani yunkuri ne inganta gamsuwar mutane da ‘yan sanda.

Sanarwar ta ce an tura wasu tawagogi na musamman domin domin kamawa da bincike da kuma hukunta duk wani dan sanda da ya saba wa wannan umarnin.

Yanzu ya zama dole ga ko wacce rundunar ‘yan sanda ta nemi yardar sufeto janar na ‘yan sanda kafin ta kafa shingaye.

Wannan daya ne daga cikin matakan da sufeto janar na ‘yan sanda ya dauka domin ya inganta mutuncin ‘yan sanda.

Amman zai dauki lokaci mai tsawo tare da kwararan dalilai kafin yawancin ‘yan Najeriya su yarda da taken da ake rubutawa a ofisoshin ‘yan sanda: “Dan sanda abokinka ne.”

Har Yanzu Makarantu Da Yawa A Yankin Da Yakin Boko Haram Ya Shafa A Rufe Suke – Hukumar UNICEFShekara ta zagayo da dalibai zasu koma makaranta wasu kuma zasu fara zuwa, amma a sanadiyyar yakin Boko Haram sama da rabin makarantu a jihar Borno a rufe suke, a bangaren da yakin Boko Haram ya shafe su, anda zai sanadiyyar yara da yawa su rasa ilimin boko.
Hukumar kula da kare hakkin yara ta duniya (UNICEF) ta fitar da rahoton cewa sama da rabin makarantu a yankin da yakin Boko haram ya shafa har yanzu a rufe suke, yayin da yakin ya shafe tsahon shekara 9 ba a samu zaman lafiya a garin ba.

Yara da yawa sun rasa ilimin boko sakamakon yakin Boko Haram – Hukumar UNICEF

Daga wani bincike kuwa an nuna yadda rashin ilimi ne yayi sanadaiyyar wasu daga ‘yan yankin arewa maso gabashin Najeriya shiga kungiyar ‘yan Boko Haram. Rashin samun ilimi zai iya zama wani abu da zai yunkura samun cigaba da ta’addancin Boko Haram.

Tun shekarar 2009 a kididdigar da majalisar dinkin duniya tayi ya nuna sama da mutane 20,000 sun rasa ran su da kuma a kalla mutane miliyan 10 da suke bukatar tallafi.

A kalla makarantu 1,400 ne suka ruguje a snadiyyar yakin, malamai kuwa sama da dubu biyu sun rasa ran su, wasu kuwa sun rasa muhallin su.

Duk da cewa hukumar UNICEF tana kokari wajen kafa makarantun da yara zasu fara samun ilimi, amma har yanzu kungiyar bata cinma nasara ba.

Ga shi an sami barkewar cutar kwalara a sansanin ‘yan gudun hijira da kuma wasu kauyuka a jihar Borno. Yunwa da rashin lafiya na cikin matsalolin da ‘yan arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta, wanda kungiyar UNICEF da wasu kungiyoyin suke kokarin magancewa.

'Rashin jin kamshi na da alaka da cutar mantuwa'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Masu ilmin kimiyya a Amurka sun ce rashin jin ƙamshi ko wari ka iya zama alamun farko na kamuwa da cutar mantuwa.

An gwada kusan mutum dubu uku a wani ɓangare na wani dogon nazarin masu bincike daga jami’ar Chicago.

Sun ƙarƙare cewa mutanen da ba za su iya tantance ƙamshin alewar minti ko na lemo ko na furanni ko kuma ƙarnin kifi ba, na da ninki biyu na yiwuwar kamuwa da cutar matsananciyar mantuwa bayan shekara biyar.

Daya daga cikin masu binciken Farfesa Jayant Pinto ya ce daina jin ƙamshi ko wari wata babbar alama ce cewa an gamu da matsala.

Ya ce akwai tarin nazarce-nazarcen da ke nuna cewa gaɓoɓin karɓar saƙwanni na jiki na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar manyan mutane da tsoffi.

Haka ma baiwar gani da ji, da kuma a yanzu shakar ƙamshi ko wari na ba da gudunmawa wajen tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Kuma wata kafa ce ta tantance mutanen da ke cikin hatsarin kamuwa, in ji Farfesa Pinto.

Matashin Yaro Ya Bindige Mahaifinsa Saboda Ya Ki Siya Masa Babur A Filato


 


Wannan mugum yaro ya harbe babansa ne da bindiga yayin da yake kwance a karkahsin bishiya, yana barcin rana a kauyen Dorowa, a kauyen Vwang Gwong, cikin karamar hukumar Shendam.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Alkalin kotun, mai shari’a A.I Shoms ya yanke hukuncin bayan ya kama da Yakubu da laifin kisan mahaifin, inda ya danganta laifin da sashi na 221 na kundin tsarin mulki.

“Game da laifin da Yakubu ya aikata na kisan mahaifinsa Domsing Yakubu, don haka muka yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya.” Inji Alkali.

Lauya mai kara, Gideon Azi ya shaida ma kotu cewa Yakubu ya amsa laifin kisan mahaifinsa, inda yace masa ya kashe baban nasa ne sakamakon yaki siyan masa babur.

Yakubu ya bukaci mahaifinsa ya siyan masa babur dinne, bayan ya girbi sama da doya guda dubu daya a daminan bana, wanda ya siyar a kasuwan kauye.

El-Rufai Ya Ce Ya Samu Iko Daga Dokar Jihar Ya Kama Matasan Arewa Da Suka Ba Igbo Wa’Adin 1 Ga Oktoba


 


Rahotanni sun kawo cewa a yanzu gwamnatin ihar Kaduna ta sanar da samun iko na kama yan kungiyar matasan arewa da suka ba yan kabilar Igbo mazauna yankin wa’adin barin gari a ranar 1 ga watan Oktoba.

A cewar jaridar Premium Times Hausa, gwamnan na jihar Kaduna ya roki mazauna ihar dasu bayar da bayani kan inda suka san za’a ga daya daga cikin su ko kuma gidajen su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da sa hannun kakakin sa Samuel Aruwan a Kaduna.

Tun a watan Yuli da kungiyar matasan Arewa suka ba yan kabilar Igbo mazauna yankin Arewa wa’adin barin garin inda gwamna Nasir El-Rufai ya sanar cewa sai ya taso keyar wadannan matasa da shugabannin kungiyoyin da suka sa hannu a takardar.

Mutane sun fito sun nuna rashin goyon bayan wannan kudiri na gwamna El-Rufai cewa tunda kungiyar tsagerun Biyafara suke yi ta muzguna wa ‘yan Arewa bai taba nuna fushinsa ko ya fito yayi nuna rashin giyon bayansa akai ba sai da matasan Arewa suka fito suka fadi nasu matsayar.

El-Rufai ya zaiyano bayanai da sashen da ya ba shi ikon kama wadannan matasa da gurfanar dasu a gaban kuliya.

Sergio Aguero Yaji Ciwo A Hatsarin Mota
An ba da rahoton cewar dan kasar Argentina mai shekara 29 yana hanyar shi ta zuwa filin jirgin sama ne a motar haya bayan ya kalli wakar da mawaki Maluma ya yi.

City ta ce “ya kasance a kasar Holland ne a lokacin hutunsa, kuma ya ji raunuka”.

Ana tsammanin Aguero ya koma Manchester ranar Juma’a, kuma likitocin City za su gwada shi kafin tafiyarsu wasan gasar Firimiya a Chelsea ranar Asabar.

‘Yan sanda a Amsterdam sun tabbatar wa BBC cewar mutum biyu ne cikin motar tasi din da ta yi hatsari a unguwar De Boelelaan da ke cikin birnin.

Kafin hatsarin dai, dan kwallon ya wallafa hotonsa da mawaki Maluma a shafinsa na Instagram da sakon da ke cewa: “ina godiya da gayyatata”.

Tsohon kulob din Aguero, Independiente, ya tura wa dan wasan sakon fatan alkhairi ta shafin Twitter, yana mai cewa”Kuzari tare da warkewa cikin gaggawa ga aguerosergiokun! Ilahirin @Independiente na tare da kai a wannan mawuyacin lokaci.”

Kuma ya tallafa wa kungiyar Pep Guardiola ta hau saman teburin gasar Firimiya tare da yin nasara a wasanninsu biyu na farko a gasar zakarun Turai.

Sauya fasali ya fi dacewa ba raba Nigeria ba – Ohaneze


Jama’a dadama a Najeriya na kiraye-kirayen sake fasalta kasar, ciki har da mutanen kudu maso gabashin kasar wadanda suke ganin sake fasalta kasar ne zai magance dumbin matsalolin da ake fama da su.

Wannan batun ne ma ya kai ga majalisar wakilan Najeriya ta kafa wani kwamiti domin duba batun.

Cif John Nwodo shi ne shugaban kungiyar. Ya ziyarci ofishinmu na Landon a kwanakin baya, ya kuma tattauna da Editan Sashin Hausa na BBC, Jimeh Saleh a kan abin da ya sa suke goyon bayan sake fasalin mulki a Najeriya, da kuma adawar da suke yi da ballewar yankin Biafra daga kasar.

Ya bayyana cewar sauya fasalin Najeriya shi ya fi dacewa da muradun ‘yan kabilar Igbo na nan gaba maimakon fafatukar kafa kasar Biafra.

Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da Editan BBC Hausa Jimeh Saleh ya yi da John Nwodo, idan ku ka latsa alamar lasifika da ke sama.

Ban Gamsu Da Shugabancin Buhari Ba – Buba Galadima


A hirarsa da BBC Buba Galadima ya ce a yanayin salon jagorancin jam’iyyar da kuma mulkin da ake yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.

Ya ce abin takaicin shi ne Allah ya jarrabi Shugaba Muhamadu Buhari da rashin lafiya, kuma dadin dadawa sai jam’iyyar ta kasa samar da wani kyakkyawan shugabanci, wanda duka wadannan abubuwa sun shafi yanayin mulkin.

Game da rashin ba shi wani mukami ko tafiya da shi a gwamnatin Buharin, Buba Galadima ya musanta cewa akwai wani sabani a tsakaninsu da Shugaban, wanda ake rade-radin cewa saboda hakan ne ba a tafiyar da shi.

Ya ce a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka assasa tafiyar har ta kai an kafa gwamnati ba ya bukatar har sai ya yi kamun kafa, ko wani tumasanshi a wurin Shugaba Buhari kafin a san da shi har a ba shi wani mukami.

Injinyan ya ce rashin ba shi mukami bai dame shi ba, domin kusan duk wadanda suka faro tafiyar tabbatar da kasancewar Buharin ya zama shugaban kasa, babu wanda aka ba wa wani mukami.

Don haka ce shi ba komai ba ne, yana mai shagube da cewa: ”Ni ai a cikin miya ban kai komai ba.”

Kawo yanzu babu wani martani daga bangaren Shugaba Buhari ko kuma jam’iyyar APC.

Dan siyasar ya dangantaka ba shi mukami ga lamari na Ubangiji, yana mai cewa duk abin da mutum ya samu Allah ne, haka kuma in mutum ya rasa Allah ne, amma ba ya nadamar gwagwarmayar tabbatar da Buhari Shugaban kasa, don bai samu mukami ba.

Ya ce ba wata gafara da zai nema daga Shugaban, ko zai waiwaye shi da mukami, domin shi a saninsa ba wani abu da ya yi na sabamasa.

Game da dantakarar da Buba Galadiman zai mara wa baya a zabe na gaba na 2019, ya ce lokaci bai yi ba tukuna, amma idan lokacin ya zo zai karkata ga ra’ayinsa, ko da kuwa za a kashe shi ne.

Sai dai ya ce in har Buhari ya neme shi a tafiyar 2019, idan zai yi takara zai iya mara masa baya, amma ba wai haka kawai ya kai kansa tafiyar ba, ba tare da an gayyace shi ba.

Amma ya ce ko a yanzu Buhari ya kirawo shi ya ba shi mukami zai karba, domin magana ce ta kokarin ciyar da kasa gaba da yi wa al’umma hidima, amma ya wuce a ce ya je ya nemi a ba shi aiki a gwamnatin.

Buhari ne da kansa ya ɓata lamarin – Kungiyar Igbo


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jagoran Ohaneze Ndigbo ya ce ba sa goyon bayan masu rajin ballewa daga Najeriya amma suna son a sake wa kasar fasali

Kungiyar Ohaneze Ndigbo a Najeriya ta zargi shugaba Muhammadu Buhari da abin da ta kira “bata lamari” ta hanyar watsar da al’ummar Igbo a gwamnatinsa.

Yayin hira da BBC lokacin wata ziyara, shugaban kungiyar, Cif John Nwodo ya ce batun mayar da ‘yan kabilar Igbo saniyar ware, ba boyayyen abu ba ne.

Hakan na faruwa ne, tun bayan jawabin da ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cewa zai bambanta tsakanin ‘yan kasar bisa la’akari da kuri’un zaben da suka ba shi.

A cewarsa: “Buhari ya fada wa duniya cewa zai bambanta kulawar da zai yi wa mutanen da suka kada masa kashi 97 cikin 100 na kuri’unsu da wadanda suka kada masa kashi biyar na kuri’unsu.”

Jagoran Igbon ya ce ba a ba wa ‘yan kabilarsa gwargwadon hakkokin da suka cancanci samu.

John Nwodo ya buga misali da gwamnatin jamhuriyar ta biyu. Inda ya ce kuri’ar da Shagari ya samu a yankin Kudu Maso Gabas ba ta kai wadda ya samu a yankin Middle belt ba, kuma ba ta sa shi nuna wa Igbo bambanci ba.

“Ka ga! Ni tsohon dan jam’iyyar NPN ne, na rike mukamin minista a gwamnatin Shagari, in ji shi.”

Ya ce bai kamata Buhari ya yi fatali da ‘yan kabilar Igbo, don kawai ba su kada masa kuri’a ba.

A cewarsa, shugaban kasa baban kowa ne, don haka bai dace ya kori ‘ya’yansa don kawai sun bijire masa ba.

Ka duba hukumomin tsaro a Najeriya, babu ko da daya da dan kabilar Igbo ke jagoranta.

“Mu, ba ga babban hafsan tsaro ba, mu ba ga babban hafsan sojin kasa ko na ruwa ko sojin sama ba. Ba a ba mu shugabancin hukumar kula da shige da fice ba, ko ta leken asiri ko ta tsaron farin kaya ko ta kiyaye hadurra ba.”

“Ba mu da komai. Wannan ta sa aka mayar da mu tamkar al’ummar da aka ci ta da yaki,” a cewarsa.

Ya yi ikirarin cewa an girke musu shingayen ‘yan sanda a duk manyan hanyoyin yankin Kudu Maso Gabas babu gaira babu dalili.

John Nwodo ya ce kusan illahirin kwamishinonin ‘yan sandan jihohin yankin Igbo, sun fito ne daga arewacin Najeriya.

“Babban kwamandan da ke kula da runduna ta 82 da ke Enugu, dan arewa ne. Shin sun san yankin ne?” Nwodo ya tambaya.

Cif John Nwodo ya ce yana alla-alla ya samu ganawa da Buhari don zayyana masa wadannan batutuwa da ke ci wa kabilar Igbo tuwo a kwarya.

Cameroon Zata Rufe Iyakarta Da NigeriaWata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta hana mutane fita daga maraice zuwa safiya, da kuma rufe kan iyakar kasar da Najeriya da sauransu.

Shugaba Paul Biya ya kuma bayar da umarnin shirya sojoji domin kare kasar tare da tabbatar da tsaro ga dukkan ‘yan kasar masu mutunta doka, in ji wata sanarwar da gwamnan yankin kudu maso yammacin kasar, Bernard Okalia Bilai, ya saka wa hannu.

Wata sanarwar ta daban da Bilai ya fitar ta bayyana ka’idojin takaita zirga-zirgar inda ya ce dokar za ta yi aiki ne daga 29 ga watan Satumba zuwa 2 ga watan Oktobar shekarar 2017, a fadin yankin kudu maso yammacin kasar.

Magoya bayan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Kamaru ta Kudu suna son gudanar da zanga-zanga a yankin domin tunawa da samun ‘yancin Kamaru ta Kudu daga Birtaniya a ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1961.

An dade ana takun saka tsakanin gwamnatin kasar da mutanen kudancin kasar da ke amfani da harshen Ingilishi kan abin da masu fafatuka suka kira rashin yi wa yankin adalci.

Sojojin Najeriya Sun Kara Jadadda Biyayyar Su Ga Shugaban Kasa BuhariMun samu labari daga Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN cewa Sojojin kasar nan sun ce babu gudu babu kuma babu ja da baya wajen yaki da ‘Yan banza.

Mai magana da bakin Sojin kasar Manjo Janar John Enenche ya bayyana wannan dazu a Birnin Tarayya Abuja wajen wata zantawa da ‘Yan jarida. Sojojin Najeriyar sun kara jadadda biyayyar su 100 bisa 100 ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma Janar din ya kara magana game da jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu wanda ya tabbatar da cewa ba ya hannun Sojoji ya kuma ce Gwamnatin kasar za ta dauki mataki game da matasan da su kayi barazanar korar Inyamurai daga Arewa.

Janar John Enenche yayi magana game da ayyukan da Sojojin kasar ke yi a kusan kowane sashe na kasar wanda dai yace sauran kasashen Duniya sun wuce lokacin da za a ce sai Sojoji sun kawowa sauran Jami’an tsaro dauki.Sojojin dai sun sha alwashin kawo tsaro a fadin kasar.

Gwamnatin Saliyo Ta Kama Wani Faston Najeriya Don Yin Maganganu Masu Ban Tsoro Game Da Islama


Wani faston Najeriya mazaunar kasar Saliyo, Victor Ajisafe ya shiga hannun jami’an tsaron kasar bayan da aka same shi da laifin yin maganganu masu ban tsoro game da addinin Islama a lokacin ibada na ranar Lahadi.

An kama faston ne bayan rikodin maganansa a kan musulumai ya yadu a shafukan yanar gizo a kasar.

Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ruwaito cewa Ajisafe, wanda shi ne shugaba kuma wanda ya kafa cocin “The Sanctuary Praise Church” daya daga cikin cocin da yafi girma a kasar.

Yayin da yake magana da mabiya addininsa ya zargi addinin Musulunci a matsayin addinin tashin hankali da ƙarya da kuma yaudara, ya kara da cewa Musulmai suna da alhakin duk wani ta’addanci a tarihin duniya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kasar Saliyo na da kusan 78% na musulmi, bisa ga wani bincike ta shekarar 2015 wanda cibiyar bincike ta Pew Research Center estimate ta gudanar.

An kama fasto a ranar Talata da ta gabata, amma ba’a caje shi ba har yanzu.

Shugaban sashen bincike na laifuka na Saliyo, MB Kamara, ya ce, ” Sakonsa ya ba kowa haushi” .

“Mu masu addini ne kuma babu wanda ya damu da cewa wani musulmi ko krista. Dukanmu muna zama da juna cikin lafiya har tsawon zamani, kuma babu wanda yake so wannan dagantakar ta baci”, inji shi.

Biyafara: Gwamnonin Kudu Maso Gabas Basu Kaddamar Da IPOB A Matsayin Kungiyar Ta’Addanci Ba – IkpeazuYa bayyana hakan ne yayinda yake magana a wani shiri mai suna Osasu Show, inda har ila yau yayi bayanin cewa gwamnonin sunyi nadi kan ayyukan kungiyar ne kadai, don tashin hankali da yankin ta tsunduma ciki.

Ikpeazu yayi gargadi cewa nadin da aka yi wa kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci tana dauke da gagarumar sakamako.

“A sa matakin gwamnonin kudu maso gabas cikin mahalli. Ya rage ga gwamnonin kudu maso gabas da su dubi umurnin su, ” inji Ikpeazu.

Biyafara: Gwamnonin kudu maso gabas basu kaddamar da IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci ba – Ikpeazu

“Hakkin da ya rataya a wuyana a matsayin gwamna shine kare rayuka da dukiyan yan Abia da na duk wani mai kasuwanci a yankin mai suna Abia.

“Don haka a wannan lokacin, dole in kare har da masu fafatukan kafa Biyafara. Na kasance daga kasar da ake ganin muhimmancin rayuka da dukiyan bakin garinka fiye da naka rayuwan.

“Wajibi ne kuma hakki ne a kaina tun daga ranar wajen ganin ba a zubar da jinni da zai zama gwargwadon abin tunawa ba.

“Mutane su kan yi fafatuka a duk fadin Najeriya. Amman gare ni a matsayin gwamna, na goyi bayan nadi da aka yi wa kungiyan tun daga ranan saboda bamu so a taro labarai a wuri guda ko wani wuri karkashin kungiyar IPOB.

“Amman cigaba da fadin cewa kungiyan ta kasance na yan ta’adda yana da sakamako kan kasa da kasa.

“Bana tunanin an yi wa yan kabilan Igbo adalci a kasan nan. Babu wata kabila a kwarewar adalcin kasan nan da ta yarda da kadaicin Najeriya fiye da kabilar Igbo.

“Labarai da aka mika wa gwamnatin tarayya bata isa gareni ba, kuma idan cewarsu ne, ya rage garesu su kare.

“Amman gareni, zama a karamar kwana na, ina iya magana kan duk wani dan Najeriya, ‘kan shawara wanda aka yanke cikin gaggawa’ amman wani bangare ne kuma idan aka duba daga gefen Gwamnatin Tarayya”.

Harkar Gona: Najeriya Ta Samu Makudan Kudi Daga Kwallon Kashu


Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa Najeriya ta samun makudan kudin shiga a harkar noman kashu.

Shugaba Buhari ya maida hankali wajen harkar noma yayin da kasar ta fara karkatar da akalar ta daga harkar man fetur. Ministan harkar gona Audu Ogbeh ya bayyana cewa Najeriya ta saida kwallon kashu har na Naira Biliyan 13.5 a Kasar waje.

Ministan ya bayyana wannan ne wajen tattalin arzikin kasar nan a karshen makon nan. Najeriya dai tana fitar da kwallon kashu zuwa kasashen India da Vietnam. Saukar farashin man fetur ne dai ya sa Najeriya ta komawa harkar noma.

Haka kuma Ministan kasafin kasar Udo Udoma Udoma ya bayyana cewa Gwamnatin kasar na kokarin ganin an aika kasafin kudin shekarar 2018 domin manoman rani su ji dadi a Kasar a shekarar.

Mata za su fara ba da fatawa a Saudiyya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A karon farko babbar majalisar bada shawara a Saudiyya ta kada kuri’ar amincewa da a bawa mata damar yin fatawar addini.

Majalisar ta amince da shawarar da aka gabatar, kwanaki kadan bayan janye dokar hana mata tuka mota a kasar.

Ana dai bukatar sarkin kasar ya yi wata doka da za ta samar da yawan matan da ake bukata da za su iya ba da fatawar addini.

A baya malaman addinin kasar sun sha ba da fatawowi da ke janye ce-ce ku-ce, da ake dauka cewa suna nunawa mata wariya.

An Yi Taron Dinke Rarrabuwan Kawuna Da Ya Addabi NajeriyaMatasan Najeriya daga sassa daban daban

A babban birnin tarayyar Najeriya , Abuja, an yi wani taro da ya tattaro masana, shugabanni, ‘yan kasuwa, jami’an tsaro da dai sauransu domin lalubo bakin zaren dinke rarrabuwan kawunan ‘yan Najeriya saboda kasar ta cigaba

Taron yayi kokarin gano bakin zaren banbance banbance da kowane bangaren kasar ke ikirari domin a zauna lafiya.

Farfasa Anya O. Anya daga jihar Abia shi ya fara shimfida a wajen tattaunawar. Yana mai cewa a duba banbance banbancen al’adunmu wadanda “idan aka yi la’akari dasu ka iya zama madaurinmu da zasu karfafa zamantakewarmu”. Ya cigaba da cewa “idan an yi la’akari da yadda matasan kasar daga sassa daban daban ke yin tawaye dole ne dattawan kasar su tashi su shawo kansu domin a cigaba da zama kasa daya dunkulalla”.

Tsohon ministan labarai Farfasa Jerry Gana yana ganin sai an sake fasalin kasar tukun. Yana mai cewa “a kowace kasa dake da banbancin addini, al’adu, harsuna, dabi’u da dai sauransu gwamnatin tarayya a keyi yadda akwai abubuwan da jihohi zasu yi kana akwai na jihohi”. Yace “amma a shirin Najeriya komi ya taru a hannun gwamnatin tarayya ne. Komi za’a yi sai an tunkari Abuja. Bai kamata a yi haka ba. Ana mulki kaman na soja wanda lokacinsu komi na hannun gwamnatin tarayya. Idan ana son zaman lafiya, jihohi a basu isasshen aiki da zasu yiwa mutanensu. Idan an yi hakan mutane ba zasu damu da Abuja ba”.

Shi kuwa Injiniya Buba Galadima yana ganin ana “yamutsa addini da siyasa da kuma son zuciya a harkokin kasar”. Ya bada shawara yana cewa “babbar matsalar da ta shafi kowa ita ce katsalandan da shugabannin addinai su keyi kamar suna gasa da juna. Sun manta hanyoyin addini sun koma kan siyasa”. Yace “Muddun bamu kawar da irin wadannnan daga cikin halayenmu ba Najeriya ba zata taba cigaba ba”.

Paul Pogba zai yi doguwar jinya – Mourinho


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Paul Pogba ya buga duka wasannin da Man U ta yi a kakar bana gabanin jin rauninsa

Dan wasan Manchester United Paul Pogba zai yi doguwar jinyar raunin da yake fama da shi, kamar yadda kafar yadda kocin kungiyar Jose Mourinho ya bayyana.

Dan wasan ya ji raunin ne a minti 19 lokacin da suke karawa da Basel a gasar Zakarun Turai.

Da farko an yi zaton cewa dan wasan zai yi jinyar wata guda ne biyo bayan raunin da ya ji a ranar 12 ga watan Satumba.

Sai dai kocin ya ce bai san ranar da dan wasan zai koma taka leda ba.

Mai Yiwuwa Shugaban ISIS Na Da Rai

 


Shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi

Sabanin ikirarin kasar Rasha cewa ta yi nasarar hallaka al-Baghdadi, kungiyar ISIS ta fito da muryarsa wadda aka nada ya na maganganu kan wasu al’amuran kwanan nan ciki har da rigimar Amurka da Koriya Ta Arewa.

Jiya Alhamis kungiyar ISIS ta fitar da wata murya da aka nada wadda ta ce ta sako ne daga babban shugabanta Abu Bakr al-Baghdadi, wadda, muddun aka tabbatar, zai zama karon farko da jagoran ‘yan ta’addan ya furta wani abu cikin kusan tsawon shekara guda.

Ba a san lokacin da aka dauki wannan muryar ba, koda yake an ji shi yana magana akan barazanar Koriya Ta Arewa ga Amurka da Japan, abinda ke nuna cewa mai yiwuwa kwanan nan aka nada.

Akasarin muryar mai tsawon minti 46, wadda kafar labarai ta Al-Furqan ta fitar, ayoyi ne da al-Baghdadi ke ja.

Idan aka tabbatar cewa muryar al-Baghdadi ce, hakan zai saba da ikirarin Rasha cewa wani harin da ta kai a watan Yuni a kusa da birnin Raqqa na kasar Siriya ya hallaka jagoran ISIS din mai yawan buya.

Kodayake, dama, jami’an gwamnatin Amurka sun ce sun yi imanin cewa al-Baghdadi na da rai bayan ikirarin na Rasha na kashe shi.

Amurka Ta Ce Ta Yi Luguden Wuta Kan ISIS A LibiyaShugaban Amurka Donald Trump

A cigaba da samun koma baya da kungiyar ISIS ke yi, Amurka ta ce ta yi barin wuta kan kungiyar ta’addancin, wanda ya hallaka da dama daga cikin mabiyanta a kasar Libiya

Wasu hare-haren jiragen sama da Amurka ta kai a kasar Libiya sun hallaka karin mayakan ISIS – wanda wannan ne karo na biyu da Amurka ta kai irin wadannan hare-haren a wannan kasa ta arewacin Afirka ciki kasa da mako guda.

“Tare da hadin gwiwar gwamnatin hadin kan kasar Libiya ta GNA, sojojin Amurka sun kai hare-haren jiragen sama da aka auna kan ‘yan ISIS ranar Talata, inda mayakan ISIS din da dama su ka mutu,” a cewar Rundunar Sojin Amurka mai kula da aiyukkan soji a Afirka, a wata takardar bayani da ta fitar.

Kwanaki hudu kafin nan, wasu hare-hare shida da jiragen sojin Amurka su ka kai, sun auna wani sansanin da ake amfani da shi wajen shigarwa da kuma fitar da mayakan ISIS a kasar, inda mayaka 17 su ka hallaka sannan uku daga cikin motocinsu su ka yi kaca-kaca.

Rundunar sojin Amurka din ta ce wannan sansanin, wanda ke a wuri mai nisan kilomita 240 kudu maso gabashin Sirte, ana kuma amfani da shi wajen shirya hare-hare da kuma boye makamai.

Ashura: An ta da bam a masallacin 'yan Shia


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Bam din ya tashi ne lokacin da Musulmi ‘yan Shia suka halarci masallacin don sallar Juma’a

Wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa da kuma mutum biyar a wani masallacin ‘yan Shia a birnin Kabaul na kasar Afghanistan, yayin da ake shirye-shiryen ranar Ashura.

Maharin ya boye kansa ne a matsayin makiyayi don samun damar isa masallacin, kamar yadda wani jami’in dan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Maharin ya isa wurin ne da garken dabbobinsa gabanin ya tayar da bam din da ke jikinsa,” kamar yadda wani ganau ya ce.

Kungiyar da ke ikirarin kafa Daular Musulunci (IS) ce ta dauki nauyin kai harin.

Akalla mutum 20 ne suka jikkata sanadiyyar harin.

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce adadin mutanen da harin ya shafa zai iya karuwa.

Ana zaton cewa an hari masallacin ‘yan Shi’a na unguwar Qala-e Fatullah a birnin Kabul ne, amma sai bam din ya tashi gab da masallacin.

A bara ma kimanin mutum 14 suka mutu a hubbaren Karte Sakhi yayin shirye-shiryen ranar Ashura.

Galibin Musulmin Afghanistan mabiya Sunni ne, amma akwai mabiya Shi’a kimanin kaso 10 zuwa 20 cikin 100 na jama’ar kasar.

Ruhina Ba Zai Bini Ba Idan Na Yanke Shawarar Komawa APC – LamidoTsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi watsi da duk wani kudiri dake bayyana yiwuwar barinsa jam’iyyar PDP zuwa APC, jaridar The Cable ta ruwaito.

Lamido ya yi wannan furucin ne a wajen wani taro tare da tsofaffin shugabannin majalisun dokoki na jiha a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Ya ce: “Duk wani kokari da zanyi, idan na koma jam’iyyar APC, ruhina ba zai bi ni ba”.

NAIJ.com ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa idan ba don masu sauya sheka daga PDP da jam’iyya mai ci bata kai labara a zaben 2015 ba.

Ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su gudanar da taro mai yanci a watan Disamba.

Lamido ya kuma yi tsokaci akan kaddamar da tsayawa takarar shugabancin kasa da gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose yayi.

A cewar Lamido, duk da cewar jam’iyyar ta rigada ta mika tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa na 2019 ga yankin arewacin kasar, gwamnan na jihar Ekiti na da damar da zai nemi kujerar.

Jakadan Kasar Amurka Ya Bayyana Yawan Dalibai Yan Najeriya Dake Karatu A Kasar AmurkaAn bayyana yawan yan asalin Najeriya dake karatu a kasar Amurka ta bakin shugaban ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya, John Bray, inji rahoton Daily Post.
John ya shaida haka ne a ranar Alhamis 28 ga watan Satumba, yayin dayake jawabi taron tallar makaratun Amurka inda yace daliban sun kai 10,000, yayin da yace dalibai daga nahiyar Afirka kuwa sun kai miliyan daya.

John yace taron ya samu tagomashi,inda jami’o’i guda 25 suka samu damar bajakolinsu ga dalibai dake son cigaba da karatunsu a kasar, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

“A bana, yawan dalibai dake shigowa daga kasashen Duniya sun kai miliyan guda, daga cikinsu kuwa, akwai sama da 10,000 da suka fito daga Najeriya, hakan ke nuna Amurka ce ta daya wajen diban dalibai baki.

“Yadda yan Najeriya ke son zuwa karatu a Amurka ya nuna dangatakar dake tsakanin Najeriya da Amurka kyakkyawa ce, shima hakan wani hanya ce ta inganta alakar Diflomasiyya dake tsakanin.” Inji John.

Cikin wasu jami’o’in da suka halarci zaman sun hada da jami’ar Washington, Drexel, Winsconsin da Western Kentucky.

Cameroon za ta rufe iyakarta da Nigeria


Hakkin mallakar hoto
STRINGER

Image caption

Har ma a birnin Bamenda da ke Kamaru, masu fafatuka sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da wariyar da suka ce ana yi wa ‘yan kasar masu Ingilishi

Rahotanni daga Kamaru sun ce hukumomin kasar sun gindaya dokar ta baci a yankin kudu maso yammacin kasar mai amfani da harshen Ingilishi gabannin zanga-zangar masu neman ballewa daga kasar da aka shirya yi a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.

Wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta hana mutane fita daga maraice zuwa safiya, da kuma rufe kan iyakar kasar da Najeriya da sauransu.

Shugaba Paul Biya ya kuma bayar da umarnin shirya sojoji domin kare kasar tare da tabbatar da tsaro ga dukkan ‘yan kasar masu mutunta doka, in ji wata sanarwar da gwamnan yankin kudu maso yammacin kasar, Bernard Okalia Bilai, ya saka wa hannu.

Wata sanarwar ta daban da Bilai ya fitar ta bayyana ka’idojin takaita zirga-zirgar inda ya ce dokar za ta yi aiki ne daga 29 ga watan Satumba zuwa 2 ga watan Oktobar shekarar 2017, a fadin yankin kudu maso yammacin kasar.

Magoya bayan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Kamaru ta Kudu suna son gudanar da zanga-zanga a yankin domin tunawa da samun ‘yancin Kamaru ta Kudu daga Birtaniya a ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1961.

An dade ana takun saka tsakanin gwamnatin kasar da mutanen kudancin kasar da ke amfani da harshen Ingilishi kan abin da masu fafatuka suka kira rashin yi wa yankin adalci.

Barazanar Masu Son Raba Kasa Yana Hana Shugaba Buhari Barci, Inji Farfesa King


Shugaban kwamitin kaddamar da litafai na kasa, Farfesa Richard King yace shugaba Muhammadu Buhari baya iya barci sosai bisa dalilin yan a ware da ke fafutikan raba kasa da kuma yin garambawul.

King yayi magana ne jiya a birnin Uyo inda yace shugaban kasar na bukatan hadin kai da zaman lafiya shi yasa ma ya kafa kwamitin domin tabbatar da hadin kan kasa.

”Babbu shaka Najeriya na bukatar hadin kan kowa da kowa musamman a irin wannan lokaci mai wahala domin tabbatar da hadin kan Najeriya a matsayin kasa daya dunkulaliya .

”Samar da wannan hadin kan shine dalilin da yasa aka kirkiri wannan kwamitin, kuma ina sa ran ni da abaokanan aiki na zamu dage domin cin ma wannan manufan, ” Inji shi.

Jam’iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom tace shugaban kasa da ma sauran yan kasa nagari duk sunyi amana cewa cigaban kasan nan yana tattare akan hadin kan kabilu daban-daban da suke zama tare cikin kasar.

Farfesan da ya kware a fanin kimiyan Kifi ya kara da cewa kwamitin zatayi kokarin wayar da kan yan Najeriya kan kokarin da shugaba Buhari yakeyi domin canja akalar masu kokarin raba kan Najeriya da kuma tada hankali.

Hukuncin Kisa Ya Wajaba Akan Masu Garkuwa Da Mutane – Majalisar Dattijai


 


Majalisar ta zartar da dokar hukuncin kisa ga duk wani wanda aka kama da aikata wannan laifi na yin garkuwa da mutane tare da neman kudin fansar su. Sannan kuma ta zartar da hukuncin dauki a gidan kaso na tsawon shekaru 30 ga duk wani wanda yayi taimakekeniya wajen aikata wannan laifi.

Wannan sabuwar doka ta zo ne yayin da Isa Misau mai wakiltar jihar Bauchi na jam’iyyar APC ya dauki nauyin jagorantar kwamitin kula da harkokin shari’a da kare hakkin dan Adam na majalisar suka gudanar.

Yayin da dan majalisar Chukwuka Utazi mai wakiltar Arewacin jihar Enugu ya gabatar da wannan sakamako na kwamitin a gaban majalisar ya bayyana cewa, wannan sabon hukuncin da doka zai yi yaki da kuma rage faruwar aikata laifikan yin garkuwa da mutane tare da neman kudin fansar su a fadin kasar nan, kuma hakan zai baiwa Sufeto Janar na ‘yan sanda karin karfin gwiwa wajen ci gaba da kula da kuma sanya ido akan masu aikata wannan laifuka.

Idan ba a manta ba a watan Yunin shekarar nan siyasarnigeria.com  ta kawo muku rahoton cewa, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi nasarar cafke kasurgumi kuma shahararren mai garkuwa da mutanen nan Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sanin sa da inkiyarsa ta Evans.

A watan Agustan da ya gabata, kotu ta gurfanar da Evans inda ta kama shi da laifuka biyu na da suke da alaka da yin garkuwa da mutane sakamakon tuhuma da gwamnatin jihar Legas ta yi masa.

Mutum 22 sun mutu a turereniya a tashar jirgin kasa ta India


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Matafiya suna kokarin ceton wadanda suka sami rauni

Wata turereniya a tashar jirgin kasa da ke birnin Mumbai ta janyo mutuwar mutum 22 inda fiye da mutum 30 kuma suka jikkata, in ji jami’ai a kasar Indiya.

Iftila’in ya faru ne a lokacin da ma’aikata ke rububin zuwa wajen aiki da safe a tashar jirgin kasa ta Elphinstone, wacce mahada ce ga manyan layukan jirgin kasa guda biyu na cikin birnin.

Cunkoso ne ya jawo wannan iftila’in saboda yawan mutanen da ke neman fakewa daga mamakon ruwan saman da ya rinka sauka.

An tafi da wadanda suka sami rauni zuwa wani asibiti da ke kusa da tashar kuma manyan jami’an tashar jirgin kasan na wurin domin taimakawa.

Yaya lamarin ya faru?

“Iftila’in ya auku ne a daidai lokacin da ake mamakon ruwan sama na Monsoon a birnin Mumbai, kuma matafiya sun taru a tashar domin neman mafaka.

Sai kawai wadanda ke gaba suka zame, dalilin da yasa na bayansu suka zubo kansu. Daga nan sai aka fara turereniya”, in ji Ravindra Bhakar, kakakin kamfanin jirgin Kasa na Indiya a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Mun tabbatar da mutum 22 sun mutu, maza 14 da mata takwas… Kuma wasu fasinjoji 32 sun sami raunuka.”

Hakkin mallakar hoto
BBC Marathi

Image caption

Masu aikin ceto sun yi gaggawar zuwa wajen

Akash Koteja na cikin wadanda suka sami rauni, kuma ya ce: “A lokacin jiragen kasa na isa tashar kuma wasu fasinjojin na neman ficewa daga tashar, amma wasu kuma sun hana su ficewa.

“Da wasu suka gwada fita sai aka fara turereniya.”

Hotunan talabijin sun nuna wasu matafiya na kokarin ceto abokan tafiyarsu daga cikin wadanda aka danne, kuma wasu ana danna kirjinsu domin a farfado da su.

“Mun saka wadanda suka sami rauni a motoci, da motocin ‘yan sanda da motocin daukar ma’aikata wadanda suka tafi da su asibiti cikin gaggawa”, in ji daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin kamar yadda AFP ta ruwaito.

Me yasa iftila’in ya faru?

Wani bincike da aka kaddamar ya bankado sanadiyyar wannan hatsarin, amma cunkoso shi ne babban dalilin yawan hadurran da ke addabar hanyoyin jiragen kasan Indiya.

Wakiliyar BBC a Mumbai, Yogita Limaye, ta ce hatsarin ya sake bayyana halin tabarbarewar da bangaren sufuri na birnin Mumbai ke ciki.

Kuma an sha sukar yadda gwamnati ba ta sabunta jirage da taragun da ke safarar miliyoyin fasinjoji a hanyoyin jiragen kasa a kullum.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan uwan wadanda iftila’in ya faru sun tafi asibitin domin neman labarin halin da ‘yan wansu ke ciki

Boko Haram ta kashe malamai 2,295 a Borno – UNICEF


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yara da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce har yanzu mafi yawan makarantun jihar Borno inda rikicin Boko Haram ya fi kamari a rufe suke, wanda aka danganta hakan da cewa ‘yan kungiyar na kai hare-haren ne da gayya don lalata fannin ilimi.

A wani rahoto da ta fitar a ranar Juma’a, UNICEF ta ce a kalla kashi 57 cikin 100 na makarantun Borno a rufe suke, a yayin da aka fara sabuwar shekarar karati, inda yawan malaman ya ragu kuma gine-ginen makarantun suke a lalace.

A wata sanarwa da UNICEF ya aikawa manema labarai ya ce, fiye da malamai 2,295 aka kashe, yayin da aka raba 19,000 da muhallansu, sannan kuma makarantu 1,400 suka lalace a shekaru takwas din da aka shafe ana rikici a yankin.

Makarantun sun kasance a rufe ne saboda yadda aka lalata su, wasu kuma suna yankunan da har yanzu babu tabbataccen tsaro, duk kuwa da irin yadda sojoji ke kokarin ‘murkushe’ ‘yan kungiyar tun a shekarar 2015.

UNICEF ya yi gargadi cewa lamarin na barazanar sanyawa a rasa yara masu tasowa, inda hakan zai rushe duk wani buri na makomarsu da makomar kasarsu idan har ba a yi komai ba kan hakan.

Mataimakin hukumar ta UNICEF Justin Forsyth, ya kai ziyara yankin arewa maso gabashin Najeriyar, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “koma bayan da hakar ilimi ta fuskanta sakamakon ta-da kayar baya ba tsautsayi ba ne.”

“Wannann wani abu ne da Boko Haram ta shirya yin sa da gayya, don hana yara samun ilimi,” a hirar tasa da AFP.

Mista Forsyth ya kara da cewa, kusan yara miliyan uku na bukatar taimakon gaggawa ta fannin ilimi, sai dai akwai wawagegen gibi a kudaden da UNICEF ke samar wa don yin ayyuka a yankin.

Kusan yara 750,000 ne suka samu komawa makaranta a bana a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, jihohin da su ma ayyukan Boko Haram suka yi wa illa.

Wadansu da dama na samun iliminsu ne a matakin farko a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Mutu Ka Raba, Takalmin Kaza: Mutuwa Kaɗai Zata Raba Ni Da Kujerar Sanata – Inji Bukar AbbaTsohon gwamnan jihar Yobe, kuma Sanatan al’ummar yankin Yobe ta gabas, Sanata Bukar Abba Ibrahim yace ba zai taba dai na tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa ba har iya rayuwarsa.

Sanata Bukar Abba ya bayyana haka a bainar majalisar dattawa, yayin da ake tafka muhawara akan bikin cikar Najeriya shekara 57 da kafuwa, inda yace mutuwa ce kadai zata raba shi da kujerar Sanata. 

Sanata Bukar na majalisar dattawan ne a karo na uku, inda ya dare kujerar tun a shekarar 2007, bayan daya kammala wa’adin mulkinsa a jihar Yobe, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Siyasarnigeria.com  ta ruwaito a yanzu haka Bukar shine shugaban kwamitin kulawa da sauyin yanayi a majalisar dattawa, yayin da matarsa kuma tsohuwar yar majalisar wakilai, daga nan kuma ta zama ministan Najeriya.

Sai dai ana tunanin Sanatan ya aika da sakon ne ga gwamnan jihar Ibrahim Geidam, wanda zai kammala wa’adinsa na gwamnan jihar Yobe a shekarar 2019, kuma ya fito daga mazaba daya da gwamnan jihar, wanda ake gani shima na sunsunan kujerar.

“Mun gode ma Ubangiji Allah da yan Najeriya, ina bayyana ma shugaban majalisar dattawa ce ba zan bar majalisar dattawa ba iya rayuwana, har sai na mutu, saboda jama’a na ma haka suke kira na.” Inji Sanata.

Da yake mayar da martani, Sanata Bukola Saraki cikin raha yayi kira ga Sanata Ahmad Lawan da Sanata Mohammad Hassan wadanda dukkansu yan jihar Yobe ne da su kula da maganan da Sanata Bukar Abba yayi.

Takaicin Maza Ne Ke Sanya Matan Katsina Shiga Shaye Shaye – SaulawaWata matashiya a jihar Katsina da aka ambata da suna Khadija Saulawa ta bayyana yadda takaicin maza a ke sanya matan jihar shaye-shaye.

Saulawa, ma’assashiyar wata kungiya mai zaman kanta ‘Queen Dijah Women and Children Awareness Initiative’ tace kudirin ta shine ta wayar da kawunan mata akan illolin dake tattare da wannan harka.

A wata zantawa da tayi da jaridar Vanguard, Saulawa tace idan ba’a shawo kan wannan matsala cikin gaggawa ba, za’a samu karin tabarbarewa tarbiya a nan gaba.

Saboda a cewar ta “Idan kullum uwa na cikin maye wa zai kula da yara?”

Ta ce yawanci mata na shiga harkar shaye-shaye ne da zaran an fada masu cewa zai kawar masu da bakin cikin da mazajen su suka sanya su a ciki. Ta ce da sun dandana suka ji dadi, shikenan ba za su iya dainawa ba.

Saulawa ta kuma ce kungiyar ta ta za ta mayar da hankali a bangaren fyaden kananan yara, wanda ta ce shi ma ya zama ruwan dare a Katsina da samar da tsaftataccen ruwan sha.

LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Tsige DG Na NAFDACGwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da murabus na babban darektan hukumar kula da abinci da magunguna, NAFDAC, Yetunde Oni nan da nan.

R.P Ugo, sakatare na dindin a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, j, ya ba da umurnin yin murabus nan da nan ga Misis Oni.

NAIJ.com ta tattaro cewa, sakataren ya ba da umurnin ne a yau Alhamis, 28 ga watan Satumba yayin mayar da martani ga wasiƙar da Misis Oni ta rubuta wa SGF game da wata rikici tsakanin ma’aikata da shugabancin hukumar.

Ma’aikata na NAFDAC sun fara yajin aiki na rashin iyaka a makon da ya wuce, inda suke buƙatar cire Misis Oni, wanda suka ce ta kai ta yi ritaya.

Hukumar INEC Ta Fitar Da Jadawalin Zaben Shekarar 2019

 


A yayin da ya rage saura kwanaki 505 daga yau ga babban zaben shekarar 2019 a Najeriya, hukumar zabe ta kasa, INEC, ta fitar da jadawalin yadda zaben zai kasance.

A shafin INEC, dake kafar yada labarai ta tuwita, ta bayyana cewar za ta fara gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya ne a ranar asabar da yayi daidai da 16 ga watan fabrairun shekarar 2019, yayin da ta ce zata gudanar da zaben gwamnonin jihoshi da ‘yan majalisun jiha a ranar asabar, 2 ga watan Maris na shekarar ta 2019.

INEC ta bayar da tabbacin cigaba da gudanar da rijistar masu zabe duk da kasancewar a yanzu haka ta yi nasarar yiwa wasu karin mutum 2,786,405 rijista.

Sergio Aguero ya ji ciwo a hatsarin mota


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sergio Aguero ya buga wasan da Manchester City ta doke Shakhtar Donetsk 2-0 ranar Talata

Dan wasan gaban Manchester City Sergio Aguero ya ji rauni a wani hatsarin mota a birnin Amsterdam, sa’o’i bayan ya halarci wani bikin rawa da kade-kade.

An ba da rahoton cewar dan kasar Argentina mai shekara 29 yana hanyar shi ta zuwa filin jirgin sama ne a motar haya bayan ya kalli wakar da mawaki Maluma ya yi.

City ta ce “ya kasance a kasar Holland ne a lokacin hutunsa, kuma ya ji raunuka”.

Ana tsammanin Aguero ya koma Manchester ranar Juma’a, kuma likitocin City za su gwada shi kafin tafiyarsu wasan gasar Firimiya a Chelsea ranar Asabar.

‘Yan sanda a Amsterdam sun tabbatar wa BBC cewar mutum biyu ne cikin motar tasi din da ta yi hatsari a unguwar De Boelelaan da ke cikin birnin.

Kafin hatsarin dai, dan kwallon ya wallafa hotonsa da mawaki Maluma a shafinsa na Instagram da sakon da ke cewa: “ina godiya da gayyatata”.

Hakkin mallakar hoto
KaWijKo Media

Image caption

Hatsarin ya auku ne a unguwar De Boelelaan na Amsterdam

Tsohon kulob din Aguero, Independiente, ya tura wa dan wasan sakon fatan alkhairi ta shafin Twitter, yana mai cewa”Kuzari tare da warkewa cikin gaggawa ga aguerosergiokun! Ilahirin @Independiente na tare da kai a wannan mawuyacin lokaci.”

Dan wasan gaban ya ci kwallaye bakwai a wasanni takwas a Man City a wannan kakar.

Kuma ya tallafa wa kungiyar Pep Guardiola ta hau saman teburin gasar Firimiya tare da yin nasara a wasanninsu biyu na farko a gasar zakarun Turai.

Hakkin mallakar hoto
10aguerosergiokun

Image caption

Sergio Aguero (daga hagu ) da Maluma a wani hoton da ya wallafa a shafin Instagram sa’o’i kafin hatsarin motar

Gwamnatin Amurka Na Neman Ta Rage Adadin ‘Yan Gudun Hijira Masu Shigowa Kasar.USA–New York/Televised debate between the presidential candidates of the Democratic and Republican Party Hillary Clinton and Donald Trump, Donald Trump/video grab

Fadar White ta aike da wani kudirin data ke neman samun damar rage adadin ‘yan gudun hijira da zasu shigo Amurka.Gwamnatin ta shugaba Donald Trump ta nemi a rage adadin wadannan mutanen kwarai da gaske

A nan Amurka kuma…Gwamnatin shugaba Donald Trump tace tana niyyar ta rage yawan mutanen dake shigowa cikin Amurka da sunan ‘yan gudun hijira – kuma ragi mai yawan gaske, duk kuwa da rokon da kungiyoyin kare hakkokin Bil Adama ke yi na cewa, maimakon a rage, kwanda ma a kara yawan wadanda zasu iya shigowar.

A cikin wani rahoton da ta aikawa Majalisar Dokokin Amurka din a jiya ne, fadar shugaban Amurka ta White House take cewa yawan mutane, ‘yan gudun hijiran da gwamnatin zata bari su shigo a cikin shekarar da za’a shiga ba zasu wuce 45,000 ba, wanda kuma wannan itace jimilla mafi kankanta a cikin shekaru 35 da suka gabata.

Kafin ya sauka daga karagar mulki, tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bada shawarar ribanya yawan ‘yan gudun hijiran da za’a bari su shigo Amurka, inda ya nemi a bude hanya ga akalla masu yawan 110,000.

A zaman mulkin shekaru takwas da yayi, ‘yan gudun hijira kusan 885,000

Obama ya budewa hanyar shigowa Amurka.

Nigeria: An Sace Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Da MatarsaRahotanni a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sace wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda tare da matarsa a yayin da suke tafiya a mota.

An sace mataimakin kwamishinan nan ne a wani dajin da ke tsakanin Funtua a jihar Katsina da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wata majiya mai karfi ta tsaro a jihar Kaduna ta shaida wa BBC cewa, mataimakin kwamishinan na ‘yan sandan na aiki ne a jihar Zamfara ko kuma a jihar Katsina.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta jihar ba ta ce komai ba kan wannan batu.

Amma kakin rundunar ya shaida wa wakilinmu Nura Muhammad Ringim cewa suna wani taro, inda ya bukace shi da ya sake kiransa bayan sun kammala.

Dajin da aka sace wannan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda dai dama sanannen wuri ne da aka yi amannar na kunshe da ‘yan ta’adda kamar ‘yan fashi da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Jihar Kaduna dai ta yi kaurin suna wurin sace-sacen mutane, inda ko a kwanakin baya sai da aka sace tsohon ministan kasar, Ambasada Bagudu Hirse.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cewa suna daukar tsauraran matakai domin magance matsalar tsaro a jihar.

Ba zan nemi gafara wajen Buhari ba – Buba Galadima


Hakkin mallakar hoto
BUBA GALADIMA

Image caption

Buba Galadima ya ce ba wani sabani tsakaninsa da Shugaba Buhari, saboda haka ba zai nemi wata gafararsa ba, don a ba shi mukami

Daya daga cikin jigogin da aka kafa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, tare da kasancewa na gaba-gaba wajen fafutukar ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya samu mulkin Najeriya, Injiniya Buba Galadima, ya ce bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin ba.

A hirarsa da BBC Buba Galadima ya ce a yanayin salon jagorancin jam’iyyar da kuma mulkin da ake yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.

Ya ce abin takaicin shi ne Allah ya jarrabi Shugaba Muhamadu Buhari da rashin lafiya, kuma dadin dadawa sai jam’iyyar ta kasa samar da wani kyakkyawan shugabanci, wanda duka wadannan abubuwa sun shafi yanayin mulkin.

Game da rashin ba shi wani mukami ko tafiya da shi a gwamnatin Buharin, Buba Galadima ya musanta cewa akwai wani sabani a tsakaninsu da Shugaban, wanda ake rade-radin cewa saboda hakan ne ba a tafiyar da shi.

Ya ce a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka assasa tafiyar har ta kai an kafa gwamnati ba ya bukatar har sai ya yi kamun kafa, ko wani tumasanshi a wurin Shugaba Buhari kafin a san da shi har a ba shi wani mukami.

Injinyan ya ce rashin ba shi mukami bai dame shi ba, domin kusan duk wadanda suka faro tafiyar tabbatar da kasancewar Buharin ya zama shugaban kasa, babu wanda aka ba wa wani mukami, don haka ce shi ba komai ba ne, yana mai shagube da cewa: ”Ni ai a cikin miya ban kai komai ba.”

Dan siyasar ya dangantaka ba shi mukami ga lamari na Ubangiji, yana mai cewa duk abin da mutum ya samu Allah ne, haka kuma in mutum ya rasa Allah ne, amma ba ya nadamar gwagwarmayar tabbatar da Buhari Shugaban kasa, don bai samu mukami ba.

Ya ce ba wata gafara da zai nema daga Shugaban, ko zai waiwaye shi da mukami, domin shi a saninsa ba wani abu da ya yi na sabamasa.

Game da dantakarar da Buba Galadiman zai mara wa baya a zabe na gaba na 2019, ya ce lokaci bai yi ba tukuna, amma idan lokacin ya zo zai karkata ga ra’ayinsa, ko da kuwa za a kashe shi ne.

Sai dai ya ce in har Buhari ya neme shi a tafiyar 2019, idan zai yi takara zai iya mara masa baya, amma ba wai haka kawai ya kai kansa tafiyar ba, ba tare da an gayyace shi ba.

Amma ya ce ko a yanzu Buhari ya kirawo shi ya ba shi mukami zai karba, domin magana ce ta kokarin ciyar da kasa gaba da yi wa al’umma hidima, amma ya wuce a ce ya je ya nemi a ba shi aiki a gwamnatin.

Kasar Saudiyya Ta Dakatar Da Yada Karatun Babban Malamin Salafiyyar Kasar


 


Sakamakon fatawar da ya bada akan ranar bikin kafuwar kasar da ya gudana a makom nan inda aka cakudu maza da mata ana murnanr wannan ranar zagayowar kafa kasar da suke kira da abun da ba’a taba samun irin shi ba tun kafuwar kasar.

Kasar Saudiyya ta dakatar da yada karatun babban malamin salafiyyar kasar

Labaran duniya.com  dai ta samu cewa wannan dalilin yasa Babban Malamin yace wannan abu da akayi Bidi’a ne hakan yasa Hukumar kasar duk da irin mutuncin da yake dashi Suka dakatar da yada duk wani karatun Shi har illa Masha’Allah.

Idan dai mai karatu ba zai manta ba kasar ta Saudiyya tayi wani gagarumin taro domin tunawa da ranar ta game ta zama kasa guda daya tilo.

Duk Abinda Hukumar EFCC Zata Yi, Bazai Razana Ni Ba, Inji Fayose


 


Gwamnatin jihar Ekiti tace cafke kwamishinan kudi na jihar, Cif Toyin Ojo da kuma babban Akanta janar na jihar ta hukumar EFCC tayi ba komai bane ila rashin da’a da sanin ya kamata.

A wata sanarwa da ta fito ranan Alhamis daga mai taimakawa gwamna Fayose a fanin hulda da jama’a da kafafen yadda labarai, Lere Olayinka tace: ” Ko shakka babu shahunan da ke zagaye da shugaba Muhammadu Buhari suna jin tsoron fitowar takara da Gwamna Ayodele Fayose yayi na shugabancin kasa a shekarar 2019, hakan ne yasa suka razana suka fara tsare ma’aikatan jihar Ekiti a ranan da gwamnan ya sanar da niyyar sana tsaya wa takaran domin kawai a bata wa gwamnatin sa suna a idon mutane. ”

Sanarwan ta cigaba da cewa abin dariya ne yadda hukumar EFCC tayi watsi da da umurnin kotu da tayi hani da hukumar EFCC ta tsare ma’aikatan jihar Ekiti, kuma har yau babu wanda ya daukaka kara akan umurnin kotun.

Gwamnatin Ekitin ta kallubalanci hukumar EFCC ta fada wa jama’a abin da tayi da dimbin wasikun koke da ake aike mata akan tsohon gwamnan jihar Ekiti na jami’iyyar APC Dr. Kayode Fayemi, har ila yau mene gwamnatin tayi akan badakallar yanke ciyayi da kuma zunzurutun kudi dallan Amurka miliyan 43 da aka gano a Ikoyi?

Gwamnatin na Ekiti da kara da cewa masu son su karbe mulki daga hannun Fayose ne da kuma yan koran shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin hanna ruwa gudu a jihar.

”Ya kamata hukumar EFCC ta da masu daure musu gindi su sani cewa ba yau muka saba karo da irin wannan makircin ba, kuma baza mu firgita ba da hukumar gwamnatin tarayya da ta maida kanta a matsayin makamin kuntatawa, firgitawa da cin zalin wanda suke adawa da gwamnati. ” Inji sanarwan

Cin Hanci Da Rashawa Na Iya Halaka Najeriya Idan Ba A Sanya Matakan Gaggawa ba – Inji Farfesa Oyebode

 


Akin Oyebode, Farfesa na dokar kasa da kasa, ya ce idan ba a sanya matakan gaggawa ba, cin hanci da rashawa zai iya haifar da wargajewar Najeriya a matsayinta na kasa.

Oyebode ya yi wannan magana ne a wni taron da kungiyar SERAP tare da haɗin gwiwar kungiyar NED suka shirya.

An gudanar da taron ne a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba a CITIHEIGHT Hotel wanda ke hanyar Sheraton Opebi Link Road, Ikeja, Legas.

Ya ce ana bukatar ‘yan Najeriya su dauki mataki na gaggawa don kalubalanci shugabannin a kan cin hanci da rashawa da ta zama ruwan dare a kasar.

“Ya kamata ‘yan Nijeriya su fara kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa a makarantu, shirye-shirye a gidan radiyo domin yaki da cin hanci da rashawa, zanga-zangar lumana kamar yadda kungiyar SERAP ke yi yanzu” , inji shi.

Ya ce “Bai kamata a bar yaƙin ga kungiyoyi kamar SERAP kadai ba domin idan gwamnati ta na so ta far wa kungiyoyi kamar SERAP jama’ar kasar ya kamata su jeje su”.

Oyebode ya ci gaba da cewa: “Cin hanci da rashawa yanzu ya fi kamari fiye da kowane lokaci, duk da yaki da cin hanci da rashawa na wannan gwamnatin”.

2019: Ni Kaɗai Ne Wanda Zai Iya Karawa Da Buhari A Shekara Ta 2019 – Inji Fayose


Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a lokacin da yake bayyana ra’ayinsa na tsaya takarar shugaban kasa a Abuja, ya yi ikirarin cewa shi kadai zai iya kara da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekara ta 2019.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Fayose ya kalubalanci shugabannin jam’iyyar PDP na yankin arewa. Ya ce shugabannin PDP a arewa na tsoron fitowa kamar yadda ya yi don bayyana manufar neman mulkin kasar.

“Idan akwai maza a arewa, bari su fito yanzu. Menene suke jin ma tsoro”, in ji Fayose.

Ya ce: “Ba zan jira watanni 6 kamar ‘Buhari’ kafin in zabi ministoci na ba, saboda na san inda mutanen da suka cancanta suke. 

Da yake jawabi game da tashe-tashen hankulan makiyaya, Fayose ya ce zai yi amfani da dabarun da ya yi amfani da ita a jihar Ekiti don dakatar da barnar makiyayan.

Gwamnan jihar Ekiti ya kwatanta kansa da dutse, yana cewa duk wanda ya kalubalanci shi zai fadi.

A wata bikin da aka gudanar a Chelsea hotel da ke birnin tarayya ta Abuja a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, gwamnan ya ce ya yanke shawarar tsaya takarar shugaban kasa saboda kaunarsa ga Najeriya.

Kamfanin Sadarwa Na Airtel, Ya Kaddamar Da Aikin Gudummawarsa Ta Fannin Ilimi A KadunaKamfanin sadarwa na Airtel ya yi bikin bude, firamaren Yahaya Hamza dake Zaria, daya daga cikin makarantun da suka dauki nauyn tallafawa da kayan koyarwa domin inganta ilimin yara marasa galihu.
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Elrufa’i, yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron, godewa kamfanin sadarwar na Airtel bisa kokarin su na tallafawa bangaren ilimi a fadin Najeriya. Gwamnan ya kara da cewa, makarantar firamare yanzu ta samu karin jerin dakuna 6 masu dauke da ajuzuwan koyarwa 12, bencina, kujeru, ofishin malamai, allon bango, da kuma bandakunan malamai dana dalibai maza da mata. Gwamnan ya rufe jawabin sa da kira ga ragowar kamfanunuwa da suyi koyi da aikin kirki irin na Airtel.

A yayin jawabin sa, babban manajan kamfanin Airtel a Najeriya, Segun Ogunsanya, ya bayyana cewar sun zabi tallafawa bangaren ilimi ne saboda muhimmancin ilimin a rayuwa.

Makarantar firamare ta Yahaya Bello dake Zaria ita ce makaranta ta biyar da kamfanin na Airtel ya zaba domin tallafawa. Ragowar sune; Oremeji firamare a jihar Lagos, firamaren St. John’s dake Ogun, firamaren Amumara dake Imo, firamaren Iyeru Okin a Kwara, da firamaren Presbyterian a jihar Kuros Riba.

Shugaba Donald Trump Na Amurka Yace Za Ayi Wa Aikin Gwamnati Kwaskwarima.


GOP 2016 Convention

Shugaba Donald Trump yace ba makawa sai anyi wa tsarin ayyukan gwamnati kwaskwarima,Ga bisa dukkan alamu yana shagube ne ga sakataren lafiya Tom Price.

Shugaba Donald Trump na Amurka, wanda yace ya zo ya yi wa harakar aikin gwamnati “wankan tsarki”, bisa ga alama yana fushi da akalla daya daga cikin ministocinsa da ake zargin yana almubazzaranci da mankudan kudade wajen shawagin da yake yi da jiragen sama.

Wanda Trump ke hararan kuwa ba wani bane illa Sakataren lafiya na Amurka, Tom Price wanda, da ‘yanjaridu suka tambayi Trump ko zai kore shi, sai yace “zamu dai gani.”

Amma dai Trump ya fito fili yace bai ji dadin rahottanin da aka bada ba na yadda Price, akalla sau biyu, yayi hayar jiragen tafi-da-gidanka maimakon ya shiga jiragen kasuwa, hayar da akace ta janyowa muitanen Amurka asarar $400,000 .

A jiya ne Kwamitin Maida hankalin Kan Kashe Kudaden Gwamnati na Majalisar Wakilan Amurka ya aika wasiku zuwa ga fadar ta White House da wasu ma’aikatu, yana neman bayani akan kusoshin gwamnati masu yawan atfiye-tafiye a cikin jiragen haya don gudanarda aiyukkansu ko don ganin damarsu.

Shi wannan sakataren lafiyar Price da ake zance a kansa a yanzu, ya taba sukar lamirin jagabar ‘yanmajalisar jam’iyyar Democrats, Nancy Pelosi a shekarar 2010 , akan cewa wai ta cika anfani da jiragen tafi-da-gidanka wajen yawace-yawace.

Europa: Arsenal ta yi rawar-gani, ta doke Bate 4-2


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Theo Walcott ya ci wa Arsenal kwallo uku a wasa biyu da ya yi mata na karshen nan

Theo Walcott ya zura kwallo biyu a raga a wasan da Arsenal wadda bisa ga dukkan alamu ta farfado daga yanayin da ta shiga na rashin katabus, inda ta doke Bate Boristov a wasan Europa.

Wasan da suka tashi 4-2, ranar Laraba, ya kasance na biyu da Arsenal ta ci a rukuninsu na takwas (Group H) na gasar kofin Turai ta Europa.

Walcott ya fara daga raga ne a minti na tara da shiga fili, sannan ya kara ta biyu a minti na 22.

Rob Holding ya ci wa Arsenal kwallonsa ta farko a minti na 25, wadda ta kasance ta uku ga kungiyar, kafin kuma Giroud shi ma ya ci tasa a minti na 49 da bugun fanareti, kwallon da ta kasance ta 100 da ya ci wa kungiyar.

Bate ta samu kwallayenta ne ta hannun Ivanic a minti na 28 da shiga ili, yayin da a minti na 67 Gordeychuk ya ci musu ta biyu.

Arsenal ce kungiya ta farko da ta doke Bate a gida a wata gasar kofin Turai, tun bayan da Barcelona ta ci ta a wasan rukuni na kofin zakarun Turai a 2015- a wasa bkawai kenan.

Arsenal ce ta daya yanzu a rukunin da maki shida, yayin da Red Star Belgrade take zaman ta biyu da maki hudu, bayan da ta ci Cologne, wadda ta sha kashi a wasanninta biyu, da daya mai ban haushi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Nikola Vlasic ya ci wa Everton kwallon farko

A karawar da aka yi tsakanin Everton da Apollon Limassol, Sardinero Corpa ne ya fara daga ragar Everton a minti na 12, kafin Rooney ya rama a minti na 21.

Vlasic ya ci wa mai masaukin baki Everton ta biyu a minti na 66, kafin kuma can a minti na 88 Yuste Canton ya rama wa bakin.

Everton ta ci gaba da kasancewa ta karshe a rukuninsu na biyar (Group E), bayan da Lyon ta yi kunnen-doki 1-1 da Atalanta.

Ga sakamakon sauran wasannin na Europa na ranar Alhamis :

Östersunds FK 1-0 Hertha BSC

Everton 2-2 Apollon Limassol

FC Astana 1-1Slavia Prague

Ath Bilbao 0-1 Zorya Luhansk

Lazio 2-0 SV Zulte Waregem

Nice 3-0 Vitesse

Rosenborg 3-1 Vardar

Zenit St P 3-1 Real Sociedad

Lugano 1-2 Steaua Buc

Viktoria Plzen 3-1Hapoel Be’er Sheva

FC Köln 0-1Crvena Zvezda

FC Red Bull Salzburg1-0 Marseille

Konyaspor 2-1Vitória Guimarães

Sheriff Tiraspol 0-0 FC Copenhagen

Lokomotiv Moscow 3-0 Zlín

Lyon 1-1 Atalanta

Ludogorets Razgrad 2-1 Hoffenheim

AC Milan 3-2 HNK Rijeka

AEK Athens 2-2 Austria Vienna

Sporting Braga 2-1 Istanbul Basaksehir

Skenderbeu 1-1 Young Boys

Partizan Belgrade 2-3 Dynamo Kiev

Zenit St Petersburg 3-1 Real Sociedad

Rosenborg 3-1 Vardar

An Kulla Yarjejeniya Tsakanin Jami’ar Maiduguri Da Ta Kasar Sudan.
Domin habbaka ilmi tsakanin su,Jami’ar Maiduri a Nigeria da jamia’ar kasar Sudan Wacce take Birnin Khartoun na kasar Sudan sun kulla yarjejeniya.Wadannan jami’oin dai zasu rika musayar dalibai.Da sauran bayanai dake da nasaba da bincike.

harakokin ilmi tsakanin jami’oin biyu , wadanda daga yanzu zasu rika musanyar dalibai da aiyukkan bincike.

Wani attajiri dan asalin jihar ne Alhaji Mohammed Indimi ya taimaka wajen kulla wannan zumunci a tsakanin manyan jami’oin guda biyu na Nigeria da Sudan.

Sanatocin Amurka sun soki Twitter


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sanatocin sun zargi kamfanin Twitter da kin bayar da cikakkun bayanai kan zargin kutsen Rasha a zaben Amurka na 2016

An soki kamfanin shafin Twitter saboda ‘yar takaitacciyar bayyana wadda ba ta wadatar ba, da wakilansa suka yi a gaban kwamitin da ke binciken katsa-landan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata.

An gayyaci jami’an kamfanin na Twitter da su bayyana domin su bayar da bahasin da suke da shi na amfani da shafin wajen yada bayanan karya ga masu zaben Amurka.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron ganawar da jami’an kamfanin, dan majalisar dattawan Amurka, Mark Warner, ya bayyana bahasin da wakilan shafin suka bayar a matsayin babban abin takaici.

Ya zargi kamfanin da kin fahimtar muhimmancin lamarin, ta yadda kawai ya maimaita irin bayanan da masu shafin Facebook suka ba wa kwamitin.

Shi dai Sanata Warner yana fafutukar ganin an sanya wa kamfanonin fasaha ne tsauraran matakai kan ayyukansu, musamman ma a kan saba dokokin tallace-tallace ta intanet.

A wani sako da shafin Twitter ya wallafa ranar Alhamis, ya ce, kafar watsa labarai ta Russia Today, wadda ke da alaka ta kut da kut da fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta kashe dala dubu 274, wajen tallace-tallace a lokacin yakin neman zaben na Amurka.

Shafin na Twitter ya kuma ce ya gano tare da dakatar da shafuka daban-daban har 22 da ake amfani da su wajen yada bayanai da sakonni na karya.

Shugabannin Kabilun Nigeria Sunyi Taro A jihar Niger Domin Samar Da Zaman Lafiya.NIGER: Taro kan dokokin ma’adanai

Domin inganta zaman lafiya a jihar Niger kabilu daban-daban dake zaune cikin jihar sun gudanar da taron kara fahintar juna.

Wakilan k abilun Nigeria daban-daban suka sami halartar wannan taron da niyyar inganta zaman lafiya.

Wakilin gwamnan jihar Neja a waje taron ya s haidawa mahalarta taron cewa jihar ta kowa da kowa ce, ba wani bare.

Wasu daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana muhimmacin zaman tare.

IS ta fitar da sakon murya na al- Baghdadi


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tun bayan watan Yulin shekarar 2014, al-Baghdadi bai kara fitowa baynar jama’a ba

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta IS, ta wallafa wani sautin murya da aka nada wanda ta ce na shugabanta ne, Abu Bakr al-Baghdadi.

Sakon da mai maganar ke yi a cikin sautin, ga alama yana yi ne a kan barazanar da Koriya ta Arewa ke yi wa Japan da kuma Amurka.

Kazalika sautin muryar ya tabo batun yakin da ake yi a babbar tungar kungiyar ta IS da ke birnin Mosul, birnin da dakarun Iraqi suka karbe a watan Yulin da ya gabata.

al-Baghdadi, wanda aka sanya ladan dala miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da labarin in da yake, ba a kara ganinsa a bayyanar jama’a ba tun watan Yulin shekarar 2014, lamarin da ya janyo rade-radin cewa ko yana raye ko kuma ya mutu.

Karshen ganinsa da aka yi a baynar jama’a shi ne, lokacin da ya yi wa’azi a babban masallacin birnin Mosul wato al-Nuri, bayan IS din ta karbe ikon birnin.

Ko da aka tambayi kakakin rundunar sojin Amurka da ke yaki da IS, Ryan Dillon, ya ce tunda babu wata kwakkwarar shaida da za mu ce ya mutu, to za mu dauka yana nan da rai.

Najeriya Zata Fice daga Wasu Kungiyoyin Kasa Da Kasa Guda Casa’In


Ministar harkokin kudin Najeriya da Kemi Adeosun da shugabar hukumar bada lamuni ta duniya Christine LagardeMatsalar kudi da Najeriya take fama dashi ya sa ta fara nazari kan kasancewa cikin wasu kungiyoyin duniya da nufin rage kashe kudi bisa wadanda basu da mahimmanci

Kawo yanzu Najeriya nada wakilci a kungiyoyin kasa da kasa har guda 310 lamarin da ya jawo mata basussuka na fiye da $120m.

A duk shekara Najeriya na kashe kudi kimanin $70m a ire-iren wadannan kungiyoyin.

Ministar Kudin Najeriya Femi Adeosun tace Najeriya zata fice daga kungiyoyi casa’in yayinda zata cigaba da kasancewa a sauran 220.

Dan Masanin Fika Alhaji Abba wanda ya taba zama shugaban daya daga cikin kungiyoyin, wato, kungiyar raya kogin Neja yana mai cewa kasashe tara ne suke cikin kungiyar amma rabin kudin aikin kungiyar Najeriya ce take samarwa. Idan Najeriya bata fita daga cikin irin kungiyar tafiyar da kogin Neja ba, zata cigaba da daukan nauyi. Bugu da kari Najeriya na cikin wasu kungiyoyi dake da alaka da kogin Neja.

Illar fita daga kungiyoyin zai yiwa Najeriya ya dangantaka ne da irin kungiyoyin da zata fita daga cikinsu inji Dr Kabiru Lawanti na Jami’ar Ahmadu Bello. Yana mai cewa akwai wadanda suke moran Najeriya saboda haka idan ta fita daga irin wadannan kungiyoyin babu wata illa. Inji Dr Lawanti wasu kungiyoyin ma basu da wani anfani da zasu yiwa kasar.

Yau Ce Ranar Samun Bayanai Ta Majalisar Dinkin DuniyaAntonio Guterres Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

A shekarar 2015 hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta amince da ranar 28 ta kowane watan Satumba a matsayin ranar samun bayanai ta duniya

Hukumar EUNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta amince da tsayar da kowace ranar 28 din watan Satumba a matsayin ranar samun bayani ta duniya.

A wannan shekarar an fara bikin rananr ne tun rana 25 ta wannan watan wanda yake gudana a kasar Tunisia, kasar da aka ce yanzu haka dai ta fi kowace kasa mai tasowa hanyoyin samun bayanan gwamnati.

Najeriya na cikin kasashen duniya da aka tsayar da dokar samun bayanan gwamnati ko kuma jami’an tsaro.To sai dai ba kasafai ba ne jami’an gwamnati ko na tsaro ke bin umurnin kotu ba dangane da bada bayanai.

Sau tari hakan ‘yan jarida ko lauyoyi na samun bayanai daga hukumomin gwamnati ba ya cimma ruwa.

Dr Danlami Alhassan kwararre kan harkokin sadarwa na Jami’ar Bayero dake Kano yace da yake ‘yan jarida ma basu ba ranar wani mahimmanci ba ta hanyar yin gangami ko shirya kasidu hukumomin gwamnati su kan ki su bada rahoton da ake nema.

‘Yan jarida na fuskantar matsaloli a Najeriya wajen tara bayanai saboda dari dari da jami’an gwamnati keyi da ‘yan jarida. Idan kuma su jami’an gwamnatin suna wata muna-muna ba zasu so bada bayani ba.

Dr. Danlami Alhassan ya bayyana abun da dokokin bada bayanai suka kunsa.

Yana mai cewa na daya duk wani dan kasa nada ‘yancin ya nemi bayani daga gwamnati ba tare da gindiya masa wasu sharuda ba. Na biyu an ba dan kasa ya je kotu ta tilastawa ma’aikatar gwamnati bada bayanan da mutum ke nema.

Abu na uku akwai hukumcin daurin shekara daya ga duk jam’in gwamnatin da yaki bada bayanan da ake nema. Abu na hudu duk wani jami’in gwamnati da ya ga ana almundahana ya kuma bayyanawa jama’a doka ta kareshi daga duk wani hukumci.

Doka kuma ta ce cikin kwana bakwai a baiwa mutum bayanan da ya bukata, idan kuma ba’a bayar ba to a bada cikakken bayanin dalilin da ya sa ba’a yi ba cikin kwanaki bakwan.

Zaben 2019: Gwamna Fayose Ya Samu Goyon Bayan Tsohoninistan Obasanjo


Tsohon ministan harkokin waje a lokacin Gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo kuma daya daga cikin manyan aminan sa Cif Femi Fani Kayode ne dai ya fara fitowa fili ya ayyana goyon bayan sa ga dan takarar ta shafin sa na Tuwita.

Siyasarnigeria.com  dai ta samu cewa tsohon ministan ya rubuta a shafin Tuwita din tasa cewa ya halarci taron kaddamar da takarar ta aminin sa Gwamna Fayose sannan kuma ya jinjinawa irin karfin zuciyar ta sa tare kuma da yi masa fatan samun nasara.

Mai karatu dai zai iya karantawa cewa mun ruwaito maku da safe cewar Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019.

A wani kayataccen taro da aka gabatar a Chelsea Hotel, Abuja a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, gwamnan ya ce kudirinsa na tsayawa takara ya kasance saboda soyayyar da yake ma Najeriya.

Majalisar Wakilai Ta Shiga Rikicin Sanata Kwankwaso Da Gwamna Ganduje
Majalisar dai ta nada wani kwamiti da zai binciki Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano kan yadda ya tafiyar da rikicin da ke faruwa tsakanin magoya bayan Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da kuma ‘yan akidar Kwankwasiyya.

Siyasarnigeria.com  dai ta samu cewa bangaren Kwankwasiyya dai na zargin Kwamishinan ‘yan sandan da takura masu kan duk wasu harkoki da suka shirya ya yi a jihar inda yake fifita bukatar gwamnatin jihar.

A kwanan nan ne,bangarorin suka gwabza a lokacin hawan Daushe wanda masarautar Kano ke shirya a duk shekara.

Abin da har yanzu mata ba su da izinin yi a Saudiyya?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sarkin Saudiyya ya zartar da dokar da ta amince wa mata yin tukin mota, abin da ya kawo karshen bambancin da ake nuna wa, yayin da ita kadai ce kasar da ta haramta wa mata tuka mota a duniya.

Sai dai duk da cewa sai a watan Yunin badi ne dokar za ta fara aiki, amma kuma akwai abubuwa da dama da mata ba za su iya samu ba, a kasar da ke bin tsattsauran ra’ayin addinin musulunci.

Har yanzu dai akwai abubuwa da dama da sai mata sun nemi izinin maza kafin su aiwatar.

Wadannan abubuwa sun hada da:

 • Neman takardun yin tafiye-tafiye ko fasfo
 • Yin balaguro zuwa wasu kasashe
 • Yin aure ko neman saki
 • Bude asusun ajiya a banki
 • Idan za su fara wata harka ta kasuwanci
 • Idan za a yi musu aikin tiyata amma ba na gaggawa ba
 • Idan za su bar gidan kaso

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Har yanzu akwai abubuwan da ba a bai wa mata izinin yi ba

Wadannan ka’idojin dai, na tasiri ne a karkashin tsarin muharami na Saudiyya.

Tun bayan kafuwarta, kasar ta ke bin tafarkin addinin musulunci na masu tsattsauran ra’ayi – wahhabism.

Bayan boren da masu tsananin kishin Islama suka yi a 1979, aka sake karfafa ka’idojin.

A cewar wani rahoto na shirin tattalin arziki na duniya na 2016, tsarin ya taimaka wajen sa kasar ta zamo daya daga cikin kasashen da ke nuna bambanci tsakanin jinsuna a Gabas ta Tsakiya, tana gaban Yemen da Syria, wadanda kasashe ne da ake yaki.

Sai dai duk da haka, akwai wasu fannoni na rayuwar mata da ba a shinfida musu ka’idoji ba, fiye da yada ake tsammani.

Tun a shekarar 2015 ne mata suka samu damar kada kuri’a.

Ilimin boko wajibi ne ga yara mata da kuma maza, har sai sun kai shekara 15, kuma an fi samun mata da suka kammala karatun jami’a a kan maza.

Kusan 16% na ma’aikatan kwadago mata ne.

Ana bukatar mata a Saudiyya su saka abaya mai tsawo, wadanda ba su kama jiki ba, a wuraren da za su yi tozali da maza wadanda ba danginsu ba ne.

Sai dai akwai wasu, da wannan doka ba ta tasiri a kansu.

An yi wa matan da suka fito daga kasashen waje sassauci game da irin rigunan da za su saka, kuma idan ba musulmai ba ne an amincesu su bar gashinsu a bude.

Wasu mata da suka fito daga kasashen ketare da suka yi tattaki zuwa kasar, sun ce sai da suka saka abaya kafin suka bar filin jirgin sama.

Amma kuma an samu matan shugabannin kasashen waje da suka kai ziyara Saudiyyar, wadanda ba su saka abaya ko kuma suka rufe gashinsu ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Melenia Trump da Michelle Obama ma ba su rufe kansu ba a lokutan da suka kai ziyara Saudiyya

Kasashe kalilan ne suke amfani da dokoki da suka fayyace abubuwan da mata za su iya yi da wanda kuma ba za su iya yi ba, sai dai kuma akwai wasu wurare da aka haramta wa mata yin wasu abubuwa.

Ga wasu daga cikinsu:

China: Ma’aikatar ilimi ta China ta hana mata neman ilimin hakar ma’adinai, da na aikin gina hanyar da jirgin kasa yake bi ta karkashin kasa ko ruwa da kuma wasu darussa.

Ta ce ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsaron lafiyar mata.

Isra’ila: A Israila mata ba za su iya neman saki daga wurin mazajensu ba, saboda kotunan addini ne suke da hurumin yin haka.

A shari’ar da ba kasafai ake gani ba, alkalai a Birtaniya sun fada wa wata matar da ta nemi rabuwa da mijinta cewa hakarta ba zata cimma ruwa ba saboda mijinta ba ya son rabuwa da ita.

Rasha: Akwai wasu ayyuka da aka haramtawa mata a Rasha, ciki har da na kafinta da na aikin kwana-kwana da tuka jirgin kasa da kuma jirgin ruwa.

Indonesia: Haka kuma an haramta wa mata da ke wani gari a Indonesia zama a bayan maza a kan babur.

Magajin garin Lhoksuemawe ya bukaci mata su dinga zama a gefen babur domin kare dabi’un al’umma masu kyau.

A baya ma sai da hukumomin garin suka haramta wa mata saka wanduna masu kama jiki.

Sudan: A Sudan kuwa, hukuncin da ake yanke wa mata da suka saka wando shi ne bulala.

Kano: Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Gargadi Kwankwaso

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga Sufeto janar na ‘yan sanda, IGP, Ibrahim Idris, don ya ja kunne tsohon gwamnan jihar, sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya gargadi magoya bayansa game da ayyukan da zai iya kawo rikici a jihar.

Majiyar Siyasarnigeria.com  ta tabbatar da cewar, majalisar ta yi wannan kira ne bayan tattaunawa akan wani motsi na muhimmancin jama’a wanda dan majalisa mai wakiltar Sumaila, Hamza Massu ya gabatar.

Mista Massu, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar, ya ce wannan kira ta nada muhimmanci bayan jerin kokawa na mazaunar jihar a kan ayyukan kungiyar Kwankwassiyya.

Majalisar dokokin jihar Kano

Ya tuna cewa rikicin tsakanin kungiyar Kwankwassiyya da kuma magoya bayan gwamna Abdullahi Ganduje a lokacin bikin murnar Sallah inda mutane da dama suka jikkata.

“Idan an yarda kungiyar ta ci gaba da irin wannan hali, abin da ya faru a lokacin sallah zai ci gaba da faruwa har ma fiye da tsammanin”, inji dan majalisar kuma memba na jam’iyyar APC.

Bayan shawarwarin da ‘yan majalissar suka yi, sun amince da kiran IGP don ya gargadi sanata Kwankwaso, don yin la’akari da kungiyar da kuma dakatar da ayyukan da zai iya jefa jihar a cikin rikici.

Bayern Munich ta kori Carlo Ancelotti


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kocin mai shekara 58 ya jagoranci Real Madrid tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sallami kocinta, Carlo Ancelotti, kwana guda bayan ta yi rashin nasara a hannun Paris St-Germain (PSG).

A ranar Laraba ne PSG ta doke Bayern da ci 3-0.

Ancelotti ya maye gurbin Pep Guardiola a kakar bara.

Ancelotti dan asalin Italiya ya taimaka wa Bayern ta lashen kofin Bundesliga a baya, amma kuma kungiyar ta iya kai wa wasan gab da na kusa da na karshe a kasar Zakarun Turai.

Mataimakinsa Willy Sagnol ne zai maye gurbinsa a matsayin kocin wucin gadi.

Wanda Zai Gaje Ni Ba Zai Gaji Boko Haram Da Sansanonin Gudun Hijira Ba – Inji ShettimaGwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya sha alwashin cewa magajinsa ba zai gaji rikicin Boko Haram da sansanonin yan gudun hijira ba.

Ya bayyana haka ne jiya a Maiduguri yayinda yake rantsar da wata kwamiti a gidan gwamnati, don mayar da yan gudun hijira miliyan 2 kayyukan su.

Yayi gargadi kan mayar da yan gudun hijiran ba tare da neman tsaro ba martaba, kamar yanda yazo sharadi ga yan gudun hijira a Kampala.

Kwamiti din ta bada sharruda ga takardun shaida hade da hakikantaka da rajistan dukkan yan gudun hijiran, da bayar da katin shaida, lambar sake ginin gidaje da mayar day an gudun hijiran.

Wanda zai gaje ni ba zai gaji Boko Haram da sansanonin gudun hijira ba – Inji Shettima

Ya bukaci kwamitin da ta tabbatar cewa an kafa kungiyoyin jama’a yanda aka saba, tare da makarantu, asibitoci, ruwa da kayan more rayuwa kafin komawar yan gudun hijiran zuwa kauyukan su.

Har ila yau, mai kula da harkokin yan gudun hijira na majalisan dinkin duniya a Najeriya, Mr. Edward Kallon, yayi gargadi akan gusawar yan gudun hijiran mara tabbass.

Ya bayyana cewa matsa da yan gudun hijira da daga sashen dake mawbakja na ci gaba da zama kalubale ga hukumomin agaji.

Yanzu Yanzu: Gwamna Fayose Ya Kaddamar Da Kudirinsa Na Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa A 2019 A Abuja

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019.

A wani kayataccen taro da aka gabatar a Chelsea Hotel, Abuja a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, gwamnan ya ce kudirinsa na tsayawa takara ya kasance saboda soyayyar da yake ma Najeriya.

Ya bayyana cewa shine mutumin da zai jagoranci Njeriya wajen fita daga halin da take ciki a yanzu.

Siyasarnigeria.com  ta gano tarin magoya bayan gwamnan sanye cikin riga da hula da aka rubuta ‘Fayose shugaban kasa’, inda suke rawa da waka a wajen taron.

Yanzu Yanzu: Gwamna Fayose ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019 a Abuja

A baya Siyasarnigeria.com  ta rahoto cewa kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa na Gwamna Ayodele Fayose ya samu cikas tunma kafin ya fara yayinda jam’iyyar PDP wanda yake niyan tsayawa takara a karkashinta ta bukaci da ya daina bata lokacin sa.

Jam’iyyar ta fada masa cewa kujerar shugabancin ta na yankin arewacin kasar ne inda ta kara da cewa dukkanin mambobinta sun san da haka.

Wani Gwamna Zai Mika Kami’An Gwamnatin Sa Da Ya Nada Hannun ‘YansandaGwamnan jihar kuros Riba, Ben Ayade, ya bayar da umarnin tantance masu rike da mukaman siyasa a jihar. Da yawa daga cikin nadaddun jami’an gwamnatin jihar da yawan su yakai 600 ba gwamnan ne ya nada su kai tsaye ba. Mai bawa gwamna shawara a kan yada labarai a jihar, Mista Christian Ita, ne ya bayyana hakan.

A wata takarda da sakataren gwamnatin jihar ya sanyawa hannu, gwamna, Ayade, ya bayar da umarnin gaggauta tantance duk masu rike da mukaman siyasa dake jihar. Za a gudanar da tantancewar ne karkashin hadin gwuiwar ofishin babban akawu na jihar da ofishin shugaban ma’aikata tamkar yadda aka gudanar da tantance ma’aikatan jihar. Sanarwar ta ce duk wani mai rike da mukamin siyasa da aka gano ba gwamna ne ya nada shi ba za a mika shi hannun jami’an tsaro domin bincike.

Sanarwar ta ce tantancewar ta zama dole ne biyo bayan yawaitar kudaden da jihar take kashewa da sunan albashin masu rike da mukaman siyasa hadi da sunaye baki da gwamnati ke gani cikin jerin masu rike da mukaman.

Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, yana neman shugabancin Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Fayose twitter

Image caption

Fayose ya fara zama gwamnan jihar Ekiti ne a shekarar 2003

Gwamnan jihar Ekiti a Najeriya Ayodele Fayose ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2019.

Mista Fayose wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, yana yawan sukan manufofin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, mai mulki.

Jam’iyyar APC, wanda ta karbi shugabancin Najeriya kusan shekara biyu da su wuce, ba kasafai ake jin duriyar jam’iyyar adawa ta PDP wanda take fama da rikicin cikin gida.

Jam’iyyar PDP wanda tayi shekara 16 tana shugabancin Najeriya kafin ta sha kayi a hannun a APC a shekarar 2015.

Fayose ya fara zama gwamnan jihar Ekiti wadda yankin take kudu-maso-yammacin kasar ne a shekarar 2003, kafin ya sake zama gwamnan jihar a shekarar 2014.

Zuwa yanzu dai shi ne mutum na farko da ya bayyana aniyyarsa ta neman shugabancin kasar a hukumance.

Lafia: ‘Yan anda Sun Cafke Masu Mambobi 2 Na Kungiyar Masu Sata Mota A Nasarawa


 


Hukumar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta sanar a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba cewa ta kama wasu mambobi 2 na’ yan bindiga guda 3 masu satar mota wadanda suka haddabi al’ummar jihar.

Mista Idrissu Kennedy, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya shaida wa NAN majiyar NAIJ.com a Lafia cewa an gano wata mota wanda ake sa ran sun sace a lokacin da aka kama su.

Hukumar ta ce ta na samun rahotanni game da kungiyar ‘yan bindigar 3 a kan sace motoci a sassa daban-daban na jihar.

“Ta hanyar tattara bayanai ta hankula, mutanen mu sun kaddamar da hare-hare a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, kuma muka kama mutane biyu a Masaka a yankin karamar hukumar Karu” , inji Kennedy.

“Daya daga cikinsu ya tsere, amma muna biye da shi kuma za mu kama shi”, in ji shi.

Ya ce sun gano wata motar da suka kwace a hannun Mista Yusuf Manga ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba a garin Akwanga.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana wadanda aka kama a matsayin Nasiru Danjuma da Collins Osaye, mazauna Agwan Zakara a Uke da ke karamar hukumar Karu, inda ya kara da cewa ana binciken su don gano sauran wadanda ke tallafa masu.

An sace mataimakin kwaminishin 'yan sanda a Nigeria


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan lamarin ya auku ne a lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya take cewa tana iya kokarinta wajen ganin ta dakile sace-sacen mutane a fadin kasar

Rahotanni a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sace wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda tare da matarsa a yayin da suke tafiya a mota. An sace mataimakin kwamishinan nan ne a wani dajin da ke tsakanin Funtua a jihar Katsina da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wata majiya mai karfi ta tsaro a jihar Kaduna ta shaida wa BBC cewa, mataimakin kwamishinan na ‘yan sandan na aiki ne a jihar Zamfara ko kuma a jihar Katsina.

Har yanzu dai rundunar ‘yansan da ta jihar Kaduna ba ta ce komai ba a bisa wannan batu, to sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar wanda wakilinmu na Kaduna ya tuntuba, ya ce suna wani taro, inda ya bukace shi da ya sake kiransa bayan taron.

Dajin da aka sace wannan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda dai dama sanannen wuri ne da aka yi amannar na kunshe da ‘yan ta’adda kamar ‘yan fashi da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Jihar Kaduna dai ta yi kaurin suna a sace-sacen mutane, kuma kwanakin baya an sace tsohon ministan kasar, Ambasada Bagudu Hirse a cikin birnin Kaduna.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cewar suna daukar tsauraran matakai domin magance matsalar tsaro a jihar.

Ana zubar da ciki sau miliyan 56 a duniya duk shekara – WHO


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wata mata na shan fama da azabar ciwon mara sakamakon zubar da ciki da tay a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta ce kashi 50 cikin 100 na zubar da ciki da ake yi a duniya na cike da hadari.

Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ambato wani rahoto na wani bincike da hukumar WHO ta gudanar, wanda ya nuna cewa ko wacce shekara ana zubar da ciki kusan sau miliyan 56 a fadin duniya, kuma kusan rabi na cike da hadari.

Yawan zubar da ciki da ake yi mai cike da hadari na faruwa ne a Afrika, inda zubar da ciki daya cikin hudu ne kawai ba ya zuwa da hadari, kuma a nan ne aka fi samun yawan mace-mace sakamakon zubar da cikin.

A cikin wani bincike da aka wallafa a wata mujallar lafiya ta Lancet, ya ce an zubar da ciki sau miliyan 55.7 a ko wacce shekara daga 2010 zuwa 2014 a duniya.

Binciken ya kuma ce miliyan 17.1 na cikin da aka zubar ya zo da hadari, saboda matan da suka aikata haka din sun sha magunguna ne da kansu ko kuma wasu kwararru sun taimaka musu amma ba ta ingantacciyar hanyar da ta dace ba.

Mutumin da ya kirkiro mujallar 'batsa' ta Playboy Hugh Hefner, ya mutu


Hakkin mallakar hoto
AFP

Hugh Hefner, dan Amurkar nan da ya kirkiro mujallar da ke nuna mata tsirara ta kasa da kasa Playboy, ya mutu yana da shekara 91.

Kamfanin Playboy Enterprises Inc ya ce Mista Hefner ya mutu ne a gidansa da ke Los Angeles.

Hefner ya fara buga mujallar Playboy ne a wajen da yake dafa abinci a shekarar 1953.

Mujallar ta zamo mujallar da ta fi ko wacce kasuwa a duniya inda take sayar da kwafi miliyan bakwai a ko wanne wata a lokacin da mujallar ta fi yin kasuwa.

Cooper Hefner, dansa, ya ce: “mutane da yawa za su” yi kewarsa.

Cooper ya yaba da rayuwarsa babansa “ta musamman mai gagarumin tagomashi,” inda yake ganin mahaifin nasa a matsayin wani mai fasaha a fannin ala’ada da kafafen watsa labarai.

Ya kuma bayyana babansa a matsayin mai fafatukar ‘yancin tofa albarkacin baki da ‘yancin jama’a da kuma ‘yancin jima’i.

Mujallar Hefner da ta kafa tarihi ta sa ana kallon nuna tsiraici ba komai ba ne a kafofin yada labarai, duk da cewar mujallar ta fara fitowa ne a lokacin da jihohin Amurka ka iya hana anfani da magungunan hana daukar ciki.

Mujalallar ta kuma mayar da shi miloniya, lamarin da ya haifar da wata daular kasuwanci da ta kunshi gidajen caca da gidajen rawa.

Mujallar ta farko tana dauke ne da hotunan Marilyn Monroe tsirara, wadanda asali an daukesu ne domin bugawa a wata kalandar shekarar 1949, amman shi Hefner ya sayi hotunan kan kudi $200.

Attajirin wanda aka san shi da yawan son saka kayan barci, ya shahara da dabi’arsa ta fifita sha’awa da nema tare da auren ‘yan matan da ke fitowa a mujallarsa tare da gudanar da bukin fitsara a kawataccen gidan Playboy da ke Los Angeles.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ga katafaren gidan Playboy wanda ya yi kaurin suna a Beverly Hills

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Hefner da ‘yan matan da yake daukar hotunansu tsirara sun yi tafiya kan jirgin Playboy a lokacin da mujallar take tashe a shekarun 1970

A shekarun 1980, gogayya daga wasu mujallun da suka fi Playboy nuna tsiraici ta sa kasuwar mujallar ta ragu, kuma Hefner da kansa ya yi fama da mutuwar wani sashe na jikinsa a shekarar 1985.

‘Yara, Christie ta karbi jagorancin kamfanin bayan shekara hudu, kuma Hefner ya koma katafaren gininsa tare da wasu mata.

A shekarar 2014 ne Cooper Hefner ya taka gagarumar rawa a kamfanin bayan Christie ta yi murabus a shekarar 2009.

Mujalar ta yanke shawarar nuna tsiraici a watan Maris din shekarar 2016, amman ya sake shawara a farkon wannas shekara ta 2017.

Wani makwabcin Hefner ya sayi katafaren gidan Playboy kan kudi dala miliyan 100 a watan Augustan shekarar da ta gabata, amman ya amince da cewar Hefner ka iya ci gaba da zama a ciki har sai ya mutu.

Takaitaccen tarihinsa

An haifi Hefner ne a shekarar 1926 a birnin Chicago, kuma ya yi aikin sojin Amurka a tsakiyar shekarun 1940.

Ya kammala karatun digiri a fannin nazarin halayyar dan adam, kuma ya yi aiki a matsayin marubuci a mujallar maza da ake ce wa Esquire, kafin ya ranci kudi $8,000 domin ya fara wallafa Playboy a shekarar 1953.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Hefner ya mutu bar matarsa ta uku, Crystal Harris

Nigeria: Yaron da mayakan BH suka take da babur ya fara tafiya


Image caption

Masu ta da kayar baya na Boko Haram ne suka take shi da babur a shekarar 2014

Wani dan Najeriya dan shekara biyar, wanda ya ji mummunan rauni a lokacin da mayakan Boko Haram suka take shi da babur, ya fara tafiya a karon farko tun lokacin da ya ji ciwon.

Mayakan sun hau doron bayan Ali Ahmadu da babur ne a lokacin da yake neman tserewa tare da mahaifiyarsa daga farmakin da aka kai wa kauyensu, Chibok.

A yanzu dai Ali ya fara tafiya, bayan an yi masa aikin kashin baya a Dubai.

Wata kungiyar agajin Najeriya ce ta biya kudin aikin da aka yi masa bayan ta tara kimanin fam 45,000 domin a yi wa yaron aiki.

Ana tsammanin Ali zai zauna a Dubai na kimanin wata uku inda za a yi masa magani na motsa jiki domin a farafado da karfinsa.

Image caption

Ali yana dan shekara biyu ne kawai a lokacin da mayakan Boko Haram suka take shi

Shugaban kungiyar ba da agajin da ta shirya samar wa yaron magani, Nuhu Kwajafa na kungiyar Global Initiative for Peace, Love and Care, ya shaida wa shirin Focus on Africa na shahen Turancin BBC, cewar Ali bai samu ganin likita ba tsakanin lokacin da lamarin ya auku da kuma lokacin da ya isa Dubai.

“Yana kwance ne da ciwon a kashin bayansa,” in ji mista Kwajafa.

“Yana da wani nau’in tarin fuka wanda bai fara tasiri ba, tare da wasu cututtuka, kuma an bar shi a kauyen.”

A yanzu, bayan an yi masa aiki, “yana kai wa da komowa a daki, yana magana, yana surutu, ban taba ganinsa a cikin irin wannan halin ba.”

EFCC: Lauyoyi Da Kungiyoyi Daban-Daban sun gabatar da kara 17 a kan MaguKimani kara 17 aka gabatar a gaban kotu daban-daban a fadin kasar game da kujerar shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Malam Ibrahin Magu.

Wasu daga cikin karar na bukatar cire Ibrahim Magu ko kuma a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar EFCC.

Duk da yake wasu daga cikin karar suna bukatar tabbatar da Magu yayin da mafi yawansu ba su yarda a tabbatar da shi ba. Daga cikin wuraren da ake samu jinkirin al’amuran sun hada da babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja da ta Yola a jihar Adamawa da ta Kano a jihar Kano da kuma Legas. Game da karar 7 suna jira a gaban babbar kotu ta Abuja, yayin da sauran 12 suka kasance a wasu sassa 

Wasu lauyoyi da kungiyoyi suka gabatar da mafi yawan wadannan karar. Wani babban lauya na Abuja, Johnmary Jideobi ya gabatar da daya daga cikin karar yayin da yake neman umarnin kotu don dakatar da Magu daga bayyana kansa a matsayin shugaban EFCC.

Wani lauya na Abuja, Wale Balogun shi kuma ya na neman kotun ta dakatar da Magu daga ci gaba da zama shugaban hukumar.

Wani lauya daga Legas, Ebun-Olu Adegboruwa, shi ma ya gabatar da kara a kan Magu, amma daga bisani sai ya janye karar. Har ila yau, wasu kungiyoyi biyu, Save Nigeria Group da kuma kungiyar kare hakkin dan Adam wato Kingdom Human Rights Foundation sun gabatar da kara game da Magu, amma daga bisani suka janye.

Duk da haka, ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya bukaci babban alkali na kotun tarayya, Abuja, Justice Abdul Kafarati ya sulhunta tsakanin kara 17 da aka shigar don kauce wa yin shara’a daban-daban a karkashin ikon kotun.

Jam’iyar PDP Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Yi Taron SulhuBakin ‘ya’yan jam’iyyar PDP shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, ya zo daya da batutuwa da suka rage kimarta a idon masu kada kuri’a da ya kai ta ga shan mummunan kaye daga jam’iyya mai jihohi hudu zuwa biyu a shiyyar.

Jam’iyar PDP ta bada bayanin haka ta bakin shugaban kwamitin sasantawa da shiga tsakani kuma gwamnan jihar Taraba Arc. Darius Dickson Ishaku a zaman babban taron ta da kaddamar a Yola fadar jihar Admawa gabannin babban taron ta na kasa da shirye shiryen shiga zabubbukan shekarar 2019.

Da yake jawabi a taron shugaban jam’iyar PDP ta kasa shiyyar arewa maso gabas, Jakada Emmanuel Njuwa ya ce daga cikin batutuwa da suka sa PDP ta sha kaye akwai gunaguni game da yadda ake tafida lamura daga sama wanda ya sa ‘yan jam’iyar suka juya mata baya lokacin zabubbuka.

Batun da ya fi daukar hankulan mahalarta taron sune yadda jam’iyar zata kauda rashin adalci da dauki dora lokacin zaben fidda da gwani da rashin kamanta gaskiya wajen gudanar da lamuran jam’iyar wanda shugaban rikon kwarya na PDP jihar Adamawa Hon Mohammed Alkali Imam ya ce na bukatar a magance su cikin gaggawa.

Bayanin bayan taro da Sanata Grace Bent ta bayar ya nuna jam’iyar PDP shiyyar arewa maso gabas zata karawa mata da matasa guraben da za a rika damawa da su a harkokin shiga takara da gudanar da jam’iyar.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia Ta Ce Bata Da Masaniyar Inda Nnamdi Kanu Ya KeRundunar ‘yan sandan jihar Abia, ta bayyana cewa bata da wata masaniya akan inda madugun kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yake a halin yanzu da ake ci gaba da tofa albarkacin baki a kan batun a kudancin Najeriya.

A wata hira da suka yi da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Alphonsus Okoroigwe, Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Abia, Mr Anthony Okwueze, ya bayyana cewa basu da masaniya akan inda Nnamdi kanu yake.

Jami’in ya bayyana cewa da suna da masaniya da sun fahimtar da shi akan tunani mai armashi, dan haka ya kara da cewa idan manema labarai na da masaniya, akwai bukatar su shaidawa jami;an domin tafiya tare wajan shawo kan lamarin.

Lamarin batan dabon da madugun kungiyar ya yi ya haifar da musayar ra’ayoyi a tsakanin jama’ar jihar, Mr Moses Okoye, wani dan kasuwa ne kuma ya bayyana cewa tana iya yiwuya Nnamdi Kanu na raye ko kuma baya raye ganin yadda sojoji suka kai hari a fadar mahaifinsa, dan haka idan yana raye a taimaka a sake shi.

A cewar Mr Emeka, wani daga cikin mazauna birin ya bayyana cewa a nasa ra’ayin shugaban kungiyar na nan a raye domin a cewar sa da anga gawar sa a ranar da sojoji suka kai hari a fadar mahaifin sa.

Kun san yadda za a kauce wa kamuwa da sankarar mama?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hoton cutar daji da ke nuna kwayoyin halittan da suka hayayyafa fiye da yadda ya kamata

Wannan makala ce kan bayanai game da yadda ake kamuwa da cutar sankarar mama da yadda za a iya kauce mata, kuma wannan makala an yi ta ne don amsa tambayoyinku da ku ka turowa BBC kan batun, wadanda muka yi alkawarin amsa muku.

Sankara dai tana aukuwa ne a lokacin kwayar halitta mai illa ta fara hayayyafa fiye da yadda ya kamata. Wannnan hayayyafar kwayar halittar yakan kai ga matakin ciwo mai tsanani, kuma a wasu lokutan yakan kai ga mutuwa.

Sankara dai ta kan kama mata da maza a sassa daban-daban na jikinsu.

Alkalluma daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ce sankarar mama (breast cancer) ita ce sankarar da ta fi kama mata a duniya, inda mata miliyan daya da rabi ke kamuwa da cutar a ko wacce shekara.

Har wa yau, alkaluman sun nuna cewar, ita sankarar mamar ce ta fi kashe mata da yawa a duniya.

Kuma a shekarar 2015 sankarar mamar ta yi sanadiyyar mutuwar mata 570,000 a duniya.

Dr Zainab Bagudu, likitar mata da kanana yara, kuma matar gwamnan jihar Kebbi, wadda ta kafa gidauniyar MedicAid da ke yaki da cutar sankara a arewacin Najeriya ta ce: “A Najeriya, muna da karancin samun tabbacin yawan ko wacce cuta, ko mura ko malariya, balle ciwo mai tsanani kamar sankara.

“Amman an yi kiyasin cewar mutum sama da 250,000 ne kamuwa da cutar a ko wacce shekara a Najeriyar,” in ji ta.

Amman ta yaya ake kamuwa ta cutar sankaran mama?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suka aiko mana ta shafinmu na BBC Hausa.com bayan da muka bukaci su turo tambayoyin da suke so sani kan wannan batu.

Dr Zainab Bagudu ta ce cutar sankara tana da wahalar ganewa kuma ba a san takamaiman dalilin da ke sa a kamu da cutar ba.

Ita ma wata kwararriyar likita da ta taba aiki a asibitin kasa na Najeriya da ke Abuja, wadda a yanzu haka ta bude nata asibitin, Dr Hajara Yusuf, ta ce har yanzu ba a gano takamaiman dalilin da ke janyo cutar ba.

Amman ta ambato dalilai da ke taimakawa wajen kamuwa da cutar.

Dalilan sun hada da yawan shekaru (a Najeriya macen da ta kai shekaru 50 na iya kamuwa da cutar), da shan barasa, da amfani da sinadarin Estrogen da kwayoyin halittar da ke dauke da bayanai na gado wadanda ke iya haifar da cutar.

Likitar ta ce sankarar mama da ta mahaifa ne suka fi damun mata.

“Amman maruru ko kurji da ke iya fitowa kan mama ciwo ne na fata,” in ji Dr Hajara.

Likitar ta bayyana cewar kurji yana jikin fata ne, bai kai ga abin da ke cikin mama ba.

Sai dai kuma ba mata kadai ne suke kamuwa da cutar sankarar mama ba, maza ma suna kamuwa da cutar.

Masana sun ce kashi daya cikin dari na masu sankarar mama maza ne.

Hakkin mallakar hoto
DrZus Instagram

Image caption

Dr Zainab ta ce akwai bukatar mata su dinga zuwa ana duba su a asibiti akai-akai

Shima kululu ba shi da wata barazana?

Likitoci sun ce in har mace ta ji wani kululu ko wani kulli cikin nononta, ya kamata ta garzaya zuwa asibiti domin a yi maganin matsalar tun tana karama.

Sai dai kuma ba ko wanne kululu ne sankara ba. Sai an cire kululun an gwada kafin a gane cewar sankarar mama ne ko kuma ba shi ba.

Har wa yau likitoci na son macen da ta lura cewar wani nononta ya fi wani girma ta je asibiti a duba ta domin a iya dakile cutar dajin da wurwuri.

Kazalika in mace ta lura cewar kan nononta ya koma ciki ta yadda jariri ba zai iya kama kan nonon ba, ana son ta je a duba domin yana daga cikin alamomin sankarar nono.

Baya ga haka idan macen da ba ta shayarwa ta ga ruwan na fitowa daga nononta a hade da jini, ita ma ana son ta garzaya asibiti domin a duba.

Sai dai kuma ba ko wacce mace da ke da daya daga cikin wadannan alamun ne ke da ciwon ba, duk da cewa alamu ne da ke nuna cewa mace za ta iya kasancewa da sankarar mama.

Ta yaya za a guje wa Sankarar mama?

Masana sun ce za a iya guje wa sankarar mama ne ta hanyar fitar da gujewa abubuwan da ke taimaka wa sankarar mama irin su barasa da sinadarin Estrogen da sauransu.

“Da farko zan ce yana da kyau mutum ya ci abinci mai kyau. Abinci, ba wanda ake saya a kanti ko ake sarrafawa a zuba a robobi ko gwangwanaye ba, abinci wanda muke nomawa, wanda za a ci.

“Ba wanda ya yi shekara daya a cikin firiza ko kuma firji ba, ko kuma an dauko shi cikin gwangwani daga can kasashen waje, ya dade a tashar jirgin ruwa, sannan kuma a zo da su Najeriya,” In ji Dr Zainab Bagudu.

Wace illa sankarar mama ke yi wa yaro? Wannan ma tambaya ce da ta fito daga wajen mutane da dama kan batun.

Masana sun ce sankarar mama ba ta yi wa jaririn da ake shayarwa illa domin shi sankarar ba ta yaduwa da jini ko nono. Saboda haka ana ganin mace mai wannan larurar za ta iya shayarwa ba tare da wani fargaba ba.

Ta yaya ake maganin sankarar mama?

Ana maganin sankarar mama ne a manyan asibitoci inda ake da kayayyakin aikin da kwararru kan maganin sankara.

Ban da maganin sha, ana maganin sanakarar mama ta hanyar cire sankarar mama ya kama da kuma gasa wurin da ya kamu da ciwon ta yadda sankarar za ta mutu.

An yi wannan makalar ne kan sankarar mama bayan masu bibiyar Sashen Hausa na BBC suka turo mana tambayoyi game da larurar.

NIGER: Kungiyar PROMAB Ta Tallafawa Mata Manoma​Wata kungiya da ake kiea PROMAB a jahar Agadez dake jamhuriyar Niger, ta talafa wa kungiyoyin mata manoma yadda za su adana kayayakin da suka noma, ta yadda baza su lalace ba kuma su dade ana amfani da su.

Mohammed, shine wakilin kungiyar PROMAB ta jamhuriyar kuma yayi karin bayanin cewa kungiyar ta mayar da hankali ne wajan ayyukan noma, wato a fannin da ya jibanci bada horo da tallafi da kuma bada shawarwari ga manoma da kungiyoyi.

Ya kara da cewa suna aiki kafada da kafada da gwamnati domin taimakawa hukumar dake kula da harkokin gona ta Nijer, cikin tsare tsaren ta na inganta harkokin noma a jamhuriyar Nijer.

Mohammed, ya bayyana cewa kungiyar ta fara aiki tun daga shekarar 2012, dan haka a cikin shekaru biyar da kungiyar ta kwashe tana gudanar da wadannan ayyuka ta sami nasarori da dama, kama daga ba manoma horo da tallafi ga mata masu sana’ar sarrafa kayayyakin gona.

Cikin kayayyakin aikin da wannan kungiya ta bayar sun hada da Tantan da injinan busar da anfanin gona da tamfal da sauran su

Ban san abin da ke damun Buhari ba – Lai Mohammed


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN GOVERNMENT

Image caption

A cikin wannan shekarar sau uku Shugaba Buhari na zuwa Landan

Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce bai san takamaiman abin da ke damun Shugaba Muhammadu Buhari ba ta bangaren lafiyarsa, don haka ba zai iya yi wa ‘yan kasar karin bayani ba.

Alhaji Lai Muhammed ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da sashen Turanci na BBC Newshour.

Ga dai yadda hirar ta kasance:

Tambaya:Ko zan iya tambayarka dangane da shugaban kasa da yanayin lafiyarsa, inda ya zo nan London a makon da ya gabata, kuma ziyararsa ta uku kenan cikin shekara, inda a wancan karon ya shafe wata uku ana duba shi. To yaya lafiyarsa take?

Lai Mohammed: Ya samu sauki sosai, ya murmure.

Tambaya:To ko wacce irin cuta ce shugaban yayi fama da ita?

Lai Mohammed: Ina ganin cewa, shugaban ne kawai yake da ikon bayyaana ciwon da yayi fama da shi.

Tambaya:To ko kai kasan cutar da yayi fama da ita?

Lai Mohammed: Ban sani ba, kuma bana son na sani.

Da gaske, a matsayinka ministan watsa labarai?

Tambaya:Eh.

Tambaya:To menene yasa haka?

Lai Mohammed:Wannan wani abu ne da ya shafi shugaban kawai.

Tambaya:Amma wannan abu ne da yake da matukar muhimmanci da ‘yan Najeriya zasu so su sani?

Lai Mohammed: Ina ganin koda a matsayinka na shugaban kasa, kana da ikon kare sirrinka, a wasu lokuta, kuma ina ganin babu wani abin sirri kamar yanayin lafiyar mutum.

Tambaya:Na fahimci wannan ikon, amma kuma akwai alhakin sanin wanda ke rike da ragama, wa yake tafiyar da abubuwa, ko zai iya rike shugabanci saboda rashin lafiya,inda ya shafe watanni uku anan London don neman sauki?

Lai Mohammed: Mr Frank, baa taba samun gibi na shugabanci a wannan gwamnatin ba, ba a taba samu ba, idan da an samu wani gibi, tattalin arzikin bazai taba farfadowa ba.

Da akwai gibin shugabanci lokacin da shugaban yake Birtaniya, da ba zamu samu nasarar da muka samu a bangaren yaki da rashawa da dawo da zaman lafiya a yankin Niger Delta ba, don haka babu wani gibi, lallai da mun ace yana nan, mun yi kewarsa, amma fa babu wani gibi da aka samu.

Tambaya:Da alama babban lamari ne, idan har shugaban bazai iya samun cikakkiyar kulawar lafiyarsa a kasarsa ba?

Lai Mohammed: Ba wani sabon abune ba, mutum ya yi ciwo na wata uku, sannan ya samu cikakkiyar lafiya.

Tambaya:Eh amma ba kamar shugaban babbar kasa kamar Najeriya ba?

Lai Mohammed: Gaskiyar lamarin shi ne, akwai shugabannin kasashe da yawa, da da wuya ake ganin su.

Tambaya:Misali kana nufin kamar su Zimbabwe?

Lai Mohammed: Aa, aa bazan kira sunan kowacce kasa ba, abinda nake nufi shine babu wani laifi a rashin lafiya, da kuma samun sauki, tare da dawowa kan aiki.

Tambaya:Kana nufin ya samu sauki, ya murmure kenan.

Lai Mohammed: Eh tabbas shugaban kasa ya mumure sosai ma kuwa.

Bashi ya sa Najeriya ficewa daga wasu kungiyoyi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta dauki iya abin da take ganin za ta iya ne wajen mu’amala da kungiyoyi.

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar ficewa daga wasu kungiyoyin kasa da kasa kusan 90, sakamakon dawainiyar da ke tattare da mu`amala da kungiyoyin.

Majalisar zartarwar kasar ce ta dauki wannan matakin, tana cewa bashin kudin gudummuwar raya kungiyoyi kadai da ake bin gwamnatin ya zarta dala miliyan 100.

Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, akwai kungiyoyi birjik ko na tsakanin kasa da kasa ko na Majalisar Dinkin Duniya ko kuma na kungiyar hadin kan Afirka da Najeriya ta shiga cikinsu wadanda kuma dukkansu akwai bukatar gudummuwar da duk kasar da ke cikinsu sai ta bayar a karshen kowacce shekara.

Malam Garba Shehu, ya ce saboda irin wadannan kudaden gudummuwar tafiyar da kungiyoyin wadanda Najeriya ba ta biya ba, har ta kai idan aka je taro akan bukaci mi wkiltar Najeriya da ke wajen ya fita, saboda kawai ana bin kasarsa bashin kudin gudunmmuwar kungiyar.

Ya ce hakan ba karamin abin kunya ba ne ga Najeriya.

Don haka shugaba Muhammadu Buhari ya ce, to ya kamata a sake lale, inda za a baje irin wadannan kungiyoyin a faifai a zabi wadanda ke da amfani ga kasar dan a ci gaba da tafiya tare da su.

Kakakin shugaban Najeriyar, ya kara da cewa wasu basukan da ake bin Najeriyar ma, wani ko shugaban kasa ko kuma minista ne zai je tarukan irin wadannan kungiyoyi ya yi alkawarin cewa, ai Najeriya za ta bayar da gudunmuwar kaza wanda kudin ma babu su a kasa.

Ya ce: ”To irinsu ne suka taru suka yi wa Najeriya yawa, har ta kai ana kunyata ta a wajen taro.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a wannan bangare, gwamnatinsa za ta dauki iya abin da take ganin za ta iya ne wajen mu’amala da irin wadannan kungiyoyi.

Malam Garba Shehu, ya ce wadannan basukan ma da aka ce ana bin Najeriyar, tun na shekara da shekaru ne, don haka a kididdige shi ma abu ne mai kamar wuya.

Hak kuma ya yi nuni da cewa, ba matsi ne ya sa Najeriya za ta fice daga wadannan kungiyoyi ba, sanin ciwon kai ne kawai.

Chadi Ta Yi Mamakin Saka Ta Cikin Kasashen Da Aka Hana Ma Zuwa Amurka Cikin Sauki


Shugaba Idris Deby na Chadi yana jawabi gaban taron Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Chadi ta yi mamakin saka ta da Amurka ta yi cikin jerin kasashen da aka haramta ma mutanensu zuwa Amurka ba tare da matakai masu tsauri ba. Gwamnatin kasar ta ce ita fa ba ta fahimci musabbabin saka ta cikin jerin kasashen da aka tsaurara masu sharuddan shiga Amurka ba.

Bayyanar sunan kasar Chadi a cikin jerin sabbin sunayen da Amurka ta fitar na wadanda aka haramtawa shiga kasar ya jefa Chadin cikin mamaki.

A wata sanarwa da Ministar sadarwar kasar ta fitar da harshen Faransanci, Madeleine Alingue, ta ce gwamnatin ta Chadi, ba ta fahimci dalilin da ya sa aka saka sunanta a jerin sunayen kasashen da aka haramtawa shiga Amurkan ba.

A ranar Lahadin da ta gabata, gwamatin Shugaba Trump ta fidda sabbin ka’idojin shiga kasar, wadanda aka dora su akan na farko da aka gindaya a watan Maris din da ya gabata, wadanda suka haramtawa wasu kasashe shida, masu mafiya rinjayen Musulmi shiga Amurka.

Sabbin ka’idojin sun hada da kasashen Venezuela da Korea ta arewa da kuma Chadi.

Jama’a da dama sun nuna mamakinsu da aka saka sunan Chadi cikin jerin sunayen, domin kasa ce da ta kasance kawa ga Amurka wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

Baya ga haka, Amurka ta sha jagorantar atisayen yaki da ta’addanci a kasar, tare da horar da dakarunta, wadanda ake musu kallon babu kamarsu wajen kwarewa a yankin tsakiyar Afirka.

Ita dai Chadi tana tsakiyar wani yanki ne mai tsauri, zagaye da kasashe irinsu Libya da Sudan da Najeriya da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Sabbin ka’idojin sun nuna cewa kasar ta Chadi ba ta ba da bayanan da suka shafi kare lafiyar jama’a da yaki da ta’addanci.

Har ila yau ka’idojin sun nuna cewa akwai kungiyoyin ‘yan ta’adda da dama a kasar ko a kewayenta da suka hada da Boko Haram da reshen kungiyar ISIS dake yammacin Afirka da na Al Qa’ida da ke yankin Islamic Maghreb.

Amurka Ba Za Ta Fasa Fada A Afghanistan Ba – Jim Mattis


Birnin Kabul ne wuri na biyu da Mattis ya je a ziyarar da yake yi a kasashen yanken kudancin Asiya, bayan da ya fara zuwa New Delhi, babban birnin kasar India.

Sakataren harkokin tsaron Amurka Jim Mattis ya ce Amurka, da sabuwar dabarar da ta fito da ita ta warware kiki-kakan da aka yi da mayakan kungiyar Taliban, ba zai sa ta daina fada a Afghanistan ba.

‘Yan sa’o’i bayan isarsa kasar, wani harin roka da aka kai a tashar jiragen saman birnin Kabul ya raunata mutane 5.

Sakataren rundunar NATO Jens Stoltenberg, wanda shima ya je birnin na Kabul, ya jaddada kudurin NATO na taimakawa Afghanistan.

Shirin da shugaba Donald Trump ya fidda akan Afghanistan, cikin watan da ya gabata, ya nuna irirn gagarumar rawar da kasashen yanken zasu taka ciki harda India.

Shugaba Muhammad Buhari Yayi Ma Majalisar Zartaswarsa Bayanin Zuwansa Amurka


 Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayi amfani da taron mako-mako na majalisar zartaswar kasa wajen bayyanawa ministocinsa yadda tattaunawarsa da shugaba Donald Trump ta Amurka ta kasance, da kuma irin hidimomin da ya gudanar a Majalisar Dinkin Duniya.

Kakakin shugaban na Najeriya, Malam Garba Shehu, ya fadawa wakilin Muryar Amurka, Umar Faruq Musa, cewa shugaban ya yaba da alkawarin da shugaba Donald Trump ya yi masa cewa Amurka zata saidawa da Najeriya jiragen yakin sama na kai farmaki samfurin Super-Tucano, domin yakar ‘yan Boko Haram.

Kakakin yace, shugaba Buhari ya lura cewa a can baya, Amurka ta ki yarda ta saidawa da Najeriya wadannan jiragen.

Haka kuma, majalisar zartaswar ta bayyana damuwa a kan yawan kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa da Najeriya ta shiga ciki, wadanda kuma ba ta cin moriyar komai daga wasunsu. A dalilin haka, majalisar ta yanke shawarar cewa daga yanzu, sai kungiyoyin da shugaban kasa ya zaba da kansa kawai Najeriya zata nemi wakilci cikinsu.

Zakarun Turai: Chelsea ta kafa tarihi bayan doke Atletico 2-1


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Cin da Michy Batshuayi ya yi shi ne na biyu a gasar kofin zakarun Turai a kakar nan

Chelsea ta bi Atletico Madrid har gida ta doke ta da ci 2-1 a wasansu na kofin zakarun Turai na rukuni na uku (Group C), a ranar Laraba.

Minti 40 da fara wasa Antoine Griezmann ya ci Chelsea da fanareti, bayan da David Luiz ya rike Lucas Hernandez lokacin da aka yo wani bugun gefe.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 59 sai Morata, wanda Chelsea ta sayo daga Real Madrid ya rama mata kwallon, kafin kuma a dakika ta kusan karshen wasan Michy Batshuayi ya ci wa Blues din ta biyu.

Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Wasan farko na kofin zakarun Turai kenan da Alvaro Morata ya yi wa Chelsea

Nasarar da Batshuayi wanda ya shigo wasan daga baya, ya sa Chelsean ta samu ta zo ne bayan damar da Cesc Fabregas da Morata suka barar.

Yanzu Chelsea ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta bi Atletico gida ta doke ta, kuma hakan ya kasance rashin nasara na farko a gasar Turai da kungiyar ta Spaniya ta yi a sabon filin wasanta.

Sannan hakan ya kawo karshen wasa 11 da Atletico wadda ta je wasan karshe biyu a shekara hudu da ta wuce ta gasar, ta yi ba tare da an doke ta ba a gida a gasar kofin na zakarun Turai.

Wannan shi ne karo na biyu da Atletico ta sha kashi a karkashin kociyanta Diego Simeone a wasa 24 na kofin zakarun Turai a gida.

Nasarar ta sa Chelsea ci gaba da kasancewa ta daya a rukunin (Group C) da maki shida, biyu kenan tsakaninta da Roma, sannan kuma biyar tsakaninta da ta uku Atleticon.

Sakamakon sauran wasannin na zakarun Turai na Laraba;

FK Qaraba 1- 2 Rom

Paris SG3-0 Bayern Mun

Anderlech 0- 3 Celtic

Juventus2- 0 Olympiakos

Sporting 0- 1 Barcelona

Ina Bin Kwamitin Yakin Neman Zaben Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Bashin Miliyan 24 Na Fastocin Zabe, Inji Wani Mai Sana’Ar Dab’i


Wani Mai sanaar dab’i ya koka a kan rashin biyan shi cikon kudin shi na aikin da ya yi wa kungiyar neman zaben tsohon shugaban kasa, Gudluck Ebele Jonathan. Shugaban Kamfanin dab’in, mista Olusegun Idowu, ya ce tun asali abinda suka shirya zasu biya shi kudin aiki, Naira miliyan 54, sai suka fara bashi naira 30m akan idan ya gama za su cika masa naira 24m, cikon da ya ce har yanzyu ya makale tun bayan faduwar tsohon Shugaban kasa Gudluck Ebele Jonathan a zaben da ya gabata na Shekarar 2015.

Mai aikin dab’in ya bayyana haka ne a ranar laraba da ta gabata, yayin da ya bayyana gaban kotu a jihar legas tare da tsohon shugaban kwamitin yada labarai na tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Femi Fani-kayode akan tuhumar su da arbar wasu kudi har naira biliyan 4.9. 

Fani Kayode na fuskantar tuhumar badakalar kudi naira biliyan 4.6 tare da wasu darektocin kwamitin neman zaben da mistoci kamarsu Nenadi Usman. Sauran masu fuskantar tuhuma sun hada da wani Danjuma Yusuf da wani kamfani mai suna Joint Trust Dimension Limited.

Zakarun Turai: Mourinho ya ce suna gaba da kaiwa matakin gaba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu Lukaku ya ci wa Manchester United kwallo 10 a wasa tara

Jose Mourinho ya ce gab suke da kaiwa matakin sili-daya-kwale a gasar zakarun Turai bayan da Manchester United ta bi CSKA Moscow har gida ta casa ta da ci 4-0.

Kociyan ya ce duk da cewa wasa hudu ne yanzu a gabansu a rukunin, kasancewar sun fara da kyau, yana ganin kamar ma sun kai mataki na gaba na gasar.

A wasan na rukuni na daya (Group A), wanda aka yi ranar Laraba, Romelu Lukaku, ya ci biyu sannan Anthony Martial ya ci da fanareti, kafin Henrikh Mkhitaryan kuma ya ci ta hudu.

Mourinho ya ce abin da ke da muhimmanci shi ne a wasa biyu suna da maki shida, sannan kuma ga su da kyakkyawan matsayi a gasar, in ji kociyan wanda kungiyar tasa ta doke Basel 3-0 a wasansu na farko.

Da wannan sakamako, yanzu Lukaku ya ci kwallo 10 a wasa tara, tun lokacin da ya koma United daga Everton a lokacin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa da ta gabata.

Yanzu dai a tarihi ba a doke Man United ba a wasa shida a waje da wata kungiya ta Rasha.

‘Yan wasan kungiyar ta Premier sun sanya rigarsu ta uku ne mai launin fatsa-fatsa, launin da rabonsu da sanyawa tun lokacin wasansu na Premier a gidan Southampton a watan Afrilu na 1996.

A wancan lokacin Southampton ta ci su 3-0 a kashin farko na wasan, abin da ya sa ‘yan United din suka sauya rigar, saboda wai ba sa ganin junansu.

To amma a wannan wasan da CSKA ba su gamu da wannan matsala ba, inda suka kwashi garabasa a karawar ta gabashin Turai.

A daya wasan rukunin tsohon dan gaba na Norwich Ricky van Wolfswinkel ya ci da fanareti, a wasan da Basel ta casa Benfica 5-0.

Manchester United ce ta daya a rukunin da maki shida, sai Basel da maki uku, yayin da CSKA mai maki uku ita ma take zaman ta uku, amma da bashin kwallo biyu, Benfica tana ta karshe ba maki ko daya.

Daga 4 Ga Watan Oktoba Ba Sassauci Ga Wanda Bai Da Lasisin Tuki – Hukumar FRSCJami’an rundunar kiyaye hadurra ta kasar Najeriya watau Federal Road Safety Corps (FRSC) na shiyyar jihar Filato a takaice sun sanar da ranar 4 ga watan Oktoba matsayin ranar karshe ga marasa lasisin tuki a fadin jihar.

Hukumar ta bayyana cewa daga ranar dukkan wanda bai da lasisin to ya ma manta da hawan mota ko kuma anfani da titunan jihar don kuwa za su fara wani muhimmin samame.

Daga 4 ga watan Oktoba ba sassauci ga wanda bai da lasisin tuki – Hukumar FRSC

NAIJ.com ta samu dai cewa shugaban rundunar ta jihar Mista Andrew Bala shine ya bayyana hakan ga manema labarai na jihar inda yace yanzu haka ma dai shire shire sunyi nisa wajen fara sintinin nasu da suka sawa suna “Operation Show Your Driver’s Licence and Vehicle Particulars”.

A wani labarin kuma mai kama da wannan, wata alkaliya dake a kotun majistare ta garin Ado Ekiti ta bayar da umurnin kulle wani matashin mota direba mai shekaru 35 mai suna Ahmed Kolo a gidan yari bisa zargin da ake yi masa na so ya kashe Gwamnan jihar Ayodele Fayose.

Yanzu-Yanzu! Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sako Uwargidan Hadimin Gwamna Masari Da Suka SaceBabban mai taimakawa gwamnan a kan kafafen sadarwar zamani Alh Abdulhadi Ahmad Bawa shi ne ya wallafa kubutar matar a shafinsa, sai dai bai bayyana yadda matar ta kubuta ba, wajen sai da aka bayar da kudin fansa ko a’a.

NAIJ.com ta samu dai cewa ga yadda ya rubuto a shafinsa na Facebook:

Yanzu-Yanzu! Masu garkuwa da mutane sun sako uwargidan hadimin gwamna Masari da suka sace

“ALHAMDU LILLAH

ALLAH CIKIN IKON SHI DA BUWAYAR SHI YA KUBUTAR DA HAJIA BINTA BUGAJE (MATAR DR LAWAL BAGIWA) DAGA HANNUN WADANDA SUKAI GARKUWA DA ITA.

A jiya ne dai muka kawo maku rahoton cewa masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da uwargidan mai baiwan gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina shawara akan harkokin da suka shafi gwamnatocin jiha da jiha Dr. Lawal Bagiwa.