Hajjin Bana: An Sake Samun Rasuwar Maniyyatan Najeriya A Kasar SaudiyyaHukumar NAHCON ta sake sakin bayanai kan karin rasuwar karin mutum biyu a kasar Saudiyya a lokacin fitar Muna a kasa mai tsarki, hanan ya kai yawan na masu rasuwar zuwa mutum bakwai kawo yanzu, daga mutum dubu tamanin da biyu daga Najeriya.

Hajjin bana: An sake samun rasuwar maniyyatan Najeriya a kasar Saudiyya

Shugaban hukumar ta NAHCON Abdullahi Muhammed ne ya fadi ma manema labarai a yau dinnan alhamis a filin arfah. Ya kuma ce dukkan rasuwar babu hadari a cikinta, mutuwar Allah da annabi ce.

Malam Muhammed dai yace bazai fadi sunayen wadanda suka mutun ba, sai an sanar wa iyalansu a hukumance, amma yace sun fito daga jihohin Kwara, Katsina da Kogi sai Kaduna. Ya kara da cewa, wannan shekarar, an yi sa’ar rage rasuwa ta mahajjata saboda sabbin tsare-tsare da ma kuma ma’aikatan kiwon laiya da aka je dasu.

A baya dai a irin wannan rana ana samun turereniya da yamutsi da kan kashe jama’a, hadari da bincike kance wai ‘yan Najeriya ko bakake ke haddasawa, saboda su fito daga kasashe marasa tsari ko wayewa.

An Doke Bill A Gasar Wanda Yafi Kowa Arziki A DuniyaA sabon rahoton da jaridar Forbes ta fitar ranar Laraba, mai kamfanin Zara, Amancio Ortega ya doke attajirin duniya Bill Gates wurin zama mutumin da yafi kowa arziki a duniya yanzu.

A yanzu Ortega ya ‘dara Bill Gates kudi da dallan Amurka miliyan 200 a dalilin tashin gwauron zabi da hannun jarin wata kamfanin mai suna Inditex tayi a makon da ya wuce, Inditex ne ta raini kamfanin Zara mallakan Ortega.

Wani mutum ya doke Bill Gate a matsayin wanda yafi kowa arziki a duniya

Jaridar Forbes tace Mista Ortega ya zama mutumin da yafi kowa kudi a duniya sau uku a baya amma ana doke shi a cikin kwana daya.

Duk da razikin Mr Ortega, mutane da yawa basu san shi ba.

An dai ce shi mutum ne shiru-shiru kuma bai cika shiga cikin mutane ba, a duk tsawon rayursa hirar da yayi da yan jaridar tsiraru ne.

Mista Ortega ya fara sana’ar sa ne a shekarar 1975 a yayinda suka fara kamfanin kayan sawa tare da matan sa a wannan lokacin mai suna Rosalia.

Sauran rassan kamfanonin sa sun hada da Mussimo Dutti da Pull & Bear wanda ke da rassa guda 7,385 a fadin duniya.

Za’a Dawo Wa Da Shugaba Buhari Diezani Gida Najeriya, Saboda Ta Fuskanci TuhumaA hirarsa da sashen Hausa na BBC, shugaban hukumar EFCC, ya ce kwanan nan kasar Ingila zata taso keyar Diezani Allison Maduekwe zuwa gida Najeriya, domin ta sami fuskantar alkali, ta kuma yi zaman kaso muddin aka same ta da laifi, hakan na zuwa ne bayan da yawa daga cikin kadarorinta sun dawo hannun gwamnati, wasu kuma an kwace a Igilar da Amurka.

Za’a dawo wa da shugaba Buhari Diezani gida Najeriya, saboda ta fuskanci tuhuma

Ana faduwa zabe a PDP a shekarar 2015 ne dai aka gano Diezani na kai gaisuwa gidan Abdussalami Abubakar mai ritaya, kuma ance kudade da yawa ta mayar wa gwamnati cikin daloli a buhunhuna.

An kara ganin hotonta a karon farko tana kai gaisuwa ga zababben shugaba na lokacin a jirgin British Airways watakil domin kamun kafa. Domin kafin nan dai Diezani shatar jirgi guda take yi domin tafi karin jirgin talakawa.

Ta kuma ki dawowa daga Ingila, tayi kwal-kwal a kanta, domin wai a cewarta, tana fama da cutar Kansa, saboda haka a tausaya mata, tayi gudun hijira a can Ingilar. Yanzu dai hakan ya kare.

Ibrahim Magu ya tabbatar wa da BBC cewa kwanan nan za’a sami damar taso keyarta gida domin ta amsa ko kare kanta daga manayn zarge-zarge daga gwamnati.

Biliyoyi ne dai cikin daloli aka kama a gidanta, a Amurka, a Ingila, da kuma a Legas da Abuja, an kuma kwace dukkaninsu an hana ta.

Idan da lokacin mulkin soja ne dai, da a jaka za’a dawo da Diezani, kamar yadda Janar Buhari yaso yiwa marigayi Ummaru Dikko a baya.

Yadda fasto ya kare Musulmi 2000 a cocinsa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar hari daga kungiyar gwagwarmayar Kristoci ta anti-Balaka.

Fasto Juan José Aguirre Munoz ya ce Musulmin ‘yan gudun hijiran ba za su bar harabar cocinsa ba a birnin Bangassou da ke kudu-maso-gabashin kasar, sai bayan ya samu tabbaci kan tsaron rayukansu.

Ya ce Musulmin da ya ba mafaka suna “fuskantar barazanar kisa” ne daga wurin mambobin kungiyar anti-Balaka.

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya Stephen O’Brien ya yi gargadin cewa akwai alamun aikata kisan kare dangi a makon jiya.

Ya ce rikicin kasar yana kara ta’azzara kuma al’amarin yana kara muni.

“Tashin hankalin yana karuwa, ana tsoron kada a kara maimaita mummunan rikicin da ya faru a kasar kimanin shekara hudu da suka wuce,” in ji shi.

Mista O’Brien ya kara da cewa: “Akwai alamomin da ke nuna yiwuwar faruwar kisan kiyashi don haka wajibi ne a dauki mataki.”

Hukumar Harkokin ‘Yan Sanda Ta Gayyaci Sanata Isah Misau Ya Bayyana A GabantaHukumar harkokin ‘yan sanda ta gayyaci shugaban kwamitin majalisar dattijai na sojojin ruwa cewa sanata Isah Misau ya bayyana a gaban kwamitin ta na musamman.

Ana sa ran dan majalisar zai bayyana a gaban kwamitin a ranar 6 ga Satumba, 2017 a karfe 11.00 na safe tare da asalin takardun wasiƙarta na ritaya don t abbatarwa.

Hukumar ta lura cewa ta samu takardu daga ofishin ‘yan sanda na bincike (SIP) a ranar 28 ga watan Agustan shekarar 2017, wanda ta shafi maganar ritaya na wasu ‘yan majalisar dattijan na Najeriya.

Sufeto Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris

Bisa ga wasikar, ” Hukumar harkokin ‘yan sanda wanda ita kadai ta ke da alhakin ba da takadar ritaya ga dukkan ‘yan sanda sai dai IGP tana da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen tantance gaskiyar wannan wasikar”.

Mene ne hukuncin daukar hoto a wuraren Ibadah?


Hakkin mallakar hoto
AHMAD GHARABLI

Image caption

Mahajjata sukan dauki hotuna a lokacin ibada musamman a kasar Saudiyya

Daukar hoton a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su gani su kuma yi tsokaci ko magana ko kuma yayata hoton.

Ba sabon abu ba ne mutun ya dauki hoto a masallacin idi ko na harami a Makka ko Madina ko kuma a filin Arfa.

Bugu da kari wasu na daukar hotuna na bidiyo a lokacin dawafi ko kuma lokacin hawa Arfa kuma su wallafa a shafukan sada zumunta na zamani.

Wata kila wasu na yin hakan ne domin su nuna wa duniya cewa sun samu zuwa wannan waje, yayin da wasu kuma suna son su nuna wa wadanda suke gida yadda wurin ibadar yake ne.

To amma wani lokacin hakan ba ya rasa nasaba da aikin riya da Musulunci ya hana.

Hakkin mallakar hoto
AHMAD GHARABLI

Image caption

Daukar hoto domin wallafawa a shafukan sada zumunta batu ne da mutane suka saba da shi a shafukan sada zumunta

Irin wannan dabi’ar ta samo asali ne tun zamanin da, inda mahajjata ke dawowa gida da kallo-kallo daga aikin hajji inda yara da sauran mutane da ba su samu zuwa aikin hajji ba za su samu ganin wuraren aikin hajji ta hotunan da ke cikin kallo-kallon.

Riya ce?

Wasu na tunanin cewar daukar hoto a irin wadannan wuraren ibadan son a-sani ne, wato riya ce. Amman mene ne hukuncin irin wannan dabi’ar a Musulunci?

Ustaz Hussaini Zakariya, ya ce, “Maganar daukar hoto idan aka je Harami ko Madina, malamai sun rabu gida biyu kan wannan batu.”

“Daya mai tsanani kwarai da gaske, shi yana ganin cewa hoton ma haramun ne a ko ina aka yi, ba sai lallai cikin Harami ba, kuma yi a cikin Haramin ma ya fi muni.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mahajjata sukan dauki hotuna a lokacin ibada a kasar Saudiyya

“Amma akwai wadanda suke ganin cewa daukar hoto ba aikin ibada ba ne. Ba wanda zai dauki hoto ya ce ya yi sunnah ko mustahabi ko kuma ya yi farilla.”

Malamin ya kara da cewa: “Don haka ba aikin ibada ba ne balle a ce in ka yi jama’a sun gani, aikinka ya baci. Don haka yana ganin cewa halal ne matukar dai mutum ba wai ya yi wannan abin don jama’a su ga cewa yana wajen wata ibada kuma burinsa ya cika ba ne.”

“Ya kwadaita wa wadanda Allah bai ba su ma su roki Allah Ya kai su wannan wurin, kuma ya sanar da danginsa da abokansa cewa ga shi Allah Ya kawo shi wurin da duk Musulmi yake son ya zo.”

“Ina ganin wani abu ne na raba abin farin cikin da ya samu mutum da ‘yan uwansa da abokansa.”

Saboda haka Ustaz Zakariya ya ce yana ganin wannan ba aikin addini ba ne kuma ba riya ba ce.

Ga yadda amsar Malam Haussaini Zakariya ta kasance:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Mene ne hukuncin daukar hoto a masallatai tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta?

Shi kuma Dokta Abdulkadir Sulaiman na Sashen koyar da addinin Musulunci a jami’ar Abuja cewa ya yi daukar hoto kansa ba ya halarta.

Amma batun ko daukar hoto tare da wallafashi a shafukan sada zumunta zai iya janyo riya, ya ce wannan wani lamari ne mai sarkakiya.

Malamin ya yi bayanai tare da kawo hadisai da ke nuna cewa yanke hukuncin riya ba hurumin dan Adam ba ne domin wannan al’amari ne da ke zuciyar dan Adam, kuma Allah (SWT) ne kawai zai iya sanin abin da yake zuciyar bawansa.

Ga yadda amsar Dokta Abdulakadir Sulaiman ta kasance kan mas’alar:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Akwai riya a daukar hoto a masalatai tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta?

Hakkin mallakar hoto
MOHAMMED AL-SHAIKH

Image caption

Ana daukar hoton dauki-kanka har ma a filin Arfa

Takaddamar cinikin ranar karshe da aka yi a Premier


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Torres ne dan kwallon da aka saya mafi tsada a duniya a 2011

A ranar Alhamis 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa ta Turai ta bana, wacce za a sake budewa a watan Janairun 2018.

Ana bude kasuwar ce domin bai wa kungiyoyin Turai damar daura damarar tunkarar kalubalen tamaula a sabuwar kaka.

Ga jerin cinikin ranar rufe kasuwar da aka yi takaddama a Premier:

Benjani

Dan wasan tawagar Zimbabwe, Benjani ya makara zuwa Etihad domin ya saka hannu kan yarjejeniyar komawa Manchester City, bayan da bacci ya kwashe shi a filin saukar jirgin sama na Southampton a Janairun 2008.

Makarar da dan wasan ya yi ya kusan sa a soke yarjejeniyar da aka kulla tun farko, daga baya aka warware matsalar bayan da aka kammala sa hannu a dukkan takardun da suka dace a kan kari.

Benjani ya fara buga wasa a City da kafar dama inda ya ci Manchester United a wasan hamayya da suka kara.

Daga baya dan kwallon ya kasa yin komai, hakan ya sa ya bar Etihad a shekarar 2010 bayan da ci kwallo biyar.

Yossi Benayoun da Mikel Arteta

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bayan da Arsenal ta sayar da Cesc Fabregas da kuma Samir Nasri ta samu kudi fam miliyan 60 a shekarar 2011, daga nan ne Arsene Wenger ya dunga jan lokaci kafin ya sayo wadanda za su maye gurbinsu.

Sai a ranar da za a rufe kasuwa ne Wenger ya sayo Benayoun da kuma Arteta, ya kuma sayo Arteka kan fam miliyan 10, inda ya yi shekara biyar a Gunners, shi kuwa Benayoun Chelsea ya koma wasa aro daga baya ba ta sayi dan kwallon ba.

Peter Odemwingie

Dan wasan Najeriya, Peter Odemwingie ya dauki hukunci a hannunsa a wani abu kamar almara da bai taba faruwa ba a Ingila, inda ya so komawa QPR daga West Brom da karfin tsiya a Janairun 2013.

Odemwingie ya tuka motarsa zuwa QPR daga West Brom, amma aka ce ya koma inda ya fito, saboda kungiyoyin biyu ba su kulla yarjejeniya ba, kuma tun da ya koma West Brom ba ta kara saka shi a wasa ba.

Rafael van der Vaart

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kocin Tottenham, Harry Redknapp ya matsu ya dauki Rafael van der Vaart daga Real Madrid a shekarar 2010.

Sai dai rashin kammala sa hannu kan yarjejeniya ya kusan hana dan kwallon komawa Ingila da murza-leda, amma daga baya mahukuntan Premier suka amince da cinikin bayan da aka rufe kasuwa.

Van der Vaart ya yi kaka biyu a White Hart Lane, inda ya ci kwallo 23.

Fernando Torres da Andy Carroll

Bayan da Liverpool ta amince ta sayar wa da Chelsea Fernando Torres kan fam miliyan 50 a ranar 31 ga watan Agustan 2011, Liverpool kuma a lokacin ta sayi Andy Carroll kan fam miliyan 35 daga Newcastle United.

An yi ta mamakin dalilin da ya sa Liverpool ta sayi Carroll kan kudi mai yawa haka, daga baya ‘yan wasan biyu suka kasa taka rawar gani a kungiyoyin da suka koma.

A kuma shekarar ce Luis Suarez ya ci kwallo 69 a yarjejeniyar shekara uku da rabi a Anfield, amma ta sayar da shi ga Barcelona a kudi mai tsoka.

David De Gea

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea ya kusan komawa Real Madrid a ranar da za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a 2015.

Tuni United da Madrid suka amince da kudin da ya kusan kai fam miliyan 30, sai dai kungiyoyin biyu sun kasa cike takaddun ka’ida da ya kamata dan kwallon ya koma Spaniya da taka-leda, hakan ya sa suka hakura da cinikin De Gea.

Andrey Arshavin

A lokacin da za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan Turai a karshen Janairun 2009 ne Arsenal ta sayi Andrey Arshavin daga Zenit St Petersburg kan kudi mai tsada da ya kai fam miliyan 15.

An samu tsaiko wajen cimma yarjejeniyar kudin dan wasan, inda sai washe gari ne Arsenal ta fadi kudin da ta dauki dan kwallon.

Mahukuntan Premier sai da suka yi bincike ko Arsenal ta karya ka’idar sayen dan wasan, daga baya aka wanke ta.

Bamuda Iko Mu Kama Mutanen Da Suke Yin Maganganun Kiyayya A Kan Yanar Gizo – Rundunar SojiDaraktan labarai na rundunar soji, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana cewa sojoji ba su shirin kama kowa game da maganganun kiyayya a kan yanar gizo saboda ba su da iko su yi irin wannan kamu.

Manjo Janar ya bayyana hakan a yayin ganawar da ya yi da tashar gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

Enenche ya ce sojoji za su lura da ayyukan yanar gizo ne kawai, amma ba ta da ikon kama duk wanda ya sa kalaman ƙiyayya a kan yanar gizo.

Daraktan labarai na rundunar soji, Manjo Janar John Enenche

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Enenche ya kasance bako a kan wannan tashar a ranar 23 ga watan Agustan inda ya bayyana cewa sojoji suna sa ido kan kafofin yada labarai don masu wallafa maganganun kiyayya don adawa da gwamnati da jami’an tsaro. Yawancin ‘yan Najeriya suna zaton wannan ma’anar cewa soja za su fara kama duk wanda ya sanya irin waɗannan maganganu a kan yanar gizo.

‘Yan Najeriya sun damu matuka a lokacin da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yayin da yake mukaddashin shugaban kasa ya sanar da cewa za a dauki maganganun ƙiyayya a matsayin ta’addanci a kasar.

EFCC Na Shirin Taso Keyar Diezani Allison-MaduekeShugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arzikin zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za su sa gwamnatin kasar Birtaniya ta tiso keyar tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madueke.

Ibrahim Magu ya shaida wa jaridar BBC cewa “Muna nan muna kokarin ganin an taso keyarta domin ta zo nan”.

Magu ya kara da cewa a wannan shekarar kadai, hukumar EFCC ta yi nasarar kwato kudi kimanin naira biliyan 409 da kuma dala miliyan 69 daga hannun mutane daban-daban da ake zargi da yin sama da fadi a kan kudaden gwamnatin a wannan shekarar.

EFCC na shirin taso keyar Diezani Allison-Madueke

A cewarsa, an gurfanar da mutanen a gaban kuliya, yana mai cewa EFCC ta samu nasara kan kararraki 137 a shekarar 2017.

Mista Magu Magu ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da ministan shari’ar Abubakar Malami, yana mai cewa “wannan labarin sharrin ‘yan jarida ne kawai. Amma buri daya muke son cimmawa”.

Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu alhazan Najeriya bakwai sun mutu a Saudiyya gabanin a fara aikin Hajji.Alhazan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna.

Sannan wata Hajiya daga Jihar Kogi ta Haihu a Madina. Shugaban NAHCON Abdullahi Mukhtar, ya ce za a hukunta jihar da matar ta fito ta hanyar rage mata kujeru a badi, da kuma hukunta shugabannin hukumar aikin hajji ta jihar

Alhazan Nigeria Kusan dabu 90 ne ke halartar aikin hajjin bana.

Tottenham ta sayi Serge Aurier daga PSG


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tottenham ta kammala sayen dan wasan baya na Paris St-Germain Serge Aurier kan fam miliyan 23.

Dan kwallon na Ivory Coast, mai shekara 24, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar har zuwa 2022.

Batun samun izinin aiki ne ya kawo tsaiko a cinikin saboda hukuncin daurin je-ka-ka-gyra-halinka da aka yanke masa saboda cin zarafin dan sanda a bara.

“Wannan kamar wata sabuwar rayuwa ce a gare ni. A shirye nake na nuna kwarewa a ciki da wajen filin kwallo,” a cewar Aurier.

“Magoya baya sun ne mafiya muhimmanci a kowanne kulob kuma a shirye nake na nuna musu cikakken Serge Aurier.”

Aurier shi ne na hudu da Spurs ta saya a bana, bayan mai tsaron gida Paulo Gazzaniga da Juan Foyth da Davinson Sanchez.

JAMB: An Bayyana Jami’Ar Da Tafi Kowace Dibar Jama’a A Shekarar NanWata mujalla mai suna Economic Intelligence ta ce babu Jami’ar da ta fi ta Ilorin farin jini a Najeriya a bana.

Mujallar tace rahotanni daga Hukumar Jarrabawar shiga Jamia’a ta JAMB sun nuna cewa babu Jami’ar da aka yi rububin ta a bana irin Jami’ar Ilorin inda sama da mutane 104,000 su ke neman shiga Makarantar.

Daga Jamia’ar ta Ilorin kuma sai Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a Jihar Kaduna wanda Dalibai har sama da 89,000 ne ke neman samun shiga zuwa Jami’ar. Sai dai duk ta kare yawanci Jami’o’in bai fi su dauki Dalibai 10,000 ba a shekara.

Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar zuwa Jami’a a Najeriya tace a shekarar bana da maki akalla 120 cikin 400 sai mutum ya samu shiga Jami’a a Najeriya.

Boko Haram: Birtaniya ta rage agajin da take bai wa Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Priti Patel ita ce mai kula da tallafin da Birtaniya ke bai wa kasashen waje

Birtaniya za ta rage yawan kuɗaden da take bai wa Najeriya a matsayin agaji domin ayyukan jin kai nan da ‘yan shekaru masu zuwa.

A shekarar 2016 Birtaniya ta kashe fam miliyan 100 wurin tallafawa ayyukan jin kai a Najeriya.

Amma a cikin shekara hudu masu zuwa ta yi alkawarin fam miliyan 200 kadai. Fam miliyan 50 ke nan a kowace shekara.

Ana san ran za a yi amfani da kuɗaden wurin tallafawa wadanda hare-haren Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin kasar.

A wata ziyarar kwanaki biyu da Sakataren Harkokin ci gaban kasashen waje ta kasar, Priti Patel ta kai Najeriya, ta nemi hukumomin kasar su kara daukar matakai na yakar masu tsattsauran ra’ayi.

Ta kara da cewa kamata ya yi wasu ƙasashe waje su taimaka wajen ba da tallafi.

Hare-haren kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar raba mutum miliyan 1.5 daga muhallansu.

Hakan kuma ya shafi harkar noma a kasar wanda ke haifar da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Gwamnatin Kasar Amurka Ta Debi Dalibai 18 Daga Kihohin Arewa Don Yin Karatu Kyauta S KasarDaliban an kwashesu ne daga jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi da Bauchi, dake tsakanin shekaru 15 da 17, inda zasu yi aji 5 a makarantun kasar Amurka, sai su dawo Najeriya su kammala karatunsu.

An kirkiri shirin ne a watan Oktoban 2003 a matsayin hanyar kare sake aukuwar harin da aka kai ma Amurka na 11 ga watan satumba 2001, kuma cibiyar ilimi da raya al’adun gargajiya ne suke daukan nauyin hakan.

Yawancin daliban da ake diba Musulma ne, kuma ana dauko su ne don su fahimci al’adun kasar Amurka da manufofin kasar, tare da koyar dasu makaman shugabanci, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito sama da dalibai 300 sun amfana da shirin tun lokacin da aka fara shirin a shekarar 2003.

Yau Take Tanar Arfa: An Canza Wa Ka’Sbah RigaA kowanne ranar 9 ga watan Zuhijja na shekarar Musulunci ne ake canza ma dakin Allah, Ka’abah riga, wannan bakin yadin dake dauke da rubuce rubuce a jikinsa.

NAIJ.com ta ruwaito a an sauya ma Ka’abah riga ne a yau 31 ga watan Agusta bayan sallar Asubah, wanda yayi daidai da ranar Arfa, inda yadin rigar falle uku ne, kuma an yi masa kwalliya da gwal mai nauyin kilo 150.

An canza ma Ka’abah riga

Ana sa ran kimanin musulmai miliyan 2 ne yau zasu tsayu a filin Arfa, inda za’a fara tsayuwar ne da zarar an kammala sallar Asubahi, sa’anann za’a gabatar da huduba daga Masallacin E-Nimra.

Gwamnatin Birtaniya Ta Bayyana Kudirin Taimakawa Da Yuro Miliyan 200 Domin Tallafawa Mutanen Da Yakin Boko Haram Ya Saka Cikin Halin Ni ‘Ya Su
Sakataren harkokin waje na birtaniya, Boris Johnson, da takawarar sa, sakatariyar raya kasashe, Priti Patel, cikin wani jadawali na shekara 5, sun bayyana kudurin kashe kudin yuro miliyan 200 domin taimakawa gwamnati a yunkurin ta na murkushe mayakan kungiyar boko haram da tallafawa wadan da yakin boko haram ya saka cikin matsanancin halin rayuwa.

Sun bayyana hakan ne a wata ziyarar hadin gwiwa da suka kai babban birnin jihar Borno, Maiduguri, in da suka gane wa idanuwan su irin barnar da mayakan da suka yi ga mutane da dukiyoyi.

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana kudirin taimakawa da yuro miliyan 200 domin tallafawa mutanen da yakin boko haram ya saka cikin halin ni ‘ya su

Mayakan boko haram dai sun kashe sama da mutum dubu 20 a jihar Borno kawai. Sannan sun raba wasu mutum kimanin milyan 1.7 da matsugunnin su tare da saka wasu mutanen sama da miliyan 8.5 a matsanancin halin kuncin rayuwa a yankin arewacin Nigeria, musamman yankin arewa maso gabas.

Kungiyar Boko haram dai na fafutukar kafa shari’ar musulunci a kasashen gefen tekun chadi da ya hada da yankunan Najeriya, Nijar, Kameru, da Chadi.

Maniyyata Kusan Miliyan 2 Sun Dukafa A Kasar SaudiyyaKusan Maniyyata Miliyan 2 ne ke Kasar Saudi Arabia a yanzu domin sauke farali a wannan shekarar.

Kimanin Maniyyata Miliyan 1.7 ne ke Kasar Saudi Arabia a yanzu domin aikin Hajjin bana. A yau ne Ranar Arafah da bayin Allah ke dukufa wajen neman gafarar Allah da kuma addua ga Ubangiji daga ko ina na sashen Duniya.

A Musulunci dai Hajji na cikin rukunin Addinin. A shekarun baya dai an samu matsala wajen aikin hajjin inda jama’a da dama su ka rasa ran su musamman mutanen Kasar Iran. A bara ‘Yan kasar Idan ba su je aikin hajjin ba amma wannan shekarar su na cikin Mahajjatan bana.

Kudin kujerar aikin Hajjin bana dai ya haura Miliyan daya da rabi. Majalisar Dattawa sun nemi Hukumar kula da aikin Hajji na kasa watau NAHCON ta rage kudin kujerar aikin Hajji na wannan shekarar amma ba ayi hakan ba.

‘Yan Kasar Angola Sun Bukaci Dai Daito Tsakanin Attajirai Da TalakawaWASHINGTON D.C — Mutanen kasar Angola sun gudanar da zaben sabon shugaban kasarsu na farko cikin kusan shekaru 40, kuma a yanzu sun ce dole ya kawo dai daiton tazarar dake tsakanin attajirai da talakawa.

Duka da kasancewar kasar a matsayin ta biyu dake da arzikin mai a nahiyar Afirka, Angola na ci gaba da kasancewa daga cikin kasashen da al’ummar ta ke ci gaba da zama a wahalce, kuma wadda ke dogaro akan kayan da ake shigowa da su kasar daga kasashen ketare.

Yawncin ‘yan kasar na zama cikin talauci da rashin ayyukan yi da kuma hauhawar farashin kayan masarufi.

Sabon shugaban kasar da aka zaba, Joao Laurenco, yace yana so ya rage yawan dogaro da kasar ke yi a kan arzikin man fetur.

Ya kuma yi alkawarin zai inganta harkokin noma da masana’antu da harkokin yawon bude ido, da kiwon kifi da sauran harkokin tattalin arziki.

Jam’iyyar adawa ta zargi jagabannin gwamnatinn dake mulki da cewa suna batar da dukiyar kasar ne wajen dadadawa kawunansu ne kawai.

Daya daga cikin shugabannin adawar, Manuel Fernandes, ya bayyana cewa wannan akubar talauci ba sanadiyyar faduwar farashin man fetur bane, rashin adalcin gwamnati ne ya haifar da shi.

Kalaman Shugaba Trump Akan ‘Yan Jarida Na Iya Jefasu Cikin Bala’i – Inji Zeid Ra’ad HusseinBabban Jami’in Majalissar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad Hussein ya ce idan bisa kaddara, aka yi wa ‘yanjarida lahani, shugaba Trump ne zai dauki alhakin wannan al’amarin saboda yadda yake caccakar su.

Babban jami’in kare hakkokin bil’adama na Majalissar Dinkin Duniya mafi babban mukami, ya gargadi shugaban Amurka Donald Trump akan cewa caccakar da yake yiwa ‘yan jarida na iya sa wasu su nemi kaiwa ‘yan jaridar farmaki.

Trump ya sha sukar manyan kafafen yada labarai kamar su New York Times, da Washington Post, da CNN, ciki harda wanda yayi a farkon watan nan, a lokacin da ya caccaki kafafen yada labaran akan yadda suka bada rahoton mummunan gangamin da wasu turawa farar fata masu ra’ayin kyamar sauran jinsunan jama’a suka shirya a garin Charlottesville dake jihar Virginia, inda Trump ya kira ‘yan jaradar da lakabin “mugayen mutane marasa gaskiya”.

Akan haka ne, shugaban Hukumar kare hakkokin bil’adama na Majalissar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad Hussein ya fada yau Laraba a Geneva cewa, “kiran kafafen yada labarai da lakabin “masu bada labaran jabu” da shugaba Trump ke yi, yana matukar muzantasu.

Nigeria: Ethiopian Airlines na son karfe iko da Arik Air


Hakkin mallakar hoto
AFP

Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines na tattaunawa domin duba yiwuwar karbe ragamar gudanar da kamfanin Arik Air na Najeriya wanda ke fama da matsaloli.

Gwamnatin Nigeria ta karbe ragamar gudanar da kamfanin a farkon bana bayan da ya sanar da yin gagarumar asara.

Wani babban jami’i a kamfanin Esayas Woldemariam, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa tattaunawar ta biyo bayan bukatar hakan ne da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta Najeriya ta yi masa.

“Hakika muna so kuma a shirye mu ke mu karbi ragamar gudanar da Arik Air,” a cewarsa.

Ethiopian Airlines shi ne kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi samun riba a nahiyar Afrika, a cewar jaridar Business Daily.

Ambaliya: Gwamna Ortom Yayi Kira Na Musamman Ga Shugaba BuhariKwanan nan mu ka ji cewa Gwannan Jihar Benuwe Samuel Ortom ya mika roko wajen Shugaban kasa Buhari.

Yanzu haka ambaliya ta addabi Jihar musamman a Babban Birnin na Makurdi. Gwamnan ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki kudin maganin ambaliyar gudun abin da ya faru a shekarar 2012 ya kara aukuwa inda aka gama da haza. 


Shugaban kasa da manyan Jihar Benuwe

Gwamnan yayi kira ga Jama’ar da ke kusa da abin yake shafa da su sauya mazauni. Gwamna Ortom ya kira Shugaban kasar ya aika masa kudin gaggawa kafin abin ya ta’azzara. A halin yanzu dai ana fama da matsi wajen biyan albashin ma’aikata a Jihar.

A can kwanakin baya wani Limamin Cocin Grace and Light Pentecostal da ke Garin Makurdi a Jihar ta Benue yace Gwamnan Jihar Samuel Ortom ba zai cigaba da zama a kujerar sa ba bayan shekarar 2019 don kuwa shi ya leka ya gano.

Sarakunan Gargajiya A Jihar Katsina Sun Yi Lale Maraba Da Buhari A DauraA safiyar ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin tarayya Abuja zuwa garinsa Daura domin yin hutun sallah, bayan da shugaban ya sauka, shugabanin da dama wadanda ke jiran izowar shugaba Buhari a Daura sun hada gwamnan jihar Katsina da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da manyan ‘yan siyasa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban kasa Muhamadu Buhari ya sadu da sarkin Daura mai martaba Alhaji Umar Faruk Umar tare da tawagarsa yayin da ya isa Daura a jihar Katsina a gaban bikin Eid El Kabir da za a yi a ranar 30 ga watan Agusta, 2017.

Daga bisani shugaba Buhari ya kuma gaisa da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da kuma kwamandan sojoji na GOC 1 Division Nigerian Army, Manjo Janar Adeniyi Oyebade a lokacin da ya isa Katsina.


Shugaban kasa Muhamadu Buhari da sarkin Daura mai martaba Alhaji Umar Faruk Umar

Shugaba Buhari da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman


Shugabana Buhari da Manjo Janar Adeniyi Oyebade

Gwamnatin Saudiyya Ta Hana Mahajjata Da Dama Shiga Kasar Saboda Rashin TakarduWannan sanarwan ya fito ne daga bakin ministan harkokin cikin gida na kasar a lokacin da yake yin jawabi ga manema labarai akan irin shirye-shiryen da kasar takeyi domin karaban mahajjata sama da miliyan 2 wanda zasu zo kasar domin sauke faralin su.

Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta hana mahajjata sama da N400,000 shiga kasar domin basu da ingantatun takardu.

Jami’an kasar sun dauki tsauraran matakai wanda suka hada da aikewa da mutum gidan kurkuku da kuma yankawa mutum tara domin dai a tabbatar da gudanar da aikin hajjin cikin yanayi mai kyau.

A Ranar Talata, ma’aikatan harkokin cikin gidan har ila yau ta sanar da cewa a kala mahajjata miliyan 1.7 daga kasashen waje sun isa kasar kana guda 200,000 yan kasar Saudi Arabia sun iso garin Makka domin shirye-shiryen fara aikin hajjin.

An tanadar da jami’an tsaro sama da 100,000 da su samar da tsaro ga mahajjatan a aikin hajjin wannan shekarar ta 2017.

Jami’in hulda da jama’a na ma’ikatan harkokin cikin gida, Mansour Turki, yace jami’an tsaro sun gano wuraren aijye mutane ba kan ka’ida ba a shekarun da suka wuce.

Turki ya cigaba da cewa jami’an tsaron zasuyi iya kokarin su wurin kiyaye irin cinkinson da ya haifar da rasa rayuka a hajjin shekara ta 2015. Ya kuma yi kira da mahajjata su bi dokokin da hukumar aikin hajjin ta shimfida.

Yadda yawan ciwon kai ke jawo mantuwa da rudin kwakwalwa


Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Lamarin ya auku ne ga Paul lokacin hutun zafi

Shekara biyu da ta wuce, Paul Bolding mai shekara 63 ya yi hutu a Croatia, inda ya ziyarci gabar kogi a wani karamin tsibiri tare da matarsa Kirsty.

Sai suka yanke wa kansu yin ninkaya da bututun shakar iska, inda suka rika yin juyi, wannan ya shiga wannan ya fita ya kula musu da kayansu.

Paul ya yi kurme sai barci ya kwashe shi a kan tabarmar gabar teku da ke shimfide kan kananan duwatsu na wani lokaci. Da farkawarsa bai san inda yake ba, ko ya aka yi ya iso wurin.

Babu mamakin jin cewa Paul ya firgita. Matarsa ta kai shi inuwa, inda ta zaku da ganin cewa ta kwantar masa da hankali ya samu natsuwa don warware matsalar da ke tattare da shi.

Ta bayyana mini a wani shirin rediyo mai taken daukacin al’amuran tunani (All in the Mind) cewa, ta gano cewa bai zai iya tuna komai ba, domin tambayoyi iri guda yake ta yi.: Kina jin zafi ne ya baibaye ni? Kina jin cewa na yi barci a rana ne?” Al’amarin da ya yi ta faruwa kenan fiye da sau 20.

Ya kasa tuna al’amuran da suka faru kwana 10 da suka yi na hutunsu.

Kirsty na ta kai-kawo a tunani cike da dar-dar jin cewa ko ya kamu da cutar mantuwa. Taraddadin cewa ko za ta shafe tsawon rayuwa tana kula da shi, sai ta dawo da shi garin da suke zaune, cike da fatan ganin al’amuran da ya saba da su ko za su dawo masa da tunaninsa.

Ita ta rika karbo masa abincin rana domin bai ma san abin da yake so ba. Ya kasa tunani kwana 10 da suka gabata na hutunsu, duk da cewa wasu al’amuran sun shaf ganawa da wasu ‘yan uwa a karo na farko.

Can tsakar rana sai ya fara warwarewa, al’amarin da ke nuni da cewa ya shirya yin tattakin da suka tattauna yinsa kafin wannan rana, wato dai ya fara tuna al’amura. Cikin sa’a guda ya dawo garas yadda yake – komai ya yi daidai ba ya ga mantuwar sa’a shidan da ya yi, al’amuran da har zuwa yau ba su dawo ba.

Da komawarsa gida Birtaniya sai ya ziyarci likitansa, wanda ya fada masa cewa ya ratsa bagiren duniyar mantuwa, wani lamari da ya saba shafar mutanen da shekarunsu suka dara 50 (kamar Paul).

Sashen kula da hadurra da kulawar gaugawa a asibiti na ganin mutum biyu zuwa uku wadanda suka auka cikin matsalar a ko wanne wata.

Lokacin aukuwar lamarin, mutane na sane da yadda ake tuki da tafiya, amma a matsala irin ta Paul ba za su iya tuna abubuwan da suka kasance suna yi a kwanakin da suka gabata ba.

Yawan maimaita tambayar wasu, kamar yadda Paul ya yi a gabar teku, nan ne jigon warware matsalar.

Sashen kula da hadurra da kulawar gaugawa a asibiti na ganin mutum biyu zuwa uku wadanda suka auka cikin matsalar a ko wanne wata.

Har yanzu musababbin matsalar bai bayyana ba.

Da farko likitoci na tsammanin irin wannan farmakin alama ce ta farfadiya ko rabin ciwon kai, ko ta yiwu an dan samu sandarewar gabban jiki.

A halin yanzu an tabbatar lamarin ba shi da alaka da sauran matsalolin rashin lafiya.

An yi hasshen cewa dunkulen sashen kwakwalwa da ke sarrafa tunani ne ke da alhakin tattara bayanai na tsawon lokaci, don haka ake ganin shi ne jigon shawo kan matsalar.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Illar matsalar na iya yin muni har ta kai ga mutane sun manta da kansu

Adam Zeman, Farfesan massarafar tunani da matsalolin kwakwalwa a Makarantar horar da Likitoci a Jami’ar Exeter ya yi nunmi da cewa: “abin da ake tsammanin yana faruwa shi ne masarrafar tunani (hippocampi) ke kullewa na wucin gadi.

Abin da ya faru ga Paul fitacce ne. Za ka manta abin da ya faru makonni da suka wuce, kuma ba za ka iya tuna sababbin al’amura lokacin da matsalar ke ci gaba ba.

Nazarin hoton kwakwalwa ya inganta wannan mahangar, inda aka gano matsalolin wucin gadi tattare da masarrafar tunani yayin aukuwar matsalar.

Mutanen da suka saba fama da yawan ciwon kai su suka fi yawan fama da matsalar.

Da ka bibiyi kadin al’amuran daidaikun mata 142, wadanda suka ratsa bagiren duniyar mantuwa, likitocin Faransa sun gano cewa, irin wadanan matsalolin dugunzumar damuwa ke haifar da su, al’amuran da suka hada da takaddamar muhawara, yayin da maza kuwa sun fi samun nasu ne lokacin da suke fama da matsin lamba ko nutso a ruwan sanyi.

Mutanen da suka saba fama da yawan ciwon kai su suka fi yawan fama da matsalar.

Hakkin mallakar hoto
(Credit: iStock)

Image caption

Cutar na nufin mutane na iya mantuwar sa’o’i ko kwanakin rayuwarsu har abada

Akai-akai, mutanen da ke fama da matsalar na da bambancin yanayin da ake kira ratsa bagiren farfadiyar mantuwa, wanda ake dauka cewa shi ne ratsa bagiren duniyar mantuwa, amma irin wannan farfadiyar.

Lamura ne na wucin gadi da ke faruwa akai-akai, da zarar an tayar da mutum daga barci.

Zeman ya ce a mafi yawan lokuta warware matsalar cutar na da sauki: “Idan ka ga wani bayan aukuwar lamarin, kuma suka bayar da bayani irin na Paul, to babu tababa a ciki.

“Idan ka hadu da su a tsakiyar aukuwar lamarin, to sha’anin na da matukar wahala, don haka sai ka yi tunanin farmakin wasu matsalolin da suka hada da sandarewa ko shanyewar gabobin jiki da farfadiya ko rudanin mantuwa.”

Babban bambancin da ke tattare da rudanin mantuwa shi ne majiyyatan ba sa iya tuna kansu, amma za su iya tuna sababbin al’amura.

Kyakkyawan batu game da matsalar ratsa bagiren duniyar mantuwa shi ne, lamari ne da ke faruwa a rudanin kwatsam ba tare da nuna alamar wasu cutttuka ba.

Sai dai kaso kadan ne daga cikin wadanda suka yi fama da yanayin za su sake kwata makamancinsa. Amma idan ya faru gareka, tabbas zai iya zama lamari mai tsananin firgitarwa.

Paul ya yi fatan ka da lamarin ya sake aukuwa har abada. Sai dai idan ya auku, to Kirsty na da masaniya kan ko mene ne.

''Yan siyasa ne kawai ke jin dadin Nigeria'


Wani masanin tattalin arziki na tambayar ko ‘yan siyasar Najeriya na ganin abun da ‘yan kasar ba sa gani ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya gamsu da tattalin arzikin kasar.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Presidency

Image caption

Mutane ba su san abun da Shugaba Buhari da ministocin da ke kula da tattalin arzikin kasar ke gani ba

Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya murna da yadda tattalin arzikin Najeriya ke habaka, wani masanin tattalin arziki a kasar ya ce shi bai ga abin da shugaban ya gani ba da ya sa ya furta kalaman ba.

“Mutane a Najeriya ba sa jin dadin tattalin arzikin kasar. Idan aka samu wani wanda ya gamsu da tattalin arzikin kasar, to dan siyasa ne,” in ji farfesa kan tattalin arziki da harkar kudi, Ayodele Momodu, a hirarsa da BBC.

Shugaban Najeriyar ya ce shi ya gamsu da yadda tattalin arzikin kasar ke habaka ne bayan ya gana da ministar kudin kasar, Misis Kemi Adeosun, tare da ministan kasafin kudi da na tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ranar Litinin.

Ita ce ganawar farko da ya yi da wadansu manyan mukarraba gwamnatin da ke kula da tattalin arzikin kasar bayan dawowarsa daga jinyar kwana 104 a Landan kan rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

A ganawar ministocin da gwamnan babban bankin Najeriya sun shaida wa shugaban kasar cewar tattalin azrikin kasar na habaka.

Amman kalaman shugaban kasar bayan ganawar sun bata wa wannan farfesan rai, lamarin da ya sa yake tamabayar cewa ko sun ga abun da ‘yan Najeriya da kwararru ke gani.

Ga sautin hirar da BBC ta yi da wani masanin tattalin arziki na tambayar ko ‘yan siyasar Najeriya na ganin abun da ‘yan kasar ba sa gani ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya gamsu da tattalin arzikin kasar.

Sai a latsa domin a jin yadda hirar ta kasance.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da masanin tattalin arzikin Najeriya

Dalilin Da Yasa Ya Kamata A Dakatar Da Sifeto Janar Na ‘Yan Sanda – AdeyanjuShugaban wata kungiyar na ‘yan Najeriya wato Concerned Nigerians civil society group, Deji Adeyanju, ya nemi a dakatar da Sifeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Ibrahim Kpotum Idris.

A cewarsa, dakatar da IGP zai ba da damar yin bincike game da zargin almubazaranci da kudi naira biliyan 120 na tsaro wanda sanata mai wakilta Bauchi ta tsakiya a majalisar tarayya, Hamman Isah Misau ya yi masa.

Sanata Misau ya zargi IGP Idris da tattara kimanin naira biliyan 120 a matsayin kudin tsaro na musamman daga kamfanoni, kamar kamfanonin man fetur, da kuma manyan mutane a kasar.

Shugaban wata kungiyar na ‘yan Najeriya, Deji Adeyanju

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Adeyanju, yayin da yake jawabi ga ‘yan jaridu a birnin Abuja, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da ofishinsa don ba da umarni kama da kuma bincike IGP Idris a matsayin shaida game da kokarin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Adeyanju ya ce: “Abi tambayar a nan shine; Shin IGP yana karba wannan kuɗi ko a’a?

“Muna farin ciki cewa shugaba Buhari ya dawo yanzu. Bari ya yaki wannan mumunar halin bera a gwamnatinsa masu fashi da baro. Muna so ya kama duk ‘yan fashi masu wawure dukiyar jama’ar kasar”.

“Ya kamata a dakatar da wannan IGP yanzu, idan da gaskiya muke yi game da yaki da cin hanci da rashawa. Buhari ya kama shi kuma ya gurfanar da shi tare da wadanda suka aikata laifin”.

“Muna so EFCC ta bincike wadannan batutuwa. Muna so EFCC ta duba wannan al’amari”, inji Adeyanju.

Sultan Ya Bukaci Al Ummar Muslumi Suyi Azumi A Ranar ArafaShugaban majalisar kula da harkokin musulunci (NSCIA) kuma sarkin Musulmi , Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bukaci musulmin da basu samu damar zuwa hajji bana ba da suyi a azumi a ranar alhamis wadda ta yi daidai da ranar Arafa, dan shirye-shiryen bikin sallar Eid-el-Kabir da za,ayi a ranar Juma’a.

A sanarwa da mataimakin sekatren majalisar,NSCIA, Ferfesa Salisu Shehu yayi, yace Sarkin musulmi a ranar Talata yace musulmai su yi amfani damar lokacin Idi wajen neman gafara da rahamar Ubangiji.

“Sallar Idin wannan shekarar yana da muhimmanci sosai. Saboda ya kunshi hudubobi da uku a cikin kwanaki biyu, huduban farko shine na ranar Arafa wanda za ayi a ranar Alhamis, 9 ga watan Dhul-Hiijah, 1438AH wadda tayi daidai da 31 ga watan Agusta, sai hudubobin ranar Idi da na Juma’a wanda za ayi a 10 ga watan Dhul-Hijjah, 1438AH wanda yayi daidai da 1 ga watanSatumba na shekearar 2017.

Sultan ya bukaci al ummar muslumi suyi azumi a ranar Arafa

“Hakika, wannan lokacin ne mai tarin albarka wanda yakamata kowani musulmi yayi amfani wannan dama wajen yin ayyukan alheri, dan dacewa da Rahamar Ubangiji,” Inji shi.

Ya ba da misali da sunnar Annabi Muhammad (SAW), Sarkin musulmi yace:

“Musulmin da basu samun damar zuwa aikin hajji ba, su dage su yi azumin ranar Arafa kuma su yawaita ayyukan alheri da niyyar Allah zai yafe musu dukan zunuban su.

“Yaku yan uwa musulmi, muhimmacincin Eid-El- Kabir shine koyar da al’umma bin dokokin Allah, Kamar yadda Annabi Ibrahim (AS), yabi Umarnin da Allah yaba shi, Allah ya fada a cikin alkurani cewa “Bana bukatan nama dabban da kuka yanka ko jinin da kuka zubar abin da nake bukata shine niyyar ku”(Q 22:37),” in ji shi.

Dalilin Da Yasa Bamu Kama Matasan Arewa Akan Wa’Adin Barin Gari Ba – Gwamnatin TarayyaGwamnatin tarayya ta yi bayanin cewa duk da matsa lamba da take samu, taki kama matasan da suka ba yan Igbo wa’adin barin gari a arewa saboda al’amarin tsaro.

Mutane da dama a kasar sun kalubalanci al’amarin barin gari da matasan arewa suka bai yan kabilar Igbo mazauna arewa.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ma ya saki wani jawabi inda ya bukaci yan sanda su kama su amma hakan bai yiwu ba.

Dalilin da yasa bamu kama matasan Arewa akan wa’adin barin gari ba – Gwamnatin tarayya

Matasan sun janye kudirin nasu bayan kira daga manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya inda suka bukaci su aikata hakan.

Vanguard ta rahoto cewa Abubakar Malami wanda shine ministan shari’a na tarayya yace ba’a kama matasan bane saboda dalilai na tsaro.

Ya kuma kara da cewa lallai gwamnati bazata gaza ba wajen hukunta duk wani ko kungiya da suka yi kalamun haddasa kiyayya ba.

An Saka Shugaban Masu Garkuwa Da Mutane EVANS A Kurkukun KirikiriAn tsare shahararren mai garkuwa da mutane wanda aka fi sani da Evans a kurkukun Kirikiri dake jihar Legas inda zai zauna kafin a cigaba da shariar sa wanda za ayi ranar Alhamis 19 ga watan Oktoba.

Alkali Hakeem Bello na babbar kotun tarayya dake Ikeja a Jihar Legas ya zantar da hukuncin a ranar Laraba 30 ga watan Agusta.

An saka shugaban masu garkuwa da mutane Evans kurkukun Kirikiri

An saka shugaban masu garkuwa da mutane Evans kurkukun Kirikiri

Shigar Evans kotu na farko kenan tunda yan sanda suka kama shi. Kuma Evans ya amsa laifufukan da ake tuhumar sa da yi, na garkuwa da mutane da yaudara.

Evans da yan kungiyan sa guda biyar ne sun gurfana a gaban kotu a safiya yau Laraba 30 ga watan Agusta da misalin karfi 8.56am karkashin kulawan jam’ian tsaro.

A cikin mutanen da Evans ya shiga kotu da su biyu sun amsa laifin su, uku kuma sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da shi.

Makwabcin Sheikh Kabiru Gombe Ya Kai Kararsa Gaban Kotu Kan Zarginsa Da Aikata Wani LafiShi dai wannan makwabci na Malam Kabiru Gombe yayi kararsa ne gaban kotu kan zarginsa da take hakkin makwabtaka, kamar yadda ya shaida ma alkalin kotun, Sarki Yola.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito makwabcin yana fadin wai Kabiru Gombe ya sanya wasu waga wagan Tagogi a turance sabon gidansa daya gina a unguwar Sabuwar Gandu, inda makwabcin ke zarginsa da samun damar liken matayensu.

Makwabcin ya kara da cewa “Wannan Malamin ya gina manyan tagogi, sa’annan ya sanya musu bakaken gilasai, ta yadda shi zai iya ganin jama’a, amma mu ba zamu gan shi ba.” kamar yadda majiyar NAIJ.com ta rwuaito.

Wannan makwabci dai ya cigaba da shaida ma kotu cewar tun lokacin da aka fara ginin gidan suka janyo hankalin Malamin, amma bai dauki wani mataki game da hakan ba.

Sai dai lauyan Malamin Ishaq Adam Ishaq ya bayyana ma kotu cewar ba wani bane ke damun wannan makwabci illa bakin ciki da hassada da suke yi Malamin sakamakon daukaka da Allah yayi masa.

Daga karshe dai Alkali Sarki Yola ya aika da jami’an kotu da su tafi su gano masa yadda wadannan tagogi suke, sa’annan su kawo masa rahoton abinda suka gani, bayan nan sai a cigaba da sauraron karar.

Ya Zama Dole Ni Da Sauran Masu Rike Da Mulki Mu Tuba -Inji Dino MelayeA yau Laraba, Senata mai wakiltan Kogi ta yamma Dino Melaye yayi amanna cewa yan Najeriya na fama da matsanancin yunwa da talauci, dalilin hakan yace ya zama dole shi da sauran masu rike da madafun mulki a Najeriya su tuba kuma su dauki hanyar magance matsalar.

Senata Melaye ya fadi wannan maganan ne a wata hira da yayi da wani shiri mai suna ‘The Osasu show’ kuma ya yadda bidiyon a shafinsa na twitter domin mutane su kalla.

Ya zama dole ni da sauran masu rike da mulki mu tuba – Dino Melaye

“Masu rike da mulki a Najeriya dole ne su tuba, har ma da ni. Ya kamata mu dukufa wajen magence yunwa da talauci da tayi ma jama’a katutu. Bai dace a bar yan Najeriya cikin irin wannan halin ba ,” Kamar yadda Melaye ya rubuta.

Idan baku manta ba, a kwanakin baya Senatan ya amince da cewa yan siyasar Najeriya sun gaza

A maganan da Melaye ya fadi a wajen hirar, yace, ” Fadin gaskiya ko karya baya hana mutum mutuwa; tunda haka ne, gara mutum ya fadi gaskiyar ya mutu a kanta. Ba kowa zai yarda dani ba amma ni dai na fadi gaskiya. Bayan mulkin kama-karya na soji, siyasa itace abun da ta kawo talauci da yunwa Najeriya.

”Abun kunya ne yadda ni da sauran masu rike da mulki muka gaza wajen gudanar da mulkin kasar yadda ya dace. Dalili kuwa shine akwai rashin yarda tsakanin masu mulki da wanda ake mulka ”.

Buhari ya tafi bikin Sallah a Daura


Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

Gwamnatin Buhari ta gurfanar da mutane da dama a gaban kuliya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina ta arewacin kasar domin yin bikin babbar Sallah.

Hotunan da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta sun nuna manyan jami’an gwamnati da Sarakuna suna tarbar shugaban kasar.

Cikin wadanda suka tarbe shi har da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da sarakunan Katsina da Daura.

A ranar 19 ga watan nan ne Shugaba Buhari ya koma Najeriya, bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a birnin London.

Hakkin mallakar hoto
Nigeria presidency

Image caption

Shugaba Buhari ya sha alwashin yaki da masu cin hanci

Hakkin mallakar hoto
NIGERIA PRESIDENCY

Image caption

‘Yan Najeriya da dama sun yi addu’a ga Shugaba Buhari lokacin da ba shi da lafiya

Mazauna Saman Dutse A Jihar Filato Sun Koka Da Cututtukan SanyiKamar yadda aka san jihar Filato da yawaitar duwatsu a kasar nan, da yawan al’ummar jihar sun maishe da saman duwatsun wajen rayuwar su.

Sanadiyar yawaitar wannan duwatsu a jihar, ta kasance jiha mafi karancin zafi kuma mafi sanyi a cikin gaba daya jihohin Najeriya.

Sakamakon wannan ne ya janyo mazauna saman dutse a jihar suke fuskantar kalubalen dukkannin wata cuta da ta ke da alaka da sanyi. Ciwon huhu, mura, tyfod, ciwon kirji da ciwon gabbai da sanyi ke janyowa sun yiwa mazauna saman dutsen katutu.

Mazauna saman dutse a jihar Filato sun koka da cututtukan sanyi

Manema labarai na gidan jaridar DAILY TRUST sun kai ziyara zuwa wasu yankunan mazauna saman dutsen a jihar Filato, inda suka lura da danshi da kuma laima a kasan gidajen dake saman duwatsun ga kuma sanyi wanda ya sha ban-ban da wuraren da ba saman dutsen ba.

Wata mata mai shekaru 67 a duniya, Joy Istifanus, wadda ke zaune a unguwar Daku ta gundumar Abbatuwan birnin Jos, ta bayyana cewa, tun a shekarar 1999 ta ke rayuwa saman dutsen, kuma ita ce mutum ta farko da ta fara zama a wannan yankin na saman dutse.

Ta ke cewa, “tun lokacin da na fara zama a saman dutsen, babu ko gida daya face nawa. Macizai da kunamai da ma sauran halittu ma su dafi su na buya karkashin duwatsu, wanda kafin mu ankara sun tafka mana sara ka cizo.”

“Wannan abu ya yi sauki ba kamar da ba, domin kuwa yanzu akwai jama’a da dama da suke zaune a saman dutsen.”

“Sai dai wani hanzari ba gudu ba game da lafiyar mu, akwai ciwon huhu da sanyi ke haifarwa kananan yara da kuma ciwon gabbai ga wadadnda suka manyanta.”

“Akwai sauro mai muzguna mana domin muna yawan fama da zazzabin cizon sauro, kuma hakan ya bayu ne sandiyar rashin magudanan ruwa da kuma ruwa sama da yake kwanciya a lokutan damina.”

“Sai dai gwamnati a kwana-kwanan nan, gwamnati ta rarraba gidan sauro wanda yake taimaka mana kwarai da gaske.”

Wani malamin makarantar Firamare ta Mount Zion dake saman dutsen, Alpha Ibrahim, ya bayyana irin na shi kalubalen da ya ke fuskanta sanadiyar rayuwa da yake a saman dutsen.

Ya ce, “Babu wasu bishiyu a saman dutsen da su taimaka wajen zama ganuwa tsakaninsu da iskar bazara, wanda hakan yake janyo barazana ga lafiyarsu da kuma muhallansu.”

“Akwai ‘ya ta da take fama da ciwon sanyi na huhu sanadiyar sanyi da bangon dakin mu ke dauka kuma yanzu ba ta gama shan magungunan ta ba.”

Ma’Aikatan Asibiti Na Zanga-Zanga A Jihar Ondo Ta Kai Sun Hana Kowa Shiga SsibitinA safiyar yau Laraba 30 ga watan Augusta, daruruwan ma’aikata na asibitin gwamantin tarayya da ke jihar Ondo, Federal Medical Centre, Owo sun gudanar da zanga-zanga a dalilin rashin biyan su albashi har na taswon watanni 18.

Ma’aikatan asibiti na zanga-zanga a jihar Ondo, sun hana kowa shiga asibitin

Ma’aikatan, wanda sun hada da masu shara, dirbobi, masu ban ruwan fulawa da kuma masu gadi maza da mata sun kulle kofar shiga asibitin. Hakan yasa babu wani ma’aikacin lafiya ko kuma mara lafiya da ya samu shiga asibitin

Wata majiya ta sanar da jaridar Premium Times cewa babu wani aiki da ke tafiya a asibitin tun safiya har zuwa yanzu

EFCC na shirin taso keyar Diezani Allison-Madueke


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku saurari hirarmu da Ibrahim Magu

Shugaban riko na hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ya ce nan ba da dadewa za su sa gwamnatin Birtaniya ta tiso keyar tsohuwar ministar mai Diezani Allison Madueke.

Ibrahim Magu ya shaida wa BBC cewa “Muna nan muna kokarin ganin an taso keyarta domin ta zo nan”.

Ya kara da cewa a wannan shekarar kadai, EFCC ta yi nasarar kwato kimanin Naira Biliyan 409 da kuma Dala Miliyan 69 daga hannun mutane daban-daban da ake zargi da sace kudaden gwamnatin a wannan shekarar.

A cewarsa, an gurfanar da mutanen a gaban kuliya, yana mai cewa EFCC ta samu nasara kan kararraki 137 a shekarar 2017.

Mr Magu ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da ministan shari’ar Abubakar Malami, yana mai cewa “wannan labarin sharrin ‘yan jarida ne kawai. Amma buri daya muke son cimmawa”.

Shugaban na EFCC ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da ba shi hadin kai a yakin da hukumar ke yi da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati.

Gwamnonin Kudu Maso Gabashin Najeriya Na Tattauna Da Nnamdi KanuGwamnonin jihohin Kudu maso gabashin kasar suna ganawa da shugaban ‘yan asalin yankin Biyafara, IPOB, Namdi Kanu a yanzu haka.

Ganawar wanda ta samu halartar gwamnonin guda 5 daga yankin kuma ana gudanar da taron yanzu haka a dakin hutu na gwamnan jihar Enugu.

Emmanuel Uzor, babban sakataren gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana hakan a shafinsa ta Facebook a yau Laraba, 30 ga watan Agusta.

Shugaban kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu

A cikin jawabinsa, Mista Uzor ya ce kiran da IPOB ta yi don kauracewa zaben gwamnan jihar Anambra wanda za a yi a watan Nuwamba 18 na cikin muhuimmin batun da za a tattauna a taron.

NAIJ.com ta tattaro cewa, wannan ne ganawar ta farko wanda shugaban kungiyar Nnamdi Kanu ya yi tare da gwamnonin kuma ya zo bayan da Kanu ya ki a gana da shi.

Mutane 8 Sun Mutu, 7 Sun Ji Rauni Yayinda wani hatsarin Mota Akan Gadar Jihar DeltaAkalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu sannan wasu bakwai sun ji rauni a yayinda wata motar kasuwa ta fado daga gada sannan ta sauka kan hanyar jirgin Itakpe-Aladja.

Motar da tayi hatsarin na dauke da lamba BMA 524XA, sannan hatsarin ya auku ne a jiya a Agbor/Ogwashi-Uku dake hanyar Benin-Asaba-Onitsha.

Jaridar Sun ta rahoto cewa, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai maza shida da mata biyu, sannan daga cikin wadanda suka ji rauni akwai manya shida da yaro daya.

Mutane 8 sun mutu, 7 sun ji rauni yayinda wani bas ya fadi a gadar Delta

A yayinda aka kai gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu dakin ajiye gawa, an tafi da wadanda suka jirauni asibitin dake Agbor a jihar Delta domin duba lafiyarsu.

Haka zalika, idon shaida ya rahoto cewa da wuya masu raunin su rayu saboda tsananin rauni da suka ji. Sannan ba’a san menene dalilin barin hanya da direban yayi ba.

Amman shugaban sashen hukuma dake kare hadaruka dake jihar Delta, ya tabbatar da hatsarin, ya bayyana dalilin hatsarin ga rashin hutu.

Ya kara da cewa mai yiwuwa direban ya rasa gane kan motar ne a lokacin.

Dattawan United za su kara da na Barcelona


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United ce za ta karbi bakuncin Barcelona a Old Trafford

Dattawan Manchester United za su karbi bakuncin na Barcelona a wasan sada zumunta domin tuna wadan da suka mutu a harin ta’addacin da aka kai biranensu.

Tsoffin ‘yan wasan da za su buga wa United karawar sun hada da Edwin van der Sar da Ruud van Nistelrooy da Ji-sung Park da kuma Wes Brown.

Ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Old Trafford da Edgar Davids da Patrick Kluivert da Gaizka Mendieta da kuma Eric Abidal.

Dattawan za su daura bakin kyalle a hannunsu da kuma sunan biranensu a bayan rigunan da kowa zai saka a fafatawar da za su yi a ranar Asabar a Old Trafford.

A cikin watan Mayu ne aka kai harin ta’addanci a birnin Manchester daga baya aka kai hari a birnin Barcelona da na Cambrils a farkon watan nan.

Kamfanin Kula Da Harkokin Mai Na NNPC Ya Tankade Manyan Manajojinsa Guda 55An yi tankadar manyan manajojin kamfanin kula da harkokin mai na kasa, NNPC. Shugaban NNPC, GMD Maikanti Baru ya ce ana yin canje-canjennan ne don gyara ma’aikatar NNPC, da kuma cike guraben da wasu suka yi ritaya.

Kamfanin mai na NNPC ya tankade manyan manajojinsa guda 55

A cikin sabon tsarin, tsohon manajin darekta na Integrated Data Services Ltd (IDSL), Roland Ewubare, an maida shi sabon GGM na NAPIMS. Tsohon GGM Diepriye Tariah zai zama sabon manajin darekta na IDSL.

Shi kuma shugaban kamfanin tace mai na Kaduna (KPRC), Malami Shehu, ya koma shugaban kamfanin tace mai na Fatakwal. Shi kuma shugaban kamfanin tace mai na Warri, Adewale Ladenegan, an mai da shi shugaban KPRC. Muhammed Abah, direkta opereshin ya zama shugaban kamfanin Warrin.

Wadannan sune kadan daga cikin canje-canjen da aka yi. Mai Magana da yawin NNPC, Ndu Ughamadu, ya ce da yawun Shugaba Buhari aka yi wannan canje-canjen.

Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Na Karbar Zakarun ‘Yan Kwallon Kwando Ta Afirka Yanzu A Fadar Aso RockA yau shugaba Buhari na cike da farin ciki, bayan da ‘yan kwallon kwando ta mata da suka ciwo kofin gasar na Afirka suka kawo masa kofin har gida, dubi hotunan nasu cikin nishadi.


Labari cikin Hotuna: Shugaba Buhari na karbar ‘yan kwallon kwando a fadar Aso Rock

Shugaban dai ya baiwa kowacce ‘yar wasa kyautar naira miliyan daya, su kuma ma’aikata naira dubu dari biyar biyar.


Minista Solomon Dalung ma dai na cikin nishadi sosai.

A tarihin Najeriya, a bangaren wasanni, duk sanda maza suka kasa, matan ke fitar da kasar Najeriya kunya a idon duniya.

Yaushe rabon Buhari da yin taron ministoci?


Hakkin mallakar hoto
Novo Isioro

A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar ministoci na farko cikin bayan tafiyarsa jinya Birtaniya, wata uku da suka gabata.

Mai magana da yawun shugaba Buhari kan yada labarai Femi Adesina ne ya wallafa shigar shugaban taron a shafinsa na Twitter.

A zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban ya karbi bakuncin kungiyar kwallon kwando ta mata ta kasar, D’Tigress.

Shugaban ya koma Najeriyar ne daga Birtaniya a ranar 19 ga watan Agusta, inda ya shafe kwana 104 yana jinya.

A lokacin da baya nan Mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ne ya dinga tafiyar da al’amuran gwamnati, yake kuma jagorantar taron majalisar ministocin.

A wancan makon ne Shugaba Buharin ya soke taron, wanda aka sa ran shi ne na farko da zai jagoranta bayan dawowarsa daga jinyar.

Sai dai a ranar ce shugaban ya karbi rahoton binciken da ake yi wa sakataren gwamnatin kasar da aka dakatar kan zargin cin hanci Babachir Lawal, da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar Ayo Oke.

Ana sa ran taron na ranar Laraba zai tattauna kan batun yajin aikin da Malaman Jami’a ke yi.

Hakkin mallakar hoto
Novo Isioro

Image caption

Buhari ya gana da tawagar kwallon kwando ta mata kan nasarar da suka yi

Hakkin mallakar hoto
Novo Isioro

Chamberlain ya fi son Liverpool kan Chelsea


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chamberlain ya koma Arsenal daga Southampton a 2011

Dan kwallon Arsenal mai tsaron baya, Alex Oxlade-Chamberlain ya ki yadda ya koma Chelsea da taka-leda duk da Gunners ta amince da tayin fam miliyan 40.

Chelsea na son yin amfani da Chamberlain a gurbin mai tsaron baya daga gefe, shi kuma dalilin da ya sa yake son barin Arsenal saboda baya buga wasa daga tsakiyar fili.

Dan kwallon tawagar Ingila mai shekara 24, na son ya koma Liverpool, kuma kungiyar tana son sayen sa.

Ana sa ran Liverpool za ta taya dan Chamberlain kafin ranar Alahmis, watakila kasa da fam miliyan 40 da Chelsea ta ce za ta biya.

Sai dai Arsenal na fatan kammala sayar da tsohon dan kwallon Southampton din ba tare da ba ta lokaci ba, wanda yarjejeniyarsa da Gunners za ta kare a karshen kakar badi.

Wa Zai Cika Mata Burin Ta: Wata Yarinya Na Nema Ta Ga Shugaba BuhariMun samu labari cewa wata yarinya ‘yar shekara 10 ta aikawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasika cewa tana so ta gan shi.

Wasika zuwa ga Shugaba Buhari

Wannan yarinya mai suna Aisha Aliyu Gebi daga Jihar Bauchi a Arewa maso gabashin kasar ta fara wasikar ne da tambayar halin lafiyar Shugaban kasar a yanzu wanda daga nan tace abin da ya sa ta rubuta takardar shi ne tana kaunar ganin Shugaban kasar fuska da fuska.

Wata ‘yar uwar ta ce mai suna Hasna Gebi ta yada wannan takarda a shafin ta na Tuwita kuma tuni har daya daga cikin Hadiman Shugaban kasar Malam Bashir Ahmad ya nemi zantawa da wannan mata goggon yarinyar. Watakila dai a cika mata burin ta na ganin Shugaban kasa.

Kwanaki kun ji kamar dai yadda kowa yake gani ba shakka rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na iya hana sa takara a 2019.

Juventus ta kusa kammala daukar Howedes


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jamus ce ta lashe kofin duniya a Brazil a 2014, bayan da ta ci Argentina 1-0 a wasan karshe

Dan wasan tawagar kwallon Jamus, mai taka-leda a Schalke, Benedikt Howedes yana Juventus ana duba lafiyarsa a shirin komawa can da buga tamaula.

Howedes mai shekara 29, ya yi wasanninsa na tamaula tun yana da kuruciya a Schalke, ya kuma yi kyaftin dinta shekara shida.

An nuna hoton dan kwallon a shafin intanet na Juventus domin a duba lafiyarsa a ranar Laraba.

Howedes ya buga wa Jamus wasa 44 har da na gasar cin kofin duniya a 2014 da kasar ta zama zakara a Brazil.

World Cup 2018: Nigeria za ta kara da Kamaru


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nigeria ce ke mataki na daya a rukuni na biyu da maki shida

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta karbi bakuncin ta Kamaru a ranar Juma’a a wasan shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci.

Super Eagles za ta buga wasan ne ranar 1 ga watan Satumba a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.

Kwanki uku tsakani ne Super Eagles za ta ziyarci Kamaru a wasa na biyu da za su fafata a Yaounde.

Super Eagles ce ta daya a rukuni na biyu da maki shida bayan da ta yi nasara a kan Zambia da Algeria, Kamaru ce ta biyu da maki biyu wacce ta yi kunnen doki da Algeria ta tashi babu ci da Zambia.

Kocin Kamaru, Hugo Bross ya ce idan har ba su samu maki hudu ba a kan Nigeria a fafatawar da za su yi gida da waje zai yi wahala su halarci Rasha a badi.

Ga wasannin da za a buga a karshen mako:

 • Alhamis: Litinin:
 • Uganda v Egypt (Grp E)Cameroon v Nigeria (Grp B)
 • Guinea v Libya (Grp A)Libya v Guinea (Grp A in Tunisia)
 • Juma’a: Talata:
 • Ghana v Congo (Grp E)Congo v Ghana (Grp E)
 • Nigeria v Cameroon (Grp B)South Africa v Cape Verde (Grp D)
 • Cape Verde v South Africa (Grp D) Ivory Coast v Gabon (Grp C)
 • Morocco v Mali (Grp C)DR Congo v Tunisia (Grp A)
 • Tunisia v DR Congo (Grp A)Burkina Faso v Senegal (Grp D)
 • Asabar:Egypt v Uganda (Grp E)
 • Zambia v Algeria (Grp B)Mali v Morocco (Grp C)
 • Gabon v Ivory Coast (Grp C)Algeria v Zambia (Grp B)
 • Senegal v Burkina Faso (Grp D)

Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu


Image caption

Police found several human body parts during a raid in a traditional healer’s house

An tsinci gawar wata matashiya da ta fara rubewa mako guda bayan da wani mai maganin gargajiya ya mika kansa ga ‘yan sanda ya ce ya gaji da cin naman dan adam.

Mutanen yankin KwaZulu na cike da fargaba bayan da aka gano gawar Zanele Hlatshwayo mai shekara 25, an ciccire wasu sassan jikinta, a kuayen Shayamoya a Afirka Ta Kudu.

Iyayen yarinyar wacce ta bata tun a watan Yuli, sun yi amannar cewa tana daga cikin wadanda masu cin naman mutane ne suka kashe, inda tuni aka kama biyar daga cikinsu.

Da farko dai ‘yan sanda sun ki saurarar batun mutumin da ya mika musu kan nasa, amma sai suka yarda da abin da yake fada a lokacin da suka ga jini dumu-dumu a hannayensa da kafafuwansa, suka kuma kama shi.

Mutumin ya kai ‘yan sandan gidansa, inda aka samu kunnen mutum har takwas a cikin tukunya.

An yi amannar cewa ya yi niyyar sayarwa abokan huldarsa ne, wadanda aka shaida wa cewar suna da sirri na taimakawa mutum ya yi kudi ko ya samu mulki.

An kuma samu wasu sassan jikin da dama a wani akwati.

Image caption

An tsinci gawar Zanele Hlatshwayo a cikin duwatsu

An samu tufafin Ms Hlatshwayo da jini kaca-kaca a jiki a dakin mai maganin gargajiyar da aka samu sassan jikin mutanen.

Iyayenta ne suka gane tufafin nata.

Haka kuma, ‘yan sansa na jiran sakamakon gwaje-gwajen kwayoyin halitta domin a tabbatar ko daga cikin sassan jikin mutanen akwai na wata mata mahaifiyar wani yaro dan shekara biyu.

Har yanzu iyayen Ms Hlatshwayo ba su binne ta ba. A yayin da na shiga gidansu Hlatshwayo, ba abin da nake ji sai koke-koken ‘yan uwanta.

Babbar yayarta Nozipho Ntelele, ta ce min a lokacin da take share hawaye, “Muna jin ciwon salon da aka bi aka kasheta, an mata kisan wulakanci.”

Image caption

‘Yan uwan Hlatshwayo suna zaman makoki

Ta kara da cewa, “Duk tufafinta ya yi duku-duku da dattin kasa, alamar ta sha artabu wajen ganin ta ceci ranta,” “in ji Ms Ntelele.

Warin rubabben naman mutum

Mai maganin gargajiyar na zaune ne a wata bukka a Rensburgdrift kusa da Estcourt.

Ana kiransa da “Mkhonyovu” wanda ma’anarsa ke nufin “mai tafka almundahana” a yaren Zulu na kasar.

Ya karbi hayar gidan ne daga wajen Philani Magubane, wanda shi ma ake zargin kaninsa da irin wancan laifin.

Image caption

Wannan ne dakin da mai maganin ya kama haya

Image caption

‘Yan sanda sun samu kunne takwas a dakin mutumin da kayan tsafi

“Na kadu matuka da jin cewa kanina ya yarda da tatsuniyar mai maganin gargajiyar nan, inda ya yi musu alkawarin arziki bayan kuwa shi talaka ne futuk,” in ji Mr Magubane.

Ya ce daya daga cikin masu zaman haya a gidan ya yi ta korafin cewa yana jin warin rubabben nama na fitowa daga gidan makwabcinsa.

“Mkhonyovu bai fi wata biyu da tarewa a gidan ba, ban taba sanin cewa yana ajiye sassan jikin mutane ba saboda ni ba anan nake zama ba,” in ji Mr Magubane.

Mr Magubane ya ce ya tabbata kaninsa da sauran mutanen sun rudu ne da karairayin mai maganin da ya ce zai musu tsafi su yi arziki.

Ana zargin cewa yana aika mutane su tone kaburburan jama’a ne da tsakar dare don ya hada wani tsafi da ake kira “muti”.

Yadda mutane suka ci naman mutum suna sane

Mthembeni Majola, wani dan siyasa a garin ya kira taron al’ummar yankin jim kadan bayan da daka gabatar da masu cin naman mutanen a gaban kotu.

Image caption

Mthembeni Majola ya ce daya daga cikin mazauna garin ya san cewa naman mutum yake ci

“Mazauna garin da dama suna zaune cikin tsoro tun bayan fallasuwar siriin mutanen, amma Mr Majola ya ce wasu mutanen ba su yi mamaki ba.

“Wasu da dama sun tabbatar da cewa sun san abin da mai maganin ke yi har ma sun ci naman mutum suna sane,” in ji shi.

“Amma abin da ya bata mana rai shi ne yadda mutanenmu suka zama sakarkaru, yawancin wadanda suke zuwa wajen mai maganin barayin shanu ne wadanda yake cewa zai ba su sa’a su dinga bacewa ko ba su maganin karfe don ko ‘yan sanda sun harbe su bindiga ba za ta same su ba, in ji Mr Majola.

Phepsile Maseko, wata jagora ce a kungiyar masu magain gargajiya ta Afirka Ta Kudu, ta kuma yi Allah-wadai abin da masu cin naman mutanen ke yi.

Ta ce, “Mkhonyovu mai maganin karya ne wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya shigo da mugun abu cikin sana’armu.

Image caption

Phepsile Maseko ta ce, “Mkhonyovu mai maganin karya ne wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya shigo da mugun abu cikin sana’arsu

“Kashe mutane da yin tsafi da sassan jikinsu ba ya cikin tsarin maganin gargajiya, abin da ya yi ya bata mana rai saboda a yanzu dole sai mun fito mun kare aikinmu da kyau gudun bacin suna,” in ji Ms Maseko.

Mutane biyar din da aka kama wadanda aka gurfanar da su a kotu ranar Litinin sun yi watsi da belinsu da aka bayar, za kuma su sake gurfana a gaban kotun a karshen watan Satumba.

Gwamnatin Iran Zata Halatta Auren Dandano Domin Rage BarnaMun samu labari daga Jaridar Daily Mail cewa ana kokarin kawo karshen kwanciya da maza kafin ayi aure a Kasar Iran.

Za a kawo karshen zinace-zinace a Iran

Gwamnatin Kasar Iran za ta halatta auren dandano domin a rage barna a Kasar domin kuwa bincike ya nuna kashi 80% na ‘Yan matan kasar kan kwanta da wani kafin su yi aure. Kusan daya cikin biyar kuma na wannan kason kan bi ‘Yan uwan su ne mata.

Auren dandano kan bada dama mutum ya sadu da wata na dan lokacin kafin a rabu. Wannan zai yi maganin zinace-zinacen da ake tafkawa a Kasar. Gidan labarai na Fox News yace tun yara mata su na kanana ake fara kwanciya da su. Mafi yawan mutanen kasar dai yara ne matasa.

Kwanaki kun ji cewa rashin Maza na aure a Najeriya na nema ya zama wani tashin hankali. Mazan aure su na matukar wahala a halin yanzu saboda jiran mai kudi.

Arsenal ta ki sayar wa da City Sanchez


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal ta yi rashin nasara a wasa biyu daga ukun da ta buga a Premier

Arsenal ta ki sallama tayin fam miliyan 50 da Manchester City ta yi wa Alexis Sanchez domin ya koma Ettihad da murza-leda.

A karshen kakar badi yarjejeniyar Sanchez mai shekara 24 za ta kare da Gunners, kuma yana son ya koma buga tamaula a Manchester City.

Arsenal ba ta yadda da duk wani kokarin da City ke yi na sayen Sanchez ba, kuma tana son Raheem Sterling ya koma Emirates da wasa a cikin cinikin kafin ranar Alhamis.

Shi kuwa kocin Manchester City, Pep Guardiola yana son sayen Sanchez ba tare da bayar da Sterling ba.

Sterling ya buga wa City wasa uku da ta yi a Premier, amma ba a yi masa alkawarin saka shi a wasa akai-akai ba, sakamakon sayen Bernardo Silva da ta yi daga Monaco.

Yadda Wata Malamar Asibiti Ta Kashe Marasa Lafiya Kusan 100Mun samu wani labari na yadda rashin imani ya sa wata Malamar asibiti ta hallaka marasa lafiya rututu.

Malamar asibiti Niels Hoegel tana rufe fuska

Wannan Nas Niels Hoegel mai shekaru 40 a Duniya tayi aiki a Birnin Bremen da ke Kasar Jamus inda kwanaki aka daure ta saboda ta yi sanadiyar mutuwar maras lafiya har 2 bayan ta dura masu magani.

Sai dai wannan din somin-tabi ne kamar yadda binciken ‘Yan Sanda ya nuna. Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda Arne Schmidt yace ba mamaki wannan mata tayi sanadiyar arcewa da sama da marasa lafiya 180 a Kasar lahira.

Ana cewa kusan tun bayan yakin Duniya ba a taba samun wanda ya hallaka Jama’a a kasar Jamus haka ba. Haka kuma kwanan nan kun ji rahoto game da yadda Asibitin koyarwa na Jamia’ar Ahmadu Bello da ke Garin Shika ya kama hanyar sukurkucewa a halin yanzu.

Arsenal ta ki sayar da Sanchez, Liverpool za ta sayar da Coutinho?


Tottenham ta kusa sayan dan Ajentina mai shekara, mai shekara 19, Juan Foyth daga Estudiantes kan kudi fam miliyan 8 kuma tana sake kokarin kammala cinikin Serge Aurier kan kudi fam miliyan 23, in ji Guardian.

Hakkin mallakar hoto
ALEJANDRO PAGNI

Image caption

Juan Foyth

Liverpool ta yarda ta sayar da dan wasan Brazil mai shekara 25, Philippe Coutinho, ga Barcelona a wata yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 148, in ji Yahoo Sports.

Duk da haka jagoran Liverpool, Peter Moore, ya nuna cewar ba za a sayar da Coutinho ba a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter kafin lokacin a rufe kasuwar ‘yan wasan ranar Alhamis, in ji Liverpool Echo.

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan gaba, Alexis Sanchez, mai shekara 28, idan yarjejeniyar ta yi mata kyau, in babban wakilin Daily Mirror kan kwallon kafa, John Cross.

Hakkin mallakar hoto
Dean Mouhtaropoulos

Image caption

Ana ta rade-radi kan makomar Sanchez a kwanakinnan

Inter Milan ta sake sabon tayi wa dan wasan gaban Arsenal mai shekara 25, Shkodran Mustafi, in ji Sky Sports.

Tottenham tana tunanin ko za ta jinkirta taya dan wasan tsakiyar Everton, Ross Barkley saboda matsalolin ciwon da dan shekara 23 din yake da su, in ji London Evening Standard.

Dan wasan West Brom na baya, mai shekara 29, Jonny Evans, zai ki komawa Arsenal saboda yana son komawa Manchester City, in ji Daily Mail.

‘Yan Baggies din sun shirya domin sayan dan wasan Poland mai shekara 27, Grzegorz Krychowiak daga Paris St-Germain, in ji Sun.

Hakkin mallakar hoto
Michael Steele

Image caption

Jonny Evans

West Brom, za ta kammala sayan dan wasan bayan Arsenal Kieran Gibbs kan kudi fam miliyan 7 nan da sa’o’i 24, in ji Daily Mirror.

Dan wasan bayan Southampton Virgil van Dijk, mai shekara 26, yana da fatan komawa Liverpool, duk da cewar Arsenal da zakarun Firimiya Chelsea ka iya taya shi, in ji Independent.

Crystal Palace za ta goyi bayan kociya Frank de Boer da sayayya uku, in ji Daily Star.

Stoke City tana son sayan dan wasan tsakiyar Manchester City, Fabian Delph, mai shekara 27, kuma a shirye take ta taya dan wasan da aka saya daga Asoton Villa fam miliyan 8 , kan kudi fam fam miliyan 12, in ji Daily Telegraph.

Kociyan Newcastle United, Rafael Benítez, zai sayar da dan wasan gaba mai shekara 26, Dwight Gayle kan kudi fam miliyan 18, in ji Guardian.

Barcelona Tayi Magana Game Da Tashin Manyan ‘Yan Wasan TaA ‘yan kwanakin nan aka fara jin kishin-kishin din cewa wasu manyan ‘Yan wasan Barcelona za su tashi.

‘Yan wasa Messi da Iniesta za su tashi?

Hakan ya zo ne bayan Kyaftin kuma babban Dan wasan tsakiya na Kulob din Andres Iniesta yace yana duba yiwuwar barin Kulob din. Kungiyar Juventus dai na zawarcin sa. Shi kuma Lionel Messi har yanzu bai amince sa sabon kwantiragi da Kulob din ba.

Wani Darektan kulob din Ariedo Braide ga bayyanawa wani gidan rediyo a can cewa babu inda manyan ‘Yan wasan za su je. Kwanan nan dai Kungiyar tayi rashin babban Dan wasan gaban ta Neymar Jr. zuwa Kungiyar PSG kan wasu makudan kudi.

Ku na da labari cewa har yanzu Messi bai amince da sabon kwantiragi ba a Kungiyar. Barcelona ta dai jaddada cewa Dan wasan zai kara kwantiragi nan ba da dadewa ba. Yanzu haka dai yarjejeniyar Dan wasan ta tike ne zuwa badi.

Nigeria: Evans ya amsa lafinsa na 'satar mutane' a kotu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A baya Evans ya yi karar rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa zargin suna tsare shi ba bisa ka’ida ba

Madugun nan da ake zargi da satar mutane don karbar kudin fansa a jihar Legas da ake kudancin Najeriya, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na hada tuggu don sace mutane ya yi garkuwa da su a gaban wata babbar kotu a Legas.

An gurfanar da Evans ne a ranar Laraba a babbar kotun Legas da ke Ikeja a gaban mai shari’a Akin Oshodi.

Tun a farkon watan Yuni ne aka cafke Evans da wasu mutum biyar inda daga bisani aka gurfanar da su a gaban babbar kotun kan tuhumarsu da satar mutane don karbar kudin fansa.

Abba Kyari: ‘Evans ya so ya gagari jami’an tsaron Nigeria’

Evans ya shigar da ‘yan sandan Nigeria kara a Kotu

‘Yan sandan Nigeria: ‘Evans yana nan bai mutu ba’

Kotu ta ci tarar lauyan Evans

Image caption

‘Yan sanda na cikin shirin ko-ta-kwana don raka Evans gidan yari

Hakkin mallakar hoto
AFP

A ranar Talata ne wani sashe na babbar kotun ya sanya ranar 5 ga watan Satumba don sauraron uzurin lauyan Evans da lauyoyin ‘yan sanda a kan dalilin da ya sa kotu ba za ta yanke hukunci kan karar da Evans ya shigar kan tauye ‘masa hakki’ na ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi gaban shari’a ba.

A ranar Talata ne kuma, wadda tun farko alkali ya so yanke hukunci kan korafin Evans din, lauyan ‘yan sanda David Igbodo, ya shaida wa manema labarai cewa, “Yin hakan rashin adalci ne ba tare da jin nasu uzurin ba.”

Ya kuma kara da cewa, binciken da ‘yan sanda suke yi kan Evans din ya kusa kammala.

Mr Igbodo ya kuma ce binciken da suke yi din ne dalilin da ya sa suke ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi a gaban shari’a ba, kuma kotu ce ta ba su wannan umarnin.

“Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su san mece ce makomar Evans kan irin abin da ya aikata,” in ji Mist Igbodo.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce Evans ya kwashe fiye da shekara 20 yana aikata laifuka a kasar.

Tun a shekarar 2013 ne dai aka yi yekuwar neman Evans ruwa a jallo.

Boko Haram: ‘Yan Majalisar Amurka Sun Ziyarci Borno, Sun Tabbatar Da Tallafin Fasaha A NajeriyaDan majalisar kasar Amurka, sanata Christopher Coons, ya tabbatar wa gwamnatin Najeriya da goyon bayan gwamnatin Amurka akan magance matsalar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Sanata Coons wanda ya yi magana da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Talata, 29 ga watan Agusta ya ce sun ziyarci jihar Borno ne don ganin wa idanun su mumunar barnar da ‘yan kuna bakin wake Boko Haram suka haddasa a yankin da kuma kokarin ta yadda amurka za ta hada kai tare da gwamnatin Najeriya don kawo karshen rikicin.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sanatan, wanda ya yi magana a madadin tawagar wakilai daga Amurka wanda jakadan Amurka a Nijeriya ya jagoranci zuwa hedkwatar rudunar sojoji na Operation LAFIYA DOLE wanda ke barikin soja na Maimalari a Maiduguri, sun kuma yaba da kokarin jami’an sojoji da cibiyar gudanarwa game da nasarorin da aka samu a yaki da ta’addanci da ake gudanarwa.

Tawagar ‘yan majalisar kasar Amurka a Maiduguri

Coon ya ce, ” Mun zo ne don nuna goyon bayanmu ga sojojin Najeriya a yaki da ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya. Za mu kara goyon bayan fasahar mu don tabbatar da cewa an kawao karshen wannan rikicin a yankin”.

Yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar, babban kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya ce ziyarar wakilai na Amurka ta na matukar amfani don nuna yadda Amurka ke nuna goyon baya a kan rikicin ta’addanci a arewa maso gabas.

Kwamandan ya lura cewa Amurka ta ki sayar da kayan makamai ga Najeriya a baya bayan rashin amincewa da gwamnatin mai mulki a wancan lokacin, amma sun nuna sha’awar yanzu saboda kokarin da gwamnati mai ci yanzu ta nuna a yaki da ta’addanci a kasar.

Al’hakin Mutuwar ‘Yan Fensho Baya Kaina – OkorochaGwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a ranar Talata, 29 ga watan Agusta ya ce jinin wasu ‘yan fensho da suka mutu yayin da suke jiran biyan kudin fensho ba ya kansa.

Wannan ikirarin ya kunshe ne a cikin wata sanarwar babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Sam Onwuemeodo a Owerri, babban birnin jihar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa ya gano wasu makudan kudi na naira miliyan 650 wanda wasu jami’an gwamnati ke shirin sace daga asusun ‘yan fensho kuma yanzu an kama mutane 30 dangane da zamba.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

Kamar yadda ya ce, ” Fiye da ma’aikata 30 a Fensho Board muka mika ga jami’an ‘yan sandan farar hula ta DSS a kan zargin sace kudin ta hanyar littafin kudi na fensho wanda suka shafi naira miliyan 650”.

Littafin kudin fenshon sun kasance 92 tare da wasu daga cikinsu wanda ke dauke da naira miliyan 10 zuwa sama. An gano cewa mutum ɗaya zai iya samu littafin kudi guda 3 ko 4 wanda za a rubuta sunansa da kuma yawancin sunayen da ba na masu karbar fensho ba.

Al’amarin bai yiwa gwamnan dadi ba, ya ce: “Kafin a ba da wanda ake zargi da zamba ga jami’an tsaro wasu ‘yan fensho sun rasa rayukansu sanadiyar rashin biyarsu a cikin lokaci kuma jijinsu zai kasance a kansu”.

Hajj 2017: Alhazan duniya sun fara aikin Hajji a yau


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Maniyyata fiye da miliyan biyu ne ake sa ran za su fara zaman Mina daga ranar Larabar nan, a wani bangare na ibadar aikin hajjin bana tsawon kwana biyar a kasar Saudiyya.

Dubban daruruwan maniyyata musulmi na ta isa Saudiyya daga sassa daban-daban na duniya domin aikin hajjin, ciki har da maniyyatan kasar Iran, bayan sun kauracewa aikin bara saboda turereniyar shekarar 2015 da ta yi sanadin mutuwar maniyyata kimanin 2,000.

Maniyyata na fuskantar kalubalen sauke farali, inda Saudiyya kuma ke fuskantar kalubalen samar da yanayi mafi kyau da ingantaccen tsaro ga maniyyatan.

Abin alfahari

A bana kawai, kasar ta tanadi dakaru fiye da dubu 100 domin tabbatar da tsaro da doka da oda a wuraren da ake gudanar da ayyukan ibada.

Dakaru sun yi atisaye na musammam domin tabbatar da shirin ko-ta-kwana da kuma tunkarar barazanar da ka iya tasowa.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Sai dai, ba batun tsaro ba ne kawai ke damun hukumomin Saudiyyar. Karuwar maniyyata masu isa kasar ya kasance batun da ke daukar hankali.

Saudiyya ta samar da jiragen kasa masu gudu, kuma ta fadada hanyoyi domin rage cunkoso a wurare daban-daban.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Shekaru biyu da suka gabata fiye da maniyyata dubu biyu sun rasu sakamakon turereniya. Kasar Iran ta rasa wasu daga cikin ‘yan kasarta, dalilin da ya sa ta dora wa Saudiyya alhakin lamarin.

A bara Iran ta hana maniyyatan kasarta zuwa aikin hajji, amma a bana sun je. A wani bangaren kuma akwai batun siyasar yankin — inda rikicin Saudiyya da Qatar ya shafi maniyyata daga kasar, wadanda a da har sun fitar da rai ga halartar aikin hajjin a bana.

Ban da wannan kuma akwai batun kiwon lafiya.

Shugaban kungiyar Red Crescent a Saudiyya ya ce sun kammala shirye-shirye tare da ma’aikatar lafiya domin tunkarar barkewar cutuka ko annoba a lokacin wannan aikin hajjin.

Barayi Sun Kai Hari Gidan Man NNPC Sun Raba Kyautar Mai Ga Masu Motoci A KatsinaA daren ranar Asabar, barayi sun rarraba kyautar man fetur ga masu motoci a hanyar Katsina/Jibia bayan barayin sun kai farmaki gidan man NNPC dake a hanyar, sannan kuma suka kwashe cinikin da akayi a gidan man.
Idon shaida ya bayyana cewa al’amarin ya auku ne da misalin karfe 8 na dare.

Idon shaidan ya ce masu motocin sun shiga shan mai ne a lokacin da barayin suka kawo farmakin, barayin sun yi irin shigan jami’an tsaro ne.

Barayi sun kai hari gidan man NNPC sun raba kyautar mai ga masu mota a Katsina

Bayan haka sun kwashe cinikin da akayi a gidan man ba tare da sunyi wa kowa rauni ba.

Idanun shaidan basu san adadin yawan barayin ba saboda yanayin kayan da suka sanya. Yace harin ya dauki ‘’yan mintuna ne.’’

Manema labarai basu kai ga samun mai magana da yawun yansandan Katsina, DSP Gambo Isa ba a lokacin.

Kalli Kyautar Da Sanatocin Amurka Suka Yi Wa Gwamna El-RufaiDa yammacin ranar Litinin 28 ga watan Agusta ne gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya karbi bakoncin wasu yan majalisun dokokin Amurka a garin Abuja.
Cikin wadanda suka kawo ziyarar akwai Sanatocin majalisar dokokin, da kuma yan majalisar wakilan kasar Amurka, inda suka samu jagorancin jakadan kasar Amurka a Najeriya, W Styart Symington.

Kyautar da suka bashi

Siyasarnigeria.com  ta ruwaito musabbabin zuwan tawagar shine neman hanyar kulla alakar kasuwanci daya shafi Ilimi, tsaro, noma, hakehaken ma’adanan kasa da kuma sha’anin lafiya a tsakanin jihar Kaduan da kasar Amurka.

Sanatocin Amurka da gwamna El-Rufai

Daga karshe Sanatan Amurka, Sanata Christopher Coon ya mika ma gwamnan jihar Kaduna El-Rufai wata kyauta, sa’annan ya yaba masa kan yadda yake gudanar da mulki a jihar.

Bayan nan tawagar ta kai ma shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ziyara, tare da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Dalilin Da Yasa Buhari Da Osinbajo Suka Zama Tamkar Ɗanjuma Da Ɗanjummai
Tun bayan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari Najeriya, ake raderadin cewa wai manyan jami’an fadar shugaban kasa sun mayar da mataimakin shugaban kasa Osinbajo saniyar ware.

Sai dai fadar shugaban kasa tayi raddi ga masu yada wannan jita jita, kamar yadda suka bayyana labaran, inda tace wannan wani shiri ne kawai ma makiya gwamnatin shugaban kasa Buhari.

Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC Hausa, inda yace wannan shaci fadi ne kawai, har ma ya kara da cewa abu daya ke raba Buhari da mataimakinsa, shine Sallah.

Garba Shehu ya karyata duk wata majiya mai tushe da ake cewa ta bada bayanai na karkashib kasa game da haka, inda ya kalubalance su idan gaskiya suke nufi, toh su fito su bayyana kansu mana.

“Ko a satin data gabata, sai Osinbajo ya wakilci Buhari a taron bude ayyuka a jihar Taraba a ranar juma’a, inda shi kuma ya tafi Masallaci, ina tabbatar muku cewa Buhari bashi da wani abokin shawara da yafi mataimakinsa Osinbajo.” Kamar yadda Garba Shehu ya shaida ma majiyar Siyasarnigeria.com 

Ku biyo mu a Facebook SIYASARNIGERIA.COM 

Kiwon Lafiya: Tsohon Shugaban Kasa Atiku Ya Tallafa Wa Asbitocin Jihar AdamawaKwamishinan lafiya ta jihar, wanda kuma diya ce ga tsohon mataimakin shugaban kasan, Dakta Fatima Abubakar ce ta bayyana haka a ranar Litinin 28 ga watan Agusta a garin Abuja.

Kwamishiniyar tace Atiku Abubakar ya bada wannan tallafi ne ga asibitoci domin inganta lafiyar jama’a tare da taimaka ma tsarin gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Bindow na fadada aikin inganta kiwon lafiya a jihar.

Atiku

Cikin taimakon da ya bayar akwai GE Brivo, na’urar daukan hoton kashi, da kuma na’urar daukan hoton ciki. Inda tace sakamakon tallafin daya bayar, tuni babban asibitin garin Jada ya inganta.

“Baya da wannan, Atiku ya sanya kayan aikin gudanar da gwaje gwaje don gano cututtukan dake damun jama’a, haka zalika ya samar da wuta mai amfani da hasken rana a asibitin.” Inji Kwamishiniyar.

Daga karshe tace wanann tallafi zai taimaka wajen samar da jama’a dayawa marasa lafiya wadanda zasu samu kulawa a asibitocin gwamnati, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

An Shirya Taron Fadakar Da Manoma Da Makiyayan NijarBazoum Muhammad, ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar

Rikicin manoma da makiyaya babbar matsala ce da ke yawan addabar kasashen nahiyar Afirka, lamarin da kan janyo hasarar rayuka da dumbin dukiyoyi. Hakan ya sa wata kungiya mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar d ake kira FRAPS ta shirya wani taron wayar da bangarorin biyu kan muhimmancin zaman lafiya.

Wata kungiya mai zaman kanta da ke bin diddigin harkar manoma da makiyaya da ake kira FRAPS a takaice, ta shirya wani taron bita da ya tattaro manoma da makiyayan Jmahuriyar Nijar domin a tattaunawa.

Kungiyar ta tattaro bangarorin biyu ne daga jihohin Maradi da Damagaram da Diffa domin kara karfafa dangantakar da ke tsakaninsu ta yadda za a rika kaucewa rikici da kan taso ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi.

A Jamhuriyar Nijar, rikicin manoma da makiyaya, matsala ce da aka sha fuskanta a kasar ta yadda akan shirya taruka daga bangaren gwamnati da kungiyoyi irinsu FRAPS kan kaucewa aukuwar rikici-rikicen.

Mafi yawan rikice-rikicen kan samo asali ne daga batun afkawa gwanakin manoma da makiyaya kan yi dabbobinsu, ko kuma su manoman su yi noma a kan burtalin makiyaya.

Shugaban kungiyar manoma da makiyaya na kasa, Abdu Nino Gajango ya ce maksudin wannan taro shi ne “mu hada su ta yadda za su zauna lafiya, su guji rashin zaman lafiya, su gane cewa ba abu ne mai kyau ba.”

Taron ya gudana ne a jihar Damagaram.

Saurari rahoton wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka Tamar Abari daga Damagaram domin jin karin bayani kan wannan taro:

Yawan Tafiyar Gwamna Ben Ayade Yasa Ma’Aikatan Gwamnatin Jihar Sun Daina Zuwa Aiki​Rashin zaman gwamnan jihar Cross Rivers, Prof Ben Ayade ya durkusar da aikin gwamnati a jihar, saboda ma’aikatan jihar suna barin bakin aikin su, zuwa wajen biyan bukatun su. A binciken da yan jaridar Daily Post suka yi sun gano cewa wasu ma’aikatan kasuwanci suke zuwa yi. Abun da ke faruwa kenan duk lokacin da gwamnan yayi tafiya zuwa Turai.

Yanzu haka, masu aiki karkashin ofishin gwamnan sun bar bakin aikin su, zuwa wajen kasuwancin su. Ofishin gwamna ya zama Kaman makabarta inda babu kowa.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa babu gwamnan da yakai Ben Ayade yawan tafiye-tafiye.Kuma duk lokacin da yayi tafiya sai tattalin arzikin jihar ta samu matsala.

Yawan tafiye tafiyen Ben Ayade yasa ma’aikatan gwamnatin jihar sun daina zuwa aiki

Kungiyan CTRNI ta yi kira da majalissar dokokin jihar cross Rivers da su fara yunkurin tsige gwamnan jihar Ben Ayade saboda yawan tafiya tafiyen da sa, wanda ya saba ka’ida.

A wani taro da kungiyan tayi a Calaba ta ce tun da Ayade ya zama gwamnan jihar yafara tafiye tafiyen banza. A tarihin Najeriya ba a taba samun gwamnan da yakai shi yawan tafiya ba.

Mai kula da harkokin kungiyan , Kwamared Jonathan Agbor, yace ya zama dole majalissar dokokin jihar su tsige Ayade dan saba dokar tafiya, saboda ya mika wa mataimakin sa mulki duk lokacin da zai yi tafiya haka yake barin jihar ba jagora. Da kuma barnatar da kudaden jihar saboda yawan tafiyar sa

Agbor yace “Tunda Ayade ya hau mulki, kwanakin da yayi a Abuja da kasashen waje yafi kwanakin da yayi a jihar sa yawa, yakara da cewa a cikin ranaku 365 da ake da shi a shekara Ben Ayade bata yi kwana dari a ofishin sa ba” .

Gwamnatin Buhari 'ta kai karar mutum 6,646 kotu a shekara daya'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yaki da cin hanci na cikin manyan alkawuran da Shugaba Buhari ya yi

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi karar mutum 6,646 a kotu bisa aikata laifuka daban-daban a tsakanin shekarar shari’a ta 2015-2016.

Wata sanarwa da kakakin ministan shari’a Abubakar Malami, ya aikewa manema labarai ta ce 325 cikin laifuka 1,330 kanane.

Kakakin, Comrade Salihu Othman Isah, ya ce an yanke hukuncin da ya goyi bayan gwamnati kan kashi 90 cikin dari na karar da ta shigar.

Ya kara da cewa gwamnati ta yi tsimin sama da N119 bn da kuma $14bn a cikin wadannan kararraki.

Kazalika, a cewar sanarwar, gwamnati ta hana masu laifi guje wa biyan harajin da ya wuce N10bn wanda ya kamata su biya hukumar kwastam.

“Wadannan kararraki sun hada da na manyan laifukan, ta’addanci, satar mai, kisan kai, fyade, fashi da makami da mallakar makami ba bisa ka’ida ba dai dai sauransu”, in ji sanarwar.

Gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ta dare kan mulki a shekarar 2015, ta sha alwashin yaki da cin hanci da ta’addanci da makamantansu.

Sai dai masu sharhi na ganin har yanzu gwamnati ba ta daure manyan jami’an da ake zargi da wawure kudin kasar ba.

Labari Yanzunnan: Mahajjatan Najeriya 5 Sun Kara Rasuwa A Can Kasar Saudiyya Yayin Aikin HajjiSabon rahoto daga kasar Saudiyya na cewa an sami wasu karin alhazan Najeriya hudu da suka riga mu gidan gaskiya yayin wannan aikin hajji na bana, bayan fitar Muna da aka yi a makon nan, domin haramar hajjin bana.

Labari yanzunnan: Mahajjatan Najeriya 5 sun kara rasuwa a can kasar Saudiyya yayin aikin Hajji

Sanarwar dai ta fito daga hannun shugaban NAHCON, wato hukumar aikin hajji ta kasa, Alhaji Abdullahi Muhammed, wanda ke gaya wa manema labarai a yau talata, cewa an sami labarin rasuwar maniyyata daga Najeriya hudu, kari kan daya da ta rasu a kwanan baya.

Da majiyar NAIJ.COM dai ta tambaye shi ko su waye mamatan, kuma ko me yayi ajalin su? Sai yace wannan bayani bazai fitar ba tukun, har sai an sanar da iyalin mamatan a hukumance.

Da yawa dai da suke zuwa aikin hajji kanyi fatan Allah ya karbi ransu a kasa Manzo, kasa mai tsarki, ko sa gana da ma’aiki. A baya kuma an sami hadurra da dama da suka kashe alhazai ko garin jifan shaidan, ko kuma a hadarin kayan aikin masallacin harami.

atan mu dai, Alhazanmu su dawo gida ga iyalinsu lafiya, da hakorin makka, mamata kuma, Allah kyauta makwanci.

An Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Berkeley Na Jihar Califonia


​Tituna a birnin Berkeley a jihar Califonia dake nan Amurka ya cika makil da dan mutun domin gudanar da zanga-zangar maida martani duk ko da kokarin hana wannan zanga-zangar

Duk da soke zanga-zangar ‘yan ra’ayin rikau, wadda ta janyo zanga-zangar mai da martani, masu zanga-zangar mai da martanin sun cika titunan Berkeley na jahar California jiya Lahadi.

Jiya Lahadi ta zama rana ta biyu a jere da ake ta zanga-zanga a San Francisco Bay. Ranar Asabar masu zanga-zangar mai da martani sun fito da dama don kalubalantar taron masu ra’ayin rikau, wanda aka yi wa taken Taron ‘Yan Kishin Kasa, to amma, shi dinma, an soke shi. Magajin Garin San Francisco ya ayyana nasara kan abin da ya kira kungiya mai yada kiyayya.

‘Yansanda a Berkeley, a tsallaken San Francisco Bay, sun kafa shinge a zagayen wani wurin shakatawa, inda aka shirya yin daya gangamin jiya Lahadi. Hukumomi sun kuma kafa shingayen karafuna da ‘yansanda ke kula da su.

Sai Inda Karfinmu Ya Kare Wajen Taimakawa Al’umar Texas – TrumpShugaban Amurka Donald Trump

Al’umar jihar Texas da bala’in ambaliyar ruwa ya afkawa, na ci gaba da samun tabbaci daga hukumomin kasar kan tallafa masu da za a yi domin su koma rayuwarsu ta da yayin da shugaba Donald Trump ya ce har ya fara magana da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin agaza wa mutanen Texas da Louisiana domin ganin sun samu saukin bala’in da ya auka musu na ambaliyar ruwa.

Shugaba Trump ya shaidawa taron ‘yan jarida a Fadar White House jiya Litinin cewa wadanda wannan lamari ya rutsa da su, su kwana da sanin cewa za su samu taimakon gaggawa nan ba da jimawa daga majilisar dokokin kasa domin samun kudin da suke bukata don kimtsa gidajen su da ruwa ya mamaye.

“Za ku samu duk abinda kuke bukata, kuma cikin gaggawa, na riga har na fara tattaunawa da wasu ‘yan majalisar dokoki, sun kadu da irin halin da ‘yan jihar Texas kuke ciki.” In ji shugaba Trump.

Shi ma shugaban hukumar ba da agajin gaggawa Chief Brock Long ya shaidawa manema labarai a jiya cewa hukumar za ta dauki shekaru tana aiki a Texas.

Long ya ce yanzu haka hukumar ta fara shirin aiki na tsawon lokaci, irin wanda ta jima ba ta yi irinsa ba.

Mene ne bambancin son jima'i tsakanin mace da namiji?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Makalun kimiyya kadan ne suka bayar da tabbacin cewa mutane sun yi ce-ce-ku-ce da muhawara fiye da ikirarin sanin bambancin yadda ake zaburarwar likon alakar kwakwalwar mace da namiji.

Daukacin abin da ake ta kai-kawo a kai su ne dabi’un da ke tattare da tarawar jima’i. Sai dai an sha samun hujjojin da ba su da nagarta imma har ba a yanke cewa daukacinsu shaci-fadi ne.

Haska hoton kwakwalwa da aka yi ya nuna cewa wuraren da ke lailaye da launin toka-toka “mabubbbugar farin ciki” a maza da mata ba su nuna hakikanin sassan sarrafa al’amura da ke cikin kokon kai.

Al’amarin kamar shaci-fadi ne yadda wasu masanan bunkasar kwakwalwa da ke nuni da cewa kwakwalen maza da mata dole suna da mabambantan muhimman kullin alakar, bisa la’akari da bambancin dabi’a.

Ta yiwu ka yi hasashen cewa saboda cunkoson masu tafiya makaranta da safiyar nan, sabanin jiya, tuni da an karkatar da akalar hanyar bisa dole.

Lamarin a bayyane yake ganin yadda wata makala ta bi kadin bambance-bambancen darsuwar tunkarar tarawar jima’i a tsakanin maza da mata da ke da alaka da hakikanin bazuwar tartsatsin sakonni a jijiyoyi.

Saura da me, bayan gano likon alakar da gungun masu bincike na majisalar likitanci da ke da dakin binciken kimiyyar rayuwar halittu a Cambridge da ke Ingila, al’amari ne mai sauki da ke nuni da bijirowar darsuwar jima’i tamkar kunnawa da kashewar bazuwar lantarki; ingiza jijiyoyi su fitar da sinadaran aikewa da sakonnin ankararwa ga jijiyoyi ta wata hanya ga maza, da kuma wata hanyar daban ga mata.

Abin da aka fahimta bai yi nuni da dabi’ar mutum da muke magana akai ba. Sai ma dai a ce an yanka ta tashi.

Abin da ke ingiza darsuwa da daukar al’amura bai daya a jikin wannan da waccan, lamari ne da masu bincike suka yi takatsantsan wajen kauce masa, ko da yake sun yi kwatanceceniya da jaba.

Misali kamar yadda aka fitar da su ta yadda za su dauki hankalin abokin Barbara ko tantance cewa abokin hadin Barbara shi ne na hakika.

Daukacin batutuwan shahararrun mujallu, abin mamakin shi ne, duk abin da suka yi nuni da shi kadan ne aka gano game da sinadaran aikewa da sakonnin tarawar jima’i a mutum.

Sinadarin “steroid androstenone” da ake ce yana daukar hankalin mata idan maza suka fitar da shi, kuma yana ankarar da maza cewa kwayayen mata na bukatar kyankyasar maniyi, amma dai babu wata kakkwarar hujja kan haka.

Mun fahimci cewa dai sakon ankararwar sinadaran tarawarar jima’i ba shi da makama. Akwai wani sinadari na musamman da ake yi wa lakabi da cVA (11-cis-vaccenyl acetate) da ke da maganadisun jawo macen kuda su yi ta soyayya, al’amarin ya hadar da waka da rawa daga nan kawai sai su hada baki da al’aura.

Amma a jikin maza sinadarin cVA tasirin aikinsa akasin haka ne; tauye soyayya, a wasu lokutan ma yakan harzuka musu tada jijiyar wuya, al’amarin da ke nuni da gasar namiji.

Kulla alaka

Abin tambaya a nan shi ne ko mene ne ke haifar da mabambantan salon tunkarar lamarin. A wasu daya daga cikin jinsunan ne ke yin “warin sinadarin jan hankalin jima’i,” saboda yana da managarciyar makarbiyar sinadaran protein da ke shigar da sinadarin ankararwar.

Sai dai akai-akai, sinadarin cVA, wanda ke bijiro da darsuwar dabiar son jima’i a maza da mata irin guda ne, don haka za su iya gano shi, tare da ‘fahimtar’ sauye-sauyen salonsa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ayyukan binciken da suka gabata bambanci kadan suka nuna a tsakanin maza da amta, inda daukacin tartsatsin sakonnin mafi akasari nan take da zarar sinadarin cVA ya bijiro da shi, sannan sakonnin kan yi juyin sadarwa (karo na biyu a tunkudowar tartsatsinsu).

Gregory Jeffens da abokan aikinsa a Cambridge sun gano bambancin da ke tattare a matakin tartsatsin sakonni na gaba wato juyin sadarwa na uku. Bambanci na da ban mamaki kai tsaye; wadannan tartsatsin sakonni kullin alaka ne a hanyoyi daban-daban, wadanda ke ankararwa a wani sashe na kwakwalwar kuda (mai zukar furanni), sabanin turakun tafiyar tarragon jirgin kasa mabambanta.

Samun irin wadannan bayanai na tattare da aiki na kwarewa da jajircewa wajen gwaji a fannin kimiyyar kai-kawon sakonnin jijiyoyi a kwakwalwa.

Masu bincike sun hada hotunan mitsi-mitsin kwakwalwar kuda, al’amarin da ya yi nuni da raunin hanyoyin tafiyar sako guda, wanda ke “juya akalar” ma’aunin tafiyar tartsatsin sakonni a zirin silin jijiya.

Ta haka ne za su iya gano sashen ankararwa a kwakwalen namiji da mace, sannan a nuna bambancin da ke tsakaninsu bayan sun kai ga juyin sadarwar sakonni karo na uku.

Wadanne al’amura suka haifar da bambancin alaka? Jefferis da abokan aikinsa sun danganta ala’amarin da kwayar halitta guda, da ake kira “fruitless – mara-katabus,” wadda masana kimiyya suka san cewa tana da muhimmanci a dabi’ar namiji.

Kwayar halittar ke tattare bayanai game da sinadaran proteins, sannan masu bincike sun nuna cewa samar da wadanann sinadaran proteins a juyin sadarwar sakonni mataki na uku shi ke kulle su a tsarin kwakwalwar namiji.

Da masu binciken suka jirkita wadannan tartsatsin sakonni a kwakwalwar mace sai aka samar da sionadaran proteins, kuma kwakwalwar mace ta kulla alaka da su tamkar ta namiji.

Shin juya wannan gudan sakon sadarwar ya isa yin tasirin sanya mace ta darsu da salon matakin namiji ga sinadarin cVA?

Saura dai a jira a gani, kuma ta yiwu irin wanan juyin-juya halin jinsi na bukatar Karin wasu “su juya irin na namiji” a samu kwaranyar sinadarin darsuwar jima’i.

Amma abin takaici ne a ce a kalla kan al’amarin da ya shafi tarawar jima’i, akwai al’amura karara game da bambancin da ke damfare a tsakanin kwakwalwar namiji da mace.

Shin Ya Kamata Buhari Ya Yi Wa Gwamnatinsa Garambawul?


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a tsakiya sanye da fararen kaya, bayan daya dawo daga jinyarsa ta farko da ya je London a watan Maris din 20

 Najeriya ana ci gaba da kiraye-kiraye kan cewa lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa gwamnatinsa kwaskwarima.

Batun kiraye-kiraye da ake yi na neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a gwamnatinsa na janyo ka-ce-na-ce tun bayan da shugaban ya dawo daga jinya a London inda ya kwashe sama da watanni uku.

Wannan korafi da mutane ke gabatarwa na zuwa ne yayin da gwamnatin ta APC ta kwashe sama da shekaru biyu akan karagar mulki.

A lokacin yakin neman zabe, jam’iyar APC, ta yi alkawarin kawo sauyi daga irin mulkin da ‘yan kasar suka gani a zamanin mulkin babbar jam’iyar adawa ta PDP.

To amma kiraye-kirayen da ake yi na cewa shugaban ya sauya wasu ministocinsa na ci gaba da karuwa.

Yanzu haka kungiyar kwadago ta NLC ta kasa ta shiga jerin bangaren da ke kiran a sauya wasu ministoci domin a cewarta wasunsu babu abinda suka tabuka.

Shugaban kungiyar ta NLC, Comrade Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.

Masana kimiyyar siyasa irinsu Dr. Abubakar Umaru Kari, su ma sun bi sahun wannan kiraye-kirayen, inda ya ce tunda an kwashe shekaru biyu, ya kamata a kawo wasu su ba da ta su gudunmuwar.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin jin cikakken abinda dukkanninsu suka fada:

Arsenal za ta sayar wa da West Brom Gibbs


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dan wasan yana tattaunawa da Watford da kuma Galatasaray

West Brom ta kusa kammala daukar dan wasan Arsenal mai tsaron baya, Kieran Gibbs mai shekara 27.

Arsenal ta amince ta sayar da Gibbs kan kudi fam miliyan biyar, haka kuma dan kwallon na tattaunawa da Watford da kuma Galatasaray ta Turkiya.

Gibbs na bukatar a duba lafiyarsa kafin ya saka hannu kan yarjejeniya.

Haka kuma Arsenal ta bi sawun Manchester City da Leicester wajen zawarcin mai tsaron baya na West Brom, Jonny Evans.

Man City na son daukar Sanchez kafin Alhamis


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An ci Arsenal wasa biyu a karawa uku da ta buga a gasar Premier ta bana

Manchester City na son ta sayi dan kwallon Arsenal, Alexis Sanchez kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai a ranar Alhamis.

Sanchez mai shekara 24, ya ci kwallo 24 a Premier bara, sai dai yarjejeniyarsa za ta kare da Arsenal a badi, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa a Emirates ba.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola na son sayen Sanchez kai tsaye kuma ba tare da ba ta lokaci ba.

Sai da kuma idan Sanchez ya koma City, makomar Raheem Sterling za ta zama kila-wa-kala a kungiyar.

Sterling ya buga wa City wasa uku da ta yi a Premier, amma ba a yi masa alkawarin saka shi a wasa akai-akwai ba, sakamakon sayen Bernardo Silva da ta yi daga Monaco.

BBC ta fahimce cewar Sterling zai so ya koma Landan da taka-leda, idan har Arsenal na bukatar hakan a cikin yarjejeniyar cinikin Sanchez.

City ba ta taya Sanchez ba, amma ana sa ran za ta sayi dan kwallon nan ba da dadewa ba.

Dalilin Da Yasa Fani Kayode, Fayose Suke Son Buhari Ya Mutu-Laureta OnochieHadimin shugabankasan Muhammadu Buhari na kafofin watsa labarai, Lauretta Onochie ta zargi gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da tsohon ministan sufurin jirgin sama Femi Fani Kayode da yiwa shugabankasa fatan mutuwa.

Onochie ta yi ikrarin cewa, Fayose da Fani Kayode wanda jigajigai ne a jam’iyyar PDP, suna burin mutuwar Buhari ne saboda tuhumar da ake musu na sace kudin al’umma

A wani bidyo da aka saka a yanan gizo, Onochie ta ce, “ Mun san makiyan Buhari, su FFK ne, da Fayose da sauran su. Bana tsoron kiran sunayen su. Mun san irin abubuwan da suke fada a kasannan.

Dalilin da yasa Fani Kayode, Fayose suke son Buhari ya Mutu-Laureta Onochie

“Kwanakin baya wani hadimin Fayose, Lere Olayinka ya rubuta a shafin sa na yanan gizo cewa shugabankasa ya mutu.

“Mun san ta inda abubuwan nan suke fitowa kuma mun san dalilin da yasa suke haka, hukuma tana bin su.

“Amma Buhari bai damu da su ba, idan ka karya doka, dole doka ta cika, Wannan shine batu.

“Sunce wai yan jam’iyyar PDP ne kadai ake hukunta wa, dalili shine ba mu a cikin gwamnatin da ta gabata, kuma bamu saci kudi ba, ta yaya hukuma za ta biyo mu.

“Na fada sunayen su kuma bana tsoro. Burin su shine su ji ance ya mutu amma Allah ya fi su.

Jawabin Onochie ya zo ne bayan Buhari ya dawo daga Landan, bayan ya kwashe sama da kwanaki 100 wajen ganin likitocin sa .

Chelsea na daf da daukar Chamberlain


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal ta buga wasa uku a Premier ta bana ta ci karawa daya aka doke ta sau biyu

Dan kwallon Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain ya kusa ya koma kungiyar Chelsea mai rike da kofin Premier da taka-leda kan fam miliyan 40.

A karshen kakar badi ne yarjejeniyar Chamberlain mai shekara 24 za ta kare a Emirates, kuma bai saka hannu kan tsawaita zamansa a kungiyar ba.

Oxlade-Chamberlain bai yanke shawarar kungiyar da ya kamata ya koma ba tsakanin Chelsea ko Liverpool, sai dai Chelsea ce kawo yanzu ta taya dan wasan.

Sai dai Arsenal na fatan kammala sayar da tsohon dan kwallon Southampton din ba tare da ba ta lokaci ba.

Dan wasan ya buga wa Arsenal wasannin Premier uku da ta buga a bana, ciki har da karawar da Liverpool ta ci Gunners 4-0 lokacin da aka cire shi a karawar.

Chamberlain zai zama na biyar da Chelsea ta dauka a bana bayan Alvaro Morata da mai tsaron raga Willy Caballero da mai tsaron baya Antonio Rudiger da mai wasan tsakiya Tiemoue Bakayoko.

Ko Dembele zai taka rawar da Neymar ya yi a Barca?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dembele ya koma Barcelona a matsayin na biyu mafi tsada da aka saya a tarihin tamaula

A ranar Litinin Osmane Dembele ya kammala komawa Barcelona daga Borussia Dortmund a matsayin na biyu mafi tsada da aka saya a duniya kan fam miliyan 135.3.

Barcelona ta dauki dan kwallon ne domin ya maye gurbin Neymar wanda ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 a matakin wadda aka saya mafi tsada a duniya.

Tuni Barcelona ta bai wa Dembele riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a Barca, shin ko Dembele zai taka rawa irin wacce Neymar ya yi?

Ga jerin kungiyoyin da ya buga wa tamaula da kwallayen da ya ci:

 • Cikakken suna:Ousmane Dembélé
 • Ranar Haihuwa:15 May 1997 (age 20)
 • Wurin da aka haife shi:Vernon, France
 • Tsawonsa:1.78 m (5 ft 10 in)[1]

Taka-leda a matsayin matashin dan kwallo

 • 2004-2009Madeleine Évreux
 • 2009-2010Évreux
 • 2010-2015Rennes

Taka-leda a matsayin kwararren dan wasa

 • 2014-2015Rennes II wasa 22 kwallo 13
 • 2015-2016Rennes wasa 26 kwallo 12
 • 2016-2017Borussia Dortmund wasa 32 kwallo 6

Wasanni a tawagar kwallon Faransa

 • 2013-2014 Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 wasa 8 kwallo 4
 • 2014-2015 Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 18 wasa 5 bai ci kwallo ba
 • 2015 Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 19 wasa 3 kwallo 1
 • 2016- Tawagar France ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 wasa 4 bai ci kwallo ko daya ba
 • 2016- Babbar tawagar France wacce ya yi wa wasa 7 ya ci kwallo 1

Shugabanin Yankin Kudu Sun Ki Amince Da Matsayin Buhari Akan Sake Fasalin Tsarin NajeriyaKungiyar shugabanin yankin kudancin Najeriya, SLF, a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta ta bayyana rashin amincewa da matsayin shugaba Muhammadu Buhari a kan kiraye kiraye na sake fasalin kudin tsarin mulkin kasar. Shugabanin sun lura da cewa wannan gyaran zai tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da kuma bunkasa asar.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, shugabannin sun nuna rashin amincewar ne bayan jawabin shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya bayan dawowarsa daga wani hutun kula da kiwon lafiyarsa, sun ci gaba da cewa, gyaran zai taimaka wajen magance matsalolin da ake ciki a kasar yanzu.

Wannan dai ya zo ne a bayan da fadar shugaban kasa a ranar Laraba ta ke gargadi ‘yan Najeriya musamman shugabanni masu bayyana ra’ayoyin su game da sake fasalin tsarin mulkin kasar, cewa shugaba Buhari ba zai iya tilasta sake fasalin tsarin mulkin kasar ga ‘yan Najeriya ba.

Kungiyar shugabanin yankin kudancin Najeriya, SLF

Kungiyar shugabanin kudancin ta bayyana matsayinta a cikin wata sanarw bayan ganawar ta a Legas.

Shugabannin daga kudu maso yamma da kudu maso gabas da kuma kudu ta Kudu sun hada da: shugaban Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, tsohon babban darakta na hukumar ‘yan sandan farin kaya, DSS, Cif Albert Horsfall, shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif John Nwodo, tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo , Farfesa Joe Irukwu, tsohon ministan harkokin kasashen wajen, sanata Ike Nwachukwu, tsohon ministan harkokin watsa labaru da al’adu, Walter Ofonagoro da kuma shugaban kungiyar OPC, Otunba Gani Adams.

Sauran sune Farfesa Adebanji Akintoye, Cif Guy Ikokwu, Mista Denzik Kentebe, Kanal Tony Nyiam (mai ritaya), Cif Supo Shonibare da kuma Mista Tony Uranta.

An gayyaci 'yan Madrid 17 tawagar kasashensu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid ta tashi wasa 2-2 da Valencia a ranar Lahadi a wasan mako na biyu a La Liga

Kimanin ‘yan kwallon Real Madrid 17 aka gayyata tawagar kasashensu, domin zuwa wasan gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 da na ‘yan kasa da shekara 21.

‘Yan wasan da za su buga wa kasashensu fafatawar shiga gasar kofin duniya sun hada da Marco Asensio da Dani Carvajal da Isco da Nacho da Sergio Ramos da Lucas Vazquez.

Sauran sun hada da Cristiano Ronaldo da Luka Modric da Mateo Kovacic da Keylor Navas da Gareth Bale da Casemiro da Marcelo da Toni Kroos da kuma Achraf.

Su kuwa Borja Mayoral da Dani Ceballos za su buga wa Spaniya wasan matasa ‘yan kasa da shekara 21 na sada zumunta da Italiya da na neman shiga gasar Zakarun Turai da Estonia.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na uku a gasar La Liga a ranar 9 ga watan Satumba, kwanaki hudu tsakanin ta buga wasan gasar cin kofin Zakarun Turai da Apoel Nicosia a Santiago Bernabeu.

Koriya ta haraba makami mai linzami ta saman Japan


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda aka tashi da bala’in giftawar makami mai linzami a Japan

Koriya Ta Arewa ta harba wani makami mai linzami ta sararin samaniyar Japan, wani al’amari da Firai Ministan Jaan Shinzo Abe ya ce hakan wata babbar barazana ce da ba a taba samun irin ta ba.

An harba makamin ne a ranar Talata da sassafe agogon Koriya, wanda ya bi ta tsibirin Hokkaido kafin daga bisani ya fada cikin teku.

Ana sa ran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa don mayar da martani kan lamarin.

A baya-bayan nan ne Koriya Ta Arewa ta aiwatar da wasu gwaje-gwajen makamai masu linzami, amma wannan ne karo na farko da ta harba mummunan makami mai linzami ya bi ta samaniyar Japan.

A karo biyu a baya da rokokinta suka bi ta samaniyar Japan a shekarar 1998 da ta 2009, Koriya Ta Arewa ta ce tana kaddamar da tauraron dan adam ne ba makamai ba ne.

Wakilin BBC a Tokyo Rupert Wingfield-Hayes, ya ce ga alama wannan makami na farko da aka harba wanda ka iya daukar makamin nukiliya.

An umarci mazauna kasar su nemi mafaka

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

N Korea’s Japan missile: The key questions

Rundunar sojin Koriya Ta Kudu ta ce an harba makami mai linzamin ne ta gabas kafin karfe 6:00 na safe, wanda ya yi daidai da karfe 9:00 na daren Litinin agogon GMT, daga Pyongyang, babban birnin kasar, wanda ba a cika samun hakan ba.

Wani sharhi da aka yi na farko ya nuna yadda harbin makamin ya kasance:

 • ya yi tafiyar fiye da kilomita 2,700
 • ya yi kama da samfurin Hwasong-12, wani sabon samfurin makami da ba a dade da kera irinsa ba
 • nisansa daga kasa ya kai kilomita 550, wanda hakan shi ne gwajin da ya fi yin kasa-kasa a duk gwaje-gwajen makamin da Koriya ta yi a baya-bayan nan
 • ya fada tekun Arewacin Pacific kilomita 1,180 kusa da gabar tekun Japan, bayan ya ragargaje zuwa gida uku

Japan dai ba ta yi wani kokarin harbo makamin ba amma ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan kasar da ke Hokkaido da su nemi mafaka a gine-ginen da suke karkashin kasa.

Kwanan nan ne dakarun Amurka da na Japan suka kammala wani atisaye na hadin gwiwa a Hokkaido yayin da ake ci gaba da wani atisayen na dubun-dubatar dakarun Koriya Ta Kudu da Amurka a Koriya Ta Kudun.

Koriya Ta Arewa na kallon wannan atisaye na hadin gwiwa da ya hada da sojojin Amurka a matsayin wata tsokana, inda suke ganinsa a wani yunkuri na kai mata hari.

Shugaban kasar Koriya Ta Kudu Moon Jae-in, ya bayar da umarnin dakarun kasar su fito su yi gagarumin atisaye don mayar da martani ga harin. Jiragen yakin Koriya Ta Kudu sun yi ta atisayen harba bama-bamai a ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Firai Minsitan Japan Shinzo Abe ya yi mummunar suka ga harin

Mr Abe ya ce ya yi magana da Shugaba Donald Trump kuma duk su biyun sun amince a kara matsa wa Koriyta Ta Arewa lamba.

Sai dai cibiyar tsaro ta Amurka ta ce wannan hari ba barazana ce ga kasar ba, amma sojoji na aiki don tattara bayanan sirri game da harin.

China ta yi gargadi cewa tashin hankali ya kai kololuwa a yankin Koriya, amma ta ce Amurka da Koriya Ta Kudu ne abin zargi. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron China Hua Chunying, ta soki kasashen biyun da ci gaba da atisayen sojin da suke yi wanda ke zama kamar matsin lamba ga Koriya Ta Arewa.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov, ya ce, kasar ta damu matuka a kan yiwuwar tabarbarwar da lamarin zai yi, amma ya ce atisayen da sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudu ke yi yana kara harzuka Koriya Ta Arewa.

Sharhi: Rupert Wingfield-Hayes, na BBC a Tokyo

Ana ganin wannan ne gwajin makami mai linzami mafi muni da Koriya Ta Arewa ta yi a lokaci mai tsawo. Kwarai jiragen Koriya Ta Arewa na bi ta sararin samaniyar Japan a da, amma wannan ne karo na farko da Pyongyang ta harba makamin nukiliya ta saman Japan.

Sharhin farko da aka yi ya nuna cewa makamin samfurin Hwasong-12, wanda aka fara ganinsa a wani babban faretin soji a Koriya Ta Arewa a watan Afrilu. Daga bisani kuma aka fara harba shi cikin teku a watan Mayu.

Me ya sa Koriya Ta Arewa ta zabi yin hakan a yanzu? Na farko dai tana son nuna jajircewarta. Tana nuna cewa barazanar Amurka ba ta bai wa kasar tsoro, kamar yadda Shugaba Trunp ya fada mako biyu da suka gabata.

Na biyu, Koriya na son sake gwada makamin nata a gwaji na hakika. Na uku irin wannan gwaji na zama matsin lamba ga kawancen Amurka da Koriya. Yana sa Japan na jin rauni sosai yayin da yake kalubalantar jajircewar Amurka.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An yi ta tura wa mutane sakon kar-ta-kwana a Hokkaido ana gaya musu su nemi mafaka


'Buhari ne ya jefa Nigeria a yunwa da talauci'


Hakkin mallakar hoto
PRESIDENCY

Image caption

Shugaba Buhari ya taba cewa ‘yan Najeriya za su dara

Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin kan yadda tattalin arzikin kasar ya fara gyaruwa ne, wasu ‘yan kasar suka fara yi masa raddi musamman a kafofin sada zumunta.

Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

Shugaban ya gana da su ne har tsawon kimanin sa’o’i biyu ranar Litinin, kamar yadda Mataimakinsa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana.

Sai dai masu muhawara a shafinmu na Facebook sun bayyana mabambantan ra’ayoyi kan hakan.

Ga kadan daga cikinsu:

Haruna Suleiman Utono ya ce, “Har yanzu talakan Najeriya bai san da farfadowar tattalin arziki ba. Saboda har yanzu babu abin da ya sauya”.

“To a ina arzikin yake farfadowa bayan kun jefa kasa cikin talauci da yunwa”, in ji Usman Ibrahim

Shi kuwa Abubakar Kawu Girgir yabawa ya yi da kalaman shugaban kasar yana mai cewa Hakika muna godiya da irin kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na ganin ya dawo mana da tattalim arzikinmu”.

Shi ma Abdurahaman Gangarawa cewa ya yi, “Allah Ya sa alheri kan farfadowar tattalin arzikin Najeriya, ya ninninka farfadowarsa, ya ba mu ikon amfana da shi.”

Kotu ta sake mallaka wa gwamnati kudi N7.6bn na Diezani


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana zargin Diezani da sata, zargin da ta sha musantawa

Wata kotun tarayya da ke birnin Laegas na Najeriya ta mallaka wa gwamnatin kasar N7.6bn, kudin da ake zargin tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Madueke ta sace.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati, EFCC ce ta gano kudin a wani banki, inda ta yi zargin cewa tsohuwar ministar ta same su ne ta hanyar da bata dace ba.

EFCC ta ce an ajiye kudin ne a asussa da dama.

Alkalin kotun mai shari’a Abdulaziz Anka ya yanke hukuncin ne bayan da EFCC ta nemi kotun ta mallakawa gwamnati kudin dindindin.

A farkon watan nan ma wata babbar kotun da ke Lagos ta mallaka wa gwamnatin Najeriya kaddarorin tsohuwar ministar man da suka kai $40, wato kimanin naira biliyan 14.

Kotun ta mallaka wa Najeriya wani katafaren gidan Ms Diezani da ke yankin Banana Island da ke Lagos, wanda kudinsa ya kai $37.5m, kimanin naira biliyan 13.

Haka zalika, mai shari’a Chuba Obiozor ya mallaka wa gwamnatin Najeriya naira sama da naira miliyan 84 da kuma sama da dala miliyan biyu, wasu kudaden da aka karba a matsayin na haya na gidan na Banana Island.

A kwanan baya dai kotun ta bai wa gwamnatin kasar damar kwace kadarorin na wucen gadi, bayan hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta nemi kotun ta mallawaka wa gwamnati kadarorin.

Bayan haka ne dai kotun ta ba da umarnin a buga hukuncin a kafafen yada labarai, domin duk wanda ke da wani dalilin da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin na din-din-din ba ya kawo dalilinsa gaban kotun.

A watan Afrilun 2016, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai naira miliyan 593 daga hannun tsohuwar ministar.

Ana zargin ta da sace wa da kuma yin facaka da kudin kasar a lokacin da take ministar man, ko da yake ta sha musanta zargin.

A watan Fabrairun 2017 ma, wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince a halatta tare da mallakawa gwamnatin kasar kudaden da aka samu daga wajen tsohuwar ministar man, Diezani Allison-Madueke.

'Ko Buhari ya tambaye su aikin yi nawa aka samar?'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An sha takaddama a Nijeriya cewa bayanan da hukumomi kan fitar game da ci gaban tattalin arzikin kasar kan saba da yadda rayuwa take zahiri a wajen ‘yan kasa.

Wasu masana tattalin arziki a Nijeriya, sun fara kalubalantar shugaban kasar Muhammadu Buhari game da farin cikin da ya nuna kan bayanin farfadowar tattalin arzikin da ministocinsa suka ce ya yi.

Dr. Nazifi Darma ya ce kamata ya yi shugaban ya tambayi ministocinsa ko mutum nawa aka samarwa ayyukan yi sakamakon ci gaban da suke ikirarin (tattalin arzikin) kasar ta samu. “Ayyuka miliyan nawa aka samar?”

“Kuma game masana’antun da suka durkushe, guda nawa ne suka bude suka ci gaba (da aiki). Kuma me suka sarrafa?”, ya tambaya.

An sha jayayya don nuna cewa alkaluman bunkasar tattalin arziki da hukumomin Nijeriya kan fitar ba sa zuwa daidai da yadda ainihin rayuwar talaka take a zahiri.

Shugaba Buhari ya bayyana farin cikin ne bayan ganawar da ya yi da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da takwaranta na Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele.

Sai dai, masanin ya ce akwai bambanci tsakanin alkaluma na ci gaban tattalin arziki da kuma ainihin yadda rayuwar mutane ta kasance a wannan kasar wanda zai yi daidai da wadannan alkaluma.

Dr. Darma ya kara da tambayar wacce irin raguwa aka samu game da hauhawar farashin kayayyaki idan an kwatanta kan yadda (abin) yake kafin (yanzu)?

“Ta yadda mutane za su samu dama, su iya sayen kayayyaki da sauki, da kuma masu yawa a kan yadda suke saya da kafin shiga matsin tattalin arziki.”

Kimanin shekara biyu kenan da Nijeriya ta shiga wani mummunan matsin tattalin arziki, wanda ya janyo gagarumar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Alhazai 65,000 ne za su sauke farali daga Nigeria


Shugaban hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) Abdullahi Muktar ya ce an kammala kwashe maniyyatan kasar wadanda suka yi rijista ta hannun jihohi kimanin guda dubu 65 ranar Lahadi.

“Ba wani Alhaji jiha yanzu da ya rage duk an riga an kwashe su zuwa Saudiyya,” kamar yadda ya shaida wa BBC ta waya yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya ranar Litinin.

Ya ce adadin alhazan ya dara wanda aka samu bara, don bara alhazai kimanin dubu 61 suka sauke farali.

Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da abokin aikinmu, Haruna Mararabar Jos ya yi da shi idan kuka latsa alamar lasika da ke hoton sama.

Na ji dadin farfadowar tattalin arzikin Nigeria – Buhari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi arin ciki da farfadowar tattalin arzikin Najeriya.

Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

Shugaban ya gana da su ne har tsawon kimanin sa’o’i biyu ranar Litinin, kamar yadda Mataimakinsa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana.

Adesina ya ce sun tattauna batutuwan manofofin kudin kasar da tattalin arziki da dai sauransu.

Shugaban ya kara jadaddawa ministocin da gwamnan CBN da cewa gyara tattalin arziki shi ne babban alkawarin da jam’iyyarsa ta yi wa ‘yan kasar, kamar yadda ya ce.

Adesina ya ce shugaban ya nuna “farin cikinsa da yadda al’amura suke tafiya bayan shekara biyu da tabarbarewarsu.”

Shugaban ya bukaci ministocin da su ci gaba da ba da himma don babban aikin gwamnati shi ne samarwa ‘yan Najeriya saukin rayuwa.

Me kuke son sani kan birnin Awamiya da 'yan Shia'a suka fi yawa a Saudiyya?


Hakkin mallakar hoto
REUTERS/FAISAL AL NASSER

Image caption

Masu fafutika sun ce sama da farar hula 20 da ‘yan bindiga biyar ne suka mutu sakamakon rikicin da ake yi a garin

Birnin Awamiya na Saudiyya shi ne garin da mafi yawan mazauna cikinsa mabiya Shi’a ne, sai dai a baya-bayan nan rahotanni ke nuna yadda ake ba-ta-kashi tsakanin mazauna garin da dakarun kasar.

Me kuke so ku sani game da wannan gari da kuma wainar da ake toyawa a cikinsa?

Bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa birnin Houston Amurka


Hakkin mallakar hoto
Rex Features

Kamar yadda jami’ai a jihar suka nuna Houston na cikin juyayi bayan shaida wata babbar guguwa mai tafe da ruwa a cikin tarihin jihar Texas.

An shaida saukar ruwan sama mai yawan centimita 75, yayin da guguwar hurricane harvey ke ratsawa ta koguna – al’amarin da ya janyo ambaliyar ruwa a kan hanyoyi ya mayar da titunan birnin kamar koguna.

Ana dai hasashen cewa cikin wannan makon a bana yankin zai shaida saukar ruwan sama mai yawa. An rawaito cewa mutum biyar sun hadu da ajalinsu a yayin da kuma jirage masu saukar ungulu ke ciccibo mutanen da suka makale a kan runfunan gine-ginen gidaje.

Daukin da ake kai wa mutanen dai na neman gazawa – wannan ne ya sa mutane ke ta kokari tsira da kansu.

An dai yi kiyasin guguwar hurricane za ta kai girman ma’auni na hudu . To amma daga bisani aka rage girma ma’aunin zuwa guguwa da ke keta dazuzzuka.

Kimanin mutum 2,000 ne aka ceto daga ciki da kuma kewayen Houston – birni na hudu mafi girma a Amurka. Birnin Houston dai na da yawan bil’adama kimanin miliyan shida da dubu dari shidda.

Tuni dai aka janye wani gidan kula da gajiyayyu a Dickson ta jirgi mai saukar angulu zuwa wani waje mai nisan kamar kilomita hamsin (50km) da ke a kudu maso gabashin wajen birnin.

Wannan kuwa ya biyo bayan wasu hotuna da aka warwatsa ta hanyoyin sadarwa irin na zamani a kan yadda tsoffi d ake zaune a gidan gajiyayyu ke neman a kai musu dauki.

Hukumar kula da yanayi da saukar iska ta bayyana cewa al’amarin da ya faru ya zo musu a ba zata. Ana dai ci gaba da shaida barazanar ambaliyar ruwa a wasu yankuna sa’annan har zuwa wannan lokaci akwai yankunan da kaiwa a gare su ke bai wa hukumomi wahala.

Dubban gidaje ne aka yanke musu hasken lanatarki, tun bayan afkuwar wannan al’amari. Da yawa daga makarantu na ci gaba da zama a rufe. Sa’ilin da biyu daga manyan filayen jirgin sama ambaliyar ruwa ta yi makil a cikinsu.

Birnin Houston na cikin matsala- a cewar James Cook na BBC.

A yanzu ruwan sama ya mamaye daukacin birnin -an kulle shaguna da sauran harkokin kasuwanci. An killace hanyoyin mota da a ke bi a cikin birnin. Sa’annan kuma an kulle tasoshin filin jirgin sama – akwai yiwuwar tafiye-tafiye su fuskanci matsala watakila ba masu yiwuwa ba ne.

Bayan ka iwa mutane dauki, an kuma tashi wani asibiti – dab da lokacin da injiniyoyi ke ci gaba da aiki bil hakki don a saki ruwan da ya bakam daga madatsun ruwa biyu.

Ana ci gaba da gargadin masu gidaje da ke makwabtaka a kusa da madatsar ruwa da su kwana da shirin fuskantar ambaliyar ruwa cikin wasu sa’oi masu zuwa.

Wasu daga mazauna wadannan yankuna dai na zaune cikin damara tun bayan da ruwan ya nausa zuwa yankin Gulf a Mexico a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Akwai wani yanki da ke makwabtaka da wadannan yankuna da suka fara shaida ambaliyar ruwa – wasu mutane na cike da fushi tun bayan da aka sanar da su cewa su kaurace yankunansu cikin dare daya.

Wannan dai ya zo a lokacin da ruwan ke tinkaro su da tsanani.

Hukumomi dai na ci gaba da gudanar da ayyukansu To sai dai ana duba ko ta wacce hanyar ce za su samarwa shugaban kasar Donald Trum muhalli a daidai lokacin da ayke shirin kai wata ziyara jihar Texas a Talatan nan. In har shugaba Trump y ace zai ci gaba da kai ziyara birnin to lalle idanunsa za su gane ma sa yadda birni mai arzikin mai ya zama abin tauayi

Anya ana samun saukin kawar da ambaliyar ruwan?

Za a ce babu alama. Bisa la’akari da yadda ruwan mai tafe da guguwa ke ci gaba da ragargazar kudu maso gabashin Texas. Sa’annan ruwan na ci gaba da tumbatsa kuma ke nausawa zuwa Houston.

Magajin garin Houston Sylvester Turner, ya fadawa mazauna birnin cewa, ‘Kar ku yi gaggawar kusantar hanyoyi birnin. Kar ku yi tunanin cewa wannan guguwa ta zo kuma ta wuce.’

Dubban mutane ne da aka umarce su da su bar yankin Fort Bend kamar tsawon kilomita hamsin da biyar kudu maso yammacin Houston – wani yanki da ake tinanin kogunan yankin za su cika su batse.

Kawo wannan lokaci hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a game da shirin janye mutane daga yankin ba.

Kome ya sa basu bayar da sanarwar ba?

Magajin garin Turner a wannan Lahadin da ta gabata ya kare kansu daga shirin da aka yi na kwashe mutum kimanin miliyan biyu da dubu dari uku.

Ya bayar da misali da abin da ya faru a Houston a yayin da aka dauke mazauna yankin a dab da lokacin da mahaukaciyar guguwar Hurricane ta sauka a watan satumba a shekara ta 2005.

Mutane sun makale sama da sa’a 20 a kan hanyoyi ba tare da an kai musu dauki ba. Hakan ya haifar da mutuwar gomman mutane.

Ana dai hasashen cewa guguwar Rita za ta nausa zuwa Houston ta tsallaka zuwa gabashin birnin.

Masu kula da al’amura dai na bin bahasin yadda aka yi jigilar mutane ta hanyoyin da ba su dace ba kafin saukar mahaukaciyar guguwar Hurricane Katrina da ta ci yankin Nw Orleans a cikin watan Agustar da bala’in ya sauka.

Dubban mutane sun yi zaman wahala a wani yanayi da suka fuskanci karancin ruwa.

Wacce illa guguwar Harvey za ta yi ga tattalin arzikinsu?

Yankin gabar tekun Texas wani bangare ne mai muhinmanci ga harkokin man fetur da isakar gas a kasar Amurka. Dalili kuwa wasu daga manyan matatun man fetur da ke a jihar Texas sun dakatar da ayyukansu.

Wannan na haifar da damuwa bisa la’akari da cewa zai jefa al’ummar kasar cikin matsalar karancin man fettur da kuma tashin farashin man fetur.

Ana dai ci gaba da kiyasta hasarar da guguwar mai tafe da ruwan sama ta haifar.

Kwararru a kan harkokin Inshora kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, suna cewa babu mamaki wannan bala’i ya kasance wani mafi girma da Amurka ta taba shaidawa.

Idan akayi la’akari da cewa guguwar Katrina ta haifar da hasarar kimanin dala biliyan 15 da ambaliyar ta haifar a jihar Liousiana.

Magoya bayan Barca na son shugabanta ya sauka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A bana ne Real Madrid ta doke Barcelona 5-1 gida da waje a Spanish Super Cup

Bikin gabatar da sabon dan kwallon da Barcelona ta saya, Ousmane Dembele ya ci karo da cikas, bayan da magoya bayan kungiyar suka yi ta rera wakokin neman shugabanta ya yi ritaya.

Dembele mai shekara 20, ya zama na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin tamaula a duniya kan fam miliyan 135.5, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain da murza-leda kan fam miliyan 200.

Bikin ya ci karo da cikas bayan da aka yi jinkirin sa’a biyu, sakamakon rashin samun takardun rijistar dan kwallon daga Dortmund.

A lokacin ne magoya bayan Barcelona 18,000 suka rinka busa usur da rera wakokin cewar Bartomeu ya yi ritaya.

Mahukuntan Barca na shan matsi kan yadda kungiyar ke koma-baya a wasanninta da kuma sayar da Neymar da aka yi zuwa PSG.

Taron bikin bai kai yawan magoya bayan Barcelona 50,000 da suka tarbi Neymar a Nou Camp a shekara hudun da suka wuce ba.

Liverpool ta sayi Keita mafi tsada a tarihi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sai a ranar 1 ga watan Yulin 2018 Keita zai koma Anfield da taka-leda

Liverpool ta amince ta sayi dan kwallon Leipzig, Naby Keita a matsayin mafi tsada a kungiyar, amma sai a ranar 1 ga watan Yunin 2018 zai koma Anfield.

Liverpool ta yadda ta biya fam miliyan 48 kudin da Leipzig ta gindaya idan yarjejeniyarsa ba ta kare da kungiyar ba, kuma zai koma Anfield da taka-leda a badi.

Jurgen Klopp ya dade yana zawarcin Keita daya daga cikin ‘yan kwallon da ya so ya saya a bana, amma Leipzig ta ki amince wa ya bar Jamus a bana.

Kudin da Liverpool za ta sayi Keita ya dara fam miliyan 35 da kungiyar ta dauko Andy Carroli daga Newcastle United.

Liverpool za ta taya Lemar fam miliyan 60


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Thomas Lemar ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasa biyar

Liverpool na shirye-shiryen taya dan kwallon Monaco, Thomas Lemar kan fam miliyan 60 kafin a rufe kasauwar saye da sayar da ‘yan wasan tamaula a ranar Alhamis.

Jorgen Klopp ya dade yana bibiyar wasan Lemar mai shekara 21, amma har yanzu Liverpool ba ta tuntubo Monaco ba kan cinikin dan wasan.

Sayan Lemar da Liverpool ke son yi, bai shafi makomar Philippe Coutinho a Anfield ba.

Liverpool ta ki sallama tayi uku da Barcelona ta yi wa dan kwallon Brazil da kudi ya kai fam miliyan 114.

Barcelona ta kammala sayen Dembele


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ta gabatar da Dembele a gaban magoya bayanta a Nou Camp a ranar Litinin

Barcelona ta kammala daukar Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 96.8 daga baya zai kai fam miliyan 135.5 idan aka hada da tsarebe-tsarabe.

Dan wasan mai shekara 20 dan kwallon Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Nou Camp a gaban shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu a ranar Litinin.

Dembele shi ne na biyu da aka saya mafi tsada a tarihin kwallon kafa a duniya, bayan Neymar wanda ya koma Paris St Germain daga Barcelona kan fam miliyan 200.

Barcelona ta ce ta gindaya kudi fam miliyan 400 ga duk kungiyar da ke son sayen dan kwallon idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Nou Camp.

Dembele zai saka riga mai lamba 11 wacce Neymar ya yi amfani da ita a Barcelona.

Dortmund ta maye gurbin Dembele da Yarmolenko


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yarmolenko ya koma Dortmund domin ya maye gurbin Dembele

Borrusia Dortmund ta dauki Andriy Yarmolenko kan yarjejeniyar shekara hudu, domin ya maye gurbin Ousmane Dembele wanda ya koma Barcelona da taka-leda.

Yarmolenko mai shekara 27 wanda ya buga wa Dynamo Kyiv wasa 228 daga tsakanin 2008 zuwa 2017 ya ci mata kwallo 99, ya sauka a Signal Iduna Park filin wasa na Dortmund.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Ukraine wanda ya fara buga wa tamaula tun yana da shekara 19, ya yi mata wasa 68 kuma ya ci kwallo 29 kawo yanzu.

Dambele ya koma Barcelona kan fam militan 135.5 a matsayin wanda ta dauka mafi tsada a bana, kuma na biyu da aka saya kudi da yawa bayan Neymar da ya koma PSG daga Barcelona.

Ban mayar da Osinbajo saniyar-ware ba — Buhari


Hakkin mallakar hoto
Presidency

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce mataimakin Shugaba Buhari na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, kuma ba a mayar da shi saniyar-ware ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.

Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buharin ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, bayan da wata jarida ta ce tun bayan dawowar Shugaba Buhari daga jinya wasu daga cikin ‘yan fadarsa da suka yi baba-kere sun ware Farfesa Osinbajo inda ba a damawa da shi a harkokin gwamnati.

“Wannan magana karya ce da jita-jita, maganganu ne marasa tushe da ake kirkiro don ganin an shiga tsakanin wadannan shugabanni masu kwazo,” in ji sanarwar.

“Wannan maganar ba abar kamawa ba ce, a ce daga dawowar shugaban kasar cikin mako guda har an fara batun ware mataimakinsa cikin harkokin mulki.

“Abin da nake so a sani shi ne, shi Mr Osinbajo shi ne mutum na kut-da-kut ga shugaban kuma mashawarcinsa na musamman.”

Malam Garba Shehu ya kara da cewa, cikin mako guda da ya gabata bayan dawowar Shugaba Buhari, Farfesa Osinbajo ya halarci tarurruka daban-daban a madadin shugaban, ‘in ban da sallar Juma’a.’

Ya kuma yi nuni da cewar masu yada wannan kalamai na karya suna danganta batun ne da cewa Shugaban Ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari, shi ne yake yin ruwa da tsaki wajen gabatar da al’amura a fadar, da kuma kin shigar da Farfesa Osinbajo cikin al’amuran gwamnati.

“Babu wani shugaban ma’aikata ciki kuwa har da shi Abba Kyari, da zai aikata irin wannan abu sannan kuma ya ci gaba da kasancewa kan kujerarsa. Wannan mukami ba ya bukatar yada irin wadannan karairayin,” in ji Garba Shehu.

Ya kara da cewa a lokacin da Shugaba Buhari yake jinya a London, ya bai wa Mr Osinbajo goyon baya sosai, “don kuwa ya san maigidansa Shugaba Buhari ba zai so wani abu mara dadi ya faru ba.”

Hakkin mallakar hoto
Presidency

Image caption

Fadar shugaban kasa ta ce ana kokarin kawo rarrabuwar kawuna ne tsakanin manyan na hannun damar Shugaba Buharin biyu

“Ni ina ganin Abba Kyari na samun matsala da mutane ne saboda yana son ubangidansa sosai, ba zai dinga bai wa mutane kudi kawai don ya faranta musu rai ba.

“A takaice ma Abba Kyari kudi ba sa gabansa, don ya ki karbar naira miliyan 200 da ake bai wa ofishinsa duk wata don tafiyar da al’amura. Don yana ganin ba a bukatar wannan makudan kudin don tafiyar da al’amuran ofishin nasa,” a cewar Garba Shehu.

Dama dai ko a karon farko da SHugaba Buhari ya tafi jinya Birtaniya, an sha yada maganganu irin wadannan da ke cewa wasu ‘yan fadar shugaban kasar ba goyon bayan mataimakin shugaban, yayin da wasu kuma ke cewa suna hakan ne don Mr Osinbajon ya fi Shugaba Buhari iya rike mulkin kasar.

Ina Kan Bakana Kuma Ba Zan Nemi Gafarar Buhari Ba – Inji FayoseGwamna na jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa maganganunsa da kuma matsawa ya yi sanadiyar dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar da ta gabata.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Fayose, wanda yake jawabi ga shugabannin jam’iyyar PDP a ofishinsa, ya ce yana kan bakansa da duk abinda ya yi ikirari game da shugaban kasa a ranar 6 ga watan Yuli, ya kara da cewa ba shi da nadama ga duk abin da ya fada a wancan lokacin.

Gwamnan wanda ya sake kira ga shugaba Buhari ya yi murabus, ya ce:

“Idan ba don kokarin mu ba Buhari ba zai dawo yanzu ba. Buhari bai da isashen lafiya na shugabancin kasar kuma yana bukatar komawa gida ya hutawa”.

Gwamna na jihar Ekiti, Ayodele Fayose

“Gaskiyar al’amarin ita ce, matsa lamba daga gare ni da kuma sauran ‘yan Najeriya yasa shugaban ya dawo gida. Sun ki bayyana asalin ciwon da shugaba Buhari ke fama da, sun manta cewa rayuwar shugaban kasa wani abu ne da ya kamata ‘yan Naajeriya su sani”, inji Fayose.

Ya ce, “ Fadar shugaban kasa ta soke zaman taron majalisar zartarwa ta tarayya. Ba za ku iya ɓoye gaskiyar har abada ba, zai bayyana da kansa wata rana. Ba za ku ci gaba da yaudari ‘yan Najeriya ba”.

Fayose ya ci gaba da cewa, “ Abin da nake faɗar ita ce, yana da sha’awar cewa muna da shugaban kasa wanda yake da ƙarfin gudanar da aikinsa”.

Likitocin Arewa Sun Kafa Tarihi, Sun Yi Nasarar Yankawa Wata Yarinya Gurin Fitar Da KashinIta dai wannan yarinyar kamar yadda majiyar mu ta bayyana cewar kasantuwar larurar da aka haife ta da ita hakan yasa take fitar da kashi da fitsarin ta duka a ta hanya daya wanda kuma hakan na da matukar illa a gare ta.

Likitocin arewa sun kafa tarihi, sun yi nasarar yankawa wata yarinya wurin fitar da kashin

NAIJ.com dai ta samu cewa likitocin da suka yi wannan gagarumin aikin sun hada da tsohon kwamishinan lafiya na jihar Zamfara mai suna Dakta Sa’ad Idris da kuma Dakta Suleiman Zakariya da kuma wasu daga cikin malaman asibin ta Ogoja.

An dai ruwaito cewa aikin ya dauki wasu yan awannin kafin a gama shi kuma wata kungiya ce da ba ta gwamnati ba ta dauki nauyin sa domin taimakawa mata masu yoyon fitsari da kuma matsaltsalu irin watannan.

Rikicin Shugabanci Ya Barke A Tsakanin Wasu Masoya Shugaba Buhari​Jim kadan bayan da rikicin ya barke sai aka ga yan sandan Najeriya sun zagare babban ofishin kungiyar rike da bingigu dake a kan hanyar Kubwa suna yi wa bankagorin biyu magana inda ake neman sasanta su.

Rikicin shugabanci ya barke a tsakanin wasu masoya shugaba Buhari

NAIJ.com dai ta samu cewa wasu jiga-jigan kungiyar da suka hada da Alhaji Danladi Pasali da kuma Alhaji Isa Bayero sune suke ta jayayya akan shugabancin kungiyar tun tale-tale.

To sai dai majiyar mu ta samu labarin cewa rikicin ya sake fitowa fili ne a kwanan nan bayan da bangaren Alhaji Danladi suka rufe babban ofishin lokacin da suke son yin taro da manema labarai game da dawowar shugaba Muhammadu Buhari.

Kashedi! Yanzu Haka Sojin Najeriya Na Bibiyar Abunda Kuke Yadawa A Dandalin Sada ZumuntaBabban daraktan yada labarai na rundunar sojin Majo Janar John Eneche shine ya shaidawa gidan Talabijin na Channels hakan inda yace sun yake shawarar yin hakan ne don kawo harshen kalaman harzuka mutane da wasu keyi.

NAIJ.com ta samu kuma cewa wannan jawabin nasa ya zo ne kimanin kwanaki biyu kacal da shugaba Muhammadu Buhari yayi game da masu son yin kalaman batanci da kuma tada-zaune-tsare a kasar.

Majo Janar Enenche haka kuma sai ya sake bayyana cewa wannan abu ba wani sabo bane don kuwa a ko ina a duniya jami’an tsaron kasar kan bibiyi yadda yan kasar ke anfani da shafukan sada zumuntar su domin tabbatar da doka da oda da kuma samun dawwamammen zaman lafiya.

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Matsayinsa A Kan Sake Fasalin Kudin Tsarin Mulkin NajeriyaSarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya shawarci ‘yan Najeriya su sauke kira don sake gyara kudin mulkin Najeriya da kuma mayar da hankali akan al’amurra da zasu hada kai al’ummar kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Sultan na Sakkwato ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta a lokacin bikin bude taron koli na kasa wanda kungiyar ma’aikatan Najeriya, NLC ta shirya a kan sake fasalin kudin tsarin mulkin Najeriya.

Sultan ya ce: “Yana da kyau a zauna a tattauna kuma dole ne a girmamawa juna. Dole ne in girmama ku kuma dole ne ku girmama ni. Kuma mafi girma abin da za mu iya yiwa wannan ƙasar shine yana kyau koyaushe mu yi la’akari da tarihin mu”.

Sarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar

“Domin ba mu fado daga sama ba, mun zo daga wani wuri ne. Mun zama ‘yan Najeriya a shekara ta 1914 ta hanyar haɗin gwiwa. Wasu mutane suna ta maganganu cewa haɗuwar mu a matsayin kasa daya a shekarar 1914 kuskure ne, amma Allah ba ya kuskure. Idan Allah bai so irin wannan abu ba kamar yadda aka kafa Najeriya, babu wanda zai iya yin hakan”, in ji Sultan.

Har ila yau, sultan ya bukaci kungiyar NLC da su kasance a gaba a kan batutuwa da suka shafi kasar.

Sarkin musulmi ya ce yawancin kungiyoyi daga arewa, yammacin, kudu maso kudu da kuma kudu maso gabas suna matsawa don a sake gyara kudin mulkin kasar, suna da matsayin su.

Niger : Ambaliyar ruwa ta yi barna a Yamai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ambaliya ruwan sama a Niamey jumhuriyar Niger

Mutane 16 sun mutu daga watan Yuni zuwa yanzu sanadiyar ambariyar ruwan sama a birin Yamai na jumhuriyar Nijar.

Hukumomin kasar sun yi kira ga jama’ar da ke zaune a kewayen wuraren da ruwan sama ke wa barazana da su gaggauta barin gidajensu.

Ruwan saman da ake yi kamar da bakin kwarya, ya sa an samu mummunar ambaliya a wasu unguwani na birnin, ganin cewa jama’a sun yi gine-gine a kan tsoffin magudanan ruwa.

Bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin na Yamai, wadanda masana kimiyya suka kiyasta cewa, yawan ruwan ya haura milimita 100 , kwatankwacin sama da inci 4, kuma ruwan ya zuba ne a cikin sa’o’i kalilan.

Hakan ne ya hadasa ambaliyar da ta yi sanadiyar faduwar wasu gidaje a ranar Asabar a wasu shiyoyi na birnin Yamai, inda har wani magidanci da dan sa suka rasa ransu.

A yanzu haka gidaje da dama da aka gina a kan tsofaffin magudanan ruwa a wasu unguwani kamar Guntu Yena, da suke bakin kwazazaben kogin kwara wato gulbin Isa -Fleuve Niger, sun cika makil da ruwa, inda su ke fuskantar hadarin faduwa.

Ruwan saman ya yi sanadiyyar rusa da gidaje sama da 300 tare da jikkata mutane da dama a kauyen Gabagura da ke yammacin birnin na Yamai.

Yanzu haka mutane da dama na fakewa wa ne a cikin azuzuwan wasu makarantun boko.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ambaliyar ruwa a Niger

Tuni dai mahukunta a birnin na Yamai, su ka yi kira da babbar murya ga wadanda ke zaune har yanzu a wuraren da ke fuskantar ambaliyar da su tattara na su ya na su su bar wuraren.

Rahotanni sun sanar da cewa tun farkon damunar bana zuwa yanzu, adadin mutanen da suka mutu a hukumance, sanadiyar ambaliyar ruwa a fadin kasar ta Nijar , sun kai mutun 41, kuma sama da 68, 000 ne lamarin ambaliyar ya shafa.

A bara kuma a dai-dai wannan lokaci, ambaliyar ta kashe mutum 50, tare da tagayyarar wasu 145, 000, musaman a yankin Tahaoua da Agadez, duk da cewa yankunane na hamada masu kekasashshen yanayi.

Kenya ta haramta amfani da leda


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jakar leda matsale ce

A fadin kasar Kenya, an haramta amfani da leda.

Dokar haramcin za ta fara aiki ne daga yau Litinin, kuma duk wanda aka kama da jakar leda zai ya bawa aya zakinta.

Wannan haramci ya shafi masu sarrafa ledar a kamfanoni da masu sayarwa ga jama’a da ma jama’ar da ake sayarwa ledar domin saka kaya ko kuma yin wata bukata ta daban.

Daga wannan lokaci , yin mu’amala da ledar a kasar ta Kenya zai sa mutum ya fuskanci tarar da za ta kai dala 38 ko kuma yi zaman wakafi har na tsawon shekaru 4 tare da yin aikin karfi.

Ministan ma’aikatar kare muhalli a kasar, Judy Wakhunghu, ya sanar da cewa, wannan haramci zai taimaka gaya wajen kare muhalli.

To sai dai wani hanzari ba gudu ba, masu sana’ar ledar da ke sarafata a kamfanoni da kuma masu sayarwa ga jama’a, sun ce wannan haramci zai sa dubban mutane su rasa aikin yi a.

Kazalika sun shigar da kara a babbar kotun kasar domin kalubalantar matakin da gwamnatin ta dauka.

To amma kotun ta yi watsi da karar da suka shigar a gabanta .

Akwai dai kasashen da suka haramta amfani da ledar kamar Rwanda da kuma Eritrea.