Trump ya sallami mai ba shi shawara Anthony Scaramucci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori daraktan sadarwa na fadar White House Anthony Scaramucci kusan kwana goma bayan an nada shi kan mukamin.

Mr Scaramucci ya sha suka bayan ya bukaci wani dan jarida ya caccaki abokan aikinsa.

Shugaban ma’aikatan Shugaba Trump Reince Priebus da kakakinsa Sean Spicer sun bar aikinsu ne bayan an nada Scaramucci.

Sabon shugaban ma’ikatan Mr Trump John Kelly ne ya dauki matakin korar Scaramucci bayan an rantsar da shi ranar Litinin.

Wata sanarwa mai layi uku da aka fitar daga fadar White House ta ce: “Anthony Scaramucci zai sauka daga mukaminsa na daraktan sadarwa na White House.

“Mr Scaramucci yana ganin zai fi kyau ya bai wa shugaban ma’aikata John Kelly damar kafa tawagarsa. Muna yi masa fatan alheri.”

Tsohon daraktan sadarwar ya sha yin takama cewa yana bin umarnin shugaban kasa ne ba na shugaban ma’aikatansa ba.

Nigeria: 'Ba za mu daina neman mai a Borno ba'


Hakkin mallakar hoto
NNPC Facebook

Image caption

Ma’aikatan jami’ar Maiduguri da na kamfanin NNPC na aiki ne dan gano arbarkatun kasar da ke yankin tafkin Chadi

Shugaban Jami’ar Maiduguri Farfesa Ibrahim Njodi ya ce suna tare da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) game da neman danyen mai da ake yi a tafkin Chadi bayan wani hari da masu tada kayar baya suka kai kwanakin baya.

Farfesa Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da Karamin Ministan Man Fetur din kasar Dokta Ibe Kachikwu da kuma wasu manyan jami’an NNPC suka kai masa ziyara a karshen makon jiya.

“Al’ummar jami’ar nan sun damu bayan harin da aka kai wa masu aikin neman mai ciki har da wasu ma’aikatan jami’ar. Amma ba za mu janye daga aikin neman man ba. Muna tare da kamfanin NNPC don a koma a ci gaba da aikin neman,” in ji farfesan.

Har ila yau, kamfanin NNPC ya ba da tabbacin cewa za su taimaka wa iyalan wadanda harin ya shafa da kuma jami’ar.

Hakazalika kamfanin ya ce za su ci gaba aikin neman mai a yankin.

A makon jiya ne kamfanin ya ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace masu binciken mai guda goma da suke masa aiki a jihar Borno.

Rahotanni sun ce sakamakon kwantan baunar da kungiyar ta kai, mutane fiye da 40 ne suka mutu da suka hada da sojoji da kuma ‘yan sintiri.

An kama mutum uku da laifin kisan daliban Jami'ar Fatakwal


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kashe daliban ne saboda zargin sata

Wata babbar kotun da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ta kama mutum uku da laifin kisan dabilan Jami’ar Fatakwal hudu ta hanyar kona su da wuta.

A shekarar 2012 ne aka kona daliban a kauyen Aluu, lamarin da ya sa aka yi wa batun lakabi da Aluu 4.

An kashe Ugonna Obuzor, Toku Lloyd, Chiadika Biringa, da Tekena Elkanah, bayan an zarge su da laifin yin sata a Aluu, ranar biyar ga watan Oktoban 2012.

Batun dai ya jawo suka sosai a kasar, inda aka rika kiraye-kirayen yi wa daliban adalci.

Alkalin kotun Mai shair’a Nyordee ya kuma wanke hudu daga cikin mutanen da aka zarga da kisan daliban.

A cewar alkalin, masu shigar da kara ba su iya gamsar da kotu kan laifin da ake zargin mutanen hudu da aka wanke ba.

Sai dai ya ce “mutane uku na farko na da laifi dumu-dumu kan kisan daliban.”

Masu sharhi a kasar dai na ci gaba da korafi kan yadda ake kwashe shekara da shekaru ba a yanke hukunci kan wasu shari’u ba.

'Liverpool ba za ta sayar da Coutinho ba'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona na son ta maye gurbin Neymar da Coutinho

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba za su sayar da Philippe Coutinho ga Barcelona duk da zawarcin da take yi wa dan wasan ba.

Klopp ya ce Liverpool ba kungiyar sayar da ‘yan wasa ba ce, bayan da ake rade-radin cewar ta ki sallama tayin fam miliyan 72 da aka yi wa dan wasan tawagar Brazil.

Coutinho shi ne kyaftin din Liverpool a karawar da ta ci Hertha Berlin 3-0 a wasan sada zumunta a ranar Asabar.

Ana sa ran dan kwallon zai buga fafatawar da Liverpool za ta yi da Bayern Munich a gasar Audi Cup a ranar Talata.

Man United ta kammala sayen Matic


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matic ne na uku da United ta dauka a bana

Manchester United ta kammala daukar Nemanja Matic daga Chelsea kan kudi fan miliyan 40 kan yarjejeniyar shekara uku.

Matic mai shekara 28, shi ne na uku da United ta dauka a bana, bayan mai tsaron baya Victor Lindelof daga Benfica kan fam miliyan 31 da mai cin kwallo Romelu Lukaku kan fam miliyan 75 daga Everton.

Mourinho ya taba sayen Matic kan fan miliyan 21 daga Benfica a Janairun 2014 zuwa Chelsea.

Manchester United za ta buga Uefa Super Cup a karawar da za ta yi da Real Madrid a ranar 8 ga watan Agusta.

Me kuke son sani game da shirin YouWin?


Hakkin mallakar hoto
Facebook/YouWin

Image caption

Toshon shirin YouWin dai ya taimaka wa matasa wajen kafa sana’o’in kai-da-kai. Ko me kuke son sani game da sabon shirin yanzu?

A shekarun baya gwamnatin Najeriya ta bullo da wani shiri na tallafa wa matasa masu son kafa sana’o’in kai-da-kai, inda ta taimaka musu da miliyoyin nairori. A yanzu kuma gwamantin kasar ta sake dawo da shirin. Me kuke son sani game da shi?

NNPC: Muna tare da ma'aikatan Jami'ar Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
NNPC Facebook

Image caption

Ma’aikatan jami’ar Maiduguri na kamfanin NNPC na aiki ne dan gano arbarkatun kasar da ke yankin tafkin Chadi

Kanti BaruHakkin mallakar hoto
NNPC Facebook

Image caption

Ma’aikatan jami’ar Maiduguri na kamfanin NNPC na aiki ne dan gano arbarkatun kasar da ke yankin tafkin Chadi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya ce zai yi duk abin da zai iya don ganin ya tallafa wa Jami’ar Maiduguri da iyalan mutanen da mayakan Boko Haram suka sace a makon da ya gabata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ndu Ughamadu, ya fitar ta ambato babban jami’i mai kula da sashen ayyukan iskar gas da makamashi na kamfanin NNPC Injiniya Sa’idu Mohammed, yayin ziyarar da ya kai a karshen makon jiya, na cewa sun kasance manyan abokan aiki da jami’ar Maiduguri tsawon shekaru.

Ya kara da cewa, kuma tabbas duk lokacin da al’amari irin wannan ya faru, a cikin irin wannan hali, ba za su gudu su bar abokansu ba.

Sanarwar ta ambato shugaban jami’ar Maiduguri Farfesa Ibrahim Njodi na alkawarta ci gaba da aiki da kamfanin NNPC wajen binciken makamashin da ke jibge a yankin tafkin Chadi duk da harin baya-bayan nan na ‘yan ta-da-kayar-baya da ya ritsa da ma’aikatan jami’arsa.

A cikin makon jiya ne rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kubutar da ma’aikatan binciken, kafin daga bisani ta nemi afuwa kan abin da ta ce kuskure a bayanan da ta bayar.

Ta ce ya zuwa lokacin dakarunta sun gano karin gawawwakin soja biyar, da ‘yan kato da gora su 11 da kuma gawawwakin jami’an binciken man fetur guda biyar.

Sanarwa ta ci gaba da cewa ba a ji duriyar “mutum shida cikin ma’aikata 12 da suka fita aikin binciken ba, amma ma’aikacin kamfanin NNPC 1 ya kubuta, in ji ta.

Tuni dai mukaddashin shugaban Nijeriya, Yemi Osinbajo ya bukaci dakarun sojin kasar su ceto ragowar ma’aikatan binciken da aka sace, bayan an ga wasu uku a hoton bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar.

Bangare guda kuma, babban hafsan sojin Najeriyar, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya umarci kwamandan rundunonin da ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, Manjo Janar Ibrahim Attahiru da ya kamo shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a mace ko a raye.

Hafsan sojin ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya aike wa manema labarai, inda ya kara da cewa an bai wa kwamandan kwanaki 40 kacal ya kawo jagoran kungiyar ta Boko Haram.

A halin da ake ciki dai, sojojin sun yi kwana tara cikin 40 din da aka deba musu na gudanar da wannan aikin.

Kuma ‘yan Najeriya sun zuba ido dan ganin ko hakan mai yiwuwa ce, ganin ko a farkon hawan shugaba Muhammadu Buhari karagar mulki, ya bai wa sojojin kasar wa’adin watanni bakwai su kawo karshen kungiyar Boko Haram amma har yanzu ba a kai ga nasarar murkushe su ba.

Kun san wanda ya mari matarsa don ta fadi sunansa a karon farko?


Miliyoyin mata a kasar Indiya ba su taba fadar sunayen mazajensu ba, wannan wata hanya ce ta nuna da’a da biyayya ga mazajen. Sai dai kuma a halin da ake ciki masu fafutuka na kokarin sauya wannan dabi’a ta hanyar sanya matan fadin sunan miji a karo na farko.

Wannan al’ada dai an fi yinta a yankunan karkara, duk da cewa ana samun kalilan daga cikin matan birane da ke amfani da al’adar. Amma yanzu wasu masu fafutuka na kokarin sauya matan karkara ta hanyar sanya su fadar sunan miji a karon farko.

Abin tambayar shi ne me ye a cikin sunan?

Idan har ke ‘yar Indiya ce, kuma mutumin da ake maganar sunansa a kai ya kasance mijinki ne akwai tarin kalubale wajen fadar sunansa. Na kuma gane hakan ne tun ina karama.

Iyayena sun yi aure shekara 73 da ta wuce, amma a bara mahaifina ya rasu. A lokacin da suka yi aure, mahaifiyata ba ta kai shekara 11 ba, mahaifina kuma 15.

Tun da suka yi aure, suna zaune ne a wani dan karamin kauye da ke arewacin jihar Uttar Paradesh, daga bisani kuma ya zama Kolkata, tsawon lokacin da suka yi tare ba ta taba kiransa da sunansa ba.

A duk lokacin da take magana da mu ‘ya’yanta ba ta taba fadar sunan babanmu sai dai ta ce ”babuji” – da harshen Hindu hakan na nufin ”uba”. Sannan a duk lokacin da take magana da shi sai dai ta ce ”Hey ho”, hakan na nufin ”Ji mana”.

A lokacin da muka fara girma, muka kuma fahimci abin da ta ke nufi ko da yaushe muna tsokanarta da yin dariya kan yadda ta ke kiran babanmu. Akwai lokacin da muka shirya mata gadar zare don dai ta fadi sunansa ko da sau daya ne, amma sam ta ki fada.

Haka sauran matan da ke gidanmu kai har da makwabta, sam ba sa fadar sunan mazajensu. Haka ya ke ga miliyoyin mata a kasar Indiya ba sa fadar sunan mazajensu, abin kuma babu ruwansa da banbancin addini ko al’ada ko shiyyar da ka fito.

Hakan bai rasa nasaba da yadda aka dauki miji kamar wani Ubangiji a kasar Indiya, kuma yarinya tun tana karama ake dorata kan tarbiyyar girmama miji.

A kan fadawa mace idan tana fadar sunan mijinta, wani bala’i zai iya fada mata sannan shi kansa mijin ba zai yi tsawon rai ba. Ba sunansa ne kadai ya haramta mace ta saya ba, har da sunan surukanta. Kuma idan har ta fadi sunansa, hakan yana nufin ta gayyato bala’i da musiba ga iyalanta.

Akwai wata mace da ta fito daga yammacin jihar Orissa, da ta gamu da fushi da Allah-wadai saboda fadar sunan mijinta da ta yi.

Wata mace mai suna Malati Mahato, ta shaidawa masu shirya fina-finan sa kai na wata kungiya mai fafutukar ganin an sauya dabi’ar sakaya sunan miji cewa: ”Wata rana, kanwar mijina ta tambayi wa ye zaune a wajen gida, sai na fada mata sunayen mazajen da ke wajen ciki har da sunan kawun mijina”.

Hakkin mallakar hoto
Video Volunteers

Ai kuwa sai kanwar mijin ta kai kararta wajen dagacin garinsu, ai babu bata lokaci aka kore ta daga kauyen baki daya, har da ‘ya’yanta aka kai su can wani kebantattacen wuri a kauyen da ake kai mutanen da suke aikata babban zunubi, kuma mutane su kai mata tofin Allah-tsine. Ta kwashe wata 18 ita da ‘ya’yanta a wurin.

Farfesa A R Vasavi, daya daga cikin masu fafutukar kawo karshen al’adar ko rage ta ya yi karin haske kan yadda ake kallon mijin aure a al’adar kasar Indiya.

“Ka san a Indiya ana kallon miji kamar wani Ubangiji, dan haka dole a bauta masa. Sannan al’ada ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hakan, ana kallonsa a matsayin wanda iyalai suka dogara da shi, wajen ciyarwa da tufatarwa da dauke dukkan lalurorin iyali.

Shi ne mai karfin fada aji a cikin iyali, dole abi shi a kuma yi masa biyayya”.


Sunayen da mata a Indiya suke kiran mazajensu ba tare da sun ambaci sunansa ba

 • Mata kan kira mazajensu da sunan ”Uba”, ko su kira shi da sunan ”Baban wane/wance” a cikin ‘ya’yansa, su kan kuma kira shi da aikin da y ke yi misali idan likita ne ”dakta sahib”, idan kuma lauya ne su kira shi da ”vakil sahib”, da sauransu.
 • Idan suna son yin magana da shi, sukan ce ”Ji mana”, ko kuma ”kai”, ko su ce ”ji mana”, ko kuma ”ka na ji na”.
 • A wasu yankunan Indiya sukan kira miji da sunan ”dan uwa”, ko ”babban yaya”, ko idan za su yi magana da shi su ce ”ina magana”, da sauransu.

A halin da ake ciki masu daukar hotunan bidiyo na sa kai, suka fara wani gangami a wasu kauyukan Indiya, don ganin ko za su iya rage al’adar .

A watan Oktobar da ya gabata wata ma’aikaciyar sakai mai sunan Rohini Pawar wadda ke zaune a kusa da wani kauye da ke yammacin birnin Pune, ta tayar da maganar rage al’adar sakaya sunan miji, a wani taro da aka shirya na mata zalla don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi matan.

Amma kafin ta gabatar da maganar, sai da ta fara gwadawa da kanta.

Pawar ta shaidawa BBC cewa, an yi mata aure tana da shekara 15, kuma cikin shekara 16 da ta yi a gidan aure ba ta taba fadar sunan mijinta Prakash ba.

Farkon aurensu tana kiransa da sunan ”baba”, saboda ‘ya’yan ‘yan uwansa haka su ke kiran sa. Wasu lokutan ta kan kira shi da suna ‘aaho”, ma’ana ‘kai’ da yaren Marathi na kasar.

Prakash ya na jin dadin yadda ta ke kiran sunansa, amma kuma sauran mutanen kauyen ba su so hakan ba.

Hakkin mallakar hoto
Video Volunteers

Image caption

Rohini Pawar: Mutane na yawan tambayar ko me ya sa muke kiran sunan haka?

Matan da suke tattaunawa a kan batun sun yi na’am da wannan sauyi.

“A ranar mun yi dariya, mun yi raha da junanmu. Ko wacce ka kalla tana cike da farin ciki. A karon farko a rayuwarmu mun fadi sunayen mazajenmu duk da a tsakaninmu abin ya faru, amma dai akwai annashuwa kan hakan,” in ji Pawar, tana kuma kyalkyata dariya.

“Sai kuma muka kunna abin daukar hoton bidiyo, muka umarci ko wacce mace ta fadi sunan mijinta cikin yanayi guda uku: yanayin soyayya, da bakin ciki da kuma farin ciki.”

“Daya daga cikin matan, ta koma gida cike da nishadi, ai tana ganin mijinta sai kawai cikin zumudi ta fadi sunansa, ba kuma tare da bata lokaci ba ya falla mata mari.”

”Ya kuma ce idan ta kuskura ta kara fadar sunansa, sai ya lakada mata duka.”

Hakkin mallakar hoto
Video Volunteers

Lamarin ba haka ya ke ba a cikin birane, don ba wani abu ba ne dan mace ta fadi sunan mijinta, wanda hakan ga matan da ba su waye ba ko kuma da ba ‘yan boko ba su ke kallo a matsayin babban zunubi.

Da alama a hankali al’adar fadar sunan miji na dan raguwa tsakanin matan karkara, musamman wadanda ke cudanya da wasu mutanen na birane.

Wata ma’aikaciya ta ce mijin da ta aura abokin aikinta ne, kuma ta dade tana kiran sunansa don haka ba ta ga dalilin da zai sa yanzu da suka yi aure za ta daina fadar sunansa ba.

Amma duk da haka farfesa A R Vasavi, ya ce har yanzu wasu mutanen ba lallai sai a kauyuka ba su kan sakaya sunan mazajensu.

Rohani Pawar ta ce duk da cewa miliyoyin mata na ci gaba da al’adar kin fadar sunan miji, kuma a kan samu sauyi a wasu wuraren na fadar haka, ba a zuwa ko ina idan sabuwar amarya ta fadi sunan mijinta uwar mijin da sauran dattijan gida suke taka mata burki, ba kuma za ta sake fadar sunan ba.

“Akwai matukar wahala a kawo sauyi a lokaci daya, mutane na yawan tambayar mata wai menene dalilin da ya sa muka nace kan lallai sai an fadi sunan miji? Ko akwai wata boyayyar manufa kan hakan? ”

A ganina idan ana son kawo sauyi, ana farawa ne daga batutuwa masu sassauci zuwa manya.”

Akwai jan aiki matuka, kafin a cimma nasarar abin da ake son sauyawa.

Join the conversation – find us on Facebook, Instagram, Snapchat and Twitter.

Tsawa ta kashe mutane 11 a India


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

India ta shafe shekaru da dama bata ga irin wannan yanayi na damuna ba

A kalla mutane 11 ne suka mutu bayan tsawa ta fada kan u, a jihar Odisha da ke Indiya.

Mutanen na aikin noma ne a yayin da ake kwarara ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Jami’ai sun ce wasu mutum 15 kuma sun samu rauni.

An shiga wani yanayi na damina gadan-gadan, inda ake da rahotannin da ke cewa hakan ya jawo matsaloli da dama a wasu jihohin daban, wanda ya kai ga lalacewar tituna da layukan wutar lantarki.

Daminar ta yi sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka shafe shekaru rabon da a ga irinsa.

Rahotanni sun ce kusan mutum 700 ne suka rasu a wannan daminar, yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu.

Cristiano Ronaldo zai gurfana a gaban kuliya kan haraji


Hakkin mallakar hoto
AFP

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo zai bayyana a gaban kuliya nan gaba a birnin Madrid domin ya bayar da bahasi kan tuhumar sa da ake yi da zamba cikin aminci wajen biyan haraji.

Masu shigara da kara dai na zargin Ronaldo, wanda shi ne mai rike kanbun gwarzon dan kwallon duniya, da kin biyan harajin da ya kai dala miliyan 17.

Sai dai kuma dan kwallon ya yi watsi da wannan zargi.

Idan dai har aka samu dan wasan dan asalin kasar Portugal da laifi kan abin da ake tuhumarsa da shi to zai iya fuskantar zaman gidan kaso.

Ronaldo, mai shekara 32, shi ne na baya-bayan nan a jerin ‘yan wasan da hukumomi a Spaniya ke tuhuma kan batun haraji.

A kwanakin baya ma wata kotu ta samu dan kwallon Barcelona Lionel Messi da laifin kin biyan haraji, inda aka yanke masa hkuncin daurin shekara biyu.

Sai dai an mayar da hukuncin tara kamar yadda wani shashi na dokar kasar Spaniya ya tanada.

‘Yan wasa da dama dai na fuskantar tuhumar kin biyan haraji a kasar ta Spaniya, abin da wasu ke dangantawa da rashin kyawun tsarin tattara haraji na kasar.

Me ya sa matan Boko Haram ke son komawa wurinsu?


Hakkin mallakar hoto
ADAOBI TRICIA NWAUBANI

Image caption

Mijin Aisha, wanda kwamanda ne a kungiyar Boko Haram, ya yi ta bata toshin kayayyaki masu tsada

A jerin wasikun da ake aiko mana daga nahiyar Afirka, Adaobi Tricia Nwaubani, wadda’yar jarida ce ta duba yadda matan da dakarun Najeriya suka ceto ke komawa ga masu tsattsaurar ra’ayin da suka sace su.

Bayan an samu labarin cewa wasu ‘yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram suka sace a shekarar 2014 sun ki komowa ga iyayensu tare da wasu 82 da aka ceto a watan Mayu, duniya ta yi matukar mamakin wannan abin.

Hatta wani faifan bidiyo ya nuna ‘yan matan, sanye da hijabai, kuma dauke da makamai suna cewa ba za su koma gida ba, duniya ta gasgata batun mai ban mamaki, inda wasu suke ta cewa: “Ta yiwu an dai tirsasa su ne kawai.”

Har ila yau, wasau cewa suke “ba su iya gane abin da ya sa wata mace za ta so ta kasance da miyagun maza”

Hakazalika, akwai wasu matan da sojojin Najeriya suka ceto da ke komawa dajin Sambisa, bisa radin kansu – Sambisa ita ce maboyar mayakan Boko Haram din da suka sace su tun farko, wato a arewa maso gabashin Najeriya.

‘Rayuwar tatsuniya’

A watan Junairu, na gana da Aisha Yerima, mai shekara 25, wacce Boko Haram suka sace fiye da shekara hudu da suka gabata.

A lokacin da take hannun mayakan, ta auri wani babban kwamandansu, wanda ya nuna mata kauna sosai, tare da bayar da toshin kayayyaki masu tsada, har da rera mata wakoki yake da harshen Larabci.

Labarin da ta ba ni kan rayuwar Sambisa, tamkar wata tatsuniya na ji, kafin dirar da sojojin Najeriya suka masu yayin da mijinta ya fita yaki da sauran kwamnadojin kungiyar.

A hirar mu ta farko da Aisha, tana hannun gwamnati har tsawon wata takwas, domin a sake mata tunani kan akidar da aka cusa mata, cikin wani shiri da wata likitar kwakwalwa Fatima Akilu ke gudanarwa, karkashin gidauniyarta Neem.

Aisha ta ce min, “Yanzu na gane cewa duk abubuwan da Boko Haram ke gaya mana karya ce kawai,”

Ta kara da cewa, “Yanzu idan na ji su a rediyo sai kawai in yi dariya.”

‘Giyar Mulki’

A watan Mayu, kasa da mako biyar bayan sojoji sun mayar da ita hannun iyayenta a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriyar, sai ta koma maboyar Boko Haram din.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Sojojin Najeriya ta fara fafatawa da kungiyar Boko Haram a shekarar 2009

Dokta Fatima ta shafe shekaru biyar tana aiki da ‘yan kungiyar Boko Haram, ciki har da yaransu da matansu da kwamandojin kungiyar, da daruruwan mata da aka ceto daga hannunsu.

Dokta Fatima ta ce, “yanayin da ko wace macce ta samu kanta a hannun Boko Haram, ya danganta ne da irin sansanin da ta tsinci kan ta a ciki.”

Ta kara da cewa, “Wadanda ke samun kula mai kyau, su ne wadanda suka amince da auren ‘yan kungiyar, ko kuwa sun shiga ne da kan su, amma kuma irin su basu da yawa, domin yawancin su ana yi musu ne kamar yadda ake yi wa kowa.”

Aisha ta bayyana mini yawan bayin da take da su a lokacin da take dajin Sambisa, da kuma daukakar da ta samu a hannun kwamandojin kungiyar, haka kuma irin yadda ta mallaki mijinta.

A cewar Aisha, har ta taba yi masa rakiya zuwa yaki sau daya.

“Yawancin ire-iren wadannan mata ba su taba wani aiki ba a rayuwarsu, ba su da wata daraja tsakanin al’ummarsu, sai kawai kwatsam ya zamana suna da iko da mata sama da 30 har zuwa 100 da ke mana bauta,” in ji Dokta Fatima.

A cewar Dokta Fatima, abin da ya sa ke nan matan ba su iya zama idan an ceto su, saboda ba za su iya samun wannan ikon tsakanin al’ummarsu.

Boko Haram ta sako ma’aikatan NNPC

‘Yadda Boko Haram ta raba mu da mazajenmu’

Mayakan Boko Haram ‘700 sun mika wuya’

‘Yanayin kaduwa’

Baya ga tube rigar mulki, a cewar Dokta Fatima, babban abin da ya sa matan ke komawa wajen Boko Haram shi ne wariya da kyama da suke fuskanta a tsakanin al’umma, wadanda ke tsangwamarsu saboda alakarsu da kungiyar, inda suke shigar da su cikin wani yanayi na kuncin rayuwa.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wasu iyayen na fama da takaicin sace ‘ya’yan nasu har yanzu

Dokta Fatima ta ce, “Akwai batun cire musu tsattsaurar akidar da aka cusa masu, a daya bangaren kuma shi ne samar masu karbuwa kuma tsakanin ‘yan uwansu. Wasun su ba su da wata madogara a rayuwa.”

Ta kara da cewa, “Irin tsarin taimakon cire akidar da ake yi baya binsu idan sun bar hannun mu. Sai su yi nasara samun lafiya a shirin na mu, amma da zarar sun koma gida, sai su shiga wani kangin rayuwa tsakanin al’ummarsu.”

Adaobi ta ce, kwanan nan na kai wa ‘yan uwan Aisha ziyara, wadanda har a wannan lokacin ke cikin kaduwa, saboda tafiyar ta, kuma suna cikin damuwa game da halin da take ciki.

Mahaifiyarta mai suna Ashe, ta ce ta tuna da wasu ‘yan mata da Boko Haram suka aura, da suka koma hannun mayakan a dajin Sambisa, da dadewa kafin Aishar, ta kuma san wasu daga cikinsu.

Ashe ta ce, “Duk sanda daya daga cikinsu ta bace, sai iyayenta su zo wajen Aisha suna tambayarta ko ta ji daga garesu,” ta ce “Ta haka ne na sani.”

Wasu daga cikin ‘yan matan sun ci gaba da yin waya da Aisha, ko bayan komawarsu hannun Boko Haram, inda kanwarta Bintu ma ta ce sau biyu tana shaida hakan.

Rayuwa ta cigaba

Ba kamar sauran matan Boko Haram din da na hadu da su ba, da ke fama da mummunar yanayin rayuwa cikin tsangwama da kyama, Aisha ta samu ni’ima wajen ci gaba da rayuwarta.

Ta kama sana’ar kasuwancin atamfofi, kuma tana yawan zuwa bukukuwa inda take yawan wallafa hotunan ta a shafukan sada zumunta, inda take kurewa adaka, kuma take samun masu kyasawa da dama.

“Akalla mutane biyar ne suka neme ta da aure,” in ji mahaifiyar Aisha, inda ta jaddada cewa babu abin da ya fi hakan nuna samun karbuwa tsakanin al’umma, haka kuma a cewarta hakan ya tabbatar da cewa diyarta ba ta fuskanci wata tsangwama ba.

“Daya daga cikin masoyan nata ma mazaunin Legas ne, kuma har tana tunanin aurensa,” in ji Ashe.

Amma kuma duk komai sai ya watse, bayan da ta ji labarin cewa mijinta dan Boko Haram ya auri wata mata da suke kishi da ita.

Daga nan ne Aisha ta yi tutsu, ita da aka sani da shiga jama’a, sai ta koma tana boye kan ta.

Kanwar ta Bintu ta ce, ta koma ba cin abinci, ba magana, sai kullum ta zauna cikin kunci.

Bayan makwanni biyu ta gudu daga gida, da wasu ‘yan kayayyakin ta.

Aisha ta kashe wayoyinta, ta kuma dauki dan ta namiji da ta haifa tare da mijinta kwamandan Boko Haram, a dajin Sambisa, amma kuma ta bar babbar diyarta mace da ta haifa tare da tsohon mijinta, kafin Boko Haram su sace ta.

Cire masu akidar tsattsaurar ra’ayi na da sarkakiya, saboda har yanzu ana fama da tarzomar.

“An fi samun sauki idan har aka samu daidaito tsakanin kungiyoyin ta’addan da gwamnatin kasar, inda har suka amince da su mika wuya su ajiye makamai.” in ji Dokta Fatima.

Ta akara da cewa.”Matsaslar idan akwai iyaye ko mazaje da ‘ya’ya maza da ke ci gaba da rikicin, to sai ka ga suna bukatar komowa da iyalansu, musamman matansu.”

Asta, wata matar ‘yan Boko Haram ce, kuma ta shaida min cewa yawancin matan na komawa ga kungiyar, amma ita ba ta da bukatar yin haka.

Amma ‘yar shekara 19 da ta bayyana min yadda take matukar kewar mijinta, da kuma yadda take bukatar shi da kuma komawa a gareshi.

Amma kuma ta ce ita ba za ta koma dajin Sambisa ba, ko da an bukace ta da hakan, sai dai ya zo su zauna tsakanin al’umma tare.

Sai dai kamar Aisha, akwai yiwuwar bukatar ganin mijin nata ya mamaye tunaninta, har ya sha gaban cewa kungiyar ce ke da alhakin dubban mutane da suka rasa rayukansu a arewa maso gabashin Najeriya, da kuma rasa muhallan miliyoyi, haka kuma a yanzu suka jefa wasu dama cikin mummunar hali a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Hakkin mallakar hoto
ADAOBI TRICIA NWAUBANI

Image caption

Adaobi Tricia Nwaubani ce ‘yar jaridar da ta yi wannan bincike

'Yan sanda sun kama masu luwadi 42 a hotal a Legas


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan sandan sun ce su na gudanar da bincik akan mutumin da suke tsare da shi

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a Najeriya ta ce ta kama wasu maza guda 42 da ake zargi da luwadi.

An dai kama mutanen ne a wani hotel, bayan da rundunar ta kai wani samame sakamakon samun bayanan sirri kan abun da mutanen ke aikatawa.

Yanzu haka rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kuliya ranar Litinin.

Neman jinsi guda a Najeriya dai abu ne da ya saba wa al’ada da addini ‘yan kasar.

Auren jinsin guda kuma ya haramta a dokar kasar, tun lokacin da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya rattaba hannu kan hakan.

Sai dai wasu masu rajin kare hakkin ‘yancin bil’adama na cikin gida da waje na sukar irin matakan da hukumomi ke dauka kan masu luwadi da madigo.

Saudiyya ta saki matar da ta yi wa doka karan-tsaye


Image caption

Sarki Salman na Saudiyya

Rahotanni daga Saudiya sun ce an sako matar nan mai fafutuka, wadda ke adawa da kasancewar mace karkashin kulawar namiji ko maharrami, bayan ta shafe fiye da kwana dari tana tsare.

An dai ce an sako Maryam Al-Otaibi ne ba tare da ta gabatar da wani namiji mai kula da ita ba, abin da mata da yawa masu rajin kare hakkin dan Adam suka yi maraba da shi.

An kama ta ne bayan ta bar gidan mahaifinta domin yin zaman kanta.

A farkon shekaran nan ne sarki Salman na Saudiya ya bayar da umurnin yin gyara ga dokokin zama da muharrami.

Dokar dai tana tilastawa mata a kasar ne neman izinin maza wurin gudanar da akasarin harkokinsu na yau da kullun da suka hada da yin bulaguro zuwa wata kasa.

Arsenal ta sake lashe Emirates Cup


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal ta lashe Emirates Cup duk da rashin nasara da ta yi a hannun Sevilla

Kungiyar Arsenal ta sake lashe Emirates Cup na bana, duk da rashin nasara da ta yi a hannun Sevilla da ci 2-1 a wasan karshe da suka fafata a yammacin Lahadi.

Sevilla ta ci kwallo ta hannun Joaquin Correa da kuma Steven N’Zonzi, ita kuwa Arsenal ta zare daya ta hannun Alexandre Lacazette wanda ta dauko a bana daga Lyon.

Arsenal ta ci kofin na bana duk da doke ta da aka yi, bayan da dokar wasan ta ce yawan cin kwallo shi ne yawan maki.

Sevilla ta fara cin RB Leipzig daya mai ban haushi da kuma doke Arsenal 2-1, ita kuwa Gunners ta cin Benfica 5-2, sannan ta yi rashin nasara a hannun Sevilla.

Saboda haka Arsenal ce ta daya a kan teburi da kwallaye shida, sai Sevilla ta biyu biye da ita.

Arsenal za ta kara da Chelsea a Community Shield a Wembley ranar 6 ga watan Agusta, daga nan ta fara buga gasar Premier da Leicester City kwana biyar tsakani.

Real Madrid za ta yi wasa shida a Agusta


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid ce mai rike da kofin Zakarun Turai da na La Liga a kakar da ta kare

Da zarar Real Madrid ta kammala wasannin atisayen tunkarar kakar bana da take yi a Amurka, za ta mayar da hankali wajen lashe kofi biyu da suke gabanta a Agusta.

Real za ta buga wasan sada zumunta da fitattun ‘yan wasan da suke buga gasar Amurka a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta, kuma shi ne na karshe da za ta yi sannan ta koma Spaniya.

Daga nan ne Real Madrid za ta kara da Manchester United a UEFA Super Cup a Macedonia a ranar Talata 8 ga watan Agusta.

Kwanaki biyar tsakani Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan farko a gasar Spanish Super Cup, wanda ake karawa tsakanin Zakaran La Liga, Real da na Copa del Rey, Barca.

Barcelona za ta halarci Santiago Bernabeu a gumurzu na biyu a ranar 16 ga watan Agusta a gasar ta Spanish Super Cup.

Daga nan Real za ta fafata a wasan farko a gasar La Liga a ranar 20 ga watan Agusta da Deportivo La Coruna, sannan ta buga karawar mako na biyu a gida da Valencia a ranar 27 ga watan.

Enyimba ta hada maki uku a kan Pillars


Hakkin mallakar hoto
LMCNPFL

Image caption

Enyimba ta ci Kano Pillars 1-0 a wasan mako na 32 a gasar Firimiyar Nigeria

Kungiyar Enyimba ta ci Kano Pillars daya mai ban haushi a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 32 da suka kara a yammacin Lahadi.

Enyimba ta ci kwallon ta hannun Mfon Udoh a bugun fenariti saura minti 19 a tashi daga fafatawar.

Ga sauran sakamakon wasannin mako na 32 da aka yi:

 • Katsina Utd 2-2 ABS FC
 • Remo Stars 0-1 MFM
 • Plateau Utd 2-0 3SC
 • Gombe Utd 0-0 Lobi
 • Abia Warriors 0-0 FCIU
 • Nasarawa Utd 1-0 Tornadoes
 • El-Kanemi 1-0 Akwa Utd
 • Wikki 2-1 Sunshine Stars

Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya


Wasu kayatattun hotuna daga sassan nahiyar Afirka daban-daban da kuma na wasu sassan duniya a makon jiya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yar wasan tennis daga Najeriya Adetayo Adetunji wadda tauraruwarta take haskawa ta doke takwararta Zeel Desai ta Indiya ranar Jumaa’a a gasar matasan kasashen renon Ingila da ake yi a kasar Bahamas. ‘Yar wasan mai shekara 18 ta doke abokiyar karawarta ta Ghana Miriam Ibrahim a zagaye na biyu, sai dai daga baya ta fita a lokacin da ta kai matakin kusa da karshe.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani wurin gyaran mota a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, an baje-kolin kayayyakin motoci domin sayarwa a wajen wurin ranar Litinin. Kasuwanci dai na habaka a kasar tun bayan da dakarun kungiyar kasashen Afirka da sojojin gwamnati suka fitar da mayakan sa-kai daga yankin.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wasu masunta a kogin Nilu na birnin Alqahira a kasar Masar, suke kamun kifi ranar Juma’a.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wani mai goyon bayan jam’iyya mai mulki a kasar Kenya (Jubilee Party) ya sanya hoton fuskar Shugaba Uhuru Kenyata ya yin yakin neman zabe a Nairobi ranar Juma’a – ranar 8 ga watan Agusta ne za a yi babban zabe a kasar.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Wadansu mutane suna tafiya kusa da wani bango da wani mai zane-zane Solomon Muyundo ya yi rubutu kan bukatar wanzar da zaman lafiya a wata unguwa da Nairobi a kasar Kenya ranar Lahadi.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wadansu magoya bayan kasar Kongo suna rera taken kasar a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny, a Abidjan babban birnin Ivory Coast ranar Lahadi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Masassaki, Kaba Abdoulaye na kasar Guinea, yana sassaka gunki a birnin Abidjan, inda yake sa ran sayar wa masu sha’awar wasanni da suka kawo ziyara kasar ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mai dakinsa Aisha Buhari (daga dama), da mai dakin gwamnan jihar Benue (daga hagu) a Landan, a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnoni a gidan da yake jinya wato Abuja House ranar Laraba, inda yake jinya karo na biyu a bana.

An fara jigilar alhazai a Nigeria


Hakkin mallakar hoto
WHATSAPP

Image caption

Akwai kimanin alhazai dubu 60 da za su je Kasa-Mai-Tsarki don sauke farali a bana

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta ce ta fara jigilar maniyya aikin hajjji bana a Najeriya inda alhazai suka fara tashi daga shiyyar Abuja ranar Lahadi.

Shugaban Hukumar Alhazai Abdullahi Muktar shaida wa BBC cewa “an yi sahun farko daga Abuja inda aka kwashe alhazai 480 da misalin karfe 3:16 na ranar Asabar.”

Akwai kimanin alhazai dubu 60 da za su je Kasa-Mai-Tsarki don sauke farali a bana, kamar yadda ya ce.

Har ila yau ya ce ana sarar kammala jigilar hajjazan ne a ranar 20 ga watan Agusta.

Ya ce adadin zai iya karuwa saboda yadda har yanzu ake ci gaba da karasa biyan kudin a jihohin kasar.

“Don haka kofa a har yanzu kofa a bude take ga duk wanda bai kammala biyan kudin hajjin ba,” in ji shi.

Man United na daf da sayen Nemanja Matic


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan ne karo na biyu da Jose Mourinho zai sayi Nemanja Matic

Manchester United ta kusa daukar dan kwallon tawagar Serbia mai wasan tsakiya, Nemanja Matic daga Chelsea mai rike da kofin Premier.

Matic mai shekara 28, shi ne dan kwallo na uku da zai koma United a bana, bayan da ta sayi mai tsaron baya Victor Lindelof daga Benfica da mai cin kwallo Romelu Lukaku daga Everton.

‘Yan wasan da kocin United, Jose Mourinho ke bukata sune mai raba kwallo tun daga tsakiyar fili da gwanin taka-leda daga gefen fili.

Rahotanni na cewa United za ta sayi Matic daga Chelsea kan kudin da zai kai fan miliyan 50, kuma wannan ne karo na biyu da Mourinho ke daukar dan wasan.

Mourinho ya taba sayen Matic kan fan miliyan 21 daga Benfica a Janairun 2014 zuwa Chelsea.

'Naby Keita ba zai koma Liverpool ba'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallaye takwasa Keita ya ci wa Leipzig a kakar da ta kare

Dan wasan RB Leipzig, Naby Keita zai ci gaba da taka-leda a kungiyar a bana duk da zawarcinsa da Liverpool ke yi in ji koci Ralph Hasenhuttl.

Dan kwallon tawagar Guinea mai shekara 22, ya taka rawa a gasar Bundesliga, bayan da Leipzig ta yi ta biyu a wasannin da aka kare.

Kungiyar da ke Jamus ta ki sallama tayin da Liverpool ta yi wa dan kwallon har karo biyu a bana.

Leipzig ta tabbatar da cewar ba ta sallama tayin fan miliyan 67 da aka yi wa Keita ba, sai dai ba ta fadi sunan kungiyar ba.

Keita ya ci kwallo takwas a wasa 31 da ya buga wa Leipzig, wadda ta samu gurbin shiga gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana a karon farko.

Nigeria: An yi hatsaniya a sakatariyar 'yan jarida a Kaduna


Hakkin mallakar hoto
WHATSAPP

Image caption

‘Yan jarida da sauran mahalarta taron sun tarwatse bayan da aka fara hatsaniyar

An samu hatsaniya a sakatariyar ‘yan jarida da ke jihar Kaduna yayin da wasu sanatoci guda biyu sun kira wani taron manema labarai, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

“Wadansu mutane ne dauke da makamai suka kai hari cibiyar ‘yan jarida da ke kan hanyar Muhammadu Buhari Way (Waff Road) ranar Lahadi,” a cewar rahotanni.

Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hukunyi da kuma wasu ‘yan siyasa jihar ne suka kira taron manema labaran.

“Yau (Lahadi) a sakatariyar ‘yan jarida da ke Kaduna muna cikin taro da ‘yan jarida kan yadda za mu kaucewa yunkurin gwamnatin jihar na karbe jam’iyyar (APC) da kuma rusa ta,” kamar yaddda Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“Sai wasu ‘yan daba suka far mana bisa taimakon ‘yan sanda, inda suka lalata motocinmu suka kuma kai wa wasu mutane da ba su ji ba, ba su gani ba hari,” in ji shi.

Kodayake rahotanni sun ce ba a samu asarar rayuka ba daga al’amarin, amma wani dan jarida ya jikkata.

Sai dai Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’i ya yi Allah-wadai da al’amarin a wani sako da ya aike wa kungiyar ‘yan jarida reshen jihar ta hannun maitaimaka masa kan kafofin yada labarai Samuel Aruwan.

Gwamnan ya umarci fara bincike kan al’marin, yayin da ya ce ya aike da “karin jami’an tsaro satakariyar don tabbatar da tsaro.”

An dade ana samun takun sada tsakanin bangarorin jam’iyyar APC biyu a jihar wato ‘yan APC akida da kuma maso goyon bayan gwamnatin jihar.

‘Yan APC akida suna zargin gwamnatin jihar da kin cika alkawuran da ta daukar wa jama’a, yayin daya bangaren yake musanta zargin.

Hakkin mallakar hoto
WHATSAPP

Image caption

Dan jaridar da ya ji rauni yayin hatsaniyar

Hakkin mallakar hoto
WHATSAPP

Image caption

Wani gilas din kofa da aka fasa

Hakkin mallakar hoto
WHATSAPP

Image caption

Wata mota da aka fasa gilashinta

Turmi biyu suka dambata babu kisa aka raba


Damben da aka yi tsakanin Nuran Dogon Sani daga Arewa da Shagon Abata Mai daga Kudu, turmi biyun da suka kara babu kisa a safiyar Lahadi a Dei-Dei da ke Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada rahotan

Wasanni 12 aka dambata a gidan wasa na Ali Zuma da ke Abuja a safiyar Lahadi, inda aka yi kisa a karawa uku sauran aka tashi canjaras.

Ga wasannin da aka yi kisa:

 1. Dan Shagon Abata Mai daga Kudu ya buge Shagon Ali Kanin Bello daga Arewa
 2. Shagon Ali Kanin Bello daga Arewa ya doke Gulafa Shagon Wale daga Kudu
 3. Bahagon Sama’ila daga Kudu ya yi nasara a kan Bahagon Katsinawa daga Arewa.

Wasannin da babu kisa:

 1. Shagon Bahagon Balan Gada daga Arewa da Shagon Bahagon Fandam daga Kudu
 2. Bahagon Katsinawa daga Arewa da Shagon Dogon Jamilu daga Kudu
 3. Dan Yellow Gusau daga Arewa da Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu
 4. Dan Shagon Abata Mai daga Kudu da Shagon Shagon Buzu daga Arewa
 5. Shagon Inda daga Arewa da Shagon Shagon Abata Mai daga Kudu
 6. Bahagon Sama’ila daga Kudu da Shagon Shagon Bahagon Musa daga Arewa
 7. Shagon Dan Jamilu daga Kudu da Shagon Cika aiki daga Arewa
 8. Shagon Shagon Lawwali daga Arewa da Dan Shagon Abata Mai daga Kudu

Barca ta lashe International Champions Cup


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ce ta lashe International Champions Cup

Barcelona ta ci International Champions Cup, bayan da ta doke Real Madrid da ci 3-2 a karawar da suka yi a Amurka.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin Spaniya masu buga wasan hamayya da ake kira El-Clasico suka kara ba a cikin kasar ba, tun bayan wanda suka yi a 1991.

An buga karawar a filin wasa na Hard Rock da ke Miamin Amurka wanda ‘yan kallo 66,014 suka kalli kwallayen da Lionel Messi da Ivan Rakitic suka fara ci wa Barcelona.

Daga baya ne Real Madrid ta farke ta hannun Mateo Kovacic da kuma Marco Asensio.

Barcelona ta ci kwallo na uku ta hannun Gerard Pique a bugun tazara da Neymar wanda PSG ke son dauka ruwa a jallo ya buga.

Barcelona ta yi nasarar cin kofin ne bayan da ta doke Juventus da Manchester United da Real Madrid a gasar.

Ita kuwa Madrid din ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da Manchester City da kuma Barcelona.

Mun yi kuskure kan harin Borno – Sojin Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana alhininta game da harin da kungiyar Boko Haram ta kai wanda ya zama saniyyar mutuwar ma’aikatan da ke binciken mai a gundumar Borno Yesu ta karamar hukumar Magumeri dake jihar Borno.

Ma’aikatan da suka rasa rayukansu sun hada da ma’aikatan kamfanin mai na kasa, NNPC, da wasu ma’aikatan jami’ar Maidugui har da da sojojin da ke raka su tare da ‘yan kato da gora.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman ya sanya wa hannu, rundunar sojojin ta ce abin takaici ne yadda suka sanar da al’umomin Najeriya cewa sun riga sun ceto dukkan ma’aikatan kamfanin NNPC, inda sanarwar ta kara da cewa ba da gangar a ka yi haka ba.

“Kawo yanzu, masu bincike sun gano karin gawarwakin wasu sojoji 5, da ‘yan kato da gora 11 da na jami’ai masu binciken guda 5, kuma ta ce ba a ji duriyar mutum shida cikin ma’aikata goma sha biyun da suka suka fita aikin binciken ba, amma ma’aikacin kamfanin NNPC daya ya tsira da ransa”, in ji sanarwar.

Sanarwa ta kuma bayyana wasu kayan yaki da rundunar sojin da ke yaki da kungiyar Boko Haram ta kwato a hannun kungiyar ta Boko Haram. Kayan sun hada da bindigogi, da motoci, da bama-bamai har da kayan bincike na GPS.

Sanarwar ta cigaba da cewa rundunar sojojin na cigaba da neman inda aka tafi da sauran ma’aikata masu bincike. Ta kuma nuna farin cikinta da irin goyon bayan da take samu daga ilahirin jama’ar yankin.

Yadda kayan lefe ke kawo wa aure cikas


 • Akwai ci gaban cikakkiyar zantawar da Fatima Zarah Umar ta fara da wasu mutane game da tasirin kayan lefe, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Daya daga cikin manyan batutuwan da suke tasowa game da batun aure a kasar Hausa shi ne kayan lefe.

Idan ana maganar lefe kowa ya san cewa batu ne na kudi musamman idan aka yi la’akari da gidan da amaryar ta fito.

Shin ta fito daga gidan masu hali ne ko kuwa ‘yan rabbana ka wadata mu.

Ta fito daga birnin ne ko kauye? Da kuma yadda ‘yan uwanta za su rika tambaya cewa akwati nawa aka kawo?

Wadannan kayayyaki aka sanya a akwatin? Manyan atamfofi nawa ne a ciki? Akwai atamfa Super ko Java?

Wadanne irin gyale aka sa a akwatin kuma ko kayan sun burge surukan angon?

Yadda na fahimci abin shi ne kayan lefe wani abu ne da ya yi kama da kyauta amma ba wani abu ba ne da wajibi ya burge mutum. Ba wata dama ce ta bayyana yawan arzikin mutum ba.

Aure bai dogara kacokan a kan lefe ba.

Ko miji da gidansu sun yi lefe, ko ba su yi ba, nauyin samar wa mace tufafi ya rataya ne a wuyan mijinta.

Yadda muka ba lefe muhimmanci abin kamar ita amarya ba za ta kara sanya wasu kayan ba idan ba na lefe ba duk tsawon rayuwarta.

A wasu lokuta iyaye ba sa tambaya kan yadda ko ya dace a saye irin wadannan kayayyaki.

Yana da wuya ka ga wani yana tambaya game da yadda lefe zai amfani zamantakewar aure.

Mene ne amfanin kayan lefe a aure?

Ko wajibi ne sai an yi kayan lefe? Yana da wani tasiri wajen zamantakewa? Ko idan aka yi wa amarya akwatuna da dama na samar da kyakkyawan zaman aure?

Wane ne yake cin moriyar kayan lefe? Bayan mutanen da suke yada tsegumi da kananan maganganu?

A duk lokacin da na ga samari suna kokorin hada kayan lefe, nakan tausaya musu.

Bai kamata aure ya zama kamar wani cinikin kasuwanci ba. Aure ana so ne ya kasance har abada.

Ko al’umma za su daina damuwa da lefe da kayan daki, don su mayar da hankali kan kyawawan dabi’u da kuma tarbiyya?

Ina tausayawa ‘yan uwana wadanda suka fito daga yankin arewa-maso-gabashin Najeriya saboda hada kayan lefe a wannan yanayi na matsin tattalin arziki ba abu ba ne mai sauki.

Sai dai komai ya yi tsanani maganinsa Allah.

Har ila yau, ina tausayawa iyaye wadanda suke hada wa ‘ya’yansu kayan daki saboda yadda hakan yake cin makudan kudi.

Ya kamata ne kowannenmu ya sauke nauyin da ke wuyansa.

Mata da dama sun shaida min cewa bayan da aka yi musu lefe, mazajensu ba su damuwa wajen tufatar da su.

Lefe ba ya dauke nauyin tufatarwa da ya rataya a wuyan mai gida.

Mata da dama sun san cewa ana fara rikici ne da zarar dara ta fara karewa.

Wacce irin al’umma muke ciki wadda iyayen amarya suke yi wa ango kusan komai – ciki har da dara wadda takan kai tsawon kimanin shekara guda bayan aure, amma abin mamakin shi ne yadda har yanzu ake kara samun yawaitar mutuwar aure.

'PSG na daf da biyan kudin Neymar'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau 123 Neymar yana taka wa Barcelona leda

Dan wasan Barcelona Neymar ya amince da kwantiragin shekara biyar da kulob din Paris St-Germain inda suka ce za su saye shi a kan Yuro miliyan 220 a cikin mako mai zuwa, kamar yadda jaridar Metro ta bayyana.

Haka kuma PSG za ta bayar da tsohon dan wasan Manchester United Angel di Maria a cikin yarjejeniyar don ta samu kudin biyan harajin sayen Neymar, kamar yadda kafar yada labarai ta AS ta bayyana.

Idan Neymar ya bar Barcelona, kungiyar za ta maye gurbinsa da daya daga cikin ‘yan wasa uku da ke murza-leda a Ingila – Philippe Coutinho na Liverpool ko Eden Hazard na Chelsea ko kuma Dele Alli na Tottenham, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.

Dan wasan gaban Barcelona Andres Iniesta ya ce Neymar ne kawai ya san makomarsa, sai dai “ba na jin dan kwallon zai fi zama wa Barcelona alheri a kan a biyata Yuro miliyan 200 zuwa 300,” kamar yadda kafar yadaa labarai ta Marca ta bayyana.

Ko Ronaldo, Mahrez da Sanchez za su sauya kulob?

Tarihin tsofaffin ‘yan wasa da nasarorinsu

Wanne kulob ne zai lashe Premier ta bana?

Kungiyar Monaco ba ta son rabuwa da Thomas Lemar duk da cewa sau uku Arsenal ta yi zawarcinsa a kan Yuro miliyan 45, a labarin da Telegraph ta wallafa.

Daily Mail kuwa cewa ta yi Manchester City za ta bai wa dan kwallon Arsenal Alexis Sanchez albashin fan 320,000 a duk mako a kunshin yarjejeniyar ya buga mata tamaula.

Har ila yau, golan Manchester City Claudio Bravo wanda kasa guda suka fito da Sanchez wato Chile, ya ce za a karbi dan wasan hannu biyu-biyu idan ya koma City, kamar yadda Metro ta ruwaito.

Kungiyar West Ham za ta ki amincewa da duk wani tayi da Liverpool za ta yi wa Manuel Lanzini, a labarin da Evening Standard ta ce.

Daily Express ta ce Manchester United za ta tsawaita zaman Ander Herrera don ta dakile zawarcin da Barcelona ke son yi wa dan kwallon.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Herrera ya koma United ne daga Athletic Bilbao a shekarar 2014

Liverpool ta dakatar da zawarcin da take yi wa dan wasan kungiyar RB Leipzig Naby Keita, amma za ta ci gaba da nemansa a kakar badi lokacin da take ganin kila Keita ya amince da tayin Yuro miliyan 48, kamar yadda jaridar Liverpool Echo ta bayyana.

Har ila yau, Express ta ruwaito cewa Arsenal tana zawarcin Jakub Jankto daga kungiyar Udinese ta kasar Italiya.

Har yanzu Manchester United na neman dan wasan Inter Milan Ivan Perisic in ji Independent.

Daga karshe dan kwallon Real Madrida, Gareth Bale zai bijirewa duk wani yunkuri na sayar da shi ga Manchester United, ya ce bai shirya barin Madrid ba, kamar yadda jaridar Daily Star ta wallafa.

Hana daukar waya yayin tsallaka titi a Amurka na tayar da kura


Image caption

Ana yawan kade mutane saboda yawan yin amfani da waya

Birnin Honolulu na jihar Hawaii na kasar Amurka ya haramta amsa ko kuma kira da wayar hannu yayin tsallaka titi.

Dokar za ta ci tarar duk mai tafiyar da aka samu yana rubuta ko kuma ya kafa idanunsa kiri a kan wayar, kama daga dala 15 zuwa 35.

Kuma za a ci gaba da rubanya yawan tarar ga mutanen da aka samu da laifin karya dokar fiye da karo daya.

An dai dauki wannan matakin ne wanda ake sa ran zai fara aiki a watan Oktoba da manufar rage yawan mace-macen ‘yan kasar sakamakon hatsarin mota.

To sai dai masu sukar dokar na ganin gwamnati ta wuce makadi da rawa.

Sai dai magajin garin birnin, Kirk Caldwell ya ce da alama mutane ba su inda yake yi musu ciwo ba.

Barcelona da Real Madrid za su kara a Amurka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Watakila Barcelona da Real Madrid su kara fiye da sau biyar a bana

Barcelona da Real Madrid za su kece raini a wasan hamayya da ake kira El-Clasico a gasar International Champions Cup a ranar 30 ga watan Yuli.

Kungiyoyin da ke buga gasar Spaniya za su fafata ne a filin wasa na Hard Rock da ke Miami a birnin Floridan Amurka.

Wannan ne karo na biyu da Barca da Real za su buga El-Clasico ba a Spaniya ba, na farko shi ne wanda suka kara a Barquisimeto da ke Venezuela a ranar 30 ga watan Mayun 1982.

Kungiyoyin biyu za su sake karawa a ranar 13 ga watan Agusta a Spanish Super Cup wasan farko a Camp Nou, sannan Madrid ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar 16 ga watan na Agusta.

Real za ta yi karawa ta uku a wasan International Champions Cup, bayan da Manchester United ta doke ta a bugun fenariti, sannan Manchester City ta zura mata 4-1.

Ita kuwa Barcelona ta ci Juventus 2-1, sannan ta doke Manchester United 1-0.

Mutum biyu sun mutu a filin wasan Afirka ta Kudu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka ji raunuka a wani turmutsitsi filin wasan kwallon kafa na kasar Afirka ta Kudu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

Al’amarin ya faru ne a wani filin wasa da ke birnin Johannesburg yayin da ake wasa tsakanin kungiyoyi biyu wato Kaizer Chiefs da Orlando Pirates.

Sai dai ba a san abin da ya jawo turmutsitsin ba tukuna a filin wasan wanda ke daukar ‘yan kallo kimanin dubu 87.

Afirka ta Kudu ta kori kocinta Mashaba

Afirka ta Kudu: Zuma ya shiga tsaka mai wuya

Ra'ayi: Ko rage shekarun 'yan takara zai ba matasa dama a Najeriya?


Ga alama hankoron matasan Najeriya na ganin an rage shekarun takarar mukaman siyasa a kasar, domin a rika damawa da su, na gab da biyan bukata. Yanzu haka dai majalisun kasa sun amince a yi sauyi ga sassan kundin tsarin mulkin kasar da ya shafi wannan batu. Matasan dai na zargin tsaffin ‘yan siyasa da mayar da su ‘yan kallo. To shin rage yawan shekarun ne zai kai su ga samun madafun iko ko kuwa akwai wani abu daban? Batun da aka tattauna a kan shi kenan a filin Ra’ayi Riga.

Hotunan manyan masallatan 10 ma fi kyau a duniya


Masallacin wani wuri ne na bauta ga mabiya addinin Islama, inda al’ummar Musulmi ke taruwa su yi sallah cikin jam’i.

Akwai gine-ginen masallatai masu kayatarwa a duniya wadanda wata kila ba ku taba sanin da su ba, don haka muka kawo muku wasu daga cikinsu.

1. Masallacin Haramin Makkah da ke Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masallacin Al Haram a yanzu ya mamaye kimanin murabba’in mita 400,800, wanda ke daukar mutane miliyan hudu a ciki da wajensa lokacin Hajji.

Al-Qur’ani ya bayyana wannan masallacin a matsayin na farko da aka gina a ban kasa domin dan Adam ya bauta wa Allah.

Wannan masallacin, mai suna Al Haram, wato “Mafificin Masallaci” shi ne ya fi ko wanne daraja a duniya baki daya, yana da dadadden tarihi, ya fi ko wanne masallaci daraja da girma da kayatuwa.

A zagaye yake d a gine-ginen manyan otal-otal masu kyau da tsari wadanda idan kana daga cikisu ma kana iya hango harabar masallacin da cikinsa.

2. Masallacin Annabi SAW da ke Madinah a kasar Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Kingdom of Saudi Arabia Ministry of Information

Image caption

Mafi darajar wuri a wannan Masallaci shi ne daga tsakiyarsa, inda kabarin Annabi Muhammad SAW ya ke

Wannan masallacin da aka fi sani da masjid An Nabawi, watau “Masallacin Annabi,” shi ne masallaci na biyu mafi daraja da kyau da girma bayan na Makkah.

Annabi SAW da kansa ya gina masallacin a lokacin da ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina shekara 1439 da ta gabata.

A ciki kabarin fiyayyen halitta yake da na manyan abokansa biyu kuma sahabbansa Abubakar da Umar Allah ya kara musu yarda.

Gidan Annabi SAW a yanzu haka duk ya shiga cikin masallacin.

Ana yi wa masallacin lakabi da ‘Koriyar Hubba ta Dan Abdullahi.’

3. Masallacin Kudus da ke Jerusalem a Isra’ila

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tarihi ya nuna cewa a baya, Annabi Muhammad SAW na jagorantar sallah ne a yayin da ake fuskantar wannan masallaci, kafin daga wata na 17 na hijira, Allah ya umurce shi da maya da alkiblar zuwa Ka’aba, da ke Makkah

Masallaci na uku mafi girma da daraja a ban kasa.

Ana kiransa da Al-Aqsa kamar yadda ya zo a Al-Kur’ani mai tsarki ko kuma Baytul-Muqaddas.

An gina Masallacin Al-Aqsa ne a garin birnin Kudus da ke kasar Isra’ila.

Masallacin shi kan sa an gina shi ne a wani yanki na Al-Haram ash-Sharif, wato “Mafificin mafaka mai tsarki”, wanda su Yahudawa suke kira Temple Mount, wanda shi ne mafi tsarki su kuma a wurinsu.

Ta Baitul Mukaddas ne Annabi SAW ya tafi Mi’iraji.

4. Masallacin Hassan na Moroko

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masallacin na kallon tekun Atlantika, inda aka shimfida kasa sa da gilashi, ta yadda ake iya ganin cikin ruwa

Wannan masallacin yana birnin Casablanca ne a Moroko, kuma shi ne masallaci mafi girma a kasar, haka kuma na bakwai a jerin masallatai masu girma a duniya.

Hasumiyarsa ita ce wadda ta fi tsayi da kimanin mita 210.

An kammala ginin masallacin ne a shekarar 1993.

Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin a Brunei

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An zagaye Masallacin da bishiyoyi da furanni da dama, domin kamanta ni’imar Aljannah Firdausi

Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddien, wani masallacin ‘yan sarauta ne da ke garin Bandar Seri Begawan, babban birnin masarautar Brunei.

Ana yi wa masallacin kallon wanda ya fi ban sha’awa a yankin Asiya, kuma wata matattara ce ta masu yawon bude ido a Brunei.

An kammala gininsa a shekarar 1958, kuma yana daya daga cikin gine-gine da ke nuna bajintar taswirar gine-gine a duniya.

6. Masallacin Zahir da ke Kedah a Malaysia

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Duk shekara ake gudanar da musabaka a cikin wannan Masallaci

Masallacin Zahir, shi ne masallacin jihar Kedah, wanda ke kasar Malaysia, wanda ke tsakiyar garin Alor Star.

An gina masallacin a shekarar 1912, da tallafin Tunku Mahmud, dan Sultan Tajuddin Mukarram Shah.

Wannan masallaci babba ne sosai kuma yana da kayan kawa na zamani.

7. Masallacin Faisal da ke Islamabad a Pakistan

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masallacin Faisal da ke birnin Islamabad a Pakistan shi ne mafi girma a kudancin Asiya, kuma shi ne na hudu da ya fi girma a duniya

Wannan masallacin shi ne mafi girma a kudu maso gabashi da kudancin Asiya, kazalika shi ne na hudu cikin mafi girman masallatai a duniya.

A shekarun 1986 zuwa 1993 shi ne masallacin da ya fi ko wanne girma a duniya, kafin masallacin Hassan na biyu da ke Casablanca a Morocco, da kuma bunkasa Masjid Al-Haram na Makkah da aka yi daga baya, wadanda duk suka doke shi.

8. Masallacin Taj ul da ke Bhopal a Indiya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masallacin na da babban lambu a tsakiyarsa, inda aka dasa wani babban tankin ruwa

Ma’anar sunan wannan masallaci, “Sarkin duk masallatai”, kuma yana garin Bhopal ne a Indiya. Ana gudanar da karatun Qur’ani ma a masallacin, da rana. Masallacin shi ne mafi girma a nahiyar Asiya baki daya.

9. Masallacin Badshahi a Lahore, Pakistan

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masallacin na daukar masu ibadah dubu 55 lokaci guda wajen sallah, kuma daga waje yana iya daukar masallata dubu 95

Sarkin daular Mughal, Aurangzeb ne ya kaddamar da Masallacin Badshahi, ko kuma “Masallacin sarauta” da ke Lahore, a shekarar 1673, wanda shi ne masallaci mafi girma na biyu a Pakistan da kudancin Asiya.

Haka kuma shi ne masallaci na biyar mafi girma a duniya. Masallacin ya yi fice a kyau, wanda ya fito da irin kasaitar daular ta Mughal.

10. Masallacin Sultan na Singapore

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An mayar da wannan Masallacin wani gini na tarihin Singapore a hukumance daga ranar 14 ga watan Maris din 1975

Ana yi wa wannan masallacin da ke layin Muscat da ke gundumar Glam Rochor a Singapore, kallon mafi daraja tsakanin dukkan masallatan kasar. asallacin Sultan ya dade ba tare da an sauya masa komai ba tun da aka gina shi, sai wasu ‘yan gyare-gyare da aka yi a harabarsa a shekarar 1960, da wasu kare-kare da aka yi a shekarar 1993.

Wanne kulob ne zai lashe gasar Premier ta bana?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chelsea ce ta lashe kofin Premier na 2016/17 kuma na shida jumulla

A ranar 12 ga watan Agusta ne za a fara gasar Premier ta 2017/18, kuma tuni kulob-kulob suka fara daura damara domin tunkarar gasar.

Kawo yanzu an kashe kusan fam biliyan daya wajen sayen sabbin ‘yan wasa.

Kungiyoyi 20 ne za su fafata a wasannin da za a fara, inda ake sa ran uku za su bar gasar, kuma tuni suka tashi tsaye wajen shirye-shiryen yadda za su taka rawar gani.

Shin wacce kungiya ce za ta dauki kofin kakar bana ta 2017/18.

Manchester City ta kashe fiye da fam miliyan 200, takwararta United ta kashe sama da fam miliyan 100, Everton kuwa fam miliyan 90 ta kashe, yayin da Swansea City ta yi wa Gylfi Sigurdsson kudi fam miliyan 50.

Tuni aka kashe fiye da fan miliyan 580 wajen saye da sayar da ‘yan wasa a gasar Premier tun lokacin da aka kammala kakar da ta kare.

Kamfanin Deloitte ya ce za a sake kafa tarihin kashe kudade da dama kafin a rufe kasuwar ciniki a tsakar daren ranar 31 ga watan Agusta.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Image caption

Yadda ake saye da sayar da ‘yan wasan gasar Premier

‘Yan wasa nawa Chelsea ta saya a bana?

Chelsea ce ta lashe kofin Premier da aka kare, kuma kakar farko da koci Antonio Conte ya ja ragamar kungiyar da ke buga wasanninta a Stamford Bridge.

Hakan ne ya sa ta dauko sabbin ‘yan wasa a bana:

 1. Willy Caballero (Manchester City)
 2. Rudiger (Roma, Yuro miliyan 35),
 3. Bakoyoko (Monaco, Yuro miliyan 40),
 4. Morata (Real Madrid, Fam miliyan 80)

Cikin wasannin atisayen da ta yi ta doke Arsenal 3-0, ta yi rashin nasara da ci 3-2 a hannun Bayern Munich.

Har ila yau, Chelsea ta ce ba za ta yi amfani da Diego Costa ba a kakar da za a fara duk da kwallayen da ya ci wa kungiyar da suka ba ta nasarar cin kofin Premier.

Tottenham ce ta yi ta biyu a gasar Premier bara, sai dai kuma ana ganin kungiyar na son yi wa kanta sakiyar da babu ruwa, ganin har yanzu ba ta sayi dan kwallo ba, amma kuma ta sayar da wasu.

 1. Bentaleb (Schalke, Yuro miliyan 19),
 2. Fazio (Roma, Yuro miliyan 3.2),
 3. N’Jie (Marseille, Yuro miliyan 7),
 4. Kyle Walker (Manchester City, Yuro miliyan 56.7)

Tottenham za ta buga gasar Premier da ta Zakarun Turai da FA Cup da League a shekarar nan.

Manchester City ce ta yi ta uku a gasar Premier da aka kammala, kuma ta buga wasan atisayen tunkarar kakar bana da Manchester United, inda ta yi rashin nasara da ci 2-0.

Sai dai ta doke Real Madrid da ci 4-1 a gasar International Champions Cup a Amurka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

AC Milan na son daukar Costa, shi kuwa so yake ya koma Athletico Madrid

Shin wadanne ‘yan wasa Manchester City ta dauka a bana?

 1. Bernardo Silva (Monaco, Yuro miliyan 50),
 2. Ederson (Benfica, Yuro miliyan 40),
 3. Kyle Walker (Tottenham, Yuro miliyan 56.7),
 4. Danilo (Real Madrid, Yuro miliyan 30)
 5. Benjamin Mendy (monaco, fan miliyan 52)

Pep Guardiola na fatan City za ta taka rawar da ta dace a wasannin da za a fara, ganin cewa kakar farko bai tabuka abin a zo a gani ba duk da irin nasarorin da ya yi a Barcelona da Bayern Munich.

Rabon da Liverpool ta dauki kofin Premier tun 1989/90 kuma har yanzu tana fatan ta ci Premier bayan da ta yi ta uku a kakar da ta kare, hakan ne ya sa kungiyar za ta buga wasannin cike gurbin shiga gasar Zakarun Turai da FA Cup da League Cup a kakar da za a fara.

Tuni kungiyar ta dauki ‘yan wasa da suka hada da

 1. Salah (Roma, Yuro miliyan 42),
 2. Solanke (Chelsea),
 3. Robertson (Hull City)

A kakar da ta kare Arsenal ta kammala gasar a mataki na biyar a teburi, wanda rabon da ta yi hakan tun shekara 20, hakan ya sa kungiyar za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa bayan da ta je gasar Champions League 20 a jere.

Da kyar magoya bayan Arsenal suka amince kungiyar ta tsawaita zaman Arsene Wenger a kungiyar, wanda yanzu zai kara kaka biyu a Gunners.

Rabon da Arsenal ta ci kofin Premier tun kakar 2002/03.

Hakan ne ya sa Arsenal ta sayo sabbin yan wasa tana kuma ci gaba da zawarcin wasu.

 1. Kolasinac (Schalke),
 2. Lacazette (Lyon, Yuro miliyan 53)

Manchester United ta shida ta yi a Premier 2016/17, sai dai kungiyar ta ci Europa League wanda ya ba ta damar shiga gasar kofin Zakarun Turai da za a yi ta bana, hakazalika za ta yi gumurzi a FA Cup da League Cup.

A karshen kakar da ta kare yarjejeniyar Zlatan Ibrahimovic ta kare da Manchester United, kuma kungiyar ba ta kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ibrahimovic ya taka rawar a Manchester United a kakar da ta kare

Tuni dai United ta sayi ‘yan wasa da suka hada da

 1. Lindelof (Benfica, Yuro miliyan 35),
 2. Lukaku (Everton, Yuro miliyan 85)

Sauran kungiyoyin da ake ganin za su taka rawa a Premier da za a fara sun hada da Everton da Southampton da West Brom da West Ham wadanda su ma suka daura damarar shiga gasar bana.

Leicester ma ta yi sayayya, ita ma Swansea wadda da kyar ta sha a bara na fatan yin abin kirki a bana.

Newcastle United wadda ta dawo gasar Premier tana daga cikin sabbin da ake sa ran yin abin azo a gani a shekarar nan.

Kungiyar Chelsea ce ta lashe gasar da aka kammala ta 2016/17, wadda bayan da aka buga wasa 38 a gasar, ta ci 30, ta yi canjaras a karawa uku, aka doke ta sau biyar.

Jerin kungiyoyin da suke 10 farko bayan da Chelsea ta lashe kofin

 • 2 Tottenham Hotspur 86
 • 3 Manchester City 78
 • 4 Liverpool 76
 • 5 Arsenal 75
 • 6 Manchester United 69
 • 7 Everton 61
 • 8 Southampton 46
 • 9 Bournemouth 46
 • 10 West Bromwich Albion 46

Kungiyoyin da suka fi yawan daukar Premier a tarihi

 • 20 Manchester United
 • 18 Liverpool
 • 13 Arsenal FC
 • 9 Everton FC
 • 7 Aston Villa
 • 6 Chelsea FC
 • 6 Sunderland
 • 4 Manchester City
 • 4 Sheffield Wednesday FC
 • 4 Newcastle United FC
 • 3 Blackburn Rovers FC
 • 3 Leeds United FC
 • 3 Wolverhampton Wanderers FC
 • 3 Huddersfield Town

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Magoya bayan kungiyar Brighton & Hove Albion

Sabbin kungiyoyin da za su buga gasar 2017/18

Kungiyar da ta fara samun tikitin shiga gasar Premier ta bana ita ce Brighton & Hove Albion, bayan da ta doke Wigan Athletic da ci 2-1.

Wannan ne karon farko da Brighton za ta buga babbar gasa a tarihin kwallon kafar Ingila tun 1983, kuma wannan ce gasar Premier ta farko da za ta fafata.

Kulob na biyu da ya samu tikitin shiga Premier na bana shi ne Newcastle United, bayan da ya doke Preston North End 4-1 a gida a ranar 24 ga watan Afirilu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Newcastle United ce ta lashe gasar Championship

Ta uku da ta samu gurbin shiga Premier shekarar nan ita ce Huddersfield Town, wadda ta ci Reading 4-3 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasa babu ci a fafatawar cike gurbi.

Wannan ne karon farko da kungiyar za ta buga babbar gasar Ingila tun bayan shekara 45, kuma karon farko da za a yi gumurzu da ita a wasannin Premier.

Boko Haram ta saki bidiyon ma'aikatan hako mai


Image caption

Ranar Talata ne dai Boko Haram din ta yi wa tawagar da mutanen suke kwantan bauna

Kungiyar Boko Haram bangaren Albarnawi ta saki wani bidiyo da ke nuna mutane uku da ta ce ta kama lokacin wani harin sunkuru da ta kai wa ma’aikatan hakar mai a jihar Bornon Najeriya.

Bidiyon wanda gidan talbijin na Channels a Najeriya ya ce an aike masa, ya nuna mutanen uku zaune sannan bayansu akwai wani kyalle.

Biyu daga cikin mutanen sun ce ma’aikatan sashen kimiyyar kasa ne na jami’ar Maiduguri, a inda shi kuma na ukun ya ce shi direba ne.

Mutanen dai sun nemi gwamnati da ta kai musu dauki.

Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya


Image caption

Ma’auratan na tafiya ne a cikin jirgin ruwa na Emerald Princess

‘Yan sanda na zargin wani mutum da kashe matarsa a cikin jirgin ruwa a jihar Alaska ta Amurka saboda “ta ki daina yi masa dariya”.

Ana zargin Kenneth Manzanares da laifin kisan matarsa mai shekara 39, wacce aka gano gawarta an yi mata raunuka da dama a kanta a cikin jirgin ruwan.

An tsare shi bayan jami’an tsaro sun ga jini a hannu da tufafinsa, kamar yadda wasu takardun kotu suka nuna.

Lauyan da kotu ta nada domin ya kare Mista Manzanares bai ce komai a kan batun ba.

Kafofin watsa labaran Amurka sun ce sunan matar Kristy Manzanares, daga jihar Utah.

Wani shaida da ya shiga jirgin ruwan tare da ma’auratan ya ce ya ga lokacin da mijin ke jan gawar matarsa a bayan dakinsu na jirgin.

Da aka tambayi Mista Manzanares kan hakikanin abin da ya faru, ya yi zargin cewa: “Ta ki daina yi min dariya.”

Daga bisani lokacin da jami’an hukumar FBI suka yi bincike a jirgin, mutumin ya shaida musu cewa: “Tawa ta kare.”

Lamarin ya auku ne a daren Talata lokacin da jirgin ruwan na Emerald Princess, na kamfanin Princess Cruises ke tafiya.

A ranar Lahadi ne jirgin ya tashi daga Seattle inda zai yi tafiyar mako guda da fasinja 3,400.

An ceto 'yan makaranta shida da aka sace a Lagos


Hakkin mallakar hoto
Peeter Viisimaa

Image caption

Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya

Hukumomi a birnin Lagos da ke kudancin Najeriya sun ce sun ceto ‘yan makarantar da aka sace a birnin.

A watan Mayu ne dai wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan makaranta guda shida.

‘Yan bindigan sun kai hari ne a makarantar Igbonla Model School, inda suka tafi da ‘yan makaranta 10.

Amma rahotanni sun ce sun saki hudu daga cikinsu, bayan da suka binciki asalin iyayensu.

‘Yan sanda sun ce ‘yan bindigar sun samu shiga makarantar ta cikin wani daji da ke gefen makarantar ne, inda suka yanka wayar da ta zagaye makarantar kana suka shiga ciki.

Kudin da EFCC ta kama a Lagos sun haura N400m

Lagos: Hukuncin kisa kan masu satar mutane

An kama wasu da shigar da bindigogi Nigeria

Sace yaran dai ya sa mazauna birnin sun rika sukar gwamnatin jihar ta Lagos.

Sai dai gwamnatin ta sha ba iyayen yaran tabbacin cewa za ta ceto su.

An taba sace dalibai shida a watan Oktoban da ya gabata a wannan makaranta.

Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya.

Ashley Fletcher: Middlesbrough ta sayi dan wasan West Ham United kan £6.5m


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ashley Fletcher ya si nasara a bahsin da ya tafi Barnsley a kakar 2015-16

Middlesbrough ta sayi dan wasan gaban West Ham United, Ashley Fletcher, a yarjejeniyar shekara hudu kan Fam miliyan 6.5.

Fletcher, mai shekara 21, ya bar sansanin atisayen Hammers a Jamus ne ranar Alhamis domin som tattaunawa da kungiyar da ke gasar Championship.

Kawo yanzu Boro ta kashe kimanin Fam miliyan 30 kan ‘yan wasan gaba a lokacin bazaran nan bayan ta riga ya ta sayi Britt Assombalonga da Martin Braithwaite.

Fletcher, wanda ya koma West Ham daga Manchester United a shekarar 2016, ya ci kwallo daya a wasanni 20 da ya buga wa Hammers.

A lokacin da ya je Barnsley kan bashi a kakar 2015-16, Fletcher ya ci kwallaye takwas a wasanni 27 da ya yi wa Tykes yayin da suka samu hayewa zuwa gasar Championship.

Nigeria: Arzikin Aliko Dangote 'ya ragu'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Aliko Dangote ya dade yana shiga cikin jerin attajiran dduniya da Forbes ke wallafawa

Hamshakin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya yi kasa a jerin masu kudin duniya inda ya fado daga mataki na 51 zuwa 105, in ji mujallar Forbes.

Mujallar ta ce arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 15.4 a shekarar 2016 zuwa biliyan 12.2 a bana.

Hakan dai ya faru ne, a cewar Forbes, saboda faduwar darajar kudin Najeriya.

Alhaji Dangote, wanda ya fi karfi a harkar siminti da sukari da filawa, ya ja hankalin duniya lokacin da ya ce yana son sayen kulob din Arsenal cikin shekara hudu masu zuwa.

A ranar Alhamis ne, Shugaban kamfanin Amazon Jeff Bezos ya maye gurbin Bill Gates na wani dan lokaci a matsayin mutumin da ya fi kowa arziki a duniya.

Sai dai ba a jima ba ya koma mataki na biyu, inda mutumin da ya kirkiro kamfanin Microsoft din ya koma kan matsayinsa.

Ina Lemar da Bale da Keita da Coutinho da Barkley za su je?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A yanzu dai Thomas Lemar yana taka leda ne wa kungiyar kwallon kafa ta Monaco

Latsa nan domin sanin cinikin ‘yan wasan da aka kammala a turance.

Labaran cinikin ‘yan wasa

Arsenal na dab da sayen Thomas Lemar daga Monaco kan Fam miliyan 45m . (Sun)

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya ce ba zai iya tabbatar da cewar dan wasan gaban nan, Gareth Bale, mai shekara 28- wanda Manchester United take so- zai tsaya Bernabeu ba a lokacin bazarar nan. (Mirror)

Kociyan Chelsea, Antonio Conte, na shirin sayan ‘yan wasan tsakiyar Ingila biyu – dan Everton, Ross Barkley da kuma dan Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain. (Sun)

Jagoran Tottenham, Mauricio Pochettino, yana son ya sayi Barkley a lokacin bazaran nan domin ya mayar da shi dan wasan tsakiya. (Times – subscription required)

Roma ta shirya sake tayin dan wasan Leicester City kuma dan asalin Aljeriya Riyad Mahrez, mai shekara 26 kan Fam miliyan 32.(Mirror)

Chelsea ta yi tayin dan wasan tsakiyan Bayern Munich, Renato Sanches kan bashi. (Telegraph)

Liverpool ta shirya domin ta yi tayin karshe wa dan wasan tsakiyan Guinea Naby Keita kan sama da Fam miliyan 70.(Mirror)

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Philippe Coutinho yana taka leda ne a Liverpool a halin yanzu

Har ila yau, Reds na kan bakansu cewar dan wasan gaban Brazil, Philippe Coutinho, mai shekara 25, ba na sayarwa ba ne a dadai lokacin da Barcelona ke sha’awar sayansa.(ESPN)

Kociyan Inter Milan, Luciano Spalletti ya ce yana son dan asalin Croatia mai shekara 28, Ivan Perisic – wanda Manchester United ke hako- ya tsaya a kulob din, amma shi ba zai iya tabbatar da abin da zai faru ba. (ESPN)

Juventus ta mayar da hankalinta kan dan wasan Paris St-Germain, Blaise Matuidi, mai shekara 30, yayin da suke neman sayan dan wasan tsakiya mai tsaron baya, lamarain da ya sake saukaka wa Manchester United da Chelsea hanyar sayen dan wasan tsakiya, dan asalin kasar Serbi, Nemanja Matic, mai shekara 28.(Independent)

Shugaban AC Milan, Marco Fassone ya bayyana cewar kungiyar ta tuntubi wakilin dan wasan kungiyar Chelsea dan asalin Spaniya, Diego Costa, mai shekara 28. (Sky Sports)

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kylian Mbappe mai shekara 18 na taka leda ne a Monaco

Ana tsammanin dan wasan gaba, Karim Benzema, mai shekara 29, zai sake kulla yarjejeniya da Real Madrid domin kaka mai zuwa ko kulob dinsa ya sayi dan wasan Monaco mai shekara 18, Kylian Mbappe, ko bai saya ba.(Marca)

Dan wasan gaban Argentina,Paulo Dybala, mai shekara 23 – wanda Manchester United da Barcelona ke hako- ba shi da niyyar barin Juventus a lokacin bazarannan.(Talksport)

Agen din Lucas Perez ya kai ziyara Landan domin tattaunawa kan komawar dan wasan gaba dan asalin Spaniyan mai shekara 28 zuwa Deportivo La Coruna.(AS)

Tsohon dan wasan gefe na Arsenal da Liverpool, Jermaine Pennant, mai shekara 34, ya shirya domin rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Billericay Town duk da cewar kungiyar kwallon kafa ta gasar Firimiyar Scotland, Hibernian na son sayan sa. (Sun)

Kotun koli ta sa Firai Ministan Pakistan ya yi murabus


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kotun kolin Pakistan ta ce Mr Sharif bai cancanci ya ci gaba da zama kan mukaminsa ba

Firai Minista Pakistan Nawaz Sharif ya yi murabus bayan kotun kolin kasar ta ce bai cancanta ya ci gaba da rike mukaminsa ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan wani bincike da aka yi kan dukiyar iyalinsa sakamakon abin kunyar nan na Panama Papers ya gano cewa yana da dukiya a kasashen da ke zille wa biyan haraji.

Mr Sharif ya sha musanta aikata ba daidai ba a kan wannan batu.

Bakin alkalai biyar din da suka yanke hukunci a kotun Islamabad, wacce ta cika makil da jama’a, ya zo daya kan hukuncin.

“Nawaz Sharif daga mukamin Firai Minista sakamakon hukuncin kotun,” in ji wata sanarwa da kakakinsa ya fitar.

An yi ta zaman dar-dar a babban birnin kasar kafin hukuncin kotun, inda aka sanya dubban dakarun soji da ‘yan sanda cikin shirin ko-ta-kwana.

Daya daga cikin alkalan, Ejaz Afzal Khan, ya ce Mr Sharif “ba shi da gaskiyar da zai ci gaba da zama dan majalisar dokoki”.

Tun da fari dai, Ministan cikin gidan Pakistan Chaudhry Nisar Ali Khan ya bai wa Mr Sharif shawarar amincewa da hukuncin kotun.

Kotun ta ba da shawarar gudanar da bincike kan mutane da dama game da hannu a cin hanci, cikin su har da ‘yar Mr Sharif, Maryam da mijinta Safdar, da ministan kudi Ishaq Dar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan hamayya sun yi ta murna

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An jibge jami’an tsaro a kusa da kotun kolin ta Pakistan

BH: An umarci jami'an tsaron Nigeria su koma Maiduguri


Hakkin mallakar hoto
AP

Image caption

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare duk da ikirarin soji na murkushe su

Mukaddashin shugaban Najeriya ya manyan hafsan sojojin kasar da su tattara su koma Maiduguri, mahaifar Boko Haram.

Yemi Osinbajo ya bayar da umarnin ne bayan da mayakan kuingiyar suka kashe sama da mutum 40 a wani harin kwantan-bauna da suka yi wa tawagar masu binciken mai na kamfanin man kasar.

Ministan tsaron Najeriya ya ce za a sayi karin kayan aiki na zamani wadanda za su bai wa jami’an tsaro damar ganin abokan gaba daga nesa.

Ma fi yawancin mutanen da aka kashe a harin na ranar Talata a jihar Borno sojoji ne da ‘yan sintiri ko kuma kato da gora.

Yawancin masana kimiyyar sun fito ne daga jami’ar Maiduguri, inda wani malami ya shaida wa BBC cewa an kashe biyar daga cikin ma’aikansu, yayin da ba a ji duriyar wasu guda hudu ba.

Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da jami’an sojin kasar, Ministan Tsaro Mansur Dan-Ali ya ce jami’an tsaro na fuskantar matsala wurin tunkarar mayakan a lokacin damuna.

Sai dai ya kara da cewa jama’a su kwantar da hankalinsu domin matakin da za a dauka “zai kawo karshen irin wadannan hare-hare”.

'Ba mu amince da sauya fasalin Obamacare ba'


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Burin shugaba Trump shi ne ya sauya tsarin lafiya na Obamacare

Dazu-dazun nan ne ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi watsi da kudirin yi wa shirin tsohon shugaban kasar, Barack Obama na lafiya da aka fi sani da Obama care garanbawul.

Hakan kuwa ana ganin ba karamin cikas ya kawo wa gwamnatin shugaba mai ci, Donald Trump ba.

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo shi ne yadda ‘yan majalisar jam’iyyar shugaban ta Republican da suka hada da sanata John McCain sun taka rawar gani wajen kashe wannan batu a dandamalin majalisar.

Hakan kuwa ana ganin ba karamin cikas ya kawo wa gwamnatin shugaba mai ci, Donald Trump ba.

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo shi ne yadda ‘yan majalisar jam’iyyar shugaban ta

Nigeria: Me ya sa matasa ba sa sha'awar zaben kansu a mukamai?


Image caption

Matasa na zanga-zangar lumana a Abuja, kan damar yin takarar mukamai a shugabancin Najeriya

A kan ce mata su ne makiyan mata ‘yan uwansu, amma kuma sai ga shi matasa a Najeriya ma na bin sahu, inda ga dukkan alamu ba su bayar da cikakken goyon bayan su ga masu neman takarar shugabancin kasar.

A ranar Talata ne 25 ga watan Yuli 2017 ne gamayyar wasu kungiyoyin matasa fiye da 50 suka yi tattaki zuwa zauren Majalisar dokokin Najeriya, domin nuna rashin amincewa da yunkurin da ake zargin ‘yan Majalisar suna yi, na janye wani kuduri da zai rage shekarun da mutum zai iya yin takarar mukaman siyasa.

Matasan sun ce sun yi zanga-zangar lumana ne domin matsawa majalisar lamba su bar kudurin, wanda ake ganin zai bai wa matasa damar shiga a dama da su a harkokin shugabancin kasar.

Hakazalika sun ta tafka muhara a shafukan sada zumunta kan maudu’in #NotTooYoungToRun.

Bayan haka ne Majalisar dattawan Najeriya, a ranar Laraba 26 ga watan Yulin 2017, ta amince da kudirin da zai bai wa matasan damar takarara mukaman shugaban kasa da gwamna da dan majalisar dattawa da na wakilai.

Kudirin dai ya bai wa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Hakazalika, kudurin ya amince ‘yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan kasar.

Ko me ya sa matasa ke kashe kansu a Ghana?

Kokarin matasa na zama marubuta

‘Matasan N-Power ba su ba matsalar albashi’

Duk da wannan nasarar da matasan Najeriya suka samu, akwai masu kokwanto da kamun ludayin matasa a shugabancin.

Wani lamari ba wai a Najeriya ne kadai ba, har da kasashen yamma ma, misali Amurka, inda a yayin yakin shugabancin kasar, Matasa suka bayar da goyon bayan su sosai ga Bernie Sanders, wani tsohon da siyasar kasar.

Amma kuma idan aka yi waiwaye adon tafiya, wadanda suka kafa gwamnatin Najeriya tun farko ma matasa ne, daga kan Primiya Sir Tafawa Balewa wanda ya yi Firayi Minista a kasa da shekara 50, da Sir Obafemi Awolowo wanda a shekara 45 ya yi Primiyar yankin kudu yammacin Najeriya, haka shi ma Ahmadu Bello Sardaunar Sakwatto, wanda ya yi Primiyar yankin arewa a kasa da shekara hamsin, dai dai sauransu.

Tsohon shugaba Yakubu Gowon, wanda shi ne shugaba mafi kankantar shekaru da aka taba yi, inda a shekara 32 kacal ya shugabanci Najeriya.

To ko menene ya sa a yanzu matasa ba su da kwarin gwiwar yin takara?

Ahmed Buhari, wani matashi ne da a yanzu ke neman yin takarar shugabancin Najeriya nan da shekarar 2019, ya bayar da nasa dalilin da ya sa matasa ke zillimin zaben ‘yanuwansu matasa.

Hakkin mallakar hoto
Ahmed Buhari Facebook

Image caption

Wani matashi da ke goyon bayan ‘yanuwan sa su yi takarar mukamai

“Yanzu matsalar matasa ba sa siyasa in ba da kudi ba, duk inda kudi yake nan suke, duk da cewa yanzu a yayin gudanar da kamfe din mu, mun gano cewa, yanzu ma matasan idanun su ya bude, saboda ko sun amshi kudi ma idan Allah Ya kawo lokacin zabe, ba sa kada kuri’arsu ga wanda ya basu.”

Game da ko matasan ba sa tunanin wani cikin su na da kwarewar shugabanci, Ahmad Buhari ya ce,

“Ba komai ba ne sai don sun saba da ganin tsoffi a mulki, matasan sun kuma dade suna zaune kawai, ba tare da nuna kishin neman wani mukami ba, don haka matasa suke ganin babu abun da zasu iya musu,”

“Baya ga haka kuma matasan namu na yanzu sun taso tun suna ‘yan shekaru kalilan wadanda ke mulki a wannan lokaci, su ne har yanzu rike da kasar.” In ji Ahmed Buhari

Ahmed ya kammala da cewa matasa na bukata su san cewa goyon nasu na da fa’ida, kuma su daure su daina sanya son zuci a lamuran da ya shafi siyasa, sai dai cigaban kasa da al’ummarsu.

Ga alama dai wannan zanga-zangar lumana da matasa suka yi ya yi tasiri, ganin yadda a yanzu Majalisa ta amince da kudirin dokar da za ta ba matasa damar takarar mukamai.

Amma kuma ba nan gizo ke sakar ba, tunda ana bukata matasan su nuna kwazo wajen ganin wani nasu ya hau mukami, domin su nuna kwarewarsu wajen tafiyar da mulki.

Image caption

Sakwannin shafin BBC Hausa Facebook inda ake tafka muhawara kan wanna batu

Kamar yadda a cewar Muhammad Asheeru Babaji, wani ma’abocin BBC na shafin Facebook, wanda shi a ra’ayin sa ya ce,

“Ni matashine amma bana goyon bayan a ba wa matashi wannan dama, ta a rage shekaru, domin tsayawa takara, hujja — Matasa yawancin su basu mallaki hankalin kan su ba, misali, matasa a kasarinsu manema matane, da shaye-shaye, su ne sata, su ne harkar da duk bashi da amfani, za ka ga matasa ne, sh iyasa wadanda suka kawo tsarin mulkin duniya, suka tsara dattawa su adda mulki, saboda ana tunani in mutum ya manyanta ba za a same su da hayaniya ba.”

Dr Usman Isyaku, kuma wani mai sharhi kan siyasa a Najeriya, ya ce a ganin sa, dalilin da ya sa matasa ba sa goyon bayan ‘yanuwansu, shi ne saboda rashin kudi, suna ganin sai masu kudi ne ke takara.

A cewar Dokta Usman, babu hadin kai tsakanin matasa, musamman saboda an samu rabuwar kawuna ta fannin kabilanci da addini da bangaranci, a yayin da masu shekaru da ke takara a siyasa su ke da basirar hada kansu har su kafa jam’iyyar siyasa mai dorewa.

A ra’ayin Usman Gurama kuma, wani matashi mai sharhi kan harkokin yau da kullum a shafukan sada zumunta, dalilin da ya sa matasa ba sa samun amincewa al’umma wajen shugabanci, shi ne saboda rashin kudi.

Hakkin mallakar hoto
Usman Gurama Facebook

Image caption

Usman Gurama ya ce matasan Najeriya damban su ke da na sauran kasashe

Manyan a cewarsa, ba su sakan masu mara ba, sun riga sun dandana mulki, don haka ba sa son su saki, haka kuma ba sa sakin kudin da zai bai wa matasan damar yin takarar.

Duk da haka, Gurama ba ya goyon bayan matasa su yi shugabanci, duk da cewa shi kan sa matashi ne, ga kuma dalilansa,

“Matasan Najeriya damban su ke da na sauran kasashe,” in ji Gurama.

Ya kara da cewa, “Yawanci suna kosawa su gama karatu ne domin su yi kudi, ba wai saboda kasa ta karu da su ba, ko wata akida ta su mai inganci.”

Masu fashin baki dai sun jaddada cewa, mafi yawan al’ummar Najeriya, na da tunanin cewa abin da babba ya hango, yaro ko ya hau tsauni ba zai hango shi ba, don haka ake wa matasa kallon ba su nisan tunanin daukar shawara game da mulki.

Najeriya dai na sauraro su ga gudun ruwan shugaban su da suka zaba, watau Muhammadu Buhari, wanda ya hau mulki yana da shekaru 72, kuma an zabe shi ne bisa bukatar ganin canji a kasar.

Canji kuma na iya daukar kamanni iri-iri, ciki har da zaben matashi da zai jagoranci al’ummar kasar, kamar yadda shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi nasarar samu yardar al’ummar kasarsa a shekara 39.

BH: 'Mutum fiye da 40 ne suka mutu'


Image caption

Sojoji da ‘yan sintiri sun mutu

Wasu wadanda suka ce sun shiga dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun ce mutum fiye da 40 ne suka mutu a harin da Boko Haram ta kai wa ma’aikatan aikin hakar mai a Magumeri, ranar Talata.

Ma fi yawancin mutanen da aka kashe din sojoji ne da ‘yan sintiri ko kuma kato da gora.

Tun da farko dai sojojin kasar sun ce sojojin tara suka mutu a kokarin ceto ma’aikatan wadanda da yawansu ma’aikatan jami’ar Maiduguri ne.

Wakilin BBC Abdullahi Kaura Abubakar wanda shi ma ya ziyarci dakin ajiyar gawar, a inda ya ce ya ga gawarwakin mutane duk sun rube.

Ya ce “Biyar na ‘yan kato da gora ne a inda kuma ta shidan ta soja ce.”

A ranar Talatar ne dai kungiyar ta Boko Haram ta abka wa wata tawagar ma’aikatan aikin hakar man fetir da ke tafe cikin rakiyar sojoji da ‘yan sintiri.

Yawancin ma’aikatan sun fito daga jami’ar Maidguri ne.

Yanzu haka karamin ministan man fetir na Najeriya, Dr. Ibe Kacikwu ya sanar da dakatar da ci gaba da neman mai a yankin.

Sanchez zai koma Arsenal ranar Lahadi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sanchez ya yi hutu bayan da ya buga wa Chile Confederation Cup

Bayan da ake ta samun rahotannin da ke cewar Alexis Sanchez zai bar Arsenal a bana, Arsene Wenger ya sanar da cewar dan kwallon Chilen zai koma atisaye a ranar Lahadi.

Sanchez bai buga wa Arsenal wasannin atisayen tunkarar kakar badi da ta yi a Australia da China ba, sakamakon hutun da ya yi, bayan da ya buga wa Chile Confederations Cup.

A karshen kakar badi yarjejeniyar Sanchez za ta kare da Arsenal kuma bai saka hannu kan sabon kwantiragi ba.

Sanchez ya bukaci Arsenal ta biya shi Yuro miliyan 300 a duk mako, kafin ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya, abin da kungiyar ta ce ba za ta iya biya ba.

Hakan ne ya sa ake cewa dan kwallon zai iya komawa Paris Saint Germain ko Manchester City ko Juventus ko kuma Bayern Munich da taka-leda.

Shi ma Shkodran Mustafi zai koma atisaye a ranar Lahadi, bayan da ya gama hutun murnar lashe Confederation Cup da Jamus ta yi.

Boko Haram: An kashe ma'aikatan jami'ar Maiduguri biyar


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An ba wa rundunar sojin Najeriya wa’adin kwana 40 da su kamo shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Wasu ma’aikatan Jami’ar Maiduguri guda biyar sun mutu yayin da sojojin kasar ke kokarin kwato su daga hannun masu garkuwa da su da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya (ASUU) reshen Jami’ar Maiduguri, Dokta Dani Mamman, ya ce ma’aikatan jami’ar biyar ne suka rasu cikin ma’aikata tara da suka je aikin binciken danyen mai a yankin Tafkin Chadi.

Tun daga farko dai rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwar cewa ta ceto wasu daga cikin ma’aikatan da Boko Haram ta kama a lokacin da suka je binciken danayen mai a yankin.

A sanarwar da kakakin rundunar, Sani Usman Kukasheka, ya fitar rundunar sojin Najeriya dai ta ce sojoji tara ne suka rasu a lokacin da suke neman kwato malaman daga hannun kungiyar Boko Haram.

A hirarsa da abokin aikinmu, Aliyu Tanko, Dokta Mamman ya ce mutanen jami’ar na fatan za a samo sauran ma’aikatan jami’ar hudu da rai yayin da yake jajantawa sojin kasar game da rasa dakarunta da ta yi.

Ga hirar da Aliyu Tanko ya yi da Dokta Dani Mamman, sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraro

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaban malaman jami’ar Maiduguri ya ce: ‘An kashe ma’aikan jami’ar Maiduguri biyar’

Yadda na ji rauni a fim din Dakin Amarya — Aisha Tsamiya


Hakkin mallakar hoto
AISHA TSAMIYA

Image caption

Aisha ta ce tana daukar fim a matsayin sana’a

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa BBC cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar Dakin Amarya.

Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama – ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu.

“Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin”, in ji Aisha Tsamiya, a hirar da ta yi da Nasidi Adamu Yahaya.

Jarumar ta kara da cewa tun tana karama take sha’awar fitowa a fina-finan Kannywood “saboda suna matukar burge ni”.

A cewarta, “Na dauki yin fim a matsayin sana’a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa.”

Hakkin mallakar hoto
YOUTUBE

Image caption

Aisha Tsamiya ta ce tana jin dadin yin fim da kowane dan wasa

Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta “kuma ina zaune da kowannensu lafiya”.

“Jarumarai irinsu su Adamu (Adam A. Zango), Sadiq Sani Sadiq, Zahraddeen Sani, da dukkansu sauran jarumai suna burge ni. Haka ma mata jarumai, dukkansu ina zaune da su lafiya kuma suna burge ni”, in ji Aisha Aliyu.

Ta ce ta soma fitowa a fim din Tsamiya ne shi ya sa aka sanya mata wannan suna.

Aisha dai ta fi fitowa a fina-finan da ke nuna ta a mutuniyar kirki, wacce kuma ake tauyewa hakki.

Hakkin mallakar hoto
YOUTUBE

Image caption

Halima Atete ce uwar gida a fim din Dakin Amarya

Ana iya rayuwa da cin naman daji da 'ya'yan itace kawai?


GARGADI: Sai a yi hattara da hotunan dabbobin da aka kashe.

Al’ummar Hadza na daya daga cikin kabilun da suka dogara da farauta wajen rayuwa a duniya. Ana jin suna rayuwa ne a yankin guda a arewacin Tanzania ta hanyar cin ‘ya’yan itatuwa dangin magarya da kanya da rogon daji da kuma farautar dabbobi irin daban-daban tsawon shekara 40,000. Wakilin BBC Dan Saladino ya fita don ganin yadda suke farauta da fafutukar neman abinci, tare da tambayar ko nau’in abincin da suke ci ka iya zame wa kowa darussa.

Dan Saladino ya ce yayin da na kwanta rub da ciki, na sanya kaina ina kallon cikin wani rami mai duhu tare da shinshina kasar ciki.

Naman daji…

Sai dai na kasa yarda cewa mutum zai tura kansa ciki don ciro naman dajin da ke ciki. Mutumin dai shi ne Zigwadzee. Naman dajin kuma? Bushiya ce.

Bayan ya ba da ajiyar kwari da bakarsa da kuma gatarinsa na shan zuma ga wani abokin farautarsa, Zigwadzee ya tube riga, inda ya dauki wata gajerar sanda da aka fike ya shige cikin ramin.

A tunanina, an tura Zigwadzee ne saboda shi ne mafi kankanta, amma kuma na fahimci cewa an tura shi ne saboda bajintarsa, don kuwa akwai yiwuwar samun macizai ko ma ita bushiyar ta harbo kaya.

Har a wannan lokaci, ganye ne cimar kabilar Hadza, kuma sukan tsinki ‘ya’yan itatuwa, lokacin da suke tafiya cikin Kungurmin dajin savannah, wanda ke cike da kaya da busassun ciyayi.

Image caption

Matan kabilar Hadza kan tattaro ‘ya’yan itace da dangin doya, a matsayinsu na abincin yau da kullum

Muna hako doya mai taushi, mu gasa a wuta domin ci, mun kuma samu bishiyar kuka, inda muka yi ta shan ‘ya’yanta, wasu farare da ke dauke da dumbin sindaran Bitamin C.

Image caption

‘Ya’yan bishiyar kuka na da dimbun sinadarin Bitamin C

Masana ilimin tarihi sun gano cewa mutanen Hadza sun yi shekaru aru-aru suna neman abin kai wa baki, amma ba su taba fama da matsalar yunwa ba, saboda yanayin cin abincinsu ya samu kwarin gwiwa da yalwar ire-iren abincin da suke da su a yankin, ga su kuma gwanayen farauta.

Ga cima a wadace sai dai ni ba ma na iya gane wanne ne abin ci, amma sai ka ga yaran kabilar Hadza, wadanda wasunsu ba su wuce shekara hudu ba, sun je sun samo.

Daga can nesa sai na fara jiyo muryar Zigwadzee, inda ya kutsa cikin ramin da ya yi nisan mita biyu karkashin kasa, ga kuma wasu hanyoyi iri-iri, da bushiyar takan buya.

Bayan ya gane inda dabbar take ta hanyar bin sawunta a ramin, sai ya bayar da umurni ga wadanda ke waje su toshe sauran ramukan, don kada ta tsere.

Can bayan minti 40 sai ya fito daga ramin, budu-budu da kura da kudaje sun baibaye shi, yana kuma shirin sake kutsawa inda bushiyar ta makale a ciki.

Image caption

Ana dasa sanduna jikin bishiyar Kuka, domin saukin hawa a debo zuma a cikin amiya.

Duk da yake, kabilar Hadza sun kai yawan mutum dubu daya mata da maza da yara, cikinsu akwai mafarauta 200 zuwa 300 wadanda ba sa noma kwata-kwata, ko kuma wani abu mai alaka da noma.

Wadannan mafarautan suna mamakin manoma kwarai da gaske, inda wani cikinsu yake tambaya ta:

“Wai ta yaya mutum zai tsaya a gona cikin rana kwana da kwanaki yana jiran abinci ya tsiro? bayan ga ‘ya’yan itatuwa nan birjik a daji, ga zuma nan da yawa da za ka iya sha, ko kuma ka shiga rami cikin sa’a daya, ka kama bushiyar da za ta ciyar da rukunin jama’a guda?”

Hakan shi ne yadda iyayenmu ke neman abincin su a da. Nau’in abincin da Zigwadzee da ‘yan’uwansa na kabilar Hadza ke ci, shi ne abin da ya rage na alakar abincinmu na yanzu da na mutanen da ke ci, wanda a cewar masanan kimiyya, ya nuna yadda tsarin taswirar cikin mutum ya sauya a yanzu, ciki har da nau’o’in bakteriyar da ke cikin dan’adam.

Haka kuma kabilar Hadza na da mafi yawan bakteriyar ciki a tsakanin dan’adam, saboda irin nau’in abincin da suke ci.

Image caption

Sai an yi amfani da baka mai dafi wajen harbin dabbobi da suka kai girman alfadari

Image caption

Jakin dawa ya fi saukin farauta lokacin rani, saboda babu wuraren shan ruwa sosai…

Image caption

… amma kuma sun soma bacewa, saboda yadda manoma ke tsorata su

Cikin abokan tafiyar tawa har da Tim Spector, Farfesa a fannin kwayoyin halitta na jami’ar Kings College da ke London, wanda ke ta kwakwar sanin ko idan ya koma cikin nau’in abincin kabilar Hadza, cikinsa ka iya zama irin nasu.

Don haka ne ya debi samfurin kashinsa don yin gwaji, bayan ya kwana uku yana cin irin abincinsu, da nufin duba ko nau’in bakteriyan da ke jikinsa ya sauya.

Sakamakon gwajin ya nuna nasara sosai, saboda bayan kwana uku kacal da cin abincin kabilar Hadza, sai ya samu karin bakteriyar da kashi 20 cikin 100, wanda hakan ke nuna ya samu karin lafiya matuka.

Image caption

Mafarauta sai sun yi tafiyar kilomita da dama bayan sun kama nama, domin raba naman da aka kamo

Sai an shafe tsawon shekaru, kafin Farfesa Spector ya kammala bincikensa kan alfanin nau’in abincin da mutane ke ci a zamanin yanzu, amma cikin gaggawa ana neman masaniya kan irin abincin da kabilar Hadza ke ci, saboda al’amura sun fara sauya musu.

Shekara da shekaru manoma na ci gaba da mamaye filaye, har cikin yankunan al’ummar Hadza, kuma a shekara goma da ta gabata, sukan mamaye kadada 160 na filayensu duk shekara, inda suka yanke bishiyoyi da ciyayi domin shuka, da kuma bai wa shanu abinci. Lamarin da ya janyo korar namun daji iri-iri har 30 da kabilar Hadza suka shafe shekara dubu suna farautarsu a matsayin abinci.

Image caption

Wani burgu kafin a babbaka shi a wuta

A ganina, abu mafi ban mamaki shi ne yadda manyan kamfanonin abinci suka iya riskarsu, ‘yar tafiya ta minti 30 daga ramin bushiyar nan, sai ga wata bukka dauke da makunshin biskit da lemon kwalba, ana sayarwa.

Sai da na yi tafiyar sa’a tara a mota kirar Jeep kafin na gano yankin wannan al’umma, da na taras manyan kamfanonin duniya sun riga ni isowa.

Image caption

Lemon kwalba ya kai ga yankin kabilar Hadza

Zigwadzee dai na daukaka al’adun al’ummar Hadza, wadanda ka iya janyo karewar namun daji kamar bushiya.

Mafarautan kabilar Hadza na taimakawa junansu, saboda suna da hadin kai da zumunci.

Ba su da wani jagora ko mai fada-a-ji tsakaninsu, kuma musammam a kan nama, babu wani tsari wajen rabo, ba kuma lallai ne kowa ya samu kashi daidai da na dan’uwansa ba.

Ana dafa kayan cikin naman dajin da aka kama ne kuma a cinye nan take, sannan a kai sauran naman sansanoni don rabawa.

A yayin da nake kallonsu, ina kuma dan gutsurar naman bushiya, sai na lura da wani abin sha’awa;

Farautar, da kuma abincin da nake ci, sun ba ni wata alaka da mutanen da.

Duk da rashin Mendy Man City ta lallasa Real Madrid 4-1


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Danilo (a hagu) zai iya taka leda a baya ta gefe ko kuma a tsakiya.

Manchester City ta lallasa Real Madrid da ci 4-1 a Los Angeles a wasan sada zumunci da suka buga domin shirin tunkarar kakar wasa ta bana.

Kociya n City Pep Guardiola ya ce Benjamin Mendy wanda ya saya kan kudi fam miliyan 52 ba zai taka leda na mako biyu ba bayan wasan na Amurka.

Mutun 93,000 ne suka kalli yadda City ta samu nasararta ta farko a wasannin shirin sabuwar kaka da kwallaye daga Nicolas Otamendi da Raheem Sterling da John Stones da kuma dan shekara 17, Brahim Diaz.

A rashin Mendy, Danilo ya buga wasansa na farko a filin wasan Los Angeles Memorial Coliseum, inda mai shekara 26 din wanda dan asalin kasar Brazil ne ya buga baya ta gefen hagu.

Ya dai fuskanci tsohon kulob dinsa bayan Man City ta saye shi kan kudi fam miliyan 26.5.

Manchester City ta kashe sama da fam miliyan 200 a lokacin bazarar nan kan Kyle Walker (fam miliyan 45) da Bernardo Silva (fam miliyan 43) da Ederson Moraes (fam miliyan 43) da Benjamin Mendy (fam miliyan 52) da kuma Danilo (fam miliyan 26.5).

Nigeria: EFCC ta kwato 'naira biliyan 329 daga kamfanonin mai'


Hakkin mallakar hoto
EFCC

Image caption

An dade ana zargin cewar ana tafka almundahana a harkar man Najeriya inda kasar ta fi samun kudaden shiga

Hukumar yaki da cin hanci da rshawa ta Najeriya EFCC, ta ce ta kwato kimanin naira biliyan 329 ($1.4 biliyan) da wasu kamfanonin mai suka karkatar tare da hadin gwiwar kamfanin mai na kasa na NNPC.

Wata sanarwar da ta fitar ta kara da cewar an kwato kudaden ne tsakanin Yulin 2016 zuwa watan Yulin 2017 bayan wani korafi da ta samu kan zargin aikata ba daidai ba.

Hukumar ta ce bincike ya nuna cewar kamfanonin sun karbi mai da yawa daga gwamanti ba tare da biyan kudi yadda ya kamata ba.

Sanarwar ta ambato mai magana da yawun hukumar, Wilson Owujaren, yana cewar kamfanonin man sun hada da NNPC da Conoil Plc da Total Plc da OVH Energy da Oando Plc da Forte Oil and Gas da MRS Oil Plc da kuma NIPCO Oil Plc.

Kawo yanzu babu daya daga cikin kamfanin da ya ca uffan game da sanarwar ta EFCC.

An dade ana zargin cewar ana tafka almundahana a harkar man Najeriya inda kasar ta fi samun kudaden shiga.

Kakakin EFCC din ya ce takardar koken da aka tura wa hukumar EFCC ta yi zargin cewar kamfanonin da ke sayar da man sun yi sama da fadi da naira biliyan 40 tare da shugabannin NNPC.

Daga nan ne aka mika batun ga wata runduna ta musamman wadda ta gudanar da bincike a cikin sirri, in ji Mista Owujaren.

Ya kara da cewa bayanan da jami’anmu suka samu sun nuna cewar gwamnatin tarayya na bin kamfanonin man bashin naira biliyan 91.5 tsakanin 2010 zuwa 2016.

“Da aka zurfafa bincike kan zargin, sai aka gano cewar kamfanonin na ci gaba da karbar mai daga gwamnati ba tare da biyan kudi kamar yadda dokokin bashi na NNPC/PPMC suka tanada ba.

Karin bincike kan wannan ya sa an ganon naira biliyan 258.9,” in ji kakakin na EFCC.

Mista Uwujaren ya yi bayanin cewa jumullar bashin ta tsaya ne kan naira biliyan 349.8.

Wannan ne ya sa kawo yanzu bashin da ya yi saura ya kasance naira biliyan 20.7.

Wadannan kamfanoni na yin huldar kasuwanci dadab daban na kamfanin NNPC, ciki har da yi masa dillancin danyan mai da kuma batun shigo da tataccen man fetur kasar.

Amurka ta saka wa jami'an Venezuela 13 takunkumi


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ana zargi Mr. Maduro dan son yin mulkin kama-karya.

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi fatali da takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wasu manyan ‘yan siyasa da jami’an sojin kasarsa goma sha uku.

Amurka dai ta ce ta dauki matakin domin nuna wa Mr. Maduro cewa da gaske take a barazanar ta yi na kakaba wa Venezuela takunkumi karya tattalin arziki cikin sauri idan ya ci gaba da shirinsa na gudanar da wata kuri’ar da aka shirya yi ranar Lahadi mai zuwa domin kafa wata sabuwar majalisar dokoki.

Wadanda aka kakabawa takunkumin dai sun hada da shugabannin rundunonin soji da ‘yansandan kasar da daraktar hukumar zabe ta kasa, da da kuma mataimakin shugaban kamfanin mai na kasar kazalika da wani tsohon mataimakin shugaban kasar bisa zarginsu da hannu dumu-dumu wajen tafka almundaha da kuma keta hakkin bil’adama.

Kasar ta Amurka haka kuma ta bukaci shugaban na Venezuela da ya yi watsi da shirinsa da gudanar wani zaben ‘yan majalisar dokoki masu ikon sake rubuta kundin tsarin mulki; da ke jawo takaddama a kasar.

Takunkumin dai ya zo ne rana guda da soma wani yajin aikin gama-gari na kwanakki biyu da ‘yan adawa suka kira domin kara hurawa shugaban wuta ya soke shirin zaben sabbin ‘yan majalisar.

Hakkin mallakar hoto
JUAN BARRETO

Image caption

Mutum daya ya rasa ransa a ranar farko ta yajin aiki.

Madugun ‘yan hamayyar Leopoldo Lopez wanda yanzu ake yi wa daurin talala a gidansa; ya yi magana da magoya bayansa ta wani faifan bidiyo.

”Ina son fada wa daukacin ‘yan Venezueala cewa wannan fadan ya soma ne a kan tituna, kuma haka ya kasance a kan tituna kuma zai ci gaba da gudana kan tituna. Dole mu ci gaba da shi har sai mun samu ‘yanci, da wanzuwar dimokradiyya da kuma zama lafiya ga dukkanin ‘yan Venezuela”

Sai dai Shugaba Maduro ya lashi takobin gudanar da zaben na ranar Lahadi domin zabar sabuwar majalisar mai ikon sake rubuta kundin tsarin mulki kuma ta maye gurbin wadda ake da ita yanzu da ke karkashin jagorancin ‘yan adawa.

Ya ce yin hakan ne zai kawo zaman lafiya bayan kwashe watanni hudu ana zanga-zangar kin jinin gwamnati wadda ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da dari daya.

Me ya sa ake rikici kan masallacin Kudus?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Majami’u daban-daban na kiristoci ne ke ibada a cocin

Ana ci gaba da tada jijiyar wuya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa game da makomar masallacin Kudus, daya daga cikin lamuran da suka fi ko wanne ce-ce-ku-ce a gabas ta tsakiya.

Birnin Kudus na da muhimmanci ga addinin Yahudawa da na Kiristoci da kuma na Musulmi, addinai ukun da ke da nasaba da Annabi Ibrahim (AS).

Kudus- Suna ne da yake da jan hankali Musulmi da Kiritoci da Yahudawa a daruruwan shekarun da suka shafe suna zama tare da kuma ce-ce-ku-ce kan birnin.

A harshen Yahudanci ana ce wa birnin Yerushalayim kuma a larabci ana ce masa al-Quds, yana daga cikin biranen da suka fi dadewa a tarihi.

Sau da yawa an ci birnin da yaki tare da lalata shi.

Kazalika an sake gina shi sau da yawa. Ko wani mataki na kasan birnin na dauke da wani bangare na tarihin birnin Kudus.

Duk da cewar duk birnin ne silar daya daga cikin abubuwan da suke jawo ta da jijiyar wuya tsakanin mabiya addinan uku, dukkansu sun yi tarayya kan girmama wannan wuri mai tsarki.

Tsohon birnin Kudus yana tsakiyar birnin ne a yanzu inda kwaroro-kwaroro masu yawa da kuma tsarin gine-gine na tarihi sun bambance bangarorin Kiristoci da na Musulmai da na Yahudawa da kuma na Aarmeniyawa.

Tsohon birnin yana kewaye ne da wata ganuwa mai kama ta dutse kuma tana dauke da wasu wurare mafiya tsarki ga al’ummun duniya.

Ko wacce unguwa na wakiltar al’ummarta ne. Kiristoci na da anguwanni biyu saboda Armeniya ma Kiristoci ne kuma anguwarsu – wacce ta fi karanci cikin hudun – daya ce daga cikin tsoffin cibiyoyin Armeniyawa a duniya.

Wani abu ne na daban saboda al’ummar Armeniyawa sun adana al’adarsu cikin Majami’ay St James wadda ta kunshi da yawa daga cikin unguwarsu.

Majami’ar

A cikin unguwar Kiristoci akwai Majami’ar da ake ce wa Church of the Holy Sepulchre a turance, wadda take da muhimmanci ga Kiristoci a fadin duniya. Majami’ar na wani wuri da aka yi imanin cewar yana da alaka da labarin Annabi Isa (AS).

Da yawancin Kiristoci sun yi imanin cewar an gicciye Annabi Isa ne a wurin nan tsaunin Golgotha, ko kuma tsaunin Calvary, inda suka yi imanin cewar an binne shi yana cikin inda ake ce wa sepulchre din, kuma nan ne suka yi imanin cewar ya tashi.

Wakilai daga majami’u daban-daban, ciki har da Cocin Girka da ta darikar Katolika da ta Armeniyawa da ta Kibdawa ne suke gudanar da lamuran cocin.

Majami’ar daya ce daga cikin wuraren ibada ga miliyoyin Kiristoci da ke zuwa bauta inda suka yi imanin cewar an bunne Annabi Isa (AS) domin neman kwanciyar hankali da kuma tabarruki ta addu’a a wurin.

Masallacin

Unguwar Musulmai ita ce unguwa mafi girma daga cikin unguwanni hudu kuma a cikinta akwai Qubbat al-Sakhrah da massalcin Alaqsa da ke kan wani tudu wanda Musulmi suka fi sani da Haram al-Sharif, ko kuma wuri mai tsarki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dubun dubatan Musulmai ne ke sallar juma’a a harabar masallacin al-Aqsa a watan Ramadan

Masallacin shi ne masallaci na uku a tsarki cikin addinin Musulunci kuma yana karkashin gudanarwar wani kwamitin amintattu da ake kira Waqf.

Musulmi sun yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya taho nan daga Makka a daren Isra’i da Mi’iraj kuma ya ja dukkannin annabawa sallah.

Wasu ‘yan taku kadan daga wannan wuri a Qubbat al-Sakhrah akwai wani dutsen da Musulmi suka yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya tashi zuwa sama bayan sallar.

Musulmai sukan ziyarci wannan wuri mai tsarki a ko wane lokaci cikin shekara, amma ko wacce ranar Juma’a a cikin watan Ramadan dubun dubatar musulmi sukan zuwa domin su yi sallah a masallacin.

Bangon

A cikin unguwar Yahudawa akwai wani katanga ta yammaci da ake ce wa Kotel, ko kuma katangan yammaci, saurn katangan hana zaizayar tudun da ada wurin ibadan Yahudawa ke zaune.

A cikin wurin Ibadar akwai inda ake ce wa Holy of Holies a turance, wato wuri mafi tsarki a addinin Yahudanci.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yahudawa suna fuskantar bangon yamma ne domin gabatar da addu’o’insu

Yahudawa sun yi imanin cewar nan ne tushen inda aka halicci duniya, kuma inda annabi Ibrahim (AS) ya nemi ya yi hadya da dansa annabi Is’hak (AS). Wasu da dama kuma sun yi imanin cewar inda Qubbat al-Sakhrah yake a yanzu nan ne wuri mafi tsarki a addininsu wanda ake ce wa Holy of Holies.

A yau katangar yammaci ita ce wuri mafi kusa da Yahudawa za su iya ibada ga wuri mafi tsarki a gunsu da ake kira Holy of Holies.

Limamin Yahudawa na katangan yammaci shi yake lura da lamura a wanna wuri, kuma a ko wacce shekara miliyoyin baki kan zuwa wurin katangar. Yauhudawa daga fadin duniya sukan ziyarci wannan wuri a lokacin hutun Yahudawa da ke ce wa High Holidays a turance domin yin addu’a da kuma tunawa da tarihinsu.

Rikicin Baya bayan nan

Ranar 14 ga watan Yulinnan ne wasu larabawa ‘yan Isara’ila suka kashe ‘yan sandan Isra’ila biyu ta hanyar bude musu wuta a cikin harabar masallacin.

Saboda haka sai Isra’ila ta tsaurara matakan tsaro a hanyar shiga masallacin. Matakan sun hada da kafa na’urar gano karfe.

Amman wanna matakin bai zo yi wa Falasdinawa dadi ba domin sun fito suna zanga-zangar kin wannan mataki da suke gani a matsayin wani yunkuri na Isra’ila na neman iko da masallacin.

Kuma an samu arangama tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Isra’ila kan wannan matakin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tun daga ranar da hukumomin Isra’ila suka gindaya sabbin matakan tsaro a hanyar masallacin ne aka fara sallar juma’a a wajen masallacin kudus

A dai-dai lokacin da ake zaman dar-dar kan lamarin sai Isra’ila ta kafa na’urar nada bidiyo (CCTV) a masallacin.

Wannan ya sa kwamitin amintattun da ke lura da masallacin ya ce Musulmai su kaurace wa sallah cikin Masallacin har sai Isra’ila ta janye matakan tsaron ta gindaya.

Matakan da Isra’ila ta dauka sun sha suka daga Musulmai a sassan duniya.

A ranar Litinin kuma, Majalisar ministocin Frayim ministan Isra’ila, Benyamin Netanyahu, ta amince da a janye na’urar gane karfen da aka saka a hanyar shiga masallacin, amman za ta ci gaba da sa ido daga nesa.

Amman kwamitin amintattun da ke lura da masallacin ya ce Musulmai za su ci gaba da kaurace wa masallacin domin Isra’ila ba ta cire na’urar nade bidiyo (CCTV) ba.

Isra’ila ta mamaye wurin da ke gabashin birnin Kudus ne tun yakin gabas ta tsakiya na shekarar 1967.

Pakistan: An yi wa wata fyaden ramuwar gayya


Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Image

Image caption

Wani mutumin yankin yana nuna gidan da aka yiwa matashiyar fyade a kauyen Muzaffarabad, na garin Multan

‘Yan sanda a Pakistan sun cafke mutum 20 a garin Multan, kan bayar da umarnin a yi wa wata matashiya fyade, a matsayin ramuwar gayya kan zargin da ake yi wa dan uwanta na aikata fyaden.

Yan sanda sun ce iyalan ‘yan matan biyu suna da dangantaka, kuma duka bangarorin biyu ne suka hada kai wajen yanke shawarar abin da ya kamata a yi.

” Wata kungiyar dattawan kauye ce da ake yi wa lakabi da Jirga ta bayar da umarnin da a yi wa budurwar mai shekaru 16 fyaden a matsayin ramuwar gayya,” jami’in dansanda Baksh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya ce wani mutum ne ya kai kara wurin majalisar hukumar kauyen cewa an yi wa kanwarsa mai shekara 12 fyade.

Hukmar sai ta bai wa mai kai karar umarnin shi ma ya je ya yiwa kanwar wanda ake zargin fyade a matsayin ramuwar gayya- wanda ‘yansanda suka ce sai ya aikata.

Jaridar ‘Dawn’ ta kasar Pakistan ta bayar da rahoton cewa an tliastawa yarinyar bayyana a gaban taron jama’a har da iyayenta, inda aka yi mata fyaden.

Daga bisani uwayen ‘yan matan biyu sun gabatar da kara a caji ofis na ‘yansanda.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

Wani daki a kauyen Muzaffarabad a Pakistani inda aka bayyana an yiwa matashiyar fyade

Binciken da likitoci suka yi ya tabbatar da cewa duka ‘yan matan an yi musu fyade.

Wani jami’in ‘yansanda Ahsan Younas, ya shaida wa BBC cewa yarinyar ta farko da aka yi wa fyaden za ta kai tsakanin shekara 12 zuwa 14, yayin ta biyun wacce aka yi ramuwar gayyar a kan ta za ta kai tsakanin shekara 16 zuwa 17.

Ya kuma ce ‘yansanda sun yi rajistar koke-koke kan mutane 25, kana wanda ake zargi da yi wa ‘yar shekara 12 fyade ya gudu.

Kungiyar dattawan da ake wa lakabi da Jirga, ana kafa ta ne don shawo kan matsaloli ko rikici a kauyukan kasar Pakistan.

Amma kuma hukumomi na daukar irin wannan kungiya a matsayin haramtacciya—wacce ta sha yanke hukunce-hukunce masu cike da takaddama.

Hakkin mallakar hoto
BHASKER SOLANKI/BBC

Image caption

Mukhtar Mai, a shekara ta 2011, da aka yi wa fyaden taron dangi a bisa umarnin kungiyar dattawan yankinsu

Ko a shekara ta 2002 wannan kungiya ta Jirga ta taba bayar da umarni a yi wa wata mata mai suna Mai Mukhtar mai shekara 28 fyaden taron dangi, bayan da aka zargi kanenta mai shekara 12 da yin mu’amala da matar da da girme shi.

Ms Mai ta kai karar wanda ya yi mata fyaden gaban kuliya – matakin da ba kowa ke da karfin gwiwa dauka ba saboda fargabar nuna kyama.

Nigeria ta rasa sojoji 9 sun garin kubutar da masana Kimiyya


Hakkin mallakar hoto
Nigeria Army

Image caption

An dai kai gawwakin sojojin tare da wadanda suka raunata zuwa wani asibiti a Maiduguri

Rundunar sojan Najeriya ta ce kawo yanzu sojojinta 9 sun mutu tare da wani farar hulla daya a garin kubutar da wani ayarin masana masu bincike da mayakan Boko Haram suka kama a cikin wani kwanton bauna a jihar Borno.

Sai dai ta ce sun yi nasarar kubutar da yawancin mutanen, ko da yake sai nan gaba ne za ta fitar da cikakken bayani a kan batun.

A ranar Talata ne ‘yan Boko Haram suka yi wa mutanen da suka haka da malaman jami’ar Maiduguri kwanton bauna a kauyen Jibi a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojan kasar Brigadiya-Janar Sani Usman Kukasheka ya fitar ranar Laraba da dare, sojojin sun ce duk da wannan hasarar da suka yi, kokarin binciken inda sauran wadanda ake garkuwa da sun na ci gaba da zimmar kubutar da su.

Sanarwar ta ce sojojin sun kuma kashe tare da raunata adadi mai yawa na mayakan kungiyar Boko Haram da ake zargi da sace mutanen.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Daga cikin sojojin 9 da suka kwanta-dama akwai wani mai mukamin leftanant.

Haka ma sojojin sun ce sun kwato motoci guda hudu da suka hada da motoci 2 kirar hilux da suka masu garkuwar kwace daga ma’aikatan kamfanin na NNPC da wata daya ta mayakan sa-kai na Civilian JTF.

Sai dai sanarwar bata bayyana ko mutane nawa sojojin suka kubutar ba daga cikin masu binciken kawo yanzu da kuma ko nawa ake nema.

Masana kimiyyar albarkatun kasa goma ne daga Jami’ar Maiduguri kamfanin man na NNPC ya bai wa aikin wani bincike kan danyen mai a yankin dake daura da tafkin Chadi kuma kafin sanarwar sojojin ya tabbatar cewa an kubutar da uku daga cikinsu.

Sai dai Wani ganau ya shaida wa BBC cewa an kashe da dama daga cikin masu binciken da wadanda ke yi musu rakiya kuma akwai wasu da har yanzu ba a san inda suke ba.

Wasu majiyoyin kuma sun ce daga cikin sojojin da aka kashe a cikin arangamar kubutar da su dai har da wani mai mukamin leftenant.

Nigeria: Za mu yi wa jihohi zamiyar kudaden bashi


Hakkin mallakar hoto
Google

Image caption

Hukumar tarawa da rabon arzikin Nijeriya ta ce tana bin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi basussukan kudade da dama

Hukumar tarawa da rabon arzikin kasa ta Nijeriya, ta bayyana aniyar zame basussukan da suka taru a kan jihohi da kananan hukumomi, da kuma wasu ma’aikatu da hukumomi na gwamnatin.

Ta ce ya kamata a ce jihohin sun shigar da kudaden a asusun rabon arzikin kasa, amma sun gaza yin hakan.

Kudin dai kimanin Naira biliyan 115, sun hada da harajin da jihohin da ma’aikatun suka karba amma suka kasa zubawa a asusun tarayya tsawon kimanin shekara 10.

Malam Hassan Mahe Abubakar, daraktan kula da kudaden shiga da ba na man fetur ba na hukumar, ya shaida wa BBC cewa wannan haraji na daya daga cikin hayoyin samun kudin shiga.

Ya ce wadannan kudade su ne ake tattarawa duk wata ana rarrabawa tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi.

”Kudaden da kasar ke samu daga bangaren albarkatun man fetur yanzu al’amura sun ja baya”, don haka biyan wadannan basussuka na da matukar muhimmancin”, in ji Malam Mahe.

Hukumar dai ta ce akwai jihohin da har yanzu suka ki amincewa su tattauna da jami’an hukumar da suke zagaya wa, domin tabbatar da kididdigar da aka ba ta.

Sai dai a wasu lokuta gwamnatocin jihohin da kananan hukumomi kan koka da rashin biyan su kudaden da suka yi wasu ayyukan gwamnatin tarayya a jihohin su.

Nigeria: Boko Haram ta sako ma'aikatan NNPC


Hakkin mallakar hoto
AP

Image caption

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuar sama da mutum 30,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya tabbatar da kubutar da wasu daga cikin ma’aikata goman da ya dauki nauyinsu zuwa binciken mai a yankin Tafkin Chadi.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da sace masanan, wadanda wasunsu suka fito daga Jami’ar Maiduguri.

Rundunar sojin kasar kuma ta ce dakarunta suna can suna farautar mayakan na Boko Haram.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kuka-sheka ya shaida wa BBC cewa dakarunsu sun yi nasarar kubutar da wasu, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu.

Sai dai bai fadi adadin wadanda aka kubutar ba, ko kuma wadanda suka mutu.

Shi ma kakakin kamfanin NNPC, Ndu Ughamadu ya ce an kubutar da uku daga cikin jami’an safiyo da masu nazarin halittun karkashin kasa da aka sacen.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato rundunar sojin Najeriya na cewa ta gano gawar ma’aikatan tara tare da ta farar hula daya da ke tare da su.

NNPC ya ce masu nazarin halittun karkashin kasar sun shafe sama da shekara guda suna bincike kan abin da ya bayyana da tarin albarkatun mai a yankin Tafkin Chadi.

An yi awangaba da mutanen ne bayan wani kwantan bauna da aka yi musu a kusa da kauyen Jibi.

Mista Ndu Ughamadu ya ce mutanen sun “hada da malaman jami’a da direbobi da sauran ma’aikata”.

A baya-bayannan dai kungiyar Boko Haram ta matsa da kai hare-hare, duk kuwa da ikirarin da hukumomin Najeriya ke yi na cewa sun karya kashin bayanta.

Akalla mutum 62 aka kashe a birnin Maiduguri da kewaye tun farkon watan Yuni. Sha-bakwai kuma sun rasa rayukansu a birnin a mako guda a wannan watan.

Ko a ranar Litinin ma wasu ‘yan kunar bakin wake biyar sun kai hari wasu sansanonin ‘yan gudun hijira biyu a Maiduguri, inda suka kashe mutum bakwai.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuar sama da mutum 30,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da wasu fiye miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.

Nigeria: Majalisa tana neman rage karfin shugaban kasa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An samu takun saka tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa a kwanakin baya

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kuduri da ke neman rage karfin shugaban kasar wajen tsarawa da kuma amincewa da doka.

‘Yan majalisar sun amince a ragewa shugaban kasar karfin ikonsa na hawa kujerar na ki kan kudurin dokokin da majalisar ke tsarawa, a wani bangare na gyaran da suke yi wa tsarin mulkin kasar.

Masu sharhi na ganin majalisar na kokarin rage ikon da shugaban kasa ya ke da shi da kuma mayar da shi hannunta.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun-saka tsakanin bangaren zartarwa da kuma na majalisa kan wasu batun nadin mukamai.

Majalisar ta kuma amince da kudurin da ke neman gindaya lokaci mafi kankanta da shugaban kasar zai mika sunayen ministocin da zai nada ga majalisar.

Har wa ya daya daga cikin kudurorin ya bai wa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Haka zalika, kudurin ya amince ‘yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar dokokin kasar.

‘Yan majalisar sun kuma amince da dan takara mai zaman kansa.

A ranar Talata ne dai matasa suka yi gangami a kan titunan Abuja, babban birnin kasar, domin yin tur da yunkurin watsi da kudurin, kuma suka yi ta tafka muhara a shafukan sada zumunta kan maudu’in #NotTooYoungToRun wato babu wanda ya yi kankanta wurin tsayawa takara.

Mambobi 86 daga cikin ‘yan majalisar sun amince da kudurin gyara tsarin mulkin yayin da 10 daga ciki suka ki amince wa da shi kuma dan majalisa daya ya ki kada kuri’a.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya gana da karin gwamnoni


Hakkin mallakar hoto
Borno State Government

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da karin wasu gwamnonin kasar da suka masa ziyara a London inda ya ke jinya.

Hakkin mallakar hoto
Borno State Government

Image caption

Buhari yana gaisa da wasu gwamnoni da suka kai masa ziyara

Cikin gwamnonin bakwai da suka kai wa Shugaba Buharin ziyara har da gwamnonin PDP.

Hakkin mallakar hoto
Borno State Government

Image caption

Shugaba Buhari ya dauki hoto da gwamnonin da suka kai masa ziyara.

Gwamnonin da suka ziyarci shugaban na Najeriya sun hada da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, da Dave Umahi na jihar Ebonyi, da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, da Kashim Shatima na jihar Borno, da Samuel Ortom na jihar Benue, da kuma Abiola Ajumobi na jihar Oyo.

Hakkin mallakar hoto
Borno State Government

Image caption

Buhari yana cikin nishadi a wannan hoton

Shugaba Buhari yana cikin nishadi a wannan hoton.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Presidency

Image caption

Shugaba Buhari da matarsa Aisha da kuma wata matar

Baya ga gwamnonin, shugaba Buhari ya kuma gana da matarsa Aisha.

Nigeria: Rikicin kabilanci ya sa an tura jirgin yaki Taraba


Hakkin mallakar hoto
Nigerian Air Force

Image caption

Jirgin sojin zai je daniyyar taimakawa dakarun kasa

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta tura wani jirgin saman yakinta jihar Taraba da zummar dawo da zaman lafiya.

Wata sanarwa da ta fitar ta ce “ta tura daya daga cikin jirage masu saukar ungulu karamar hukumar Takum da ke jihar domin tallafawa dakarun da ke kasa a yunkurin tabbatar da tsaro a yankin”.

A cewar sanarwar, aikawa da jirgin zai hana bangarorin da ke fada da juna sake gwabzawa.

Ta kara da cewa jirgin ya soma shawagi a yankin Mambilla da zummar wanzar da tsaro.

Daruruwan mutane ne ake fargabar sun mutu a tashin hankalin da ya barke a makon jiya tsakanin Fulani da Mambilawa a karamar hukumar Sardauna a kwanakin baya.

Fulanin sun zargi gwamnatin jihar da hada baki da Mambillawa wurin far musu da yaki, zargin da gwamnatin ta musanta.

Sai dai babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ke kula da jihar ta Taraba, ya bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a matsayin “kisan-kare-dangi”.

Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a fadar Sarkin Mambila da ke jihar ta Taraba yayin wani taro da shugabannin al’ummomin yankin.

Ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila.

A cewarsa, “An yanka kananan yara ‘yan shekara biyu, an kashe mata masu ciki; abin da aka yi musu ya fi abin da ‘yan Boko Haram ke yi, domin ‘yan Boko Haram ba sa kashe kananan yara. Niyya aka yi ta yi musu kisan-kare-dangi”.

Rundunar sojin saman ta ce nan gaba kadan za ta tura jirgi mai saukar ungulu Kafanchan da ke jihar Kaduna domin tallafawa dakarun kasa da ke yankin.

Shi ma wannan jirgin za a tura shi ne a wani mataki na samar da zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Madrid za ta kara da Man City a Amurka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real da City za su kece raini a International Champions Cup a Amurka

Kungiyar Real Madrid za ta kara da Manchester City a gasar International Champions Cup a ranar Alhamis a Amurka.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin za su kara a gasar ta International Champions, kuma a wasan farko da suka yi a Australia kaka biyu da ta wuce, Real ce ta doke City 4-1.

Cikin haduwa hudu da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu, Real Madrid ta ci wasa biyu sannan suka yi kunnen doki a karawa biyu.

A gasar bana Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 2-0, sannan United ta yi nasara a kan Madrid a bugun fenariti, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1.

Nigeria: Majalisa ta amince da kudirin takarar matasa


Image caption

A ranar Talata ne dai matasan suka yi gangamin nuna goyon baya ga kudurin ba matasa damar takarar mukaman siyasa a Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin da zai bai wa matasa damar takarara mukaman shugaban kasa da gwamna da dan majalisar dattawa da na wakilai.

Kudirin dai ya bai wa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Haka zalika, kudurin ya amince ‘yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan kasar.

A ranar Talata ne dai matasa suka gangami a kan titunan Abuja babban birnin kasar domin yin tur da yunkurin watsi da kudurin kuma suka yi ta tafka muhara a shafukan sada zumunta kan maudu’in #NotTooYoungToRun.

A zamansu ta ranar Laraba, ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun kada kuri’u kan wasu kudurori na yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.

86 daga cikin ‘yan majalisar sun amince da kudurin yayin da 10 daga cikin suka ki amince da shi kuma dan majalisa daya ya ki kada kuri’a.

Nigeria: An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Buhari ya mayar da batun abin dariya, saboda jahilcin wanda ya sanya wa karensa sunansa

A Najeriya, hukumomi sun kori wata kara da aka shigar ana tuhumar wani mutumi mai shekara 41, wanda ya sanya wa karen sa sunan shugaab Muhammadu Buhari.

An kama Joachim Iroko, wani dan kasuwa da ake cewa Joe Fortemose Chinakwe, a shekarar 2016, bisa zargin sa da neman tayar da rikici a kasar.

Wani alkali a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar ne ya yi watsi da karar, inda ya ce masu shigar da karar ba su bayar da kwakkwarar hujja a kan sa ba.

Tsare Mista Iroko da aka yi ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar, inda masu suka suka zargi jami’an ‘yan sanda da take hakkin mutum na walwala.

A lokacin dai, jami’i na musamman mai ba wa shugaban Najeriya shawarar kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce ya tabbata shugaban na can ya mayar da lamarin abun dariya, ganin yadda duk wanda ya iya alakanta shi da kare ke nuna jahilcinsa ne kawai a fili.

Inter Milan za ta iya sayar da Ivan Perisic ga Man United


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ivan Perisic ya ci kwallo 18 a gasar Serie A cikin kaka biyu a Italiya

Kociyan Inter Milan Luciano Spalletti ya ce kulob din zai yarda ya sayar da dan wasan gefe Ivan Perisic, idan aka yi masa kakkyawan tayi.

An na rade-radin cewar dan wasan gefen dan asalin Crotia zai koma Manchester United kan kudi fan miliyan 48.

Spalletti ya ce Inter tana son Perisic, mai shekara 28, ya tsaya, amman za su sayar da tsohon dan wasan na Wolfsburg domin samun kudin da za su sayi sabbin ‘yan wasa.

“Yana da muhimmi a cikin ‘yan wasanmu kuma muna sa ran zai fara mana wasa a sabuwar kaka,” in ji tsohon kociyan na Roma.

Spalletti, wanda aka nada a matsayin kociyan Inter a watan Yuni, ya kara da cewar: “Da gaske akwai rade-radi, amman a halin yanzu dai muna son Perisic ya tsaya.

“Baya ga haka, idan wani ya zo ya taya shi da irin kudin da ba za mu iya raina wa ba, za mu iya sayar da shi.

“Amman kuma za mu nemi mu samu wanda ka iya maye gurbin Perisic.”

Wakilan United sun ziyarci Milan domin su tattauna kan wata yarjejeniya ta dan wasan.

Perisic ya ci kwallo18 a wasanni 70 da ya buga a gasar Serie A tun lokacin da bar Wolfsburg ta Jamus zuwa Italiya kan kudin da aka ce ya kai fan miliyan 14.5 a watan Augustan 2015.

Nigeria: Boko Haram ta sace masu bincike na NNPC goma


Hakkin mallakar hoto
AP

Kamfanin mai na Najeriya ya ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace masu binciken mai goma da suke masa aiki a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

NNPC ya ce masana kimiyyar, wadanda wasunsu suka fito daga Jami’ar Maiduguri, sun shafe sama da shekara guda suna bincike kan abin da ya bayyana da tarin albarkatun mai a yankin Tafkin Chadi.

An yi awangaba da mutanen ne bayan wani kwantan bauna da aka yi musu a kusa da kauyen Jibi.

Mai magana da yawun NNPC Ndu Ughamadu ya ce mutanen sun “hada da malaman jami’a da direbobi da sauran ma’aikata”.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito mai magana da yawun Jami’ar Maiduguri yana cewa suna jiran karin bayani kan lamarin daga jami’an tsaro.

Sai dai ya tabbatar da cewa ma’aikatansu da suka yi tafi aikin bincike tare da jam’ian tsaro ba su dawo ba ranar Talata kamar yadda aka tsara.

Rikicin Boko Haram ya kashe sama da mutum 30,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da wasu fiye miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.

Buhari 'ba ya boye-boye kan rashin lafiyarsa'


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London

Wani mai taimakawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shugaban kasar ba ya boye-boye kan rashin lafiyarsa.

Mallam Bashir Ahmad, mai bai taimakawa shugaban na Najeriya kan shafukan sada zumunta, ya shaida wa BBC cewa fitowar da ake yi ana sanar da ‘yan kasar a duk lokacin da shugaban zai tafi kasar waje domin yin jinya alama ce da ke nuna cewa ba shi da abin boyewa.

A cewarsa, “Rashin lafiyar Shugaba Buhari ba a boye take ba domin dukkan tafiye-tafiyen da ya yi domin yin jinya babu wadda bai gaya wa ‘yan Najeriya cewa zai tafi ba. Ya yi tafiya sau hudu zuwa biyar kuma babu wacce bai fada wa ‘yan kasar cewa zai je a duba lafiyarsa ba.

“Tafiya ta baya bayan na ita ce wacce ya ce zai kwana goma, kuma da aka ga ba zai dawo ba saboda likitoci ba su amince ba, sai da aka fada wa majalisun dokoki.”

Kakakin na shugaban Najeriya ya ce fadar shugaban kasar ba ta fadi lalurar da Shugaba Buhari ke fama da ita ba ne saboda abu ne da ya shafi mutum da likitansa.

Image caption

Mallam Bashir Ahmad ya ce Shugaba Buhari zai koma kasar da karfinsa

“Kowa yana kwanciya rashin lafiya kuma hakan tsakaninsa ne da likitansa, don haka abin da ya fi muhimmanci shi ne shugaban ya mika ragamar tafiyar da kasar ga mataimakinsa wanda zai ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban kasa,” in ji Mallam Bashir Ahmad.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”

5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”

28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba

3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu

7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya

25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya

11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a London

23 ga watan Yuli – Wasu gwamnoni da shugaban jam’iyyar APC sun ziyace shi a London

Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba a taba jin Shugaba Buhari da Osinbajo ba, tun bayan da suka lashe zabe a shekarar 2015

Rawar da Fiye da Farfesa Yemi Osinbajo yake takawa a matsayin mukaddashin shugaban kasa sakamakon rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shafe watanni a wajen kasar na ci gaba da jan hankalin jama’a. Yayin da wasu ke cewa yana taka rawar gani, wasu kuwa cewa suke yi yana dari-dari.

Rashin lafiyar shugaban, wanda ba a bayyana takamaiman abin da ke damunsa ba, da kuma halin da kasar ke ciki ya sa fagen siyasar kasar daukar dumi a wasu lokuta.

Akwai wadanda suke ganin babu abin da ya sauya bayan da Mista Osinbajo ya fara tafiyar da kasar a watan Janairun da ya gabata.

Masu irin wannan tunanin su kan kafa hujja da yadda Farfesan ya jira sai da ya samu umarni daga Shugaba Buhari gabannin ya sanya a kasafin kudin kasar a watan Yuni.

“Akwai wasu abubuwa da za mu ce shi ne ya kirkiro su, misali akwai abubuwa da ya yi musamman ta fuskar tattalin arziki wato yadda ya yi hobbasa wajen farfado da darajar naira,” in ji Malam Kabiru Danladi Lawanti na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Ya ci gaba da cewa, “Mutum ba zai yanke hukunci gaba daya ba, tun da an ce duk wani muhimmin mataki da zai dauka sai ya tuntubi Shugaba Buhari.”

“Idan ban da tsare-tsare ta fuskar tattalin arziki, to babbu wani abu da za a ce Mista Osinbajo ya yi daban daga Buhari,” in ji Malam Kabiru.

Sai dai ana sa bangaren, Malam Mahmud Jega, mataimakin babban editan jaridar Daily Trust, ya ce mukaddashin shugaban “yana taka tsan-tsan.”

Ya ce ba ya tsammanin akwai wani mataki da ya dauka nasa na kashin kansa ba wanda Shugaba Buhari ya tsara ba.

“A duk tsawon makonnin nan da Osinbajo yake rikon-kwarya, gaskiya yana sassarawa ne ta gefe, ba ya taba manyan abubuwa na babban aikin gwamnati ko na siyasa, ko kananan abubuwa ma ba duka yake taba wa ba,” in ji Jega.

Daga nan ya ba da misalin yadda mukaddashin shugaban ya kasa nada ministoci duk da cewa Shugaba Buhari ya aike da sunayensu wadanda majalisar dattawan kasar ta amince da su, “amma a rantsar da su, a ba su mukami ya gagara”.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yemi Osinbajo ne ke tafiyar da al’amura tun bayan tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari

Game da batun tattalin arziki da ake cewa Mista Osinbajo ya tabuka wani abu yayin da Buhari yake jinya, Mahmud Jega ya ce aikinsa ne a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa.

“Mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban da ke kula da majalisar tattalin arzikin kasa wadda ta kunshi gwamnoni da wasu manyan ministoci da kuma gwamnan babban bankin Najeriya,” in ji shi.‘Dole ne Osinbajo ya yi taka tsantsan’

Malam Kabiru Lawanti ya ce yana ganin mukaddashin shugaban yana tsoron zakewa ne saboda iya siyasa da kuma neman karbuwa ga kowanne bangare na kasar.

“A takaice Osinbajo ya zama cikakken dan siyasar Najeriya, wanda yake taka tsan-tsan da yadda siyasar bangaranci da addini ta ke tafiya a Najeriya.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

“Yana jin tsoro ne saboda kada ya zake da yawa a ce yana so ya gaje kujerar Shugaba Buhari. Idan ka duba abin da ya faru da Jonathan lokacin jinyar ‘Yar Adua, to dole Osinbajo ya yi taka tsantsan.

Ya raba kafa ne idan Buhari ya dawo su ci gaba da tafiya tare idan ma Buhari bai dawo ba to akwai mutanen da bai ba ta da su ba,” in ji shi.

Farfesa Osinbajo ne mutum na biyu da ya taba rike mukamin mukaddashin shugaban kasa a siyasar Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ne ya fara rike mukamin yayin da marigayi Shugaba Umaru ‘Yar Adua yake jinya.

Ba a taba jin Shugaba Buhari da Osinbajo ba, tun bayan da suka lashe zabe a shekarar 2015, ko da yake, akwai wasu masu sharhi da suke ganin a kwana a tashi, wata ran za a iya jin kansu.

Yayin da Osinbajo ya kai wa Shugaba Buhari ziyara domin duba shi a Landan, shugabannin biyu sun shafe fiye da sa’a guda suna tattaunawa, wacce ita ce ganawar su ta farko tun bayan tafiyar shugaban jinya sama da wata biyu da ya gabata.

Har yanzu ba a bayyana cutar da shugaban ke fama da ita ba, ballantana lokacin da zai dawo don ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar.

Sai na ksua da shi na cewa nan ba da jimawa zai koma gida.

An nemi Falasdinawa da su ci gaba da kaurace wa Al-aqsa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Falasdinawan dai sun rika sallah a waje don nuna rashin amincewa da saka shingayen.

Hukumar gudanarwar masallacin Bait-al-mukaddas ta bukaci masallata da su ci gaba a kaurace wa haramin duk da cewa Isra’ila ta ciccire shingayen tsaron da ta kafa da suka jawo takaddama.

Hukumar wadda aka fi sani da Waqf Foundation ta ce kada kowa ya shiga masallaci har sai wani kwamitinta na kwararru ya kammala wani aikin dudduba sauye-sauyen da aka yi wa ma sa.

An ciccire na’urorin ne cikin daren Talata sakamakon amincewa da cire su da majalisar tsaron gwamnatin Isra’ila ta yi.

An saka su ne kusan makonni biyun da suka gabata bayan wani ya bindige ‘yansandan Isra’ila biyu lokacin suke tsaron masallacin.

Falasdinawa dai sun ki yarda su bi ta cikin na’urorin su shiga masallacin saboda fargabar kada su bayar da kafar sauya wata dadaddiyar yarjejeniya kan shigarsu masallacin.

Jamhuriyar Niger: 'Karin kudin awon kaya zai fi shafar talaka'


Wani kudiri da ma’aikatar Custom ko Douane da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka fitar kan karin kudi ga kayayakin ‘yan kasuwa na awo, ya hadassa bacin rai ga yan kasuwa.

A cewar ‘yan kasuwan dai halin da ake ciki ba lokaci bane na karin kudi, kasancewar kudaden kayayakin masarufi ne zasu kara tsada.

Tun a shekara ta 1994 ne kasar ta Jamhuriyar Nijar din ta rattaba hannu kan yarjejeniyar nan ta kungiyar cinikayya ta duniya– dokar da ta kamata a ce kasar ta fara amfani da ita tun a shekara ta 1999, shekaru biyar bayan yarjejeniyar.

Sai bayan shekaru 18 ne bayan wannan yarjejeniya ne dai Nijar din ta yi alwashin fara amfani da ita.

A wata sanarwa ce dai hukumar kula da shige da ficen kaya ta Kwastan ko kuma Douane ta sanar da karin kudi kan dukkan kayyaki na shige da ficen.

Wani jami’in hukumar ta Doaune din ya shaida wa BBC cewa yanzu an saka wani tsarin da ake aiki da shi a fadin duniya.

” Wannan tsari shine daidai kudin da mutum ya biya na kayanshi ya kawo su ofishin Douane din, sune aka ce ya biya kudin haraji daidai da su.”

Jami’an ya kara da cewa ya kamara jama’a su yi aiki da doka, wacce ta tanadi cewa da zarar kayyaki sun kai watanni hudu mai su bai je ya biya kudin fito ya karba ba, za su yi gwanjon su.

Shugaban kungiyar kwadago ta masu shiga da fita da kaya ta Nijar din, Alhaji Sani Shekarau ya ce da wannan doka talaka ne kawai zai tagayyara, saboda farashin kayayyaki za su yi tashin gwauron zabi.

” Abin dala goma idan ya koma dala ashirin,wadanda kawai za su ji dadi sai masu hali, amma talaka ne zai dandana kudarsa,” in ji Sani shekarau din.

Ya kuma ce hukumomi ba su shawarce su ba, sai kawai suka ga takardar sanarwa.

Yanzu haka dai ‘yan kasar ta Jamhuriyar Nijar din da dama ne ke fama da matsin tattalin arziki, talauci da kuma fatara.

Osinbajo zai rantsar da sabbin ministoci 2 ranar Laraba


Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Wannan dai shi ne karon farko da Osinbajo zai rantsar da wasu masu manyan mukamai tun bayan da ya soma rikon kwarya a watan Janairu.

Mukaddashin Shugaban Nigeria Yemi Osinbajo zai rantsar da sabbin ministocin nan biyu da suka kwashe fiye da wata biyu suna dakon shan rantsuwar da safiyar Larabar nan.

A wani sakon a shafinsa na twitter, Mataimakinsa kan Watsa Labarai Laolu Akande ya ce za a rantsar da su ne a farkon taron majalisar ministocin kasar na mako-mako da ake yi kowace Laraba.

Sabbin ministocin da za a rantsar su ne Stephen Ocheni daga jihar Kogi da kuma Sulaiman Hassan daga jihar Gombe – wadanda majalisar dattawa ta tantance tun a farkon watan Mayu lokacin da kasar ke cikin wani rudani game da halin da Shugaba Muhammadu Buhari ke ciki.

Mr. Ocheni dai zai maye gurbin tsohon Ministan Kwadago marigayi James Ocholi wanda ya rasu cikin wani hadarin mota a bara; yayin da Sulaiman Hassan zai maye gurbin tsohuwar ministar kare muhalli Amina Muhammad wadda aka nada mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya.

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu zanga-zangar ba su samu damar ganawa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba, saboda gwamnatinsa ta hana gudanar da macin

Wasu mata sun gudanar da zanga-zanga kan yadda al’umma a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ke yin wasarairai da matsalar karuwar fyade.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Hajiya Aisha Dan kani ta ce sun gudanar da zanga-zangar ce don zaburas da jama’a kan alhakin da ya rataya a wuyansu na shawo kan karuwar fyade.

Zanga-zangar wadda tsoffin daliban makarantar St. Louis suka shirya amma gwamnatin jihar Kano ta ce kada a yi, ta ci gaba da gudana duk da rashin samun damar ganawa da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje kamar yadda aka tsara.

Likitoci dai sun ce fyade na karuwa maimakon raguwa a Kano, inda wata kididdiga ke nuna cewa tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2017, an samu rahotannin aikata fyade fiye da 700 a jihar, kuma kashi 45 cikin 100 na wadanda aka yi wa fyaden yara ne ‘yan kasa da shekara 10.

Matan wadanda suka jure wa ruwan saman da ake yi yayin zanga-zangar da safiyar ranar Talata na dauke da rubuce-rubucen da suka hadar da “kada a yi fyade” da kuma “a rika hukunta masu fyade”.

Aisha Dan kani ta ce al’amarin yana ba ta kunya…kuma dole ne wasu daga cikin al’umma su tashi tsaye don magance karuwar fyade.

A cewarta, kamata ya yi a ga jama’a sun kai ruwa-rana a kan wannan laifi don kawo sauyi amma sai ga shi hakan ba ta samu ba.

Ta ce “So muke a sanya batun magance fyade a gaba. Kamar batun shigar da kara kan zargin fyade, ba zai yiwu mutumin da yake kokawa wajen samun abin da zai ci ka ce ya zo kotu ko caji ofis sau talatin ko hamsin ba.”

“Kamata ya yi gwamnati ta samar da wata manufa ta yadda za a hana mutane barin kango a tsakanin gidaje tsawon shekara goma ba tare da ana sa ido a kai ba, kuma babu wanda zai yi magana.”

Haka ita ma wata likita, Dr. Safiya Al-hakim Dutse wadda tana cikin masu gudanar da zanga-zangar ta ce alhaki ne na iyaye da al’umma kuma dole ne su tsaya su kula da ‘ya’yansu.

“Kada a rika barin matasa a baya, al’umma su kafa kwamitoci tare da limamai da masu unguwanni da sauran masu fada-a-ji don a rika fadakar da su, don sa ido kan abubuwan da ke faruwa a unguwanninsu,” in ji ta.

An kara wa sojojin da ke yaki da Boko Haram mukami


Image caption

Sojojin Najeriya sun kara zafafa yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar-Janar TY Buratai ya sanar a ranar Talata cewa ya amince da karin girma ga sojoji 6,199 da ke aiki da runduna ta musamman, Lafiya Dole, wadda ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan watsa labarai na runduna ta bakawai ta sojin kasar Laftanar Kanar Kingsley Samuel ya fitar ta ce Laftanar-Janar Buratai ya taya sojojin murnar sabbin mukaman nasu.

Ya umarce su da su kara azama wajen fafutikar da ake yi ta yaki da Boko Haram, a arewa maso gabashin kasar.

Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ta Lafiya Dole, tare da wasu ‘yan kato da gora suka kama wasu ‘yan Boko Haram hudu a kayukan Kurnari da Nayinawa da ke wajen garin Damaturu a jihar Yobe.

Mutanen da aka tabbatar cewa ‘yan Boko Haram din ne sun hada da Bukar Waziri, mai shekaru 25, da Mammade Lawan dan shekara 20, haka kuma an samu wani yaro, Isah Muhammadu, mai shekara 15 da mahaifinsa Muhammadu Damina, mai shekara 40, da suka fito daga Talala.

Binciken farko ya gano cewa sun tsere ne daga wata maboyarsu da ke Talala da Buk da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno, saboda yadda sojojin Najeriya ke fatattakarsu.

Rundunar ta Lafiya Dole ta kara zafafa yunkuri na dakile masu harin kunar bakin wake a jihar Bornon Najeriya, inda sojojin yankin suka sha yin nasara kan sama da mata ‘yan kunar bakin wake takwas, da Boko Haram suka aiko domin tarwatsa al’ummar da basu ji ba basu gani ba.

Sojojin rundunar Lafiya Dole na aiki ne da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, domin dakile maharan kunar bakin wake.

Sanarwar ta jaddadawa al’ummar Najeriya cewa su rika sa ido sosai, kuma su tabbatar sun yi shaida wa hukuma duk wani abu da suka gani da bai kwanta masu ba.

Madrid za ta sayi Mbappe mafi tsada a duniya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Monaco ta yi zargin cewar ana tuntubar Mbappe ba tare da izininta ba

Real Madrid ta shirya sayen Kylian Mbappe kan kudi Yuro miliyan 180 daga Monaco a bana in ji jaridar Marca.

A labarin da ta wallafa ta ce wannan kudin da Madrid za ta biya Monaco zai haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a 2016.

Madrid din za ta fara biyan Monaco Yuro miliyan 160 daga baya ta karasa biyan Yuro miliyan 20 da sauran tsarabe-tsaraben da zai saka hannu kan yarjejeniya.

Jaridar ta ce da PSG ta dauki Neymar kan Yuro miliyan 222 daga Barcelona wanda ya ce zai ci gaba da zama a Nou Camp, da shi ne zai zama mafi tsada a banar.

Wannan kuma ba shi ne karon farko da Real Madrid ke sayan ‘yan kwallo mafi tsada a duniya ba.

Yawan maniyyin Turawa ya ragu


Hakkin mallakar hoto
JUERGEN BERGER/SCIENCE PHOTO LIBRARY

Wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa a kasa da shekara 40, yawan maniyyin da maza ke da shi ya ragu da sama da rabi a kasashen Turawa na yammacin duniya.

Masana kimiyya sun wallafa sakamakon nazari daban-daban har 185 na yawan maniyyin mutane daga 1973 zuwa 2011.

Masanan sun gano cewa raguwar ba za ta iya kasancewa saboda bambancin yawan al’umma ba ne ko kuma bambancin hanyoyin binciken da aka yi amfani da su ba.

Daya daga cikin masu binciken, Dr Hagai Levine, na jami’ar Hebrew University ta Birnin Kudus, ya ce abin da aka gano, wata zaburauwa ce da ya kamata a gaggauta daukar mataki a kai, idan aka yi la’akari da muhimmancin yawan maniyyi ga maza wajen haihuwa da kuma rayuwar dan’adam.

Real da Barca za su kara sau uku a kwana 16


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid da Barcelona za su fara El Clasico a ranar 30 ga watan Yuli a Amurka

Real Madrid da Barcelona za su fafata a wasan hamayya da ake kira El-Clasico sau uku a tsakanin kwana 16.

A karon farko Real da Barca za su buga El-Clasico a filin wasa na Hard Rock da ke Miami a birnin Floridan Amurka a ranar 30 ga watan Yuli.

Kungiyoyin biyu za su sake karawa a ranar 13 ga watan Agusta a Spanish Super Cup wasan farko a Camp Nou.

A kuma rana ta 16 ga watan Agusta za a buga wasa na biyu tsakanin Real Madrid mai rike da kofin La Liga da Barcelona mai Copa del Rey a Santiago Bernabeu.

Haka kuma kungiyoyin za su kara a La Ligar bana, inda Barcelona za ta fara ziyartar Bernabeu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a wasan mako na 17 a gasar.

Sai dai kuma watakila a sauya ranar fafatawar domin Real za ta buga gasar kofin zakarun kungiyoyin nahiyar duniya, domin za a yi wasan karshe a ranar 16 ga watan Disamba.

Ita kuwa Real za ta je Camp Nou a ranar Lahadi 6 ga watan Mayu a wasan mako na 36 a gasar ta La Liga.

Bayern Munich ta ci Chelsea 3-2 a Singapore.


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kungiyoyin sun kara a gasar International Champions Cup

Bayern Munich ta yi nasarar doke Chelsea 3-2 a gasar International Champions Cup da suka kara a Singapore.

Munich ce ta fara cin Chelsea kwallaye uku tun farko ta hannun Rafinha da Thomas Mueller wanda ya ci biyu a fafatawar.

Sai daga baya ne Chelsea ta zare kwallo biyu ta hannun Marcos Alonso da kuma Michy Batshuayi.

A ranar Alhamis Bayern Munich za ta kara da Inter Milano, yayin da Chelsea za ta buga wasan gaba da Inter Milan a ranar Asabar.

Nigeria: 'Dole a rage yawan shekarun tsayawa takarar shugaban kasa'


Masu zanga-zanga na yin tattaki a titunan Abuja, babban birnin Najeriya, domin neman ‘yan majalisar kasar su rage adadin shekaraun tsaya wa takarar shugaban kasa daga 40 zuwa 35.

Ana sa ran ‘yan majalisar za su fara tattaunawa kan kudurin rage yawan shekarun tsayawa takarar a ranar Talata.

Batun na daya daga cikin batutuwan da za su tattauna a wani yunkuri na yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar.

Tuni dai maudu’in “#NotTooYoungToRun” wato ba kankantar shekaru a batun tsayawa takara, ya mamaye shafukan sada zumunta da muhawara na kasar.

Wannan zanga-zanga na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari, mai shekara 74, ke fama da rashin lafiya.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa BBC cewa dole ne a rage yawan shekarun domin a bai wa matasa dama su bayar da gudummawarsu.

Yawancin masu rike da madafun iko a Najeriya manya ne sosai.

Kuma kungiyoyin matasa sun dade suna korafin cewa ba a damawa da su a harkokin mulkin kasar.

''Yan Nigeria ne fiye da rabin yaran duniya da ba sa makaranta'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yaran da rikicin ‘yan ta-da-kayar-baya ya raba da gidajensu na daga cikin kananan yara miliyan 10 da rabi da ba sa zuwa makarantar Boko a kasar

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan alkaluman da ke cewa fiye da rabin kananan yaran da ba sa zuwa makarantar boko a fadin duniya, sun fito ne daga kasar.

Yayin gabatar da jawabi a taron majalisar kasar kan sha’anin ilmi karo na 62 a Najeriya, Babban Sakataren ma’aikatar ilmi, Adamu Hussaini ya ce a cikin kananan yara kimanin miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a duniya, kaso mafi yawa na miliyan 10.5 suna Najeriya.

Ya ce: “Duk da gagarumar gudunmawa daga hukumomin ba da agaji da kuma kokarin da gwamnati ke yi don shawo kan matsalar, amma har yanzu yara kalilan ne ke zuwa makarantar Boko, baya ga karancin samun shiga da na kammala makarantun a tsakanin rukunin al’ummomin da aka mayar da su gefe da kuma wadanda ke da bukatar agaji.

A cewarsa, Gwamnatin Najeriya ta yi imani cewa babu kasar da za ta samu budin arziki, ba tare da wani ingantaccen tsarin ilmi mai tasiri da ke ba kowa dama don a tafi da shi ba.

Hakan kuwa ba za ta samu ba, sai da tabbataccen tsaro da kwanciyar hankali a kasa.”

Adamu Hussaini ya ce kananan yaran da wannan matsala ta fi shafa sun hadar da: ‘ya’ya mata da almajirai da ‘ya’yan Fulani makiyaya da ‘ya’yan masunta da manoman da ke kaura da kuma yaran da ke gararamba a kan tituna da sauransu.

Sauran su ne ‘ya’yan nakasassu da kuma a baya-bayan nan, yaran da rikicin ta-da-kayar-baya ya raba da gidajensu.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Yarinyar da ke fafutuka don ganin yara mata sun sami ilimi Malala Yousafzai ta ziyarci Najeriya makon da ya gabata

A cewar babban sakataren batun samar da kudi na da matukar muhimmanci ga bunkasar ilmi a Najeriya.

“Gwamnatin Najeriya a karkashin dokar ilmin bai-daya ta 2004, na ba da kashi 2% daga dunkulallen asusun tara kudaden shigarta don aiwatar da shirin ilmin bai-daya,” in ji Adamu Hussaini.

Don haka ya bukaci taron ya bullo da hanyoyin magance matsalolin da suka shafi halin ko-in-kula da bahagon tunanin da ake yi wa yara masu bukata ta musammam.

Ina samun sauki sosai — Shugaba Muhammadu Buhari


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kawo yanzu ba a bayyana cutar da ke damun Shugaba Muhammadu Buhari ba

Shuagban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai, kuma da zarar likitoci sun ba shi dama zai koma gida domin ci gaba da ayyukansa.

A wata hira ta wayar tarho da Shugaban kasar Guinea Alpha Conde, Shugaba Buhari ya yabawa al’ummar kasar kan addu’o’in da suka yi masa.

Wannan na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar Imo ya shaida wa BBC cewa shugaban zai koma gida nan da mako biyu.

Kusan kwana 80 kenan da Shugaba Buhari ke jinya a birnin Landan kan cutar da ba a bayyana ba kawo yanzu.

Za mu kawo muku karin bayni

Image caption

A farkon shekarar nan ma Shugaba Buhari ya yi jinyar mako bakwai a London


Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
 • 5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
 • 28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
 • 3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a London

West Ham ta Javier Hernandez daga Bayer Leverkusen


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Javier Hernandez shi ne kan gaba a zura kwallo a tarihin tawagar Mexico

West Ham ta kammala sayen tsohon dan wasan Manchester United Javier Hernandez daga Bayer Leverkusen kan kudi fan miliyan 16.

Dan kwallon na kasar Mexico ya sanya hannu kan kwantiragin shekara uku.

A watan Mayu, Hernandez – wanda aka fi sani da Chicharito, ya zamo dan kwallon da ya fi zira wa kasarsa kwallo.

Hernandez, mai shekara 29, ya zura kwallo 59 a wasa 156 da ya buga wa United tun bayan zuwansa Old Trafford a 2010, kafin ya koma Leverkusen a watan Agustan 2015.

Ya ci kwallo 39 a wasa 76 da ya buga a kulob din na gasar Bundesliga.

Daliban Kudancin Kaduna sun kai karar gwamnatin jihar


Hakkin mallakar hoto
Kaduna Government

Image caption

Jami’ai dai sun musanta zargin cewa gwamnatin na son sauya wa makarantun mazauni ne.

Kungiyar matasa da dalibai ta yankin Kudancin jihar Kaduna ta Najeriya ta koka kan rashin bude wasu manyan makarantunsu 3 da gwamnatin jihar ta rufe a karshen shekarar data gabata.

Yanzu haka dai Kungiyar ta kai kara ga hukumar kare hakkin bil’adama da kuma Majalisar dokokin kasar don neman a tursasawa gwamnatin jihar ta bude makarantun.

A watan Disamba bara ne gwamnati ta rufe reshen jami’ar jihar da ke Kafanchan da Kwaleji Nazari Aikin Malanta da ke Gidanwaya da Kuma wata kwalejin koyon aikin ungozoma bayan wani rikici a yankin da haddasa salwantar rayukka da dukiyoyi; har sai tsaro ya inganta.

Sai dai da yake zantawa da BBC bayan gabatar da koken nasu a birnin Abuja ranar Litinin, Shugaban kungiyar Comrade Galadima Jesse ya ce gwamnatin ba ta da dalilin kin bude makarantun domin yanzu tsaron ya inganta.

”Ba wani takaimaimen dalili cewa kan tsaro ne aka rufe makarantun nan; idan ka duba akwai kananan makarantu na firamare da sakandare suna nan suna tafiyar da lamurransu. Idan har saboda tsaro ne to bai kamata a bar yara kanana suna ci gaba da zuwa makaranta ba.”

Amma gwamnatin ta nace kan cewar fargabar kan rashin tsaron ce ta sa makarantun ke ci gaba da zama a rufe.

”Majalisar tsaro ta jiha ce ke da hakkin cewa yanzu tsaro ya inganta; to in sun ba da shawarar cewa a kara ba da lokaci ai dole a dan kara hankuri,” inji Kwamishinan Ilimi na jahar Farfesa Andrew Nok.

Isra'ila za ta cire shigen tsaro a masallacin Bait Al Mukaddas


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wannan matakin ya fuskanci da turjiya daga Falasdiwa, abin da har ya kai ga mutuwar Falasdinawan 3 .

Jami’an tsaron Isra’ila sun yanke shawarar cire na’urorin binciken kwakwaf da suka saka a masallacin Kudus, matakin da ya kawo karuwar zaman tankiya tsakanin Falasdinawa da Yahuwadawa.

Wannan ya biyo bayan da Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da hakan amma tare da fito da wasu matakan tsaro da za su maye gurbinsu.

An dai saka na’urorin binciken ne a kofar shiga haramin na Baitul Mukaddis mai tsarki ga duka musulmai da yahudawa da nasara ne, bayan wani dan bindiga ya harbe wasu ‘yan sandan Isra’ila biyu da ke tsaron wajen a farkon watan nan.

Mahukuntan Isra’ila dai sun dauki matakin ne domin hana ‘yan bindiga shiga da makamansu cikin masallacin.

Sai dai matakin ya janyo jerin zanga-zanga da arangama da jami’an tsaro musamman ranar Jumu’ar da ta gabata.

Dama dai manzon Majalisar Dinkin Duniya zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, Nikolay Mladenov, ya yi gargadin cewa dole ne a warware wannan takaddama kafin wata Jumu’ar in ba haka ba lamarin zai kara muni.

”Abu ne mai matukar muhimmanci a samo bakin zaren warware wannan takaddamar kafin ranar Jumu’a ta wannan makon, domin ina ganin rikicin da ke kwance a kasa zai iya tashi idan muka yi wata Jumu’a ba tare da warware rikicin ba.”

Mr. Mladenov ya ce idan ba a yi wa tufkar hanci ba cikin sauri, to tashin hankalin zai iya bazuwa zuwa sassa daban-daban na duniyar musulmi, yana mai kara cewa:

”ba wanda zai musun cewa lamarin hatsaniya ce irin ta unguwa amma kuma tana tasiri ga miliyoyi ko biliyoyin mutane a sassa daban-daban na duniya.”

Ko ya kamata a kayyade amfani da intanet a ma'aikatu da makarantu?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Amfani da intanet din dai ya zama tamkar jini da tsoka musamman a tsakanin matasa maza da mata

Yawan amfani da shafukan intanet a makarantu da wuraren aiki ya zama wani babban abun damuwa ga hukumomi a Nigeria.

Ana kuma ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan ko ya dace a sa ka`ida dangane da yadda matasa za su dinga amfani da intanet a makarantun, da su kan su ma’aikata a wuraren aikinsu.

Sakamakon shagalar da ake yi daga internet, wasu ma`ikatun ma har sun haramta wa ma`aikata amfani da kuma shiga dandalin sada zumunta a lokacin aiki.

Haka ma hukumar kiyaye hadura ta kasa ta haramta amfani da waya a lokacin tuki don kauce wa hadurran da ke ciki.

Amfani da intanet din dai ya zama tamkar jini da tsoka musamman a tsakanin matasa maza da mata, inda a lokuta da dama kan shafe tsawon dare suna cikin dandalin sada zumunta daban-daban.

Wasu dalibai matasa da suka tattauna da BBC sun ce amfani da shafukan intanet ya zame musu tamkar iskar da suke shaka saboda muhimmancin su a gare su.

Zulaiha Tukur Musa ta ce ta kan shiga shafukan Facebook da Google don ta karanta labaran da abinda duniya ke ciki.

”Bani da ka’idar lokaci, ina yi da rana da kuma dare, na kan yi hira da kawaye na da ‘yan uwana”.

Amfani da intanet in ji wasu daga cikin irin wadannan dalibai yana da shiga rai da ya kan kasance rayuwa bata yiwuwa in babu shi.

Rabi Ibrahim Babina wata matsashiya ce ita ma da ta ce idan wayarta ta samu matsala takan shiga damuwa.

” Kai wayata ta zama babu kudin da zan iya shiga intanet ai na kan shiga wani hali, na gwammace a ce bani da ko kwabo a hannuna.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manyan jami’an gwamnati na kuka da yadda ma’aikata kan shagala wajen amfani da shafukan intanet din da kan kawo cikas wajen tafiyar da al’amura.

Shima dai wani matashi dalibi Abba Ibrahim ya ce, a cikin sa’o’i 24 yana iya sa’o’i 15 yana amfani da shafukan sada zumunta muddin dai akwai waya a hannuna.

Dukkan wadannan dalibai dai sun ce su kan ajiye wayoyinsu ne a lokutan karatu, amma ga wasu ba haka batun yake ba, ko ana karatu su kan saci jiki su leka shafukan na intanet; in ji Dr Ashiru Tukur Haruna, wani malamin jami’a.

Ya ce wannan wata babbar matsala ce musamman idan yana koyarwa sai ka ga wasu dalibai hankulansu ba ya kan darasin da ake koya musu saboda amfani da wayoyin salula suna shiga shafukan na intanet.

A wasu ma’aikatun gwamnati ma haka batun yake, ana kuka da yadda ma’aikata kan shagala wajen amfani da shafukan intanet din da kan kawo cikas wajen tafiyar da al’amura.

Masana dai na ganin cewa idan sharuddan da akan gicciya su yi aiki ba, to takaita shiga intanet din kan iya zama jan aiki.

Idan aka raba Nigeria a kai ta ina? – Okorocha


Hakkin mallakar hoto
Google

Image caption

Ban ga dalilin da zai sa a raba Nijeriya ba, inji gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo Cif Rochas Okorocha ya ce babu mutum daya daga cikin gwamnonin ko sarakunan kabilar Igbo ta kudu maso gabashin Nigeria dake goyon bayan fafutukar kafa kasar Biafra.

Kiraye-kirayen aware da kuma zargin rashin adalci a karkashin mulkin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu ‘yan kabilar ta Igbo ke yi na karuwa a kasar.

Ko a kwanakin baya ma, sai da shugaban kungiyar MOSSOB,mai fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya yi wani gangami inda ya jaddada kiran warewa daga Najeriya.

A wata hira da BBC, Cif Okorocha gwamnan jihar Imo a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda kungiyar take ya ce da farkon fari ma batun cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na nuna banbanci bai taso ba.

Gwamna Okorocha ya ce babu zancen cewa ba a damawa da ‘yan kabilar Igbo a gwamnatin kasar, kodayake ya akwai bukatar a kara jan ‘yan kabilar tasa a jiki.

” Ai muna da ministoci, muna da wasu da ke kan wasu manyan mukamai, akwai abubuwan da ya kamar gaskiya a duba, bai kamata ace ba a yi da Ibo ba.”

Cif Okorocha ya ce in dai batun mukamai ne a wasu lokutan akwai abubuwan da ake dubawa ba wai kawai batun kabilanci ba. Ya kuma kara da cewa ;

” Misali kamar yadda aka bayar da mukaman manyan hafsoshin sojin kasar, an yi la’akari da matsalar Boko Haram kan me za a yi don samun wanda zai shawo kan matsalar.”

Kan batun da ake yi cewa gwamnonin yankin kudu maso gabashin Nijeriyar na mara wa Nnamdi Kanu baya a fafutikar da yake yi ta kafa kasar Biafra, gwamna Rochas Okorocha ya musanta da cewa sam hakan ba gaskiya bane.

” Tambayata a nan ita ce, kana ganin a zama na na Rochas haka, sai Nndamdi Kanu zai zo ya kira ni yaki kuma in bi shi?, ka san ba mai yiwuwa bane”, babu wani gwamna ko basarake a kudu maso gabashin Nijeriya da ke goyon bayan Ndamdi Kanu da fafutikar da yake yi ta raba Nijeriya.” in ji Rochas.

Gwamna Okorocha ya ce batun raba Nijeriya ‘yan kabilar Ibo su ware abu ne da hankali ba zai dauka ba.

”Wai shin Nnamdi Kanu wanene shi a cikin kabilar Ibo?, kuma idan aka raba Nijeriya a kai ta ina?”.

Cutar AIDS: Wani yaro ya warke a South Africa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yaron ya kamu da cutar ne a daga mahaifiyarsa a lokacin da aka haife shi

Likitoci a Afirka ta Kudu sun ce wani yaro dan shekara tara da haihuwa, wanda ya kamu da kwayoyin cutar HIV, mai karya garkuwar jiki, a lokacin haihuwa, a yanzu ba a ganin alamun cutar a jikinsa.

An dai ba wa yaron, wanda ba a bayyana ko wane ne ba, kwayoyin rage kaifin cutar, tsawon wasu ‘yan watannin farkon haihuwarsa, domin gwaji, amma tun bayan wannan ba a yi masa wani magani ba na cutar.

A yanzu haka yaron ya shafe shekara takwas da rabi ba tare da alamun kwayoyin cutar HIV ba.

Rahotanni sun ce iyayen yaron sun yi matukar farin ciki game da lamarin.

Yawancin mutane na bukatar magani kullum domin hana kwayar cutar HIV karya garkuwan jikinsu, lamarin da ke jawo AIDS

Gane yadda yaron ya samu kariya ka iya taimakawa wajen samun magunguna ko kuma riga kafin da zai dakile HIV.

Yaron ya kamu da cutar ne daga mahaifiyarsa a lokacin da aka haife shi a shekarar 2007. Yana da kwaoyin cutar HIV din da yawa a jikinsa a lokacin.

A lokacin da yaron ya kamu da cutar ba ya cikin ka’ida byar da maganin da ke dakile girman HIV a farkon rayuwa, amman an bai wa yaron maganin a lokacin da yake da makon tara da haihuwa a matsayin wani mataki na gwajin magani.

Sai aka gane cewar matakin kwayoyin cutar HIV ya yi kasa a jikinsa sosai ta yadda ba za a iya gane su ba.

Sannan aka daina masa maganin bayan mako 40. Kuma ba kamar sauran wadanda aka yi wa irin wannan maganin, cutar ba ta dawo masa ba.

Sau biyu ana samun irin maganin da ake amfani da shi a farko-farkon kamuwa da cutar yana da illa ga yara.

An fara yi wa wata ‘yar jihar Mississipi ta Amurka sa’o’i 30 bayan haihuwa kuma ta shafe wata 27 ba tare da magani ba kafin cutar ta sake kunno kai.

An kuma samu wani lamari a Faransa inda kawo yanzu wani majinyaci ya shafe shekara 11 ba tare da magani ba.

Dr Avy Violari, shugabar sashen bincike kan lafiyar yara a cibiyar Perinal ta bincike kan cutar HIV da ke birnin Johannesburg, ta ce: “Ba mu yi imanin cewar maganin hana girman kwayoyin cutar HIV kawai zai iya rage cutar ba.

“Bamu san dallilin da ya sa wannan yaron ya samu saukin nan ba- mun yi imanin cewar lamarin na da alaka da kwayoyin halittarsa da garkuwar jikinsa.”

Tamkar warkewa

Wasu sun fi wasu iya jure wa kwayar cutar HIV. Amman abun da yaron yake da shi ya sha bamban daga abin da aka taba gani.

Sabunta abin da yaron yake da shi a matsayin wani magani ko kuma riga kafi zai iya samun damar taimakawa wa sauran majinyata.

Duk da cewar babu wata kwayar cutar HIV mai aiki a jikin yaron, an samu kwayoyin halittar garkuwan jikinsa.

HIV ka iya buya a cikinsu – abun da ake ce wa HIV mara aiki – na tsawon lokaci, saboda haka akwai fargabar cewar yaron zai iya bukatar magani nan gaba.

Ma’aikatan da suka yi aikin a birnin Johannesburg sun yi aikin ne tare da bangaren gwajin magani na cibiyar binciken magani ta Birtaniya.

Nigeria: 'Muna goyon bayan Buhari ko zai shekara a London'


Hakkin mallakar hoto
Nigerian Government

Image caption

A ranar Lahadi ne Shugaba Buhari yana da wasu gawmnonin jam’iyyar APC a Landan

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gawmnonin kasar a Landan inda yake jinya.

A muhawarar da aka tafka a shafin sada zumunta na BBC Hausa Facebook mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu.

Ga kadan daga cikinsu:

M Baban Yusurah Gusau cewa ya yi: “Samun labarin murmurewar Shugaba Muhammadu Buhari daga bakin gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, wani babban abin farin ciki ne, Allah Ya kara mashi lafiya da sauran marasa lafiya na duniya baki daya.

Nuraddeen Ashiru Mani: Tabbas, mu talakawan Najeriya mun yi murnar samun labarin Shugaba Buhari yana samun sauki har ma kuma ya gana da tawagar gwamnoni a Landan, wannan kuma zai zama kalubale ga masu shaci fadi game da rashin lafiyar shugaban”.

Sai dai Rukaiyya Usman Fari Jebuwa ita ta bukaci karin haske ne game da shugaban da kuma lokacin da zai dawo.

“To fadar gwamnatin taraiyar Najeriya yakamata ki bayyanawa al’ummar kasar dangane da halin da Shugaba Muhammadu Buhari yake ciki don sanin ko yaushe zai dawo gida,” in ji ta.

Murtala Ibrahim Zangon Daura kara nunawa goyon bayansa ga shugaban ya yi: “Ko shekara guda Buhari zai yi a birnin Landan, talaka yana tare da shi wajen yi masa addu’ar samun lafiya,” in ji shi.

Sai dai kuma akwai wadanda suka nuna rashin amincewarsu da halin da gwamnonin suka ce sun gani na ci gaba tattareda shugaban kasar.

Nuhu Guzalla shakku ya nuna game da kalaman Gwamna Rochas.

Duk yaudara ce. Rochas ka ji tsoron Allah ka yi bayani gaskiya kan rashin lafiyar Buhari don babu wanda ya fi karfin rashin lafiya a duniya. Tambayata kawai ita ce me yake damun Buhari? Me ya sa Buhari baya so yayi hira da ‘yan jarida tunda yana samu lafiya?,” in ji shi.

Suleiman Lawal Giwa cewa ya yi:”Ya kamata a sanar da ‘yan kasa ranar da Shugaba Muhmadu Buhari zai dawo, domin ci gaba da aikinsa.”

Har ila yau, akwai wadanda suka bayyana jin dadinsu game da ganin shugaban a karon farko cikin fiye da wata biyu.

“Masha Allah, Farin ciki ya lullubeni zuciyata bayan na ga hoton Buhari tare da gwamnoni,” in ji Auwal Salihu.

Abbas Yusuf cewa ya yi: “Allah Ya karawa Buhari lafiya da tsawon kwana da hikiman gudanar da mulki da yin adalci ga talakawa, ameen,”

Ya kamata Martial ya jajirce – Mourinho


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Martial ya koma United a 2015 daga Monaco

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya bukaci Anthony Martial ya zama yana kan ganiyarsa a koda yaushe.

An alakanta cewar Martial zai koma Inter Milan da taka-leda kan cinikin da zai bai wa Ivan Perisic damar barin buga gasar Italiya.

Martial shi ne ya bai wa Jesse Lingard kwallon da aka ci Real Madrid a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 a Santa Clara, inda United ta yi nasara a bugun fenariti.

Har yanzu United ba ta mori matashin dan wasan da ta dauko daga Monaco a 2015 kan kudi fan miliyan 36 ba.

An tsawaita hukuncin dakatar da Erik Bailly


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

United ta ci Real Madria a International Champions Cup a Amurka

Dan kwallon Manchester United, Eric Bailly ba zai bugawa kungiyar wasa uku ba, sakamakon jan kati da aka yi masa a karawa da Celta Vigo a gasar Europa League.

An kori dan kwallon ne mai shekara 23 a wasan daf da karshe a ranar 11 ga watan Mayu, inda hakan ya sa bai buga karawar karshe da United ta ci Ajax 2-0 ba.

Yanzu kuma hukumar kwallon kafa ta Turai ta tsawaita hukuncin dakatarwar zuwa wasa biyar, karin kwana biyu kan ukun da ta fara yi masa.

Bailly ba zai bugawa United karawar da za ta yi da Real Madrid a ranar 8 ga watan Agusta da wasan farko na gasar cin kofin Zakarun Turai ba.

Haka kuma hukumar ta jan kunnen United kan lattin fara wasan daf da karshen a kofin na Europa da aka yi.

Shugaba Buhari zai koma Nigeria nan da mako biyu — Rochas


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku latsa nan domin sauraren hirar da BBC ta yi da Gwamna Rochas

Gwamnan jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Rochas Okorocha, ya ce nan da mako biyu Shugaban kasar Muhammadu Buhari zai koma gida daga jinyar da yake yi a Landan.

Mista Okorocha, wanda na daga cikin gwamnoni hudu da suka ziyarci shugaba, ya shaida wa BBC cewa “muna ganin daga nan zuwa sati biyu insha Allah zai koma gida ya ci gaba da aikinsa”.

Gwamnan ya kara da cewa shugaban yana cikin koshin lafiya “kuma zancen da ake yi cewa yana cikin mawuyacin halin ba gaskiya ba ne. Yana nan lafiya lau.”

“Na yi mamakin yadda na gan shi. Yana da koshin lafiya. Abubuwan da ake cewa game da rashin lafiyarsa ba haka muka gani ba,” in ji gwamnan na jihar Imo.

Tawagar da ta ziyarci shugaban ta hada da gwamna Umar Tanko Almakura na jihar Nasarawa, da Nasir Elrufai na jihar Kaduna da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi. Sai kuma Shugaban Jam’iyyar na kasa Cif John Oyegun da Ministan Sufuri Rotimi Ameachi.

A cewar Mista Okorocha sun dauki kimanin sa’a guda suna cin liyafa tare da shugaban kasar a bayyanarsa ta farko a bainar jama’a tun bayan da ya tafi jinya a birnin London kwanaki 78 da suka gabata.

Ya kara da cewa “Shugaba Buhari ya gaya mana cewa da zarar likita ya sallame shi zai komo gida. Kuma da ni ne likitan zan sallame shi ganin yadda jikinsa ya yi kwari”.

A cikin wata sanarwa da ya fitar dangane da wannan ganawar, mai ba shugaban shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya ambato Gwamna Rochas Okorocha na cewa shugaban na cike da annashuwa kuma har yanzu yana nan da halayyarsa ta yin raha da mutane.

Gwamnan ya ce tawagar tasu ta dauki kimanin sa’a daya tana liyafa tare da shugaban kasar, kuma inji shi daga tattaunawar da suka yi ga dukkan alamu yana sane da dukkan abubuwan da ke faruwa a gida Nigeria.

Mr. Okorocha ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa da ziyarar tasu kuma ya tambayi ko wnane daga cikin gwamnonin abin da ke faruwa a jiharsa.

Sanarwar ta ce da suka nemi jin abin da zai ce game da suka da miyagun kalaman da wasu ‘yan kasar ke furtawa game da halin da yake cikin, sai ya yi dariya kawai tare da bayyana abubuwan da ake fadan a zaman karairayi, ya kara da cewa abin da shugaban ke jira kawai shi ne likitocinsa su bashi dama ya dawo gida.

Hoton da fadar shugaban ta saka a shafinta na Twitter dai ya nuna shi sanye da jamfa da wando bakake, da shudiyar hula, da kuma farin tabarau; yana murmushi a gaban wani teburi da aka jera wa abubuwan sha da kuma ayaba.

Ziyarar gwamnonin dai na zuwa ne kwanaki 12 bayan da mataimakinsa – wanda ya bar wa rikon kasar – ya kai masa wata gajeruwar ziyarar kuma ya shaida wa al’ummar kasar cewa mai gidan nasa na samun sauki cikin sauri kuma zai dawo kasar ba da jimawa ba.

Harin sansanin 'yan gudun hijira na Dalori ya hallaka mutane


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan gudun hijira na yawan kokawa kan rayuwar kunci da suke yi a sansanoni

Hukumomi a Najeriya sun ce wasu ‘yan kunar-bakin-wake sun kai hari a wasu sansanonin ‘yan gudun-hijira guda biyu da ke kusa da garin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gaabashin kasar.

Maharan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla hudu tare da jikkata wasu kusan 20.

An kai hare-haren ne ranar Lahadi da daddare da kuma safiyar Litinin din nan a sansanin da ke Dalori 1 da Dalori 2.

Rahotanni sun ce ana ganin a kalla daya daga cikin maharan mace ce.

Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake gargadin cewa matsalar karancin abincin da yankin na arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta ka iya kara kazancewa daga yanzu zuwa watan Agusta.

Dubun-dubatar jama’a ne wadanda hare-haren kungiyar ‘yan Boko Haram, masu ikirarin jihadi, suka tilasta wa barin gidajensu, ke zaune a sansanonin gudun hijira.

Man City ta dauki dan wasa na biyar a bana


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mendy shi ne na biyar da ya koma City a bana

Manchester City ta kammala sayen mai tsaron baya na Monaco, Benjamin Mendy kan kudi fan miliyan 52 kuma na biyar da ta dauka a bana.

Dan wasan mai shekara 23, wanda ya koma Monaco daga Marseille a bara ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Mendy shi ne dan kwallo na biyar da City ta dauka a bana, wanda ta kashe fan miliyan 200 wajen sayo ‘yan wasan.

City ta sayi Kyle Walker kan fan miliyan 45 da mai wasan tsakiya Bernardo Silva kan fan miliyan 43 da mai tsaron raga Ederson Moraes kan fan miliyan 35 da kuma Danilo kan fan miliyan 26.5.

Haka kuma kungiyar ta Ettihad ta sayar da Aleksandar Kolarov ga Roma kan kudi fan miliyan 4.5.