Nigeria: Majalisa ta amince da kudurin goyon bayan yaki da cin hanci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Majalisa za ta mara wa yaki da cin hanci da rashawar Buhari

A Najeriya Majalisar dattawa ta amince da wani kudurin doka da zai karfafa yakin da gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari take yi da cin hanci da rashawa a kasar.

Kudurin dokar ya amincewa hukumomi su hada karfi da karfe da takwarorinsu na kasashen waje wajen kwato kadadorin da aka saya da kudaden haram ko kudaden kasar da aka sace da aka kai kasashen waje.

Sanata David Umar shi ne shugaban kwamitin sharia na Majalisar Dattawa kuma a hirarsa da BBC ya ce, “Wannan kuduri ne da ya bayar da dama ga Najeriya da sauran kasashe su yi cudanya, ta hanyar taimaka wa juna domin a samu hujjoji da za a yi amfani da su a shari’ar da ake yi, ko kuma za a gabatar.”

“A ko wacce kasa akwai wannan cudanya tsakaninsu, idan akwai shari’ar da ake bincike a kan cewa an yi laifi, a wannan kasar ko kuma a Najeriya, to wannan kasar ko kuma Najeriyar za ta iya neman taimakon waccar kasar da ta taimaka mata ta samu shaidu, ko shaida, ko mai bayar da shaida, wanda zai zo ya bada shaida domin a samu cimma burin wannan shari’ar da ake yi” in ji shi.

Da aka tambaye batun kudaden da aka sata ko kadarorin da aka saya da kudaden da aka sata, aka kuma boye a wasu kasashen, sai ya ce: “Najeriya za ta iya nema daga kasashen da ake zargin an boye wadannan kudude, domin a binciko wadannan kudaden domin a samu a dawo da su, kamar yadda aka tsara”

Dangane da tasirin da kudurin ke da shi dangane da yunkurin da gwamnati ke yi, na yaki da cin hanci da rasahawa idan aka amince da shi, sai ya kara da cewa: ” Zai taimaka kwarai da gaske domin akwai kasashe da dama wanda ba a iya samun a shiga domin a nemi irin wadandan shaidu da kuma taimako, yanzu idan an amince da wannan kuduri zai ba da dama a samu wannan taimakon, wanda za a dawo da kudaden da aka ce an kwashe daga nan”.

An ƙaddamar da layin dogo da zai ratsa ƙasashen gabashin Afirka


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

China ce ta gina layin dogon

Kasar Kenya ta kaddamar da sabon layin layin dogo da zai hade birnin Mombasa da babban birnin kasar Nairobi, cikin watan 18.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce layin dogon wanda ya lamushe kudi dala biliyan 3.2 da aka ciwo bashinsu daga kasar China, zai bude sabon shafi ga kasar.

Ya yi gargadin cewa zai dauki matakin dakile masu barnatar da dukiyar gwamnati, bayan da aka kama mutum hudu da laifin lalata wani bangare na hanyar.

Shirin dai shi ne babban ci gaba da kasar ta samu tun samun ‘yancin kai.

Image caption

Sabon layin dogon zai hade daukacin kasashen gabashin Afirka

Layin dogon mai nisan kilomita 470 a na sa ran zai hade kasashen kudancin Sudan da kuma gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da Rwanda, da Burundi da kuma Ethiopia zuwa tekun Indiya.

A makon da ya gabata ne, Mista Kenyatta ya samo karin kudi dala biliyan 3.6 domin fadada layin dogon mai nisan kilomita 250 yamma daga tsakiyar garin Naivasha zuwa Kisumu.

Sai dai aikin na fuskantar suka daga masu adawa, wanda suka ce ya yi tsada matuka, kuma zai kawo wa tattalin arzikin kasar nakasu

Gwamnatin ta ce tana bukatar inganta harkar sufuri saboda jan hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.

Mista kenyatta, wanda ke ganin ci gaban a matsayin wata dama da zai yi amfani da ita wajen sake tsayawa takara a zaben watan Agusta, ya ce Layin dogon wani sabon sauyi ne a tarihin kasar.

“Tarihin wannan aiki ya fara ne shekara 122 da suka shude, lokacin da da Birtaniya, kasar da ta yi wa Kenyan Mulkin mallaka ta fara aza harsashin aikin, inda tun daga wancan lokacin ba a samu wani karin ci gaba ba.”

“A yau duk da cewa muna shan suka, a yau muna bikin bude ‘Madaraka'(Sunan ranar da Kenya ta samu ‘yancin kai) wanda zai fara sauya tarihin Kenya a shekaru 100 masu zuwa,” in ji Shugaba Kenyatta.

'Man City za ta dauki kofi hudu a badi'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A bara Manchester City ta lashe League Cup karkashin Manuel Pellegrini

Shugaban Manchester City, Khaldoon Al Mubarak ya ce burin kungiyar ne ta lashe kofi hudu a badi.

Mubarak ya ce idan har City ta yi hakan, zai zama babban ci gaban da kungiyar za ta samu a tarihin tamaula.

A kakar farko da Pep Guardiola ya ja ragamar kungiyar, ta kare a mataki na uku a gasar Premier, da kaiwa wasan daf da karshe a kofin FA da matakin kungiyoyi 16 a Gasar Zakarun Turai a bana.

Mubarak ya ce ‘Pep na fatan lashe kofin da yake gabansa, kuma dalilin da ya sa nake kaunarsa, nima hakan nake bukata’.

Kungiyar Manchester United ce ta lashe kofi hudu a kaka daya, inda ta ci Community Shield da League Cup da Premier League da kofin Zakarun nahiyoyin duniya da ta yi a 2008-09.

Manchester City za ta fafata a badi a gasar Premier League da FA da EFL Cup da kofin Zakarun Turai.

Super Eagles ba ta gayyaci Mikel da Moses ba


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nigeria da Afirka ta Kudu sun kara a 2015 inda suka tashi wasa 2-2

Genort Rohr bai gayyaci Mikel Obi da Victor Moses zuwa tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ba.

Tawagar ta Nigeria za ta buga wasan shiga gasar cin kofin Afirka da za a yi a 2019, wanda Kamaru za ta karbi bakunci.

Super Eagles ba ta gayyaci Moses ba duk da yana kan ganiyarsa a tamaula, yayin da Mikel ke fama da jinya.

Haka suma Brown Ideye da Odion Ighalo ba za su buga wa Nigeria karan battar ba.

Rohr ya sanar da ‘yan wasa 23 da za su kece raini da Afirka ta Kudu a ranar 10 ga watan Yuni a filin wasa na Akpabio da ke Uyo.

Ga jerin ‘yan wasan da Super Eagles ta gayyata:

Masu tsaron raga: Daniel Akpeyi, Ikechukwu Ezenwa da Dele Alampasu.

Masu tsaron baya: Elderson Echiejile, Kenneth Omeruo, Tyrone Ebuehi, Chidozie Awaziem, Shehu Abdullahi, William Ekong da Maroof Youssef.

Masu wasan tsakiya: Ogenyi Onazi, John Ogu, Oghenekaro Etebo, Alhassan Ibrahim, Mikel Agu da Wilfred Ndidi.

Masu cin kwallaye: Ahmed Musa, Kelechi Iheanacho, Alex Iwobi, Moses Simon, Henry Onyekuru, Olanrewaju Kayode da Victor Osimhen.

De Rossi ya tsawaita zamansa a Roma


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Daniele de Rossi da Francesco Totti sun yi wa Roma wasa 1347 su biyun

Kyaftin din Roma, Danielle de Rossi ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar zuwa shekara biyu.

Rossi ya cimma yarjejeniyarce kwanaki uku, bayan da Francesco Totti ya yi ritaya daga buga wa kungiyar tamaula.

De Rossi zai karbi fam miliyan 5.24 a shekara, wanda hakan ya sa ya zama dan kwallon da ya fi karbar albashi a Serie A.

Dan kwallon mai shekara 33 ya yi wasa 561 tun lokacin da ya fara buga wa Roma tamaula a shekarar 2001.

A ranar Lahadi Totti ya yi ritaya a Roma, bayan da ya yi mata wasa 786, zai kuma zama daraktan kungiyar.

Kungiyoyi na zawarcin Ibrahimovic – Raiola


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ibrahimovic ya kwallo 17 a fafatawa 28 da ya yi wa Manchester United

Wakilin Zlatan Ibrahimovic, ya ce kungiyoyi da dama na son daukar dan kwallon, amma ba su yanke shawara ba a kai.

Mino Raiola ya ce suna ta samun karin kulub-kulob da suke zawarcin Ibrahimovic daga wurare da yawa.

A ranar 30 ga watan Yuni ne yarjejeniyar Ibrahimovic za ta kare da United, kuma har yanzu bai amince ya tsawaita zamansa a Old Trafford ba.

Raiola ya ce ‘ya dace su tattauna da United domin fayyace idan dan wasan yana da daraja a wajensu’.

Ibrahimovic ya koma United da murza-leda a bara bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St-Germain.

Dan wasan na yin jinyar raunin da ya ji a watan Afirilu, inda ake fata zai warke kafin fara gasar Premier ta badi.

An ɗaure Malamin addini saboda ɓata wa ɗan fim suna


Image caption

A watan Maris din 2017 ne aka yi wani bikin baje kolin fina finai a birnin Dammam

An yanke wa wani Malamin addinin Musulunci hukuncin ɗauri a kasar Saudiyya, saboda ya ɓata wa wani sanannen jarumin fim suna.

An yankewa Saeed bin Farwa hukuncin zaman kwana 45 a gidan yari, saboda ya kira Nasser al-Qasabi a matsayin “kafiri”.

Malamai sun gudanar da wani gangami a kan Mista al-Qasabi don mayar da martani ga wata shahararriyar gidan talabijin inda jarumin kuma mai barkwanci ke yin ba’a ga kaifin kishin Islama.

Mista al-Qasabi ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, wannan ya nuna cewa ba wanda ya fi karfin hukunci.

Priyanka Chopra na shan suka kan bude cinyoyinta gaban Firai Minista


Hakkin mallakar hoto
Priyanka Chopra

Image caption

Misis Chopra ta wallafa wannan hoton a shafin Facebook

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani na yin suka ga jaruma Priyanka Chopra a kan kayan da ta saka da yake bayyana cinyoyinta a wata ganawa da ta yi da Firai Ministan Indiya Narendra Modi.

Wasu masu amfani da shafukan Facebook sun shaida mata cewa hakan nuna rashin girmamawa ne ga Firai Ministan.

Jarumar ba ta nuna nadamar yin hakan ba, inda ta saka wani hotonta tare da mahaifiyarta sanye da guntuwar riga, mai taken, “legs for the day,” wato “kafafun wannan rana.

Dama dai wasu taurarin fina-finan Indiyan ma na fuskantar suka daga wajen jama’a kan yanayin sa tufafinsu.

A shekarar 2014 ma, wata jarida a Indiya ta bayyana Deepika Padukone ta saka wani hotonta inda ake iya ganin mamanta a shafinta na Tweeter.

Padukone ta yi wa jaridar martani a shafinta na Tweeter. inda ta ce, “Eh! Ni mace ce, ina da mama! Ko akwai matsala ne?” Kuma jarumai da dama sun fito sun nuna mata goyon bayansu.

An fara ce-ce-kucen a kan Priyanka Chopra ne, bayan da wani gidan talbijin ya sanya wani hotonta tare da Mista Modi, tana mika masa godiyarta, a kan ganawar da ya yi da ita a Berlin na kasar Jamus, “Duk da yawan ayyukansa amma ya sadaukar da lokacinsa,” in ji Priyanka.

Ko da yake ba a dauki lokaci mai tsawo ba, kafin shigar tata ta zama wani batu da ake ce-ce-kuce a a kansa, inda mutane da yawa ke sharhi cewa hakan da ta yi cin mutunci ne ga Mista Modi suna da kuma magoya bayansa.

Ga wasu daga cikin masu sukar a shafukan sa da zumunta:

Hakkin mallakar hoto
Avani Borkar

Hakkin mallakar hoto
Shirish

Hakkin mallakar hoto
Raviteja Reddy

Da farko dai kamar Misis Chopra ba ta yi niyyar mayar wa mutane martani ba, sai dai daga baya ta shammace su a shafinta na Instagram inda har ta sanya hotonta da na mahaifiyarta, kuma tabbas kafarta a bude take.

A kasa da sa’a hudu, an samu sama da mutum 100,000 da suka nuna sha’awarsu ga hoton.

Hakkin mallakar hoto
Priyanka Chopra

Hakkin mallakar hoto
Raj Singh

Hakkin mallakar hoto
Priyanka Bhaduri

United za ta sake hana Madrid daukar De Gea


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

De Gea bai buga wa United wasan Europa da ta kara da Ajax a ranar 24 ga watan Mayu ba

Manchester United na fatan sake dakile zawarcin da Real Madrid za ta yi wa mai tsaron ragarta David de Gea a bana.

A shekarar 2015 Real Madrid ta cimma yarjejeniyar daukar golan na United mai shekara 26.

A lokacin Madrid ta ci karo da tsaiko bayan da ta kasa hada takardun da suka dace kan cinikin dan kwallon.

Masu sharhi da bayanai na hangen watakila Real Madrid ta sake yunkurin sayen golan dan kasar Spaniya.

United ta saka Sergio Romero a ragarta a madadin De Gea a wasan karshe a Kofin Zakarun Turai na Europa da ta ci Ajax 2-0.

Harin bam ya kashe ma'aikacin BBC da wasu mutum 80


Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yawanci fararen hula ne suka mutu a harin

A kalla mutum 80 ne suka mutu ciki har da wani ma’aikacin BBC yayin da wata mota ta tayar da bam a yankin da ofisoshin jakadancin kasashen waje suke a Kabul babban birnin Afghanistan.

An kai harin ne kusa da dandalin Zanbaq inda yake da matsanancin tsaro, kuma mutum 350 ne suka jikkata yawancin su fararen hula.

Fashewar bam din — wanda aya faru da safiyar Laraba ya yi tsananin karfin da sai da ya sa tagogi da kofofin gine-ginen da ke da nisan daruruwan mitoci suka farfashe.

Kungiyar Taliban da ke yawan kai hare-hare birnin ta ce ba ita ta kai harin na yau ba. Sai dai har yanzu ba a ji ta bakin kungiyar IS ba da ita ma take kai hare-hare.

Dukkan kungiyoyi biyu dai sun musanta cewa su suka kai hare-hare na baya-bayan nan kasar.

BBC ta tannatar da mutuwar wani direbanta da ke aiki a Afghanistan Mohammed Nazir.

A ina harin ya faru?

Bam din ya tashi ne da misalin karfe 8.25 na safe a lokacin da zirga-zirga ta fi yawa a yankin da ofisoshin da jakadancin kasashen waje suke.

Motar daukar marasa lafiya ta dauki wadanda suka jikkata a harin, yayin da ‘yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su suka taru a inda lamarin ya faru, da kuma asibitocin domin gano ‘yan uwansu.

Hotuna sun nuna yadda gomman motoci suka kone. Inda sama da motoci 50 suka lalace.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Kabul Basir Mujahid, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bam din ya fashe ne a kusa da ofishin jakadancin Jamus, sai dai ya kara da cewa “Abu ne mawuyaci a gano inda maharan suka yi niyyar kai harin.”

Akwai manya-manyan gine-gine a yankin da harin ya faru, wadanda suka hada da fadar shugaban kasa, da kuma ofisoshin jakadancin kasashen waje, ciki har da na Burtaniya.

Rahotonni sun ce bam din ya tashi ne a cikin wata babbar mota ta daukar ruwa.

Wakilin BBC a Kabul Harun Najafizada ya ce an yi ta tambaya game da yadda motar ta tarwatse a yankin da ke da matukar tsaro.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Motocin daukar marasa lafiya sun yi ta daukar mutenen da suka jikkata

Da farko dai rahotonni sun ce fararen hula ne suka fi jikkata a lamarin.

Ma’aikatar Lafiyar kasar ta ce ana sa ran yawan wadanda suka jikkata na iya karuwa.

Mai magana da yawun ma’aikatar Ismael Kawoosi, ya ce: “Har yanzu ana kawo gawarwaki tare da marasa lafiya asibitoci.”

Ma’aikatar cikin gidan kasar ta yi kira ga mazauna kasar da su bayar da gudunmowar jini, yana mai cewa “ana tsananin bukatarsa”.

Wani mai shago Sayed Rahman, ya shaidawa Reuters cewa shagonsa ya lalace, inda ya ce: “Ban taba ganin mummunan hari ba a rayuwata kamar wannan.”

Wani mazaunin garin Abdul wahid, ya shaidawa BBC cewa tashin bam din “kamar girgizar kasa ne”

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mutane sun taru a wajen da lamarin ya faru cikin tashin hankali don neman ‘yan uwansu

Su waye suka mutu a harin?

 • BBC ta tabbatar da cewa, Mohammed Nazir, wanda yake aiki da BBC a matsayin direba fiye da shekara hudu ya mutu a harin. Sannan kuma hudu daga cikin abokan aikinsa sun ji rauni. Sai dai raunin nasu ba mai tsananin da ake tsammata musu mutuwa ba ne.
 • Ministan harkokin wajen Jamus Minister Sigmar Gabriel ya ce ma’aikatan ofishin jakadancin kasar sun jikkata kuma wani mai gadin ofishin dan Afghanistan ya mutu.
 • Jami’an Faransa sun ce harin ya lalata ofishin jakadancin kasar amma ba wani ma’aikacinsu da ya mutu ko ya ji rauni.
 • Ofishin jakadancin Birtaniya ya ce babu wani ma’aikacinsu da ya bace.
 • Ministan harkokin wajen Indiya Sushma Swaraj ya ce ba abin da ya sami ma’aikatansu.
 • Wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Japan sun samu raunuka.
 • Turkiyya ta ce ofishin jakadancinta ya lalace amma babu wanda ya jikkata.
 • Kamfanin dillancin labarai na Afghanistan Tolo news agency ya sanya a shafin Twitter cewa maa’ikacinsu daya Aziz Navin ya mutu.
 • Wani dan jaridar kamfanin Tolo ya ce mafi yawan wadanda suka mutun ma’aikatan kamfani waya na Roshan ne, amma ba a tabbatar ba a hukumance tukunna.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakilin BBC Justin Rowlatt ya ziyarci wajen da aka kai hari a watan Afrilu

Manyan hare-haren da aka kai Kabul a baya-bayan nan

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Harin da aka kai masallacin Baqir ul Olum a watan Nuwambar 2016

 • 8 ga Maris 2017 – Fiye da mutum 30 sun mutu bayan wasu mahara sun yi shigar likitoci suka kai hari asibitin sojoji na Sardar Daud Khan
 • 21 ga Nuwamba 2016 – A kalla mutum 27 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin Baqir ul Olum lokacin wani taron ‘yan Shi’a
 • 23 ga Yuli 2016 – A kalla mutum 80 ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren bam da aka kai kan wasu ‘yan Shi’a da suke tattaki a dandalin Deh Mazang
 • 19 ga Afrilu 2016 – A kalla mutum 28 ne suka mutu a wani babban harin bam da aka kai kusa da ma’aikatar tsaro ta Afghanistan
 • 1 ga Fabrairu 2016 – Mutum 20 sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai hedikwatar ‘yan sanda
 • 7 ga Agusta 2015 – A kalla mutum 35 ne suka mutu a wasu hare-haren bam da aka kai a yankuna daban-daban na Kabul

Tsohon shugaban kasa zai tsaya takarar majailsar dokoki


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Abdoulaye Wade ya yi watsi da kiran da aka yi masa na ya sauka daga mulki

Tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade, zai tsaya takara majalisar wakilan kasar.

Mista Wade mai shekara 91 zai tsaya takarar ne a zabukan da za a yi a watan Yuli mai zuwa.

Zai tsaya takarar ne a jam’iyyar adawa ta PDS.

Mista Wade ya shugabanci kasar ta Senegal daga shekarar 2000 zuwa 2012. Ya kuma sha kaye a hannun shugaba mai ci yanzu Macky Sall, a zaben 2012.

Senegal dai kasa ce a yankin yammacin Afirka.

An yi arangama tsakanin 'yan sanda da sojoji a Calabar


Hakkin mallakar hoto
Nigeria Police

Image caption

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta wallafa barnar da aka yi mata a shafinta na Facebook

Rahotanni daga birnin Calabar na jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya na cewa an tafka wani fada tsakanin ‘yn sanda da sojojin ruwan Najeriya, inda ake tunanun an yi asarar rayuka da wasu da dama kuma sun jikkata.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatarwa BBC faruwar lamarin, inda ta har ta wallafa hotunan barnar da ta ce sojojin sun yi a ofishin ‘yan sandan.

Amma rundunar ba ta yi karin bayani kan asarar rayuka ko jikkata ba.

Wasu rahotanni sun ce rikicin ya fara ne a yayin da wani dan sanda ya yi kokarin tsayar da motar sojojin, wadda ta ki bin umarnin danjar bayar da hannu.

Fadan ya yi kamari ne yayin da wasu manyan jami’ai suka yi kokarin sasantawa, amma daga bisani sai al’amura suka rincabe.

Kafar yada labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa wani ganau ya shaida mata cewa daga nan sai sojojin suka shiga cikin ofishin ‘yan sandan na Akim inda suka fara harbe-harbe suka kuma kona ofishin.

Za mu kawo muku karin bayani nan gaba.

An kai samame kan masu jabun ruwan zamzam a Saudiyya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hukumomin Saudia sun gargadi jama’a da su yi hattara game da jabun ruwan Zamzam

Hukumar kula da ingancin abinci ta Saudiyya ta ce ta lalata dubban kwalaben ruwan zamzam na jabu sannan kuma ta rufe wasu gidajen da ake yin ruwan a wani samame da ta kai a fadin kasar.

Jaridar Saudi Gazette wadda ta rawaito labarin ta ce mutane na yin ruwan na jabu ne saboda tsananin bukatar zamzam da jama’a ke da ita musammam don yin buɗa-baki a wannan wata na Ramadan.

Hukumar ta gargaɗi mutane su kula kada su faɗa tarkon masu yin jabun zamzam.

Wannan lamari dai na jabun ruwan zamzam ya haifar da damuwa ga hukumomin kasar ta Saudi Arabia.

Baya ga ‘yan kasa, mahajjata daga kasashen daban-daban kan sayi ruwan zamzam din da dama su kai gida.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mahajjata daga kasashen daban-daban kan sayi ruwan zamzam din da dama su kai gida

Don taka birki ga ‘yan kasuwar jabun, tare da tabbatar da mutane sun samu ingantaccen ruwan zamzam, gwamnati ta yi wa wasu zababbun kantuna rajistar sayar da ruwan mai daraja.

Duk da haka, hukumomi sun ce an samu wasu kantunan da ba a amince da su ba na yin kafar-ungulu wajen yi wa ruwan zamzam din algus da na famfo.

A wani samame a baya-bayan nan, hukumomi a birnin Madinah sun ƙwace kwalabe fiye da 3,000 na zamzam ɗin da aka yi masa gauraye.

An kuma manna takardu masu tambarin kamfanin ruwan zamzam na Sarki Abdalla, a wani wurin ajiyar motoci a wata unguwa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutane na yin jabun zamzam din saboda tsananin bukatarsa da jama’a ke yi don buda-baki a wannan wata na Ramadan.

Har ila yau, ma’aikatar ciniki da zuba jari ta Saudiyar ta sanar da rufe wata masana’anta a yankin Buraidah, kan samunta da ɗura ruwan famfo a kwalaben zamzam.

Sun kuma gano kwalabe 6,500 na jabun zamzam.

Ma’aikatar ta kuma rufe wani wurin ajiyar kaya da ta gano a birnin Makka, inda ake ajiye ruwan ana sayar wa shaguna. An kuma lalata kwalabe dubu dari biyu.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Saudiyyar ta gargadi jama’a su guji sayen ruwan zamzam a kantunan da ba su da rijista.

Man U ta fi kowacce ƙungiya tarin arziƙi bana a Turai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manchester United ce ta lashe gasar Europa ta bana

Manchester United ita ce ƙungiyar ƙwallon ƙafa mafi arziƙi a illahirin Turai, inda darajarta ta kai kimanin fam biliyan 2.6 a cewar wata cibiyar harkokin kasuwanci KPMG.

Zakarun gasar Europa League ɗin sun shiga sahun gaba na ƙididdigar cibiyar inda ta sha gaban gaggan ƙungiyoyin Spaniya, Real Madrid da Barcelona.

Nazarin ya bibiyi haƙƙoƙin yaɗa wasannin ƙungiya, da yiwuwar kawo ribarta da shahara da damammakin buga wasanni da mallakar filin wasa.

Nazarin wanda ya ƙunshi ƙungiya 32, kulob-kulob ɗin Ingila sun yi mamaya, inda suka kankane matsayi shida a cikin gurbi guda goma na sama.

Shugaban harkokin wasanni a cibiyar KPMG kuma mawallafin rahoton, Andrea Sartori ya ce ɗaukacin darajar harkar wasannin ƙwallon ƙafa ta bunƙsa a shekarar da ta gabata.

A cewarsa: “A lokaci guda wannan ya bayyana wani ɓangare na bunƙasar yaɗa wasannin ƙwallon ƙafa da faɗaɗa harkokin kasuwancin kulob-kulob a faɗin duniya, da jarin da suke zubawa don mallakar kadarori na ƙashin kai, da na zamani, bugu da ƙari kuma tsare-tsaren gudanarwa masu ɗorewa na daga cikin manyan dalilan da suka janyo wannan bunƙasa.”

“Ta fuskar darajar haƙƙin yaɗa harkokin wasanni, Gasar Firimiyar Ingila ta yi wa sauran takwarorinta na Turai zarra, ko da yake su ma sauran manyan gasannin ƙasashe sun fito da fayyatattun tsare-tsare don yin gogayya wajen samun magoya baya a faɗin duniya.”

Manyan ƙungiyoyin Turai guda 10 ta fuskar ‘darajar harkokin cinikayya’

Manchester United -3.09bn euros

Real Madrid – 2.97bn euros

Barcelona – 2.76bn euros

Bayern Munich – 2.44bn euros

Manchester City – 1.97bn euros

Arsenal – 1.95bn euros

Chelsea – 1.59bn euros

Liverpool – 1.33bn euros

Juventus – 1.21bn euros

Tottenham – 1.01bn euros

Majiya: KPMG

Sai dai Mista Sartori ya ce ƙungiyoyin sun gaza yin tasiri a ɗaiɗaikunsu wajen bunƙasa kuɗin shiga ta fuskar yaɗa wasanni.

A bana, darajar ƙungiyoyin Turai 10 ta ƙaru da fiye da yuro biliyan ɗaya, ninki biyu idan an kwatanta da shekarar 2016.

Tottenham Hotspur da Juventus ta Italiya ne sabbin shiga rukunin hamshaƙan ƙungiyoyin Turai, inda Tottenham ta jeho Paris Saint-Germain ta Faransa daga matsayi na goma.

Duk da mamayar da ƙungiyoyin Firimiya suka yi, Spaniya ce ƙasa guda ɗaya da ke da ƙungiya biyu da rahotanni suka ce na da “darajar harkokin kasuwanci” ta fiye da yuro biliyan biyu, Real Madrid da Barcelona.

An dakatar da ɗan wasan da ya sumbaci 'yar jarida


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Lamarin ya faru ne bayan da Pablo Cuevasda na kasar Uruguay ya fitar da Hamou a zagayen farko na gasar a ranar Litinin.

Wani ɗan wasan kwallon Tennis na Faransa ya fuskanci dakatarwa saboda sumbatar wata ‘yar jarida sau da dama a lokacin da take hira da shi kai tsaye ta gidan Talbijin.

Jami’an shirya gasar manyan wasannin kwallon Tennis na ‘French Open’ ne suka dauki wannan mataki a kan Maxime Hamou .

Ɗan wasan mai shekara 21, ya sumbaci ‘yar jaridar Maly Thomas bayan ya kamo wuyanta, duk da ƙoƙarin kufcewa da ta yi.

Hukumar wasan kwallon Tennis ta kasar Faransar (FTT) ta yi tir da abin da ta kira “mummunar dabi’a”, ta kuma buƙaci a gudanar da bincike.

Lamarin ya faru ne bayan an fitar da shi daga wasannin zagayen farko na gasar a ranar Litinin.

Wannan shi ne al’amari na baya-bayan nan da ya haifar da zarge-zargen cin zarafin mata masu aiko da rahotannin wasanni.

Lamarin dai ya fusata masu mu’amala da shafukan sada zumunta ciki har da Cécile Duflot wata ‘yar siyasa a Faransa.

“Ya sumbace ta ta karfin tsiya, ta yi ƙoƙarin kufcewa, ya riƙo wuyanta kuma kowa yana ta…dariya,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

Wata jaridar ƙasar Faransa Huffington Post ta ambato Ms Maly Thomas na bayyana halayyar ɗan wasan a matsayin “rashin kan gado”.

“Da ba don an hasko mu kai tsaye a talbijin ba, da na kai masa naushi, in ji ta.

Hakkin mallakar hoto
EUROSPORT

Image caption

Hamou ya yi ta maimaita sumbatar ‘yar jaridar a lokacin hirar kai tsaye

Dan wasan dai, Hamou ya nemi afuwa kan abin da ya aikata.

A wata sanarwa a shafin sada zumunta na Facebook a ranar Talata, Hamou ya ce: “Ina matuƙar neman gafara ga Maly Thomas, idan ranta ya ɓaci, ko ta kaɗu game da halayyata a lokacin hirarmu.

“Har yanzu a kullum ina ƙara koyon darasi daga kura-kuraina don zama ɗan wasa na gari, kuma mutumin kirki.”

Gidan talbijin na Eurosport ya yi lale marhabin da matakin ɗan wasan na neman gafara, tare da isar da batun ga masu kallo da mai yiwuwa ba su ji daɗin abin da suka gani ba.

“Muna matuƙar nuna nadamarmu kan abin da ya faru lokacin hirar da muka watsa a jiya,” in ji Eurosport a wata sanarwa.

“Halayyar wanda ake hira da shi ɗin sam ba ta dace ba, kuma ba za mu taɓa yarda da irin wannan abu ta kowanne hali ba.”

Kotu ta ci tarar wani mutum da ya yi 'like' a Facebook


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Akwai fargabar cewa hukuncin ka iya zama mummunan ɗan-ba a Switzerland

Wata kotu a Switzerland ta ci tarar wani mutum kwatankwacin naira N1.5m, saboda ya latsa alamar yin na’am ko “like” da wasu kalamai a shafin Facebook waɗanda kuma ake ɗauka a matsayin ɓata-suna.

Shari’ar ta shafi wasu kalamai ne da aka yi a kan shugaban wata ƙungiyar kare dabbobi, Erwin Kessler.

Kafofin yaɗa labarai sun ce an zargi Erwin Kessler da ƙin jinin Yahudawa kuma nuna wariyar launin fata a cikin kalaman.

Kotun lardin Zurich ta ce wanda ake ƙara “ƙarara ya amince da ƙunshin kalaman da ba su dace ba kuma ya mallaka wa kansa” ta hanyar yin na’am.

A cewar jaridar Le Temps mutumin mai shekara 45 ya danna alamar na’am har sau shida ga kalaman.

Bayanai sun ce Mista Kessler ya yi ƙarar fiye da mutum goma sha biyu saboda kalamai daban-daban da suka yi a shafin Facebook cikin 2015.

Jaridar Tages Anzeiger ta ce an wallafa kalaman ne game da wata tattaunawa a kan ko ya dace a bar ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi su shiga a dama da su a bikin da masu ƙauracewa cin nama suka shirya.

Kotun ta yi hukuncin cewa mutumin da ake ƙara bai iya tabbatar da hujjar cewa kalaman da ya yi na’am da su gaskiya ne ba.

Ta kuma ce matakin yin “na’am” da kalaman “ya sanya su ƙara bazuwa ga adadin mutane da yawa”, abin ya kuma wani “nakasu ne ga mutuncin Kessler”.

Daga nan sai kotu ta ci shi tarar Swiss francs dubu huɗu kwatantwacin dala 4,100, a cewar AFP. Ko da yake, yana iya ɗaukaka ƙara.

Wani lauya ga ɗaya daga cikin mutanen da Mista Kessler ya yi ƙara ya ce hukuncin ka iya “yin gagarumin tasiri” duk da yake kotun lardi ce ta zartar da shi.

Amr Abdelaziz ya ce akwai buƙatar kotuna Switzerland su fayyace wa masu amfani da shafukan sada zumunta iyakokinsu ƙarara, ya kuma yi gargaɗi game da jefa ‘yancin faɗar albarkacin baki cikin hatsari matuƙar kotuna za su riƙa yanke wa mutane hukunci a kan sun danna alamar na’am da kalaman shafin Facebook.

Ka san dakin da ya fi shiru a duniya?


Hakkin mallakar hoto
Microsoft

Image caption

An dauki kusan shekara biyu a zayyana da ginin dakin

Kamfanin Microsoft ya gina wani daki da yake shiru ba a jin karar komai, ta yadda hatta kasusuwan jikinka ma za ka ji motsinsu. Kuma dakin na taimaka wa wajen kirkiro kayan laturoni da za a bullo da su nan gaba. Richard Gray ya yi mana nazari.

Idan LeSalle Munroe ya tsaya cik na dan wani lokaci a cikin ofishinsa, wani abu mai tsoratarwa yakan faru. Zai iya jin karar tafiyar jininsa a cikin jikinsa da motsin idanuwansa a cikin kwarminsu.

Yayin da wasu mutanen ke aiki a wurin da ke cike da karar kwamfuta da sauran na’urori da surutai da kai-kawo na abokanan aiki, Munroe yana cikin wurin da babu wani motsi ko kara. Ofishinsa shi ne wurin da ya fi shiru a duk duniya.

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Image caption

Hatta karar tafiyar jinin jikinka za ka iya ji a dakin

Shi dai wannan daki na musamman yana boye ne can a karkashin Gini na 87 a hedikwatar kamfanin Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, inda dakunan binciken kimiyya na manhajar kamfanin suke.

A nan ne aka kirkiro fitattun kwamfutoci da manhajar kamfanin irin su Surface computers da Xbox da Hololens. Injiniyoyin kamfanin ne suka kirkiro tare da gina dakin ( anechoic chamber), domin ya taimaka musu wurin gwajin sabbin na’urorin da suka kirkiro. Kuma a shekarar 2015 dakin ya kafa tarihin zama wurin da ya fi zama shiru a duk duniya.

Ta yadda za ka kara fahimtar yanayin wurin karara, shi ne, idan mutum ya yi rada tana linkawa kusan sau talatin a kara, yayin da karar numfashin mutum kuma ke linkawa sau goma.

Munroe ya ce, ”Idan aka rufe kofar dakin yanayin wani ne na daban wanda ba ka taba ji ba, idan ka tsayar da numfashinka za ka iya jin zuciyarka tana bugawa da tafiyar jininka a jiki. Ni kaina ba kasafai nake zama a ciki ba da kofar a rufe.”

Hakkin mallakar hoto
Microsoft

Image caption

Ba karar da take daga waje da za ta shiga dakin

Sai da aka dauki kusan shekara biyu ana zayyanawa da gina dakin, inda a yanzu Munroe da abokan aikinsa ke aiki a kullum na kirkiro da kayayyakin fasaha na kamfanin Microsoft.

Hatta samo ginin da ya dace inda za a yi wannan daki sai da aka dauki kusan wata takwas ana gwaje-gwaje domin samun wurin da yake shiru ba hayaniya ko wata kara da za a iya yinsa.

Dakin dai an yi shi ne can a cikin tsakiyar wasu dakuna wadanda kowanne bangonsa ya kai kaurin inci 12, wanda hakan ya sa ba wata kara daga waje da za ta shigo cikinsa.

Idan jirgin sama na yaki zai tashi a kusa da ginin gidan da dakin yake abin da za ka ji a daki na karshe da wannan ofis yake ciki bai wuce kamar rada ba.

An tsara gin ofishin ta wata hanya ta musamman ta yadda ba inda gininsa kai tsaye ya taba ainahin ginin gidan da yake ciki. In ji Hundraj Gopal, babban injiniyan al’amuran da suka shafi mutane na kamfanin na Microsoft.

Wannan daki ko ofis yana da fadin kafa 21 ta kowane bangare. Kuma a dukkanin bangarorinsa shida an shinfida masa abin da ke hana sauti wucewa mai tsawon kafa hudu, wanda ke hana amsa amo na duk wani sauti da aka yi a cikin dakin.

Ita kanta kofar da sauran duk wasu tsare-tsare na dakin an yi su ne na musamman ta yadda ba wani sauti ko kara daga ciki da zai fita ko kuma ya shigo ciki daga waje.

Hakkin mallakar hoto
Alamy

Image caption

Saboda shirun dakin an ce za ka iya jin karar kasusuwan jikinka idan kana tafiya

Gopal ya ce; ”Ga duk wanda yake bukatar irin wannan daki zai iya saye akwai shi.” Sirrin abin kawai shi ne yadda muka yi dabara da bata lokaci wurin sarrafa hanyar da iska za ta kai ga dakin.

Kafin jami’an littafin bajinta na duniya na Guiness Book of Records su je wurin su yi nazarinsa har ya zama na daya a duniya (-20.6), dakin bincike na kimiyya na Orfield Laboratories da ke Minneapolis shi ne ke da wannan bajinta ta dakin da yake mafi shiru a duniya (-9.4 decibels).

Gopal ya ce; ”Ba wai mun yi niyyar gina wurin da shi ne ya fi shiru ba a duniya. Niyyata mu yi wurin da babu hayaniya ko iya karar da kunnen mutum zai iya ji (0 decibels).

Za ka dauka cewa wurin da yake shiru kamar wannan, zai kasance wuri ne da yake lami lafiya. To amma ga wadanda suka taba shiga dakin lamarin ba haka yake ba ko alama.

Gopal yakan ba wa bakin da suka ziyarci hedikwatar ta Microsoft damar ziyarar dakunan bincike da gwaji na kamfanin, har ma da wannan daki na musamman.

Kuma yawancin mutanen ba sa jin dadi idan suka shiga dakin, ta yadda wasu nan da nan da shigarsu dakin sai su nemi hanyar fita, in ji Gopal.

”Sukan ce ba za su iya zama a dakin ba. Kusan kowa za ka ga ba ya jin dadi. Suna iya jin numfashin wadanda suke can gefe a dakin, da kuma kugin cikin mutane. Wasu mutanen ma ‘yan kadan sukan ji juwa ko jiri.”

Wannan zai zama kamar wani abin mamaki kasancewar yawancinmu muna kokarin samun kanmu a wurin da za mu kaurace wa hayaniyar yau da kullum da ke damunmu.

Amma Peter Suedfeld, masanin tunanin dan adam a jami’ar British Columbia, ya kwatanta lamarin da rashin sabo, inda ya ce kamar shiga dakin da yake da duhu ne dudum.

”Da farko za ka ga ba ka ganin komai, amma da ka dan jima a ciki sai idonka ya saba da duhun ka fara gani.”

Idan ka kaurace daga wurin da ake jin kara ko sauti na yau da kullum, to za ka iya jin hatta motsin kasusuwa ko gabban jikinka a lokacin da kake motsi, har ma ka ji karar ta dame ka matuka.

Amma Gopal ya ce; ”Duk da haka akwai wadanda suke jin dadin kasancewa a dakin, suna ma daukar kamar yanayi ne na daidai da zaman natsuwa na ibada.”

Sai dai ya ce mafi dadewa da ya gani wani ya yi a dakin daga cikin masu ziyara shi ne sa’a daya, shi ma din domin tara kudin bayar da agaji ne.

Ya ce, ”ina jin idan ka dade a dakin ka za ka ji ya dame ka. Duk yawun da ka hadiya za ka ji karar hadiyar ta dame ka.”

Hakkin mallakar hoto
Microsoft

Image caption

Microsoft na amfani da dakin wurin gwaje-gwajen na’urorinsa

A wurin Munroe wannan shirun na dakin yana da wani amfanin wanda shi ne mafi muhimmanci, fiye da jin karar jikin mutum.

Akwai karar da kayan da aka harhada aka tashi na’ura suke yi lokacin da lantarki ya shige su, wanda kila karar zai iya damun mai amfani da na’urar.

Ya ce: ”Ta wannan hanya muke iya gano inda karar ke fitowa sai mu duba yadda za mu yi mu dakatar ko rage karar.

Haka kuma akan yi amfani da hanyar wajen saitawa ko dadada karar da misali danna wayar salula ke haifarwa ta yadda za ta yi dai ga kunnen mutum maimakon ta sa ya ji ba dadi, idan karar ta kasance wata iri.

Hatta masu bincike a fannin lafiya sukan nemi izinin amfani da dakin na Microsoft domin gunar da wasu gwaje-gwaje.

Sai dai Gopal yana taka-tsantsan wajen barin a yi amfani da dakin a fannin likitanci da ya shafi kwakwalwa ko masu larurar tabin hankali, domin abu ne da ke bukatar matakai na izini daga hukuma, saboda hadarin dake tattare da sanya mutumin da ke da larurar kwakwalwa a irin wannan daki.

Ainahin tasirin dakin akan Munroe da Gopal na bayyana ne idan sun fita daga dakin bayan sun dan jima a ciki.

Munroe ya ce; ”Da ka bude kofa za ka ji kamar wata kara mai karfin gaske tana ta bugun kunnuwanka. Kamar ka shiga wata sabuwar duniya ne, za ka ji karar da idan da haka kawai ne ba za ka ji ba, kuma zai sa ka fahimci wani abu.”

'Kila ba zan yi hajjin bana ba'


Hakkin mallakar hoto
AP

Image caption

Maniyyata aikin hajji zasu biya fiye da Naira miliyan daya da rabi a bana

Maniyyata aikin hajji daga Najeriya zasu biya fiye da Naira 1,500,000 kafin su sami sauke farali a bna.

Zuwa yanzu, hukumar kula da ayyukan Hajji ta Najeriya ta fitar da farashin da kowane maniyyaci daga jihohi 22 cikin 36 na kasar zai biya.

Mafi kankantar farashin shi ne na Naira 1,480,000 da maniyyatan jihar Katsina zasu biya. Maniyyatan jihar Oyo sune zasu biya farashi mafi yawa na Naira 1,584,069.

Bashir Abubakar mazaunin Abuja kuma maniyyaci ne a bana ya koka da yadda aka sami karin farashin aikin hajjin na bana.

“A gaskiya farashin nan da aka fitar bai yi mana dadi ba”, in ji Bashir. “Wannan karin kudin ba kadan ba ne, kuma ya bata ma maniyyata lissafin su.”

Mallam Bashir ya shafe shekara guda yana ajiyar kudaden aikin hajjin.

“Kafin karin dai na ajiye miliyan daya, sai kwatsam muka ji an kara Naira 500,000. A da muna fatan karin da zamu yi bashi da yawa”, in ji shi.

A bara dai maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, kana masu babbar kujera sun biya Naira 1,145,998.92.

Su kuma maniyyata daga kudancin kasar sun biya Naira 1,008,197.42, su kuma masu matsaikaiciyyar kujera kuma sun biya N1,057,447.42, inda masu babbar kujera suka biya Naira 1,155,947.42.

A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade.

A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka.

A nata bangaren, hukumar jin dadin maniyyata ta Najeriya ta kare karin saboda hauhawan farashin kaya da koma bayan tattalin arziki ya jawo.

Ga jaddwalin kudaden da maniyyata daga Najeriya zasu biya:

 • Nasarawa:1,544,894.16
 • Niger:1,525,483.30
 • Kaduna:1,535,503.68
 • Kano:1,537,859.97
 • Katsina: 1,498,502.70
 • Adamawa:1,530,101.18
 • Yobe:1,520,101.18
 • Kano:1,537,859.97
 • FCT:1,538,218.62
 • Bauchi:1,523,122.41
 • Plateau:1,529,036.80
 • Zamfara:1,510,461.65
 • Sokoto:1,524,618.90
 • Gombe:1,516,118.90
 • Benue:1,522,118.90
 • Kebbi:1,534,659.85
 • Taraba:1,521,138.21
 • Osun:1,548,153.42
 • Armed Forces:1,538,379.22
 • Ogun:1,561,943.97
 • Anambra:1,511,173.77
 • Kwara:1,501,571.27
 • Ekiti:1,525,191.27
 • Edo:1,551,331.87.
 • Oyo:1,584,069.02.

Banda wadannan kudaden, akwai Naira 38,000 na hadaya da kowane maniyyaci zai biya daga aljihunsa a Makkah.

Bashir Abubakar yace yawancin maniyyata ba zasu iya biyan karin kudin ba.

“Nima kaina da nake magana, idan ban samu karin ba, gaskiya hakura zan yi. Na tabbata kashi 50 cikin dari na wadanda suka yi niyyar zuwa wannan aikin hajjin ba zasu sami daman zuwa ba saboda karin yayi yawa.”

Hegerberg ta lashe kyautar gwarzuwar BBC


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta BBC ta bana

‘Yar wasan Olympique Lyon, Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta BBC ta bana.

Dubban mutane ne suka zabi ‘yar wasan mai shekara 21 ta tawagar kwallon kafar Norway.

Mata ‘yar wasan tawagar Brazil ce ta yi ta biyu, sai Christine Sinclair ta Canada ta yi ta uku a zaben.

Sauran ‘yan wasa biyar da sunansu ya shiga takarar ta gwarzuwar ‘yar kwallon kafa ta BBC sun hada da Hedvig Lindahl ta Sweden da kuma Melanie Behringer ta Jamus.

An karrama likitan da yake duba mutum 750,000 shi kadai


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An karrama wani likita, wanda shi kadai yake duba lafiyar mutane fiye da 750,000 domin ya rika yin aikin fida fiye da 1,000 a ko wacce shekara a kasar Sudan.

Likita Tom Catena, mai shekara 53 da haihuwa, mabiyin darikar katolika ne daga birnin New York, an karrama shi da lambar girma ta Tallafa wa Bil Adama ta Aurora.

Yayi aiki a Sudan na tsawon shekara fiye da 10, a lokacin yakin da aka fafata tsakanin gwamnati da mayaka ‘yan tawaye.

A kalamansa a lokacin bikin, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka a warware rikicin da ke hana samar da taimakon jin kai ga al’ummar yankin.

Hakkin mallakar hoto
Adriane Ohanesian/Aurora Humanitarian Initiative

Dokta Catena shi ne likita daya tilo a yankin tsaunukan Nuba, inda yaki tsakanin sojojin gwamnatin shugaba Omar al-Bashir da ‘yan tawayen kungiyar SPLM-Arewa ya ki ci, ya ki cinyewa.

An sha yaba masa domin kokarin da ya yi na shawo kan matsalolin rashin kayan aiki da magunguna a asibitin katolika na Mother of Mercy da ke tsaunukan Nuba, duk da aikinsa na duba wadanda suka jikkata saboda hare-haren da aka rika kai wa yankin.

“Gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen suna takaddama tsakaninsu game da wanda zai rika shigar da kayan agaji”, in ji Dokta Catena.

“Dole mu yi allurar hankali.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

The doctor called on President Omar Al-Bashir to address the medical supply problem

Dokta Catena ya sanar da wadanda suka halarci bikin cewa gwamnatin kasar na son tabbatar da ikonta a kan shige da fice na kayan agajin.

“‘Yan adawa na ganin akwai maganin hana haihuwa daga bangaren gwamnatin Sudan. Saboda haka suka fi son taimako daga Sudan ta Kudu mai makwabtaka da su.

Tun a shekara ta 2007 yake aiki a Sudan, inda ya rika duba masu raunuka da suka samu daga harbi. Ya rika karbar haihuwa da kuma yanke kafafuwa.

Dan wasan fim George Clooney ne ya mika wa likitan lambar yabon. “Dukkanmu muna da rawar da za mu taka domin wannan batun da ya shafi duniya. Muna da hakki a kanmu, dukkanmu”, in ji Mista Clooney.

Hakkin mallakar hoto
Aurora Humanitarian Initiative

“Dole mu taimaka.”

Sauran wadanda aka karrama sun hada da wani likitan hakora wanda ya yi aikin tiyatarsa ta farko lokacin yakin Siriya ta hanyar aikawa da hotunan masu bukatar aikin ga wasu kwararun likitocin da ke kasashen wajen ta hanyar shafukan zumunta.

Muhammad Darwish dan shekara 26 yana daya daga cikin likitoci uku da suka rage a garin Madaya, garin da a lokacin an yi masa kofar rago.

“Ba zan manta wannan batun ba har tsawon rayuwata”, in ji shi.

Hakkin mallakar hoto
Aurora Humanitarian Initiative

“Ka zama ka sami kanka a halin da dole ka yarda wani wanda ba shi da isasshen horo ya yi tiyata a kan danka, kuma nima in yarda da hakan har in yanka cikin mutum mai rai a bisa tebur, lallai wannan lamarin bai kamata ma ya faru ba.

An yi nasara a aikin.

Ita ma Fartuun Adan wata mai rajin kare hakkin dan adam ce da ke birnin Mogadishu ta kasar Somaliya tana cikin wadanda aka karrama.

Mayaka sun kashe mijinta a shekara ta 1996 kuma tun lokacin take aikin taimaka wa kananan yaran da yakin ya rutsa da su.

Hakkin mallakar hoto
Aurora Humanitarian Initiative

Ta kafa cibiyar farko domin tallafa wa matan da aka yi wa fyade a Mogadishu.

Sai kuma Jamila Afghani daga Kabul, wacce take fafutukar ganin malaman addini sun mayar da hankulansu ga batun hakkokin mata.

Hakkin mallakar hoto
Aurora Humanitarian Initiative

“Idan ka ilmantar da mace daya, to ka ilmantar da iyali gaba daya ne. Kowa na amfana da iliminsu”, in ji ta.

Shi kuma Dokta Denis Mukwege daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya taimaka wa fiye da mutane 50,000 a kan batutuwan cin zarafin jama’ai a kasar da aka lakaba wa sunan shalkwatar fyade ta duniya.

Hakkin mallakar hoto
Aurora Humanitarian Initiative

Mahrez yana son barin Leicester City


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mahrez ya koma Leicester City a shekarar 2014 daga Le Havre

Riyad Mahrez ya ce yana son ya bar kungiyar kwallon kafa ta Leicester City.

Mahrez ya ce ya amince ya ci gaba da buga wa Leicester wasa zuwa shekara daya, bayan tattaunawa da ya yi da shugaban kungiyar a lokacin da suka ci Premier a bara.

Dan kwallon tawagar Algeria mai shekara 26, ya koma Leicester da taka-leda a shekarar 2014 daga Le Havre kan kudi fam 400,000.

Mahrez ya buga wa Leicester City wasa 48 a kakar bana, kuma shi ne ya lashe kyautar dan kwallon da babu kamarsa a Premier a 2016.

Dan wasan ya ci kwallo 10, ya kuma taimaka aka ci bakwai a wasannin da Leicester ta yi ta 12 a gasar Premier da kaiwa karawar daf da kusa da karshe a Gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Ka san yadda ya kamata ka wanke hannunka kuwa?


Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Bayan wanke hannu da sabulu akwai matakan da za ka bi na raba hannun da kwayoyin cuta

Wanke hannu bayan an je bandaki abu ne da yake da muhimmancin gaske ko ma ya zama wajibi. To amma wace hanya ce ta fi dacewa a bi wajen wanke hannun, ko wane tsari ne mafi kyau?

Da ruwan zafi ko na sanyi ya kamata a yi? Da sabulu ko toka ko wani abu daban ya kamata a yi? Claudia Hammond ta yi mana nazari kan wannan lamari.

Idan aka yi maganar wanke hannu, sai ka dauka magana ce mai sauki kawai, to amma ba haka abin yake ba. Duk da cewa akwai sheda da yawa da ke nuna muhimmanci da amfanin wanke hannu, bayan an je bandaki, ko kafin cin abinci, ko yin wani abu da hannun, kamar shiga motar da mutane suke da yawa da sauran abubuwa da mutum zai iya diban datti a hannunsa, kiyasi ya nuna cewa kashi biyar cikin dari ne kawai na mutane suke wanke hannunsu da kyau.

Wani nazari da aka yi a kan mutane 3,000 ya gano cewa kashi 10 cikin dari ( 300) na mutanen ba su wanke hannunsu ba sam-sam bayan da suka shiga bandaki, kuma ko da sun wanke ma kashi 33 cikin dari ba su yi amfani da sabulu ba.

Wannan matsala ce saboda, za mu iya yada cuta daga hannunmu zuwa hancinmu da bakinmu, domin za mu taba fuskarmu da hannun bayan da muka fito daga bandaki, kuma daga nan kwayoyin cutar za su shiga cikin cikinmu.

Masu bincike a Amurka da Brazil sun gano cewa, mukan yi amfani da tafin hannunmu mu taba abubuwa ko wurare kusan sau 3.3 a cikin duk sa’a a daya, a wurin da ake da jama’a, sannan kuma muna taba baki ko hancinmu kusan sau 3.6 a duk sa’a daya.

To a hakan haka za ka ga lalle yana da muhimmancin gaske mu rika tsaftace hannunmu da kyau. Sai dai abin a nan shi ne akwai batutuwa da dama ko ma almara kan yadda ya kamata mutum ya wanke hannun nasa.

Shin sai ruwa yana da dimi ko zafi ne zai wanke maka hannu da kyau?

A wani bincike da aka yi a kan mutane 500 a Amurka, kashi 69 cikin dari na mutanen sun yi amanna cewa dimi ko zafin ruwa yana da tasiri ko taimakawa wajen wanke datti a hannu.

Gaskiya ne cewa zafi yakan kashe kwayoyin cuta, to amma fa sai ruwan ya yi zafi sosai kuma a bar shi ya dade a kansu kafin ya iya kashe wasu kwayoyin, wanda kuma idan har ya kai wannan zafin zai iya kona ka.

Sannan wani gwaji da aka yi na kimiyya ya nuna babu wani bambancin gaske tsakanin wanke hannu da ruwa mai sanyi ko zafi ko dimi dangane da yawan kwayoyin cutar da ke barin hannun. Sai dai kada mu manta da cewa a dabi’ar dan adam, mutum ba zai yarda ya sa hannunsa ya dade a cikin ruwan zafi ko na sanyi ba, wai domin ya wanke hannunsa da kyau, domin ba zai yarda da abin da zai cutar da shi ba.

Amma idan da ana son kashe kwayoyin cutar ne ba shakka idan aka zuba wa wasu ruwa mai zafi suka dade a ciki za su iya mutuwa.

Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Bincike da dama ya nuna amfani da takardar goge hannu da ake jefarwa bayan amfani daya ta fi amfani

Ko ruwan magani na wanke hannu na musamman ya fi sabulu amfani?

Wani nazari da aka yi a kan wannan a shekara ta 2007 ya nuna cewa sinadarin (triclosan) da yake cikin yawancin magani ko ruwan wanke hannu na musamman bai fi sabulu rage yawan kwayoyin cuta ( bakteriya) da ke hannun mutum ba. Wani nazarin na kwanan nan da aka yi a shekara ta 2015 ma ya kara tabbatar da wannan sakamakon.

A halin da ake ciki ma, karin bincike da nazari da aka yi a baya bayan nan ya nuna cewa amfani da sinadarin triclosan a ruwan magani na musamman na wanke hannu yakan iya kara wa kwayoyin cuta na bakteriya juriya, su zauna a hannun, wanda wanna kuma zai iay haddasa matsala ta sanadiyyar samun karin kwayoyin halitta (hormone) a jikin mai rai dan adam ko dabba, wanda hakan ya sa aka hana amfani da sindarin na triclosan a ruwan magnin wanke hannu a Amurka da Turai.

Bayan wanke hannu, yana da kyau ka yi amfani da tawul ko wani kyalle ko wani abu domin busar da hannunka?

Bincike da dama da aka yi ya fifita amfani da irin takardar nan ko auduga ta musamman, wadda ake amfani daya kawai da ita, wajen goge hannunka ya bushe bayan ka wanke, maimakon ka yi amfani da tawul ko wani kwalle. Domin shi kansa kwalle ko tawul mai lema matattara ce ta zaman kwayoyin cuta.

To mu dawo kan maganar amfani da sabulu da ruwa mai sanyi ko mai dimi ko zafi.

Kana bukatar tsanewa da busar da hannunka bayan ka wanke?

Idan kana sauri ba kasafai za ka iya tsayawa ka busar da hannunka ba bayan ka wanke shi. To wannan ba wata matsala ba ce idan har ba ka taba wani abu ba da hannun lokacin da kake fita daga bandakin.

Amma idan har ka taba wani abu, to zai iya kasancewa ka debi wasu kwayoyin cutar, domin su daman sun fi hawa jikin mutum cikin sauki idan da ruwa ko danshi.

Haka kuma idan ba ka busar da hannun naka ba, bayan ka wanke shi, ka rasa damar raba kanka da ragowar kwayoyin cutukan da ka iya ragewa a tafin hannun naka.

To duk ma dai tsarin da ka zaba na wanke hannunka da busar da shi, muhimmin abin da masu bincike suka gano shi ne, ka dauki tsawon lokacin wankewar fiye da yadda kake tsammani.

Ka wanke hannuwan da sabulu mai kunfa da kyau, ciki da bai, tafi da tsakanin yatsu da karkashin farce akalla daga tsakanin dakika 15 zuwa 30.

An ci kwallo 415 a gasar Firimiyar Nigeria


Hakkin mallakar hoto
NPFL Twitter

Image caption

A ranar Lahadi aka buga wasannin mako na 21 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Kwallo 415 aka ci a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka yi wasannin mako na 21 a ranar Lahadi.

Bayan da aka yi wasa 210 a gasar, an ci kwallo 23 a fafatawa 10 da aka buga a ranar Lahadin.

Kuma dukkan kungiyoyin da suke gida ne suka lashe wasanninsu.

Karawar da aka fi zura kwallo a raga ita ce wadda Abia Warriors ta doke Enugu Rangers da ci 4-0.

Ga ‘yan wasan da suke kan gaba a cin kwallayen:

 • Stephen Odey na Mountain of Fire 14
 • Samuel Mathias El-Kanemi Warriors 11
 • Sunday Adetunji Abia Warriors 11
 • Alhassan Jibrin Akwa United 10
 • Godwin Obaje IfeanyiUbah 9

Man City na daf da sayen Moraes


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Juma’a Manchester City ta amince da Willy Caballero ya bar kungiyar

Manchester City na daf da sayen mai tsaron ragar Benfica, Ederson Moraes kan kudi fam miliyan 33.

A watan Maris din bara Moraes mai shekara 23, ya fara tsaron ragar Benfica, ya zuwa yanzu ya yi wasa 37 a kungiyar da ta lashe kofin Portugal na bana.

Tun a ranar Lahadi a lokacin da Benfica ta doke Vitoria Guimaraes 2-1, Moraes ya ce wasansa na karshe ke nan a kungiyar.

Matashin dan kwallon tawagar Brazil wanda har yanzu bai buga mata tamaula ba, yana daga cikin wadanda aka gayyata wasan sada zumunta da za ta yi da Argentina da Australia a nan gaba.

Kocin City, Pep Guardiola ya dade yana son daukar Moraes a baya can, dalilin da ya sa ya bar Willy Caballero ya bar Ettihad domin dan kwallon ya samu gurbin zama a kungiyar.

Tuchel da Dortmund sun raba gari


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tuchel ya bar Dortmund kwanaki uku da ya lashe kofin kalubalen Jamus

Kocin Borussia Dortmund, Thomas Tuchel ya bar kungiyar bayan shekara biyu yana gudanar da aiki.

Tuchel mai shekara 43, ya koma horar da Dortmund a shekarar 2015, bayan da Jurgen Klopp ya koma jan ragamar Liverpool.

Tuchel ya bar Dortmund ne bayan da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da babban jami’in kungiyar Hans-Joachim Watzke kan harin ta’addanci da aka kai wa kungiyar a ranar 11 ga watan Afirilu.

Sai dai kungiyar ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce kocin ya bar Dortmund ne don radin kansa, babu tantama a tsakaninsu.

A ranar Asabar Dortmund ta lashe kofin kalubalen Jamus, bayan da ta doke Eintracht Frankfurt.

Haka kuma kungiyar ta kare a mataki na uku a gasar Bundesliga ta kakar nan, hakan ya sa kungiyar za ta buga Gasar Zakarun Turai mai zuwa.

Za mu rike Aguero – Khaldoon


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Aguero ya ci kwallo 21 a wasannin Premier 31 da ya buga wa City a 2016/17

Shugaban kungiyar Manchester City, Khaldoon Al Mubarak, ya ce ba sa tantamar makomar Sergio Aguero a kungiyar.

A watan Fabrairu Gebriel Jesus ya maye gurbin Aguero a buga wa City wasanni, dalilin da ya sa aka dinga rade-radin cewar zai bar Ettihad a karshen kakar nan.

Mubarak ya ce ‘ya dade yana jin zantuttuka kan makomar Aguero a City, amma daya ne daga fiattun ‘yan wasa a duniya kuma wajibi ne mu rike shi’.

Aguero ya ci kwallo 33 a wasa 45 da ya buga a kakar nan, kuma sai a shekarar 2020 ne yarjejeniyarsa za ta kare a Ettihad.

Dan kwallon na tawagar Argentina ya fada a watan Maris cewar baya son ya bar Manchester City da murza-leda.

Aisha Buhari ta tafi London ganin mijinta


Hakkin mallakar hoto
Twitter

Image caption

Aisha Buhari ta tafi London ne don duba lafiyar mijinta

A ranar Talata ne uwargidan shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta tafi Birtanyia domin duba mijinta da yake ganin likita a birnin London.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Hajiya Aisha ta yi tafiyar ne a ranar Talata da safe, inda ta tashi ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kafin tafiyar tata dai Hajiya Aisha ta mika godiyarta ga ‘yan Najeriya a bisa goyon bayan da suke bai wa mijinta Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai kuma babu wani bayani da ke nuna ranar da za ta dawo daga tafiyar, kamar dai yadda ba a san ranar dawowar mijin nata ba.

Hakkin mallakar hoto
Twitter

Shugaba Buhari dai ya koma London ne a karo na biyu cikin wanann shekarar a ranar 7 ga watan Mayu, domin likitoci su sake duba lafiyarsa

Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.

Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.

Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.

Wenger zai kara shekara biyu a Arsenal


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa ta badi

Arsene Wenger ya amince zai ci gaba da jan ragamar Arsenal zuwa shekara biyu.

A ranar Litinin ne Wenger da mahukuntan Arsenal suka zauna taro domin fayyace makomar kocin, kuma sai a ranar Laraba ne kungiyar za ta sanar da yarjejeniyar da suka cimma.

Arsenal ta kare a mataki na biyar a kan teburin gasar Premier da aka kammala, inda za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa a badi.

Kuma wannan ne karon farko da Arsenal ta kasa kammala gasar Premier a cikin ‘yan hudun farko tun lokacin da Wenger ya fara jan ragamar kungiyar a shekarar 1996.

Sai dai kuma Wenger wanda ya ci kofin Premier hudu a Gunners ya lashe kofin FA a ranar Asabar bayan da ya doke Chelsea da ci 2-1 a Wembley.

Hakan ne ya sa ya lashe kofin FA na bakwai kuma na 13 da Arsenal ta ci a tarihi.

Me 'yan Niger Delta ke so daga wajen Buhari?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A yanzu dai za a iya cewa an fara samun zaman lafiya da gudanar ayyukan hakar mai a yankin Naija Delta na Najeriya, bayan artabun da aka yi fama da shi na hare-hare kan wuraren hakar mai da bututan man, wadanda kungiyar masu gwagwarmaya da makamai ta Niger Delta Avengers ta rika daukar alhakin kaiwa.

Hakan kuwa ya kai ga raguwar adadin man da ake hakowa a yankin, kuma ya kara dulmuya kasar cikin matsalar koma bayan tattalin arziki.

Wannan kuwa ya biyo bayan yadda gwamnatin kasar ta fara aiki da wasu shawarwari ne, tun da ta shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki na yankin, da kuma mayar da wuka kube da masu gwagwarmaya da makamai na yankin suka yi.

Sai dai kuma, duk da haka, ana ganin wannan zaman lafiya da aka fara samu a yankin na Naija Delta, tamkar na wucin gadi ne. Saboda haka, akwai bukatar bin matakan da za su kai shi ga dorewa.

Prince Maikpobi Okareme, wani tsohon sakataren kungiyar sarakunan gargagjiya na yankunan da ke da albarkatun man fetur na Najeriya, kuma jagoran kungiyar garuruwa masu albarkatun man fetur da gas a Najeriya, ya shaida wa wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed cewa har yanzu da sauran aiki.

”Za a iya cimma nasarar tabbatar da zaman lafiya na dindin ne a zahirin gaskiya, idan muna da tsari na daidaito da gaskiya da adalci. Saboda yadda ake gudanar da abubuwa bai bayar da damar wanzar da adalci a gare mu ba”.

Prince Maikpobi Okareme yana ganin daya daga cikin muhimman abubuwan da har yanzu suke jin za a yi a kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin Naija Delta, shi ne sake fasalta kasar.

”Idan aka yi hakan ne, bangarori daban-daban da suka yi Najeriya, za su sami cikakken hakkin da ya dace da su, kuma su kasance suna rike da wuka da nama na albarkatun da ke yankunansu”.

Shi kuwa Kwamred Thomas Pepple, wani matashi mai fafutukar kare muhalli a yankin na Naija Delta, a hirarsu da wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed, ya yi tsokaci ne cewa ba yadda za a wanzar da zaman lafiya mai dorewa da barazana.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu masu sharhi sun ce sai an kawar da sojoji daga yankin in ana bukatar zaman lafiya

”Idan ana maganar wanzar da zaman lafiya (mai dorewa), to a kawar da sojojin da aka jibge a yankin na Naija Delta. Ba fa za a iya yin amfanin da makami a ce za a tabbatar da gudanar zaman lafiya ba. Duk wani zaman lafiya da za a samu ta hanyar yin amfani da tsoratarwa, to ba tabbatace ba ne. Kuma a karshe sai ka ga matsalar da ake gudu ta sake dawowa”.

Mai fafutukar kare muhallin, ya ce a duk wani shirin wanzar da zaman lafiya mai dorewa, da kuma kokarin bunkasa yankin na Naija Delta, da za a yi, dole sai an hada da kowanne bangare na mutanen yankin.

”A yi tsayuwar daka wajen sanya ainihin mutanen yankin a ciki. Su shugabanni a iya tattaunawa da su a nasu matakin, amma a sanya matasa cikin lamarin. A kuma hada da masu fafutukar kare hakkin bil’Adama da muhalli, da kungiyoyin farar hula da dai sauran masu ruwa da tsaki.

“Kuma a gano irin matsalolin da ke addabar talakawan yankin, ta fuskar noma da ilimi da dai sauransu, a dau mataki kyauatata masu.”

Akwai kuma bukatar duba batun cin hanci da rashawa game da kudaden da ake ware wa sha’anin bunkasa yankin na Naija Delta.

Domin Kwamred Pepple Thomas ya yi zargi cewa, ”Kudaden da ake ware wa yankin Naija Delta za ka tarar ko dai an sace su, ko an yi almundahanar su, ko kuma an yi amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba”.

An dade ana yin irin wannan zargi, amma kuma galibi wadanda abin ya shafa suna musanta hakan.

A yanzu dai an yi ittifaki, cewa ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta bi shawarwarin da suka dace, don ganin an ririta zaman lafiyan da aka fara samu a yankin Naija Delta, kuma a tabbatar da dorewarsa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yankin Naija Delta na da arzikin man fetur

Ko azumi na ƙarawa mutum kuzari lokacin aiki?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ko azumi na ƙarawa mutum kuzari a wajen aiki?

Yin azumi akai-kai wanda ya zama jiki da ake yi a matsayin wata hanya ta rage ƙiba,ko ya na taimakawa wajen ƙara maka kuzarin aiki a cikin mako?

Al’adar nan ta yin azumi ta zama jiki musamman irin wanda wasu mutane ke yi inda suke takaita cin abincin da ke sa ƙiba na wasu kwanaki.

Irin waɗannan mutunen su kan yi gwajin azumi na sa’o’i daban-daban kamar azumi daga sa’o’i 36 ko mafi tsanani wato sa’o’i 60 suna azumin.

Akwai wasu shaidu da suka nuna cewa taƙaita cin abinci da ke sa ƙiba yana da illa ta fuskar kiwon lafiyar mutum a nan gaba wadanda suka haɗa da ƙarfafa yanayi da kuma samun ingantaccen barci.

Sai dai wasu ma’aikata a California sun zaɓi wani ɓangaren da yake da fa’ida a al’adar inda suka ce a ranakun da basa cin abinci sun fi yin aiki a sosai a ofisoshinsu.

Sun ce sun fahimci cewar sun fi samun kuzari da kaifin tunani a lokutan da su ke aiki suna kuma azumi.

Waɗannan mutane da ke kiran kan su WeFast wasu abokai ne a shafin Internet da suka yi amannar cewa jirkita tsarin kiwon lafiyar dan adam zai iya haddasa ƙarin lafiya da kuma samun ingantaccen rayuwa.

Sun yi gwaji na sa’o’i daban daban daga sa’o’i 36 na dakatar da cin abinci zuwa mafi tsanani wato sa’o’i 60 suna azumi.

Wasu kuma sun bi sahu inda suka yi azumin na sa’o’i 23 a rana.

Manufar dai ita ce su tantance yadda azumin su ya kasance daga ƙarshe.

Hakkin mallakar hoto
Peter Bowes

Image caption

Mambobin kungiyar WeFast suna haɗuwa duk ranar Laraba domin yin buɗe baki

A birnin San Francisco ne dai wani kamfani mai suna Nootrobox ya ɓullo da tsarin azumin WeFast.

Kamfanin yana yin wasu ƙwayoyi ne na ƙara kuzari da ake kira nootropics da ke ƙara kaifin basira.

Yin azumi na daga cikin al’adar kamfanin, ko da ya ke ba wajibi ba ne, amma kusan kowa a ciki tawagar ta mutum 13 yana yi azumin a ranar Talata.

A ranar laraba da safe ne kuma su kan haɗu da sauran ‘yan ƙungiyar WeFast mai mambobi kimanin 1,200 domin yin buɗe baki.

Ana dai yin buɗe bakin ne a wurin shan shayi da ke cikin unguwanni, inda mambobin ƙungiyar kan yi wa juna bayani game da yadda su ka ji a lokacin da su ke azumin.

“Babban abu da ya faru da ni da kuma mutane da dama a wannan ƙungiyar shi ne na tunanin ƙara himma a wajen aiki,” in ji Geoff Woo, shugaban kamfanin Nootrobox.

Mai yiwuwa akwai wani abu da suka ci ko kuma suka sha.

Sai dai bincike da aka gudanar sun gano cewa nau’o’in azumi daban daban yana matukar tasiri ga jikin dan adam.

Yayin da hujjoji akan tasirin da azumi ke yi a kan ayyuka ba lallai ne ya zama gaskiya ba, mutane da dama wadanda su ke bin al’adar yin azumin sau da ƙafa- kamar rahoton mambobin kungiyar WeFast da ke cewa sun lura da yadda suka samu ƙarin himma, kamar yadda masu tseren wasanni su kan ji.

Bincike da aka gudanar a ɗakunan bincike sun nuna cewa wasu sauye sauye na sinadarai da ake samu a ƙwaƙwalwa sune ke janyo hakan.

Mark Mattson, Farfesa ne fannin ƙwaƙwalwa a jami’ar Johns Hopkins wanda ya ce binciken sa ya nuna cewa suna ƙara yanayin tunani.

Ana dai zaton cewa mutane da su ke jin ƙarin kuzari a lokacin da suka fara ƙona kitse a jikin su maimakon abinci da ke sa mutum ƙiba, in ji Dr Eric Verdin wani mai bincike a cibiyar Gladstone dake birnin San Francisco.

Sai dai azumi yana da haɗari ga wasu mutane musamman mata masu ciki ko kuma waɗanda ke shayar da jarirai, ko kuma masu cutar suga wato diabetes da wasu cututtuka masu nasaba.

Domin a duk lokacin da jiki ya gaji, kuma aka taƙaita masa samun abinci mai gina jiki, lamarin ka iya yin muni.

A don haka ga duk wani da ke da sha’awar yin azumi irin wanda masu bincike akan lafiyar dan adam a San Francisco wato ‘biohack’, zai fi kyau ya tuntubi likitan sa tukuna.

Idan kana son karanta wannan labari a harshen Ingilishi latsa nan: Can giving up food make you work better?

Al'amura sun tsaya cak a 'yankin Biafra'


Image caption

Manyan kasuwanni sun kasance a rufe

Rahotanni daga Kudu maso Gabashin Najeriya na cewa al’amura sun tsaya cak a wasu manyan biranen yankin don nuna hadin kai kan kiran da kungiyoyin da ke fafutukar kafa yankin Biafra suka yi na kasancewa a gida.

Kungiyoyin IPOB da MASSOB sun yi wannan kira ne na cewa mutane su zauna a giadajensu a matsayin zanga-zangar lumana, don tunawa da shekara 50 na fara fafutukar kafa yankin Biafra da marigayi Chukwuemeka Ojukwu ya yi.

Wakilin BBC da ke Enugu AbudsSalam Ibrahim Ahmed ya ce fiye da kashi 90 cikin 100 na shagunan da ke birnin a rufe suke, haka ma babbar kasuwar birnin ta kasance a rufe.

Sai dai kuma ana ci gaba da harkokin sufuri.

Image caption

Masu fafutukar kafa yankin Biafra sun sha yin zanga-zanga

Haka ma a birnin Umuahia inda nan ne garin jagoran masu fafutuka na kungiyar IPOB Nmandi Kanu ya fito, yawanci shaguna sun kasnace a rufe amma akwai kadan da suka bude.

A birnin Anacha na jihar Anambra kuwa, harkokin da suka hada da na kasuwanci da sufuri da makarantu da bankuna duk sun kasance a rufe.

Dukkan sauran jihohin yankin ma ana cikin irin wannan yanayi. Yankin Kudu maso Gabas dai ya kunshi jihohin Anambra da Enugu da Abia da Imo da kuma Ebonyi.

Zuwa yanzu dai babu wani rahoto na tashin hankali, amma tuni aka jibge jami’an tsaro a muhimman wurare da ke jihohin yankin.

Wenger ya gana da shugaban Arsenal kan makomarsa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal ta doke Chelsea da ci 2-1 ranar Asabar, inda ta lashe kofin FA

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya gana da mutumin da ya mallaki kulob din, Stan Kroenke, game da makomarsa ranar Litinin.

Sai dai ba a san ko sun yanke wani hukunci ba tukuna, amma ana da tabbacin cewa makomar Wenger a kulob din tana hannunsa da Kroenke da kuma daraktocin kulob din wadanda za su yi wani taro ranar Talata.

Har ila yau, Wenger, mai shekara 67, ya gana da shugaban zartarwan kulob din Ivan Gazidis a ranar Litinin.

Mista Gazidis ya sha bayyana goyon bayansa ga kocin da kuma ba shi tabbacin cewa zai samar masa da duk abin da zai bukata don ya lashe Gasar Firimiya.

A ranar Laraba ne kulob din zai fitar da sanarwa game da makomar kocin.

Arsenal ta yi rashin nasara a wasanni 12 tsakanin ranar 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Afrilu, ciki har da wasan Bayern Munich ta doke su da ci 10 – 2 (jimulla) a Gasar Zakarun Turai.

Sai dai Arsenal ta doke Chelsea ranar Asabar, inda ta lashe kofin FA.

Roma ta sallami kocinta Luciano Spalletti


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Luciano Spalletti ya jagoranci Roma tsakanin 2005 zuwa 2009

Kolob din AS Roma ya sallami kocinsa Luciano Spalletti bayan ya kammala Gasar Serie A ta bana a mataki na biyu.

Sanarwar sallamar ta zo ne bayan da kulob din ya doke Genoa da ci 3-2 ranar Lahadi.

Spalletti ya koma Roma ne a karo na biyu a watan Janairun shekarar 2016.

Shugaban Roma Jim Pallotta ya ce “muna godiya ga Spalletti bisa yadda ya yi aiki tukuru tun bayan komawarsa jogorancin kulob din.”

Ya ci gaba da cewa: “a karkashin jagorancinsa kulob din ya samu maki mai yawa kuma ya zura kwallaye a raga fiye da kowane lokaci a tarihin Roma. Muna yi wa Luciano fatan alheri a duk abin da zai yi a nan gaba”

Spalletti, mai shekara 58, ya jagoranci Roma tsakanin shekarar 2005 zuwa 2009, sau biyu yana lashe kocin Coppa Italia, gabanin ya ajiye aiki ya koma Zenit St Petersburg na kasar Rasha.

Kocin wanda kwangilarsa da Roma ta kare a kakar bana, yana shan suka game da tsawon lokacin da yake sanya fitaccen dan wasan kulob din Francesco Totti ya yi wasa.

Totti, mai shekara 40, ya yi ritaya daga tamaula ranar Lahadi bayan ya shafe shekara 25 a Roma.

Ernesto Valverde ne sabon kocin Barcelona


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ernesto Valverde ya jagoranci kulob din Athletic Bilbao har tsawon shekara hudu

Kulob din Barcelona ya nada Ernesto Valverde a matsayin sabon kocinsa har tsawon shekara biyu.

A makon jiya ne kocin wanda tsohon dan wasan Barcelona ne ya ce zai bar kolub din da yake jagoranta Athletic Bilbao bayan ya shafe shekara hudu a can.

Shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu ya yaba da kwazo da gogewar Valverde, inda ya bayyana shi da “wanda ya iya renon kananan ‘yan wasa kuma tsohon dan wasan Barca”

Sabon kocin, mai shekara 53, ya maye gurbin Luis Enrique, wanda a watan Maris ya ce zai bar Barca a karshen kakar bana bayan ya yi shekara uku da su.

A wasan karshe da Enriqueya jagoranci Barcelona, kulob din ya doke Alaves da ci 3-1, inda hakan ya ba su damar daukar kofin Copa del Rey a ranar Asabar.

Valverde ya yi wasa a Barcelona a tsakanin sheakarun 1988 zuwa 1990, inda ya ciyo mata kwallaye takwas a wasa 22 da ya buga.

Dan asalin kasar Spain, Valverde ya jagoranci Athletic Bilbao ta samu matsayi na bakwai a kakar La Ligar bana, yayin da Barcelona ta kare a mataki na biyu, Real Madrid kuma ta zama zakara

Guguwa ta sa kwashe mutum miliyan 1 a Bangladesh


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dubban mutane ne aka kwashe zuwa tudun mun tsira a Bangladesh

Wata gawurtacciyar guguwa ta auka wa gaɓar tekun Bangladesh, cikin rakiyar mamakon ruwan sama da ƙaƙƙarfar iska mai gudun da ya zarce kilomita 100 cikin sa’a guda.

Guguwar mai suna Mora ta dira ne a wani yanki tsakanin birnin Chittagong da gaɓar tekun Cox’s Bazar mai harkokin kamun kifi.

Hukumomi na kwashe sama da mutum miliyan ɗaya zuwa wasu yankuna da ba sa fuskantar hatsari.

Hukumomi sun umarci birane masu tashoshin jiragen ruwa a kudu maso gabashin Bangladesh su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Gawurtacciyar guguwar ta taso ne bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a ƙasar Sri Lanka, da ta haddasa ambaliya da zaftarewar ƙasar da ya hallaka aƙalla mutum 180.

Ambaliyar ruwa mafi muni da aka taɓa yi cikin shekara 14 a tsibirin ta shafi mutane fiye da rabin miliyan. Haka kuma, mutane fiye da 100i sun yi ɓatan dabo.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ana ta kwashe kaya daga kantuna a bakin tekun Patenga a birninChittagong

Mutane a gundumar Chittagong sun cunkusu a matsugunai kimanin 500 na tudun mun tsira, bayan da aka sanar da gargadin ta amsa-kuwwa.

An yi amfani da gine-ginen makarantu da ofisoshin gwamnati wajen tsugunnar da mutane, kuma an umarci mazauna yankunan da ke kan tsaunuka su ƙaurace.

Wani wakilin BBC ya ce Duk da cewa Bangladesh ta saba da fuskantar gawurtattun guguwa, mutane da dama ba sa zama a ingantattun wuraren da za su rika jurewa yanayi maras kyau.

Don haka rayuwarsu, da amfanin gonarsu da suka dogara da su kan fuskanci barazana a duk lokacin da irin guguwa ta auka.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ambaliyar ruwa a kasar Sri Lanka ta raba mutane fiye da rabin miliyan da matsugunansu

Bangladesh ba ta gama murmurewa daga bala’in ambaliyar ruwan da ya auka mata a yankin arewa maso gabashin kasar ba cikin watan Afrilu, wadda ta lalata gonakin shinkafa, tare da haddasa ƙazamin tashin farashinta a kasuwanni.

Haka kuma gaguwar na iya shafar wasu yankunan arewa maso gabashin Indiya da yammacin ƙasar Myanmar.

Kusurwar tekun Bengal na ɗaya daga cikin gaɓar teku mafi fuskantar baƙin hadari a duniya.

Kun san maganin kashe kwayoyin cutar da ka iya ceton rai?


Image caption

Sabon launin maganin kashe kwayoyin cutar ka iya ceto rayuka da dama in ji kwararru

Masana kimiyya sun yi bajintar ƙirƙiro wani sabon launin maganin kashe ƙwayoyin cuta, da ka iya ceto rayukan ɗumbin al’umma.

Sun ce binciken zai inganta yaƙin da suke yi da cutuka masu bijire wa magunguna – ɗaya daga cikin babbar barazana ga lafiyar al’ummar duniya.

Masu bincike sun jirkita rukunin ƙwayar atom na wani magani mai suna Vancomycin inda ƙarfinsa ya ninka har sau kusan dubu guda.

Maganin ka iya far wa ƙwayar cuta ta fuska uku, abin da zai zame mata mai matuƙar wahala ta samu kuzarin rama faɗa.

Dr. Dale Boger na cibiyar Scripps a California shi ne jagoran masu wannan nazari.

Ya ce “Sauyin da muka yi masa, zai kasance abu mai wahala ƙwayar cuta ta iya bijirewa wannan magani.”

Alƙaluma sun ce irin waɗannan cutuka na haddasa mace-mace kimanin dubu 50 duk shekara a Amurka da Turai.

'Yan adawar Borno daga su har karnukansu sun gudu'


Hakkin mallakar hoto
Borno state government

Image caption

‘Yan adawar Borno sun gudu sun tare Abuja da Kano da Kaduna in ji gwamna Shettima

Gwamnan Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, Kashim Shettima ya zargi ‘yan adawar jihar da tafka ƙeta da makirci bayan sun gudu sun bar Borno.

Jihar Borno ita ce ta fi fama da hare-haren ƙungiyar ‘yan ta-da-ƙayar-baya ta Boko Haram.

A cewar Kashim Shettima na jam’iyyar APC, ‘yan adawar gwamnatinsa duk sun gudu sun tare a Abuja da Kano da kuma Kaduna.

“Kin san ɗan adawa ba abin da za ka yi, ya yaba maka. Mafi yawansu ba sa Maiduguri, sun gudu da karnukansu da kyawoyinsu da gidajensu duka sun gudu… Suna makirce-makircensu.”

Ya ce su ‘yan adawa, idan ba a ƙeta da makirci ba, ba abin da suka sa a gaba ba, musammam ‘yan adawar Borno.

Ya yi iƙirarin cewa wasunsu shekara huɗu kenan rabonsu da Borno.

Kashim Shettima na mayar da martani ne kan zargin sace kuɗaɗen ƙananan hukumomi da ake yi wa gwamnatinsa.

A cewarsa nawa ƙananan hukumomin jihar suke samu da har za a yi batun sacewa? Yawanci sai an tallafa musu kafin ma su iya biyan albashin ma’aikatansu, in ji shi.

Ya ce gaskiya batun shi ne babu wanda yake danne kuɗin ƙananan hukumomi, kuma kuɗin da suke samu a baya, yanzu ba sa samunsu. Baya ga sansanonin ‘yan gudun hijira da suke da su a Maiduguri.

Bana 'yan gudun hijira za su yi layya a gida — Shettima


Image caption

Za mu mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu kwana talatin bayan azumin watan Ramadan

Gwamnatin jihar Borno a Nijeriya ta yi alƙawarin mayar da dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da mahallansu zuwa garuruwan da aka sake ginawa nan da wata biyu.

A baya dai gwamnatin Bornon ta yi alƙawarin mayar da waɗannan ‘yan gudun hijira garuruwansu kafin ƙarshen watan Mayun wannan shekara.

Gwamnan jihar Kasheem Shettima ya ce jinkirin mayar da mutanen na da alaƙa da buƙatar ƙarasa gine-ginen wasu muhimman wurare kamar makarantu da asibitoci da rijiyoyin burtsatsai kafin mutane su koma garuruwansu.

Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun ce mutane fiye da miliyan biyu ne rikicin Boko Haram ya tilastawa barin muhallansu a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Akasarin waɗannan ‘yan gudun hijira na zaune ne a sansanoni daban-daban a faɗin yankin, ko da yake, mafi yawan sansanonin na cikin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Baya ga haka akwai ‘yan gudun hijrar Nijeriya sama da dubu 450 da ke zaune a wasu sansanonin da ke ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi da suka nemi mafaka sakamakon hare-haren Boko Haram.

“A garin Damasak kaɗai akwai mutum dubu 72, kuma mun gina garin har zuwa kashi saba’in da biyar cikin ɗari. Inda muka samu matsalaloli su ne garuruwan Bama da Gwoza ko da yake, an ci karfin aikin.”

Duk da yake, har yanzu akwai matsalolin tsaro a wasu yankuna da ke dajin kusa da garin Bama, amma gwamna Shettima ya bayar da tabbacin cewa wannan ba zai hana mayar da mutane garuruwansu ba.

Hakkin mallakar hoto
Borno state government

Image caption

Gwamnatin jihar Borno na kan aikin gina garuruwan ‘yan gudun hijrar Boko Haram

Ya ce gwamnati za ta dauki matakan da duk suka dace na ganin ta kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

“Na bayar da tabbacin cewa kwana talatin bayan azumi za mu mayar da su, mun yi imani mutane za su yi sallar layya a garuruwansu.”

Ƙauyukan da ke bayan Dutsen garin Gwoza in ji gwamna Shettima, na daga cikin wuraren da har yanzu ba zai yiwu a mayar da mutane ba, saboda ɓurɓushin ‘yan Boko Haram da ke maƙale a can, ko da yake ya ce sojoji na ci gaba da ƙoƙarin kakkaɓe su.

Ya kuma ce ‘Yan gudun hijirar Nijeriya dubu saba’in da takwas ne a kasar Kamaru. Kuma akwai wasu dubu bakwai a garin Banki da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Kamaru, yayin da wasu ke ƙauyen Pulka na garin Gwoza.”

Gwamna Shettiman ya ce za a mayar da makarantar sakandaren garin Bama matsugunan waɗannan ‘yan gudun hijira da zarar an kwaso su, kafin a san matakan da za a ɗauka na tallafa musu da sake mayar da su wurarensu na asali.

Jihar Borno dai nan ce inda hare-haren mayaƙan Boko Haram suka fi muni, don kuwa ita ce tungar Boko Haram kafin sojin Nijeriya su fatattaki mayaƙanta.

Arwar damusa ta kashe mai kula da namun daji


Hakkin mallakar hoto
Hamerton zoo

Image caption

Gandun namun dajin na da kewayen damusoshin ƙasar Malaysia da Bangladesh

Wata mai kula da namun daji ta mutu “sakamakon tsurewa” bayan wata damusa ta shiga wani kewaye da take ciki a wani gandun namun daji.

Matar ta mutu ne a gandun namun dajin Hamerton, da ke kusa da Huntingdon, a yankin Cambridgeshire a Ingila.

‘Yan sandan Cambridgeshire sun ce: “Wata damusa ce ta ɓalle inda ta shiga wani kewaye da ita mai kula da namun dajin ke ciki. Kuma abin ya zo da ƙarar kwana, matar ta mutu a wajen.”

An fitar da masu ziyara daga gandun namun daji. Kuma ‘yan sanda sun ce babu lokacin da dabbar ta kuɓuce daga cikin kewayen.

Gandun namun dajin Hamerton ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: “Wannan (mutuwa) ga alama ta auku ne sakamakon tsananin tsurewa da mai kula da dabbobin ta yi.

“Muna matuƙar juyayi da taya abokan aiki da ‘yan’uwa da abokai alhinin wannan mummunan al’amari.”

Hakkin mallakar hoto
HAMERTON

Image caption

A bara ma sai da aka ƙara buɗe wani kewayen ajiye damusa a gandun

Gandun namun dajin ya ce za a gudanar da bincike kan wannan al’amari.

Wani mai ziyara a gandun namun dajin ya ce: “Mun kusa zuwa kewayen damusar sai wani mai kula da namun dajin ya ƙwalla mana kira cewa duk mu yi sauri mu fita.”

Gandun namun dajin wanda aka buɗe a shekarar 1990 na ƙunshe da damusoshin ƙasar Malaysia da na Bangladesh da kyarkeci da dila da sauran dabbobi da nau’o’in tsuntsaye.

Ko a shekara ta 2008 ma wani yaro ɗan shekara tara ya gano wata damusa a lambun gidansu bayan ta kuɓuce daga dandalin.

Joe Hart ya bar Torino – ko ina zai koma?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Joe Hart ya yi wa Torino wasa 36 a kakar bana

Golan Manchester City Joe Hart ya ba da tabbacin cewa zai bar kulob din Torino, bayan a zauna a kulob ɗ in da ke ƙasar Italiya a matsayin aro har tsawon kaka daya.

Hart mai shekara 29 ya koma kulob ɗin ne a watan Agustan bara, bayan da Kocin City Pep Guardiola ya ba shi zabin yin hakan.

Kocin Torino Sinisa Mihajlovic ya ce ya so dan wasan ya ci gaba da wasa da su, amma kulob din ba shi ƙarfin sayensa.

“Na gode Torino, Ina alfahari da na yi wasa a kulob din da ya fita daban da saura,” inji golan Ingilan kamar yadda ya bayyana a shafinsa na sada zumunta ranar Litinin.

“Zan dawo don ganawa da ku duka, sai wata rana, ina muka fatan kakar wasa mai kyau.”

An ƙare Gasar Serie A, Torino tana a matsayi na tara, bayan wasanta na karshe da ta doke Sassuolo da ci 5-3.

Hart ya lashe kofuna 68 a kasar Ingila kuma ana danganta dan wasan da kolob da dama na Gasar Firimiya da kuma Turai..

Zai kashe kansa don an hana shi takarar shugaban ƙasa a Kenya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hukumar zaben kasar ta hana Peter Gichira takara ne saboda ya gaza samun goyon bayan da ake bukata

Ana tuhumar wani ɗan siyasa a ƙasar Kenya da laifin yunkurin kashe kansa ta hanyar faɗowa daga bene, bayan hukumar zaɓen ƙasar ta hana shi tsayawa takarar shugabancin ƙasar.

Sai dai Mista Peter Gichira ya musanta zargin yayin zaman wata kotu a babban birnin kasar Nairobi, kuma an ba da shi beli.

‘Yan sanda sun an kama shi a ranar Asabar yayin da yake kokarin faɗowa daga benen hukumar zaɓen kasar mai hawa shida.

Peter yana daga cikin masu neman takarar shugabancin ƙasar takwas da suka kasa cika sharuddan tsayawa takara a zaɓen da kasar za ta yi a 8 ga watan Agusta mai zuwa.

Peter ba ya cikin ‘yan siyasar ƙasar da suka yi fice. An fara saninsa ne bayan yunkurin kashe kansa da ya yi a ƙarshen makon jiya.

An hana shi damar tsayawa a zaben ne bayan da ya gaza samun goyon bayan mutum 2,000 wanda ba su alaka da kowace jam’iyya kuma suka fito daga akalla jihohi 24 cikin 47 da kasar take da su.

Wasu jami’an ‘yan sanda biyu ne suka cafke Mister Gichira bayan ya fasa daya daga cikin tagar benen kuma yana kokarin faɗowa, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda yake neman wa’adi na biyu, da kuma jagoran ‘yan adawar kasar Raila Odinga, wanda yake takara a karo na hudu.

An jefe magidanci har ya mutu a Somaliya


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Al-Shabab shi ne babban reshen al-Qaeda a Gabashin Afirka

Masu tada kayar baya a kasar Somaliya sun jefa wani magidanci har sai da ya mutu bayan wata kotun ta same shi laifin aikata zina.

An binne marigayin mai suna, Dayow Mohamed Hassan ne iya wuya, inda daga nan mayakan al-Shabab suka rika yi masa ruwan duwatsu har sai da ya mutu.

Daruruwan mutane ne suka taru a lokacin da ake zartar da hukuncin a kauyen Ramo Adey da ke lardin Bay da ke kasar Somaliya.

Al-Shabab ta samu Dayow, mai shekara 44 ne da laifi yi wa wata mata ciki, duk da cewa yana da mata biyu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Kungiyar al-Shabab ta saba yanke irin wannan hukunci a yankunan da suke karkashin ikonta a kasar.

A shekarar 2014, kungiyar ta jefe wani yaro har sai da ya mutu bayan ta same shi da laifin yi wa wata mata fyade. Hakazalika, an kashe wata yarinya matar aure a irin wannan hukuncin bayan da suka same ta da laifin aikata zina.

Ernesto Valverde ne zai zamo sabon kocin Barcelona


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sabon Koci Ernesto Valverde ya taka muhimmiyar rawa yayin da yake wasa a kulob din Espanyol da kuma Athletic Bilbao

A na sa ran a ranar Litinin kulob din Barcelona zai sanar da nadin Ernesto Valverde a matsayin sabon kocin kungiyar bayan tafiyar Luis Enrique.

Tsohon dan wasan gaban Barca Valverde ya sanar a makon jiya cewa zai bar Athletic Bilbao bayan ya shafe shekara hudu yana jagorantar kungiyar.

Kocin mai shekara 53 zai maye gurbin Luis Enrique, wanda a watan Maris ya ce zai bar Barca a karshen kakar bana bayan ya yi shekara uku da su.

A wasan karshe da Enriqueya jagoranci Barcelona, kulob din ya doke Alaves da ci 3-1, inda hakan ya ba su damar daukar kofin Copa del Rey a ranar Asabar.

A ranar Litinin ne ake sa ran Shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu zai fitar da wata sanarwa kan batun.

Valverde ya yi wasa a Barcelona a tsakanin sheakarun 1988 zuwa 1990, inda ya ciyo mata kwallaye takwas a wasa 22 da ya buga.

Dan asalin kasar Spain, Valverde ya jagoranci Athletic Bilbao ta samu matsayi na bakwai a kakar La Ligar bana, yayin da Barcelona ta kare a mataki na biyu, Real Madrid kuma ta zama zakara.

Me ya sa tafiyar sa'a ɗaya ke ɗaukar kwana biyar a Afirka?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kamfanonin jiragen sama na duniya sun mamaye zirga-zirga a yammacin Afirka

Kamata ya yi tafiya a jirgin sama tsakanin manyan birane yammacin Afirka biyu wato Freetown da Banjul ayi tsawon sa’a ɗaya kacal, amma wakilin BBC Umaru Fofana ya gano cewa saboda rashin kyawun tsarin sufuri, tafiyar kan fi sauki da sauri idan aka bi ta ƙasar Morocco ko kuma Belgium, wanda hakan ya sa tafiyar ta koma kusan ta tsawon kwana guda.

A baya-bayan nan na yi tafiya zuwa kasar Gambiya don yi wa BBC aiki.

A ka’ida, wannan tafiya mai nisan kilomita 1,000 kan dauki sa’a daya ne kawai, kuma kasar Gambiya ta yi fice ta fuskar yawon bude idanu, wacce ke karbar bakuncin jirage da yawa daga nahiyar Turai.

Sai dai jirage biyu kacal ne ke tashi daga Freetown zuwa Banjul a mako, kuma na yi rashin sa’a ranakun ba su yi daidai da tafiyata ba.

Mafita daya ita ce, mu hau jirgin Royal Air Maroc mu bi ta Casablanca, wato kasar Morocco, inda za mu jiran kusan sa’o’i 30, kuma babu tabbacin samun wurin kwana ga fasinja.

To Amma ta fi sauri, kuma ta fi tsada, idan aka bi ta birnin Brussels na kasar Belgium sannan a tsallaka zuwa Banjul.

Wannan kan dauki sa’o’i 24 “kawai” wato kwana guda ke nan.

Wani zabin shi ne mutum ya shiga jirgin Air Cote D’Ivoire, wanda sabon yankan-rake ne a fagen zirga-zirgar jiragen sama.

Wannan na nufin sai an biyo ta Abidjan (Cote D’Ivoire), sannan ta Dakar (Senegal) sai kuma a tsallaka Banjul (Gambiya).

Sai dai kuma, dole in kwana a Abidjan, da kuma yiyuwar kara kwana a Dakar, domin samun jirgin Brussels, wanda shi ne kadai hanyar da aka dogara da ita, ta zuwa Banjul daga birnin na Dakar.

To ka ga tafiyar ta dauki kusan kwana uku ke nan.

A karshe dai, na zabi hawa mota zuwa Conakry (Guinea), kafin na samu jirgi zuwa Dakar, babban birnin Senegal, inda na kwana a nan domin samun jirgin da zai kai ni Banjul washe gari.

Na shafe tsawon kwanaki biyu a tafiyar, wace ba ta fi tsawon sa’a daya ba.

A dawowata ma tafiyar ta fi ba ni wahala. Na taso daga Banjul zuwa Dakar, na kwana a can, sannan na sauka Conakry washegari da yamma.

Sai dai na kara kwana a babban birnin na Guinea, sannan na shiga mota zuwa Freetown a rana ta uku.

‘Tafiyar na da tsada’

A Conakry, na hadu da wasu matafiya wadanda ke kan tafiye-tafiye daban-daban tsakanin yankin yammacin Afirka.

Mafiya yawansu ‘yan kasuwa ne, wadanda suke korafe-korafe game da rashin kyawun tsarin tafiyar, inda suke cewa hakan ya sa tafiya ta yi tsada.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kamfanonin kasashen yankin kamar su Cote D’Ivoire Air sun kasa magance matsalar

“Wannan na haifar da hauhawar farashin kayyakin masarufi,” inji wata daga Freetown wace ke saro kaya daga Guinea domin sayarwa a garin Bo, da ke Kudancin Sierra Leone.

Omodele Jones, wani dan kasuwa ne da ke zaune a Gambiya ya shaida min cewa dole ya sauya tikitinsa na jirgi daga Banjul-Brussles zuwa Nairobi saboda jirginsa ya soke saukarsa a Dakar, inda da farko aka tsara yadda zai je Nairobin.

“Da ya sa na bata lokaci, wanda zai lakume kudi masu yawa, da kuma jira akalla kwana biyu kafin zuwa Nairobi ta Dakar,” inji Omodele.


Me ya hana harkokin sufurin jiragen sama kankama a Afirka

Kasashen Afirka da dama sun fara harkokin sufurin jiragen sama bayan samun ‘yancin kansu, yawanci da niyyar zuwa kasashen da ke ketaren nahiyar.

To sai dai da yawa daga kasahen ba su cimma wannan manufa ba, saboda rashin kyawawan manufofi wadanda suka hana gogayya cikin shekarau da dama.

Hatta kamfanonin da ke da kima ta fuskan tabbatar da bin doka da oda sun fuskanci matsala bayan da aka hana su shiga kasashen Turai saboda rashin tabbacin lafiyar jiragensu.


To sai dai shekara 50 bayan samun ‘yanci, da yawa daga cikin kasashen Afirka, suna da kyakkyawar alakar sufurin jiragen sama da kasar da ta yi musu mulkin mallaka, fiye da makwabtansu.

Akwai jirage da yawa da ke tashi daga Gambiya zuwa Ingila wace ta yi mata mulkin mallaka, sai dai kuma kadan ne ke tashi zuwa makwabciyar kasar Senegal.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Filin jiragen sama na kasa-da-kasa na Gnassinge Eyadema da ke Lome,

Haka kuma akwai jirage da yawa da ke zuwa Dakar daga Faransa wace ita ce ta yi wa Senegal din mulkin mallaka.

Daya daga cikin dalilan da suka sa harkar sufurin jirage tsakanin biranen yammacin Afirka ta fadi shi ne karyewar kamfanonin kasashen yankin Ghana Airways, da Senegal da kuma da yawa a Najeriya.

Sai dai wasu kasashe a yankin sun dauki matakan magance wannan matsala, ta hanyar bullo da sababbain kamfanoni, kamar ASKY da ke Lome babban birnin kasar Togo, inda ake fadada katafaren filin saukar jiragen sama.

An kafa shi ne a shekarar 2008, amma sai dai har yanzu ba a fara daukar mutane zuwa sauran kasashen yankin ba.

Buhari da APC sun jefa Nigeria cikin haɗari — PDP


Hakkin mallakar hoto
AFP

Jami’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce shekara biyun da Shugaba Muhammadu Buhari da jami’yyar APC suka shafe a kan mulki ba abin da ya haifar sai ƙuncin rayuwa da jefa ƙasar cikin haɗari.

Ɓangaren Sanata Ahmed Makarfi na PDP, ya ce babu wani abin alfahari a ranar bikin ranar 29 ga watan Mayu – ranar da ƙasar ta koma tafarkin demokuraɗiyya – saboda al’amura sun lalace.

Wata sanarwa da PDP ta fitar ce “gwamnatin APC da Muhammadu Buhari sun lalata tushen demokuraɗiyyar da jam’iyyarmu ta kafa tare da hana ‘yan adawa rawar gaban hantsi”.

Sai dai muƙaddashin Shugaban Najeriyar Yemi Osinbajo, ya ce sun shafe shekarar 2016 suna ƙoƙarin gyara barnar da PDP ta yi a baya.

A jawabin da ya gabatar domin bikin ranar ta demokuraɗiyya, ya ce gwamnatinsu tana kan hanyar farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ta hanyar samar da ayyukanci da tsaro da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ƙara da cewa ana samun ci gaba a dukkan fannonin gwamnati, sai dai ya amince cewa yaƙi da cin hanci da gwamnatin ke yi na tafiyar hawainiya.

Amma anata ɓangaren PDP, ta ce babu abin da Buhari da APC suka sanya a gaba sai “muzgunawa ‘yan adawa da kawar da turakun da suka kafa tsarin demukuraɗiyya”.

Ta ƙara da cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, to tana matuƙar tsoron “mummunar makomar da zaɓen shekarar 2019 zai iya haifarwa”.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alƙawura da dama lokacin yaƙin neman zabe

Ra’ayin ‘yan Najeriyar dai ya rabu kan rawar da shugaban, wanda yanzu haka ke Ingila domin jinya, ya taka a kan ragar mulki.

Yayin da wasu ke ganin baikonsa tare da alkawarin ba za su sake zabarsa ba, wasu kuwa cewa suke yi shugaban ya taka rawar gani idan aka la’akari da irin matsalolin da ya gada.

Masana na ganin a yanzu da gwamnatin ta cika shekara biyu a kan mulki, hankula za su karkata ne kan harkokin siyasa da yadda za a tunkari zaɓen 2019.

Sai dai rashin lafiyar Shugaba Buhari ka iya kara jefa fagen siyasar kasar cikin ruɗani, ganin cewa babu wanda ya san matsayar shugaban game da zaɓe mai zuwa.

Ko Buhari ya taka rawar gani a shekara biyu?


Image caption

Mahmud Jega manazarci ne kuma dan jarida a Najeriya

Shekara biyun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yana mulki ba su isa a yanke hukunci ba, idan ana son yin adalci, domin shugaban ya shiga fama da rashin lafiya tun wata biyar da ya gabata.

Shugaban ya yi kwana 49 a Landan, daga watan Janairu zuwa Maris, kuma bai yi wasu ayyuka masu yawa ba a watannin Maris zuwa Mayu, sannan ya koma Burtaniya a farkon wannan watan don ƙara neman lafiya. Babu wanda ya san ranar da zai dawo.

A ragowar wata 19 da Buhari ya yi mulki kuwa, gwamnatinsa ta ɓata lokaci wajen naɗa manyan jami’an da za su tafiyar da ayyukan gwamnati ne. Misali, an shafe tsawon wata uku kafin naɗa Sakataren Gwamnatin Tarayya da shugaban ma’aikatan ofishin shugaban ƙasa.

Buhari na shan addu’a a coci-coci da masallatai

Ba za mu manta da gwamnatin Buhari ba — Shi’a

Kuma sai a watan Nuwamban 2015 ne ya naɗa ministocinsa. Hakazalika, ya ɓata wasu watannin kafin ya fara sauya shugabannin ma’aikatun da ya gada daga gwamnatin Goodluck Jonathan. Zuwa yanzu, yawancin ma’aikatu ba su da kwamitocin gudanarwa. Idan aka duba batun ma’aikata, Shugaba Buhari mai tafiyar hawainiya ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rashin lafiyar Shugaba Buhari ta jawo tafiyar hawainiya a aiwatar da al’amuran gwamnati

Buhari ya samu yawancin nasarori a shekarar 2016. Mafi muhimmanci su ne yaƙi da ƙungiyar Boko Haram, da yaƙi da cin hanci da rashawa. Duk da ƙwato yawancin yankuna da garuruwan da ƙungiyar ta Boko Haram ta mamaye a ƙarshen mulkin tsohon Shugaba Jonathan, ƙungiyar na da sauran karfinta lokacin da Buhari ya karɓi mulki.

Zuwa ƙarshen shekarar 2016, an karya lagon ƙungiyar. Akwai dalilai masu dama da suka taimaki Buhari samun wannan nasarar.

Na farko shi ne, Buhari ya san illar ƙungiyar Boko Haram, kuma bai yi kuskuren da tsohon Shugaba Jonathan ya yi ba na cewa wasu ne suke son yi wa gwamnatinsa zagon-ƙasa.

Na biyu, Buhari ya dakatar da badaƙalar sayen kayan yaƙi, kuma ya samar da makaman yaƙi ga sojojin ƙasar.

Na uku, Buhari ya naɗa sabbin manyan hafsoshin sojin ƙasar. Shugaban sojojin ƙasa Laftanal-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya kawo sabbin dabarun yaƙi da suka yi tasiri kuma ya zama abin alfahari.

Air Marshal Sadik Abubakar, babban hafsan sojin sama na Najeriya, shi ma ya ɗauki matakan da suka durƙusar da ƙungiyar Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sabbin hafsoshin sojin da Buhari ya nada sun taimaka wajen yaki da Boko Haram

Akwai kuma umarnin da Buharin ya bai wa manyan hafsoshin sojin kasar na su koma Maiduguri domin su kasance kusa da fagen daga.

Da ƙarshe ya yi nasarar samun haɗin kan ƙasashen da ke maƙwabtaka da Najeriya kamar Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin. Waɗannan matakan sun taimaka wajen ƙwato dajin Sambisa a watan Disamba.

Yaƙi da cin hanci

Fage na biyu da Shugaba Buhari ya samu babbar nasara shi ne yaƙi da cin hanci da rashawa. Wannan yaƙin ya ƙara tabbatar da farin jininsa a sassa daban-daban na ƙasar.

A karon farko, Najeriya ta yi sa’ar shugaba mai gaskiya da rikon amana. Wannan kawai ya taimaka wajen tara biliyoyin dalolin Amurka a baitul-malin ƙasar domin babu yadda za a sace arziƙin ƙasa ba tare da sanin shugaban ƙasa ba.

A ƙarƙashin Buhari, hukumomin yaƙi da rashawa irinsu EFCC sun samu ƙarfin zartar da ayyukansu, abin da ya sa suka gano kuɗaɗe masu yawa da aka ɓoye.

Binciken da Buhari ya bayar da umarnin a yi, ya sa an gano biliyoyin dalolin da aka sace lokacin tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki. An gano cewa maimakon sayen makamai don yaƙar ƙungiyar Boko Haram, an karkatar da biliyoyin naira, waɗanda aka raba wa shugabannin jam’iyyar PDP domin yaƙin neman zaɓen Shugaba Jonathan a shekarar 2015, zaɓen da bai samu nasara ba.

Image caption

Kudaden da aka gano a gidan Andrew Yakubu

Wasu bincike-binciken kuma sun bayyana yadda tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke tare da muƙarrabanta suka wawashe kuɗaɗen man fetur na ƙasar. Ban da wannan, gwamnatin Buhari ta gano wasu hanyoyin da ake sace kuɗaɗe, kamar ƙarin da ake yi wa kasafin kuɗi.

Amma mafi ban mamaki ga ‘yan Nijeriya shi ne batun dalar Amurka miliyan 10 da hukumar EFCC ta gano, wadda tsohon shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, wato Andrew Yakubu ya ɓoye a unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna.

Akwai kuma maganar dalar Amurka miliyan 40 da shugaban hukumar tara bayanan sirri na ƙasa ya ɓoye a wani gida a Ikoyi.

Amma duk da waɗannan nasarori, wasu masana suna sukar yadda shugaba Buhari ke gudanar da yaƙi da cin hanci da rashawar. Suna cewa gyaran na buƙatar sabbin dabarun zamani ne, kafin a iya shawo kan lamarin.

Tattalin arziki ya yi ƙasa

Fannin da shugaba Buhari bai samu nasara sosai ba shi ne na haɓaka tattalin arziƙi. Koma-bayan tattalin arziƙin ya zo daidai lokacin da gwamnatin ta Buhari ta kama madafun iko.

Manyan batutuwa uku mafi muhimmanci su ne – faɗuwar farashin mai a kasuwar duniya, da gagarumar sata lokacin mulkin Jonathan, da dakatar da tayar da ƙayar baya a yankin Neja Delta, da kuma batun zagon ƙasa da ake yi wa masana’antun man fetur da hanyoyin samar da wutar lantarki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ayyukan masu tayar da kayar baya na yankin Naija Delta sun jawo tabarbarewar tattalin arziki

Shugaba Buhari da masu magana da yawunsa sun ɓata lokaci mai tsawo suna tura laifin halin da ƙasar ke ciki ga gwamnatin shugaba Jonathan, wanda ba laifi ba ne. Amma gwamnatin ta riƙa yin tafiyar hawainiya, kuma kamar babu wani tsarin da take bi wajen magance al’amarin.

A halin yanzu, tattalin arziƙin ya fara farfaɗowa, saboda ƙaruwar farashin mai da kuma dakatar da rikicin ‘yan Neja Delta.

Ina aka kwana kan alƙawurran da ya yi?

Ban da waɗannan fannonin, gwamnatin Buhari ta gaza samun nasarori da dama, musammam alkawurran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zabe. Game da samar da wutar lantarki, maimakon lamarin ya gyaru, sai ma ya kara taɓarɓarewa.

Buhari ya magance tsarin nan na sata ta hanyar biyan tallafin man fetur, shi ma sai da ya ƙara farashin litar mai daga Naira 97 zuwa Naira 145.

Alƙawuran tabbatar da jin dadin al’umma, kamar bai wa matasa 500,000 aikin koyarwa, da biyan talakawa Naira 30,000 a kowane wata da sama wa masu kananan masana’antu basuka masu saukin biya, duka ba su samu ba, ko kuma a ce ana tafiyar hawainiya wajen aiwatar da su.

Sai dai a iya cewa babban alƙawarin nan na ciyar da ɗalibai abinci a makarantun gwamnati sau ɗaya a yini da ba su madara duk an kasa fara su.

A wannan lokacin da muke duba irin rawar da gwamnatin Buhari ta taka cikin shekara biyu na farko, yawancin ‘yan Nijeriya suna fatan shugaban ya samu cikakkiyar lafiya, domin ya dawo ya ci gaba da sauran aikin gyaran ƙasa na shekara biyun da suka rage.

Image caption

Da yawan ‘yan Najeriya na addu’ar Buhari ya samu lafiya ya karasa shekara biyunsa

Za mu daina dogaro ga Amurka da Burtaniya — Merkel


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mrs Merkel ta ce kasashen Turai ba za su cigaba da dogaro da Amurka da Burtaniya ba

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta yi gargadi ƙasashen Turai a kan kada su ci gaba da dogara kacokam a kan Amurka da Burtaniya, bayan zaɓen Trump da kuma fitar Burtaniya daga Tarayyar Turai.

Yayin da take jawabi a wani gangamin yaƙin neman zaɓe, Mrs Merkel ta ce wajibe ne ƙasashen Turai su fuskanci yadda za su gina makomarsu da kashin kansu– amma za su ci gaba da ƙawance da Amurka da Burtaniya.

Ta ce ta so ƙulla ƙawance mai ƙarfi da ƙasashen biyu har ma da Rasha, amma kuma dole ƙasashen Turai su tashi tsaye da kansu game da makomarsu.

Kalaman nata na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi amincewa da shiga yarjejeniyar rage ɗumamar yanayi a taron ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki G7.

“Yanzu lokaci ya yi da za mu daina dogaro kacokam a kan wasu ƙasashe. Na fahimci wani abu a cikin ‘yan kwanakin nan,” in ji Mrs Merkel.

A ranar Asabar Mrs Merkel ta bayyana tattaunawa a kan sauyin yanayi a taron G7 ɗin a matsayin maras alkibla.

Stephan Mayer ɗan majalisar dokokin Jamus ne, kuma mai magana da yawun harkokin jami’iyar shugabar gwamnatin Jamus din, ya ce ba sabon abu ba ne cewa Donald Trump mutum ne maras sauƙin kai.

“A bayyane take cewa yana neman ya kai ƙasashen Turai bango. Yana yi mana shiga hanci da ƙudundune” a cewar Mayer.

Shugabannin ƙasashen Burtaniya, da Canada, da Faransa, da Jamus, da Italia da kuma Japan sun nuna goyan bayansu kan yarjejeniyar ɗumamar yanayi ta Paris- amma Shugaba Trump ya ƙi ƙara shigar da Amurka cikin yarjejeniyar.

Mr Trump dai ya ce zai yanke shawara kan batun a cikin mako mai zuwa.

A baya dai ya lashi takobin yin watsi da batun yarjejeniyar Paris ɗin, ya kuma taɓa nuna shakku kan batun ɗumamar yanayin.

Mrs Merkel na kan yaƙin neman zaɓe ne gabanin zaɓukan da za a gudanar a cikin watan Satumba.

Kuri’un jin ra’yoyin jama’a sun nuna alamun cewa za ta sake samu galaba a karo na hudu a matsayinta da shugabar gwamnatin Jamus.

Korea ta Arewa ta harba makami mai linzami na 9 a bana


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A karo na uku cikin makonni uku Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami da ke cin gajeren zango cikin tekun Japan, karo na uku a cikin mako uku.

Matakin dai ya zafafa zaman ɗar-ɗar ɗin da ake fama da shi a yankin tekun Koriya, inda ta bijirewa yunƙurin ƙasashen duniya na yi wa shirin nukiliyarta shamaki.

Gwajin makamin, wanda shi ne tara a wannan shekara ya janyo Allah wadai cikin gaggawa.

Fira ministan Japan Shinzo Abe ya ce taron manyan ƙasashen da suka fi bunƙasar tattalin arziƙi a duniya G7 ya amince da bai wa batun Koriya ta Arewa ƙololuwar fifiko.

Ya ce Japan za ta yi aiki da sauran ƙasashe kamar Amurka don ɗaukar matakan da za su hana hukumomin birnin Pyongyang ci gaba da takalar faɗa.

Rundunar sojin Amurka da ke yankin Pacific ta ce an harba makami mai linzamin ne daga birnin Wonsan na Korea ta Arewar, kuma ya yi tafiyar minti shida a sararin samaniya kafin ya sauka.

Babban sakataren hukumar gudanarwar ƙasar Japan Yoshihide Suga ya shaida wa manema labarai cewa makamin ya sauka a wani yanki da ke tsakanin tsibirin birnin Sado da kuma tsibirin Oki na kasar Japan din.

Me 'yan Nigeria ke cewa kan alƙawurran Buhari?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawura da dama lokacin yakin neman zabe

Yayin da Nijeriya ke cika shekara biyu a ranar Asabar da hawan Muhammadu Buhari karagar mulki, wasu ‘yan ƙasar tuni sun fara yanke kauna, ganin ya cinye rabin wa’adin mulkinsa ba tare da cika wasu manyan alkawurran da ya yi ba.

Da dama dai na zargin cewa wasu mutane ƙalilan ne suka yi baba-kere a gwamnatin Muhammadu Buhari, yayin da wasu ke cewa ko a iya nan shugaban ya tsaya, ba shakka ya taka rawar-gani.

Batun taɓarɓarewar tsaro da karayar tattalin arziki da uwa-uba cin hanci da rashawa na daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya lokacin da Buhari ya karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Shugaban dai tun lokacin yaƙin neman zabe, ya faɗa wa ‘yan Nijeriya cewa ya ji ya gani, kuma zai iya, har ma ya nanata irin waɗannan alƙawarrun a yayin rantsuwar kama aiki, abin da ya ƙarfafa gwiwoyiin `yan ƙasar da dama tare da sanya ɗumbin fata.

Boko Haram

Rikicin boko-haram za a iya cewa shi ne gaba-gaba a tsakanin matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya, wanda ke haddasa asarar dubban rayukan jama`a, kuma Shugaba Buharin ya ɗauki matakin yankan shakku kan aniyarsa ta yaƙi da ‘yan tada-ƙayar-baya.

Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin mai da hankali kan yaƙi da Boko Haram, inda ya mayar da shalkwatar rundunar sojin ƙasar zuwa birnin Maiduguri, inda mayaƙan suka fi karfi.

Wannan mataki da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka na yin fito-na-fito da Boko Haram, kamar yadda mahukunta da ɗumbin `yan Najeriya ke cewa ya taimaka wajen karya-lagon ‘yan ƙungiyar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dakile rikicin Boko Haram na cikin manyan abubuwan da gwamnatin shugaba Buhari ta yi alkawari

Dakarun sojin Nijeriya sun sake kwato yankunan ƙasar waɗanda ‘yan tada-ƙayar-bayan a shiyyar arewa maso gabas suka mamaye a baya.

Sai kuma nasarar da gwamnatin ta cimma wajen ceto wasu daga cikin `yan matan sakandaren Chibok, duk da yake wasu `yan kasar na ci gaba da jayayya kan salon musayarsu da wasu kwamandojin Boko Haram.

Cin hanci da rashawa

Wani abin da ake yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari a kai shi ne rawar-ganin da take takawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Wasu dai na ganin an samu nasara, don kuwa a karon farko an gurfanar da wasu manyan jami`an gwamnati da alkalai har ma da shugabannin siyasa da ake zargin sun tafka almundahana da dukiyar ƙasa a gaban kotu.

Amma wasu na zargin cewa yaƙin ya fi karkata a kan `yan adawa ko waɗanda ba sa ɗasawa da sabuwar gwamnati.

Sai dai shugaba Buhari ya ce bai kullaci kowa ba, don haka ba shi da niyyar ramuwar gayya.

Shugaban Nijeriyar ya yi yunkurin sauya tsarin kyautata rayuwar al`ummar yankin Niger-delta mai arzikin mai.

Sai dai wannan albishir na inganta rayuwar al`ummar Niger-Delta bai ratsa zukatan masu ta-da-kayar-baya ba, idan aka yi la’akari da irin luguden bama-baman da suka yi ta yi a kan bututan mai da iskar gas da ke yankin.

Hakan dai ya haddasa asara mai yawa tare da rage yawan man da Nijeriya ke fitarwa, ga kuma jefa al`ummar ƙasar a cikin matsalar ƙaranci ko rashin wutar lantarki.

Ko da yake, za a iya cewa harin ya lafa a ɗan tsakanin nan, bayan wani rangadi da muƙaddashin shugaban ƙasar Yemi Osinbajo ya kai yankin.

Samar da ayyuka musamman ga matasa

Shirin bunkasa noma da Npower da wasu makamantansu na cikin tsare-tsaren da gwamnatin Muhammadu Buhari ta bijiro da su don samar da hanyoyin dogaro da kai a tsakanin matasa.

Za a iya cewa matasa da dama sun samu tallafi, amma har yanzu akwai wasu miliyoyi da ba su da aikin yi a Nijeriya.

Yayin da gwamnatin shugaba Buhari ke lissafa irin nasarorin da ta samu wajen sauke alƙawuran ta yi wa `yan Nijeriya, wasu kuma na ganin cewa akwai wasu manyan alƙawurran da shugaba Buhari ya yi, waɗanda har yanzu ba su gani a kasa ba.

Ko da yake, mahukunta na zargin cewa harin da masu fafutukar `yanta yankin Niger-Delta ke kai wa na shafar ƙoƙarin inganta hasken lantarki.

Har ila yau, akwai masu zargin cewa shugaban ƙasar ya mai da wani ɓangare saniyar-ware ta fuskar naɗin muƙaman gwamnati, alhali yana iƙirarin cewa shi na kowa ne:

Sarkin kabilar Ibo mazauna Kano Eze Dr Boniface ya ce Buhari mutumin kirki ne shi ya sa mutane suke binsa, amma kuma inda ya gaza shi ne rashin tafiya da ‘yan kabilar Ibo a gwamnatinsa.

“Laifinsa, ina gani bayan ya ci zaɓe sai ya bar ‘yan kabilar Ibo a baya, bai ba su mukamai ba.”

Sai dai shugaban Nijeriyar ya yi watsi da wannan zargin, inda ya ce gwamnatinsa ba ta nuna bambanci.

Yanzu dai shugaba Buhari ya cika shekara biyu a kan karagar mulki, wato ya ci rabin wa`adin mulkinsa, kuma `yan Magana kan ce juma`ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta.

Ko me `yan Najeriya za su ce game da tafiyar?

Wannan ya ce: “Mun zaɓi Buhari don buƙatar zaman lafiya, gaskiya ina nan a kan bakata na son mulkin Buhari.”

Shi ma wani cewa yake yi: “Buhari! Ni, ina goyon bayansa ɗari bisa ɗari, i(da)n Allah ya yarda zan sake zaɓensa”

“Gaskiya na zaɓi Buhari, amma shekara biyu ban ga wasu abubuwan ku zo ku gani ba, gaskiya yanzu na dawo daga rakiyarsa,” in ji wani ɗan Nijeriyar.

Shi kuwa wannan: “Gaskiya ni ma masoyin Buhari ne amma a da, sai dai yanzu ina ganin mun samu canji ne irin na rigar mahaukaci, ya cire ta jikinsa ya ɗauko ta bola ya saka.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu ‘yan Nijeriyar sun yanke kauna kan yadda shugaba Buhari ya cinye rabin wa’adin mulkinsa ba tare da sauke alkawuran da ya yi musu ba

Mahukunta dai na cewa shekara biyu ba ta kai mizanin da za a yi kididdige tasirin mulki da ita ba, a ƙasa mai tarin matsaloli irin Nijeriya, amma masu sukar gwamnati na cewa gwamnati Muhammadu Buhari ta ƙare gudu saura zamiya, lokaci ya ƙure, don kuwa a cewarsu shekara biyun da ta rage, ta ruguntsumin siyasar babban zaɓe ce.

Waɗanne Amurkawa ne suka mutu don kare musulma?


Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/AURORA DACHEN

Image caption

Mahaifiyar Taliesin Myrddin Namkai-Meche, da ya mutu a lokacin hari ta bayyana ɗanta a matsayin “tauraro mai walwali.”

An tara gudunmawar sama da dala dubu 600 ga iyalan Amurkawan da aka far wa lokacin da ƙoƙarin kare wata matashiya musulma da saurayinta a cikin jirgin ƙasa.

An kashe biyu daga cikinsu, Taliesin Myrddin Namkai-Meche da Ricky John Best, yayin da aka ji wa na ukun Micah David-Cole Fletcher mummunan rauni a yankin Portland cikin jihar Oregon ranar Juma’a.

Amurkawan sun shiga tsakani lokacin wani mutum ya far wa matasan — wadda ɗayansu ke sanye da hijabi — da kalaman cin mutunci.

Daga bisani an kama mutumin da ake zargi da far wa mutanen, Jeremy Joseph Christian.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan sanda sun fitar da hoton Jeremy Joseph Christian bayan kai farmakin

Nan gaba a ranar Talata ce mutumin ɗan shekara 35 zai bayyana a gaban kotu, don fuskantar tuhuma guda biyu kan mummunan kisan kai da yunƙurin aikata kisan kai da razanarwa da kuma aikata laifin mallakar makamin da aka iyakance amfani da shi.

Hukumar tsaro ta FBI ta ce har yanzu ba ta tabbatar da ko mutumin wanda ake zargin ya furta cewa “a kashe duk musulmai ba” lokacin harin, zai fuskanci tuhume-tuhume kan laifukan nuna ƙyama.

A lokaci guda kuma, Mr Fletcher yana ci gaba da samun sauƙi bayan yankan da aka ji masa a wuya.

Ya wallafa hotonsa daga asibitin da yake kwance tare da wata rubutacciyar waƙa da maryacen ranar Asabar. Wani ɗangon waƙar na cewa: “Na tsokane idon ƙyama kuma na rayu.”

An jinjinawa mutanen su uku a matsayin “gwaraza” a yankunansu, tun ma ba Destinee Mangum – matashiya musulma mai shekara 16 da tafiya tare da saurayinta ɗan shekara 17 ba lokacin da aka kai musu hari.

Ta faɗa wa kafar yaɗa labaran KPTV cewa: “Zan so na miƙa godiya ga mutanen da suka sadaukar da rayukansu saboda ni, don kuwa ba su ma san ni ba amma suka mutu saboda ni da saurayina da kuma irin shigarmu.”

Kusan mutum dubu ɗaya ne suka taru don tunawa da Mista Namkai-Meche, ɗan shekara 23, wanda ya kammala kwaleji kwanan nana da tsohon soja mai shekara 53 Mista Best, a ranar Asabar.

An tuhumi wadda ta kulle 'ya'yanta a but ɗin mota


Hakkin mallakar hoto
WEBER COUNTY SHERIFF OFFICE

Image caption

Uwar yaran, Tori Castillo ka iya fuskantar hukuncin ɗauri a gidan yari ko kuma tara idan aka same ta da laifi

An kama wata mata a Amurka bayan an zarge ta da kulle ‘ya’yanta, ɗaya mai shekara biyu da mai shekara biyar a cikin but ɗin mota ta tafi kanti sayayya.

Kafofin yaɗa labarai a Amurka sun ce Tori Castillo ‘yar shekara 39, na fuskantar tuhuma kan tozarta ‘ya’yan cikinta kuma tuni aka damƙa yaran a hannun mahaifinsu.

Rahotanni sun ce ‘yan kallo ne da suka taru suna taraddadi suka yi wa babban yaron mai shekara biyar kwatancen yadda zai buɗe gidan ajiye kayan daga ciki.

Masu wucewa sun lura da yadda motar ke jijjiga, ga kuma hayaniya tana fitowa daga ciki, inda aka ajiye ta a wajen wani kantin sayayya.

Al’amarin ya faru ne ranar Alhamis a yankin Riverdale cikin jihar Utah.

Ba a san ko tsawon sa’a nawa yaran suka shafe a cikin gidan kayan ba.

Jami’in ‘yan sandan yankin, Casey Warren ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta KTVX: “Ba daidai ba ne a kulle yaro a cikin mota, ballantana ma gidan ajiye kayan mota.

“Gaskiya matsaloli da dama suna iya aukuwa.”

Ya yaba wa mutane “masu kyakkyawar niyya” da suka taimaka wajen fitar da yaran.

A ƙarƙashin dokar jihar Utah, barin yaro ɗan ƙasa da shekara tara a cikin mota ba tare da kulawar wani ba, laifi ne da ake iya hukunta mutum ta hanyar tara ko ɗauri.

An kafa dokar ce a shekara ta 2011 bayan ci gaba da samun mutuwar yaran da ake bari cikin zafi a motoci.

IfeanyiUbah ta ci Kano Pillars 2-0


Hakkin mallakar hoto
NPFL Twitter

Image caption

IfeanyiUbah ta yi wasa takwas ba tare da an doke ta a gasar Premier ta Nigeria ba

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara da ci 2-0 a gasar Premier Nigeria da ta ziyarci IfeanyiUbah a ranar Lahadi.

Mai masaukin bakin ta ci kwallayen biyu ne ta hannun Godwin Obaje, kuma shi ne aka zaba wanda yafi taka rawar gani a karawar.

Bayan da aka yi wasannin mako na 21, IfeanyiUbah ta buga karawa takwas a jere ba tare da an doke ta ba.

Ga sakamakon wasannin mako na 21 da aka buga ranar Lahadi:

 • Plateau Utd 1-0 Remo Stars
 • Gombe 1-0 Katsina
 • El-Kanemi 2-1 Rivers
 • Akwa Utd 3-0 ABS
 • Nasarawa 2-0 Wikki
 • Lobi 3-0 3SC
 • Tornadoes 3-0
 • Sunshine 1-0 Enyimba
 • Abia 4-0 Enugu Rangers

Na ji takaicin rashin fara FA da ni – Fabregas


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fabregas ya koma Chelsea daga Barcelona a shekarar 2014

Cesc Fabregas ya ce ya ji takaicin rashin fara gasar cin kofin kalubale wanda Chelsea ba ta fara karawar da shi ba a ranar Asabar.

Arsenal ce ta doke Chelsea da ci 2-1, wanda hakan ya sa ta lashe kofi na 13 jumulla kuma na bakwai da Arsene Wenger ya dauka a tarihi.

Fabregas wanda ya zauna a benci a karawar ya shiga filin wasa bayan da aka dawo daga hutu a Wembley.

Dan kwallon ya buga wa Chelsea wasa 15 a kakar bana, hudu daga ciki a wasannin Premier Shida na karshe da kungiyar ta ci kofin bana.

Fabregas ya ce ‘abin kunya ne da ba a fara karawar da shi ba domin yana kan ganiyarsa’.

Dan wasan wanda ya ci kofin FA da Arsenal a 2005, ya koma Chelsea daga Barcelona a shekarar 2014.

Shin ko Zidane ya yi bajinta a Real Madrid?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid za ta kara da Juventus a wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai

Masu sharhin wasannin tamaula na hangen cewar Zinedine Zidane yana yin bajinta a matsayinsa na koci, bayan wadda ya yi a matakin dan kwallon Real Madrid.

Zinedine Zidane ya zama daya daga cikin masu horar da Real Madrid da ya lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai a kungiyar.

Koci hudu ne suka yi bajintar lashe kofin gasar kasar Spaniya da ta Zakarun Turai kafin Zinade dan kasar Faransa.

Villalonga ne ya kafa tarihin haka a shekarar 1956, inda ya ci kofin La liga biyu da na zakarun Turai biyu.

Shekara biyu tsakanin Carniglia ya lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai a kakar wasa daya, jumulla ya ci na Zakarun Turai biyu da na Spaniya kafin ya yi ritaya.

Na uku shi ne Miguel Muñoz wanda ya lashe kofin Zakarun Turai biyu da na La Liga tara, sai Del Bosque wanda ya ci kofin La Liga biyu da na Zakarun Turai biyu.

Haka kuma Zidane ya zama mai horar da Madrid na shida da ya ci kofin na kasar Spaniya a matakin dan wasa da kuma koci.

Sauran da suka yi irin wannan bajintar sun hada da Miguel Munoz da Molowny da Valdano da Del Bosque da kuma Schuster.

Messi da Iniesta sun ci kofi 30 a Barcelona


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona ta dauki Copa del Rey sau uku a jere

Lionel Messi da Andres Iniesta sun lashe kofi na 30 kowannensu a Barcelona, bayan da suka lashe Copa del Rey a ranar Asabar.

Barcelona ta lashe Copa del Rey na bana kuma na uku a jere, bayan da ta doke Deportivo Alaves da ci 3-1, wanda hakan ya sa ta dauke shi sau 29 jumulla.

Messi da Iniesta sun dauki kofin La Liga takwas da Spanish Super Cup bakwai da kofin Zakarun Turai hudu da Copa del Rey biyar da European Super Cup uku da kofin zakarun nahiyoyin duniya uku a Barca.

Jumulla ‘yan wasa hudu ne da suka kara a fafatawar karshen a ranar Asabar suka dauki Copa del Rey sau biyar-biyar da suka hada da Lionel Messi da Andre Iniesta da Gerard Pique da kuma Sergio Busquets.

‘Yan wasan hudu a Barcelona sun dauki kofin a shekarar 2009 da 2012 da 2015 da 2016 da kuma 2017.

Wasu sun yi liyafa da naman shanu a Indiya


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mabiya addinin Hindu a India suna girmama shanu

Masu adawa da gwamnatin India a jihar Kerala, sun gudanar da liyafa da naman shanu a cikin unguwanni, sannan suka yi maci dauke da kan bauna, domin nuna rashin jin dadinsu da karin matakai na rage yawan naman ci a kasar.

A karkashin sababbin dokokin, shanu, wadanda mabiya addinin Hindu ke girmamawa sosai, an hana sayar da su a kasuwa domin yankasu.

Haka ma suma baunaye da rakuma, an hana sayar da su a kasuwa domin yanka, duk da cewa su din ba dabbobi ba ne da ake girmamawa.

Shugabanni a jihohin da a ka fi mu’amala da nama, sun ce wannan wata babbar barazana ce ga sana’o’in makiyaya, da masu sana’ar sayar da nama, waddanda akasarinsu Musulmai ne marasa rinjaye.

Amurka na duba yiwuwar hana shiga jirage da laptop


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tuni dama Amurkan ta wana fasinjoji daga wasu kasashe shiga jirgi da kwamfutocin laptop

Hukumomi a Amurka suna duba yiwuwar hana mutane shiga da kwamfutocin laptop cikin dukkan jiragen sama masu zirga-zirga tsakanin kasa da kasa, saboda barazanar hare-haren ta’addanci dake kasar ke fuskanta.

Shugaban hukumar tabbatar da tsaron cikin gida ta Amurka, John Kelly, ya ce akwai tabbatacciyar barazanar hare-haren ta’addanci a bangaren jiragen sama na kasar, a don haka, a kwai yiwuwar zai aiwatar da matakin hanin.

Ya ce ‘yan ta’adda suna da burin ganin sun kakkabo jirgin sama, musanman ma na Amurka, yayin da yake cikin tafiya a sama.

Dama dai Amurkan ta hana fasinjoji dake tasowa daga wasu kasashe goma, akasarinsu daga Gabas ta Tsakiya, shiga jiragen sama da kwamfutocin na laptop.

Za a rika narkar da gawa a maimakon binnewa


Image caption

An fara amfani da injin narkar da gawa shekaru biyar da suka gabata

A shekaru da dama mutane na amfani da hanyoyi biyu wajen jaza’izar mamatansu, wato binnewa da kuma konawa.

To sai dai wannan al’ada na nema zamewa tarihi a wasu sassa na kasar Amurka da Canada, domin kuwa sun gano wata hanya da za a rika narkar da gawar ta amfani da wani sinadari.

Kuma ana dab da fara wannan sabuwar al’ada a Burtaniya.

Sunan sinadarin “Alkaline Hydrolysis”, amma ana cinikayyarsa da sunan “green cremation”.

Masu wannan sabuwar fasaha sun ce, idan za mu binne gawa mukan bukaci abubuwa masu tarin yawa, misali katako wajen yin akwatin gawa, da likkafanin da za a sanya wa gawar, da kuma duwatsu ko itatuwa da za a rufe kabarin da su.

A kasar Amurka a kan yi wa kaburbura siminti, ko kuma a sanya akwatin cikin wani wuri na musamman wanda gawar ba za ta lalace ba.

Har ila yau, shi ma kona gawa na da nasa matsalar in ji sabuwar fasahar, domin kuwa yakan jawo dumamar yanayi, domin kuwa a yayin kona gawa daya kawai, injin kona gawar kan zafafa gidan ko makabartar har na tsawon mako daya, koda kuwa a yankin Minnesota mai tsananin sanyi ne.

Bradshaw daya ne daga cikin gidajen jana’iza 14 a duniya dake amfani da wannan sabuwar fasaha na “narkar da gawa”. Kamar yadda suka bayyana sinadarin “Alkaline Hydrolysis” da ake amfani da shi, ba kawo wata matsala ga muhalli.

Suna amfani da farashi na bai daya, wato da manya da yara duk kudin daya ne, kuma sun ce wannan sabuwar fasaha na taimakawa wajen rage dumamar yanayi.

Ga abokan huldarsu da suka zabi da kar a binnesu- sukan samun rangwamen rabin kashi 80 cikin 100 na sinadarin.

To sai dai ba dumamar yanayi ne kadai dalilinsu, na bullo da wannan sabuwar hanyar ba.

Injin narkar da gawar wanda yakan lamushe kudi kimanain dala 750,000, za a girke shi ne a cikin cibiyar, kuma an fara aiki da shi shekaru biyar da suka gabata.

Jason Bradshaw, shi ne manajan cibiyar ya kuma ce, “mun so mu yi aikin cikin farashi mai sauki.

Muna jin dadin cewa mu ne na farko a wannan fannin – kuma mu ne na farko a kasarmu muna bukatar kara bunkasa wannan kasuwanci namu”.

Jason, wanda ke da digiri a fannonin Ilimin halittu (Biology), da ilimin sinadarai (Chemistry), ya bayyana cewa injin na auna nayin kowacce gawa sanna ya lissafa yawan ruwa da sinarin da za a yi amfani da su domin narkar da gawar.

An yi kiyasin cewa kusan mutum 150,000 ne ke mutuwa a kowacce rana a duniya, kuma adadin na karuwa ne kamar yadda adadin mutanen duniya ke karuwa.

A wasu kasashe, ana karancin filin makabartu. Alal misali a Burtaniya an yi kiyasin cewa rabin makabartun kasar za su cika nan da shekaru 20 masu zuwa.

A wasu sassa a birini Landan, hukumomi sun daina shirya bukukuwan jana’iza, kuma birnin ya fara amfani da tsofaffin kaburbura, ta yadda ake kara nitsar da tsohuwar gawa cikin kasa, a kuma sanya sabuwa a kai.

Masu rajin kafa wannan sabuwar fasahar, sun ce Amurka tana amfani da akwatin gawa da nauyinsa ya kai Tan miliyan 1.1, da kuma karfen da ya kai Tan 14,000 a kowace shekara.

Ga masu kona gawa, an yi kiyasin cewa kona gawa daya kacal na haifar da iska mai guba da yawanta ya kai Kilogram 320.

Don haka sun ce idan ba a dauki matakai ba, guba mai hatsari za ta yi ta yaduwa tsakanin al’umma, wanda kuma zai haifar da yawan gurbacewar muhalli.

Ɗan wasan Man United Paul Pogba ya tafi Umarah


Hakkin mallakar hoto
Marwan Ahmed

Image caption

Paul Pogba ya isa Saudiyya don fara aikin Umarah

Dan wasan kulob din Manchester United Paul Pogba ya tafi kasar Saudiyya don fara aikin Umarah a watan Ramadan, ‘yan kwanaki kadan bayan kulob dinsa ya lashe kofin Gasar Europa.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram a ranar Asabar, Pogba ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Makkah domin godewa Allah kan nasarar da suka samu a kakar bana.

Hakazalika, a ranar Lahadi ya wallafa wani bidiyo a shafin wanda yake nuna shi a tsaye a gaban Harami. Kuma sabanin yadda aka saba ganinsa a filin wasa, Pogba ya sauya irin salon askinsa.

Dan wasan wanda da ma Musulmi, ya ce yana yi wa Musulmi barka da azumi.

Rahotannin kafafen yada labarai sun ce Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, yana yin ibadarsa ta addinin Musulunci.

Pogba ya koma United a bara daga Juventus a matsayin dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya.

Hakkin mallakar hoto
Instagram

Image caption

Dan wasan ya wallafa bidiyonsa a shafin Instagram gabanin ya kama hanya zuwa filin jirgin saman garin Manchester ranar Asabar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pobga a cikin jirgi a kan hanyarsu ta koma gida bayan lashe Kofin Europa a ranar Laraba

Ko ya dace a yi gwajin cutar sikila kafin aure?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Cutar na janyo daukewar numfashi, da gajiya da jinkiri wajen girman jiki

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya.

Mun yi rashin kwararru da dama domin wannan larura. Na rasa wani abokina na kut-da-kut mai suna Nura, wanda muka lakaba ma sunan “88 soja” sakamakon wannan cutar. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen wayar da kan jama’a game da illar ciwon sikila. Muna iya dakatar da wannan ciwon. Muna iya hana yaduwarsa.

Kawata Samira Sanusi ta yi fama da wannan ciwon na tsawon fiye da kashi biyu cikin uku na rayuwarta. An yi mata tiyata fiye da sau 10, kuma an sha kwantar da ita a asibiti sabili da matsalolin da sukan biyo bayan jinyar da ciwon na sikila ke haifarwa.

A duk lokacin da na ga wani mai fama da cutar sikila yana kuka saboda radadin cutar, sai na ce dama iyayensa ba su yi son kai ba. Ka ga, abu ne mai sauki kafin mu yi aure mu daure mu yi gwaji daga nan sai mu yanke shawara a kan ko ya kamata mu mu yi auren ko a’a.

Ana gadon cutar sikila ne daga iyaye masu dauke da wasu kwayoyin halitta na jini, wato haemoglobin, masu kamar lauje. An fi samun cutar a tsakanin Larabawa da ‘yan asalin nahiyar Afirka.

Kwayoyin halittun jinin na sauyawa (su koma siffar lauje), wanda yake jawo raunata kwayoyin halittar, wanda yakan zama hanyar kamuwa da ciwon amosanin jinin.

Amosanin jinin na janyo daukewar numfashi, da gajiya da jinkiri wajen girman jiki. Yana kuma sa idanu da fatar jiki su sauya zuwa launin ruwan kwai. Duk wadannan alamu ne na amosanin jini.

Ana kamuwa da cutar amosanin jini ne idan aka gaji nau’in wasu kwayoyin halitta (SS) daga iyaye. Idan mutum ya gaji kwayar halittar amosanin jini daga daya daga cikin iyayensa, kana ya gaji kwayar halittar da ba ta da amosanin jini daga daya bangaren, zai kasance mai halittar AS.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masana na jaddada bukatar ma’aurata su rinka yin gwaji kafin a yi aure

Amma hanya mafi kyau wajen dakatar da yaduwar wannan ciwon shi ne idan muka rage auratayya a tsakanin nau’in AS/AS, da AS/SS da SS/SS. Hanyar tabbatar da wannan ita ce ta gwajin jinin masu niyyar yin aure.

Wannan kira ne ga masu niyyar yin aure da su gwada irin ‘kwayoyin halittar su, watau genotype, kafin su yi aure.

Kuma kira ne ga iyaye da shugabannin addini da su tabbata an shigar da gwaje-gwajen kafin kowanne daurin aure ya gudana. Kada mu ci gaba da raunata rayuwar ‘ya’yanmu da jikokinmu. Jahilci ba dalili ba ne.

Komai yawan soyayyar da kake yi wa masoyiyarka, abin da ya fi kyau shi ne kuje a gwada ku kafin ku yi aure, domin kada soyayyarku ta zama kiyayya. Ka ga kun ceci ‘ya’yan da za ku haifa daga rayuwa dake cike da wahala.

Daya daga cikin bakin da suka tattauna a kan wannan batu a ADikon Zamani na rediyo, Alhaji Umar Farouk, ya ce, “Rabuwa da budurwar da na so na aura yana daga cikin muhimman shawarwarin da na taba yankewa a rayuwata”.

Yau shi da tsohuwar budurwar tasa sun sami ‘ya’ya masu ingantacciyar lafiya bayan da suka auri wadanda suka fi dacewa da su. Lallai akwai darasin sadaukar da kai a cikin wannan labarin.

A je ayi gwajin amosanin jini a yau!

Ko Buhari ya gaza wajen farfaɗo da harkar ilimi a Nigeria?


Image caption

Dokta Aliyu Tilde manazarci ne kan bangarori daban-daban a Najeriya

Dokta Aliyu Tilde wani manazarci a Najeriya, ya yi duba kan ayyukan gwamnatin tarayyar Najeriya kan ilimi a shekaru biyu da ta gabata, karkashin mulkin Buhari. Shin akwai abin da ya sauya?

An jima ana kokawa kan taɓarɓarewar harkar ilimin zamani a Najeriya. Wannan ɓangare ne da ke bukatar gyara a fannoni da yawa. Misali, dukkan azuzuwa daga firamare har zuwa jami’o’i a cushe suke da ɗalibai.

A makarantun firamare a kan samu sama da yara 50 cikin aji daya, lokacin da a jami’o’i ta kan kama har sama da dalibai 500 ke ɗaukar darasi wajen malami guda cikin ɗakin karatu da ya cika ya batse har waje.

Akwai ƙarantar ƙwararrun malamai a kowane mataki na ilimi, da rashin kayan aiki a azuzuwa da ɗakunan bincike, kamar yadda ake da ƙarancin sabbin litattafai da mujallolin ilimi a ɗakunan karatu. Ga kuma satar jarrabawa da ya zama ruwan dare a kowane mataki.

A ƙarshe, akwai ƙarancin kuɗaɗen kashewa kan ilimi a kasafin kuɗin ƙasar inda hatta Gwamnatin Tarayya sau da yawa ke kashe kasa da kashi 6 cikin 100 na kasafin kuɗinta a kan ilimi. Wannan shi ya sa jami’ar Najeriya guda ɗaya tak ce ta samu shiga cikin jerin jami’o’i dubu mafi inganci a duniya.

Don haka gyara a sha’anin ilimi na daga cikin abin da ‘yan Najeriya musamman iyaye da ɗalibai da malaman makarantun zamani suka sa rai sabuwar gwamnatin APC za ta duƙufa a kansa da zarar ta hau kan mulki a 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alkawura da dama lokacin yakin neman zabensa

Ita ma jam’iyyar APC ɗin, ta ɗau wannan ƙudirin inda ta yi wa masu zaɓe alƙawurra a ƙalla 30 a kan gyaran ilimi, adadi mafi yawa da ta yi a fanni guda cikin alƙawurra fiye da 200 da ta yi a lokacin.

Yau shekara biyu ke nan da jam’iyyar APC din ta hau kan mulki a Najeriya. ‘Yan ƙasa za su so su san: Shin, wanne sauyi aka fara samu a fannin ilimi kuma alƙawura nawa jam’iyyar ta cika cikin tarin wadanda ta ɗauka lokacin kamfen ɗinta?

Ga dukkan alamu, abin da kamar wuya. Don har yanzu rahotanni na nuna cewa matsalolin da suka addabi sashin ilimin, wanda muka zayyana kaɗan daga cikinsu a baya suna nan daram, ba wanda ya gusa.

Ba abin da zai nuna wannan fiye da cewa ba a samu wani gagarumin sauyi ba a kason da ake bai wa ilimi a kasafin kuɗin ƙasar a matakin tarayya da jihohi bai daya.

A kasafin shekarar 2016, kashi 6.1 cikin 100 ne kawai Gwamnatin Tarayya ta ware wa sashin ilimi. In aka haɗa da wanda jihohi suka ware, ƙasar ta ware wa ilimi kashi 8% ne na kuɗaɗen kashewar gwamnatocinta. A hakan ma, kashe 43.7 cikin 100 zai je ne wajen biyan malamai.

Wasu ƙungiyoyi uku masu rajin kare dimokraɗiyya da ke bibiyar alƙawurran da jam’iyyar APC ta wa ‘yan Najeriya sun kasa faɗin ci gaban da aka samu a kan alƙawurra guda 30 ɗin da jam’iyyar ta yi.

Ci gaban da aka samu

Amma duk da haka akwai abubuwa na gyara da za a ce gwamnatin ta yi. Waɗannan sun haɗa da soke jami’o’in ilimin tarbiyya – wato Universities of Education – da tsohuwar gwamnati ka kafa; da ƙoƙarin daidaita kalandar karatu ta jami’o’i; da shawo kan malaman kar su je yajin aiki; da soke jarrabawar kafi-JAMB (Post UME) da jami’o’i ke yi lokacin ɗaukar dalibai ; da soke darasin addini – wato IRK da CRK – a tsarin koyawarwan ƙasar, wanda aka maye shi da ilimin ɗa’a; da daidaita kuɗaɗen da iyaye za su biya wa ‘ya’yansu a Kwalejojin Gamayya na ƙasar.

Haka kuma ƙasar ta sa hannu a yarjeniyoyin ilimi da ƙasashe kamar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Pakistan da Falasɗinu da Koriya ta Kudu da Rasha da kuma Aljeriya.

A ƙarƙashin waɗannan yarjeniyoyi, ana sa ran fannin ilimi a ƙasar zai amfana da samun taimako ta fannin kimiyya da fasaha da samun guraben karatu kamar ɗalibai 78 da aka tura ƙasashen Rasha da Aljeriya bara.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu sharhi na ganin da sauran rina a kaba wajen inganta harkar ilimi a Najeriya

Ci-baya

A wani ɓangaren kuma, za a iya cewa an samu ci baya a fannin ilimi a ƙarƙashin wannan gwamnatin. Alal misali, soke amfani da katin kuɗin Mastercard ya jawo wahalhalu da yawa ga ɗaliban Najeriya da ke ƙasashen waje, inda suke kasa amfani da kuɗaɗensu don cin abinci da biya wa kansu wasu bukatun yau da kullum.

Wannan ya jefa da yawa daga cikinsu cikin halin ha’ula’i. Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan alawus-alawus na ɗaliban da ta tura karatu a ƙasashen waje har ta kai ga wasu sun daina karatun, wasu kuwa sai da suka koma dogaro da danginsu don samun abin da za su kashe.

Ɗaliban da jihohi suka tura karatu a ƙasashen waje suma haka suke ta fama da waɗannan wahalhalun da rashin Dala da za su biya kuɗin makaranta da lura da kawunansu.

A baya-bayan nan, gwamnati ta ce ta bai wa bankuna kuɗaɗen ƙasashen waje don biyan kuɗaɗen makaranta , amma an ci gaba da kokawa kan yadda bankunan ke ɓoye kuɗaɗen su ƙi bai wa mabukata.

Haka ma ɗalibai da malamai da ‘yan kasar baki ɗaya ba za su iya amfani da katunan bankinsu ba don sayen litattafai daga dillalan litattafai da mujallu irinsu Amazon. Duk da kokawa da ake yi, Babban Bankin Najeriya ya jaddada dokar hana amfani da katin banki a kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Da sauran rina a kaba

Da alama za a ɗau lokaci mai tsawo kafin harkar ilimi ta gyaru a Najeriya.

A bara kaɗai, akwai sama da ɗalibai miliyan guda da rabi da suka nemi shiga jami’a a ƙasar; ɗaliban firamare kaɗai sun kai miliyan 25; makarantun firamare na gwamnati kuwa sun kai 54,434 da malamai 631,160.

Kawo sauyi a fanni mai faɗi irin wannan ba zai yiwu ba sai da kashe kuɗaɗe masu yawa, da fito da tsari na zamani da zai warware matsoli da yawa na koyarwa, da rashin kwarewar malamai, da sauransu.

Don haka Hukumar UNESCO ta ba da shawara ga ƙasashe masu tasowa su ware abin da ya kai kashi 26 cikin 100 na kasafin kuɗinsu don raya ilimi muddin suna so su samu ci gaba mai ma’ana. To amma ina Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin APC ta tsaya a cimma wannan buƙata?

In aka duba kason ilimi a kasafin kuɗin 2017, sai a ce ma an samu ci baya don kashi 5.5 cikin 100 ne kawai ta ware wa ilimi. Wannan ya kasa kan na bara inda ta ware kashi 6.1 cikin 100.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Alƙalumma kuma sun nuna cewa wannan gwamnatin ba ta kai gwamnatin da ta wuce ware kuɗi wa harkar ilimi ba. Ko kasafin da ta yi wa ilimi na bara da bana sun kasa kason biliyan 426.5 da waccar gwanatin ta ware wa ilimi a shekarar 2013; da biliyan 493 a 2014; da biliyan 492 a 2015.

Wannan shi ya sa malaman jami’a irin su Dokta Laja Odukoya, Shugaban Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa reshen Jami’ar Lagos, suke ganin da sakel a yadda wannan gwamnati take gazawa wajen bai wa sashin ilimi isassun kuɗaɗe. A faɗar Dokta Odukoya, “akwai rikici a gaba.”

ADIKON ZAMANI: Yadda za a magance cutar sikila


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Cutar na janyo daukewar numfashi, da gajiya da jinkiri wajen girman jiki

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya.

Mun yi rashin kwararru da dama domin wannan larura. Na rasa wani abokina na kut-da-kut mai suna Nura, wanda muka lakaba ma sunan “88 soja” sakamakon wannan cutar. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen wayar da kan jama’a game da illar ciwon sikila. Muna iya dakatar da wannan ciwon. Muna iya hana yaduwarsa.

Kawata Samira Sanusi ta yi fama da wannan ciwon na tsawon fiye da kashi biyu cikin uku na rayuwarta. An yi mata tiyata fiye da sau 10, kuma an sha kwantar da ita a asibiti sabili da matsalolin da sukan biyo bayan jinyar da ciwon na sikila ke haifarwa.

A duk lokacin da na ga wani mai fama da cutar sikila yana kuka saboda radadin cutar, sai na ce dama iyayensa ba su yi son kai ba. Ka ga, abu ne mai sauki kafin mu yi aure mu daure mu yi gwaji daga nan sai mu yanke shawara a kan ko ya kamata mu mu yi auren ko a’a.

Ana gadon cutar sikila ne daga iyaye masu dauke da wasu kwayoyin halitta na jini, wato haemoglobin, masu kamar lauje. An fi samun cutar a tsakanin Larabawa da ‘yan asalin nahiyar Afirka.

Kwayoyin halittun jinin na sauyawa (su koma siffar lauje), wanda yake jawo raunata kwayoyin halittar, wanda yakan zama hanyar kamuwa da ciwon amosanin jinin.

Amosanin jinin na janyo daukewar numfashi, da gajiya da jinkiri wajen girman jiki. Yana kuma sa idanu da fatar jiki su sauya zuwa launin ruwan kwai. Duk wadannan alamu ne na amosanin jini.

Ana kamuwa da cutar amosanin jini ne idan aka gaji nau’in wasu kwayoyin halitta (SS) daga iyaye. Idan mutum ya gaji kwayar halittar amosanin jini daga daya daga cikin iyayensa, kana ya gaji kwayar halittar da ba ta da amosanin jini daga daya bangaren, zai kasance mai halittar AS.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masana na jaddada bukatar ma’aurata su rinka yin gwaji kafin a yi aure

Amma hanya mafi kyau wajen dakatar da yaduwar wannan ciwon shi ne idan muka rage auratayya a tsakanin nau’in AS/AS, da AS/SS da SS/SS. Hanyar tabbatar da wannan ita ce ta gwajin jinin masu niyyar yin aure.

Wannan kira ne ga masu niyyar yin aure da su gwada irin ‘kwayoyin halittar su, watau genotype, kafin su yi aure.

Kuma kira ne ga iyaye da shugabannin addini da su tabbata an shigar da gwaje-gwajen kafin kowanne daurin aure ya gudana. Kada mu ci gaba da raunata rayuwar ‘ya’yanmu da jikokinmu. Jahilci ba dalili ba ne.

Komai yawan soyayyar da kake yi wa masoyiyarka, abin da ya fi kyau shi ne kuje a gwada ku kafin ku yi aure, domin kada soyayyarku ta zama kiyayya. Ka ga kun ceci ‘ya’yan da za ku haifa daga rayuwa dake cike da wahala.

Daya daga cikin bakin da suka tattauna a kan wannan batu a ADikon Zamani na rediyo, Alhaji Umar Farouk, ya ce, “Rabuwa da budurwar da na so na aura yana daga cikin muhimman shawarwarin da na taba yankewa a rayuwata”.

Yau shi da tsohuwar budurwar tasa sun sami ‘ya’ya masu ingantacciyar lafiya bayan da suka auri wadanda suka fi dacewa da su. Lallai akwai darasin sadaukar da kai a cikin wannan labarin.

A je ayi gwajin amosanin jini a yau!

British Airways ya dawo da zirga zirgar jiragensa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dubban fasinjoji sun yi cirko cirko a filayen jiragen sama a sassa daban dabam na duniya

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya maido da zirga zirgar jiragen sa yau lahadi, bayan wata babbar matsala ta na’urar kwamfuta da katsewar wutar lantarki ta haddasa, ta sukurkuta tsarin zirga-zirgar dubban fasinjoji a sassa daban daban na duniya.

Matsalar dai ta sa kamfani zai biya makuden kudade ga fasinjoji da suka yi cirko cirko a filayen jiragen sama a sassa dabam dabam na duniya.

Wakilin BBC ya ce an soke tashi da saukar jiragen kamfanin daga manyan filayen jirgin sama na London wato filin jirgi na Heathrow da kuma Gatwick saboda cunkoso.

Shugaban kamfanin na BA Alex Cruz, ya musanta zargin da kungiyar ma’akatan sufurin jiragen sama suka yi cewa an samu matsalar ce saboda yadda aka mayar da wasu ma’aikata na sashen fasahar sadarwa zaman kashe wando, da kuma mika ayyukan su ga kasar India.

Trump ya zama saniyar ware cikin G7 kan dumamar yanayi


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Babu shakka Mista Trump, wanda ke tare da matarsa Melania a wanna hoton, yana fatan za a yaba wa rangadinsa na farko zuwa kasashen duniya.

Mista Trump, wanda ya halarci taron na G7 a karon farko, ya taba karyata dumamar yanayi a matsayin shaci-fadi.

Duk da cewar Amurkan ta yi tarayya da sauran kasashen da suka hada da Birtaniya da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da kuma Japan kan yaki da ta’addanci, Shugaba Trump ya ki kara shigar da Amurka yarjejeniyar dumamar yanayi ta Paris, wadda kasashen shida suka yi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban Amurkan ya ce zai yanke shawara kan batun a mako mai zuwa.

Da yake bayani bayan tattaunawar kasashen G7 din, Firayim ministan Italiya, Paolo Gentiloni, ya ce an cimma matsaya kan wasu batuwa amma banda dumamar yanayi.

Ya ce: “Akwai batun da har yanzu ba cimma matsaya akai ba wanda shi ne batun yarjejeniyar Paris ta dumamar yanayi. Bisa wannan, shugaban Amurka da gwamnatin Amurka suna nazari kan yarjejeniyar.”

Ya kara da cewar: “Sauran kasashen da suke goyaon bayan yarjejeniyar Paris ta dumamar yanayi wadda muhimmiyar aba ce ga makomarmu sun gane hakan. Muna da karfin guiwar cewar bayan wannan nazari na cikin gida, Amurka ma za ta so shige ta.”

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Trump ya ki sassautawa kan shige-dafice da cinikayya da kuma dumamar yanayi

Shugabar Jamus, Angela Merkel, ta bayyana tatattaunawa kan cinikayya da dumamar yanayi a matsayin lamuran da ke cike da ce-ce-kuce, tana mai cewa ta gabatar da hujoji da dama domin kare yarjejeniyar dumamar yanayi ta Paris.

“Game da Dumamar yanayi, munyi magana da Amurka, kuma mun bayyana hujojinmu cewa muna son Amurka ta cigaba da goyon bayan yarjejeniyar dumamar yanayi,” in ji ta.

Ta ce: “Ni ma da kai na bayyana cewar samun aikin yi nan gaba zai dogara ne kan amfani da albarkatu ta yadda ya dace, kuma wannan na daga cikin yarjejeniyoyin duniya kadan da kasashe masu tasowa da kasashe na tsibiri da kuma Afirka ke fatan amfana. Amman Amurka ta bayyana cewar ita ba ta yanke shawara ba, kuma ba za ta yi hakan a anan ba, amman za ta ci gaba da nazari a kansa. Amman mun tafka zazzafar muhawara, kuma sauran mahalarta taron sun mayar da hankali ne kan cewar ya kamata Amurka ta ci gaba da yarjejeniyar dumamar yanayin baya.”

Mai baiwa shugaba Trump shawara kan tattalin arziki, Gary Cohn, ya ce shugaban ya halarci taron ne domin neman ilimi kuma ra’ayinsa na sauyawa kamar yadda ya kamata.

Amman Sakatare Janar na na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres wanda ya halarci taron a Sicily, ya shaida wa BBC Cewar ko wace matsaya Trump ya dauka yarjejeniyar za ta tsira.

Nigeria: An kammala aikin ruwan Zaria


Hakkin mallakar hoto
KADUNA STATE GOVERNMENT

Image caption

An kwashe shekaru gwamnatoci na alkawarin samarwa al’ummar yankin da ruwan sha.

A Najeriya, wata matsala da ta dade tana ciwa al’mmomin yankin Zaria na jihar Kaduna tuwo a kwarya ita ce ta rashin ruwan Famfo.

An dai kwashe shekaru gwamnatoci na alkawarin samarwa al’ummar yankin da ruwan famfo, amma shiru kake ji.

Sai dai yayin da gwamnatin APC a kasar ke cika shekaru 2 akan karagar mulki, gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta cika daya daga cikin manyan alkawuran da ta yi wa al’ummar jahar na kammala aikin ruwan na Zaria.

Hukumomi dai sun ce yanzu matsalar ruwa a yankin ta zama tarihi, koda ya ke kashi daya na aikin aka kammala wanda zai bada ruwa ga al’ummar Zaria da Sabon Gari.

Ana saran nan gaba kadan za’a kammala aikin baki daya wanda zai bada damar samar da ruwa ga wasu kananan hukumomi dake yankin.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El- Rufai ya bukaci al’umma da su rika biyan kudin ruwan Fanfo don samun damar ci gaba da samun ruwan akai-akai.

Wasu al’ummomin yankin sun shaida wa BBC cewa kammala aikin zai taimaka wajen magance matsalolin da suka dade suna fuskanta sakamakon rashin ruwan Fanfo.

FA Cup: Ba tabbas kan makomata a Arsenal–Wenger


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Kociyan Arsenal,Arsene Wenger, ya ce sai bayan zaman kwamitin gudanarwan Arsenal ranar Talata ne za a fitar da matsaya kan makomarsa a kungiyar

Duk da cewar ya ci kofin kofin FA a ranar Asabar, kociyan Arsernal,Arsene Wenge, ya ce babu tabbas kan makomarsa.

A bayanin da ya yi bayan lashe kofin FA dinsa na bakwai, Wenger ya ce za a fitar da matsaya kan makomarsa a kungiyar ne ranar Laraba ko Alhamis bayan zaman kwamitin gudanarwar Arsenal ranar Talata.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lashe kofin FA din ne bayan ta doke Chelsea da ci 2-1 a wasan da aka buga a ranar Asabar a filin wasan Wembley.

Alexis Sanchez ne ya sha wa Arsenal kwallo na daya a minti 4 da fara wasa.

Amman bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Victor Mosee, dan Najeriyar da ke buga wa Chelsea ya samu jan kati lamarin da ya rage ‘yan wasan Chelsea zuwa goma.

Duk da hakan Diego Costa ya rama wa Chelsea a minti na 76 da fara wasa.

Bayan minti uku da kwallon Diego Costa, Aaron Ramsey ya tura kwallon da Girou ya bugo masa cikin ragar Chelsea.

Wannan kofin FA din shi ne kofin FA na 13 da Arsenal ta ci.

Kyamar Musulmai: An kashe mutane 2 a Amurka


Hakkin mallakar hoto
CBS/EVN

Image caption

Harin ya aukune a cikin jirgin kasa na MAX a tashar Hollywood

‘Yan sanda a birnin Portland na Amurka sun ce an kashe wasu mutane biyu, yayin da suka yi kokarin hana wani mutun cin zarafin wasu mata biyu Musulmai.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a a cikin jirgin kasa.

‘Yan sandan sun ce mutumin wanda ya rika furta kalaman cin zarafi ga matan, ya dabawa mazan biyu wuka saboda sun yi yunkurin sa baki.

Wani fasinja guda a cikin jirgin ya samu rauni, kafin a kama maharin.

Majalisar kyautata mu’amala ta Musulunci a Amurka ta ce dole ne shugaba Trump ya dauki mataki kan yawaitar tsanar Musulunci a Amurka.

Majalisar ta zargi shugaba Trump da rura kyamar Musulmai saboda irin kalamansa da kuma manufofinsa.

Kun san matan da al-Shabab 'ta mayar bayi'?


Image caption

Wasu matan da suka kubuta daga kungiyar al-Shabab

A lokacin da Salama Ali ta fara bincike kan wasu ‘yan uwanta biyu da suka bata, a shekarar da ta gabata, ta gano wani al’amari mai ban tsoro – ba matasan Kenya masu tsattsauran ra’ayi ne kawai ke shiga kungiyar al-shabab ba, ta gano kungiyar na sace mata kuma tayi safararsu zuwa makwabciyar kasar Somaliya, inda ake mayar da su bayi domin a yi lalata da su.

Dole Salama ta gudanar da binciken neman ‘yan uwan nata cikin sirri, saboda duk wata alama dake nuna tana da alaka da kungiyar al-Shabab mai biyayya ga al-Qaeda na iya janyo tuhuma daga hukumomin tsaron kasar.

Sai ta rika ganawa da wasu mata, a cikin sirri a birnin Mombasa, domin neman bayanai ne game da ‘yan uwansu maza da suka bata.

Salama ta ce, “Mun fahimci cewar muna da yawa”.

Amma Salama ta gano wani batu na daban – labarin wasu mata da aka kaisu Somaliya ba da san ransu ba.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Saurari bayanin matan da al-Shabab suka mayar bayi

Matan sun hada da matasa da kuma tsofaffi, Musulmai da kuma Kirista, daga yankin Mombosa, har da wasu daga yankunan gabar tekun Kenya. Akan yi masu alkawarin samar masu ayyuka masu albashi mai tsoka a birane ko a wasu kasashe, daga nan sai a yi garkuwa da su.

A watan Satumbar da ya gabata Salama ta samu horona musamman, kuma ta kafa wata kungiya ta sirri don taimaka ma irin wadannan matan. Matan da suka samu labarin kungiyar sun rika nemanta domin su shiga kungiyar.

Ta ce, wasu sun zo da jarirai, wasu da cutar kanjamau, wasu ma da tabin hankali, wanda hakan sakamakon matsalolin da suka fuskanta ne.

Na gana da wadannan matan masu karfin hali, a cikin wani daki mai duhu, wanda suka ba ni labarin da ba a taba jin irinsa ba.

Daya daga cikin matan ta ce, “A lokacin, maza na zuwa domin su yi lalata da ni, ba zan iya fada miki adadinsu ba”.

“A shekarun nan uku kowa ne namiji na zuwa ya yi lalata da ni”, ta rika girgiza kanta sabili da tuna halin da ta shiga.

Wata matar kuma cewa ta yi,”Su kan kawo maza biyu ko uku ne suyi lalata da kowace mace a kowane dare. An yi mana fyade ba adadi”.

Wasu matan an tilasta masu zama “matan” ‘yan kungiyar al-Shabab, wasu kuma an mayar da su karuwai ne a wani gida.

Image caption

Wasu matan da suka kubuta daga kungiyar al-Shabab

Kungiyar al-Shabab na neman kafa daular Islama ne a Somaliya, suna kai hare-hare har cikin makwabtan kasashe, kuma an tura sojojin Kawancen Afirka don su yake su.

Wata sabuwar mamba a kungiyar Salama mai suna Faith kwananan ta tsere daga kungiyar.

Tana ‘yar shekara 16 ne wasu tsofaffin ma’aurata suka ce mata sun dauke ta aiki a Malindi. Saboda tana matukar neman aikin yi, kashe gari sai ta shiga wata mota tare da wasu fasinjoji 14 kuma an ba su ruwa mai bugarwa suka sha ba da saninsu ba.

Faith ta ce, “A lokacin da muka dawo hayyacinmu, akwai wasu maza guda biyu a cikin dakin. Sun rufe mana fuskokinmu da bakaken kyalle kuma sun yi mana fyade a dakin”.

An kara ba Faith ruwa mai bugarwa, daga baya sai ta ganta a cikin wani kungurmin daji, inda aka shaida mata cewa idan ta yi yunkurin tserewa za a kashe ta.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Dajin da ‘yan Al-Shabab suke boye mata su mayar da su bayi

Ta samu ciki sakamakon fyaden da aka yi mata, kuma ta haifi danta a dajin ita kadai.

Ta ce, “Kakata unguwarzoma ce, saboda haka na san yadda ake wasu abubuwan, ni kadai na yi komai a dajin, ni kadai na fitar da wannan jaririyar.”

Daga karshe Faith ta samu kubuta da ‘yarta, bayan da wani mai maganin gargajiya wanda ya shiga dajin domin neman sauyoyi ya gamu da ita. Ya kuma nuna mata hanyar da zata fita daga dajin. ‘Yarta tsirara ta rayu a cikin dajin, kuma yanzu rayuwar cikin gari na mata wahala, kuma ba ta iya yin barci da daddare har sai an fita da ita waje kuma sai tana hannun mahaifiyarta.

Faith ta ce ‘yarta ta saba da “rayuwa tamkar ta dabbobi a dajin”.

Wasu matan da suka tattauna da BBC sun haihu a wurin da aka tsaresu.

Matar wani tsohon dan kungiyar al-Shabab mai suna Sarah ta ce wannan an tsara ne da gangan, domin samar da ‘yan kungiyar da zasu gaji wadannan. Abu ne mai wuya mutane su iya rayuwa a sansanoni a Somaliya, amma abu ne mai sauki a canza tunanin yara.

Image caption

Faith da ‘yarta

Sarah ta ce, “A sansanin da aka tsare ni, akwai wasu matan da ake tura su domin su nemo matan da za su shiga kungiyar. Suna son matan domin su rika haihuwa ne”.

Ta ce, yawancin mata 300 da suke sansanin ‘yan Kenya ne.

Har ila yau, Salama na taimaka wa wadanda suka rasa ‘yan uwansu, kamar Elizabeth, wacce ta yi wa ‘yar uwarta ganin karshe shekaru biyu da suka gabata bayan da aka yaudare ta da wani aiki a Saudiyya.

Elizabeth ta ce, “Ta shaida mana cewa tana cikin hadari a Somaliya, a sansanin al-Shabab”. Layinta ya daina aiki, kuma tun daga wancan lokacin ba ta kara ji daga ‘yar uwarta ta ba.

Gwamnatin Kenya ta yarda cewa akwai matasala, amma kwamishinan yankin Mombasa Evans Achoki, ya ce, abu ne mai wahala a gano gaskiyar al’amarin, saboda matan ba su kai kukansu ba wajen hukuma ba.

Duk da cewa akwai wani shirin afuwa ga mayakan da suke dawowa daga Somaliya, amma ana samun rahotannin cewa wasunsu na bacewa, wasu kuma ana harbesu har lahira.

“Ana kallon duk wadanda suka tafi can da son ransu, ko ba da san ransu ba a matsayin masu laifi.”

Mun boye sunayen matan dake cikin labarin saboda kare lafiyarsu.

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a wannan makon


Wasu zaɓaɓɓun hotuna abubuwan da suka faru a sassan Afirka a makon nan.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Asabar ne, ‘yan uwan ‘yan matan Chibok 82 da aka sako a watan Mayun nan, suke shewa da tafi tare da gaisawa da juna a lokacin da suke jira domin ganawa da ‘ya’yan nasu.

A father being reunited with one of the released Chibok girls in Abuja.Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Ranar farin-ciki ce ta musamman ga ‘yan uwa da suka dade ba su gana ba, wadanda suka yi tafiya mai nisa daga jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya zuwa babban birnin kasar, Abuja.

Families unite with the released Chibok girlsHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Yan matan da aka sako na cikin 276 da mayakan Boko-Haram suka yi garkuwa da su daga makarantar ‘yan mata ta Chibok a shekarar 2014

People hold placards picturing Ethiopian Candidate for the post of Director General of World Health Organization (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, during a rally on his support, in front of the United Nations offices.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Talata ne, ‘yan kasar Habasha suka taru a kofar hedikwatar Hukumar Lafiya ta Duniya a Geneva da ke Switzerland, don nuna goyon bayansu ga sabon shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, kuma shi ne dan Afirka na farko da ya fara shugabantar Hukumar.

Supporters of Dakar mayor Khalifa Sall carry placards and chant slogans during a demonstration calling for his freedom from detentionHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Magoya bayan magajin garin Dakar ta kasar Senagal Khalifa Sall, sun yi gangami a birnin, suna kira da a sake shi, wanda aka kama bisa zargin zamba da kuma halatta kudaden haram.

An Egyptian seller dusts a traditional Ramadan lantern called "fanous" at his shop stall ahead of the Muslim holy month of RamadanHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An dauki wannan hoton ne a ranar Laraba lokacin da wani dan kasar Masar yake karkade fitilar da yake sayarwa wacce ake amfani da ita a watan azumin Ramadan, a birnin Alkahira.

Egyptian women carry traditional Ramadan lanterns called "fanous" ahead of the holy fasting month of Ramadan in Cairo, Egypt May 24, 2017.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana amfani da irin wannan fitilar da ake kira ‘fanous’ wajen yin ado lokacin watan azumin Ramadan.

A woman buys a packet of maize flour subsidised by the government at a supermarket in Kenya's capital, Nairobi, on Wednesday.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A ranar Laraba ne wata mata take sayen jakar garin masara a wani shagon sayar da kayayyaki wadanda gwamnati take tallafawa wajen rage farashinsu.

A woman buys oranges from a street vendor in central Harare, ZimbabweHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A nan kuwa wata mata ce ke sayen kayan marmari a gefen titi a Harare, babban birnin Zimbabwe.

A robot performs during the final of the national robotics competition on May 20, 2017 at the Marius Ndaye stadium in the Senegalese capital Dakar.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Asabar ne, aka yi gasar mutum-mutumi ta kasa, ta karshe a Dakar babban birnin Senegal.

A robot performs during the final of the national robotics competition at the Marius Ndaye stadium in the Senegalese capital Dakar.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Gwamnatin Senegal ce ta shirya gasar, don janyo hankalin matasa da kara musu sha’awar ilimin kimiyya.

A competitor prepares a robot during the final of the national robotics competitionHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dalibai da dama sun shiga gasar, wadda aka yi a filin wasa na Marius Ndiaye, inda ake wasan kwallon raga.

A robot performs during the final of the national robotics competition on May 20, 2017 at the Marius Ndaye stadium in the Senegalese capital DakarHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mutum-mutumin na da na’urori da danja masu daukar hankalin jama’a.

Residents of drought-hit Cape Town in South Africa crowd at night around a fresh water source from a stream off Table Mountain to collect safe drinking water amidst the water crisisHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mazauna Cape Town da suke fama da fari a kasar Afirka Ta Kudu sun taru a kan wani ruwa mai kyau da aka debo daga koramar ‘Table Mountain’ da daddare, don su samu su karbi wanda za su sha.

On Friday, French President Emmanuel Macron and his Mali counterpart President Ibrahim Boubacar Keita inspect a guard of honour during a visit in Gao, northern MaliHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A ranar Juma’a ne, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Mali Ibrahim Boubacar Keita ke karbar gaisuwar girmamawa a birnin Gao, da ke arewacin Mali, a ziyarar da shugaban Faransan ya kai Mali.

Images courtesy of AFP, EPA, Getty Images and Reuters

Silva ya koma Man City a kan fam 43m


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Silva ya taka gagarumar rawa wajen nasarar da kulob din Monaco ya samu a Gasar Ligue 1 da kuma matakin gab dana kasar da kulob din ya kai a Gasar Zakarun Turai

Kulob din Manchester City ya saye dan wasan tsakiyar kulob din Monaco Bernardo Silva a kan fam miliyan 43.

Dan wasan mai shekara 22 zai fara taka leda ne a Man City a ranar 1 ga watan Yulin bana. Silva ya ce: “Yanzu zan yi wasa a daya daga cikin manyan kulob din duniya.”

Silva ya yi wa Monaco wasa sau 58 a kakar bana – ciki har da wasa biyu da suka buga da Man City a Gasar Zakarun Turai, inda a duka ya ciyowa kulob din kwallaye 11 ya kuma taimaka wajen ciyo kwallo har sau 12.

Hakazalika, ya ce kwadayin yin aiki da Pep Guardiola yana daga cikin abin da ya sanya shi amincewa da tayin da Man City ta yi masa.

“Shakka babu idan mutum ya samu damar yin aiki da Guardiola, ba za ka iya cewa a’a ba,” inji dan wasan wanda ya buga wa kasarsa wato Portugal wasa sau 12.

Ya ci gaba da cewa “Idan ba Guardiola ba ne kocin da yafi kwarewa a duniya, to yana daya daga cikin wadanda suka fi kwarewa.”

An kammala Gasar Firimiyar bana ne Manchester City tana a mataki na uku, wanda hakan yake nufi cewa ta samu tikitin shiga Gasar Zakarun Turai ta badi.

Matakin rage hakko danyen mai bai shafi Najeriya ba— OPEC


Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC ta yi karin haske kan matakin da ta dauka tare da wasu manyan kasashe masu arzikin man amma wadanda basa cikin kungiyar irin su Rasha, na ci gaba da rage adadin danyen man fetur da ake kai wa kasuwar duniya.

A wannan makon ne bangarorin biyu suka kara wa’adin ci gaba da rage danyen man da watanni tara, bayan karewar wa’adin watanni shida da suka cimma yarjejeniya a kai tun farko.

Alhaji Muhammad Sanusi Barkindo, shi ne Babban Sakataren kungiyar ta OPEC, ya kuma yi wa Is’haq Khalid karin bayani ta wayar tarho:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Alhaji Muhammad Sanusi Barkindo, babban Sakataren kungiyar OPEC

Ingantattun hanyoyin yaƙi da talauci guda biyar a Nigeria


Hakkin mallakar hoto
EFCC

Image caption

Cin hanci na cikin matsalolin da suka fi addabar Najeriya

A daidai lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika shekara biyu a kan mulki, manazarta da dama suna ta sharhi kan salon mulkinsa, da nasarorinsa da kuma matsalolin da aka ci karo da su da yadda za a magance su. Muhammad Jameel Yusha’u wani manazarci ne kuma yana aiki da Bankin Raya Kasashen Musulmai wato Islamic Development Bank.

Yaƙi da talauci batu ne da ke ci wa kasashe da dama tuwo a ƙwarya. Wannan shi ya sa da dama daga ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke aiki kan raya ƙasa suka mai da hankali wajen yin bincike da gano ingantattun hanyoyin da za a yi amfani da su wajen magance fatara da talauci.

Abin tambaya a nan shi ne, me ake nufi da talauci, ta ƙaƙa za a iya fahimtarsa?

A wani sharhi na musamman da cibiyar ilimi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya wato (UNESCO) ta wallafa, ta bayyana cewa za a iya fahimtar talauci ne ta fuskoki guda biyu: wato matsanancin talauci, da kuma talauci sese-sese.

Shi matsanancin talauci ana fahimtarsa ne gwargwadon yawan kudaden shigar da mutum ke samu, da wadatar wadannan kudade wajen biyan bukatu na yau da kullum. Wadannan bukatu sun hada da ci da sha da matsuguni da sauransu. A takaice, matsanancin talauci shi ne yanayi na matsi da rashin samun ingantanciyyar rayuwa ta yadda dan Adam zai rayu cikin mutunci ba tare da tagayyara ko tozarta ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Talauci yana gallabar mutane sosai a Afirka

Talauci sese-sese kuwa ana duba shi ne gwargwadon irin kudaden da mutum yake samu idan aka kwatanta da sauran al’umma. Abin da hakan ke nufi shi ne, za a iya samun bambanci tsakanin kasashe bisa yanayinsu da karfin tattalin arzikinsu.

Alal misali, a kasashen Turai mallakar gida, da samun kiwon lafiya, da cin abinci mai kyau, ingancinsa ya kai rayuwar mai tagomashi a wasu yankunan na duniya. Hakazalika idan ka dauki yanayin rayuwa a kasashen Larabawa masu arzikin man fetur, wanda yake matsayin talaka a wasu kasashen zai iya zama mai wadata ne a wasu kasashen.

Daga cikin alkaluman da ake amfani da su wajen gane talauci, shi ne duk mutumin da yake rayuwa da kasa da dalar Amurka biyu, wato kimanin Naira dari bakwai a kudin Nijeriya (bisa canji na kasuwar bayan fage), to wannan mutumin shi ake kira da talaka.

Abin tambaya shi ne: wadanne hanyoyi za a iya amfani da su wajen rage radadin talauci? Wannan makala za ta yi bayani kan guda biyar daga ciki:

Hanya ta daya: Samar da ingantaccen ilimi:

Babbar hanya ta farko wajen magance talauci ita ce samar da ilmi ga jama’a. Domin shi ilmi yana bude kwakwalwar mutum ya fahimci muhimmancin rayuwa cikin alfarma, da kaucewa zaman wulakanci da ci-ma-zaune. Kamar yadda tsohon Shugaban Kasar Tanzaniya Julius Nyerere ya taba bayyanawa, shi ilimi ba wai hanya ce ta kaucewa talauci ba, ilimi makami ne na yakar talauci.

Ko da yake a kasashe masu tasowa ana kallon ilimi a matsayin wani abu ne da sai gwamnati ta gina aji, da samar da malamai sannan za a same shi; tabbas hakan yana da amfani, amma wannan fahimtar takaita hanyar samar da ilimi mai inganci ne.

Wajibin kungiyoyi masu zaman kansu ne, da shugabannin al’umma su duba irin jama’ar da ke cikin wadannan al’umma su tsara hanyoyin ilimantar da jama’a, kan karatu, da rubutu da kuma sana’o’i. Ta haka sai kowanne sashe ya taimaki sashe.

Hanya ta biyu: Koyar da sana’o’i

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bunkasar kasuwanci na rage radadin talauci

Hanya ta biyu wajen yaki da talauci ita ce koyar da sana’o’i kanana da manya. Hakan kuwa ya kamata a fara shi ne tun lokacin yarinta da samar da tsarin ilimi wanda yake nuna muhimmancin sana’a da dogaro da kai, maimakon mayar da hankalin wajen neman aikin albashi.

Wannan na daga cikin hanyoyin da kasar China ta yi amfani da su wajen karfafa tattalin arzikin jama’arta, da tallafa musu wajen inganta fasahar sana’o’i, wanda hakan ya taimaka gaya wajen habaka tattalin arzikin kasar.

Hanya ta uku: Inganta aikin noma

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Manoma na kokawa kan rashin tallafi

Muddin ana son magance talauci, to sai an koma ga naduke tsohon ciniki. Bincike da tarihi sun tabbatar da cewa mayar da hankali wajen aikin noma shi ne yake taimakawa kasashe da daidaikun jama’a fita daga kangin talauci.

A wani bincike da hukumar Kungiyar Hadin kan Tattalin Arziki ta kasashen da suka ci gaba wato (OECD) ta wallafa a shekara ta 2010, ta auna yanayin tattalin arzikin kasashe guda 25 domin gano wadanne hanyoyin ne suka fi taimaka musu wajen yaki da talauci.

Sakamakon ya yi amfani da hanyoyi guda uku wajen wannan bincike, wato inganta aikin noma, da hanyoyin samar da ci gaba amma ba na aikin noma ba, sai kuma kudaden da ‘yan kasashen waje suke aikawa da su zuwa kasashensu na asali.

Binciken ya tabbatar da cewa kashi 12 cikin 25 sun rage radadin talauci a kasashensu ta hanyar noma. Don haka duk mai son yin sallama da talauci, ya dauki fatanya ya nufi gona.

Hanya ta hudu: Bayar da bashi da tallafi ga masu son yin sana’a

Hanya ta hudu ta magance talauci ita ce samar da ba shi musamman mara sharadi ko kudin ruwa ga masu son zuba jari kan karamar sana’a. Hakan za a iya yi ne ta bangaren gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma tsarin adashi tsakanin jama’a.

Misali na kusa shi ne shirin Babban Bankin Najeriya (CBN) na tallafawa manoma da kudade domin inganta aikin noma. Kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, daga cikin wadanda za su fi zuwa aikin Hajji a bana a wasu jihohin Najeriya, akwai manoma wadanda suka ci gajiyar irin wannan shiri.

Amma bai kamata jama’a su ce sai sun jira gwamnati ba. Mazauna unguwanni za su iya yin adashin gata tsakaninsu, sannan duk wanda ya dauka, maimakon ya yi watanda da kudin sai ya zuba jari a wata sana’a.

Hanya ta biyar: Yin amfani da hanyoyin zamani na kimiyya da fasaha

Hakkin mallakar hoto
Instagram

Image caption

‘Amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen tallata kaya na da fa’ida’

A wannan karnin, hanyoyin fasaha na zamani suna saukake yadda yanayin rayuwa yake. Don haka koyawa jama’a yadda ake amfani da wadannan hanyoyi zai taimaka su yi amfani da basirar da Allah Ya yi musu wajen tallata sana’a ko koyar da ita.

Misali, kusan matasa a yanzu da dama suna da shafin sada zumunta na Facebook, ko Twitter, ko Instagram da sauransu.

Maimakon yin amfani da wadannan shafuka domin yin hira, za a iya sauya su wajen tallan sana’oi da kuma koyar da dabarun yaki da talauci.

Bugu da kari, za a iya yin amfani da su wajen neman jari. Akwai tsari na neman tallafi ta duniyar gizo wato Crowdfunding, duk wadannan dabaru ne na samun jari a zamanance domin kaucewa rayuwar kunci.

Kamar yadda Hausawa ke cewa, dabara ta ragewa mai shiga rijiya.

Dokta Muhammad Jameel Yusha’u, tsohon ma’aikacin BBC ne.

Ga aikin da zai iya samar da sama da naira miliyan uku a wata


Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Yanzu hannayen jarin kamfanonin sadarwa na zamani sun fi na kamfanonin mait tsada

Shin kun san gina manhajar kwamfuta mai farin jini ka iya samar wa mutum akalla dala dubu goma, wato sama da naira miliyan uku kowane wata?

Wannan na cikin albishir din da Zubairu Dalhatu Malami, wani dan Najeriya mai kamfanin sadarwar intanet da ke hulda da kamfanin Google, ya yi wa matasan Najeriya.

Zubairu ya ziyarci ofishinmu na London ne bayan ya halarci wani taron da kamfanin Google ya shirya wanda aka yi wa lakabi da ‘Google Cloud Next’ da zummar wayar da kan ma’abota shafukan Intanet kan yadda za su iya amfani da rumbun adana bayanai na GOOGLE.

A hirarsa da abokin aikinmu, Aliyu Abdullahi Tanko, Zubairu ya ce: “ina tabbatar maka yanzu a Najeriya muna da mutanen da ke samun dala dubu goma (sama da naira miliayan uku) daga goggle ko wani wata.”

Ya ce da yawan irin wadannan mutanen suna dakinsu ne, ba sa fita kuma ba wani rashin dai-dai suke yi ba.

“Suna zaune ne a cikin gida suna irin wannan tsare-tsaren na manhaja ta waya domin yanzu idan kana da mahaja mai kyau kuma aka sauke ta sau miliyan daya amman bai fi ace mutum dubu dari suke amfani da ita ba , toh ina tabbatar da cewa cikin yardan Allah ko mutum bai ajiye dala dubu goma (sama da miliyan uku) ba, zai ajiye dala dubu shida (sama da miliyan biyu) a ko wani wata,” in ji shi.

Ya ce mutane za su iya koyar fasahar sarrafa manhajar ta kwasa-kwasai da ake yi na koyan yarukan sarrafa kwafuta.

Watan Ramadan ya kama


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Watan Ramadan dai wata ne da Musulmai ke dagewa da ibada da addu’o’i

Musulmai a kasashe daban-daban na duniya ciki har da Najeriya za su fara azumin watan Ramadan ranar Asabar bayan ana sanar da ganin wata.

A najeriya majalisar kolin kasar kan addinin Musulunci ne ta sanar da ganin watan Ramadan din.

Mai alfarma sarkin Musulmi, wanda shi ne shugaban majalisar, Sultan Sa’ad Abubakar III, shi nne ya bayyana ganin watan a garuruwa daban-daban a Najeriya a wani taron manema labarai da aka gudanar a daren Juma’a.

Baya ga Najeriya Musulmai a wasu kasashen duniya irinsu Saudiyya da ma za su fara azumin na watan Ramadana ranar Asabar.

Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi inda ake matsa kaimi kan ibada da addu’o’i.

Ramadan: Me ya kamata a kauracewa a shafukan zumunta?

Man Utd: Valencia ya tsawaita zamansa


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Valencia ne ya jagoranci kungiyar Manchester United a wasan Europa

Dan wasan baya na Man Utd Antonio Valencia ya sanya hannu a kwantiragin karin shekara daya da kungiyar, wanda hakan zai sa ya ci gaba da zama a old Trafford har 2019, kuma yana da zabin karin shekara daya.

Valencia, mai shekara 31, ya bugawa kungiyar United wasannin 43 da ta yi a kakar bana, ya kuma jagoranci kungiyar a matsayin kyaftin a wasan karshe na gasar Zakarun Turai ta Europa da suka doke Ajax.

Dan wasan wanda dan kasar Ecuador ne, ya koma Old Trafford da murza leda daga Wigan a shekarar 2009.

Ya ce, “Ina matukar farin cikin sabunta kwantiragina”

“Manchester United ta shiga rayuwata tun 2009. Ina so in mika godiyata ga manajan mu saboda kwarin gwiwar da ya bani a kakar wasa ta bana, na kuma tabbata za mu taka muhimmiyar rawa a kaka mai zuwa.”

A watan Janairun da ya gabata ne United ta tsawaita wa Valencia kwantiragin shekara guda, a lokacin ta ce zai zauna a kungiyar har zuwa shekara ta 2018.

Ta'addanci: Za a yi wasan Madrid da Juventus a rufaffen filin wasa


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sama da mutum miliyan 200 ne ake sa ran za su kalli wasan karshen a fadin duniya

Za a rufe saman babban filin wasan kwallon kafa na Wales don yin wasan karshe na gasar Zakarun turai ta 2017 da za a yi a birnin Cardiff saboda dalilai na tsaro.

Sama da ‘yan kallo 170,000 ne ake sa ran za su je birnin domin kallon karon-batta tsakanin manyan kungiyoyin Juventus da Real Madrid ranar uku ga watan Yuni.

Shi ne zai kasance wasan karshe na farko da aka buga cikin rufaffen filin wasa.

Hukumar kwallon kafa ta Wales dai ta ce tabbatar da tsaro shi ne “babban abin da ke gabanta”.

An bayar da shawarar rufe saman filin wasan ne saboda fargabar kai hari da jirgi maras matuki a kan abin da aka bayyana da wasa mafi girma tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a duniya.

Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, hukumar ta ce ta dauki matakin rufe saman filin wasan bayan yin la’akari da “bukatar hakan daga hukumomi”.

Za kuma a rufe saman filin wasan a lokacin da kungiyoyin za su yi atisaye a filin wasan ranar Juma’a biyu ga watan Yuni.

Man City za ta amince da dauko Bernardo Silva daga Monaco


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bernardo Silva ya ci wa Monaco kwallo 11 a kakar wasa ta bana

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, ta amince da kulla kwanitiragi da dan wasan tsakiya na Monaco Bernardo Silva a kan kudi fam miliyan 43.

Dan wasan mai shekara 22 dan asalin kasar Portugal zai zo City ne idan aka bude kasuwar cinikin ‘yan wasa ranar daya ga watan Yuli, kungiyar ta sanar da cinikin ne ranar Alhamis.

Silva dai ya yi wa wa Monaco wasa 58 a kakar bana, da suka hada da wasa biyu da kungiyar ta kara da City a gasar Zakarun Turai,. Ya kuma ci kwallo 11 ya taimaka an ci 12.

Ya yi wa kasarsa ta Portugal wasa 12, inda ya ci mata kwallo guda.

Manchester City dai ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun turai ta badi, bayan da ta kare Premier a matsayi na uku.

Manchester: Wayar salula ta ceci ran wata a harin bam


Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Lisa Bridgett na asibiti tare da iyalanta

An nuna hotunan wata wayar salula wacce ake zaton ta taimaka wajen ceto rayuwar wata mata ‘yar yankin Gwynedd, kuma matar da ta sami raunuka masu yawa a lokacin da aka kai harin bom a birnin Manchester.

Matar mai suna Lisa Bridgett ‘yar asalin garin Pwllheli na kasar Wales ce, tana cikin amfani da wayar ne a ranar Litinin, lokacin da bam din ya tashi, kuma wani notin karfe ya buge ta.

Lamarin ya sa ta rasa yatsarta ta tsakiya kuma notin ya fasa wayarta da kuncinta, inda ya makale a cikin hancinta.

Mijinta ya ce yana ganin wayar ce ta karkatar da notin ta kuma rage karfinsa.

Hakkin mallakar hoto
Steve Bridgett / Facebook

Image caption

Ana ganin wayar salular Lisa Bridgett ta ceci rayuwarta

Harin da aka kai a dandalin wasanni na Manchester Arena ya kashe mutum 22 kuma ya raunata wasu 64. An kama mutane takwas a sanadiyyar harin da Salman Abedi ya kai.

Madam Bridgett waddad ta tafi wajen kallon mawakiyar tare da ‘yarta da kuma ‘yar kawarta, ta ce ta yi “sa’a ba ta halaka ba”, in ji mijinta Steve.

An yi mata tiyata ranar Talata kuma za a sake yin wani tiyatar ranar Alhamis bayan da aka gano ta sami raunuka a wurare daban-daban har da karaya a kafarta da wani katon rauni a cinyarta.

Mista Bridgett ya shiga shafinsa na Facebook yana cewa, “Ina ganin amfani da wayar salularta a daidai lokacin ya ceci rayuwata.”

“Da alama wayar ta karkatar da notin kuma ta rage masa sauri kwarai”, in ji shi.

Mista Bridgett ya ce shi da mai dakinsa suna mika godiyarsu ga jami’an ‘yan sanda da ma’aikatan asibiti, da wani mutum mai suna Peter, “domin taimaka wa Lisa da suka yi daga wurin harin zuwa asibiti”.

Man United: Jose Mourinho na san sayo 'yan wasa uku ko hudu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jose Mourinho ya bayyana wa mataimakin shugaban hukumar gudanarwar kungiyar aniyarsa

Man Utd na son takaita kashe kudinta wajen sayen manyan ‘yan wasa uku ko hudu, da ake ganin za su hada da Griezman da Michael Keane.

United za ta buga gasar Zakarun Turai ta badi, kuma koci Jose Mourinho ya ce mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar Ed Woodward na sane da wannan aniya tasa “sama da wata biyu da suka gabata”

Mourinho na son kara karfafa ‘yan wasan gaban kungiyar tare da ‘yan wasan baya, saboda fuskantar kalubalen gasar Premier a kaka mai zuwa.

Ana dai alakanta kungiyar da son daukar dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antoine Griezmann, da kuma dan wasan baya na Burnley Michael Keane.

Kocin dan Portugal wanda ya bayyana haka ranar Laraba, bayan da kungiyar ta dauki kofin Zakarun Turai na Europa ya ce “Ed Woodward na sane aniyata.”

Ya kara da cewa “yanzu ya rage nasa da kuma masu kungiyar”.

Burin Mourinho

Griezmann, dan wasan Faransan mai shekara 26 da ke da farashin euro miliyan 100 a kwantiraginsa, ya fada a farkon makon nan cewa, damar da yake da ita ta zuwa United kashi “shida ce cikin goma”

Samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai zai bai wa kungiyar kwarin gwiwar nemansa kai tsaye.

Griezmann dai na da gudu da kuma waskiya abin da United ta rasa, amma idan hakan bai samu ba, to kungiyar ka iya koma wa ga dan wasan gaba na Torino Andrea Belotti dan asalin Italiya wanda ya ci kwallo 25 a gasar Serie A ta bana.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Griezmann ya ci wa Faransa kwallo 15 a wasa 41 da ya yi mata

Keaneya bar United zuwa Burnley a watabn Janairun 2015, amma yanzu Mourinho ya zaku ya dawo da dan wasan bayan mai shekara 24 zuwa Old Trafford.

A ka’ida kashi 25 cikin dari na yarjejeniyar da aka amince da ita a baya za a rage.

To sai dai Kocin Burnley Sean Dyche ya ce kungiyar ba ta da matsalar kudin da zai sa ta sayar da Keane, wanda ya fara bugawa kasar Ingila kwallo a watan Maris.

'Yan bindiga sun kashe Kiristoci Kibdawa 23 a Masar


A kalla mutum 23 aka kashe bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wata motar safa da ke dauke da Kirista Kibdawa a tsakiyar kasar Masar.

Lamarin ya faru ne a jihar Minya mai kilomita 250 (mil 155) kudu da birnin Alkahira, a daidai lokacin da Kibdawan ke kan hanyar zuwa wani Coci.

A watannin da suka gabata, an sha kai hare-hare kan Kibdawa, lamarin da mayakan kungiyar IS suka dauki alhakin kai wa.

Ranar 9 ga watan Afrilun da ya gabata an kai wasu hare-harekunar bakin wake biyu a biranen Tanta da Iskandariya, harin da ya jawo mutuwar a kalla mutum 46.

Lamarin da ya sanya Shugaba Abdul Fattah al-Sisi kafa dokar ta-baci a kasar baki daya.

Sannan ya yi alkawarin yin duk abin da ya kamata domin tunkarar masu ikirarin jihadi.

'Yan bindiga sun sace 'yan makaranta shida a Legas


Hakkin mallakar hoto
Peeter Viisimaa

Image caption

Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya

‘Yan sanda a Legas sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace ‘yan makaranta guda shida.

‘Yan bindigan sun kai hari ne a makarantar Igbonla Model School ranar Alhamis, inda suka tafi da ‘yan makaranta 10.

Amma rahotanni sun ce sun saki hudu daga cikin yaran, bayan da suka binciki asalin iyayensu.

‘Yan sanda sun ce ‘yan bindigar sun sami shiga makarantar ta cikin wani daji da ke gefen makarantar ne, inda suka yanka wayar da ta zagaye makarantar kana suka shiga ciki.

Suka kara da cewa a yanzu jami’an tsaro sun dukufa domin binciken inda ‘yan bindigar suka tafi da yaran.

An taba sace dalibai shida a watan Oktoban da ya gabata a wannan makaranta.

Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya.

Fursunoni sun tsere a gidan yari a Brazil


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yan sandan Brazil sun cafke 9 daga cikin fursunoni 91 da suke tsere

Kimanin fursunoni casa’in da daya ne suka tsere daga wani gidan yari a arewa maso gabashin Brazil bayan da suka sulale ta wata ‘yar karamar hanya dake karkashin kasa.

Ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda a yankin Parnamirim, dake jihar Rio Grande do Norte, sun cafke mutum tara daga cikin fursunonin yayin da suke fafutikar nemo sauran da suka tsere.

Wannan lamari dai ya faru ne ‘yan watanni bayan da wasu fursunoni 56 suka tsere daga wani gidan yari a jihar sakamakon kazamin fada tsakanin wasu gungu da basa ga maciji da juna.

Kamar dai akasarin gidajen yari da dama a Brazil, gidan yarin na Parnamirim ya yi matukar lalacewa baya ga cunkuson fursunoni da ake fuskanta.

Shugabannin kasashen G7 zasu fara taro a Italiya


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Donald Trump ya isa birnin Sicily da matar sa ranar alhamis don halartar taron G7

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki wato G7 za su fara wani taro a birnin Sicily na kasar Italiya,

Taron dai shi ne na farko da shugaban Amurka Donald Trump zai halarta yayin da yake kammala ziyarar sa a wasu kasashen duniya.

Tun bayan harin da aka kai a birnin Manchester, ana saran shugabannin za su amince da bukatar kara matsa kaimi don yaki da ta’addanci a duniya.

Sai dai wakilin BBC kan harkokin dilomasiyya ya ce Mr Trump zai fuskanci adawa kan wasu manufofi da suka hada da matsayin sa game da sauyin yanayi.

Takaddama ta kaure a Niger kan sarauta


A Jamhuriyar Nijar, wata takaddama ta kaure tsakanin wasu bangarori 2 da ke neman sarautar garin Tsibiri da ke cikin yankin Dogon Dutsi a jahar Doso.

Hakan ya biyo bayan wani hukunci da wata babbar kotu a Yamai ta yanke ranar Alhamis inda ta hana bangaren Arawa yin takaran neman Sarautar.

Sai dai wani mai magana da yawun bangaren Arawa, Shekarau Kwabo Sarkin Nassarawa ya ce ba zasu amince da matakin ba, sai dai a yi musu ta su masarautar.

Ya kuma yi zargin cewa an sanya siyasa kan batun masarautar.

Ana su bangaren Alhaji Salisu mai Fada, daya daga cikin masu neman sarauta a bangaren Gubawa ya ce tun da kotu ta yanke shari’a bai kamata bangaren Arawa su rika ja da hukuncin kotu ba.

An dai sha fuskanta takaddama akan sarauta a Jamhuriyar Nijar, lamarin da kan kaiga mummunar rikici har da asarar rayuka.

Nigeria: INEC na zargin gwamna da laifin rijistan zabe sau biyu


Hakkin mallakar hoto
.

Image caption

Hukumar INEC ta ce Gwamna Yahaya Bello ya saba wa dokar Najeriya

A sanarwar da ta fitar a daren Alhamis, hukumar zaben Najeriyar ta nesanta kanta daga sake rijistan katin zaben da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogin ya yi ranar 23 uku ga watan Mayu a fadar gwamnatin jihar da ke Lokoja bayan rijistan da ya yi a shekarar 2011 a unguwar Wuse da ke birnin Abuja.

Sanarwar ta ce hukumar tana da cibiyar rijista daya tilo ne a ko wacce karamar hukumar kasar domin aikin cigaba da masu yin zabe rijista, tana mai cewar yi wa gwamann rijista a fadar gwamnatin jihar Kogi da ke lokoja ya saba wa doka.

Hukumar ta ce kashi na farko a karamin shashi na daya karkashin sashi na 308, na kundin tsarin mulkin kasar ne ya hanata gurfanar da gwamnan a gaban kotu.

Amman duk da haka ta soke rijista na biyun da gwamnan ya yi, kuma za ta dauki matakan ladabtarwa kan jami’inta da ya sake yi wa gwamnan rijista sabanin tsarin hukumar.

Tun ranar 23 ga watan ne wata kungiya mai suna Kogi for Change ta yi barazanar kai gwaman kotu tana mai cewar laifi ne yin rijistan zabe sau biyu.

Na nemi jin ta bakin mai magana da sakataran watsa labaran gwamnan Kingsley Fanwo, amman haka ta bata cimma ruwa ba domin wayarshi ba ta shiga.

Kuma mai taimaka wa gwamnan kan yada labarai ta rediyo da talabijin, Gbenga Olorunpomi, bai amsa tambayar da muka tura masa ta sakon imail ba.

Saida kuma kafafan yada labarai a Najeriya sun ambato Mista Kingsley Banwo yana cewar gwamna ya shiga wani yanayin da ya tilasta masa sake rijistan ne bayan kokarin mayar da rijistarsa ta farko Kogi daga Abuja ya ci tura.

Matsalar yin rijista fiye da daya na daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga samun sashihin zabe a kasar. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa aka fara amfani da na’urar tantance masu zabe a zaben shekarar 2015.

"Yadda 'rashin ingancin' ilimin Nigeria ke sa mu tafiya waje"


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dumbin ‘yan Najeriya ke barin kasarsu don zuwa Ghana karatu

Matsalolin da suka addabi Najeriya, kama daga rashin ingantattun asibitoci zuwa rashin kwararrun Malaman makaranta, na cikin abubuwan da ke tilastawa ‘yan kasar fita kasashen waje domin neman biyan bukatunsu.

Tun ma lokacin hankali na kwance, ‘yan Najeriya kan fita kasashe irin su Amurka da Burtaniya domin neman ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.

Daga bisani kuma, lokacin da al’amura suka tabarbare ‘yan kasar sun mayar da hankalinsu zuwa kasashen Larabawa da nahiyar Asia domin neman lafiya da ilimi.

Yanzu ba wani abin mamaki ba ne idan aka ji dan Najeriya ya tafi kasashen Indiya ko Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman ma birnin Dubai domin neman lafiya.

Haka kuma ‘yan kasar ta Najeriya kan fita zuwa Malaysia da Singapore domin neman “ingantaccen” ilimi.

A Afirka kuwa, ‘yan Najeriya sun mamaye Jami’o’i a kasashen Uganda da kuma Ghana.

Na leka Jami’o’i da dama a nan kasar Ghana inda na ga daruruwan ‘yan Najeriya da ke karatu a fanni daban-daban.

Hakkin mallakar hoto
Halima Umar

Image caption

Nasidi Adamu Yahaya na tattaunawa da wasu dalibai

Ba mu da mafita

Akasarin ‘yan Najeriyar da na tattauna da su sun ce sun shigo wannan kasa domin yin karatu ne saboda al’amarin karatun Najeriya ya tabarbare.

Nuhu Mustapha Hunkuyi, wani dalibi ne a wata Jami’a mai zaman kanta, kuma ya shaida min cewa Jami’o’in Najeriya sun ki ba shi gurbin karatu duk da yake ya cika dukkan sharudan samun gurbin.

“Na rubuta jarrabawar SSCE kuma na yi nasara a dukkan darussan da na rubuta amma duk Jami’ar da na tuntuba babu wacce ta amince ta ba ni gurbin yin karatun Digiri, sai kawai na yi tahowa ta nan Ghana,” in ji shi.

Ya kara da cewa zuwansa Ghana ya zamar masa gobarar titi a Jos “domin kuwa karatun da nake samu a nan ya fi na Najeriya inganci”.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Daliban sun ce a Ghana an fi koyar da karatu a aikace ba a baki kawai ba kamar NAjeriya

Shi kuwa Ismail Abari ya gaya min cewa ya zo kasar Ghana ne saboda babban makasudin da ya sa shi da mahaifansa suka yanke shawarar zuwansa kasar Ghana karatu shi ne rashin samun ilimi mai inganci a Najeriya.

“Ya kamata ka sani cewa a Najeriya an fi koyar da karatu a baki; su kuwa kasar Ghana suna koya wa mutum karatu ne a aikace. Ka ga kuwa ba za a hada abin da za a yi maka da baki da wanda za a koya maka a aikace ba,” in ji Ismail Abari.

Ina mafita?

Ya kara da cewa Najeriya ta yi kaurin suna wajen yajin aikin Jami’o’i, lamarin da kan sanya “dalibin da ya kamata ya yi shekara hudu a Jami’a zai yi shekara da shekaru bai kammala jami’a ba. Amma ba mu taba fuskantar yajin aiki a nan ba.”

Wani Malamin Jami’ar Legon da bai so a fadi sunansa ba, ya shaida min cewa ingancin ilimin kasarsu ya fi na Najeriya ne saboda muhimmancin da gwamnati ke bai wa fannin ilimi, ko da yake ya kara da cewa su ma suna fuskantar matsalolin da ba a rasa ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana yawan yin yajin aiki a jami’o’in Najeriya in ji daliban

Hukumomin Najeriya dai sun sha cewa suna kokarin magance matsalolin da suka addabi harkar ilimi, wadanda ke sa wa ‘yan kasar ke fita kasashen waje neman ilimi.

Sai dai sun ce tabarbarewar ilimi ya soma ne tuntuni saboda kawar da kai daga gwamnatocin baya.

Masana dai na ganin har yanzu gwamnatin kasar ba da gaske take ba a shirinta na farfado da ilimi saboda har yanzu kasafin kudin da ake ware wa fannin bai kai mizanin da hukumar kula da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Watakila a tuhumi Ronaldo da kin biyan haraji


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lokacin da ‘yan wasan Real Madrid ke murnar lashe kofin La Liga wanda rabon da ta dauka tun 2012

Watakila a tuhumi dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo da laifin kin biyan haraji a Spaniya.

Masu shigar da kara sun mika takardu ga ofishin tara kudin haraji, wadanda za su fayyace ko za a tuhumi dan kwallon ko akasin hakan.

Rahotanni a Spaniya na cewa ana zargin Ronaldo mai shekara 33 da kin biyan harajin kudi fam miliyan 13 daga shekarar 2011 zuwa 2014.

Wasu takardun sirri da aka fitar a watan Disamba sun nuna yadda Ronaldo ya kaucewa biyan haraji a kudin da yake samu don amfani da hotunansa a ma’ajiyar da ya tanada a wajen Spain.

Ronaldo ya karyata aikat ba daidai ba.

Shi ma kocin Manchester United, Jose Mourinho yana cikin wadanda aka zarga, amma ya karya ta batun.

An kama tattabara ɗauke da miyagun ƙwayoyi


Hakkin mallakar hoto
AL-RAI

Image caption

An yi amanna cewa kwayoyin wadanda doka ta haramta yin ta’ammali da su ne

Jaridar al-Rai ta kasar Kuwait ta bayar da rahoton cewa, Jami’an kwastam na kasar sun kama wata tattabara mai dauke da mugayen ƙwayoyi a bayanta.

Jaridar ta kara da cewa, an samu ƙwayoyi da suka kai 178 a cikin wani dan aljihu da aka manna a bayanta.

An kama tsuntsuwar ne a kusa da wani ginin kwastam da ke Abdali, kusa da kan iyakar Iraki.

Abdullah Fahmi ya shaidawa BBC cewa, jami’an kwastam sun dade da sanin cewa ana amfani da tattabaru wajen yin fasa-kwaurin kwayoyi, amma wannan ne karo na farko da suka kama tsuntsuwa a hukumance.

Hakkin mallakar hoto
Al-RAI

Image caption

Ana amfani da tattabara wajen aika sako

A shekarar 2015 ma, masu gadin wani kurkuku a Costa Rica sun kama tattabara dauke da hodar iblis da tabar wiwi a cikin wata ‘yar jaka da aka manna mata.

A shekarar 2011 ma, ‘yan sandan Kolambiya sun gano wata tattabara da ta kasa tashi wajen tsallake wani kurkuku mai tsayin gini, saboda nauyin da ya yi mata yawa na hodar iblis da nau’o’in tabar wiwi.

Tun zamanin Romawa ake amfani da tattabaru wajen aika sako.

Tattabaru na iya komawa gidajensu daga nisan tafiyar daruruwan kilo mita.

Majalisa ta amince da dokar man fetur ta Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kudurin dokar zai kawo sauyi mai amfani a bangaren man fetur na Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudurin dokar yin sauye-sauye ga dokokin sarrafa mai da iskar gas a kasar wanda ake kira Petroleum Industry Bill.

Kwamitin hadin gwiwa da majalisar ta kafa kan man fetur da albarkatun gas ne ya gabatar da rahoton a ranar Alhamis.

Bayan duba ga kudirin, tare da yin ‘yan kananan sauye-sauye, majalisar ta amince da kudurin, inda ya kusa zama doka.

An shafe shekaru ba a amince da kudurin ba saboda hakan ba zai rasa nasaba da fatan da ake da shi na kawo sauye-sauye a bangaren man fetur da iskar gas na Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki ya ce, ” Ina yi wa Majalisar Dattawa murna na amincewa da suka yi da wannan kuduri wanda ya dade a majalisar

Sharhi, Naziru Mika’il

Kuduri ne da yake son kawo sauye-sauye kan yadda ake gudanar da al’amura a bangaren man fetur, da kuma kawo sauye-sauye a kamfanin mai na kasa NNPC, ta yadda kamfanin zai dinga gogayya da manyan kamfanonin mai na duniya domin samun riba maimakon faduwar da yake yi wanda ake ganin zargin cin hanci da rashawa da ya adabi kasar ne ya jawo hakan.

Akwai zargin cewa wasu manyan kamfanonin mai na duniya kamar ba sa farin ciki da kudurin, shi ya sa ake ganin kamar hake ne ya jawo tarnaki a baya.

Ainihin kudurin ya zo ne daga bangaren zartarwa, amma amincewar na yanzu ya zo ne daga bangaren ‘yan majalisa wato yunkurinsu ne na ganin an kawo sauyi a wannan fanni shi yasa aka zo wannan gaba.

Sai dai har yanzu da sauran tafiya domin akwai bukatar Majalisar Wakilai ita ma ta amince da wannan kuduri sanan kuma a aika shi zuwa fadar shugaban kasa kafin daga bisani ya zama doka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana zargin cin hanci ya mamaye bangaren man fetur na Najeriya

Wani zai sha ɗaurin shekara 6 kan kalaman da ya yi a Facebook


Hakkin mallakar hoto
Twitter

Image caption

Yonatan Tesfaye zai sha daurin shekara shida

Wani ɗan jam’iyyar adawa a kasar Habasha Yonatan Tesfaye, zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekara shida bayan da aka kama shi da laifin goyon bayan ta’addanci a kalaman da ya yi a Facebook.

Wata jaridar kasar Addis Standard, ta ruwaito labarin inda ta kara da cewa kotun ta yi masa hanzari inda ta saurari wasu hujjojinsa, ta kuma yi masa sassauci wajen yanke hukuncin.

A farkon wannan watan ne, kungiyar Amnesty International ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ba a yi wa mutumin adalci ba.

An kama shi ne a watan Disambar 2015 a lokacin da zanga-zangar adawa da gwamnati da ake yi a yankin Oromia ke kara yaduwa.

Hukumomi sun nuna rashin amincewa da rubuce-rubuce masu yawa da ya yi da suka hada da inda ya ce, “gwamnati na amfani da karfin tsiya a kan mutane maimakon tattaunawar zaman lafiya.”

An yi ta Allah wa-dai da Habasha kan amfani da dokokin da ake adawa da ta’addanci don rufe bakin ‘yan adawa.

Kofin FA: Arsenal za ta kara da Chelsea


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Arsenal tana da kofin FA guda 12, ita kuwa Chelsea tana da guda bakwai

Kungiyar Arsenal za ta fafata da Chelsea a wasan karshe a kofin kalubale na kakar wasan bana a Wembley a ranar Asabar.

Chelsea ce ta lashe kofin Premier da aka kammala na bana, yayin da Arsenal ta kare a mataki na biyar.

Arsenal ta lashe kofin FA sau 12, ita kuwa Chelsea tana da shi guda bakwai.

Sai bayan an kammala karawar ce mahukuntan Arsenal za su tattauna domin fayyace makomar Arsene Wenger a kungiyar.

Haka kuma za a tanadi matakan tsaro domin kaucewa abin da ya faru na harin kunar bakin wake a Manchester Arena a ranar Litinin.

Ronaldo ya ci kwallo 405 a Madrid


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ronaldo ya koma Real Madrid a shekarar 2009

Cristiano Ronaldo ya ci wa Real Madrid kwallo 405 a kakar wasa bakwai da yake murza-mata leda.

Dan kwallon na Portugal ya ci 40 a wasannin shekarar nan, kuma kaka bakwai a jere yana cin fiye da 40.

Ronaldo ya ci kwallo 25 a La Liga da 10 a Gasar cin Kofin Zakarun Turai da hudu a Kofin Zakarun nahiyoyi da guda daya a Copa del Rey.

Real Madrid za ta buga wasan karshe da Juventus a Kofin Zakarun Turai a ranar 3 ga watan Yuni.

Dan wasan ya koma Madrid a shekarar 2009 daga Manchester United.

Ga jerin kwallayen da dan wasan ya ci a Madrid.

 • 2009/10 – 33
 • 2010/11 – 54
 • 2011/12 – 60
 • 2012/13 – 55
 • 2013/14 – 51
 • 2014/15 – 61
 • 2015/16 – 51
 • 2017/18 – 40

Ingila ta ki gayyatar Wayne Rooney


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wayne Rooney ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Inbgila wasa 119

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ba ta bai wa Wayne Rooney goron gayyata zuwa wasan da za ta yi da Scotland da Faransa ba.

Rooney wanda ya yi wa Ingila wasa 119, ya buga wa Manchester United fafatawa 15 a kakar bana.

Ingila za ta kara da Scotland a wasan shiga gasar cin kofin duniya a ranar 10 ga watan Yuni a Hampden Park.

Daga nan ne tawagar za ta buga wasan sada zumunta da Faransa a ranar 13 ga watan Yuni.

Ingila ce ta daya a kan teburin rukuni na shida da maki 13, yayin da Scotland ke matsayi na hudu da maki bakwai a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018..