Wariyar launin fata: An ba wa Sulley Muntari katin gargadi kan korafi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sulley Muntari ya fice daga fili yana nuna wa magoya bayan Cagliari: ”Ku duba launina kenan”

Dan wasan kungiyar Pescara ta Italiya Sulley Muntari ya fice daga fili domin nuna bacin ransa kan katin gargadi da alkalin wasa ya ba shi bayan da ya yi korafin cewa ana masa cin mutuncin wariyar launin fata.

Tsohon dan wasan tsakiya na Ghana mai shekara 32 ya bukaci alkalin wasa Daniele Minelli ya dakatar da wasan na ranar Lahadi na gasar Serie A wanda suke yi a gidan Cagliari.

Amma sai alkalin wasan ya ba shi katin gargadi a minti na 89 bisa laifin kawo rudu a wasan, lamarin da ya harzuka tsohon dan wasan na Portsmouth da Sunderland ya fice daga fili cikin fushi, yana nuna wa magoya bayan Cagliari hannunsa yana cewa: ”Wannan ne launi na.”

Kociyan Pescara Zdenek Zeman, wanda aka ci kungiyarsa 1-0, ya ce, dan wasan ya bukaci alkalin wasan da ya dau mataki a kai, amma sai ya ce shi bai gani ba bai kuma ji komai na cin mutuncin da danwasan ya yi korafi ba.

Kociyan ya ce Muntari ya yi dai dai amma da bai fice daga fili ba, domin za mu iya yin korafi amma ba mu da ikon yin hukuncin.

Muntari yana AC Milan lokacin da abokin wasansa a kungiyar Kevin-Prince Boateng ya fice daga fili saboda wakar warinyar launin fata da magoya bayan Pro Patria suka rika yi masa a watan Janairu na 2013.

Lamarin ya jawo korafi da nuna goyan bayan ga Boateng a shafukan sada zumunta a lokacin, har Fifa ma ta mara masa baya, amma ta ce bai dace ba da ya fice daga wasan.

Kungiyar Pescara ita ce ta karshen teburin Serie A kuma tuni ta riga ta fadi zuwa gasar rukuni na biyu na Italiya.

Boksin: Fury ya amince da kalubalantarsa da Joshua ya yi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tyson Fury ya ce yana son su dambata da Anthony Joshua, domin ‘yan kallon da ba a taba samun yawansu ba, su kashe kwarkwatar idanunsu

Tyson Fury ya amsa kalubalantarsa da zakaran damben boksin na ajin masu nauyi na duniya Anthony Joshua na Birtaniya, dan asalin Najeriya, ya yi na su gwabza bayan doke Wladimir Klitschko da zakaran ya yi ranar Asabar.

Joshua, wanda ya gama da tsohon zakaran, dan Ukrania a turmi na 11 a filin wasa na Wembley, nan take ya kalubalanci Fury wanda shi ma dan Birtaniya, wanda shi ma ya doke Klitschko da yawan maki a karawar da suka yi a watan Nuwamba na 2015.

Bayan nasarar ta ranar Asabar ne, Joshua ya tambaya, ”Fury ina kake ne?” Ya ce: ”Na san yana ta magana, to ina son in ba wa ‘yan kallo dubu 90 damar ganinmu.”

Fury, wanda bai kara wani dambe ba tun lokacin da ya doke Klitschko, ya amsa kalubalantar da Joshua ya yi masa inda ya ce : “Ba ri mu taka rawa.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan shi ne karo na biyar da ake doke Wladimir Klitschko a sana’arsa ta damben boksin

Yanzu dai ba a taba doke Joshua a damben da ya yi 19 ba. Kuma nasarar da dan damben dan asalin Najeriya mai shekara 27 a gaban yawan ‘yan kallo 90,000 da ba a taba samu ba a Birtaniya tun bayan yakin duniya a babban filin wasa na Wembley, ya kara hada kambin WBA a kan na IBF da yake rike da shi.

Shi ma Fury, mai shekara 28, ba a taba doke shi ba tun da ya fara damben boksin na kwararru, inda ya doke abokan karawarsa 18 a dambe 25.

Amma kuma ya saryar da kambinsa biyu na duniya, domin ya samu dama ya mayar da hankalinsa wajen maganin larurar kwakwalwa da ke damunsa, sannan a yanzu ba shi da lasisin yin dambe.

Tottenham ta ci gaba da bin Chelsea bayan doke Arsenal 2-0


Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

A duk haduwarsu da Arsenal biyar a jere a Premier Harry Kane sai ya ci Arsenal, wadda ya taso daga kungiyar matasan ‘yan wasanta

Tottenham ta ci gaba da bin jagorar Premier Chelsea bayan da Dele Alli da Harry Kane suka zura kwallo biyu a ragar abokan hamayyarsu na arewacin Landan, Arsenal bayan hutun rabin lokaci.

Tottenham na bayan Chelsea da maki hudu yayin da ya rage wasa hudu a gama gasar, bayan da tun da farko Chelsean ta bi Everton gida ta doke ta 3-0.

Nasarar ta wasan na hamayya ta sa a karon farko tun kakar 1994-95 Tottenham za ta gama Premier a saman Arsenal.

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci masu masaukin bakin suka barar da damar kasancewa a gaba a wasan, inda Christian Eriksen da Dele Alli kowannensu ya barar da damar da ake ganin ruwa-ruwa za su ci.

Sai bayan da aka dawo daga hutun rabin lokacin ne a minti na 55 Alli ya ci kwallon wadda ita ce ta 21 da ya ciwa Tottenham a bana.

Dakika 146 tsakanin sai kuma Kane ya ci ta biyu da fanareti, bayan da Gabriel ya yi masa keta ya fadi a cikin da’irar Arsenal.

Kwallon da ta sa Kane ya zama kan gaba a ‘yan wasan Tottenham da suka ci Arsenal, inda yake da shida, yayin da Gareth Bale, da ya koma Real Madrid, yake da biyar.

Arsenal mai kwantan wasa daya ta ci gaba da zama ta shida a tebur, maki shida tsakaninta da ta hudu Manchester City wadda take da maki 66.

Za kayi mamaki idan kaji wanda yayi kokarin kashe Dino Melaye


wp-1493570322032.jpg

– Kwanaki muka samun labarin cewa an yi yunkurin hallaka Sanata Dino Melaye

– Melaye yace an kama wasu cikin masu nema su ga bayan sa

– Ciki har da hannun wani shugaban karamar Hukuma

Kuna da labari kwanaki Sanata Dino Melaye mai wakiltar Jihar Kogi ya sha da kyar.

Sanatan ya bayyana cewa an yi kokarin ganin bayan rayuwar sa.

Jami’an tsaro sun gano masu hannu cikin lamarin.

Saura kiris a aika Sanata Melaye lahira

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Yammacin Kogi yayi da’awar cewa wasu sun kai masa hari a gidan sa da ke Unguwar Ayetoro-Gbede da ke karamar Hukumar Ijumu na Jihar Kogi kwanakin baya.

Wanda wannan ya jawo ‘yan magana tsakanin sa da abokan gaban siyasar ciki har da Gwamnan Jihar Yahaya Bello. Inda Melaye yake cewa Gwamnan ne ke kokarin ganin bayan sa don dama ba su ga maciji.

Yanzu dai mai magana da bakin ‘Yan Sanda Jimoh Mashood kamar yadda ku ka samu labari daga NAIJ.com ya gurfanar da wadanda ake zargi. Abin mamaki dai wani Taofiq Isah ne ya shirya wannan mummunan abu ta hannun wani wai shi Abdulmumuni Iron.

A wancan lokaci Sanata Melaye yace an dauki dogon lokaci ana luguden wuta a gidan cikin tsakiyar dare har yi masa asarar motoci. Rundunar ‘Yan Sanda lallai ta tabbatar da wannan ta kuma shirya bincike.

'Yan sanda sun kama Sule Lamido


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alhaji Sule Lamido ya na daya daga cikin jigajigan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya

‘Yan sanda a jihar Kano dake arewacin Najeriya sun kama tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.

Rahotanni sun ce an kama tsohon gwamnan ne bisa zargin ingiza magoya bayansa don su kawo tarnaki ga zaben kananan hukumomi a Jihar Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru ce ta shirya zaben kananan hukumomin da za a gudanar ranar daya ga watan Yuli.

An kama Sule Lamido ne a gidan shi dake Sharada, Kano da safiyar Lahadin nan.

Har yanzu dau hukumomin ‘yan sandan ba su fitar da sanarwa a hukumace ba game da dalilan da suka ka a ka kama tsohon gwamnan.

Alhaji Sule Lamido, yana daya daga cikin jigajigan ‘ya’yan babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, kuma a ‘yan kwanakin nan, ya yi ta sukar irin kamun ludayin gwamnatin kasar ta jam’iyyar APC.

Mutanen Garin Gulak sun dawo gida bayan an kora Boko Haram


wp-1493570502369.jpg

– Makon jiya Kasar Bangladesh tace za ta taimakawa Najeriya wajen yaki da Boko Haram

– Mutanen da rikicin ya afka da su su na ta dawowa gida

– Gwamnatin shugaba Buhari tayi kokarin wajen kauda ‘Yan Boko Haram

Mutanen Madagali na Jihar Adamawa sun soma dawowa gidajen su.

Yanzu haka an ci karbinn ‘Yan Boko Haram.

Gwamnatin kasar tayi gagarumin kokari wajen yakar ‘Yan Boko Haram.

Kadan daga barnar ‘Yan Boko Haram

Makon jiya NAIJ.com ta kawo rahoto cewa Shugaban hafsun Sojin kasar Bangladesh ya kawo wata ziyara Najeriya inda yace suna da shirin taimakawa Najeriya karashe murkushe ‘yan ta’ddan Boko Haram.

Yanzu haka dai Mutanen Garin Madagali su na ta bikin dawowa gidajen su bayan an ga bayan ‘Yan Kungiyar ta’addan na Boko Haram. Sai dai fa an yi raga-raga da Garin ana sa rai Gwamnati ta kawo wani doki.

Har da dai hawa aka rika yi a Kauyen Gulak inda abin yayi kamari domin murna. Sai da ‘Yan Boko Haram su ka shafe kusan rabin shekara a Garin na Jihar Adamawa da ke makwabtaka da kasar Kamaru.

Chelsea ta fara jin kanshin kofi bayan ta doke Everton 3-0


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Conte na murna da Cesar Azpilicueta bayan wasan, da ya kawo karshen karawarsu 11 ba tare da an ci su ba

Jagorar Premier Chelsea ta kara matsawa kusa da kofin sakamakon kwallo uku na bayan hutun rabin lokaci da ta zazzaga wa Everton a gidanta Goodison Park.

Chelsea ta yi jinkiri da kuma hakuri wajen neman kwallayen wadanda har sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 66 Pedro ya daga ragar masu gidan.

Bayan minti 11 da fara cin sai Cahill shi ma ya zura tasa kafin Willian shi ma ya ci tasa a minti na 86, bayan wata kwallo da Fabregas ya sanya masa.

Nasarar ta sa Chelsea ta kara tazarar da ke tsakaninta da ta biyu Tottenham wadda za ta kara da Arsenal, ita ma a ranar Lahadin, da maki bakwai, inda yanzu take da maki 81 a wasa 34.

Hakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Pedro yana da hannu a kwallo hudu cikin takwas da Chelsea ta ci Everton a Premier bana

Hakan na nufin ko da Chelsea ta yi asarar maki uku a ragowar wasanninta hudu, za ta iya daukar kofin nata na biyu a shekara uku, ko da kuwa Tottenham ta ci dukkanin wasanninta.

Canjasar din da Manchester City ta yi a gidan Middlesbrough na nufin kungiyar ta Ronald Koeman (Everton), a matsayi na 7, tazarar maki 8 ne tsakaninta da rukunin hudun farko, yayin da ya rage wasa uku a gama gasar.

Wasan shi ne babban fatan Tottenham na ganin an ci Chelsea, domin Everton ce ake ganin tafi dukkanin sauran abokan karawarta hudu karfi, yayin da Chelsean za ta yi wasanni uku a gida.

Lissafin mai sauki ne ga Chelsea, domin yadda yake shi ne, idan ta ci karin wasa uku to shikenan za ta dauki kofin a karo na shida.

Kuma daga yadda kociyanta Conte da ‘yan wasansa suka rika murna bayan wasan na Everton, kai ka ce sun ma riga sun dauki kofin, kamar sun gama da Middlesbrough da West Brom da Watford da kuma Sunderland.

Idan kuma har Chelsean ta yi nasara doke Arsenal a wasan karshe na Kofin FA, ranar 27 ga watan Mayu, za a ce Conte ya yi gagarumar nasara kenan a kakarsa ta farko a Ingila.

Harin Madina: Saudiya ta kama mutane 46


Image caption

A karshen azumin watan Ramadanan bara ne aka kai harin a Madina

Saudiya ta ce ta kama mutane arba’in da shida, bayan harin kunar bakin wake da a ka kai a birnin Madina bara.

Akasarin mutanen ‘yan kasar ta Saudiya ne, amma an ce akwai goma sha hudu ‘yan wasu kasashe da suma a ke tsare da su.

Saudiya ta ce mutanen, mambobin wata kungiyar ‘yan bindiga ce da ta kai harin, a inda a ka kashe jami’an tsaro hudu.

A lokacin da a ka kai harin, an dora alhakin shi ne a kan kungiyar IS.

Harin ya auku ne a watan Yulin bara, a karshen azumin watan Ramadana.

Ba dai a san lokacin da a ka yi kamen mutanen ba.

Shugaba Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu – Inji Amaechi


– Ministan harkokin sufuri kuma ya jaddada cewa shugaba Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu a zabe mai zuwa a 2019

– Amaechi ya kara da cewa zai ba shugaba Buhari goyon baya dari bisa dari idan ya fito zai yi takara a zaben 2019

Ministan harkokin sufuri kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, daya daga cikin jihohin masu arzikin man fetur a yankin Neja Delta, Rotimi Amaechi, ya yi imani shugaba kasa Muhammadu Buhari nada isashen lafiyar takara karo na biyu a 2019.

Ministan ya yi wannan bayyana ne ganin an dauki lokaci ana kace-nace game da batun lafiyar shugaban tarrayar Najeriya da ke kara nuna alamu na kauracewa bainar jama’a. Daga dukkan alamu rudanin yana shirin kara karuwa bayan share tsawon wannan mako ba tare da ganin shugaban a cikin jama’a ba.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya kauracewa halartar taron majalisar kasar na mako-mako cikin tsakiyar wannan mako dai, bangaren gwamnatin na kafa hujja ne da zabi na shugaban na yin aiki ko dai daga kuryar daki ko kuma a cikin ofishin da gwamnatin kasar ta gina domin aikin nasa.

Shugaba Buhari na gaisawa da Rotimi Amaechi

A lokacin da aka tambaye ministan cewa zai iya goyi bayan shugaba Buhari idan ya sake tsayawa zabe a 2019, Amaechi ya ce: “Zan ba shi goyon bayana dari bisa dari”.

Shugaba Buhari dai ya yi bayyanarsa ta karshe a bainar jama’a ne a ranar Juma’ar makon jiya a massalacin fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock

Masu sana'o'i a birnin Kumasi


A ranar 6, ga watan Mayun shekarar 1957, kasar Ghana wacce a baya aka santa da cinikin zinare, ta samu ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya.

A bikin cika shekara 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, wani mai daukar hoto, Ricky Darko ya yi duba da garin da aka haife shi wato Kumasi, a kudancin kasar, don nuna ire-iren ayyukan da matasa suke da damar samu a lokacinsa.

Hakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Birnin kumasi da ke Ghana

A lokacin da Darko ke bikin cika shekaru 30 da haihuwarsa, ya kira samari sa’anninsa da su fito su dauki hotuna a wuraren da suke aiki.

Ya hadu da abokan nasa a ranakun da suke gudanar da aikinsu, inda ya tarar da kowanne yana da fannin da ya kware a sana’arsa, wanda yawanci sun gada ne daga wurin iyaye da kakanni.

Daga cikin kanikawan da suke aikin kere-kere, yawancin mazan suna aiki tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta, cikin zafin rana da ya kai maki 35 na ma’aunin Selsiyos.

Darko ya ce, yadda suke gudanar da rayuwarsu sai san barka.

ya ce, suna yin aikinsu da kwazo na tsawon sa’o’i a cikin yanayin zafi amma ba tare da yin korafi ba.

David yana daya daga cikin samarin da ya ci karo da su.

Ya zagaya cikin Kumasi yana yin ayyuka daban-daban tun daga kwashe bola zuwa kai ruwa gidaje.

David,mai kaya a KumasiHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

DavidYa zagaya cikin Kumasi yana yin ayyuka daban-daban

Kwame ya leko waje ta tagar motar da yake ciki mai launin azurfa, wacce ake aikin da ita a gidan attajiran da yake yi wa aiki.

A wannan ranar ne, zai dauki iyalansa don ziyartar abokai, sannan su wuce kasuwa su sayi kayan masarufi don amfanin yau-da-kullum.

Kwame na zaune a motarsaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Kwame ya leko waje ta tagar motar da yake ciki mai launin azurfa

Kumasi, GhanaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Ghana wacce a baya aka santa da cinikin zinare,

Nana Kwasi da ke zaune a kan Bonnet din motarsa, ya shaida wa Darko cewa yana biyan kudin balas na hayar motarsa a kan cedi 40 na kudin Ghana a kowacce rana.

Sannan ya zagaya cikin garin Kumasi, dan ya yi kokarin samun isasshen kudin da zai tallafa wa iyalansa.

Wani na tsaye kusa da motarsaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Nana Kwasi da ke zaune a kan Bonnet din motarsa,

Akwasi na tsugune a kusa da kofofin karfe da ya kera.

Garejinsa na kusa da gidaje, kuma yana aikin waldan kayayyaki daban-daban da ‘yan kasar Ghana ke amfani da su.

AkwasiHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Akwasi na tsugune a kusa da kofofin karfe da ya kera.

wani mai aikin waldaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Wani mai aikin walda

Francis na waldar kofaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Francis na aikin waldar karafuna

Francis yana aikin ne a matsayin mai sayar da kayayyakin cimaka, galibi ya fi sayar da alewa a kan titinan cikin gari da motoci suke yawan wucewa.

Ya ce, Suna gudanar da cikakkiyar rayuwarsu kuma duk lokacin da suka ganni suna min dariya, a matsayi na na wanda nake kokarin yin magana da harshen Twi (wani yare ne a harshen Aka, wanda yawancin ake magana da shi a kudancin Ghana).

Darko ya ce, ina jin harshen ba dadi, idan na cakuda shi da kalmomina.

FrancisHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Wani saurayi

Wadannan samarin ‘yan uwan juna ne ke zaune a kofar shagonsu, inda suke sayar da kayayyakin amfanin gida.

Yaw daga hagu, Poku a dama, suna gudanar da harkokin cinikinsu na tsawon sa’o’i 16 a rana.

Two men sit outside a stallHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Yaw (daga hagu), tare da Poku, suna zaune a shagonsu

A roadside hut in Kumasi, GhanaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Wasu kayayyaki a Kumasi.

Emmanuel na aiki dare da rana a matsayin mai gadin wasu kayayyaki a Kumasi.

A karshen mako ne kawai, yake samun sa’o’i uku, don ya zauna tare da iyalansa.

Emmanuel, mai gadiHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Emmanuel na aiki dare da rana a matsayin mai gadi

Michael na sayar da katin waya, a cikin wani dan akwati da aka kera da katako, da ruwan leda a cikin kula.

Michael, mai sai da katin wayaHakkin mallakar hoto
Ricky Darko

Image caption

Michael na sayar da katin waya

Dukkan wadannan hotunan mallakar Ricky Darko ne.

Swansea ta yi wa Man United fancale


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gylfi Sigurdsson ya ci wa Swansea kwallonsa ta farko tun watan Fabrairu

Swansea ta samu maki a fafutukar da take yi ta tsira a gasar Premier ba, yayin da kuma ta yi wa mai masaukinta Manchester United cikas kan neman shiga hudun farko da take yi, inda suka tashi 1-1.

Gylfi Sigurdsson ne da bugun tazara ya ci wa bakin kwallonsu a minti na 79, ya rama fanaretin da Wayne Rooney ya ci ana dab tafiya hutun rabin lokaci, wadda ‘yan Swansea suka yi korafi da cewa Marcus Rashford faduwa ya yi da gangan, ba keta aka yi masa ba.

Sakamakon ya sa yanzu maki biyu ne tsakanin Hull City ta 17 mai maki 34, da Swansea ta 18.

Man United ta cigaba da zama ta biyar, da maki 65 maki tsaya tsakaninta da abokiyar hamayyarta Man City ta shida da maki 66, wadda da ta yi canjaras 2-2 da Middlesbrough yau Lahadi.

Bayan makin da United ta yi asara a gidan nata ta kuma gamu da matsalar rasa karin ‘yan wasanta da suka ji rauni, inda a wannan karon ta rasa Eric Bailly da Luke Shaw, bayan daman ‘yan bayanta Phil Jones da Chris Smalling da Marcos Rojo suna jinya.

Shugaban NIA yana cikin wani mawuyacin hali


wp-1493563070341.jpg

– Kwanaki Shugaba Buhari ya dakatar da shugaban NIA

– Shugaban kasa ya bada umarni a hukunta duk wanda aka samu da laifi

– Shugaba Buhari yace shugaban NIA bai sanar da shi game da wadannan makudan kudi ba

Ana nan ana binciken shugaban Hukumar NIA na kasa.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya gayyaci shugaban Hukumar NIA din da aka dakatar.

Sai dai fa da alamu yana cikin matsala.

Shugaban NIA ai sanar da mu ba-Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban NIA na kasa watau Ambasada Ayo Oke bai taba sanar da shugaba Muhammadu Buhari game da wannan makudan kudi da aka samu na Hukuma NIA din a wani gida a Legas ba.

Haka kuma fadar shugaban kasar tace mai ba shugaba Buhari shawara game da harkokin tsaro Janar Babagana Munguno mai ritaya bai taba jin labarin ba. A baya dai an yada cewa Babagana Munguno watau NSA ya san da batun.

Kuna dai da labari cewa ana tuhumar Ambasada Oye Oke da kin bayani game da wasu makudan kudi kusan Naira Biliyan 15 da hukumar sa ta ajiye tun lokacin shugaba Jonathan da sunan wani aiki da za a yi sai dai shugaban kasa bai sani ba.

Majiyar mu ta bayyana cewa shugaban kasar ya bayyana cewa ka da a saurara ko a dagawa wani kafa wajen binciken. Ana dai zargi kudin na sha’anin kamfe ne aka karkatar da sunan harkar tsaro lokacin shugaba Jonathan.

Dan kasar Najeriya ya ci kanbun damben Duniya


wp-1493563227998.jpg

– Wani asalin dan Najeriya ya doke Klitschko a wasan dambe

– Yanzu haka ya karbi kambun damben Duniya

– Wladmir Klitschko ya sha kashi

A wani wasan damben Duniya da aka yi a Kasar Ingila.

Wani ainihin Dan Najeriya ne yayi nasara.

Wannan dai abin farin ciki ne ga ‘Yan kasar da kuma daukacin bakaken Mutanen Afrika baki daya.

Dan kasar Najeriya Joshua ya bar tarihi

Anthony Joshua ya gabje Wladmir Klitschko a damben Duniyar da aka gwabza a filin wasa na Wembley da ke Birnin Landan inda mutane kusan 90, 000 su ka hallara gudun a gani a bas u labari.

Yanzu haka Joshua wanda asalin sa Dan kasar Najeriya ne ya karbe kanbun damben Duniyar na Heavyweight inda ya zama zakara bayan ya tika Zakaran Duniya Wladmir Klitschko da kasa a kusan zagaye na daf da karshe.

Kuna da labari kwanaki Sanata Dino Melaye mai wakiltar Jihar Kogi ya sha da kyar. Sanatan ya bayyana cewa an yi kokarin ganin bayan rayuwar sa inda aka kai masa har gida cikin tsakar dare.

Na gargaɗi Jonathan kan makircin 'yan Arewa – David Mark


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mr Mark [daga dama] ya ce ya yi mamakin yadda Jonathan ya kasa gane makircin da ake shiryawa

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark ya ce ya gargadi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan irin makircin da ‘yan arewacin kasar ke shiryawa domin kayar da shi a zaben 2015.

Mr Mark, wanda ya bayyana hakan a littafin Against the Run of Play, wanda fitaccen mai sharhin nan na jaridar ThisDay Olusegun Adeniyi ya wallafa, ya ce da gangan jam’iyyar PDP, a karkashin Ahmad Adamu Mu’azu ta gaya wa Mr Jonathan cewa zai lashe zaben bisa dogaro da hasashe kan tsarin kada kuri’ar da ‘yan arewacin kasar za su yi.

A cewarsa, “Na tsinkayi faɗuwar sa [Jonathan] zaben kuma na nuna masa hakan, sannan na bayyana masa cewa hasashen da wasu mutane da ke kusa da shi suka yi kan tsarin kada kuri’ar da za a yi a Arewa ba daidai ba ne.”

“Na gane makircin da aka kitsa da kuma taron dangin da aka yi a Arewa domin ganin Jonathan bai cimma burinsa ba amma ba sarkin yawan ya fi sarkin karfi, domin wadanda ke kusa da shi na ganin babu yadda shugaban kasa da ke kan mulki, kuma a jam’iyyar PDP ya fadi a zabe,” in ji Mr Mark.

Tsohon shugaban majalisar ta dattawan Najeriya ya ce wasu mutane sun rika yaudarar Mr Jonathan suna gaya masa cewa ba zai sha kaye a zabe ba kuma mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo ya gane cewa yaudarar tsohon shugaban kasar ake yi “amma ban san irin tasirin da yake da shi a yakin neman zaben ba. Kuma har yanzu ian matukar mamakin yadda Jonathan ya kasa gane cewa ana yaudararsa har sai da lokaci ya kure”.

Mr Mark ya ce Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience ne suka sa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal bijire musu saboda wulakacin da suka rika yi masa.

A cewarsa, sun yi zaton shi da Tambuwal na son yin takarar shugabancin kasar a shekarar 2015, amma “na gaya wa Jonathan ni da shi cewa duk wadanda ke ba shi irin wadannan labaran karya suke yi.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau hudu Mr Mark ya zama dan majalisar dattawa

Zan faɗi gaskiya abin da ya faru

Shi dai tsohon shugaban na Najeriya ya ce tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ne suka sa ya sha kaye a zaben 2015.

Mawallafin littafin ya ambato Mr Jonathan na cewa Shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama da jami’an gwamnatinsa sun bayyana masa ƙarara cewa suna son sauyin gwamnati a Najeriya kuma za su iya yin komai domin cimma hakan.

A cikin gida kuma, tsohon shugaban ya ce shugaban hukumar zabe na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya yi masa abin da bai yi tsammani ba, saboda har yanzu nan ya kasa fahimtar abin da ya sa Jegan ya nace cewar ya shirya wa yin zabe lokacin da kashi 40% bisa dari na masu zabe ba su karbi katinsu na zabe ba.

Ya ce ya gana da shugaban hukumar zabe ya bayyana masa damuwarsa kan yi zaben a watan Fabrairun 2015, amma ya kafe cewar ya shirya wa zaben domin Amurkawa sun ingiza shi abin da ba za taba yi a kasarsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Goodluck Jonathan ne shugaba mai ci na farko da ya fadi zabe a Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya musanta wannan zargi, yana mai cewa zaben da aka yi shugaba Muhammadu Buhari zabi ne da nuna abin da ‘yan Najeriya ke so.

Shi ma tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya ya musanta hakan, inda ya ce na’urar tantance zaben da aka yi amfani da ita a 2015 ta hana kowanne irin magudi.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya ce zai buga littafin da zai fayyace gaskiyar abin da ya sanya shi faduwa zaben shekarar 2015.

Bayan ƙara kyau, ko dashen mama na da wata illa?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akan yi amfani da roba ko balan-balan ɗin silicon don mayar da tsohuwa yarinya

Dashen mama, nau’in kwalliyar mata ce ta cikin jiki da ya fara samun wajen zama a ƙasashe kamar Nijeriya, don kuwa su ma ba sa so a ga tsufansu.

Mata kan yi wannan kwalliya ce ta yadda za a riƙa ganinsu gwaɗas da ƙuruciya, bayan ƙara burgewa da jan hankali.

Tun tale-tale, mata sun shahara wajen son gyaran jiki, a cancanɗa gayu don kyaun gani da kuma fita kunya.

A baya Turawa aka sani da kwalliyar dashen mama, kafin yanzu da take ƙara bazuwa a duniya.

Matan Nijeriya, ‘yan ƙwalisa ne masu son su jera da zamani, ga kuma son tsere sa’a, kuma ba sa son a ga tsufansu.

Shin yaya ake dashen mama?

Wani ƙwararren likitan fida, Dr. Sa’ad Idris ya ce fiɗa ake yi nono, a tsarga shi don yi masa ƙari ko ciko.

Ana amfani da wani abu mai kama da balan-balan, inda ake sanya ta daidai da surar maman.

Shi wannan abin mai kama da balan-balan ana kiransa Silicon da kuma wani sinadari mai alaƙa da gishiri da ake zuba shi a cikin balan-balan ɗin silicon.

Akan yanka ƙoramu ko jijiyoyin da suka haɗa kan nono da sauran gangar jiki.

Ko mai dashen mama na iya shayarwa?

Dr. Sa’ad Idris ya ce binciken da aka yi, ya nuna cewa likitoci ba su cika ba wa wadda ta yi dashen mama shawarar ta shayar da jariri ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mata kan kashe maƙudan kuɗi don ganin sun yi wannan kwalliya ta burgewa

“Yanka ƙoramun nono da aka yi, kan sa ruwan nono zai janye.”

Haka zalika, sinadaran da aka zuba a cikin balan-balan ɗin silicon a wasu lokuta ka iya tsiyaya, kuma idan jariri ya sha, suna iya illata shi.

Ko dashen mama na da wata illa?

Dr. Sa’ad Idris ya ce dashen mama kamar kowacce irin tiyata, ta jiɓanci yanka jikin mutum da kuma ba da maganin kashe kaifi.

A cewar likita hakan na da matsaloli, don kuwa wasu idan suka kwanta, ba lallai ne su sake tashi ba, idan an gamu da matsala.

Haka kuma “akan iya samun jini ya tattaru a wurin da aka yanka, ballantana inda aka sanya balan-balan ɗin silicon.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu irin wannan dashen mama ya bazu a duniya

Ko yaushe mace za tai ta jin ciwo ga mamanta bayan an yi dashe.

“Maimakon ma a gyara…(ƙirjin mace ya zama cas a tsaye) ƙila ɗaya ya fashe,” in ji likita.

A cewarsa (fatar) nonon ka iya canza launi, ko kuma girmansa ya ragu.

Sai dai a iya sanina da kuma binciken da muka yi, “ban ga inda aka alaƙanta dashen mama da cutar sankara ba, in Dr. Sa’ad Idris.”

Barca na ci gaba da jan zarenta a La Liga


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lius Suarez ya ci kwallayensa ne saboda kuskuren da ‘yan wasan Espanyol suka yi

Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta rike matsayinta na kasance a gaba a gasar La Liga inda Lius Suarez ya ci kwallo biyun da suka sa ta yi nasara kan Espanyol.

Burin Barcelona na daukar kofi ya fuskanci koma-baya a zagayen farko, bayan Real Madrid ta samu maki uku lokacin da ta doke Valencia ranar Asabar inda ta matsa gaba.

Jose Manuel Jurado ya yi kuskuren buga wata kwallo, wacce Suarez ya samu, sannan ya doka ta cikin raga.

Image caption

Barca na ci gaba da jan zarenta

Ivan Rakitic ya zura kwallo ta biyu sannan Suarez ya kara samun damar wurga kwallo a raga bayan Espanyol sun sake yin kuskure.

Yanzu Real da Barca na da maki daidai wadaida sai dai Barca na gaba da yawan kwallaye.

Amma Real za ta dauki kofi idan ta ci dukkan wasanni hudu da suka rage mata.

Sakamakon wasan bana ya girgiza 'yan wasan Arsenal – Wenger


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wenger ya ce ‘yan wasansa sun kaɗu

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce wasu daga cikin sakamakon wasannin da aka yi a kakar wasa ta bana sun “girgiza” ‘yan ƙwallonsa, sai dai ya dage cewa a shirye ƙungiyar take ta fafata da Tottenham ranar Lahadi.

Arsenal su ne na shida a teburin gasar Premier kuma suna bayan Manchester City, wacce ke mataki na huɗu, da maki shida ko da yake suna da sauran wasa shida da za su gwabza.

Wenger ya bayyana kashin da suka sha a hannun Bayern Munich da ci 5-1 a watan Fabrairu da kuma dokewar da Chelsea ta yi musu da ci 3-1 a matsayin “babban koma-baya.”

Ya ce “Mun zama kawar wani ɗan dambe wanda aka kayar amma ya tashi sau biyu. Mun sha kashi amma mutane sun fassara hakan a matsayin abin da ba su damu da shi ba.”

Kocin, mai shekara 67, ya kara da cewa “Watakila saboda sun damu sosai ne shi ya sa muka kaɗu sosai. Mun yi matukar kaɗuwa.”

“Ina ganin ‘yan wasan sun damu. Suna da kwazo. Ina son yadda suke nuna halayensu. Muna cikin yanayi mai kyau idan ka kwatanta da wata daya zuwa biyu da suka wuce,” in ji Wenger.

A cikin wasanni 49 da Wenger, Arsenal ta yi nasara a 22, ta yi kunnen-doki a 20 sannan ta sha kaye a bakwai, amma ba ta doke Tottenham ko da sau daya ba a wasannin lig guda biyar da suka fafata.

Mauricio Pochettino shi ne kocin Tottenham na farko da ba a doke ba a gasa biyar da ya buga.

An damke wadanda sukayi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye


– An damke mutane 6 game da kisan sanata Dino Melaye

– Daga cikin wadanda aka kama wani shugaban karamar hukuma ne da kuma dan sanda

Bisa ga yunkurin kisan Sanata Dino Melaye kwanakin baya, hukumar yan sanda Najeriya ta damke mutane 6 a yanzu.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa daga cikin wadanda aka kama shine shugaban karamar hukumar Ijimu ta jihar Kogi, Taofiq Isah.

Sunayen wadanda aka kama shine Taofiq Isah, 54, James Ede, 36, Ade Obage, 29, Abdullahi Isah,32, Ahmed Ajayi, 45, da Michael Bamidele, 26.

Kakakin hukumar yan sandan tarayya, Jimoh Moshood, wanda yayi magana da manema labarai yaci an kwace wata motar asibiti, bindigar AK47 guda 5, bindigar gargajiya 2, carbin harsasai 25 da sauran su.

An damke wadanda sukayi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye

Moshood yace: “ An aika makaman dakin gwaji domin gwada su a ofishin ilimi da leken asirin hukumar da ke Legas.”

Moshood ya kara da cewa daya daga cikin wadanda suka kai harin Obage ne ya kaow kara ofishin yan sanda . amma har da shi aka kama kuma ana gudanar da binciken rawan da ya taka a harin.

Yace: “Obage ne ya zo ya bayyanawa yan sanda cewa yanada masaniya game da wadanda suka sukayi kokarin kashe Sanata Dino Melaye bayan sun kai harin.

”Kana ya sanar da yan sanda cewa shugaban makasan , Abdullahi Eko ne ya gayyacesa kuma shima yana hannu.”

Costa ne gwarzon ɗan wasan gaba na duniya – Conte


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Diego Costa ya zura kwallo 19 a gasar Premier ta bana. Da ce bai zura su ba, da Chelsea ta rasa maki 15

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce Diego Costa shi ne ɗan wasan gaban da ya fi kowanne iya murza leda a duniya.

Chelsea, wacce ke kan gaba a gasar Premier za ta je gidan Everton ranar Lahadi, inda za su yi karon-batta da Romelu Lukaku, dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar Premier ta bana.

Dan kasar ta Belgium, Lukaku, mai shekara 23, ya zura kwallo 24, yayin da shi kuma Costa, dan kasar Spain mai shekara 28, ya ci kwallo 19.

Conte ya ce, “Lukaku yaro ne mai gwaninta amma a wurinmu Diego yana da matukar muhimmanci, kuma shi ne ke share mana hawaye a bana.”

“Muna magana a kan ‘yan wasan gaba biyu mafiya iya taka leda. Amma, a wuria, Diego shi ne gwarzon dan wasan gaba a duniya,” in ji Costa.

Kocin na Chelsea ya kara da cewa “Ina ganin yana da matukar basira. Amma abin da na fi ƙauna shi ne yadda dan wasan zai nuna shi gwarzo a lokacin da yake murza leda, fiye da haka kuma, idan ‘yan wasa haziƙai suka nuna basirarsu ta yin aiki tuƙuru lokacin wasa.”

Madallah! Albishirin ku fulanin Najeriya, sako daga Gwamnatin Buhari (Karanta)


wp-image-1868015148jpg.jpg

– Hukumar ilmantar da yayan Fulani makiyaya ta kasa ta kaddamar da shirin ziyarar gani da ido makarantun yayan Fulani makiyaya a shiyyar arewa maso yamma.

– Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Alhaji Muhammad Dan-Iya Faty ya sanar da hakan jim kadan da rangadin wasu makarantun yayan Fulani makiyaya.

Yace shi da jami’an hukumar 29 an turo su jihar Jigawa domin gudanar da shirin na kwanaki 12.

Alhaji Muhammad Dan-Iya Faty yace makasudin shirin shine ganin halin da makarantun suke ciki akwai da kuma irin cigaban da ilmin yayan Fulani makiyaya ya samu da kuma akasin hakan.

NAIJ.com ta tattaro cewar yace ana gudanar da shirin ne a makarantun yayan Fulani makiyaya 281 dake shiyoyin Dutse da Birnin Kudu da Kafin Hausa da Hadejia da Kirkasamma da Kazaure da Gumel da kuma Ringim.

Daraktan ya kara da cewar shirin zai shafi dalibai dubu hudu da suka kammala karatu a makarantun yayan Fulani makiyaya na sassan jihar.

Yace bankin raya kasashen afirka ya tallafawa hukumar da cibiyoyin koyan sanaoi biyu dake Kachia a jihar Kaduna da kuma ta Abuja domin amfanin makiyaya.

,

Mutan Arewa sun fara maganganu game da rashin lafiyan Baba Buhari, musamman Katsinawa


-Mutanen jihar Katsina sun bayyana ra’ ayoyinsu game da rashin lafiyan shugaba Buhari

-Kowa dai na nuna tsoronsa idan Allah ya kaddara abinda ba’a so ya faru

Ko shakka babu rashin lafiyan shugaban Muhammadu Buhari na tayar da hankalin mutane musamman yan jiharsa ta Katsina.

Abdulrasheed Funtua, malami a wata jami’a a Katsina yayi kira ga mutane su taimakawa shugaban kasa da addu’ a.

Yace: “ Rashin lafiyan shugaba Muhamadu Buhari kaddara ne kuma rashin lafiya ba mutuwa bane. Ka dauki misali da mutuwan sanata Adeleke, bai yi rashin lafiya ba amma ya mutu. Saboda haka kaddara ne kuma babu abinda amu iya yi face addu’ a ga shugaba Buhari.”

Mutan Arewa sun fara maganganu game da rashin lafiyan Baba Buhari, musamman Katsinawa

Wani mazaunin Kankia, Ustaz Idris, yace akwai tsoro tattare da rashin lafiyan shugaban kasa saboda irin wahalan da muka sha bayan mutuwan shugaba Yar’ adua da Jonathan ya hau mulki.

Yace: “ Kawai addu’an da mukeyi shuine shugaba Buhari ya samu lafiya kuma ya karasa mulkinsa mai kyau kamar yadda ya fara.” Idris yace.

Shugaban wata kungiyar fafutuka wato Accountability and Good Governance Initiative, Lawal Saidu Funtua, shima ya bayyana irin wannan ra’ayin musamman bayan jihr Katsina tayi rashin Umaru Musa Yardaua a irin wannan hali.

Yayi addu’a ubangiji ya baiwa shugaban kasa lafiya ya karashe ayyukan da ya fara yi musamman na yaki da rashawa saboda kada a fuskanci ci baya.

Shi kuma a bangaren sa, shugaban jam’ iyyar National Conscience Party, NCP,shiyar jihar Katsina, Shehu Sani yace kawai shugaba Buhari yayi murabus.

Noma tushen arziki: Manoma a Arewa suna ci gaba da keta hazo suna sauke farali


wp-1493538373022.jpg

– Hukumar kula da jindadin mahajjatan jihar Taraba ta sanar da cewa sama da kashi 90 na maniyyata aiki hajjin bana daga jihar Taraba manoma ne.

– Babban sakataren hukumar Umar Leme ya ce manoma sun biya sama da naira miliyan 900 ga hukumar kafin gwamnati ta fadi ainihin kudin aikin hajji na bana.

Leme ya ce hakan yana da nasaba ne da irin dimbin amfanin gona da manoma suka samu a damunan bara.

“Hukumar ta kama wa maniyyatan jihar gidaje kusa da harami sannan gwamnatin tarayya ta ba jihar kujeru 1, 457 amma jihar na kokarin ganin an dan kara mata kafin lokacin tafiya.”

NAIJ.com ta samu a wani labarin kuma cewa Tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yana bin kadin ɓata-suna da ‘yan sandan ƙasar suka yi masa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata takarda da ke alaƙanta Shekarau da kashe Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.

A cewarta jami’anta ne suka gano takardar bayan wani samame da suka kai gidan sanata Danjuma Goje a Abuja.

Mai magana da yawun Shekarau, Malam Sule Ya’u Sule ya ce ba shakka suna bin bahasin wannan batu a wajen ‘yan sanda.

Hotunan Afirka a makon da ya gabata


Wasu daga cikin kyawawan hotunan Afirka da kuma wasu ‘yan Afirka a ko ina a duniya.

Hakkin mallakar hoto
Tamasin Ford

Image caption

Wasu matasa ‘yan gayu daga DR Congo da Ivory Coast sun taru ranar Talata domin tunawa da mawaki Papa Wemba wanda ya mutu a bikin wakokin Femua a Abidjan shekarar da ta gabata

SapeursHakkin mallakar hoto
Tamasin Ford

Image caption

Shi ne sarkin masu gayu, kuma shi ne ya samar da hadaddiyar kungiyar masu gayu.

Dan gayuHakkin mallakar hoto
Tamasin Ford

Image caption

Dole dan gaye ya yi kwalliya da kyau, ya sanya kaya masu daukar hankali, su kuma sanya turare, su kuma gyara gashinsu.

Wata mata ke jiran masu saen kaya a titi streetside boutique a tsakiyan birnin cibiyar kasuwancin kasar wato LagosHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wata mata kenan take sayar da gwanjon singileti, ke jiran masu saya a wata kasuwa da ke birnin Lagos ranar Laraba

Wani matashi kenan, ke tura Wul baro a kan titin OkepopoHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani matashi kenan, ke tura Wul baro a kan titin Okepopo da ke birnin na Lagos.

Wata a tsaye cikin shagon ajiye kayan tarihin KiristociHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wata mata ke zaune a wani shagon sayar da kayan tarihin Kiristoci lokacin ziyarar Fafaroma Francis zuwa birnin Alkahira, ranar Asabar.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (Hagu)Tare da Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ke wuce wani Abun girmamawaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (Hagu)Tare da Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ke wuce wani abun girmamawa lokacin wata tarbar ziyara a birnin Ankara, da ke Turkiyya.

Wani mai tura Wul baro ke dakon wasu mayan robobi zuwa shagon mai sayar da suHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani mai tura Wul baro ke dakon wasu mayan robobi zuwa shagon mai sayar da su a wajen birinin Nairobi da ke kasar Kenya.

Mai goyon bayan jam'iyyar adawa aHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani mai goyon bayan Jam’iyyar ‘Orange Democratic Party’ a Kenya lokacin da aka kaddadamar da Raila Odinga a matsayin dan takarar hadin gwiwar Jam’iyyun adawa

Hotunan na kamfanonin dillancin labaran AFP, EPA, Getty Images and Reuters ne.

Mene ne ke damun jam'iyyar APC?


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kakakin APC ya ce kan ‘yan jam’iyyar a haɗe yake

Tun bayan da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta lashe zaɓen shekarar 2015, masana harkokin siyasa ke cewa ta yi abin da hausawa ke cewa samun duniyar ɗan tsako: ba samun ba, inda za a zauna a ci.

Sun kuwa bayyana haka ne ganin cewa, ba kamar jam’iyyar PDP ba wacce aka kafa da zummar bin turbar dimokraɗiyya ba, akasarin ‘yan jam’iyyar APC haɗin gambiza ne: ‘yan tsohuwar jam’iyyar CPC irin su Shugaba Muhammadu Buhari, da na tsohuwar jam’iyyar AC, kamar su Bola Tinubu da kuma waɗanda zama a jam’iyyar PDP ya yi wa zafi, irinsu tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

A cewar Dr Abubakar Kari, na Sashen koyar da kimiyyar siyasa a Jami’ar Abuja, babban ƙalubalen da APC ke fuskanta shi ne na rashin haɗin kan ɓangarori daban-dana da suka kafa ta.

Ya shaida min cewa “Babbar matsalar jam’iyyar APC ita ce har yanzu ba ta zama jam’iyya ta dunƙule wuri ɗaya ba; har yanzu gungu-gungu na ‘yan jam’iyyu daban-daban ne irinsu tsohuwar jam’iyyar ACN da CPC da kuma tsohuwar PDP. Babu wanda yake kallon APC a matsayin jam’iyya, kuma hakan ne ya sa ake fuskantar manyan matsaloli a jam’iyyar.”

Shi ma Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma ƙusa a jam’iyyar PDP mai hamayya, ya gaya wa BBC cewa APC jam’iyya ce ta mutanen da suka yi fushi, waɗanda ba su da wata kyakkyawar manufa sai dai “cin mutuncin jama’a.”

Sai dai kakakin jam’iyyar ta APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya shaida min cewa: “APC jam’iyya ɗaya ce da ke da manufa guda: kawo ci gaba a Najeriya. Haka kuma kan ‘yan jam’iyyar a haɗe yake, ko da yake ba za a rasa ‘yar rashin jituwa tsakanin wasu ba, amma haka mulkin dimokraɗiyya ya gada.”

Wani babban batu da ya nuna cewa zama ake irin na gidan haya a APC shi ne yadda tun da aka zo zaɓen shugabannin majalisar dokokin tarayya ‘yan jam’iyyar ta APC suka ƙi zaɓar mutanen da jam’iyyar ta tsayar, abin da Dr Kari ya ce ya dasa dambar rashin jituwa tsakanin manyan ‘yan jam’iyyar.

Wasu dai na ganin hakan ba ya rasa nasaba da alwashin da Shugaba Buhari ya sha ba na barin kowanne bangare ya ci gashin kansa ba tare da katsalandan ba.

Sai dai wasu masu sharhin na ganin karan dimokraɗiyyar Najeriya bai kai tsaikon da shugaban ƙasa zai ƙi sanya hannu a sha’anin wasu ɓangarorin ba, musamman ganin cewa duk abin da ya faru a wani ɓangaren, kai-tsaye zai shafi wasu ɓangarorin.

Da alama masu wannan ra’ayi na da hujja domin kuwa shurun da Shugaba Buhari ya yi kan al’amuran da ke faruwa a majalisar dokoki da kuma jam’iyyarsa ta APC har sai da lokaci ya kusa ƙurewa ya sa al’amura sun riƙa rincaɓewa a ƙasar.

An yi ta samun rigingimu tsakanin shugaban jam’iyyar Cif John Odigie-Oyegun da wasu jiga-jiganta irinsu Bola Ahmed Tinubu a kan zaɓukan jihohin Kogi da Ondo, lamarin da ya har ya kai su yin fito-na-fito a kafafen watsa labaran ƙasar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Buhari ya kayar da Atiku a zaben fitar da gwani na APC

Shi kansa tsohon mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar sai da ya tsoma baki a cikin rigimar inda ya nuna goyon bayansa ga Mr Tinubu.

Bayan faruwar wannan lamari ne, wanda har yanzu wasu ke ganin tsugune ba ta ƙare a kansa ba, wasu rahotanni suka nuna cewa manyan jami’an na APC cikinsu har da shi Ahmed Tinubun da Atiku Abubakar na shirin kafa sabuwar babbar jam’iyya, zargin da suka musanta.

Babban taro ya gagara

A can jihar Adamawa ma, mahaifar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, an ambato wasu shugabannin jam’iyyar APC na cewa babu wanda za su mara wa baya a zaben 2019 idan ba Atiku Abubakar ba.

Kazalika wasu ‘yan kasar na ganin hatsaniyar da ke faruwa tsakanin ‘yan majalisar dattawa da ɓangaren zartarwa kan wasu batutuwa na da nasaba da hanƙoron da shugaban majalisar Bukola Saraki ke yi na tsayawa takara a 2019, ko da yake ya shaida wa BBC cewa “yanzu ba lokacin siyasa ba ne.”

Sau da dama APC na shirya gudanar da babban taro amma hakan ya ci tura.

Ko da a baya bayan nan, an shirya yin taron ranar 24 zuwa 25 ga watan nan na Afrilu amma shuru kake ji tamkar an aiki bawa garinsu.

Sai dai Malam Bolaji Abdullahi ya shada min cewa an riƙa ɗage taron ne “saboda wasu dalilai na tsare-tsare.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bola Tinubu ( na dama) ya taka muhimmiyar rawa wajen yin nasarar APC

“Tun da muka kafa jam’iyyar nan muka amince cewa ba za mu riƙa yin amfani da kuɗin gwamnati wajen gudanar da ita ba; sai dai mu riƙa samun gudunmawa daga ‘yan jam’iyya shi ya sa ake samun matsala wurin kiran taron. Na biyu kuma akwai matuƙar wahala bakin kowanne ɗan jam’iyya ya zo ɗaya a kan lokacin da za a gudanar da taron. Don haka wanna ba batu ne na samun matsala a jam’iyya ba,” in ji Mallam Bolaji Abdullahi.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin rashin gudanar da babban taron jam’iyyar na da alaka da barakar da ke tsakanin wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Dr Kari ya ce, “Rashin gudanar da tarukan jam’iyya ya sa ana samun rauni a cikinta; kuma saboda halin ko in kula da ake nuna wa jam’iyyar shi ya sa ba a tuntubarta a al’amuran da suka shafi gudanar da gwamnati, hakan ne ma ya sa kake ganin dukkan naɗe-naɗen da shugaban ƙasa ke yi wasu ‘yan tsiraru ne ke yi, ba a la’akari da irin rawar da wasu suka taka wajen cin zaben wannan gwamnatin.”

Sai dai fadar shugaban ta sha musanta cewa ba ya tuntuɓar jam’iyyar, suna masu cewa babu wata matsala tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar.

A cewarsa, matakin farko da APC za ta ɗauka domin shawo kan matsalolin da ke addabarta shi ne: ta dauki kwararan matakai na hadan kan ‘ya’yanta da kuma sakin mara ga ɓangarorin jam’iyyar irinsu kwamitin amintattu, babban kwamitin zartarwa na kasa, kwamitin gudanarwa da kuma rassanta na jihohi.

Masanin kimiyyar siyasar ya ƙara da cewa dole Shugaba Buhari ya fahimci akwai buƙatar ya tsaya tsayin daka wajen ci gaban jam’iyyar, ko da ba zai sake yin takara ba “domin kuwa ko ba komai ita ce dokin da ya hau ya zama shugaban ƙasa, bai kamata ya sa ido ya ga darewarta ba.”

‘Yan ƙasar da dama za su zuba ido su ga yadda al’amuran jam’iyyar za su ci gaba da gudana musamman a lokutan da zabukan shekara ta 2019 ke ƙara ƙaratowa.

'Halin da Nigeria ta shiga ya ƙara mana matsin rayuwa'


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Nijar na bukatar agajin tunkarar matsalar karancin abinci

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun gudanar da wani taro da cibiyoyin ba da agaji don shawo kan matsalar ƙarancin abinci da mutane kimanin miliyan ɗaya da rabi ke fuskanta a kasar.

Ba kawai mutane ne, suka samu kansu cikin halin yunwa ba, dabbobin ƙasar ma suna cikin tasku sakamakon rashin ciyawa a Nijar.

Gwamnati ta ce faɗuwar darajar Naira da ta shafi kasuwar dabbobin ƙasar a Nijeriya da kuma rashin kasuwa a ƙasashen Libya da Aljeriya duk yi tasiri wajen sanya Nijar a wannan hali.

Ta ce tana buƙatar saifa biliyan sittin da biyu don cike giɓin abincin da mutane da dabbobi ke buƙata a faɗin ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida Malam Bazoum Mouhammed ya ce Nijar ba ta taɓa fuskantar ƙarancin ciyawa musammam a wurare kamar jihar Tawa irin na bana.

“Babbar matsalar ita ce busashenmu mu…naira ta faɗi. Nairar da a da ake canzar da jaka guda (ta saifa) naira 300, (yanzu) ta kai jaka ɗaya, naira 800.

Ya bayyana damuwa game da karayar arziƙin da makiyaya da manoman ƙasar suka samu saboda dabbobi ba sa daraja.

“Abin da muka shaida a watannin da suka gabata, shi ne ake kawo busashe daga Nijeriya a sai da su a Nijar.”

Gwamnatin Nijar dai ta ce a bana ne wannan matsala ta fi ƙamari, don kuwa a baya ko an samu ƙarancin abinci, mutane ba sa shiga mawuyacin hali saboda dabbobi suna kuɗi.

Haka zalika, ana fuskantar hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar, lamarin da ya ƙara tsananta halin takura ga jama’a.

Bazoum ya ce: “Da hasashen da muka yi, har mu kai azumi kuɗin hatsi buhu guda, bai zarce jaka 20 ba, sai ga shi nan yau ya kai jaka 30.”

Ya ce ƙasar tana buƙatar tan dubu arba’in da uku na hatsi don cikawa a kan abin da take buƙata tan dubu saba’in da biyar, da za a sayar cikin farashi mai rangwame.

Haka zalika, jamhuriyar Nijar na buƙatar gudunmawar abincin dabbobi har tan dubu sittin da takwas baya ga iri tan dubu goma sha biyu don raba wa manoma a cewar Bazoum.

Mahukuntan dai na danganta wannan matsala da sauyin yanayi inda a wasu yankunan ƙasar aka fuskanci fari, yayin da a wasu kuma aka gamu da ambaliyar ruwa da ta lalata albarkatun gona da kashe dubban dabbobi.

Joshua ya tamfatse Klitscko a zagaye na 11


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bugun da Joshua ɗan asalin Nijeriya ya yi wa Klischko ya sanya tsohon zakaran boksin ɗin ganin faɗuwarsa ta biyar

Anthony Joshua ya yi wani gagarumin ƙwazo ta hanyar ƙara wa kambunsa, lambar zakaran boksin ajin masu nauyi ta duniya saboda bajintar buge Wladimir Klitschko a filin wasa na Wembley.

‘Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar tsallen-baɗake, inda Joshua ɗan boksin ɗin Burtaniya, ya buge tsohon gwarzon duniyan a zagaye na biyar, kafin a kai shi ƙasa a zagaye na shida – karon farko a fafatawa 19 da ya yi.

Duka ‘yan damben boksin ɗin sun fuskanci shan kaye a wannan karawa da za ta daɗe a zukatan mutane, kafin Joshua ya yi wa abokin karonsa dukan zauna-ka-ci-doya a zagaye na 11.

Joshua, wanda iyayensa ‘yan Nijeriya ne, ya sauke wa Klitschko wani wawan naushi da ya ba shi damar kai shi ƙasa cikin laulayi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Klitschko aka fara kai wa ƙasa a zagaye na biyar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sai dai irin wannan ƙaddara ta faɗa wa Joshua a zagaye na shida

Klitschko ya yi ta maza ya sake jan zare, bayan an sa shi a maƙatar hagu daga bisani.

Sai da lafari David Fields ya karɓe shi lokaci da aka takure shi a jikin igiya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sau biyu ana kai Klischko ƙasa a zagaye na 11 kafin lafari ya karɓe shi

Joshua ya cira hannuwansa sama lokacin da ihu da sowa suka ɓarke a filin Wembley.

Ya tsallake karawarsa mafi zafi a yau, yayin da Klitschko ya gane irin wayon da yake da shi.

Ko da yake, ya nuna har yanzu duk da shekarunsa 41, za a ci gaba da kai ruwa-rana da shi a fagen karawa ta duniya.

Klitschko zai ciji yatsa a kan rashin gama wa Joshua aiki, lokacin da ya shimfiɗe shi ƙasa, har ma aka riƙa ganin ba wata makawa ya kusa sake karɓar biyu daga cikin kambun da ya rasa a hannun Tyson Fury a shekara ta 2015.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ingila Rio Ferdinand na daga cikin mutanen da suka taya Joshua murna

“Me zan ce? Karawa 19, ba a buge ni ba, a shekara uku da rabi,” in ji Joshua. “Ban cika bakin na fi kowa ba, amma dai ludayina ne ke kan dawo. Ka san kuma ba a ƙwace wa yaro garma.

“Kamar yadda ‘yan boksin ke cewa, ajiye girman kanka a waje kuma ka mutunta abokin karawarka. Don haka ina yi wa Wladimir Klitschko jinjinar ban girma.”

Wata uwar 'boge' ta mayar da 'yar da ta saya


Hakkin mallakar hoto
CHRISTOPHER FURLONG/GETTY IMAGES

Image caption

An ba wa wani gidan marayu jaririyar (ba ita ce a wannan hoto ba) don samun kulawa

An zargi wata mace ‘yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mai da jaririyar da ta saya, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne.

An zargi matar ‘yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800, kwatankwacin naira miliyan bakwai.

An kama matar tare da mahaifiyar jaririyar ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin.

Ba da goyon ciki a ƙasar Italiya, haramtaccen abu ne kuma akan ɗaure mutum a gidan yari a ci shi tara mai tsanani.

An ce uwar ‘bogen’ ta faɗa wa ‘yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta.

Rahotannin kafofin yaɗa labarai a Italiya sun ce abokin zamanta yana ɗaure a gidan yari kan laifin safarar ƙwaya, kuma a baya-bayan nan ta yi ɓari har sau biyu.

‘Jaririyar ruwa biyu ce’

Mahaifiyar jaririyar, ‘yar ƙasar Romaniya mai shekara 25, bayanai sun ce ta yi ciki ne bayan alaƙarsu da wani mutumin ƙasar Mali.

Lokacin da gano asalin jaririyar, sai uwar bogen ta ce lallai zai yi mata wahala ta iya yin bayani game da launin fatar yarinyar.

Don haka, bayan kwana uku, rahotanni sun ce, sai ta mayar da jaririyar.

An fara nuna wasu-wasi ne farko a ofishin rijistar haihuwa na birnin Latina a kudancin Rome cikin watan Fabrairu, lokacin da wata mata ta nemi sanin yadda ake yi wa jaririn da aka haifa a gida rijista.

Bayan shafe lokaci, amma ba a je an yi rijistar ba, sai jami’ai suka sake tuntuɓa – sai dai an ce sai mai amsawar ta riƙa kwana-kwana.

Hakan ya sanya fargaba lallai da walakin, don haka sai suka ankarar da ‘yan sanda.

Masu bincike sun gano jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma mahaifinta na asali yana aiki ne a Rome.

A yanzu dai ba ta fi tsawon wata guda a duniya ba, kuma an damƙa ta gidan marayu don kula da ita.

An zargi wata mace ‘yar ƙasar Italiya da ƙaryar samun juna biyu, kuma ta je ta mayar da jaririyar da ta sayo, bayan ta gano cewa yarinyar ruwa biyu ne.

An zargi matar ‘yar shekara 35 da sayen jaririya a kan kuɗi dala 21, 800 kwatankwacin naira miliyan bakwai.

An kama matar tare da mahaifiyar jarirai ta ainihi da kuma wani ɗan ƙasar Morocco da ake zargin shi ya haɗa cinikin.

Al’adar ba da goyon ciki haramun ne a ƙasar Italiya, inda akan yi mutum ɗauri a gidan yari da cin tara mai tsanani.

An ce uwar bogen ta faɗa wa ‘yan sanda cewa ta riƙa kifa wani cikin ƙarya da ta saya ta hanyar intanet don yaudarar dangi da ƙawayenta.

Rahotannin kafofin yaɗa labarai a Italiya sun ce abokin zamanta yana ɗaure a gidan yari kan laifin safarar ƙwaya, kuma a baya-bayan nan ta yi ɓari har sau biyu.

Mahaifiyar jaririyar, ‘yar ƙasar Romaniya mai shekara 25, bayanai sun ce ta yi ciki ne bayan alaƙarsu da wani mutumin ƙasar Mali.

Lokacin da gano asalin jaririyar, sai uwar bogen ta ce lallai zai yi mata wahala ta iya yin bayani game da launin fatar yarinyar.

Don haka, bayan kwana uku, rahotanni sun ce, sai ta mayar da jaririyar.

An fara nuna wasu-wasi ne farko a ofishin rijistar haihuwa na birnin Latina a kudancin Rome cikin watan Fabrairu, lokacin da wata mata ta nemi sanin yadda ake yi wa jaririn da aka haifa a gida rijista.

Bayan shafe lokaci, amma ba a je an yi rijistar ba, sai jami’ai suka sake tuntuɓa – sai dai an ce sai mai amsawar ta riƙa kwana-kwana.

Hakan ya sanya fargaba lallai da walakin, don haka sai suka ankarar da ‘yan sanda.

Masu bincike sun gano jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma mahaifinta na asali yana aiki ne a Rome.

A yanzu dai ba ta fi tsawon wata guda a duniya ba, kuma an damƙa ta gidan marayu don kula da ita.

BURIN ZUCIYA: Sakon Wasiyya: Ko Za Ki Iya Wannan?


BURIN ZUCIYA: Sakon Wasiyya: Ko Za Ki Iya Wannan?

|

Wannan tambayar na da sauki a baki, amma tana da wahalar gaske wajen aikatawa. Za ka iya tambayar kanka, idan larurar barin duniya ta same ka, har ka tabbatar lokacin amsa kira ya yi, shin za ka iya ba wa matarka damar auren wani wanda ka sani, wa lau amini ko abokin aiki? Ko kuma a yayin da ki ke ganin cewa lokaci ya yi da za ki rabu da duniya, shin za ki iya ba wa kawarki damar ta auran miki miji, ko don ta kulan miki da ‘ya’ya, don gudun kada ya auro wata wadda za ta iya musguna wa ‘ya’yan naki?

Kamar dai yadda na fadi a fili, tambaya ce mai sauki ji da karantawa, amma idan mutum ya yi tsokaci, hakika ba karama ba ce. Na tsinkayo wata hira a tashar radiyo, inda mai gabatarwa ta yi wannan tambayar domin jin ra’ayoyin masu saurare. Ba jimawa kuwa a ka fara kiranta a waya, kowa na fadin albarkacin bakinsa. Kusan dukkanin wadanda suka rika kira gami da bayyana ra’ayoyin nasu, sun tafi ne kan cewa ba za su iya yi wa wani makusancinsu wasiccin auren mazaje ko matayensu ba.

Duk kuwa da ya kasance da harshen Turanci a ke gabatar da shirin, kwatsam, sai da wani ya kira, da Hausa ya bayyana ra’ayinsa. Cikin fushi da tsananin kishi, yake nuna cewa sam ba za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa. Yana mai cewa zancen wai ka samar wa matarka gidan hutu, bayan ba ka a duniya, domin kada ‘ya’yanka su wahala, duk bai taso ba. A cewarsa kowa da ka gani a duniya, arzikinsa ya ke ci. Saboda haka ya ce ba zai iya ba.

Haka ita ma wata matar da ta kira, ta bayyana cewa ta gwammace bayan ta mutu a yi abin da za a yi, amma ba wai ta mika ragamar rabin rayuwarta ga kawarta ba. Yawanci dai a haka a tafi, kusan kowa idan ya kira, sai ya bayyana salo da samfurin kishin da yake da shi game da matarsa. Abin mamaki da al’ajabi shi ne, yawan wadanda suka kira lambar waya suke bayyana ra’ayinsu kafatan babu wanda ya kalli wani bangare na yadda al’ada da addini suka shimfida wasu ka’idoji game da hakan.

Shin zai yiwu a yi maka wasiccin auren wata matar? Kwarai kuwa zai yiwu! An samu a tarihin addinin Musulunci, akwai daga manya-manyan matan Sahabban Manzo (SAW), wadanda suka bar wa mazajensu wasiyyar auren wadansu matayen domin su rike musu sirri da kulawa da ‘ya’ya. Wannan sanannen tarihi ne.

Babban abin da zan fadi a nan shi ne; a daidai wannan zamani da muke ciki, shin zai yiwu hakan ta faru?

Kafin na ji daga gare ku, ina fatan kowa zai natsu ya bayar da nasa gudunmawar, musamman mata. Hakan zai kara buda mana wani sabon shafin sanin tsananin kishi na mata. Shin tsakanin maza da mata, wa ya fi kishi?

Sai na ji daga gare ku.

Abban Umma (B/014/Z/KAD). 08033225331.

Abba Baban Umma

burinzuciya@yahoo.com

ADABI: Hausa: Akwai Babban Aiki A Gaban Hausawa


Abokina Malam Hassan Rabe Katsina Malami ne a babbar Kwalejin Horas da Malamai ta Isa Kaita da ke Dutsinma a jihar Katsina, sashen nazarin harshen Hausa. Ya taba yin tambaya a cikin aji, mai dauke da kusan mutum 67 duk Hausawa zalla, kuma ma daga jihar Katsina, cewa mene ne ‘moda?’ Amma duk ajin nan aka rasa wanda zai gane abin da kalmar ke nufi.

Moda dai na nufin abin dibar ruwa a cikin randa ko tulu, a nan kasar Hausa. Kuma dadaddar kalma ce. Sannan kuma ya sanya kudi tsabar Naira Dubu (N1000) akan wanda ya gane ya dauka amma ina!. Ni ma kaina na koya a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Daudawa jihar Katsina na tsawon shekaru 4 da watanni. Na kan shiga aji 6 in yi darasin Hausa har ma in yi kacici-kacici na wasu dadaddun kalmomi na Hausa, wadanda ke kusa da ko gab da bacewa ma. Abin mamaki, wai yarinya budurwa ‘yar shekara 18 a kasar Hausa ba ta san ‘turgeza’ ko ‘adaka’ ko ‘na-gani-inaso’ ko ‘gudun buya’ ba. To ballantana wakokin gargajiya na Hausa da muka gada kaka da kakanni, masu ban sha’awa masu dan karen dadi. Na kan ma sanya kudi akan kalmomi, cewa duk dalibar da ta ci, to zan ba ta su.

Abin mamaki ma, sai ka ga dalibi Bahaushe kuma ba ma inda ya je a Kudu ballanatana a ce ko ya zauna can, amma yin magana da Hausa na neman gagararsa. Sai dai wasu yarurruka da ke cakude da Hausar ke neman ma kwace harshen namu. Kullum karatu ake yi akan harshen Hausa, kuma ga mu da Malaman harsunan gida barkatai a makarantunmu, amma abin ya ki mayar da mu masu al’ada daya irin ta Malam Bahaushe. Harshen Hausa kullum sai kara samun barazana yake yi. Hausawa kullum sai wulakanta harshen suke yi. Kurum wanda harshen yake da tasiri a gare shi sai wanda ba Bahaushen ba, mu kuma muna ta kokarin komawa Yahudawa ko Turawa.

Na fara gane cewa Malam Bahaushe ya fara yada al’adarsa da ya gada ta alkunya da girmama iyaye ko manya, da suturta jikinsa tun lokacin da na yi karatu a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Minna daga 2007 zuwa 2014. A cikin kwaryar Minna sai ka tarar Hausawan can sun sha bambam da sauran Hausawan da ke jihohin Katsina da Kano da Sakkwato ko Kebbi. Ina tammanin saboda gwamutsar al’adu tare da ta wasu yare mazauna Minna a yanzu Hausawan Minna sun rikide Nupawa ko kuma Yarabawa su ma.

A sanina, yarinya kan tafi dakin saurayi ta tare ko kuma ta rika zuwa tana zama har sai idan an samu ciki, an ma haihu, sannan a daura masu aure. Wannan al’adar Yarabawa ce, ko da musulman ma. Tabbas, ko a Funtuwa da Kaduna haka ake yi. To su ma Nupawa wasu na da wannan al’adar. Wato tarayya tsakanin namiji da mace gabanin aure ba wani abin kunya ba ne, abin ma kwalliya ne ga al’adar wasu Nupawa da Yarabawa, da musulmansu da kisitocinsu, amma wasu sam ba su yarda da irin wannan, musamman masu ilimin addini a cikinsu. A nan Arewacin Nijeriya, Bahaushe ne ya ke daga gefe, ba ruwansa da wannan, tunda Hausawan farko ba su zo da wannan ba.

A lokacin ina karatu a Minna a gabanmu budurwa da saurayi za su wuce ko kunya ba su ji. Wallahi tallahi yadda ake bayyana zina ba a bayyana ta a sauran manyan biranen jihohin Arewa. Kusan ta zama abin ado. Ina sheda, watarana da daddare a Minna din ina tsaye a Unguwar da na sauka na ga keke Napep ko ‘yar kurkura ta tsaya a gabana. Ashe wata mace ce daga ciki ta hango abokin mijinta sai ta ce ma mai mashin din ya tsaya don su gaisa. Da suka gama yin magana da shi sai na ga ta miko masa hannu shi ma ya mika mata sun tafa ko sun kashe. Abin ya daure mani kai.

Sai na tambayi wani saurayi nan kusa, na ce masa waccan matar ta cikin keke Napep yaya suke da wancan mutumin? Sai ya ce mani shi abokin mijinta ne. Na ce masa ‘matar aure ce? Ya ce ‘shakka babu, matar aure ce’. Wannan abu ya dade yana ba ni mamaki. Kuma wallahi summa tallahi Hausawa ne ba Yarabawa ba ma. Wai da karfi da yaji sai mun koma Turawa ko Yahudawa.

A Minna, mun fara ganin farkon abin ga Malam Bahaushe. Tunda matarka za ta tafi Unguwa, da ta dawo sai ka ga mutum na tambayonta kin ga wane? Me ya ba ki? Wa’iyazu billahi. Allah Ka shiga tsakaninmu da shedan don alfalmar Annabi (SAW).

Su aka sani da tura ‘ya’ya wadanda ba su da galihu gidajen masu hali don su rika yin barantaka ko ‘housemaid’. Wai manufar su yarinya ta samu aikin yi don ta rika kan ta ba sai ubanta ya rika biya mata kudin makaranta ba. Ba kuma za su kula da abin da ke faruwa ga yarinyar ba, ko da za ta je ta yi ta yin zina babu ruwan su, su dai yarinya ta nemo ma kanta abin da za ta rike kanta har ma su ma ta rika sammasu. Akwai lalacewa kamar wannan? Amanar da Allah Ya ba mu mun yada mun ce ba mu iyawa. Malam Bahaushe ba ya gajiya da abin kunya.

To sannu a hankali muna ganin abin da ke faruwa a wasu wurare, na daga zamantakewa da al’adun Hausawa yana fara faruwa kadan-kadan a sauran biranen jihohin Arewa. Kuma muna ganin karshen al;adar Malam Bahaushe kadan-kadan. Don ka zauna kana sauraron wakar wani mawaki na Hausa, yaran yanzu dan shekarun 18 ko abin da ya daram ma haka sai ya rika kallonka a matsayin sakarai, bai san cewa shi ne sakarai din ba.

Bai san cewa wakokin da yake saurare na mawakan Turawa ko namu din ma na nan gida, amma masu amfani da kayan kidan Turawa shi ne shirme ba. Don ka fito daga gida daya kai da mace baliga ba hujja ba ce ka ce wai za ka rika sumbatar ta a bainar jama’a. Wannan rashin kunya da taka dokar addinin Islama ne, kuma yi wa Annabi (SAW) karan tsaye ne. Ko kuma ka ga mace ta mamuke namiji idan ya goyo ta a bisa mashin. Wannan ba al’adar Malam Bahaushe ba ce, amma a yau iyaye sun yi sakaci sun bar ‘ya’yansu suna lalacewa akan wannan turbar ko al’adar.

A yau a kasar Hausa sai ka ga ‘yan gida daya wadanda ba jinsi daya ba suna rungumar juna; idan namijin ya goya macen ya-Allah ko za su je Kafe (Cafe) duba jarabawa ko wani abu makamancin wannan. Wannan shegantaka tana tsananin bata rai matuka. Malam Bahaushe ya cika sakaci da al’adarsa. Kusan muna iya cewa bai ma san inda kansa ke yi masa ciwo ba ta wannan fuskar. Nan gaba yaya al’adarmu za ta kasance? Haba iyaye? Ba mu tunanin ranar da za mu hadu da Ubangiji Allah (SWA)? Mu fa tuna cewa ‘ya’yanmu duka kiwo ne Allah Ya ba mu, kuma zai tambayemu a ranar sakamako akan yadda muka tarbiyyantar da su.

Bahaushe ya yada al’adarsa da hanyar rayuwarsa wadanda suke abin sha’awa ga sauran al’ummomi ya dauki wata al’ada daban, ya raina tasa al’adar.

Mun saki taragon jirgin addinin Islama, mun auka cikin taragon jirgin Yahudawa marasa tarbiyya marasa addini. A yau, wai matar Malam Bahaushe ce ke sawo sabon gashin kai a kanti ta dora bisa wanda Allah Ya ba ta. Ka ga a nan ta raina yawan gashin da Maiduka Ya yi mata, sai ta kara.

Saboda lalacewar tarbiyyar Malam Bahaushe, a yau Hausawa suka kirkiro ma kansu wasan matar aure da kanen mijin, to amma ba don yana cikin addinin Islama ba. Sam Allah Bai yarda da wannan tsarin ba. To wasan kanen miji da mata ya kan haifar da abubuwa da dama na shedana.

Mu kwana nan.

Tare da

Dakta Aliyu Ibrahim Kankara 07030797630

imel: ibrahim@fudutsinma.edu.ng

MANUFAR RAYUWA: Dabi’ar Mutum: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta


A wannan makon zan mayar da hankali ne a kan dabi’un jama’a, musamman ma batun da ya shafi gini da rusa dabi’ar mutum, shin za a iya ko a’a? idan za a iya, ta wadanne hanyoyi ne za ka iya sauya dabi’ar mutum daga wani aiki zuwa ga aikata wani?

Kafin ka iya sauya dabi’ar mutum ka na bukatar ka auna yanayin fahimtarsa da kuma yadda ya ke tunani. Misali a nan shi ne, ta ya za a ka iya gamsar da mutum a kan ya fara motsa jiki, alhali a ko da yaushe ya kan yi korafi dangane da rashin lokaci, ko kuma ya cika son jikinshi, ma’ana ba ya son wahala? A irin wannan yanayin, mafita daya ce za ka yi amfani da ita wurin sauya dabi’ar mutum, shi ne ka bijiro mishi da wani sabon bayani wanda bai san da shi ba.

Misali, wanda ka ke son ya fara motsa jiki amma ya ke ce ma ba shi da lokaci, sai ka fara yi mishi bayanin yadda ka ke samarwa kanka da lokaci a kowacce rana har ka ke iya samun daman motsa jiki, kuma a sanadiyyan motsa jikin har ma ka je likitoci sun gwada ka sun tabbatar da cewa a tsawon watanni ka kara lafiya da kuzari, har ma ka samu waraka daga ciwon Basir din da ke addabanka. Wannan bayanin da za ka yi mishi zai sa kwakwalwarshi ta fahimci wani abu, sannan tunaninshi dangane da motsa jiki zai sauya.

Rusa dabi’ar mutum na bukatar a sa kokari da jajirjircewa, saboda abu ne da ke daukar lokaci. Sai dai matukar a ka bi matakan da su ka dace, a na iya nasara. ba a son mutum ya kwallafa rai a kan cewa zai iya rusa dabi’ar wani a dan kankanin lokaci.

Kamar yadda ba a lokaci guda a ke gina dabi’u ba, haka nan ba zai yiwu a rusa su a lokaci guda ba. mutum na gina dabi’a ne ta hanyar yin mu’amala da mutane. Gina dabi’un na farawa daga shekarun yarinta, saboda a sannan ne a ke koyon al’adu, tarbiyya da girmama manya. Har zuwa mutuwan mutum ya na mu’amala ne da mutane ya na gina sabbin dabi’u.

Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da nufin zagi, a wurin iyaye yara ke fara koyo. Shi ne ya sa za ka ga wani ya zama gwani a zagi, kwararren gaske. Ba a sama ya samo dabi’ar ba, abin da ya taso ya ga a na yi a gidansu kenan. Wasu kuwa gidansu mutanen kirki ne, don haka ba su iya samun daman kwaikwayon zagi a gida.

Daga gida, lokacin da yaro ya fara wayo, ma’ana zai yiwu a kyale shi ya rika fita waje, sannan ya kai shekarun fara zuwa makaranta. Wasu unguwarsu ‘G.R.A’ ne, babu hayaniya; ba irin unguwannin nan ba ne da a ke cakude da juna. A nan, dabi’un yaransu sun fi samuwa a mu’amalar da yaran ke kwaikwayo daga iyaye.

A irin unguwannin da a ke cakude, ma’ana wadanda yawanci ma gidajen haya ne masu mutane rututu, ya na wahala a iya saita dabi’un yaro. Na farko yaro zai rika kwaikwayon dabi’un iyayenshi, sannan zai rika kwaikwayon na ‘yan hayan gidansu, sannan zai rika kwaikwayon na sauran yaran kan layi; da ya ke irin wannan unguwannin kofofi a bude su ke, yaro ko da rarrafe ya ke yi, zai iya fita kan layi. Wasu yaran ma, dabi’un da su ke kwaikwayo wa a kan layi, ya fi karfin sanin iyayensu. A irin wadannan unguwannin mutane sun fi saurin diban dabi’u, masu kyau da marasa kyau.

Idan yaran wadanchan unguwannin ‘G.R.A’, su ka fara zuwa makaranta, za su iya haduwa da yaran unguwannin da a ke cakude da juna. A makaranta za su fara musayar dabi’u a tsakanin juna. Mutum ya na kwance a gida, ya yi tsammanin dabi’unshi da na matarshi da mutanen cikin gida kadai dansu ke kwaikwaya, bai san cewa ya na kwaikwayo wasu daga mu’amalarshi da wasu yara a makaranta ba. wannan na faruwa hatta a makarantun Islamiyyoyi.

Ba kawai a yarinta a ke gina dabi’u ko kwaikwayonsu ba, kowanne mataki na rayuwa a na sake kwaikwayon dabi’u ne da gina sabbi. Wani zai taso har ya balaga da dabi’u masu ban sha’awa da burgewa, amma da zaran ya fara makarantar Sakandare ko gaba da Sakandare, sai yanayin mu’amalarsa ta chanza, saboda haduwa da zai yi da wasu sabbin mutane wadanda su ka fito daga wurare mabambanta. Idan ba a yi sa’a ya hadu da abokan arziki ba, sai ya hadu da wadanda a hankali za su gina mishi dabi’un shaye shaye, ko kuma neman mata.

Musamman a jami’o’i, wata yarinyar za ta zo daga gidansu da dabi’un kwarai, babu ruwanta da sa suturar banza. Yawancin irin wadannan ‘yan matan, a kan hada su zama dakin ‘Hostel’ daya da su. Tun kafin ta fara halartan azuzuwa don daukan darasi, tun kafin ta san sauran mutanen ajinsu, da wadannan abokan zaman nata za ta fara mu’amala. Idan ba a dace ba, a hankali za su koya mata dabi’ar fita babu lullubi ballantana hijabi. Idan samarinsu sun zo zance, sai su rika takura mata a kan ta yi musu rakiya, har watarana abokin saurayin ya ganta ya ce ya na so, shi kenan ita ma ta shiga shirgin.

Kowacce irin dabi’ar mutum, idan a na son a rusa ta, ba a garaje, ba a gaggawa, ba kuma a nuna kosawa. A hankali za a rika nunawa wannan dabi’ar rashin dacewarta, da kuma nakasunta. Ba a rusa dabi’a da karfi ko da fada, ba a rusa ta da iko ko nuna isa. Dabi’u sun fi bukatar lalama da sassauci.

Kafin ka iya rusa dabi’ar mutum, dole sai ka yi nazarin yadda ya ke kallon wannan dabi’a ta sa, ma’ana fahimtarsa dangane da dabi’ar. Idan Yaro ne wanda ke shaye – shaye, dole ne sai ka fahimci menene fahimtarsa dangane da shaye shaye, tare da nazarin abubuwan da su ka jefa shi zuwa ga shaye – shayen. Shin akwai wani abu da ya ke kauna? Idan akwai menene wannan abun? Shin ya na samun daman yin tunani, wanda ba a maye ba, a hankalinshi? Idan ya kan samu lokacin yin tunani ba tare da ya sha komi ba, sai ka fahimci wannan lokacin, a sannan ne za a iya fara aikin chanza mishi tunani.

Kafin mutum ya fara wannan dabi’a da a ke son rusawa, dole a baya ya na da wasu dabi’u, kuma ya na da wasu abokai wadanda a bayan ya ke mu’amala da su. Dole a na bukatar sannan wannan. Saboda idan dabi’ar ta yi kamari, dole ne sai an sake dawo mishi da rayuwar da ya yi a baya, an dawo mishi da tsofaffin abokai, sannan a shimfida musu tsarin yadda za su tafiyar da mu’amala a tsakaninsu, idan a ka bi matakan yadda su ka dace a kan yi nasarar rusa dabi’ar da ba a so. Sai dai hanzari ba gudu ba, kwaikwayon dabi’a ya fi sauri a kan rusa ta.

 

Tare da

Suleiman Bala Idris

GSM: 07036666850

isbdaurawa@yahoo.com

 

Nigeria: An kama mutanen da suka so kashe Dino Melaye


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jami’an ‘yan sandan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi holin wasu mutane da makaman da a ka samu a wurinsu, wadanda ta zarga da yunkurin kashe wani dan majalisar dattijan kasar, Sanata Dino Melaye a watan Afrilu.

Cikin wata sanarwa da kakakinta, CSP Jimoh O. Moshood ya fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce daga cikin mutanen da a ke zargi, akwai shugaban karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Taofiq Isah, wanda ta ce shi ne ya shirya harin.

Rundunar ‘yan sandan ta ce bincike ya nuna shugaban karamar hukumar ne ya bai wa wani Abdulmumini da a ka fi sani da “iron” ko karfe, izinin kai wa Sanata Dino Melaye hari.

“Daga nan ne shi kuma Abdulmumini ya dauki hayar wasu mutane da suka kware wajen kisa domin aiwatar da nufinsu,” Inji sanarwar.

Har yanzu dai ba a kama Abdulmuminin ba, amma sauran mutanen da ya dauka hayar sun shiga hannun hukuma.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Senate

Image caption

Sanata Dino Melaye

Sanarwar ta bayar da sunan mutanen da aka kama kamar haka: Ade Obage, da Abdullahi Isah da Ahmed Ajayi da Michael Bamidele da Ede James.

Acewar sanarwar, makaman da a ka samu a wajen mutanen sun hada da bindigogin AK 47 guda biyar, da pistol daya, da bindigogi kirar gida biyu da harsasai masu yawa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce Ade Obage mai shekara 29 ne ya kai rahoto don kashin kan shi ga ‘yan sanda bayan sun yi yunkurin halaka dan majalisar.

Rundunar ta ce ta zafafa bincike domin kamo sauran mutanen da ke da hannu a cikin harin, sannan za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

A tsakiyar watan Afrilu ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan Sanata Dino Melaye a Aiyetoro-Gbede a karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, lokacin da yake cikin gidan da dare.

‘Yan bindigar ba su samu kai wa gare shi ba, amma sun lalata katangar gidan da harsasai.

ZAMANTAKEWA: Tuntube gushin gaba


ZAMANTAKEWA: Tuntube gushin gaba

|

Da dai rayuwar dan’Adam haka take cike da abubuwa na ajizanci, wato a wasu lokuta ka tafiyar da rayuwar yadda ka ke so, amma kuma a wasu lokutan sai akasi ya faru. Sai dai kuma wani abu mai ban sha’awa da rayuwa shi ne, a cikin kowane al’amarin dan’Adam na shu’unin rayuwarsa da kuma al’ummar da yake kewaye da ita, to yana koyon wasu abubuwan kuma na daban. Wannan ma shi ne dalilin da yasa masu hikimar magana kan ce “Dan’Adam tara yake, bai cika goma ba”. Ga misali, a lokacin da nake rubuta abin da tattaunawarmu da ta gabata ta kunsa ne sai ajizancin ya auku.

Wato bayan na rubuta fiye da rabi na batun namu, sai na’ura mai kwakwalwa (wato komfuta) ta yi tutsu kuma aikin ya bace. Daga baya kuma bayan na sake rubuta wani sai na’urar ta gano wanda ya bace. To a inda ajizancin ya yi aikin nasa shi ne a kokarin aiko da cikakken batun sai kaso na farko (da bai cika ba) ya riga shiga taskar aika sako kafin na biyun. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka sha yadda aka dama. Da yake waiwaye adon tafiya ne, za mu dan sake waiwayar abin da ya gabata (a kammale) kana daga nan kuma mu dora a tattaunawarmu ta gaba. Ko ba komai dai, ai masu hikimar magana na cewa “Tuntube gushin gaba”.

Kamar yadda muka kwana kuma muka sani, hikima wata baiwa ce da Allaah (SWT) yakan yi wa bayinsa a matsayinsu na daidaiku ko kuma a kungiyance. To sai dai kuma ita hikima kamar dan’Adam kansa da sauran dabbobi da kuma tsirrai (da itatuwa), tana bukatar kulawa ta musamman domin dorewar wanzuwa kwatankwacin wadannan halittu. Ita ma hikima tana bukatar ingantawa ta hanyar kulawa da tsarewa da kuma sarrafawa cikin dacewa, ta yadda hikimar za ta amfani mai ita da kuma sauran ahalinsa. Ma fi yawan mutane masu hikima, karansu ya kai tsaiko a rayuwa, to amma kuma mutanen da ba su da halayya ta kwarai ba su faye nisan zango a tafiyar ba. Rashin halayya ta kwarai lamari ne da yake kawo cikas ga ginuwar hikima. A tattaunawarmu ta yau za mu ga yadda halayya ta kwarai ta ke garkuwa ga hikimar da ta smu gindin zama a rayuwar al’umma.

Tambayar a nan ita ce, shin me yasa rashin halayya ta kwarai ke kawo cikas ga ginuwar hikima? Dalili kuwa shi ne, a rayuwa mutane ba sa wuce hurumin da halayyarsu ta ajiye su. Su kansu mutane masu hikima, a wasu lokuta sukan yi gaggawa cikin al’amuransu, to amma kuma halayya ta kwarai ce ke dakushe hakan domin rashin dacewa. Haka kuma mutane masu hikima kan ji cewa su ba dama ne, sannan kuma sun cancanci alfarma daga wurin mutane. A dukkan irin wadannan yanaye-yanaye, halayyar kwarai ce take yi masu jagora domin aiwatar da abin da ya dace. Bugu da kari ana yabawa mutane masu hikima bisa irin ayyukan da aka ga sun yi, kuma a nan din ma dai halayyar kwarai din ce kan yi tasiri a kansu. Suna kuma iya zama mutane na musamman, kuma dai halayyar ce take tabbatar da haka. Kai a kashin gaskiya ma dai, mutane masu hikima sun zamo wata baiwa da Allah (SWT) ya ba al’ummar duniya. Ta wannan haujin kuma, halayyar kwarai ce garkuwa ga dorewa da kuma hana salwantar wannan hikima. Hasali ma, ai a duk lokacin da ake maganar hikima, to ba komai ba ne mutane suke fahimta. Wato a wasu lokuta abin da ake gani ya samo dimbin nasara, to sai a tarar lamarin ba haka yake ba. A wasu lokutan kuma nan take gaskiyar al’amari kan bayyana kowa ya gani kuma ya fahimta.

Mutane kamar dusar kankara suke, wato jinsu ya fi ganinsu. Idan ka kalli dusar kankara, to wani kaso ne nata kawai ka ke iya gani da idanunka. Hikimar dan’Adam tana da kwatankwacin dusar kankara inda kaso kadan ne a bayyane amma sauran na boye. Wato sauran al’amura ne da suke tunanawa ba tare da an ba kowa masaniya ba. Haka kuma wannan din ne dai abin da suke aiwatarwa ba tare da kowa ya gansu ba. Shi ne kuma yadda suke fuskantar gwagwarmaya a rayuwa ta yau da kullum. Da haka suke samun nasarori kuma su rungumi kaddara dangane da cikas ko akasi ko kuma rashin nasara a lokacin da ta same su. Bugu da kari kuma, kwatankwacin girman hikimarsu to kwatankwacin bukatuwarsu ga halayya ta kwarai domin komai ya tafi daidai. Sai dai kuma a lokacin da hikimar dan’Adam ta yi nauyi da yawa, to a ma fi yawan lokuta takan jefa shi cikin hadari.

Gaskiyar maganar ita ce, babu wanda zai yi zaton samun nasara cikin dukkan shu’unin rayuwarsa ba tare da halayya ta kwarai ba, wato ita halayyar ce za ta ba da kariya ga hikima domin a sami dorewa ba tare da wani cikas ba. Ke nan halayya ta kwarai ita ta ke daidaita mana sahu a duk irin halin da muka sami kanmu. A ra’ayin Dabid McLendon “Halayya ta kwarai ita ce sinadarin da ke tabbatar da dorewar rayuwar mutum”. Idan halayyarka kamar tsinke take, to haka za ka kasance a gashe ba mai kuma a dafe babu romo. Wato dai duk ta inda aka juya ka babu wata mamora!

Idan kuma halayyar da zamo mai auki cikin nagarta, to ko shakka babu za ka samu cikakken biyan bukata. To amma kuma shin wai me ita halayya ta kunsa ne, da har ta zamo yaro da gari (wanda Hausawa ke cewa abokin tafiyar manya)? A gaskiya idan ka tunkari mutane da wannan mas’ala, to ko shakka babu za ka samu mabambantan amsoshi. Kokarin amsa wannan tambaya zai kara kwance mana bakin jaka dangane da kumshiyar halayya, kuma wannan batun shi ne alkiblar tattaunawarmu ta gaba.

tare da Farfesa Salisu A. Yakasai

08035073537, 08154615357 (Tes kawai)   Syakasai2002@yahoo.com

SANA’A SA’A: Sirrin Ganyen Magarya


Ina son na ruga da gudu don yi maku bayani kan amfanin ganyen Magarya, musamman ga mace. Ganyen yana dauke karni da warin jinin haila, biki da sauransu. Sannan yana taimakawa wajen warkar da mugunyar warin gaba ga mata.

Har ila yau, Magarya tana warkar da kwayoyin cututtuka masu tarin yawa a jiki. An fi son a yi amfani da danyen sai dai in hakan bai samu ba, za a iya amfani da busasshe. Yadda ake sarrafa shi kuwa shi ne a murza ko kuma a daka shi, inda hali a gyara shi, sannan a nika shi za a ga ya yi kumfa kamar kumfar sabulu.

A lura, yayin da uwargida ke amfani da ganyen wajen wanke jiki, za ta ga yana dan yauki, haka kuma duk wani dadadden datti, zai rika fita. Bincike ya nuna cewa babu sabulun da ya kai ganyen Magarya fitar da datti a jikin dan adam.

 

 • Karin Bayani Game Karin Ni’imar Mace:

Kamar yadda muka sha yin bayani a baya dangane da karin ni’ima a jikin mace, har kullum muna dada fadada wannan bangaren, inda a kullum masana harkar kiwon lafiya ke gudanar da karin haske kan wannan batu.

Uwargida za ki iya samun sassaken Baure, ki dafa shi sai bayan ya dafu sai ki juye ruwan sai ki samu mazarkwaila da zuma da kanunfari da citta, ki zuba aciki, ki tafasa ki rika sha safe da yamma.

Masana tun tabbatar da cewa dukkanin macen da ke amfani da wannan, za ta samu karin ni’ima a jikinta, sannan ta kasance mai dimbin alheri ga maigidanta. Bayan haka, za ki iya samun totuwar rake mai tsafta, sai ki bar shi ya bushe, ki samu Bagaruwa guda uku da Almuski da Kanumfari, ki hada su, waje daya ki rika tsuguno kuma ki rika goga zaitun a jiki, musamman a gabanki, hakan zai kara miki ni’ima mai yawae.

Bayan wannan, za ki iya samun RIDI, ki wanke shi, ki nika har sai ya zama gari, ki bar shi, ya bushe, ki rika sha da nono, zai kara miki ni’ima gasken-gaske, musamman wajen ibadar aure. Haka kuma yana maganin dattin mahaifa. Dangane da masu neman karin girman mama da sauransu…? A kullum na kan yi kokarin bayyana musu wasu irin sinadaran da za su yi amfani da shi, amma kuma suna bukatar karin bayani. Abin sani shi ne wasu matan daga sun yi haihuwa daya, za ka ga nononsu ya zube, wannan yana saka maigida, musamman irin mazan da suke son ganin mace da cikar mama cikin damuwa, wasu ma sai ya haifar musu da neman sabon aure.

Don haka uwargida, ki samu Habbatus-Sauda, Hulba, Alkama, Gyada, Ridi, Danyar shinkafa da Busassen Karas, duk ki daka su waje daya, kina sha da madarar ruwa na gwangwani, misali PEAK. Kina iya sha sa’o’i biyu akalla kafin barci da kuma Sa’o’i biyu bayan kin farka daga barcin.

 

*Tambayoyin Masu Karatu:

Tambayoyi Da Karin Bayani

Ganin yadda wannan shafin ya samu karbuwa gare ku ‘yan’uwana mata, kafin mu dora daga inda muka tsaya, za mu karasa tambayoyin da kuka aiko mana.

 

Ga wadansu daga ciki…

Tambaya: Shin Allah ya faranta miki duniya da lahira, amin haihuwata biyu amma wallahi ba ki ga yadda nonona ya koma ba. Duk ya yamutse don Allah ki taimaka min da hadin da zan yi ya ciko ya yi kyau. Allah ya saka da alheri.

Daga Maman Latifa.

Amsa: Maman Latifa idan kina biye da mu a satin da ya gabata na yi bayanai da dama kan maganin gyaran nono. Amma yanzu ma zan kara maki wasu:

 1. Ki samu albasa madaidaiciya ki yanyanka sai ki saka a tukunya da ruwaki ta fasa shi sosai har sai ruwan ya koma baki, sai ki juye ruwan ki sami zumar ki mai kyau inda yi daya, garin gero ludayi daya, madarar PEAK na gwangwani daya na ruwa sai ki juye su kan ruwan tafasashen albasan nan ki sha, amma fa kar ki bari ya wuce a wa 24 baki shanye ba, in Allah ya yarda in za a samu biyan bukata. Allah Ya sa mu dace.
 2. Ki sami aya, gyada, ayaba (plantain) da alkama sai madara, zaki wanke ayarki sai ki hada da gyadarki ki markada su ki tashe, already kin yanyanka plantain dinki kin busar kin yi gari da shi kin tankade sai ki rika diban garin plantain din kina hadawa da ruwan ayaba gyadarki kina sa madarar PEAK ta ruwa kina sha, zai gyara nono da yardar Allah.

 

Tambaya: Aslam, malama Jummai ina da tambaya, idan mijina yana tarawa da ni ba na jin dadin shi ma baya in dadi. Ina neman taimako.

Daga Zainab Adamawa.

 

Tambaya: Salam, malama don Allah ni matsalata mijina ba yi da kuzari kuma baya dadewa idan muna tarawa, ko mene ne maganin kara wa nami ji kuzari ko jimawa yayin jima’i da kuma yawan sha’awar iyali.

Nagode Talatu Gombe.

 

Tambaya: Assalam malama Jummai, Allah ya kara miki albarka da fahimta don Allah ina da karancin ruwan gaba kuma duk lokacin da na sa du da miji na sai naga baya fita hayyacin sa kamar yadda na ke jin sauran mata suna fada a hira koma minasha idan muka sayi kayan da’a ni da kawayena sai dai na ji kowa na tofa albarkacin bakinsa, malama har na daina saye don Allah ki taimaka min da abin da zan yi.

Daga Fatima Zamfara.

Amsa: Zainab, Fatima, da Talatu zan amsa maku amsoshinku gaba daya na baku a tare, ku sani cewa wadannan abubuwan da zan lissafo suna da matukar muhimmanci da amfani ga jikin mace hade da samun karin ni’imar sune kamar haka:

 1. Tuffa (Apple) matsayinta a jikin ki zai kara miki ni’ima a jiki har kasauki kuma jikinki ya ringa laushi yana kyau ba kamar wasu matan ba inka taba jikinsu ka ji tauri.
 2. Ruwan abarba: Shi ma yana da kyau mace ta rinka markadawa tana tacewa tana sha da sugar ko zuma.
 3. Rake: shi ma yana karawa mace ni’ima kuma yanada amfani matuka a jiki, yanda yake da zakinan da ruwa to haka mace zata ringa jin ni’imarta na karuwa.
 4. Aya: Shi ma duk tafiyar su daya da rake, ayar anaso irin bula-bulanan tana da matukar muhimmanci gurin mace tana da ni’ima kubar rainata hakama kunun aya idan yaji madarar peak.
 5. Zaitun: man zaitun yana magunguna da yawa to anaso ki ringa shafashi ajikinki yana gyara fata dasaka sautsi jiki, hakama yanada kyauki dinga shafawa a gabanku, yana saka laushi hakama idan mai gida yana iya shafawa.
 6. Bawon bagaruwa: Shi kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a tsuke kamar sabuwa ta dunga dafa bawon ta na shiga kamar yanda ake shiga ruwan dumi in kin haihu.
 7. Tsumi: akwai tsimi mai kyau da mara kyau mara kyau yana tsinka jikin mace wata har jini yake sata na ba gaira ba dalili. Ga hadin tsumi ki yi da hannun ki yafi kyau ki nemi sasaken baure, kananfari, zuma, citta, mazarkwaila. Za ki tafasa sasaken baure ya dahu sosai sai ki daka kanumfari me yawa da citta yar kadan ki zuba akai, ki saka mazarkwailan da zuma amma zaki cire icen kafin ki zuba hadin, sai ki sauke ki dinga sha daidai kima idan ya huce.
 8. Ku samu zogale ku wanke shi ku nika shi tare da dabino da kuma kwakwa sai ku tace kusa zuma tare da madara sai ku saka ya yi sanyi bayan kungama sallar mangarib sai ku sha.

 

Bayani kan wanda basajin dadin saduwa

Ana so mace ta kula da gabanta domin Allah ya sa namiji ya kwallafa ransa gare shi. Barinsa ya lalace kamar zubar da kimarki ne a wajen sa kada ki bar shi ya yi wari, kada ki bar shi ya yi fadi. Domin masana sun ce duk lokacin da aka yi jima’i farjin mace yana karafadi shi kuma nasa yana rage girma to kinga nasa na rage girma na ki na fadi zai kuma ba kya kula da shi, ba zai rika jin gamsuwa ba. Don haka sai ya fara tunanin kin tsufa ke ma ki fara ganin ya za ma rago shi ya sa yawanci ba a samun gamsuwa. Kuma ba kowane namiji ba ne zai iya fadawa matarsa gabanta ya kara girma ba.Don haka mu kula.

Macen da takeso gabanta ya yi cif icf sai ta samu farar albasa, kanunfari, citta, balmo, barkono, rihatul hulbi. Sai ki hada su waje daya ki mayar da su kamar yaji kina zubawa cikin abinci kina ci kullum. Mijinki ma za ki iya masa hadi, ki sami muruci, saiwar haukufa, namijin goro, hanno, rihatul hubbi ki daka su gaba daya, ya dinga zubawa a nono mai kyau sha. Sannan ku nemi dabino a daka shi ya sa a cikin nono mai tsami sai ya rika kama ruwa da shi, amma fa bayan ya gama shafawa zai iya wanke wa da ruwa.

Insha Allah za a samu biyan bukata. Allah ya taimake mu amin.

Tare da

Jummai Ibrahim
GSM: 08097160554 (tes kawai)
saasanaa@yahoo. com

Tattaunawa da mai safarar sassan jikin 'yan gudun hijira


Idanuwan Abu Jaafar na cike da gadara lokacin da yake bayyana hanyarsa ta samun kuɗin shiga a rayuwa.

Yana aiki ne a matsayin mai gadin mashaya lokacin da ya hadu da gungun wasu mutane da ke safarar sassan jikin bil’adama.

Aikinsa shi ne ya nemo mutane da ke cikin halin ni-‘ya-su domin su sayar da wani sashe na jikinsu, kuma kwararar ‘yan gudun hijira daga Siriya zuwa Lebanon ta sa harkarsa ta buɗe.

Ya ce “Ina ci da gumin mutane, ko da yake ya nuna cewa da yawansu ka iya mutuwa cikin sauƙi a Siriya, don haka cire wani sashe na jiki ba komai ba ne, idan an kwatanta da munanan haɗurran da suka fuskanta.

“Ina ci da guminsu, amma su ma suna ƙaruwa.” in ji shi.

Yana zaune ne a wani ɗan karamin shagon sayar da gahawa, a ɗaya daga cikin unguwannin mafi cunkoson da ke kudancin birnin Beirut, wani gini ne duk ya ji jiki da aka lulluɓe shi da tamfol.

A bayan ginin, wani daki ne da ke jikin wata iyaka da aka raba gidan cunkushe da tsoffin kujeru, tsuntsaye na ta kuka a cikin keji a kowacce kusurwa.

Ya ce daga nan ne ya tsara cinikin sassan jikin ‘yan gudun hijira kimanin 30 a cikin shekara uku da ta wuce.

“Sun fi tambayar ƙoda, amma kuma ina iya nemowa na shirya cinikin sauran sassan jiki”. in ji shi.

“An taɓa neman idon mutum, kuma na yi ƙoƙari na samo wani buƙatar sayar da idonsa.”

“Na ɗauki hoton idon mutumin, kuma na aika wa masu sayen ta shafin Whatsapp don su gani ko ya yi. Daga nan, sai na kai mai sayarwar.”

Ƙananan titunan da yake gudanar da harkarsa na cike da ‘yan gudun hijira. Mutum ɗaya cikin huɗu na ‘yan Lebanon a yanzu ya gudo ne daga tsallaken iyakar Siriya saboda rikici.

Mafi yawansu ba za a bari su yi aiki a karkashin dokar Lebanon ba, da ƙyar iyalai da yawa ke maleji.

Daga cikin waɗanda suka fi tagayyara, akwai Falasɗinawa wadanda ake ɗauka a matsayin ‘yan gudun hijira a Siriya, don haka ba su cancanci sake yin rijista da hukumar kula da ‘yan hgudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ba idan suka iso Lebanon.

Suna rayuwa a sansanoni masu cunkoso kuma tallafin da suke iya samu kaɗan ne.

Waɗanda suka yi kusan kamo su wajen tagayyara su ne mutanen da suka zo daga Siriya bayan watan Mayun shekara ta 2015, lokacin da gwamnatin Labenon ta ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta daina yi wa sabbin ‘yan gudun hijira rijista.

“Duk wanda ba a yi wa rijista a matsayin ɗan gudun hijira ba ya shiga wahala,” in ji Abu Jaafar. “To ya za su yi? Sun shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, ba su da wata hanyar rayuwa face su sayar da sassan jikinsu”

Wasu ‘yan gudun hijirar kan yi bara a tituna, musammam ƙananan yara.

Samari kuma kan yi sana’ar goge takalmi, wasu na kurɗa-kurɗa a tsakanin motoci suna sayar da cingam ko hankici, ko kuma su kare a matsayin yaran da ake bautar da su wasu su dinga ci da guminsu.

Wasu kuma kan zama karuwai. Amma sayar da wani sashen jiki hanya ce ta samun kudi na da nan.

Da zarar Abu Jaafar ya samu masu son sayarwa, sai ya ɗauke su a mota, ya rufe musu ido, zuwa wani boyayyen waje a ranar da za a cire.

Wasu lokuta likitoci kan yi tiyatar ne a gidajen haya, waɗanda aka mayar da su ƙananan asibitocin wucin-gadi, a nan ake yi wa mutum gwaje-gwajen jini kafin aikin tiyatar.

Ya ce “Da an gama tiyatar sai na mayar da mutum inda na ɗauko shi”

“Zan kula da shi har kusan mako guda, lokacin da za a cire zaren ɗinkin da aka yi. Da zarar an cire, ba ruwanmu da abin da zai faru da su”.

“Ba ruwana, idan mutumin ya mutu, na samu abin da nake bukata. Ba matsalata ba ce, abin da zai faru da shi gaba matukar an biya mutum haƙƙinsa”.

Abokin cinikin Abu Jaafar na baya-bayan nan, wani matashi ne ɗan shekara 17, wanda ya baro Siriya bayan kashe mahaifinsa da ‘yan’uwansa a can.

Tsawon shekara uku yana zaune a Lebanon ba shi da aikin yi, ga shi ya ci bashi iya wuya, yana fama ya tallafa wa mahaifiyarsa da ‘yan’uwansa mata biyar.

So, through Abu Jaafar, he agreed to sell his right kidney for $8,000 (£6,250).

To, ta hanyar Abu Jaafar, ya yarda ya sai da ƙodarsa ta dama dala dubu takwas, kimanin naira miliyan uku.

Bayan kwana biyu, ga alama yana fama da ciwo duk da magungunan da yake sha, ya kasa kwance ya kasa zaune a kan wata yagalgalalliyar katifa.

Fuskarsa ta yi sharkaf da gumi, ga kuma jini yana jiƙe bandejin da aka yi masa.

Abu Jaafar bai faɗi ko nawa ya samu a wannan harka ba. Ya ce bai san abin da ake yi da sassan jikin ba, idan an saya, amma yana jin fitar da su wasu kasashen ake yi.

Ana fama da ƙarancin sassan jikin mutum da ake buƙata don yin dashe a yankin Gabas Ta Tsakiya, saboda tasirin al’ada da addinan waɗanda za su iya ba da gudunmawar sashen jiki.

Akasarin dangi sun fi son nan da nan a binne mamaci.

Abu Jaafar ya yi iƙirarin cewa akwai aƙalla dillali bakwai irinsa da ke aiki a kasar Lebanon.

“Harka tana tafiya,” a cewarsa “Harkoki gaba suke yi ba baya ba. Tabbas an samu bunƙasa bayan ƙaurar ‘yan Siriya zuwa Lebanon.”

Ya san abin da yake yi ya saɓa wa doka, amma ba ya tsoron hukumomi. a maimakon haka ma alfahari yake da sana’arsa. Yakan rubuta lambar wayarsa a jikin bangwayen da ke kusa.

A unguwarsu ana ganin girmansa kuma ana jin tsoronsa. Mutane kan shiga taitayinsu da zarar ya tunkari waje.

Ya cusa ƙaramar bindiga a kafarsa lokacin da muke zantawa.

Ya ce “Na san abin da nake yi ya saɓa doka, amma kuma taimako nake yi”

“Ni haka nake gani. mutumin da zai sayar da sashen jikinsa, yakan yi amfani da kudin, don neman rayuwa ingantacciya a gare shi da danginsa.

“Ya samu damar sayen mota inda yake aikin taksi, ko ma ya yi tafiya zuwa wata ƙasar.

“Ina taimakon mutane ne, ba ruwana da dwata oka”

A gaskiya ma ya ce ai dokar ce ta hana ‘yan gudun hijira da yawa samun ayyukan yi da tallafi.

“I am not forcing anyone to undertake the operation,” he says. “I am only facilitating based on someone’s request.”

“Ba na tilasta wa kowa yin haka, a cewarsa. “Ni kawai ina shiga tsakani ne idan mutum ya bukaci hakan.”

Ya kunna sigari yana zare ido.

“How much for your eye?” he asks.

“Nawa za ka sayar da idonka?” ya tambaya.

Abu Jaafarba sunansa ne na ainihi bakawai ya yarda zai yi magana da BBC ne bisa sharaɗi za a sakaya sunsan

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Trump ya ce Koriya ta Arewa ba ta kyauta ba

Kasar Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makami mai linzami, a cewar jami’an Koriya Ta kudu da Amurka.

Sun ce makamin ya tarwatse jim kadan da harba shi – karo na biyu kenan a mako biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Koriya ta Arewa da nuna “rashin da’a” ga China da shugabanta.

An harba makamin ne ranar Asabar daga kudancin Pyeongan, a cewar Koriya ta Kudu.

Mr Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Koriya ta Arewa ta nuna rashin da’a ga bukatun China da shugabanta da ke da kima inda ta harba makami mai linzami a yau, ko da yake bai yi nasara ba. Hakan babu dadi.”

A kwanan baya ne Mr Trump ya barki bakuncin shugaban China Xi Jinping inda ya yabe shi kan abin da ya kira “kokarin da kake yi matuka” kan Koriya ta Arewa.

An harba makami mai linzamin da bai yi nasara ba ne sa’o’i kadan bayan kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya tattauna kan shirin Koriya ta Arewa na kera makamai masu linzami.

ADON GARI: Zai Yi Wahala In Iya Gadon Siyasar Mahaifina —Salamatu Bakin Zuwo


Hajiya Salamtu Sabo Bakin Zuwo, diya ce ga Tsohon Gwamnan jihar Kano na farar hula na biyu, wato Alhaji Sabo Bakin Zuwo. Hajiya Salamatu ta kasance Shugabar kula da sashen siyasa na gidan Rediyon ‘Edpress’ da ke kano, kuma daya daga cikin Daraktocin gidan, sannan kuma fitacciyar ‘yar Jarida ce da ta yi fice, musamman wajen gabatar da shirin siyasa, wanda ta yi suna kuma ta shahara

Ita ce mace kwaya dada tal da hadaddiyar kungiyar masu saida bulawus ta jihar Kano, wato (BOSAK), karkshin Shugabancin  Alhaji Dayyabu Salisu da sauran Mataimakansa suka karrama, tare da wasu mutane a dakin taro na tunawa da Malam Aminu Kano, kamar irnsu  Nasiru Salisu Zango na ‘Freedom’ Radio, da sauransu. Wakilinmu da ke wurin taron, Mustapha Ibrahim Tela ya samu zantawa da Hajiya Salamatu. Ga yadda hirar ta kasance:

Da farko za mu so ki gabatar da kanki a takaice?

To ni dai Sunana Salamatu Sabo Bakin Zuwo, kuma an haifeni ne a Kano, a Karamar Hukumar Nasarawa, kuma duk karatuna na yi shi ne a nan Kano. Inda na yi karatun Difloma, na yi Digiri, na kuma yi Digiri na biyu, wato Masters Degreee ke nan a Turance. Duk karatuna na yi ne a kan harkar aikin Jarida. Kuma yanzu ina aiki ne a gidan rediyo mai zamankansa na ‘Edpress’ a Kano a matsayin Darakta mai kula da sashen siyasa, kuma daya daga cikin Daraktocin gudanarwa na Hukumar Radion a yanzu haka.

 

Yanzu haka Ke ce mace kwara daya tal da wannan kungiya ta BOSAK ta zaba ta ba ki lambar yabo. Ya ki ka ji a ranki?

To gaskiya na ji dadi kwarai da gaske, musamman yadda suka zabebeni suka ba ni wannan lambar yabo. Kuma ba mamaki sun yi haka ne sakamakon aikin Rediyon da nake yi na fadakarwa da ilmantarwa da kuma nishadantarwa, da kuma irin gudumawar da suke gani ina bayarwa a wannan aiki. To in haka ne suka yi la’akari da shi, sai in ce na gode Allah, kuma na yi farin ciki. Haka kuma, wannan abin alfahari ne sosai a ce al’umma ta lura kana bada gudumuwa har a ba ka lambar yabo. Ba shakka akwai kara karfin kwiwa a gareni.

 

Kasancewarki diya ga Tsohon Gwamnan Kano, Marigayi Alhaji Sabo Bakin Zuwo, a iya cewa kin gaji siyasa ke nan, kuma kika samu kanki a fannin kula da sashen siyasa na Radiyo. Wane kalubale kike fuskanta a aikinki na jarida?

To gaskiya a kwai kalubale mai yawa da nake fuskanta, musamman wajen daidaita jam’iyyoyin siyasa, kowa ya ga ka yi masa adalci kada ka zama ka jirkita da wani bangare na siyasa. Dole ka rika taka-tsantsan, domin kowa ya ga ka ba shi dama kamar yadda doka ta tanadar masa. Tunda mu gidan Rediyo, gida ne mai zaman kansa, hakan zai sa gidan ya zauna lafiya. Tunda ka san da an ce siyasa, ka san rigar siliki ce mai wuyar sawa, ma’ana tana da wahala sosai . Amma duk da haka ana jin mu kuma na sam dai mutanen Kano na jin irin kokarin da muke yi wajen ganin mun yi abin da ya kamata a wannan sashe namu na siyasa a gidan Rediyon ‘Edpress.’

 

Samun kanki a sashen siyasa kuma a Rediyo, na san ba za ki rasa samun wani mutum ko wata mace da suka yi siyasa da mahaifinki ba. Yaya kike ji a ranki da hakan ta faru?

To ba shakka ina fuskantar kalubale sosai, na sha samun kaina idan muna hira da wani mutum, sai ka ji ya ce “ a lokacin mun yi kaza da mahaifinki, a lokaci kaza na siyasa kaza.” Duk da ya ke wasu mutanen, musamman masu saurarona ba abin fassara da cewa fadar hakan kamar ana ban toshiyar baki ne, ni kuma ba na kallon haka, domin sai in ga cewa ba yadda za ka iya raba mahaifina da siyasa. Tunda ya taso yana siyasa, kuma har Allah ya karbi abinsa yana siyasa. Kuma duk wanda ya ambace shi, za ka ji yana yabonsa ne, ba kalubalantarsa yake ba.

Domin abin da za ka ji shi ne, a lokacin da yake raye, ya yi kaza, ya yi kaza na alheri. Ni kaina sai nake ganin abin a matsayin abin alfahari a gareni, tunda ina ganin da ba na wurin sai in ga kamar wani zai fada ba mahaifin nawa ba. Sai in ga kasancewar ina wurin ne, duk wasu ke ganin ya dace su fadi alkairin mahaifin nawa, wasu kuma suna ganin bai dace ba, saboda suna ganin kamar suna fama min mutuwarsa ce. Ni kuma ina alfahari da hakan, tunda duk kowa alkairinsa yake fada, kuma da ban kasance a wannan matsayin ba, da wani za a ambata ba shi ba, amma ganina ya sa ake ambatarsa har a yi masa addu’a. Wannan abin godiya ne ga Allah sosai.

 

Siyasa irinta su Marigayi Alhaji Sabo Bakin Zuwo siyasa ce ta akida, kuma hakan ya sa kullum za ka ji ana yabonsa a koyaushe. Kasancewarki ‘yarsa, kina da sha’awar shiga harkar siyasa?

Kai! Kai! Kai! Gaskiya da wahala, domin ka san siyasarsa da siyasa ce ta akida. Na san hakan ne kuma ta hanyar wani shiri da muke gabatarwa mai suna ‘Siyasar Jiya Da Yau,’ na siyasar da mai kama da tuna baya ko ma in ce waiwaye adon tafiya. Idan muna hira da ‘yan siyasar da, za ka ji suna cewa an yi kaza an yi kaza sai, ka ji irin wahalar da suka sha jiya, ba irn ta yau ba ce.

Sai ka ga wahalar da suka sha ba karama ba ce saboda akida. Yanzu kuwa abin ba haka yake ba, domin kasuwar bukata ce kawai ta ke ci, kuma yanzu bukatu sun yi yawa a siyasa. Sai ka ga sai ka yi taka-tsan-tsan soasai. Wannan yana sa ni tunanin in ba ka da abin duniya, yanzu ba za ka iya siyasa ba. Domin tun daga mazabarka za a kayar da kai, saboda ba abin da suke kira “kayan aiki!” Wato kudi. Domin siyasar yanzu sai da kayan aiki, kamar yadda Alhaji Sani Garka ke cewa, aiki sai da kayan aiki, wato kudin bayarwa.

 

Wata mastala da ake kuka da ita kan shirye-shiryen siyasa a gidajen Rediyo shi ne rashin iya baki, ko rashin saka wa baki linzami. Ke a matsayinki na Shugabar kula da sashen Siyasa na Rediyon ‘Edpress,’ kina da wata rawa da za ki taka, da ka iya kawo karshen wannan matsalar?

Gaskiya ne, muna iyaka kokarinmu don kawo gyara soasai wajen maganar saka wa baki linzami da ka fada. Za a iya sanin hakan ne ta hanyar gane yadda muke shan wahala wajen tantance kalaman da za su fito a cikin shirinmu na siyasa mai suna “Ido Ba Mudu Ba”. Wannan shiri ne na minti 25 zuwa 30, amma mukan dauki awa 10 domin tantance kalaman da za su fita don mai sauraro ya ji ba wata matsala ta cin mutuncin wani, kuma mu cika ka’idar aikin jarida da na NBC da dokokin gidan rediyon namu.

Kuma a wannan aiki, muna shan wuya sosai da jan aiki kafin hada wannan shiri na siyasa, wanda ya ba kowa ‘yanci, wanda ake kira da ‘Freedom Of Edpression.’ Amma duk da wannan jan aiki da muke yi. Idan mun sa shirin a lokacinsa sai ka ji wani ya bugo waya yana fada yana cewa, yaya aka yanke masa Magana? Mu kuma sai mun nuna masa cewa ai dole ne hakan, domin maganar ba ta kamata ba. To da haka dai mukan danne zuciyoyin masu maganar. Wannan ke nan.

Wani kuma idan an sa maganar wani da ba ta yi masa dadi ba, sai ka ji shi ma yana korafi. Ya ce an ce masa kaza, kuma ya ce hakan ya karya doka. Shi kuma wanda ya yi maganar ko kuma yake da ra’ayin hakan, sai ka ji ya bugo waya yana murna har da tafi rab-rab. To ka ji fa yadda abin yake. Amma dai muna iya kokarinmu kamar yadda na gaya maka.

Kuma kan wannan batu, ita ma gwamnatin Kano ta shirya wa sojojin baka bita, ta yadda za su tsarkake kalamansu na Rediyo, kuma ita ma Hukumar NBC ta wayar masu da kai, kuma mun bi ofishin Daraktan SsS na baya a kan tsarkake kalamai, da dai sauransu don ganin an kauda siyasar dabanci da sare-sare. Yadda sai dai ka je Rediyo ka huce haushinka cikin minti daya zuwa uku, maimakon da, da tafiya kawai kake sai dai ka ji wani kawai ya kwada maka mari, kuma ya ce aiko shi aka yi. Duk an kawar da wannan. Sai dai ka shiga rediyo ka isar da sakonka kawai.

To mu dai muna kokari sosai, domin ka san dokar fadar albarkacin baki, wato ‘Freedom Of Edpression’ (sashi na 39 da ya bada damar fadar albarkacin baki), fadi gareta, sai ka yi mata karatu sosai za ka fahimceta.

 

Daga karshe, me za ki ce?

To abin da na ke so in fada shi ne, Allah ya ji kan Mahaifana, wato Mahaifiyata da Mahaifina, Alhaji Sabo Bakin Zuwa, wanda irin dawainiyar da suka dauka ta ilmantar da ni da tarbiyyantar da ni, shi ne ya sa yanzu nake alfari da wannan dama da na samu daga garesu, wanda ba don sun tsaya a kan ilimina da tarbiyyata ba, da yanzu kila ban samu kaina a wannan matsayi ba, wanda nake alfahari da su, wanda da an ji ni za ka ji an ce Allah ya jikansu ya gafarta masu.

Wanda da a ce ina zaune ne a wani wuri daya, kila da hakan ba ta kasance yadda za a rika yi masu yawan addua’a da ambaton alkairi ba. To wannan ina godiya ga iyayena akan dawainiyar da suka yi da ni da ma sauran ‘yan’uwana wajen ganin mun tashi a hanya ta gari. To na gode masu, kuma na gode wa dukkan al’umma masu yi masu addu’a da ma sauran masu sauraronmu a kodayaushe. Kuma muna fatan ci gaba da addu’a a kan al’amuranmu koyaushe. Na gode, na gode.

Shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga Osinbajo – Sanata Makarfi


wp-1493459552544.jpg

-Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar PDP yace Buhari ya sauka daga karagar mulki

-Yace ya je ya huta har sai ya samu cikakken lafiya

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, Senator Ahmed Makarfi, yayi kira ga shugaba Muhammdu Buhari da ya mika ragamar mulki ga mataimkainsa Yemi Osinbajo.

Makarfi yace Buhari bai da lafiyan cigaba da zama a ofishi, da zai fi idan shugaban ya mika ragamar mulki ga Osinbajo kafin ya samu cikakken lafiya.

Yace: “ Wannan ba daidai bane kuma bai kamata ba. ra’ ayina shine shugaban kasan bai da karfin zama a ofis, da yafi kawai ya bayyanawa yan Najeriya saboda mataimakinsa ya cigaba a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga Osinbajo – Sanata Makarfi

“Wannna ba zancen ko dan APC bane ke rashin lafiya. Addu’ a na shine ya samu lafiya ya karashe mulkinsa.”

“A matsayina na dan siyasa, ina son ya kareshe mulkinsa. Idan mutane suka fara yada jita-jitan su, sun sani cewa babu wani amfani ga PDP idan Buhari bai sami daman karasa mulkinsa ba.”

“Muna son ya samu lafiya, muna son ya cigaba da mulki har 2019 saboda idan muka shiga zabe zamu kayar da APC”

“Bamu son wani rikicin siyasa a kasan nan.”

TATTAUNAWA: 2019 A Bauchi Sai Wanda Ya Damu Da Al’ummarsa —Batira


ALHAJI BUHARI BATIRA, shi ne Shugaban kungiyar wayar da kan matasa game da zaben shugabanni mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana a tsakanin al’umma. A cikin tattaunawarsa da wakilinmu a Bauchi, HAMZA ALIYU ya yi fashin baki game da halin da kungiyar take ciki tun lokacin da aka kafata watanni takwas da su gabata. Ga yadda tattaunawar ta kasan ce.

Farko za mu so ka fara gabatar da kanka?

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukacin Sarki. Kamar yadda kowa ya sani ne, an haifeni a cikin garin Bauchi a yankin Unguwar Bakaro, kuma ni dan Karamar Hukumar Bauchi ne. Na jima ina harkokin siyasa lokacin da Malam Isa Yuguda ya kafa gwamnati, mun yi PDP, kafin daga bisani kuma na fice daga tsohuwar jam’iyyarmu ta PDP.

Sannan kadan daga cikin manufofin da suka sa muka kafa wannan kungiya, shi ne mu wayar da kan talakawan jihar Bauchi game da irin mutanen da ya dace su shugabanccesu tun daga matakin dan Majalisar Dokokin jiha har zuwa kan Sanatoci da ‘yan Majalisar wakilai da Kansiloli da Shugabannin Kananan Hukumomi da uwa-uba Gwamnan jiha.

Ba a sanin mutumin kirki mai gaskiya da kamanta adalci sai ka ba shi wani mukami na siyasa, daga nan ne za ka fahimci inda ya dosa a siyasance.

Misali, jihar Bauchi ta yi Gwamnoni hudu daga shekara ta 1999 da aka dawo da mulkin farar hula. Daga cikin Gwamnonin akwai Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu, ya y i shekara takwas. Akwai Malam Isa Yuguda, wanda ya yi shekara takwas shi ma. Sai kuma Gwamna Mohammed Abubakar, wanda ya karbi ragamar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2015. Wadancan tsoffin Gwamnonin biyu kowa ya ga kamun ludayinsu a dandalin siyasar jihar Bauchi.

Tarihi shi ne babban fitilar da ke haska rayuwar kowacce al’umma. Saboda haka ina tabbatar maka da cewa daga yanzu ba za mu sake zaben mutumin da ba mu san irin gudumawar da ya bayar ga al’ummar Jihar Bauchi ba.

Akwai wani Tsohon Minista wanda daga Sanata ya tafi Abuja, daga bisani Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ba shi mukamin Minista, amma har ya kammala aikinsa babu abin da ya tsinana wa al’ummar da suka turashi Abuja. Yanzu haka rahotanni sun nuna cewa wai yana so zai tsaya takarar Gwamnan jihar Bauchi a zaben shekara ta 2019. Ina tausaya masa domin, ko gobe aka shirya zaben, tabbas zai sha kasa.

Domin yanzu kan talakawa ya fara wayewa, sai mutum ya nuna mana gudumawar da ya bayar ga ’yan jihar Bauchi a lokacin da yake rike da kujerar da ta fi ta Gwamna a Bauchi. Amma akwai wasu ‘yan jagaliyya a jikinsa, inda kullum suke rudinsa da cewa wai talakawan jihar Bauchi suna tare da shi dari bisa dari. wannan magana ya kamata ya fahimci cewa ba gaskiya ba ce, suna neman kudin aljihunsa ne kawai.

Misali, lokacin da Tsohon Gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda yake rike da kujerar Minista, duk wani dan jihar Bauchi, in dai zai fadi gaskiya, ya san cewa Yuguda ya taimaki ‘yan jiharsa, wanda sakamakon taimakon da ya yi ne talakawa suka tilasta masa da dole sai ya fito takarar kujerar Gwamna a 2007.

Amma shi wancan ya rike kujerar da ta fi ta Gwamna, kuma ko mutanen Unguwarsu ya gagara ya taimaka masu. Amma Allah ya kai mu zaben shekara ta 2019 da rai da lafiya, zai ga yadda akuya take rawa a rumfar zabe.

Wannan kungiya tana tsakanin talaka da mai mulki, komai girman mutum. Idan muka ga yana wasa da alkawuran da ya dauka ga talakawa, tabbas za mu sameshi mu bayyana masa kura-kuransa ko ya gyara ko kuma ya fuskanci fushin talaka a rumfar zabe, babu zagi babu duka.

 

Tun yaushe kuka kafa wannan kungiya?

Mun kafa wannan kungiya kimanin sama da watanni takwas da suka gabata, kuma Kananan Hukumomin jihar Bauchi 20 muna da mambobi masu dimbin yawa. Akwai mambobi da muka yi masu rijista sama da mutun dubu biyu, kuma kullum sai mun yi rijista ga sabbin mambobi a babban ofishinmu da ke cikin garin Bauchi.

 

Mambobin wannan kungiya ‘yan wata jam’iyya ne?

Mambobin wannan kungiya ba sa cikin kowacce jam’iyya. A halin yanzu babban abin da muka sa a gabanmu shi ne wayar da kan matasa da mata da sauran al’umma game da muhimmancin zaben shugabanni masu inganci da kamanta adalci daidai bakin gwargwado.

Duk mutumin da ya taimaki al’umma, ko a cikin wace jam’iyya yake za mu yayata manufofinsa ta kafafen yada labarai da hanyoyin sada zumunta na zamani.

Muna daga cikin wadanda suka yi wahala sosai ga Tsohon Ministan Abuja, Sanata Bala Muhammed, tun yana Sanata kafin daga bisani ya samu kujerar Minista, amma yanzu mun raba gari da shi kowa yana zaman kansa ne.

Na fada na sake fada, har abada ba za mu taba goyon bayan mutumin da ya ki ya taimaka wa talakawan jihar Bauchi ba. Idan kuma mutum yana ganin abin da muke fada karya ne, to don Allah ya tsaya takara a zaben 2019 zai ga bambanci tsakanin tsaki da tsakuwa.

 

Akwai wata shawara da za ka ba matasa ‘yan siyasa da ke jihar Bauchi?

Tabbas ina bada shawara ga daukacin matasan jihar Bauchi da kowa ya kama sana’a, domin ta haka ne kawai zai samu damar ci gaba da adawa mai amfani.

Bayan haka, ya kamata shugabanni su fahimci cewa yanzu ba lokacin da za a rika amfani da matasa ba ne wajen tada zaune tsaye, musamman a lokacin yakin neman zabe.

A zaben shekara ta 2019 za a samu gagarumin sauyi a dandalin siyasar Nijeriya, domin duk wanda ya fito takara sai an masa hisabi kafin a kada masa kuri’a, kuma za a yi adawa mai tsafta sakamakon yanzu babu maganar siyasar uban gida.

 

Wadanne matsaloli wannan kungiya take fuskanta a halin yanzu?

Babu wata matsala da wannan kungiya ke fuskanta a halin yanzu, domin kullum muna ci gaba da samun sabbin mambobi a ciki da wajen jihar Bauchi, sama da kashi-85-cikin 100 na mambobin wannan kungiya matasa ne zalla masu neman abin kansu.

Duk wani dan siyasar da ya samu dama ya gagara taimaka wa mata da matasa, to tabbas zai sha mamaki a rumfar zabe a shekara ta 2019, domin kudi ba zai yi amfani ba a lokacin yakin neman zabe, amma ‘yan kadan ne daga cikin ‘yan siyasa suka fahimci haka.

 

Mene ne sakonka ga daukacin jam’iyyun kasar nan?

Babban sakona ga daukacin jam’iyyun kasar nan shi ne ya kamata su yi hattara a lokacin da ‘yan takara suka kunno kai, domin akwai wadanda za su fitar da makuden kudade domin ganin sun lashe zabe a shekara ta 2019.

Dole su tabbatar da ingancin mutum kafin su bada sunansa ga Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, talaka zai yi cancanta ne a lokacin zaben, idan kuma suka yi son zuciya, to za su sha mamaki.

Sannan ina kira ga talaka kada ya kuskura ya sayar da katin zabensa ga wasu mutane ‘yan tsiraru marasa kishin kasa, wadanda babu abin da suka tsinana wa al’umma.

 

Daga karshe, mene ne sakonka ga al’ummar jihar Bauchi?

Kafin in ba da amsa, ina matukar godiya ga wannan jarida ta LEADERSHIP HAUSA da ta ba ni dama domin yin tsokaci game da dalilan da suka sa muka kafa wannan kungiya, Allah ya saka maku da alheri. Bayan haka ina kira da babban murya ga al’ummar jihar Bauchi da su fahimci cewa wannan kungiya ba mun kafata ba ne don cin mutuncin wani dan siyasa ko shugabanni ba. Kamar yadda na fada maka, duk wanda ya taimaki al’umma a lokacin da ya samu dama, za mu bayyana sunansa ko mutum zai hadiye ransa ne, babu ruwanmu.

 

Hukumar EFCC ta gano N17bn sakamakon sabon shirin cinne– Ibrahim Magu


-Ibrahim Magu ya bayyana yawan kudin da hukumar EFCC ta gano

-Yace suna zage damtse wajen yakan rashawa kafin ta hallaka Najeriya

-Shugaban NUJ ya nuna goyon bayansu ga hukumar EFCC

Mukaddashin shugaban hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, a ranan Alhamis 27 ga watan Afrilu 2017 ya bayyana cewa shirin tonan asirin da gwamnatin tarayya ta samarya taimaka wajen bankado kudi N17billion.

Magu ya bayyana wannan ne yayinda yake gabatar da wata takarda mai take ‘Kafin rashawa ta kashe Najeriya’, a taron bada lambar yabon gamayyar yan jaridan Najeriya, da akayi a Ladi Kwali Hall, Sheraton Hotels, Abuja.

A jawabin, wanda Dakta A. Bello ya wakilcesa yace, “ banda wasu abubuwan da aka gano sanadiyar shirin tonan asiri, hukumar EFCC ta gano kudade N521,815,000, $53,272,747, £122,890, da €547,730.”

Ibrahim Magu

“ Hukumar EFCC ta dukufa da ganin cewa ta ceto Najeriya da mutanenta kafin rashawa ta kashe ta. Muna kira gay an jarida da yan Najeriya na kwarai su bamu goyon baya wajen wannan yaki. Da kokarin gwamnatin Najeriya d akuma mutane, hukumar EFCC zata samu nasara.”

Magu yace sunyi kamu 62 cikin watanni 3 na fari wannan shekara.

A jawabinsa, shugaban gamayyar yan jarida, Abdulwaheed Odusile, yayi alkawarin goyon bayan kungiyar ga EFCC kuma ya yabawa hukumar akan kokarin da takeyi wajen yaki da rashawa.

Yayi kira ga hukumar ta cigaba da aikinta ba tare da tsoron kowa ba ko kuma son kai. Kana kuma ya soki majalisan dattawa akan rashin tabbatar da Magu a matsayin shugaban hukumar.

NAZARI: Ya Kamata Al’ummar Igbo Su Yi Koyi Da Halayyar Al’ummar Arewa


NAZARI: Ya Kamata Al’ummar Igbo Su Yi Koyi Da Halayyar Al’ummar Arewa

|

Assalamu Alaikum Warahamul Lahi Wabaratuhu. Ina kara godiya ga Allah Madaukakin Sarki daya ba ni rai da lafiya, tare da ba ni wannan dama domin yin kira ga ‘yan uwanmu ‘yan kabilar Igbo da ke Kudu maso Gabashin Nijeriya, da su zauna su yi karatun ta-natsu, ganin cewa ci gaban kowace kasa ya ta’allaka ne da hadin kan al’ummar kasar, musamman wajen samun damar gudanar da ayyuka da kasuwanci a duk inda mutum ya tsinci kansa ba tare da wata tsangwama ba.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akwai ‘yan Kabilar Igbo akalla Miliyan 20 da ke zaune a jihohi goma sha tara na Arewacin Nijeriya, goma sha shida daga cikinsu suna zaman dindindin, wato sun zama ‘yan gida, a yayin da ragowar Miliyan hudu kan Shiga su fita domin gudanar da harkokin kasuwancinsu, ba da wata tsangwama ba.

A waje daya kuma za ka iske akwai mutanen da suka fito daga yankin Arewa kimanin Miliyan hudu da kuma suke zaune a jihohi biyar na Kudu maso Gabashi, wato jihohin Igbo, kuma daga cikin wannan adadi, za ka iske Miliyan biyu daga cikinsu suna zaman dindindin ne, a yayin da ragowar Miliyan Biyu ke shiga suna fita wajen gudanar da harkokin kasuwancin su.

Idan aka yi duba na tsanaki, za a ga cewa a dukkan fadin Nijeriya a kasar Igbo ne, wato Inyamirai kadai ake haramta wa wani dan Nijeriya, wanda ba daga yankin ya fito ba samun damar shiga Jami’o’i, ko samun aiki, ko rike wani mukami na Siyasa. Kuma yawancin ‘yan Arewa da ke zaune a kasar Igbo masu sana’ar karfi ne, kama daga aikin Leburanci, aikin gadi, wankin takalma ko aiki a mayanka.

Hana rantsuwa, sau daya aka taba samun wani dan kabilar TIB mabiyin addinin kirista daga yankin Arewaci da ya taba gina gidan Mai a Shatale-talen Enugu, a can jihar Enugu. Amma ko da shi ma a lokacin da za a kaddamar, sai da ‘yan yakin suka hana a bude, bayan da suka fahinci cewa wanda ke da gidan man ba dan kabilar su ba ne, kuma ya fito daga shiyyar Arewa ne, inda  suka yi tsayin-daka kan sai dai a sayar wa wani dan kabilarsu ta Igbo, kafin su amince a bude.

A yayin da a yankin jihohin Arewa da na Kudu Maso Yammacin Nijeriya, za ka iske ba haka al,amarin yake ba, domin za ka ga a jihohin Kano, Lagos, Borno, Sokoto, Yobe da sauransu, za ka iske an sha ba ‘yan kabilar Igbo mukaman masu ba da shawara ga Gwamna da kuma mukamin Kwamishina, ko cin zabe a jihohin.

Ka duba duk girman babbar kasuwar garin Onitsha, za ka iske babu wani Bayerabe ko kuma mutumin Arewa da ya mallaki Shago, duk kuwa da cewa ‘yan kabilar Igbo na mallakar gidaje, manyan kantuna, ba tare da wata tsangwama  ba a yankin Arewaci da kuma Kudu maso Yammaci.

Idan kuma muka yi waiwaye kadan za mu ga cewa, Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim ya kasance mutun na farko da ya rike wannan mukami da ya ki tsarma ma’aikatan da ke ofishinsa, sai dai kawai ‘yan kabilar Igbo.

A nan ne nake kara yin kira ga ‘yan kabilar Igbo da su yi karatun ta-natsu, su yi koyi da sauran al’ummar shiyyoyin kasar nan, wajen baiwa dukkan wani dan Nijeriya damar gudanar da al’amuransa a yankinsu, ba tare da wata takura ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada.

Bissalam. Na gode.

Ibrahim Musa Gwangwazo, Tsohon Babban Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kwastan, Kuma Mataimakin Kwanturola mai ritaya. Kuma Tsohon Ma’aikacin BBC a London

 

Kiwon Lafiya: Amsoshin Tambayoyinku


Kiwon Lafiya: Amsoshin Tambayoyinku

|

Assalamu alaikum. Dr. Don Allah ina neman taimako a gareka. Ni dai na yi aure tsawon shekaru uku da wata bakwai, amma sai ya zamana matata ba ta taba samun ciki ba, kuma mun damu matuka, kasancewar auren zumunci ne. Na je wajen wani Likita, sai ya ce in yi mako daya ba tare da jima’i ba. Sannan sai in zuba masa maniyyina a wata roba da ya ba ni. Bayan da na kawo masa kamar yadda ya ce, sai ya yi gwaji, ya ce ’ya’yan haihuwana ba su da yawa, kuma ba su da karfi, hasali ma maniyyina ya yi ruwa-ruwa da yawa. Saboda haka sai ya ce min ba zan haihu ba. Wannan haka ne ya jawo matsalar da na rabu da matata, saboda gidansu sun matsu. Kuma ga shi yanzu ina so in yi aure. Dan Allah ko akwai wata shawara da za ka ba ni? Daga Adam Kaduna.

To Malam Adam,  abin da Likita ke nufin yana damunka, wanda a Turanci ana ce masa ‘azoospermia.’  Kuma ita wannan matsala akwai abubuwa da yawa da ke jawota.

Na farko, tana iya yiwuwa jikinka na halittar kwayoyin maniyyin, amma akwai abin da ke hanashi fitowa idan ka zo saduwa da mace. Saboda haka sai dai wani ruwa kawai ya fito. Wani lokaci kuma saboda rashin wasu sinadarai na jiki, to yana iya hana halittar kwayoyin maniyin baki daya. Saboda haka ya kamata a tabbatar an yi bincike an gano me ke kawo matsalar, saboda akwai wanda za a iya magancewa.

Saboda haka zan ba ka shawara, ka je wurin Likita kwararre a wannan fanni ya sake duba matsalarka, saboda akwai ci gaba da aka samu a wannan bangaren na kiwon lafiya kamarsu IBF da sauransu.

 

Shin Likita, wanda wasu kuraje suka fito masa a jikin zakarinsa masu kama da makero da kuma gwaljewa, yaya zai yi?

Ga dukkan alamu ka samu ‘infection’ ne, wanda har ya kai ga bullowa ta azzakarinka, Wannan yana iya zama ko abin da ake ce ma ‘genital warts,’ ko ‘gonorrhea,’ ko ‘chlamydia,’ ko ‘syphilis’ ko kuma ‘genital herpes.’ Wani lokacin, wadannan ciwowwukan suna iya zuwa da ciwo idan an zo fitsari, ko ka zo kana fitar da wani ruwa a gabanka. Abin da ya kamata ka yi shi ne, ka je asibiti a gwada fitsarinka da kuma jininka a gano wace irin kwayar hall ice ke kawo maka wannan matsalar, sai Likita ya ba ka magani.

 

Likita na ga sauran amsata a jarida, na ga matsalata da ta shafi ‘oberies’  dina ne a bayanin da da ka yi: Ina so ne Likita ya ba ni shawara, wane asibiti ya kamata na je, amma in son samu ne na fi son na ga Doctor da ya yi wannan bayanin?

Matsalar da ta shafi ‘obaries’ matsala ce da ya kamata a yi bincike da gwaje-gwaje sosai kafin a tabbatar da ita, ko kuma a iya maganinta. Idan an je asibiti an ga Likita kuma ana neman karin bayani, to ga Lambata nan, a turo man da sakon tedt, ko kuma ta email.

 

Zan iya zuwa kotu a kan ɓata-suna – Shekarau


Image caption

A zamanin mulkin Ibrahim Shekarau ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin Sheikh Ja’afar Adam a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yana bin kadin ɓata-suna da ‘yan sandan ƙasar suka yi masa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano wata takarda da ke alaƙanta Shekarau da kashe Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.

A cewarta jami’anta ne suka gano takardar bayan wani samame da suka kai gidan sanata Danjuma Goje a Abuja.

Mai magana da yawun Shekarau, Malam Sule Ya’u Sule ya ce ba shakka suna bin bahasin wannan batu a wajen ‘yan sanda.

Ya ce sun tuntuɓi ‘yan sanda a kan su fito su binciko gaskiyar wannan al’amari kuma su yi wa jama’a bayani.

Sule Ya’u Sule ya ce suna iya zuwa kotu a kan wannan ɓata-suna da ya ce an yi wa Ibrahim Shekarau.

Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN SENATE

Image caption

Sanata Danjuma Goje ya nisanta kansa da takardar kuma ya nemi ‘yan sanda su fayyace gaskiya

A cewarsa, takardar da ‘yan sanda suka yi iƙirarin sun gano a gidan Sanata Danjuma Goje tsohuwar takarda ce da wasu abokan hamayya suka rubuta don shafa wa Shekarau kashin kaji.

Ya ce “Ni ma ina da wannan takarda. Al’umma da yawa a Kano sun samu wannan takarda…Na tabbata wannan takarda ce wannan tsohon gwamna (sanata Danjuma Goje) ya samu. Idan kuma wata ce daban, ya kamata ‘yan sanda su fito su yi wa mutane bayani.”

Shi da kansa Malam Ibrahim Shekarau ne a wancan lokaci ya nemi ‘yan sanda su yi bincike a kan wannan takarda.

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam yayin sallar asubah a Kano.

‘A yi wa jama’a bayani’

Mai magana da yawun Shekarau ya ce ‘yan sandan sun yi bincike a kai kuma sun san abin da suka gano game da batun, don haka ya kamata su fito su yi wa al’umma bayani.

Da aka tambaye shi ko Shekarau zai ɗauki matakin shari’ah a kan wannan al’amari, ya ce suna jiran bayanin ‘yan sanda kafin su san mataki na gaba da za su ɗauka.

Sule Ya’u ya ce sun ji Sanata Danjuma Goje yana bayani ta kafofin yaɗa labarai inda ya tsame kansa, don haka Shekarau ya miƙa komai ga ‘yan sanda.

A cewarsa waɗanda suka fito suka yi wannan batu, a wajensu suke neman bahasi amma ba Sanata Goje ba.

Ya yi shaguɓe kan yadda wasu mutane da bai bayyana ko su wane ne ba, da ya ce burinsu a kullum su ƙulla wa tsohon gwaman sharri, “su je su ci gaba da yi.”

FAHIMTA FUSKA: Sheikh Ibrahim Khalil


A aiko da tambaya ta wadannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko leadershiphausa@yahoo.com ko kuma sakon ‘tedt’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: .

Malam, ni matashi ne; Ina neman shawara. Yarinya ce a ka yi ma na baiko kuma a ka sa ma na rana da ita, amma sai ta ke yi min wulakanci. Na yi-na yi a fasa auren, amma iyayena da nata sun ki, ni kuma na kai karshen hakuri.

Ba wai wulakanta ka ta ke yi ba; rashin fahimta ce. Hakuri za ka yi ku yi aurenku. Idan kun yi auren, komai zai canja. Haka ya ke afkuwa tsakanin saurayi da budurwa. Na biyu kuma, ka yi biyayya ga umarnin iyayenka.

 

Malam, don Allah me ya sa da na yi magana da budurwa sai maziyyi ya kama fita daga gabana?

Saboda shekarunka ne. Za ka daina; tashen balaga ne. Ba komai wannan.

 

Malam, shin mazhabar Ja’afariyya ita ce mazhabar da ’yan Shi’a su ke bi, kuma daga ina ta samo asali?

Mazhabar Ja’afariyya ta na daya daga cikin mazhabobi na Shi’a, amma kuma ta fi kowacce mazhaba ta Shi’a kusa da Ahlussunnah. Shi’a ba mazhaba kwaya daya ba ce; Ja’afariyya daya daga cikin mazhabobinta ne. Kamar yadda Ahlussunnah su ke da mazhabobi da yawa, Shi’a ma su na da mazhabobi da yawa. Ita mazhabar Ja’afariyya a na jingina ta ne da Ja’afarul Salikh, wanda daya ne daga cikin abokan Abu Hanifa ko kuma almajiransa kuma malamin Imam Malik.

 

Me ya sa Ja’afariyya ta fi kusa da Ahlussunnah?

Saboda ka’idojinta da tsarinta irin na Ahlussunnah ne mafi yawa, amma akwai inda su ka saba, amma a akida wannan ba za a ce akidarsu daya ba. Amma akidar da ke cikin Ja’afariyya ba ta Jafarul Salikh ba ce; ta Shi’a ce… Amma a Fikihu fa a ke zance. A Fikihu mazhabar Ja’afariyya ta fi kusa da ta Ahlussunnah. Shi ya sa ma a Azhar da wasu kasashe a ke karantar da mazhabobi guda biyar; Hannafiyya, Shafi’iyya, Malikiyya, Hambaliyya da Ja’afariyya. Har ma littafi a ka yi a kan wannan. A akida (ta Fikihu), shi Ja’afarul Salikh ai Ahlussunnah ne, amma a Shi’anci akidarsa ba ta Ahlussunnah ba ce.

 

Malam, na ga wasu idan sun dago daga sujjada ta biyu maimakon su mike sai su zauna su dan jira kafin su mike. Malam, yaya abin ya ke ne?

Eh, wannan ya ga dama ya yi, wanda ya ga dama kada ya yi. Malaman mazhabar Malikiyya da Hambaliyya da Shafi’iyya da Hanafiyya sun daina yi, domin an ruwaito hadisi na Malik Ibn Uwairis da ya yi ishara kan hakan, amma kuma ba ya daga cikin sunnar Sahabbai, domin da ya na daga cikin sunnar sallar da Imamu Malik ya yi ko Abu Hanifa ko Shafi’i ko Hambali, kuma manyan sahabbai ba sa yi.

 

Malam, menene hukuncin auren wanda ya ke saduwa da mace kafin ya aure ta? Ko akwai wani gyara da za a yi?

Babu wani gyara; kawai sai dai a ce a duba a gani shin bayan an ce an ba shi ita ne ya ke saduwa da ita ko kuwa kafin a ba shi ita ne. Idan bayan an ba shi ita ne, to ba shi ita da iyayenta su ka yi wannan ya yi maganin komai. Idan kuwa kafin a ba shi ita ne ya ke saduwa da ita, to shi ma aurensu ya na nan, amma bai kyauta ba, sai ya roki Allah gafara. Su ja bakinsu su yi shiru.

 

Malam, a gaskiya ni Ina da karamin zakari. To, yaya zan yi na rika biyawa iyalina bukata?

A’a, ba za a ce ka na da karamin zakari ba sai ka duba kanka; idan ya zamana idan zakarinka ya tashi ba ya wuce girman karamin dan yatsan hannunka na karshe, to wannan shi ne karamin zakari. Amma idan ya zamana idan zakarinka ya tashi ya na iya kaiwa tsawon daya daga cikin ’yan yatsunka na tsakiya guda uku, to ba karamin zakari ne da kai ba. Sai dai kawai ka nemi magani da zai kara ma ka karfin namiji… To, idan kuma ya zamana idan zakarinka ya tashi ba ya wuce karamin dan yatsan naka wanda cindo ya ke iya fito ma ka, to akwai magani da za ka iya nema wanda ya ke sa zakari ya karu.

 

Malam, don Allah kamar sau nawa ne idan mutum ya zargi matarsa da zina, aurensu ya baci?

Ko ya zargi matarsa da zina sai dubu aurensu ya na nan. Ba ya bukatar gyara tunda aurensu bai lalace ba… Wannan duk fada ne kawai cewa wai idan mutum ya zargi matarsa da zina aurensu ya baci. Aurensu ya na nan bai baci ba tunda ba sakin ta ya yi ba.

FITATTUN MATA: Kabita Krishnamurthy


FITATTUN MATA: Kabita Krishnamurthy

|

Ko Kun San?

Kabita (Sharadda) ta na daya daga cikin fitattun mawakan kasar Indiya. Saboda irin ficen da ta yi a harkar waka, Krishnamurthy ta yi ayyuka da daman gaske a fagen waka, kuma ta yi aiki da fitattun daraktocin mawakan Indiya, wadanda suka hada da R.D. Burman da A.R. Rahman da sauransu.

Kafin ta shiga harkar wake-wake, Sharada ta kama aiki ne a hukumar ilmin kasar, kafin daga bisani ta soma shiga fagen wake-wake tare da taimako da goyon bayan wata innarta, mai suna Madam Bhattacharya wadda ta fara da koya ma ta salon wakokin ‘Rabindra Sangeet.’ Ba ta jima ba, ta kara fadada tunaninta a fagen, inda rungumi salon wakokin nishadantarwa na tsagwaron yaren Indiyan, wanda a Turance a ke kira ‘Hindustani Classical Music,’ karkashin jagorancin fitaccen daraktan wakoki, Balram Puri.

Duk da karancin shekarunta a yayin da ta soma wakar, Kabita ta samu babbar lambar yabon Zinari a gasar wakoki da a ka gudanar a kasar. Ta samu wannan gagarumar nasarar ne a lokacin da ta ke ‘yar shekaru takwas a duniya. Ba ta gushe ba, ta na shiga gasanni ta na kuma samun fice a fannonin da ta yi wa tsararrakinta fintinkau.

A yayin da ta cika shekaru tara a duniya, fitacciyar mawakiyar ta yi sa’ar samun damar gogayya da fitacciyar mawakiyar kasar Indiya, Lata Mangeshkar, bisa jagorancin Hemant Kumar. Wani abin mamaki game da Krishnamurthy, duk da karancin shekarunta, ba ta gushe ba, tana yunkurin neman hanyar fadawa katafariyar masana’antar finafinan Indiya domin ta gwada sa’arta.  Ta samun nasarar hakan ne a lokacin da ta ke ‘yar shekara 14 a duniya. Shigarta fagen wakar finafinai, bisa taimakon fitaccen mai zanen kasar Indiya, Ranu Mukherjee, Sharada ta samu karbuwa da fice cikin dan kankanin lokaci.

Ba jimawa da fara wakar finafinai, ta kuma haduwa da mahaifiyar fitacciyar jaruma Hema Malini, wato Jaya Chakrabarthy, wadda ta kara gabatar da ita ga fitaccen daraktan wakoki a lokacin, Lasmikant a shekarar 1976.

Kasancewarta kwararriya a fanni waka, ba ta dauki tsawon lokaci ba, kamar sauran mawaka ba, sunanta ya mamaye farfajiyar shirin fim na Indian, musamman a fagen waka. A daidai lokacin ne tauraruwarta ta fara haskawa, inda a ka fara lissafa sunanta tare da fitattun mawaka irn su Lata Mangeshkar da Asha Bhosle.

‘Yar asalin birnin Delhi, an haifi Krishnamurthy wadda a ka fi sani da Sharada ne ranar 25 ga Janairun 1958, inda ta yi karatun zamani mai zurfi har ta yi digiri a fannin tattalin arziki a jami’ar St. Dabier a Mumbai.

A yau, ta na daga cikin fitattun matan da kasar Indiya ke ji da su a fagen kirkirarrun wakoki da nishadantarwa.

Ta yi wakokin finafinai da dama, inda ta samu lambobin yabo a ciki da wajen Indiya.

Tare da  Al-Amin Ciroma

 (08033225331)
ciroma14@yahoo.com

 

Ko wayar salula na iya warkar da ciwon suga?


Hakkin mallakar hoto
JSHAO

Image caption

Ta hanyar shafa fuskar wayar salular ana iya gane yawan sukarin da ke cikin jini

Masana kimiyya sun yi amfani da wayar salula ta smartphone don sarrafa aikin ƙwayoyin halitta a jikin wata dabba.

An haɗa kimiyyar rayuwar halittu ce da fasaha don sarrafa yawan sukari a cikin jinin wani ɓera mai fama da ciwon suga.

Ana iya amfani da wannan dabara wadda aka bayyana a mujallar kimiyya ta Translational Medicine wajen duba lafiyar masu fama da cutuka iri daban-daban.

Masu binciken na ƙasar China sun ce dabarar ka iya buɗe wani sabon babi a fannin ba da magani.

Mataki na farko ana sauya ƙwayoyin halittun jiki zuwa wasu masana’antu.

An sarrafa sigar ƙwayoyin gadon halittun don samar da magungunan da za su iya taƙaita ƙaruwar suga a cikin jini – amma ta hanyar karɓar saƙwanni daga haske.

Ana kiran wannan fasaha a kimiyyance da optogenetics kuma ƙwayoyin halittu kan faɗa aiki wurjanjan da zarar an dallare su da wani jan haske.

Fasahar dai tana amfani da wani ɗan ƙanƙanin ƙwan lantarki da kuma wata manhajar wayar salula da ke sarrafa shi.

Masu binciken a jami’ar East China Normal da ke Shanghai kan dasa wannan fasaha ce a jikin ɓera, ta yadda za su iya daƙile ciwon suga ta hanyar ɗan taɓa fuskar wayar.

Hakkin mallakar hoto
JSHAO

Image caption

Ana iya maƙala ‘yar na’ura a ƙarƙashin fata don sadarwa a tsakani

Ayarin masu binciken ya ce nazarin “ka iya share fagen wani sabon babi na ba da magani gwargwadon buƙatar mutum ta hanyar fasahar dijital da za ta karaɗe duniya.”.

Masana kimiyyar na buƙatar ɗiban wani ɗan ɗigon jini don sanin yawan sugan da ke cikinsa ta yadda za su iya ƙididdige adadin maganin da jiki yake buƙata.

Babban burinsu shi ne ɓullo da wani cikakken tsarin amfani da na’ura don gano yawan sugan da ke cikin jini da kuma daidai kimar sinadarin laƙani da za a bayar.

A bayyane take cewa fasahar tana wani matakin farko ne, amma dai ba za ta taƙaita ga magance ciwon suga ba. Ana iya sarrafa ƙwayoyin halittu ta yadda za su iya haɗa magunguna iri daban-daban.

Wani masanin kimiyyar rayuwar halittar curin sinadari, Farfesa Mark Gomelsky a Jami’ar Wyoming, ya ce nazarin wani “cikar buri ne mai sa shauƙi”.

Ya ƙara da cewa: “Nan da yaushe ne za mu sa ran ganin mutane na tafiya a kan titi sun ɗaura ‘yar wata fitila a hannunsu da za ta riƙa dallare ƙwayoyin halittun jiki da za su samar da wani magani da ƙwayoyin halittun gado suka sarrafa, ta hanyar amfani da wayar salula?

An ɗaure angon da ya yi wa baƙuwa fyaɗe


Hakkin mallakar hoto
MET POLICE

Image caption

Derry Flynn McCann ya amsa laifi kan tuhuma uku ta aikata fyaɗe da kuma yin fashi

An yanke wa wani ango hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda yi wa wata baƙuwa fyaɗe sa’o’i kafin ɗaura masa aure da abokiyar zamansa mai juna biyu.

A ranar 13 ga watan Janairu ne, Derry Flynn McCann ɗan shekara 28, ya auka wa wadda ya yi wa fyaɗe na tsawon sa’a biyu a yankin Hackney da ke gabashin London.

Kwanan nan aka sako shi daga gidan yari saboda aikata irin wannan laifi.

Wani alƙali a kotun Snaresbrook ya bayyana Derry McCann a matsayin “wani ibilishi” kuma ya ce sai ya yi zaman gidan yari na aƙalla shekara 9.

Yayin wannan fyaɗe na tsawon lokaci, McCann ya yi duka kuma ya muzanta wannan mata sannan ya ɗauki hotunanta ya sace mata waya.

A zaman da kotun ta yi cikin watan Maris a baya, Derry McCann na unguwar Hackney ya amsa laifinsa kan tuhuma uku ta aikata fyaɗe da kuma wata tuhumar kan cin zarafin ‘ya mace gami da tuhuma ɗaya kan aikata fashi.

Masu bincike sun yi imani cewa Derry ya biyo wata mata ce amma sai ta ɓace masa don haka sai ya auka wa wadda abin ya faru a kanta.

An fahimta cewa ko a shekara ta 2006 ma an ɗaure McCann kan aikata wani dogon fyaɗe da ya yi.

Bibiyar Trump : Me da me Shugaban ya cimma ya zuwa yanzu?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Donald Trump ya cika kwana 100 a kan mulkin Amurka

Donald Trump ya hau karagar mulki ne da alkawarin kawo sauyi ta fuskar siyasa a Amurka da kuma mayar da iko hannun mutane .

Don haka me shugaban ya cim ma zuwa yanzu? Muna bibiyar ci gaban shugaba Trump kan manufofinsa da kuma yadda Amurkawa suka karbe su.


Waɗanne matakan zartarwa Trump ya ɗauka?

Wata hanya da Shugaba Trump zai iya aiwatar da iko a siyasance ita ce bayar da umarnin zartarwa, abin da ya ba shi damar tsallake majalisar dokokin kasar wajen fitar da wasu manufofi.

Bai ɓata lokaci wajen amfani da wannan iko ba, ta hanyar janyewa daga yarjejeniyar cinikayyar Pacific da rusa dokokin kasuwanci da kuma yin gaban kansa wajen shimfiɗa bututan mai guda biyu.

Duk da yake, ana ganin ya yi amfani da umarnin zartarwa ta hanyar da ba a taɓa gani ba, shi ma shugaba Obama da ya yi mulki gabaninsa ya yi amfani da irin wannan umarni a makonninsa na farko a kan mulki amma dai Mista Trump ya zarce shi.

Shugaba Trump ya bayar da umarninsa ne da niyyar cika alkawuran yaƙin neman zaɓen da ya yi, amma tasirinsu na da iyaka.

Yayin da umarni irin na zartarwa zai iya sauya yadda hukumomin gwamnati ke amfani da kudadensu, amma ba zai iya bai wa waɗannan hukumomin kudaden gudanar da harkokinsu ba, ko ma damar gabatar da sabbin dokoki – wannan iko yana hannun majalisar dokokin Amurka.

Alal misali, umarnin Trump kan shirin kula da lafiya na ObamaCare ya yi shi ne domin rage tasirin tsarin, amma alkawarinsa na soke tsarin da kuma maye gurbinsa, zai iya tabbata ne kawai da taimakon majalisar dokokin Amurka domin yana bukatar sabuwar doka.


Yaya karbuwarsa take awajen Amurkawa?

A lokacin da Mista Trump ya karɓi rantsauwar mulki ranar 20 ga watan Janairu, ya yi haka ne da mafi ƙarancin karɓuwa a ƙuri’un jin ra’ayin jama’a da aka taɓa samu game da wani shugaban Amurka mai jiran gado.

Ya yi watsi da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar a matsayin wadda aka yi murɗiya, kuma ƙarfin adawar da ya fuskanta, ya fito fili a lokacin da dubban mutane suka fita zanga-zangar nuna ƙin jininsa bayan an rantsar da shi.

Yawancin shugabanni na fara wa’adinsu ne da gagarumar karɓuwa, amma Shugaba Trump ya sauya wannan tarihi a Amurka. Yayin da Shugaba George W Bush da Shugaba Obama suka samu amincewar fiye da kashi 60 cikin 100 na Amurkawa a lokacin da suka cika kwana 100 a kan karagar mulki, Mista Trump ya samu karɓuwar sama da kashi 40 ne kawai.

Mista Trump ya lashe zaɓe ne da amincewar mutane kaɗan a ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a. Saboda haka ba abin mamamki ba ne cewa waɗanda suka amince da shi tsiraru ne har yanzu. Amma ce-ce-ku-cen da alaƙarsa da Rasha ta janyo da kuma matakinsa na haramta wa ‘yan wasu ƙasashe shiga Amurka sun sa waɗanda suka amince da shi na ƙara raguwa.

Duk da haka, yunƙurin Mista Trump na soke wasu dokokin kasuwanci da kuma tsattsauran ra’ayinsa kan harkokin shige da fice sun burge da yawa daga cikin magoya bayansa. Baya ga haka an tabbatar da wanda ya zaɓa a matsayin ɗaya daga cikin alƙalan kotun ƙolin Amurka, abin da ya dawo da rinjayen masu ra’ayin riƙau. Karɓuwarsa a tsakanin masu ra’ayin riƙau ta kai sama da kashi 80 cikin 100 kamar yadda a baya.

Shin karburwar wata abar damuwace? Ta yiwu ba wata abar damuwa ba ce, a halin yanzu.

‘Yan jam’iyyar Republicans suna jagorantar majalisar wakilai da ta dattawan kasar, saboda haka ya kamata a ce zai iya neman cim ma manufofinsa na dokoki, ba tare da damuwa game da karɓuwarsa ba- muddin ya samu goyon bayan ‘yan jam’iyyarsa ta Republican.

Amma idan har karɓuwarsa ta tsaya ƙasa-ƙasa, ana tsammanin wasu muryoyi masu ƙin amincewa da shi, za su bayyana a cikin jam’iyyarsa, a daidai lokacin da ‘yan Republican ɗin ke fara nuna damuwa game da zaɓen tsakiyar wa’adi da za a yi a shekarar 2018.


Shin Trump ya dauki matakin daƙile shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba?

Harkar shige da fice ita ce Trump ya fi mayar da hankali kanta a lokacin yaƙin neman zaɓe kuma ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa domin cika wanna alkwari.

Ɗaya daga cikin umarnin da ya fara rattaba hannu a kai, shi ne ayyana cewar Amurka za ta gina katanga ko kuma wani shamaki wanda zai hana tsallako iyakar ƙasar daga Mexico. Nisan iyakar ya kai mil 650.

Amma Mista Trump yana buƙatar amincewar majalisar dokokin Amurka kafin ya iya fara wannan gini, kuma har yanzu bai samu amincewar ba. Ya haƙiƙance cewa Mexico za ta biya kuɗin daga baya, duk da yake, hukumomin ƙasar sun ce ko kusa ba za ta saɓu ba.

Ko da yake, Shugaba Trump bai sauya dokar shige da ficen Amurka ba tukunna, amma dai ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa guda biyu waɗanda suka nemi jami’an shige da ficen kasar su ɗauki tsauraran matakai wajen aiwatar da dokokin da kasar ke da su.

Akwai wasu alamu da ke nuna cewar sauyin yin aiki da dokar shige da fice – da kuma kausasan kalaman Shugaba Trump – za su iya rage yawan mutanen da ke son shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.

A watan Maris, yawan mutanen da aka kama a lokacin da suke ƙoƙarin shiga Amurka ya ragu zuwa adadi mafi ƙaranci a cikin shekara 17, in ji Sakataren ma’aikatar tsaron cikin gida.

Mista Kelly ya ce raguwar mutanen ba abin mamaki ba ne, kuma hukumar kula da shige da ficen Amurka ta ce umarnin shugaban ya sauya salon yadda lamari ke tafiya.

Batun sabon shugaban na dakile kwararar baƙin haure ya sa ana tunanin baƙin haure sun samu yadda suke so a ƙarƙashin Shugaba Obama, amma akwai dalilai da dama da ke nuna akasin haka.

Tsakanin shekara ta 2009 – 2015, gwamnatin Obama ta kori fiye da mutum miliyan 2.5 – yawancinsu wadanda aka samu ne da aikata wasu manyan laifuka ko kuma waɗanda ba su daɗe da shiga Amurka ba, abin da ya sa wasu suka riƙa yi wa Mista Obama laƙabi da “shugaba mai korar baƙi.”

Kimanin baƙin haure miliyan 11 ne ke zaune a Amurka, yawancinsu kuma daga Mexico.

Hukumar da ke aiwatar da dokar shige da fice da hana fasa-ƙwauri ta ƙaddamar da wasu jerin samame a fadin kasar tun da aka zaɓi Mista Trump, amma lokaci bai yi ba, da za a iya yanke hukunci a kan ko korar baƙin haure ya ƙaru ko bai ƙaru ba.


Yaya tattalin arziki ke gudana a karkashin Trump?

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasa a shekara 2009, Amurka na cikin karayar arziki mafi muni wadda ba ta taɓa samun irinta ba tun shekarun 1930, inda tattalin arzikin ya janyo rasa ayyuka 800,000 a watansa na farko.

Amma bayan ɗan koma-bayan da ya samu a shekarar, tattalin arzikin Amurka ya samu lokacin mafi tsawo yana bunƙasa, inda ya janyo samar da ayyukan yi masu ɗumbin yawa. An samar da jimillar aikin yi miliyan 11.3 a karkashin Shugaba Obama.

A baya Mista Trump ya yi watsi da waɗannan alkaluman a matsayin na boge, kuma bayan ƙaddamar da shi ya siffanta tattalin arzikin ƙasar a matsayin abin da ke cikin rikici.

Sai dai, wani sabon rahoton wata-wata da aka fitar a watan Maris da ke nuna cewa an samu karin ayyuka 235,000 a watan Fabrairu, ya sa Sakataren yada labaran fadar White House Sean Spicer cewa matakin, babban labari ne ga ma’aikatan Amurka.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 25 a cikin shekara 10 da kuma “zama shugaba mai samar da aikin yi mafi yawa da aka taba samu a tarihi.”

Ya yi zargin cewar Mexico da China suna sace miliyoyin ayyuka don haka ya sha alwashin “kawo ayyukanmu gida.” Amma wani bincike ya nuna cewa yawancin ayyukan ma’aikatun ƙere-ƙere da suka salwanta a shekarun baya -bayan nan, an yi asararsu ne saboda ƙwarewar da na’urorin masana’antu ke kara samu wajen iya aiki da kansu, sabanin iƙirarin cewa hakan ta faru ne saboda ana kai ayyuka ƙasashen waje.

Kasuwannin hannayen jari na Dow da S&P 500 da kuma Nasdaq sun kai matakan habakar da ba a taba samu ba a makonnin farko na mulkin Shugaba Trump, wata alamar da ke nuna cewar masu zuba jari sun samu ƙwarin gwiwa a kan ayyukan ababen more rayuwa da Mista Trump ke son yi tare da zame hannun gwamnati daga tallafi da kuma rage harajin da yake son yi.

Amma haɓakar kasuwannin uku ta ragu a watan Maris lokacin da aka fara tunanin garambawul ɗin harajin ba zai samu da wuri ba kamar yadda gwamnatin Trump ta fada.


Me gwamnatinsa ta yi kan kiwon lafiya?

Dole ne kiwon lafiya ya kasance wani fannin da za a fara gwada Shugaba Trump bayan ya yakin neman zabensa ya mayar da hankali kan batun.

Tsarin kiwon lafiya na Shugaba Obama ya taimaka wa fiye da Amurkawa miliyan 20 wadanda ba su da inshora a da domin samun inshorar lafiya- amman Trump ya sha alwashin cewar zai gaggauta soke dokar ya kuma maye ta da wata.

Daga baya ‘yan Republican sun gabatar da kudirin dokar samar da kiwon lafiyarsu a farkon watan Maris inda kakakin majalisar Wakilan kasar, Paul Ryan, ya siffanta shi a matsayin wani gagarumin garambawul na masu ra’ayin rikau.

Shugaba Trump ya goyi bayan kudirin, amman kudirin ya sami kakkausar suka daga hukumar kasafin kudin majalisar wadda ta ce zai kara Amurkawa miliyan 24 wadanda ba su da inshora zuwa shekarar 2026.

Gwanatin Trump ta ce ita ba ta yarda da bayanan hukumar kasafin kudin ta majalisar dokokin kasar ba, amman an yi fatali da kudirin ranar 24 ga wata Maris bayan ta kasa samun isasshen goyon baya daga ‘yan jam’iyyar Reuplican.

Wani yanayi ne na cin fuska ga Shugaba Trump da kuma jam’iyyar Republican, wadda ke shugabancin kasar da kuma jagorancin majalisun dokokin kasar a karo na farko cikin shekara 11.

Mista Trump ya yi iya kokrinsa na mantawa da kayen da kudirin ya sha, yana mai cewar gwamnatinsa za ta koma ta sake hada tsarin kiwon lafiyar bayan tsarin kiwon lafiyar ObamaCrea ta “fashe.”

Yayin da tsarin samar da lafiya na Obamacare ya fuskanci kalubale tun da aka kaddamar da shi a shekara 2010, bai nuna alamu masu yawa na faduwa nan gaba ba kuma bayanin hukumar kasasfin kudin majalisar dokokin kasar ya ce kasuwannin tsarin na kiwon lafiyar sun daidaita.

Wanna zai canza in Shugaba Trump da ‘yan jam’iyyarsa ta Republican suka dau matakin rage kudin tallafin tsarin, amma wanna zai kasance wani dabara mai hatsari gabannin zaben rabin wa’adi a shekara mai zuwa, musamman a lokacin da kuri’ar jin ra’ayin jama’a na baya-bayannan ke nuna cewar shirin Obamacare na kara samun karbuwa.

‘Yan Jami’yyar Republican sun dauki alkawarin samar da sabon tsarin kiwon lafiya bayan hutun Easter, amman babu tabbacin me nene ke cikin tsarin da kuma ko jam’iyyar za ta mara masa baya ko kuma tsarin zai samu isassun kuri’u damin ya zama doka.

TATTAUNAWA: Za Mu Iya Tara Naira Bilyan 20 A Duk Shekara Idan… — Injiniya Sidi


INJINIYA SIDI SADA MOHAMMED, Shi ne Daraktan Tsimi da Tanadi na Ma’aikatar Masana’antu na Tarayya. Wakilinmu Adamu Attahiru, ya samu damar tattaunawa da shi, jim kadan bayan kamala wani taron shekara-shekara da wannan sashe na “Weight  and  Measures” ya shirya a Abuja. Injiniya Sidi, ya byyana cewa muddin gwamnati ta sakar ma su mara, to za su iya tara naira bilyan 20 a duk shekara. Haka zalika ya tabo batutuwa da dama da suka shafi ayyukan sashen dake karkashinsa, da kuma irin kalubalen da suka yi sashen dabaibayi. Ga yadda tattauanwar ta kasance kamar haka:

A daidai wannan lokacin da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani babban kwamitin habaka tattalin Arzikin kasa domin warware kalubalen da ake fuskanta a kasar nan, ko wannan taro naku yana da nasaba da wannan kudurin?

Babu shakka wannan taron da muka gabatar, yana nuna irin kudurorin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ke  son cimma, domin wannan bangaren namu  na ‘Weight and Measures’ yana taka muhimmiyar rawa  wurin  farfado da  tattalin arzikin  kasa, abu ne wanda ya shafi hulda ko kuma cinikayya da kasashe daban-daban, da zarar aka samu kayan da ake fitarwa daga kasar nan sun samu inganci da  karbuwa a kasashen da  muke hulda da su, to  babu shakka za a ga ci gaba mai yawa ta hanyar yawaitar masu son saka hannun jari a nan  gida Nijeriya da  kuma  ketare.

Sai dai wannan ba zai samu ba sai wannan bangaren namu sun auna inganci ko kuma cikar ma’aunnin da  aka amince da shi a ko’ina a fadin duniya ba tare da tawaya ko haurewa ba, kamar yadda masu hikima ke cewa “Duk abinda ba za ka iya auna shi ba, to ashe ba za ka iya sarrafa shi ba  kuwa.”

 

Ya kake ganin wannan sabon kuduri na komawa kan harkar noma da ma’adinai domin rage yawan dogaro da man fetur da aka dade ana yi a Nijeriya?

Ai tun farko rashin bada muhimmannci ga wannan bangaren na tabbatar da cikakken ma’auni yana daga cikin matsalolin da sashen noma ya samu a wannan kasa. Yanzu idan ka koma ga tarihi a lokacin Turawan mulkin mallaka ne suka kirkiro wannan sashen namu watau “Weight and Measures” sanadiyar suna cinikayya da mu.  Amma babu wata hukuma a Nijeriya da ke kula da cikar ma’auni akan kayan da suke saye daga nan, alhali a can kasashensu suna da wannan tsarin, sai nan take suka kafa wannan sashen a wannan kasa kuma suka ba shi kulawa a lokacin cikin shekarun 1960, daga nan gwamnatocin da suka biyo baya sai suka daina bawa wannan sashen kulawar da ta dace, sai aka fara samun tawaya wurin kayan amfanin gona da ake tsallakawa da su kasashen ketare, sai kayan mu suka dai na samun karbuwa.

Yanzu Alhamdulillah, wannan gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari tana son ta farfado da wannan tsarin da aka yi fatali da shi a can baya, domin yanzu haka akwai wani kwamiti da ke karkashin kulawar mataimakin Shugaban Kasa wanda muna cikin wannan kwamitin domin ganin an magance wannan matsalar ta rashin cikar ma’aunnin kayan amfanin gona da kuma ingancin su, muddin ba a samu wadannan ba, to babu shakka ba za a samu ci gaba ta fuskar tattalin arzikin kasa ba.

 

Kamar yadda ka bayyana muhimmancin wannan sashen naku, shin yanzu kamar me kuke bukata domin inganta sashe?

Gaskiya muna da bukatu da dama, muna bukatar kayan aiki da kuma su kansu ma’aikatan duk da cewa shekarar 2015 an dauki kimanin ma’aikata 150, amma gaskiya ba za su isa ba, saboda haka muna bukatar karin ma’aikata da kuma motocin aiki domin yandu haka zancen nan da muke babu wata motar da ake amfani da ita ofisoshin mu na jihohi, bayan haka kuma muna bukatar kayan aiki domin rashin kayan aikin aune-aunenmu har ya sa ba mu iya zuwa wasu wuraren domin gudanar da ayyukanmu. Kuma abin kunya wasu kamfanonin idan muka je, mukan taradda na’urorin aune -aunensu sun fi namu inganci, kuma sun fi namu zama na zamani, alhali mu ne muka fi cancanta a gani irin wadannan ababe a wurinmu, ba wai mu gani a wurin wasu ba, amma idan aka fara amfani da sabon kasafin kudi na bana muna fatan wannan matsalar za ta kau.

 

Wane kira zaka yi wa ‘yan Nijeriya akan su rungumi akidar sayen kayan gida maimakon na kasashen ketare?

Zance na gaskiya babu abinda ya sa ‘yan Nijeriya suke sayen kayan kasashen waje sai tabbatar da ingancin su da kuma cikar ma’aunnin da ake auna yawan adadin da ake sayar da kayan, wannan shi yake nuna ana kula kuma ana karfafa hukumar da ke kula da cinikayya da tabbatar da cikakken ma’auni a kasashen, wanda muma a nan kasar mu Nijeriya idan aka ba mu irin wannan kulawar kayan da muke yi za su samu wannan matsayi a idon duniya.

 

Wane mataki kake ganin Nijeriya za ta dauka domin masu saka hannun jari da kafa masana’antu daga kasashen ketare za su shigo?

Wannan abu ne mai sauki ne idan aka tabbatar da ingancin wannan sashen namu na “Weight and Measures’ domin samun ingantattun kayan da ake yi a kasa shi zai sa ‘yan kasuwa kwadayin huldar kasuwanci da ita wannan kasar ba tare da fargaba ba.

 

Ranka ya dade wannan sashen da kuke jagoranta yana tara kudin shiga kamar yadda kowa ya sani, shin kamar nawa kuke tarawa a duk shekara?

Idan ka yi maganar tara kudin shiga, ina son ka gane cewa wannan sashen ya fi bada karfi wurin ganin an yi wa al’umma adalci wurin sayen kaya ba tare da shi mai sayarwa ya cutu ba, amma duk da haka muna tara kudin shiga domin idan za ka hada karfin kudin da zamu iya tarawa a shekara  za ka iya hada mu da hukumar tattara kudaden haraji ta kasa  (Federal Inland Rebenue Serbices) Saboda a wannan shekara mun ada kudurin tara naira Biliyan 20, idan muka samu ababen da na zayyana a baya  watau kayan aiki, karin ma’aikata da kuma motoci a fadin jihohin Nijeriya, rashin wannan shi ya sanya  a shekarar da ta gabata muka tara miliyan 400 kawai,  amma idan akwai kayan aiki tara Biliyan 20  ba wani  dogon aiki ba ne.

Za A Raba Kyautuka Ga Wadanda Suka Fafata a Gasar Fim Din Rariya


Za A Raba Kyautuka Ga Wadanda Suka Fafata a Gasar Fim Din Rariya

|

Kamfanin Sadau Pictures sun shirya tsaf, domin mika kyautuka ga wadanda suka samu nasarar lashe kyautukan da aka sanya a gasar da aka kammala ta rawar fim din Rariya.

Shugabar kamfanin, Rahama Sadau, ta bayyana a shafinta na Twitter, lokacin kadan ya rage a shaidawa duniya wadanda suka lashe wannan gasa da aka shafe tsawon wata guda ana fafatawa.

Kamar yadda suka sanya a shafukansu na sada zumunta: Twitter, Facebook da Instagram, SadauPictures sun bayyana cewar gasar ta rawa ce kadai, wadda ake son a kunna wakar fim din mai take ‘Tankade na yo na sa Rariya’ sannan a taka rawa wadda ta fi ta jaruman ciki.

Tuni dai matasa suka fara gudanar da wannan gasa a shafukan Instagram, inda suke taka rawa sannan su dora, yayin da su kuma kamfanin SadauPictures za su sake sakawa a shafukansu.

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin masana’antar shirya finafinan Hausa da wani kamfani ya bugi kirji tare da sanya gasa makamanciyar irin wannan. Wadda za a ci kyautuka da suka da: Talabijin, Kayan Sauti da kuma Fanka.

Shugabar kamfanin, jaruma Rahma Sadau ta bayyana a shafinta na Instagran cewar gasar ta kowa da kowa ce, kuma za a gabatar da wadanda suka yi nasara a gidan talabijin na Arewa24 karshen watan nan da muke ciki.

Yau dai kimanin mako uku kenan ana fafatawa a wannan gasa, inda kowa yake kokarin ganin ya zamo zakaran gwajin dafin da zai lashe, sannan ya samu ganawa da Rahma Sadau.

Fim din Rariya, na daga cikin finafinan da masoya kallon finafinai ke matukar tsumayi a halin yanzu, domin ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Rahma Sadau, Sadik Sani Sadikm Fati Washa, Hafsat Idris da sauran su. Babban darakta Yaseen Auwal ne ya bada umarni.

Babban abin da masoya wannan jaruma ke son ji yanzu shi ne, lokacin da za a saki fim din, domin sun yi tanadin yin fitar dango domin su kashe kwarkwatar da ta dade tana yawo cikin idon su.

 

Bibiyar Trump : Da-me-da-me Shugaban ya cimma ya zuwa yanzu?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Donald Trump ya cika kwana 100 yana mulkin Amurka

Donald Trump ya hau karagar mulki ne da alkawarin kawo sauyi ta fuskar siyasar Amurka da kuma mayar da iko ga mutane .

Saboda haka menene ya cimma ya zuwa yanzu? Muna bibiyar cigaban shugaban kan manufofinsa da kuma yadda Amurkawa suka karbe su.


Wanne matakan zartarwa Trump ya dauka?

Wata hanyar da Shugaba Trump zai iya aiwatar da ikon zartarwa a siyasa ita ce ta bayar da umarnin zartarwa wanda ya ba shi damar tsallake matakin doka a majalisar dokokin kasar kan wasu monufofi.

Bai bata lokaci ba wajen amfani da wannan ikon wanda ya yi amfani da shi wajen janyewa daga yarjejeniyar cinikayyar Pacific da rusa dokokin kasuwanci da kuma yin kan gabansa da gina layukan bututun mai biyu.

Duk da cewar ana ganin ya yi amfani da umarni irin ta yadda ba a taba gani ba, Shugaba Obama da ya yi mulki gabaninsa ya yi amfani da umarni kusan irin hakan a makonninsa na farko a kan mulki duk da cewar Mista Trump ya zarce mishi.

Shugaba Trump ya bayar da umarninsa ne da niyyar cika alkawuran yakin neman zaben da ya yi, amman tasirin su na da iyaka.

Yayin da umarnin irin na zartarwa zai iya sauya yadda hukumomin gwamnati ke amfani da kudadensu, ba zai iya bai wa wadannan hukumomin sabbin kudade ba ko kuma damar gabatar da sabbin dokoki- ikon yin hakan na hannun majalisar dokokin Amurka.

Alal misali, umarnin Trump kan tsarin kiwon lafiya na ObamaCare ya yi shi ne domin ya rage tasirin tsarin, amman alkawarinsa na soke tsarin da kuma maye gurbinsa zai iya kasancewa ne kawai da taimakon majalisar dokokin kasar domin yana bukatar sabuwar doka.


Yaya karbuwarsa ta ke ga Amurkawa?

A lokacin da Mista Trump ya sha rantsauwar hawa karagar mulki ranar 20 ga watan Janairu, ya yi hakan ne da mafi raunin karbuwa a kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka taba samu game da wani shugaban Amurka mai jiran gado.

Ya yi watsi da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar a matsayin wata kuri’a wadda aka murda, kuma karfin adawar da ya fuskanta ya fito fili a lokacin dubban mutane suka fita zanga-zangar kinsa bayan an rantsar da shi.

Yawancin shugabanni na fara wa’adinsu ne da gagarumar karbuwa, amman Shugaba Trump ya sauya wannan yanayin. Yayin da Shugaba George W Bush da Shugaba Obama suka samu amincewar fiye da kashi 60 cikin 100 na Amurkawa alokacin da suka cika kwanaki 100 kan karagar mulki, Mista Trump ya samu karbuwar mutum sama da kashi 40 ne kawai.

Mista Trump ya lashe zaben ne da amincewar mutane kadan a kuri’ar jin ra’ayin jama’a. Saboda haka ba abun mamamki bane cewar wadanda suka amince da shi kadan ne har yanzu. Amman ce-ce-ku-cen da alakarsa da Rasha ta janyo da kuma matakinsa na haramta wa ‘yan wasu kasashe shiga kasar sun sa wadanda suka amince da shi na kara raguwa.

Duk da haka, yunkurin Mista Trump na soke wasu dokokin kasuwanci da kuma tsatsaurar ra’ayinsa kan shige da fice sun burge da yawa daga cikin magoya bayansa. Baya ga haka an tabbatar da wanda ya zaba a matsayin daya daga cikin alkalan kotun kolin kasar, abin da ya dawo da rinjayen masu ra’ayin rikau. Karbuwarsa a bangaren masu ra’ayin rikau tana sama da kashi 80 cikin 100 kamar yadda ta ke da.

Shin karburwar wata abar damuwace? Ta yiwu ba wata abar damuwa ba ce, a halin yanzu.

‘Yan jam’iyyar Republicans suna jagorantar majalisun wakilai da ta dattawan kasar, saboda haka ya kamata ace zai iya nemi cimma manufofinsa na dokoki ba tare da damuwa game da karbuwarsa ba- muddin ya samu goyon bayan ‘yan jam’iyyarsa ta Republican.

Amman in har karbuwarsa ta tsaya kasa-kasa, sai a tsammanci wasu muryoyi masu kin amincewa da shi su bayyana a cikin jam’iyyar a daiden lokacin da ‘yan jam’iyyar Republican ke fara nuna damuwa game da zaben tsakiyar wa’adi na shekarar 2018.


Shin Trump ya dauki matakin dakile shiga kasar ba bisa ka’ida ba?

Harkar shige da fice ita ce Trump ya fi mayar da hankali akai a lokacin yakin neman zabe kuma ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa domin cika wanna alkwarin.

Daya daga cikin umarnin da ya fara rattaba hannu akai ya ayyana cewar Amurka za ta gina katanga kokuma wani shamaki wanda ba za a iya wucewa ba a kan bakin iyakan kasar da Mexico, wurin da ya ke da mil 650 na katanga.

Amman Mista Trump yana bukatar amincewar majalisar dokokin kasar kafin a fara ginin, kuma har yanzu bai samu amincewar ba. Ya hakikance cewar Mexico za ta biya kudin daga baya, duk da cewar shuwagabanninta sun fadi akasin hakan.

Duk da cewar Shugaba Trump bai sauya dokar shige da ficen Amurka ba tukunna, ya rattaba hannu kan umarnin zartarwa biyu wadanda suka umarci jami’an shige da ficen kasar su dau tsatsaurar matakai kan aiwatar da dokokin da kasar ke da su.

Akwai wasu alamun da ke nuna cewar wannan sauyin yin aiki da dokar shige da fice -da kuma kakausar kalaman Shugaba Trump- za su iya rage yawan mutanen da ke son shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.

A watan Maris, yawan mutane da aka kama a lokacin da suke neman ketarawa zuwa Amurka ya fadi zuwa mataki mafi karanci cikin shekara 17, in ji Sakataren ma’aikatar tsaron cikin gidan kasar.

Mista Kelly ya ce faduwar yawan mutanen ba abin mamaki ba ne, kuma hukumar kula da shige da ficen kasar ta ce umarnin shugaban ya sauya salon yadda lamari ke tafiya.

Maganar sabon shugaban na dakile kwararar bakin haure ya sa ana tunanin bakin haure sun samu yadda suke so a karkashin Shugaba Obama, amman akwai dalilai da dama da ke nuna akasin hakan.

Tsakanin shekara 2009-2015 gwamnatin Obama ta kori fiye da mutum miliyan 2.5- yanwacinsu wadanda aka samu da nau’o’i na manyan laifuka ko kuma basu dade da zuwa kasar ba abin da ya sa wasu suka yi wa shugaba Obama lakabi da “shugaba mai korar baki.”

Amman kimanin bakin haure miliyama 11 ke zama a Amurka, yawancinsu daga Mexico.

Hukumar da ke aiwatar da dokar shige da fice da ta hana fasa kauri ta kaddamar da wasu jerin samame a fadin kasar tun da aka zabi Mista Trump, amman lokaci bai yi ba da za a iya yanke hukunci kan ko korar bakin haure ya karu ko bai karu ba.


Yaya tattalin arziki ke gudana a karkashin gwamnatin Trump?

A lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasa a shekara 2009, Amurka na cikin kariyar arziki mafi muni wanda ba taba samun irin sa ba tun shekarun 1930, inda tattalin arzikin ta rasa ayyuka 800,000 a watansa na farko.

Amman bayan faduwa kadan a shekarar, tattalin arzikin Amurka ta samu lokacin mafi tsawo na ci gaba inda ta fi samar da ayyukan yi. An samar da jumullar aikin yi miliyan 11.3 a karkashin Shugaba Obama.

A baya Mista Trump ya yi watsi da wadannan alkaluman a matsayin na boge, kuma bayan kaddamar da shi ya siffanta tattalin arzikin a matsayin abin da cikin rikici.

Amman a lokacin da aka fitar da wani rahoton wata-wata a watan Maris wanda ya nuna cewar an samu karin ayyuka 235,000 a watan Fabrairu, Sakataren yada labaran fadar White House Sean Spicer ya ce babban labari ne ga ma’aikatan Amurka.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya sha alwashin samar da ayyuka miliyan 25 a cikin shekara 10 da kuma “zama shugaba mai samar da aiki mafi yawa da aka taba yi.”

Ya yi zargin cewar Mexico da China suna satan miliyoyin ayyuaka kuma ya sha alwashin “kawo ayyukan mu gida.” Amman abincike ya nuna cewar yawancin ayyukan kere-kere da suka salwanta a shekarun baya-bayannan an yi asararsu ne sabili da mashunan masana’antu kara samu kwarewar iya aiki da kansu, sabanin cewar hakan ya faru ne domin ayyuka sun fita waje ne.

Kasuwannin hannayen jari na Dow da S&P 500 da kuma Nasdaq sun kai matakan habaka irin wadanda ba a taba samu ba a makonnin farkon Shugaba Trump, wata alamar da ke nuna cewar masu zuba jari sun samu kwarin guiwa kan ayyukan ababen more rayuwar da Mista Trump ke son yi tare da zame hannun gwamnati daga tallafi da kuma rage harajin da ya ke son yi.

Amman habakar kasuwannin uku ta ragu a watan Maris a lokacin da aka fara tunanin garambawul din harajin ba zai faru da wuri ba yadda gwamnatin Trump ta fada.


Me gwamnatinsa ta yi kan kiwon lafiya?

Dole ne kiwon lafiya ya kasance wani fannin da za a fara gwada Shugaba Trump bayan ya yakin neman zabensa ya mayar da hankali kan batun.

Tsarin kiwon lafiya na Shugaba Obama ya taimaka wa fiye da Amurkawa miliyan 20 wadanda ba su da inshora a da domin samun inshorar lafiya- amman Trump ya sha alwashin cewar zai gaggauta soke dokar ya kuma maye ta da wata.

Daga baya ‘yan Republican sun gabatar da kudirin dokar samar da kiwon lafiyarsu a farkon watan Maris inda kakakin majalisar Wakilan kasar, Paul Ryan, ya siffanta shi a matsayin wani gagarumin garambawul na masu ra’ayin rikau.

Shugaba Trump ya goyi bayan kudirin, amman kudirin ya sami kakkausar suka daga hukumar kasafin kudin majalisar wadda ta ce zai kara Amurkawa miliyan 24 wadanda ba su da inshora zuwa shekarar 2026.

Gwanatin Trump ta ce ita ba ta yarda da bayanan hukumar kasafin kudin ta majalisar dokokin kasar ba, amman an yi fatali da kudirin ranar 24 ga wata Maris bayan ta kasa samun isasshen goyon baya daga ‘yan jam’iyyar Reuplican.

Wani yanayi ne na cin fuska ga Shugaba Trump da kuma jam’iyyar Republican, wadda ke shugabancin kasar da kuma jagorancin majalisun dokokin kasar a karo na farko cikin shekara 11.

Mista Trump ya yi iya kokrinsa na mantawa da kayen da kudirin ya sha, yana mai cewar gwamnatinsa za ta koma ta sake hada tsarin kiwon lafiyar bayan tsarin kiwon lafiyar ObamaCrea ta “fashe.”

Yayin da tsarin samar da lafiya na Obamacare ya fuskanci kalubale tun da aka kaddamar da shi a shekara 2010, bai nuna alamu masu yawa na faduwa nan gaba ba kuma bayanin hukumar kasasfin kudin majalisar dokokin kasar ya ce kasuwannin tsarin na kiwon lafiyar sun daidaita.

Wanna zai canza in Shugaba Trump da ‘yan jam’iyyarsa ta Republican suka dau matakin rage kudin tallafin tsarin, amma wanna zai kasance wani dabara mai hatsari gabannin zaben rabin wa’adi a shekara mai zuwa, musamman a lokacin da kuri’ar jin ra’ayin jama’a na baya-bayannan ke nuna cewar shirin Obamacare na kara samun karbuwa.

‘Yan Jami’yyar Republican sun dauki alkawarin samar da sabon tsarin kiwon lafiya bayan hutun Easter, amman babu tabbacin me nene ke cikin tsarin da kuma ko jam’iyyar za ta mara masa baya ko kuma tsarin zai samu isassun kuri’u damin ya zama doka.

Fim Din Mansoor Na Ci Gaba Da Samun Yabo Tun Kafin Ya Fita


Fim Din Mansoor Na Ci Gaba Da Samun Yabo Tun Kafin Ya Fita

|

Fim din yanzu haka ake jira ganin fitarsa, watau Mansoor, yana ci gaba da samun yabo a wurin masu sha’awar kallon finafinan Hausa.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne, shahararre kuma gogarman Kannywood, jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewar fim din kamfanisa, Mansoor da aka kammala dauka kwanan baya za a sake shi a sinumun Nijeriya lokacin bukukuwan karamar Sallah.

Jarumin ya bayyana haka ne yayin tattaunawar musamman da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce duba da yanayin irin aikin da aka yi wa fim din, kamfanin FKD sun yanke shawarar sakinsa a bukukuwan sallah.

“Mansoor fim ne da aka kashe makudan kudade wajen yin sa, saboda haka hanyoyin tallata shi kadai sun bambanta da yadda ake yi wa saura finafinai. Mun zabi lokacin bukukuwan karamar sallah ne domin domin bawa mutane damar kallon sa kasnacewar ana hutu.” A cewar Ali Nuhu.

Ya kara da cewa yadda ake tunanin fim din, ya wuce haka, domin salon labarinsa yana da matukar rikitarwa, har ila yau da kayatarwa, kawai dai lokaci ne zai bada damar ganin hakikanin sakon da yake dauke da shi.

“Mutane da yawa sun kagu su ga wane sako Mansoor ke dauke da shi, abin da nake so in tabbatar shi ne, fim din ya zo da wani irin salo wanda ba a saba gani ba.

“Duk wanda ya ga yanayin jaruman da aka sanya a cikin fim din, zai ga cewa sabbi ne, watau wadanda ba su taba fitowa a matsayin cikakkun jarumai ba. Da ma shi kamfani FKD ba bako ba ne wajen dauko kananan jarumai ya wanke su, sannan ya saka su a finafinansa.” In ji shi.

Mansoor fim ne da ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Abba El-Mustapha, Tijjani Faraga; sai kuma sabbin jarumai, Umar M Shareef da Maryam Yahaya.

Wannan dai shi ne fim na farko da FKD ta shirya tun bayan fim din da ya tara zaratan jarumai maza zalla watau Ga Mu Nan Dai.

Bin Diddigin Labarai: Danjuma Katsina Ya Samu Lambar Yabo


Daya daga cikin jajirtattun ‘yan jaridar da ake da su a Arewa, kuma daya cikin shugabannin kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Katsina, shi ne Danjuma Katsina, wanda kuma ya shahara a tsakankanin masu karatun jaridu, musamman ma na hausa, tsayayyen memba a kungiyar marubuta ta Nijeriya. A jaridun turanci kuma, masu karatu sun san rahotanninsa da ke fita a jaridar ‘Banguard.’

Domin ganin an karfafa gwiwa tare da yin godiya ga irin ayyukan alherai da raya kasa da wasu ‘ya ‘yan jihar Katsina su ke gabatarwa ga al’umma ne ya sa aka kirkiri bukin bayar da lambar yabon gwarazan Katsina ‘Katsina Heroes Award’ wanda ‘Pleasant Library and Book Club’ ta kirkiro.

Da ma Hausawa sun ce yaba kyauta tukwici, wannan ya sa ‘Pleasant Library and Book Club’ ya gabatar da bayar da lambar yabo ga gwarazan da su ka cancanta. An yi hakan ne domin ‘yan baya da masu tasowa su dauki darasi, kuma su mayar da hankali a kan dukkan fannin da su ke da kwarewa.

Cikin wadanda a ka ba wannan lambar yabo har da leburori da masu wasu ayyukan karfi. Wadanda su ka zabi su bi hanyar yin aiki da guminsu komi wahalarshi, a maimakon su nemi kudi ta wasu hanyoyin da basu dace ba. A wurin zabo su an yi la’akari ne da jajirjicewa, sadaukarwa, da kuma hidimtawa al’umma. Sannan an duba irin tasirin da ayyukansu ke da shi ga ci gaban kasa, da rayuwar jama’a.

A muhimman abubuwan da aka duba a ka bayar da lambar yabo akwai bangarori kamar haka: matukin keke Napep na shekara, mai bayar da hannu na shekara, gidan main a shekara, mai faci na shekara, mai wankin mota na shekara, mai kosa ta shekara, mai gyaran mota na shekara, mahauci na shekara, Dan kasuwa na shekara, mai dinki na shekara, dan sanda na shekara, direba na shekara, zakaran yanar gizo na shekara, malamin jami’a na shekara, malamin sakandare na shekara, malamin firamare na shekara, unguwar zoma ta shekara, likita na shekara, matukin babur na shekara, mai daukan hoto na shekara, kwararren kafinta na shekara, da sauransu.

A cikin wadannan lambar yabo da a ka bayar masu yawa ne, cbiyar ta ‘Pleasant Library and Book Club’ ta ga dacewar ta bayar da lambar yabo ga dan jaridan da ya fi kowanne bin diddigin labara, wanda a turance a ke kira da ‘Inbestigatibe Journalist of the year’. Wanda kuma bayan tantancewa da bibiya, su ka bayar da wannan kambu ga marubuci kuma dan jarida, Danjuma Katsina.

Mahalarta wannan taro ba su yi mamakin jin kiran sunan Danjuma Katsina da a ka yi ba, saboda lambar yabon da a ka ambaci sunanshi a karkashinta, babu wani dan jarida wanda ya dace da ita fiye da shi. Kafin a ayyana shi, sai da a ka bayyana irin matakan da a ka bi wurin tantancewa, da kuma sunayen wadanda a ka jero kafin a fid da Danjuma Katsina a matsayin gwarzon cikinsu.

Daga cikin muhimman abubuwan da su ka a Danjuma Katsina nasarar lashe wannan gasa akwai rashin tsoro, fede gaskiya komi dacinta. Musamman ma la’akari da irin hadurran da gaskiyarsa ta sha jefa shi a ciki, wanda a maimakon ya saduda ya daina bibiyan labarai masu hatsari, sai dai ma ya kara kaimi da dagewa.

Baya ga dadewa da ya yi ya na aikin jarida, Danjuma Katsina ya taba kasancewa mawallafi kuma shugaban kamfanin ‘Matasa Media Links’, kamfanin da ke wallafa mujallar Matasa, wata mujalla wacce ta yi tashe da suna a shekarun baya.

Sannan kuma a kungiyance, Danjuma Katsina shi ne tsohon mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Katsina. Wannan mukamin da ya rike bai hana Danjuma sakin labarai a hakikanin yadda su ke ba.

Bayan tagomashin amsan wannan lambar yabo daga ‘Pleasant Library and Book Club’, dan jarida Danjuma Katsina ya bayyana farin cikinshi da jin dadi da irin wannan muhimmanci da cibiyar ta bashi.

Ya bayyana cewa, “Ina daya daga cikin wadanda a k aba lambar yau a wannan rana, a matsayin dan jarida mai bin diddigin labarai na shekarar 2016. Na samu wannan gagarumar nasarar ne da taimako da kuma karfafawan da na rika samu a tsawon shekarun da na dauka ina aikin jarida da rubutu, musamman ma tasirin mu’amala ta da mutanen irinsu; Ibrahim Musa, Editan jaridar Almizan. Ibrahim Sheme, da sauransu.

“Duk lokacin da na gudanar da wani bincike na musamman a kan labara, na kan kira Ibrahim Sheme na bukaci da ya yi aiki da shi. Sheme ba ya gajiya da ni, ya kan gyara labarin ba tare da ya canza hakkin mallakarsa ba. Kuma daga cikin irin wadannan labarai na bin diddigi sun taimaka kwarai wurin samar da sauyi a salon da gwamnati ke tafiyar da lamurranta.

Danjuma Katsina ya kara da cewa, “Wallahi Tallahi, babu wanda ya sanar da ni cewa za a bani lambar yabo. Ni dai kawai na halarci taron ne kamar sauran mahalarta. Ko da na ji an kira sunana, sannan a ka fara zayyano irin ayyukan da na gudanar.

“Daya daga cikin ayyukan da a ka bayyana a wurin akwai wani rubutu da na yi, wanda Sheme ya wallafa min a jaridar ‘New Nigeria’, a lokacin ma ina dalibi ne. sai da abin ya bani tsoro da mamaki, yadda su ka iya bankado wannan rubutun.

“Sannan kuma akwai wani rubutu wanda na roki Abdul’aziz Abdul’aziz ya wallafa min a jaridar ‘Premium Times’, shi ma an bayyana shi cikin jerin ayyukana da su ka bani daman lashe lambar yabon. An lissafo irin gudummawar da na ke bayarwa ga jaridun Almizan, Aminiya, da kuma Leadership Hausa.” In ji shi.

Daga karshe, Danjuma Katsina ya godiya ga Allah da wannan tagomshi da kuma jama’a bakidaya. Ya ce; “Daga Allah ne,irin wannan karramawar da jama’a suka yi zabe,sannan alkalan gasar da ba ka san su ba,kuma ga ka Yaron da bai yi kwari ba sosai.Gaskiya ba karamin farin ciki na yi ba. Dole ne na yi godiya ta musamman ga Mahaifiyata, da wadanda suka zabe ni da wadanda ba su zabe ni ba. Godiya ga kamfanin ‘Bision Media Serbices’, da Mohammed Umar Babangida, da PLBC da jama’arta, da TMC Clothing, da Madugu Photography da Malik Anas da Ibrahim Abdullahi Yunusa”

Ba zan yi takarar shugaban Amurka ba – Michelle Obama


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Michelle Obama ta kira Trump da cewa “sabon shugaban kasa”

Mai dakin tsohon shugaban kasar Amurka Michelle Obama ta nuna yiwuwar ba za ta tsaya takarar shugabancin kasar ba a karon farko da ta fito bainar jama’a tun bayan fita daga fadar White House.

Mrs Obama, wacce ta fice daga ofis a lokacin da farin jinta a idon ‘yan kasar ya kai kashi 68 cikin (fiye da kashi goma kan mijinta) ta ce “siyasa na da matukar wuya.”

Ta bayyana haka ne a Orlando kwana kadan bayan Obama ya fito bainar jama’a a Jami’ar birnin Chicago karon farko tun bayan saukarsa.

“Komai zai rika tafiya daidai amma da ka soma takara za a yi ta sukarka.”

Ta ce hakan zai bai wa iyalinta wahala, tana mai cewa: “Ba zan bari ‘ya’yana su sake fuskantar matsala ba, saboda idan mutum yana takara ba shi kadai lamarin ke shafa ba har da iyalinka .”

Sai dai Michelle Obama ta ce bautawa al’uma shi ne kan gaba a rayuwarta.

An sallami jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu daga kurkuku


Hakkin mallakar hoto
Nnamdi Twitter

Image caption

Daya daga cikin sharudan ba da balin Nnamdi Kanu shi kar ya yi zanga-zanga

An saki jagororin masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga gidan yari bayan ya cika sharudan da wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta sanya masa.

A ranar Talata ne dai kotun, karkashin mai shari’a Binta Nyako, ta bayar da belin Mr Kanu saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sai dai ta sanya masa sharuda, wadanda suka hada da cewa ya gabatar da mutum uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

Mai shari’ar ta ce ba a yarda a gan shi a cikin taron jama’ar da suka wuce mutum 10 ba.

Ta kara da cewa “kar ya yi hira da ‘yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga”.

Wannan ne karon farko da aka bayar da belinsa tunda aka fara sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Mista Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, tare da wasu mutum uku, wadanda duka suka musanta zargin da ake yi musu.

Mista Kanu ya shafe sama da shekara guda a tsare.

Babban Burina In Koya Wa Mata Sana’a — Bilkisu Zangon Aya


Babban Burina In Koya Wa Mata Sana’a — Bilkisu Zangon Aya

|

Rashin sana’o’i ga mata, musamman matan da ke da aure yana kawo matsaloli masu yawan gaske a tsakanin mata da mazajensu, musamman matan da suka dogara da samun mazajensu, amma in har mace na da sana’a, to za ta tallafa wa kanta ta tallafa wa yaranta, a wasu lokuta ma ta tallafa wa mijinta wajen warware wasu matsaloli.

Wannan ne ya sa wakilinmu a Zariya, ISA BALARABE ya sami zantawa da wata baiwar Allah da ta yi fice wajen koya wa matan aure da kuma ‘yan mata sana’o’in dogaro da kai, wacce ke zaune a Zangon Aya da ke Karamar Hukumar Igabi a cikin jihar Kaduna, HAJIYA BILKISU ABDUL’AZIZ, inda  ta warware masa zare da abawa a gidauniyar da ta bude mai suna [A.A. NAS FOUNDATION];-

Yaushe kika bude wannan gidauniya ta koya wa mata sana’o’in dogaro da kai?

Na fara wannan gidauniya ne a shekara ta 2014 a nan garin Zangon Aya ta Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna. Kuma dalilin fara gidauniyar shi ne, lurar da na yi na yadda mata ke cikin matsalolin rashin sana’o’in dogaro da kai, kuma matsaloli da daman a wuyansu da suka shafi yaransu da kuma batun zumunci.

 

Kin fara da mata nawa?

Na fara da mata 160, wadanda suka fito daga sassa daban-daban na Karamar Hukumar Igabi. Kuma na fara da koya masu sana’o’in da suka hada da saka, dinki, man shafawa da kuma yadda ake yin sabulai. Na kuma dauki maza na fara koya masu yadda ake yin takalma.

 

Akwai dalilin da ya sa kika fi mayar da hankali wajen koya wa mata sana’o’in da kika ambata?

Babban dalilin shi ne, mata su sami yadda za su dogara da kansu su samu kansu, ba wai su dogara da samun mazajensu ba. Kuma a yau ana samun tangardar aure da dama ta dalilin tsadar rayuwar da ake ciki, mai gida ba shi da shi, uwar gida ba ta da shi, ka ga in ba a kai zuciya nesa ba, sai a sami matsala. Amma in mace tana da sana’a za ta tallafa wa kanta ta kuma rungumi matsalolin yaranta da hannu biyu, ka ga duk gidan da hakan ya tabbata, za ka cimma gidan ana zaune lafiya.

 

Wadanne matsaloli kika fuskanta a lokacin da kika fara rungumar wannan shiri?

Da farko mazajen da ba su gane muhimmancin koya wa matansu sana’o’in ba, ko da sun fara zuwa inda ake koya masu sai su hana matansu zuwa. Amma da wasu matan suka koya, aka ga rayuwarsu ta canza, sai mazajen suka fara barin matansu suna halarta.

Wani abin jin dadi shi ne, wasu mazajen ma da kansu suke zuwa cibiyarmu suna karbar fom na koyon sana’a domin matansu. Kuma kyauta muke raba fom na shiga cibiyarmu, ba ma karbar ko da kwabo daya.

 

Kin taba samun wani tallafi daga gwamnati a wannan cibiya?

Ban taba samun wani tallafi daga gwamnati ba. Mun nema, amma ba mu samu ba. A tarurrukan da muke yi na yaye wadanda suka kammala koyon sana’o’in, gwamnatoci kan turo wakilansu, suna yi mana alkawarin tallafi, amma har yanzu ba abin da ya zo mana. Muna addu’ar Allah ya ba su ikon tallafa mana.

 

A karshe, ko akwai shawarar da za ki ba gwamnatoci kan batun sana’o’i, musamman ga mata da matasa?

Shawarar ita ce, gwamnati ta dubi wahalolin da muke ciki, na koya wa al’umma sana’o’i ba tare da samun wani tallafi ba, ko da in mun kammala koya wa matan sana’o’in da kuma mazajen, da a ce gwamnatoci  za su rika shiga ayyukan da muke yi, da an kawo karshen matsalolin rashin sana’o’i ga al’umma a yau.

 

Canjaras ya ishe mu zuwa gasar Zakarun Turai – Antonio Conte


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ya ce daukar kofin Premier ne babban burinsa a yanzu.

Kocin Chelsea ya ce samun nasara ko yin canjaras a wasansu da Everton ranar Lahadi zai tabbatar musu da samun gurbi a wasan Zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Ya kara da cewa “lokacin da muka fara wannan kakar wasa, burinmu shi ne samun gurbi a gasar Zakarun Turai mai zuwa.”

“Wannan shi ne burin kungiyar, da magoya bayanta, da kuma ‘yan wasan. Amma a yanzu muna matakin da muke fatan daukar kofin,” in ji Antonio Conte.

Ya ce hakan “kyakkyawan ci gaba ne amma kuma daukar kofin Premier ne babban burinsa a yanzu.”

Kocin na Chelsea ya kara da cewa a fili take cewa biyu daga cikin kungiyoyi shida tsakanin Chelsea, da Tottenham, da City, da Arsenal, da United, da kuma Liverpool, ba za su samu gurbi ba a gasar Zakarun Turai mai zuwa ba.

Yana wannan maganar ne, lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi kan wasansu na ranar Lahadi da Everton inda ya tabbatar da cewa duk ‘yan wasansa sun shirya wa wasan.

Ya ce Everton kyakkyawar kungiya ce, kuma mai karfi, tana da manyan ‘yan wasa a tawagarsu, kuma kungiya ce mai karfi.

Asalin Abin Da Ya Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Matsi — Imam Abdulrahman


Asalin Abin Da Ya Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Matsi — Imam Abdulrahman

|

Limamin Babban masallacin idi na zangon Eyaen Benin, Malam Abdurahman Yola ya bayyana cewa muddin al’umman musulmi da sauran mutanen kasa suna ci gaba da bijirewa dokokin Ubangiji da umarninsa to lallai sai sun fada a cikin bala’i da masifu daban-daban cikin rayuwarsu.

Ya bayyana haka ne a cikin sakon da ya aikewa al’ummar musulmi a nasiharsa da ya yi a ranar Jumma’ar da ta gabata.

Malamin ya ce “saboda haka wannan masifar ta tsadar rayuwa da sauransu  gaba daya babu abin da ya sa Allah ya saukar da irinsu illa yawan sabo da barnace- barnace da mutane suke tafkawa a bayan kasa, saboda haka wajibine a koma ga Allah a tsarkaka zukatu, a tuba sannan mu dukufa da addu’o’i a masallatai da sauran wurare na ibada”.

Malamin ya kara jawo hankalin al’umman musulmi da kirista a kan su sanya tsoron Allah da kaunar juna a tsakaninsu inda yake ce wa “Musulmi da kirista gaba dayansu uba dayane ya haife su kuma shi ne Annabi Adamu saboda haka al’umman kasar nan ‘yan’uwan juna ne  su daina nuna wani banbanci a tsakaninsu kuma su sanya tsoron Allah a cikin harkokinsu na ibada da na mu’amila”.

Malam Abdulrahman ya jinjina wa gwamnatin tarayyar kasar nan a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da irin kokarin da ya ce gwanatinsa ta yi na samar da zaman lafiya.

“Wannan gwamnatin ta yi abin a yaba mata da ta samar da zaman lafiya a yankunan da wasu tsirarun mutane suka mayar da su hanyar zuwa barzahul.

Da ya juya a kan ‘yan siyasa kuma Malamin ya ce “Ci gaban kasar nan da zaman lafiyarta ya rataya ne a wuyar  zababbun ‘yan siyasa don haka ‘yan siyasan da aka zabe su shugabanni kuma  suka yi rantsuwa a kan za su yi wa kasa aiki na samar da ci gaba da zaman lafiya ya wajabta su cika wannan alkawarin domin babu shakka sai Allah ya tambayesu”, in ji shi.

An kama shinkafar waje ta miliyan hudu


Image caption

Manoman shinkafa suna kokawa da irin tasirin da fasa kaurin shinkafa ke yi kan harkarsu.

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya da ke kula da yankin jihar Kano da Jigawa ta ce ta kama wata tirela makare da shinka `yar waje da aka yi yunkurin fasa-kwaurinta zuwa Najeriya.

Kwanturolan yankin, Matias Abutu Onoja yace shinkafar kudinta ya kai fiye da naira miliyon hudu. A cewarsa an kama motar ne a kusa da Dutse hedikwatar jihar Jigawa.

Hukumar ta yi wannan kamun ne kwana biyu bayan zargin da kungiyar masu sarrafa shinkafa ta yi cewa ana fasa-kwaaurin shinkafa ta wasu iyakokin Najeriya da ke tudu.

Ko da wakilin BBC ya tambayi Konturolan kan me ya sa kamun na su na zuwa kwana biyu bayan masu noman shinkafa suka fara korafi kan fasa kaurin, sai ya ce su na kamun ne in har sun gano an shigo da kayan waje ba bisa ka’ida ba.

Ya ce hukumar tana neman masu shinkafar domin ta hukunta su.

Wannan na zuwa ne a lokacin da manoma ke kukan cewar fasa kaurin shinkafa na yi wa harkar su lahani.

Na dawo wa da Man Utd martaba da farin jininta – Mourinho


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Mourinho ya zo Manchester United a watan Mayun 2016

Mourinho ya ce ya dawo wa da kungiyar farin jini, da martaba, da armashin da ta rasa a hannun tsohon kocinta Louis van Gaal.

Kocin ya ce sababbin ‘yan wasa da za su zo kungiyar a kakar wasa mai zuwa “za su taimaka wajen samun manyan nasarori.”

An kori Van Gaal ne a watan Mayun shekarar da ta gabata, bayan ya lashe kofin FA, amma kuma ya kasa kai kungiyar gasar Zakarun Turai.

A kakarsa ta farko a Old Trafford, Mourinho ya ci kofin kalubale, kuma ana sa ran zai kammala gasar Premier a matakin kungiyoyin hudun farko.

Ya kuma taimaka wa kungiyar kai wa wasan kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ta Europa, inda za ta kara da Celta Vigo.

Ya ce “Ina tunanin Mista Van Gaal ya bar kyakkyawar kungiya, wadda ‘yan wasanta ke da alaka mai kyau a tsakaninsu”.

Sai dai sun rasa farin ciki, sun rasa karsashi, da martaba, amma wannan abin da suka samu yanzu zai taimaka wa kungiyar.

“Idan muka kara hada kungiyar ranar 19 ga watan Yuli kungiyar za ta zama mai karfi. idan sababbin ‘yan wasan suka zo, kungiyar za ta shirya wa samun manyan nasarori”, in ji Mourinho.

Wasan da kungiyar ta tashi canjaras ranar Alhamis tsakaninta da City, ya kara wa kungiyar yawan wasannin da ba a doke ta ba zuwa wasa 24.

Manchester United wacce yanzu ita ce ta biyar a kan tebur, da ratar maki daya tsakaninta da City, wacce ke mataki na hudu, wadda ita kuma ke bayan Liverpool da maki biyu tare da kwantan wasa daya. Za ta kara da Swansea ranar Lahadi mai zuwa.

Shugabancin Amurka na ba ni wahala —Trump


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mista Trump ya yi alkawura da yawa a lokacin yakin neman zabe

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana kewar rayuwarsa ta baya kuma yana mamakin yadda sabon aikinsa a fadar White House ke ba shi wahala.

Mista Trump ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “yana kewar rayuwarsa ta baya soboda yana da abubuwa da dama da zai yi a wannan lokaci.”

Ya kara da cewa “wannan aiki na bani wahala fiye da rayuwata ta baya. Na yi tsammani aikin na da sauki”.

Kusan babu wani lokaci da ya fi dacewa Mista Trump ya bayyana halin da yake ciki sama da yanzu.

Ya ce ”Ina kewar rayuwata ta baya”.

Wani ya rubuta a shafin sada zumunta na Twitter cewa ”Na san yadda Mista Trump ke ji. Ni ma ina kewar rayuwata kafin a zabe ni.”

Jama’a da dama sun ta yi wa shugaban ba’a kan kalaman nasa.

Wasu kuma suka ce Mista Trump, wanda tsohon mai gabatar da shirin ne a Talbijin, na da abubuwa da yawa da zai koya.

A don haka suna ganin ya fadi gaskiya, kuma halayyarsa ta yin hakan abin koyi ne.

Akwai kuma wadanda suka yi tambayar cewa abu da zai zamo mai zafi ga Mista Trump shi ne idan wata rana majalisa ta yanke shawarar tsige shi saboda bukatunsa na kansa sun shiga harkokin gwamnati.

‘Yan Karota Sun Karya Hannun Wata Tsohuwa A Kano


‘Yan Karota Sun Karya Hannun Wata Tsohuwa A Kano

|

A yau Juma’a da misalin karfe 12 na rana, wasu ‘yan karota suka yi sanadiyar karyewar hannun wata tsohuwa a daidai lokacin da suke yunkurin juya motarsu.

Wannan abu de ya faru a titin Sani Abacha Stadium da ke birnin Kano, inda ‘yan karotan suka taho daga titin Kofar Mata suna gota kofar shiga Stadium, sai suka yi yunkirin juya motar tasu domin komawa titin Kofar Mata, juyawarsu ke wuya sai suka buge mashin din adaidaita sahu, wanda hakan ya yi sanadiyyar karyewar hannun wata tsohuwa, saboda lokacin da abun zai faru ita tsohuwa ta sanya hannunta ne ta rike wani karfe dake jikin adaidaita sahun yayin da gaban motar ‘yan karota ya daki karfen da hannun tsohuwar yake, inda nan take hannun tsohuwar ya bankara har sai da kashin wajen ya fito.

Shi ma de direban adaidaita sahun da kyar ya tsira da wani dan karamin ciyo a hannunsa.

Bayan faruwar hakan de jama’a suka yi cincirindo, inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa, yayin da wasu fusatattu ke kokarin afkawa ‘yan karotan. Sai dai daga baya Allah ya takaita abin inda inda aka umarci ‘yan karaton su dauki tsohuwar da suka karyawa hannu su garzaya da ita asibiti domin samamata lafiya, inda nan take suka aikata hakan ba tare da bata lokaci ba.

RAHOTO: INEC Za Ta Fara Ba Da Katin Zaben 2019 A Nasarawa


RAHOTO: INEC Za Ta Fara Ba Da Katin Zaben 2019 A Nasarawa

|

Hukumar Zabe ta Kasa, reshen Jihar Nasarawa za ta fara ba da katin zabe na shekarar 2019 a gobe Asabar idan Allah ya kai mu a fadin jihar.

Da yake jawabi wajen taron masu ruwa da tsaki da bangarorin tsaron sakataren hukumar zabe mai zaman kanta reshen Jihar Nasarawa,  Mista Emanuel Aken ya ce za a ba da katin ne ga yaran da a baya basu isa yanka katin ba saboda shekarunsu bai kai ba yanzu kuma shekarunsu ya kai ga su yi zabe da kuma wadanda nasu katin ya bace. Ya ce za’a gudanar da ba da katin ne a runfunan zabe.

Da yake amsa tambayoyin bangarori na Jam’iyyun siyasar da suka taru a wajen kan yadda wasu jama’an kan hana wasu jefa kuri’a a mazabun da basu da rinjaye. Kamar idan wata jam’iyyar magoya bayanta na da rinjaye a wannan mazabar sai su hana masu son kada wa wata jam’iyyar kuri’a ko kuma hana  mabiya wasu addinan kada kuri’a a mazabun da basu da yawa, saboda nuna bambamcin addini? Sakataren ya ce “wannan ba daidai ba ne kuma dokar zabe bai ce haka ba dokar hukumar zabe ya baiwa kowa ‘yancin ya zabi dan takarar da ransa yake so. Kuma batun addini wannan ba karamin kuskure ba ne babu abinda ya hada harkan jefa kuri’a da maganar addini babu dan takarar da ya tsaya siyasa da sunan addini. Saboda hukumar zabe t ayi doka duk wanda aka samu da nuna daya daga cikin wannan dabi’an na kawo rudani cikin harkan zabe za a ci tararsa Naira 500,000. Ko zama gidan wakafi na shekara biyar”.

Ya kara da cewa hukumar zabe ba za ta yarda da masu kada kuri’a sau biyu ba kuma ba za ta amince da wadanda shekarunsu bai kaiba su kusanci wajen kada kuri’an.

Ya kuma yi kira ga wadanda ke fadin ma’aikatan zabe mafiya yawansu ba su goge ba wasu kuma ana amfani dasu wajen juya kuri’u su daina.

Ya ce za su dauki mataki kuma suna kira ga duk inda aka samu matsalar wannan abin a yi gaggawar sanar da su kuma za su tura hukuma wurin.

Tattali: Naira ta sha kasa kadan a jiya


wp-1493387668327.jpg

– Darajar Naira ta dan yi kasa kadan kuma a jiya Alhamis

– Naira ta sha kasa a kan Dalar Amurka

– Sai dai ba ta motsa kan sauran kudin kasar waje ba

NAIJ.com na da labarin cewa Dala ta dan girgiza kadan a kasuwar canji.

Dalar ta dan fadi kadan kan Dalar Amurka.

Sai dai ba ta sha kasa a kan wasu kudin kasar waje ba.

Naira ta sauka kasa

An dai saida Naira a bankuna kan N305 a jiya. Hakan dai na nuna cewa Dalar ta dan daga kadan a kan Naira. Pounds Sterling da kuma Dalar EURO suna nan su motsa ba. An kuma saida Dala a kasuwa a kan N390 kenan an samu karin kusan N2 daga yadda aka saida a Shekaran jiya.

Dalar dai tana da farashi dabam-dabam. Akwai na kasuwa, da na banki, akwai kuma na mahajjata, akwai na CBN da kuma farashin BDC na yan canji wanda duk mabanbanta ne. Dalar dai ta tashi ne daga N520 zuwa kusan N380

Babban bankin kasar nan watau CBN ya bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga cikin matsin da ta shiga na durkushewar tattalin arziki. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya bayyana wannan ne bayan ya ganan da Majalisar Dattawa.

Nigeria: An 'ceto jarirai sama da 200 da aka zubar' a Lagos


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rahotanni sun ce ana yawan zubar da jarirai a Najeriya

Gwamnatin jihar Lagos a Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto jarirai 237 da aka zubar a sassa daban-daban na jihar.

Jarirn 106 maza ne, yayin da 131 kuma suka kasance mata, kuma an jefar da su ne a bara.

Jaridar Punch da Guardian, sun rawaito cewa, kwamishinan matasan jihar, Uzamat Akinbile-Yussuf, yana ganin cewa an kara samun yawaitar adadin jariran da aka tsinta a watannin baya-bayan nan.

Yara na baya-bayan nan da aka tsunta su ne guda 53 da aka zubar a kusa da wata bola a jihar.

Wani wakilin BBC a Najeriya ya ce akan jefar da jarirai ne saboda iyayensu talakawa ne ko kuma an haife su ne ba ta hanyar aure ba.

RAHOTO: Kungiyar Dalibai Ta Karrama Jagoran Kwankwasiyya Na Sakkwato


RAHOTO: Kungiyar Dalibai Ta Karrama Jagoran Kwankwasiyya Na Sakkwato

|

Kungiyar Daliban Arewacin Nijeriya ‘Association of Northern Nigerian Students’ (ANNSA) ta karrama Jagoran Kwankwasiyya na Jihar Sakkwato, Hon. Malami Muhammad Galadanci (Bajare) bisa ga hobbasar kwazon sa na inganta sha’anin ilimi a mazabarsa, jiharsa da kasa baki daya.

A taron karramawar wanda aka gudanar a Sakkwato a makon jiya, Shugaban Kungiyar Mahmud Mahmud Talba ya bayyana Dan Majalisar mai wakiltar Mazabar Sakkwato Ta Arewa Ta (1) A Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato a matsayin wanda ya himmatu tare da bayar da kulawar musamman ga inganta sha’anin ilimi da gudanar da ingantaccen wakilci a ciki da wajen mazabarsa.

“A yau mun bayar da wannan lambar karramawa ne ga Honarabul Malami Muhammad Galadanci a bisa ga kokarin da yake yi na sauke nauyin da al’umma suka dora masa. Ayyukan da yake gudanarwa a fannin ilimi da bayar da tallafin karatu ga matasan mu abin yabawa ne kwarai ainun wanda ya kamata sauran masu hannu da shuni su yi koyi da wannan gwarzon dan siyasa.” Ya bayyana.

A jawabinsa na godiya, Jagoran na Kwankwasiyya ya bayyana cewar ba zai taba yin kasa a guiwa ba wajen shayar da al’ummarsa romon mulkin Dimokuradiyya. “Ba shakka wannan karramawar ta kara mani kwarin guiwar ci gaba da ayukkan da muke yi wa al’ummar mu.” In ji shi.

A yanzu haka dai Honarabul Galadanci sh ine Jagoran Kwankwasiyya na Jihar Sakkwato, akwai kuma dimbin magoya baya da suka rungumi akidar Kwankwasiyya dari bisa dari tare da sanya jar hula a kodayaushe baya ga sababbin Kwankwasawa da ake samu.

Jigo a Kwankwasiyya reshen Sakkwato Shafi’u Bakaluzin ya bayyana cewar “Dan Majalisar ya himmatu wajen marawa kokari da maufofin Gwamnati baya a fannin ilimi, kiyon lafiya, samar da ruwan sha, rage radadin fatara da taimakon marasa galihu da ‘yan rabbana ka wadatamu da sauransu da dama baya ga ayyukan majalisa da na kwamitocin da yake bayar da gudunmuwa.”

A kwanan nan ne dai Dan Majalisar ya rabawa al’ummar mazabarsa littaffan karatu da na rubutu da tufafin makaranta da kuma jakar makaranta na milyoyin naira.

Kayayyakin sun hada da littaffan rubutu dubu goma, tufafin makaranta na maza dubu biyar da na mata dubu biyar. Haka kuma akwai litaffan addini masu koyarwa kan tsarki kwafe dubu 20, da kuma littaffan da ke ilmantarwa kan sallah dubu 20, sai kuma jakar yara ‘yan makaranta guda dubu 10.

Matashin ya ce “Hon Galadanci ya gina dakunan bahaya guda 20 a cikin makarantar ‘Yan Mata ta Kofar Marke wadda ke da dalibai sama da dubu uku amma babu wajen zagayawa. Haka kuma ya dauki nauyin saka babbar kofar shiga makarantar Furamare ta Alhaji- Alhaji. Baya ga wannan a Makarantar Mazabar Waziri (C) ya gyara dakunan karatu gyara irin na zamani kamar kuma yadda ya inganta sha’anin ruwa da dakunan bahaya a asibitin Kangiwa wadda aka fi sani da asibitin Kofar Rini tare kuma da bayar da kayatar magani na dubu 500 kyauta ga marasa lafiya.”

Bincike ya nuna tun daga siyasar 1999 har zuwa 2015, Hon Malami Bajare shi ne dan majalisa na farko a tarihin siyasar Jihar Sakkwato da ya assasa tare da fara gabatar da taron jin ra’ayoyin al’ummar mazabarsa kan wakilcin da yake gudanarwa da yadda suke son wakilcinsa ya kasance.

A yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin sake gudanar da taron na ‘Town Hall Meeting’ kashi na biyu. Taron zai sake share hanyar gabatar da matsaloli, korafe-korafe da bukatocin al’ummar mazabarsa tare da samar da hanyoyin kawar da matsalolin su da inganta jin dadin su lamarin da suka bayyana da wakilci irinsa na farko.

Nazari ya nuna yadda ya samu nasarar gudanar da aikin Tantance Malaman Makarantun Furamare na Jihar Sakkwato a lokacin da yake Shugaban Kwamitin Ilimi na majalisa a zamanin Gwamnatin Aliyu Wamakko.

Babbar nasarar da aikin ya samu shi ne tabbatar da karin albashi mafi kankanta na naira 18, 000 ga Malamai. Haka kuma daga cikin adadin malamai dubu 38 da doriya da ke akwai a Sakkwato, an tantance malamai dubu 25 a matsayin malaman gaskiya.

Baya ga wannan, Honarabul Bajare ne dan Majalisar Jiha na farko da Tsohon Jakadan Kasar Amurka a Nijeriya James F. Entwistle ya yaba wa kan yadda yake gudanar da aikin majalisa bisa tsari yadda ya kamata.

 

Yan arewa masu ci-rani a kudu sun fara koma arewa


wp-1493387902030.png

– Daruruwan ‘yan arewa masaunar kudancin kasar na komawa gida domin fara shirye-shirye na aikin gona a wannan shekara da muke ciki

– Ba dukkanin yankin arewan ne daminar ta fadi ba, a wasu sassan na jihohin ba a fara alamar ruwan sama ba har yanzu

– Yayin da wadannan ‘yan ci-ranin ke kokarin tafiya gida, wasu kuma yanzu suke zuwa kudu da nufin za su fara ci-raninsu a wannan lokaci

A yanzu haka daruruwan ‘yan ci- rani wadanda suke ’yan asalin jahohin arewa da suke kudancin kasar nan sun fara tattara nasu-da-nasu suna koma arewa da nufin tarar damina domin fara shirye-shirye na aikin gona a wannan shekara da muke ciki.

Duk da kasancewa bayanai suna nunar da cewa ba a dukkanin yankin arewan ba ne daminar ta fadi ba, a wasu sassan na jihohin ba a fara alamar ruwan sama ba amma duk da hakan sun gwammace suna gida daminar ta same su a bakin gonakinsu.

NAIJ.com ta samu labari cewa wasu daga cikin matafiyar sun bayyana dalin da ya sa suke kokarin tafiya gida saboda sun ji an ce musu an fara ruwan sama don haka za su tafi domin fara aikin gona

A yayin da wadannan ‘yan ci-ranin ke kokarin tafiya gida, sai ga wasu kuma sun baro arewan zuwa kudu da nufin za su fara ci-raninsu a wannan lokaci.

Lovren zai ci gaba da zama a Liverpool


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dejan Lovren ya buga wasa 28 a kakar wasa ta bana

Dan wasan Liverpool Dejan Lovren ya sanya hannu akan sabuwar kwantiragi wacce za ta bashi damar cigaba da zama a kulob din har zuwa shekara ta 2021.

Dan wasan mai shekara 27 ya koma Anfield ne daga Southampton a kan kudi fam miliyan 20 a shekarar 2014.

Lovren bai taka rawar gani a kakarsa ta farko ba, amma duk da haka ya buga wasa 105 inda ya zura kwallo hudu.

Dan kwallon na Crotia ya ce ”Ina ganin a yau ni ne mafi murna a duniya.”

Ya kara da cewa burina shi ne in dade a kulob daya da nake so kuma shi ne Liverpool.

Lovren ya buga wasa 28 a kakar bana.

Yana haskaka wa sosai a karkashin koci Jurgen Klopp kuma yana cikin ‘yan wasan da ake ji da su, inda ake hada shi da Joel Matip domin tsare baya.

A lokacin da yake hira da shafin intanet na ya ce ”Bayan duk abin da ya faru a kaka biyu da ta gabata, ina ganin na fi kokari a kakar farko. Kulob din ya amince da ni, haka kuma magoya bayanmu.”

Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gidajen kallo na da farin jini sosai a Najeriya

Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta ce za ta girmama magoya bayanta da suka mutu bayan turken wutar lantarki ya fada kansu a lokacin da suke kallon wasa a birnin Calabar na jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, United ta ce ‘yan wasanta za su daura wani bakin kyalle a hannayensu a wasan da za su yi ranar Lahadi “domin tunawa da magoya bayanmu bakwai da suka mutu a kwanakin baya a Calabar da ke Nigeria.”

A lokacin da lamarin ya faru, wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya kirga gawar mutum 16, yayin da wasu rahotanni ke cewa wadanda suka mutu sun haura 30.

Amma mai magana da yawun ‘yan sandan Cross River, Irene Ugbo, ta shaida wa BBC cewa mutum bakwai ne suka mutu yayin da mutum 10 suka jikkata.

Lamarin ya faru lokacin da jama’a suka taru suna kallon wasan Europa tsakanin Manchester United da Anderletch.

A sakon da ya aike na ta’aziyya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kadu kwarai da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka.

Hakkin mallakar hoto
Manchester United

Image caption

United ta ce tana alhinin rasuwar magoya bayanta na Najeriya

Rahotanni sun ce gidan kallon ya cika makil da mutane a lokacin da babban layin wutar ya katse, inda ya fado kan jama’a.

Anthony Sunday ya ce “Ni da kaina na kirga gawarwaki sun kai 16, kuma jama’ar da ke wurin sun gaya min cewa adadin zai haura 31”.

Mista Sunday ya kara da cewa jim kadan bayan lamarin sai wurin ya rikide inda jama’a suka rinka gudu domin neman mafita.

An rinka zuba gawarwaki da wadanda suka samu raunuka a motar ‘yan sanda, in ji shi.

RAHOTO:Za A Kafa Kotunan Sulhunta Iyalai A Neja


RAHOTO:Za A Kafa Kotunan Sulhunta Iyalai A Neja

|

An yi kira ga ma’aikatar shari’a ta Jihar Neja da ta canja sunan gidan horar da kangararrun yara zuwa gidan kyautata tarbiyar yara.

Babbar darakta a Hukumar Kula da Hakkin yara, Barista Mariam Haruna Kolo ta yi wannan kiran a lokacin da ta ziyarci Alkalin Alkalan Jihar Neja, Mai shari’a Maryam Zukugi a ofishinta .

Barista Kolo ta ce lallai abin farin ciki ne ga mata na samun wannan matsayin na Alkalin-Alkalai na jiha musamman tare da kara daga darajar wasu alkalai mata masu kwazo a matsayin manyan alkalai a jihar. Dan haka yanzu lokaci ya yi da ma’aikatar shari’a ta jiha da hukumar kare hakkin yara za su aiki tare dan samar da kyakkyawan yanayi a bangaren shari’a a jiha, “muna bukatar a canja sunan gidan kangararrun yara zuwa gidan kyautata tarbiyan yara, bayan nan a yi nazari a kan dokokin jihar ta yadda za a iya samar da dokoki masu sauki ga kananan yara tare da shirya taron musamman na fadakar da alkalan majastare da na kotunan shari’a dan wayar da su kan tsare dokokin da suka shafi kananan yara”, a ta bakinta.

Barista Mariam Kolo ta jawo hankalin Alkalin Alkalan kan yadda wasu Alkalai ke karbar shari’o’i wanda ba ‘yan sanda ne suka gabatar da bincike akan su ba. A cewarta bisa doka ‘yan sanda kadai ke da alhakin shigar da kara a gaban alkali ba wani jami’in tsaron kaya na cibil defens ba, irin wannan akwai kuskure sosai a kai”.

Da ta ke jawabinta, Alkalin-Alkalan ta jiha, Mai shari’a Maryam Zukugi tace lallai shiri ya yi nisa wajen shirya taruka a kan wayar da alkalai a jihar, inda ta ce yanzu ma haka sun tura wasu alkalai halarta tarukan karawa juna sani a wasu jihohi.

“Bayan nan, ma’aikatar shari’a ta jiha da kungiyar alkalai tana nazarin kafa hukuma ta musamman dan zaman sulhu a kan rikice-rikicen iyalai da kan taso, kofa a bude take dan aiki kafada da kafada da wannan hukumar ta kare hakkin yara, yana da kyau a duk lokacin da hukumar ta yi nazari a kan wani abu muhimmi da ya shafi doka da ta tabbatar ta rubutowa ma’aikatar kai tsaye dan yin nazari da mika shi inda ya dace dan samar da kyakkyawan matsaya.

LLallai hukumar kare hakkin yara da ta tabbatar ta yi aiki tsakaninta da Allah wajen ganin ana bin hakkin kananan yara kamar yadda aka dora mata alhakin hakan”, in ji ta.

A karon farko malamai mata sun yi fatawa kan auren wuri a Indonesia


Hakkin mallakar hoto
BBC Indonesia

Image caption

Taron ya hada jagororin mata Musulmai daga kasashe da dama

Manyan malaman addinin Musulunci mata sun gabatar da wata fatawa a kasar Indunisiya a kan aurar da kananan yara.

An gabatar da fatawar ne a karshen taron kwana uku da malamai mata a kasar suka gudanar, sai dai dokar ba ta zama wajibi a yi amfani da ita ba.

Malaman sun bukaci gwamnati da ta mayar da mafi karancin shekarun da za a yi wa mace aure su zama 18, ba shekara 16 ba kamar yadda suke a yanzu.

Mafi yawancin ‘yan kasar Indunisiya Musulmai ne, kuma tana daya daga cikin kasashen da suke yawan aurar da kananan yara a duniya.

A cewar ofishin kula da kananan yara na Majalisar dinkin duniya, kashi daya ckin hudu na matan kasar ana aurar da su ne kafin su kai shekara 18.

An gabatar da taron ne a birnin Cirebon a kan tsibirin Java, wannan ne karo na farko da malaman addinin Musulunci mata suka shirya taro.

Mafiya yawan wadanda suka halarci taron ‘yan kasar ne, sai dai an samu halartar wasu daga kasar Pakistan, da Saudiyya da ma sauran wasu kasashe.

Ana gabatar da Fatwa a kasar akai-kai, sai dai galibi majalisar malaman kasar ce suke gabatarwa, wacce ita ce hukuma ta koli a harkokin addinin Musuluncin kasar kuma dukkansu maza ne.

Fatawar ta kira aurar da kananan yara a matsayin “cutarwa” kuma ya zama dole a hana yin hakan.

Ninik Rahayu, wacce ita ce ta shirya taron, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Malamai mata sun san al’amuran da suka shafi mata da kuma abubuwan da suke kawo wa mata cikas, ba za mu jira har sai gwamnati ta zo ta kula da wadannan yara ba, muma za mu iya daukar mataki.

Malaman sun yi nazari inda suka gano cewa, yawancin kananan yaran da ake musu aure ba a barinsu su cigaba da karatunsu da sun fara sai ayi musu aure, daga karshe kuma a sake su.

Batun aurar da kananan yara na daya daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron, sauran sun hada da yi wa mata fyade da kuma lalata muhalli.

WASIKU: ‘Tsakanin Gwamnatin Kano Da Masarauta’


Assalamu alaikum Edita, don Allah ku bani dama na yi tsokaci akan rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnatin Kano da masarauta, domin makonnin da suka gabata babu wani labari da ke daukar hankali kamar batun kalaman mai martaba Sarkin Kano, musamman gugar zana da Sarkin ya yi, akan aikin girka layin dogo(rail line) a birnin Kano, wanda gwamnatin Kano ta karbo bashi a kasar Chana domin aiwatar wa don saukaka harkokin sufuri da kawata birnin. Koda yake Sarkin bai tsaya a nan ba, amma dai  wannan magana na daga cikin batutuwan da suka fi jawo masa martani da kausasan kalamai.

Wani abu da ya fito a yau wanda kuma ya ja hankali sosai akan wannan batu shi ne, labarin batun kaddamar da bincike akan asusun masarautar da hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta fara, domin har ta aika da sammaci ga wasu kusoshin fadar Kano, domin su amsa tambayoyi akan wannan batu. Tun lokacin da aka fara wannan sa in sa na yi niyyar sanya wa bakina takunkumi, na yi shiru saboda wasu dalilai, sai gashi an zo gabar da ya kamata ace na fadi ra’ayina tun dai zamani ne Allah ya kawo mu na kowa na iya fadin albarkacin baki. Ko da yake ‘yancin ya kansa wasu kokarin wuce makadi da rawa, Allah ya kau da bacin rana.

Dangane da binciken da Muhyi Magaji ya fara kuwa, bani da ta cewa, domin Babu laifi idan hukuma ta yi aikin bincike saboda bayyana gaskiya, ba saboda yin bita da kulli domin ramuwar gayya ba, ni dai a fahimta ta, gwamnatin Kano ta fusata da kalaman da Sarkin Kano ya yi ne a kan aikinta na gina layin dogo shi ne take son amfani da ofishin (Anti corruption) domin a ci mutumcinsa ko a tozarta shi, wannan fahimta ta ce kuma ra’ayina ne. A lokuta da dama tarihi ya kan maimaita kansa, gwamnatoci a matakai daban-daban su kan yi amfani da wasu hukumomi ko dokoki su afkawa wadanda suka yi kokarin shigar musu hanci da kudundune, su kan fake da cewar aiki ne ya biyo, amma a zahiri ramuwar gayya ce.

Idan za a yi bincike na hakika babu laifi kowa ya shafa, amma irin wannan sai nake ga zai zama tamkar wata hanya ta maye fake da Agana, akwai badakaloli da yawa da ya kamata ace an bincike su tun farko amma an kau da kai saboda watakila ba binciken ne a gaba ba an fi son a jira sai wanda ya kawo wargi, sai a gwada masa izza irin ta mulki.

Kamata ya yi mahukuntanmu su rika yin azama a lokacin da aka taba talaka ba su yi gaggawar daukar mataki mai tsauri ba don kawai an soki muradinsu ba. Kuma masu murna da wannan al’amari su yi tunani cin fuskar sarkin Kano daidai yake da cin fuskar Kanawa, domin masarautar Kano abar alfaharin duk dan asalin Kano ce, ko da akwai tuhuma akan Sarki bai kyautu a biyo ta wannan hanyar ba, ko ba komai fa har yanzu sarkinmu ne, a kawaici irin namu kuma akan bar wani abu don wani abin, in mun yi tunani sosai kujerar za mu fara dubawa kafin mu duba wanda yake kanta, kuma idan an yi wa wannan sarkin cin kashi, Allah ne kadai ya san gobe me za ta haifa, kaga shike nan mu da kanmu mun bude kofar zubar da kimar masarautarmu. Allah ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon binta.

Sako Daga Malam  Nasiru Yunusa Garko Maibulo A jihar kano  08176182761.

 

 • Ya Kamata Gwamnatoci Su Tallafa wa Manoma

Yana da mutukar muhimmanci gwamnatin tarayyar NijeriYa, da gwamnatocin jIhohi su yi tsari mai kyau da za su tallafa wa manoman damIna da masu noman rani, musamman ma kananan manoma, wadanda su ne suka fi bukatar taimako, kuma ya kamata a ba su tallafi a kan lokaci, yadda za su amfani tallalfin yadda ya kamata, hankan ne zai bawa manoman damar su yi noma yadda ya kamata, a samu abinci ya wadata a kasa, kuma da zarar abinci ya wadata a kasa, to mutane za su samu kwanciyar hankali, kuma tattalin arzikin kasa zai bunkasa.

Daga Muhammad Babangida Kiraji, 08029388699.

 

Assalamu alaikum Editan jaridar LEADERSHIP Hausa, fatan alheri ga daukacin ma’aikatan ku. Hakika dakatar da sakataren gwamnatin Tarayyar Naieriya da ma shugaban hukumar leken asirin kasar wato Babachir Dabid Lawal da Ayodele Oke din da shugaba Muhammadu Buhari yayi, tare da kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike a bisa zarge-zargen da ake yi musu na cin hanci da rashawa, hakan babban abin farin ciki ne ga Nijeriya. Shakka babu wannan ya kara jaddada wa ‘yan Nijeriya cewa, wannan gwamnati da gaske take yi a kudirinta na yakar cin hanci  da rashwa.

Kuma hakan ita ce hanya daya tilo mai bullewa, wato nuna halin ba sani ba sabo ga duK wanda ake zargi da rub da ciki akan dukiyar Nijeriya. Kuma shakka babu, shirin nan na sauyi ya fara daga kaina wato (Change begins with me) da gaske ne.  Da fatan gwamnatin shugaba Buhari za ta ci gaba da wanke hannunta ga duk wani shafaffe da mai, wanda aka samu da zargi na wani laifin cin amanar kasa.  Allah ya albarkaci Nijeriya.

Daga : Shamsuddeen Unikue Boy Makanike Rijau, Jihar Neja, 09033634375.

 

 • Kwamitin Zakka Ya Ciri Tuta A Sokoto

Hukumar  zakka da wakafi ta ciri tuta wajen rage radadin talauci a jihar Sokoto. Tun bayan da kwamitin  zakka da wakafi ya koma hukumar zakka da wakafi mai zaman kanta ta jihar Sokoto, ya ke taimaka wa matuka wajen rage talauci a jihar ta Sokoto. A baya alkaluma sun nuna jihar Sokoto ita ceke kan gaba wurin talauci a duk fadin nijeriya. Wannan ya bawa gwamnati kwarin guiwar wajen kokarin ganin an magance wannan matsalar. Alfanun da cigaban da hukumar zakka da wakafi ya samar a jihar ba zai  misaltuwa, a ciki da sassa daban-daban na jihar, wanda hukumar ta aiwatar na ayyukan a zo a gani. A kwai koyawa matasa sana’oi daban-daban, na hannu kamar dinki, Walda, Kafinta, Kanikanci, da kuma masu dabarun aiwatar da sana’oi daban-daban. Wannan kadanne daga cikin ayukkanta na bangaren koyon sana’oin hannu. A bangaren bada tallafi ga matasa da marasa karfi da jari domin gudanar da sana’oi kuwa, wannan Hukuma ka kan dauki  nauyin basu horaswa ta musamman da kuma kayan gudanar da  sana’ar, alal misali a wannan fannin sun raba wa, teloli bila adadin kayan aiki ga maza da mata, matasa, domin dogaro da kansu ta fannin sana’ar dinki. A fannin sana’ar walda,kanikanci, aski, noma, da kuma yadda ake gyaran na’urar GSM, Kwamfuyuta kuwa duk hukumar ta tallafa musu da jari duk a kokarin hukumar na yakar talauci.

Haka zalika wannan hukuma ta bawa wadanda suka shiga addinin musulunci tallafin kudi, domin dogaro da kansu, tare da daukar nauyin ilmantar dasu ilmin addini. Ayukkan hukumar basu tsaya anan ba, hukumar ta shafe shekaru da dama, tana bawa musakai da marasa karfi tallafin kudi naira 6,500 domin kafa kananan sana’oi domin dogaro da kansu, don kaucewa barace-barace a cikin jihar, wanda ta dalilin wannan musakai da dama suna sana’oin a yankuna daban-daban na fadin jihar, duk a kokarin hukumar na yakar talauci. Hakika muhimmancin wannan hukumar zakka da wakafi ya fi gaban a yi ta maimaita wa, domin ya rage talauci, da zaman kashe wando a ciki da wajen jihar. Sannan akwai shirya tarurrukan wayar da kan matasa muhimmanci kaucewa fadawa shaye-shaye.

Sannan hukumar ba ta tsaya anan ba, ta tallafawa wadanda ibtila’i ya afkawa, da kayan gini, fili, wani lokaci ma ya kan bawa wasu muhalli ma kyauta.

Bangaren lafiya ma ba a bar su a baya ba, domin ya fito da hanyoyi daban-daban na tallafawa marasa lafiya da basu da karfin siyen magunguna, ko kudaden da za’a yi musu aiki. Inda na gano hukumar ta hada kai, da babbar assibitin tarayya da ke jihar wato, (Usman dan Fodiyo Teaching Hospital), da ta (specialist Hospital), da manyan assibitoci na jihar, da kuma manyan shagunan magunguna, dake cikin jihar da mawasu rassan kananan hukumomi, uwa uba badatallafi gaggawa ga marasa lafiya, da rashin lafiyarsu ke bukatar kwararru a wasu jihohin Nijeriya, da ma kasashen waje idan bukatar hakan ta kama duka kokarin hukumar na shawo kan matsalar rashin lafiya a jihar. Sai dai kash! Duk da wannan kokarin na hukumar, ba wani takamaiman tallafi da yake samu daga masu hannu da shuni daga jihar, dama ‘yan kasuwa da sauransu, wanda wannan babban kalu-bala ne garesu.

Da wannan nake kira, da masu hannu da shuni, da sauran jama’a da su tallafawa hukumar domin ta  cimma burinta na rage radadin talauci a jihar da zaman kashe wando, a ciki da wajen jihar. A saboda haka  nake kara jinjina ga talakawa dake ba hukumar tallafi musamman a yankunan karkara, bisa gagarumar gudun mawar da suke bayar wa ga hukumar, amfanin gonarsu, ko dabbobi da makamantan su. Daga karshe nake addu’ar Allah Ya kara wa hukumar kwarin guiwar cigabada gudanar da ayukkanta, domin taimakon al’ummar dake da bukata, a fannoni daban-daba na rayuwa, musamman

Daga Aminu Dan kaduna Amanawa. 07065654787. 09035522212.

 

Gwamnatin Afghanistan za ta dandana kudarta – Taliban


Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Sojojin Afghan na fama da masu tada kayar baya na Taliban

Kungiyar Taliban ta bayar da sanarwar shiga lokacin kakar yake-yake, kwanaki kadan bayan mummun harin da suka kai wa dakarun Afghanistan.

Kungiyar ta ce za ta mai da hankali ne akan ”sojojin kasashen waje” kuma za’a kai hare-haren ne ta hanyoyi daban-daban da suka hada da yakin sunkuru da kunar bakin wake da kuma amfani da sojoji.

Har yanzu kasar ba ta gama murmure wa daga harin da aka kai wa barikin rundunar sojoji a makon jiya ba.

Ga bayanai da jami’ai suka fitar, masu tada da kayar bayan su 10 ne suka shiga sansanin horar da sojoji a Mazar-e Sharif inda suka kashe akalla sojoji 135.

Wasu rahotanin sun nuna cewa yawan wadanda suka mutu ya haura hakan.

Ministan tsaron da shugaban rudunar sojoji ta kasar sun yi murabus bayan da aka kai harin.

Taliban ta yi barazanar cewa sojojin kasashen waje da ma na gwamnatin Afghanistan za su dandana kudarsu.

‘Yan taliban sun ce kakar yake-yake ta wannan shekara za a sa mata suna Operation Mansouri domin tuna wa da shugabansu da Amurka ta kashe a wani hari ta sama.

DAUSAYIN MUSULUNCI: Yadda Allah Yake Magana Da Annabi (SAW) Cikin Tausasawa (2)


DAUSAYIN MUSULUNCI: Yadda Allah Yake Magana Da Annabi (SAW) Cikin Tausasawa (2)

|

Malam Alkadiy Iyad ya ce idan aka dubi wannan ayar, ya wajaba ga Musulmin da yake tarbiyyantar da zuciyarsa da ragamar Shari’a (tun ma ba wanda ya ce shi malami ne ba) ya rika ladabtuwa da ladabin Alkur’ani. Ma’ana kar ya dinga yin hukunci da fadar abin da ya ga dama, ya dinga lura da yadda Alkur’ani yake fadar magana musamman ma idan maganar ta shafi Annabi (SAW) da sauran Sahhabansa masu girma har zuwa kan malaman al’umma. Idan magana ta zo, kar mutum ya dinka kwakule-kwakule a ciki wai don shi yana so sai ya tona komai. Da yawa wasu daga cikin mutane idan ba su ji abu daga bakin malami ba babu ruwansu da shi amma idan suka ji a wurinsa shikenan, walau sun gane ko basu gane ba kawai za su yi amfani da fahimtarsu wurin yiwa abin hukunci bisa kafa hujjar cewa malami ne ya fadi abin. Idan laifi ne ko kuskure ka ga an dora al’umma kan wata turba da ba ta dace ba.

Alkur’ani yana da alkunya, misali; a kan maganar saduwa da mace sai ya sakaya abin ya ce “shafar mace”, malamai idan suka zo fassara sai su yi bayani cikin hikima a kan saduwa. Idan wurin lalata da maza ne ma Alkur’ani sai ya sakaya ya ce “wadanda ke zuwa wa maza maimakon mata”, bai fito da abin karara ba saboda koyar da mu dattaku. Bai kamata a yi ta warware magana babu ladabin Shari’a da koyi da ladabin Alkur’ani ba. Idan kana karatu sai ka zo wurin da aka taba manya, to ko ka ga laifin da aka ce an yi; ka yi kokarin yi masa mafita; idan ba za ka iya ba ka kame bakinka in ko ba haka ba a maimakon gyara sai mutum ya yi barna. Fir’auna kafirin da ya ce shi Allah ne, Allah ya umurci a fada masa magana mai dadi a cikin Alkur’ani. Allah ya ce wa Annabi Musa (AS) da Annabi Haruna (AS) su fada wa Fir’auna magana mai dadi ko zai wa’azantu. To ina ga wanda laifinsa ko rabin na Fir’auna bai kai ba fa? Rashin bin ladabin Alkur’ani duk ya ja mana shiga cikin halin da muka fada yau. Mutum don ya ce shi Musulmi ne ko malami ko almajiri, sai ya rika fadin abin da ya ga dama a matsayin addini ko ya yi hukunci yadda ya ga dama ga kowa, abin har ya wuce maganar baki ya kai ga daukar makami ana kashe jama’a. Duk rashin bin ladabin Alkur’ani ya kawo mana haka. Ba mu gyara bakinmu ba kuma idan baki bai gyaru ba zuciya ba za ta gyaru ba. Mu yi kokarin bin ladabin Alkur’ani cikin maganganunmu, da gogayyarmu, da ba da amsoshin tambayoyi a cikin karatuttukanmu.

Alkur’ani shi ne kololuwar sannai (jam’in sani), shi ne dausayin ladabai na addini da na duniya baki daya. Musulmi ya dinga kula da wannan tausasawa mai ban mamaki cikin tambayar da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a wannan ayar ta “Allah ya yafe ma, me ya sa ka yi musu izini, (Ma’ana Allah zai tambayi Manzon Allah (SAW) ne amma sai da ya hada tambayar da afuwa). Lallai mutum ya rika lura da fa’idodin ladabi da ke cikin ayar. A lura cewa, Allah (SWT) sai da ya fara da afuwa kafin tambayar ta rarauka. Kuma koda ma wadanda suke ganin Annabi (SAW) laifi ya yi Allah yake masa ‘fada’ a cikin ayar, to ai Allah ya ce ya yafe kuma yafiyar aka fara ambata kafin rarauka din. Wannan yana kara tabbatar da cewa babu wani laifi a cikin izinin da ya bayar (SAW). Allah ya kara amintar da zuciyar Annabi (SAW) daga tsoron a ce masa ya yi laifi kafin a tambaye shi cewa “me ya sa ya yi musu izini?”.

A cikin wata ayar Allah (SWT) yana cewa “ba domin mun tabbatar da kai ba (ya Rasulallah) ka kusa karkata kadan zuwa gare su”. Wani sashe na malaman Tafsiri sun ce Allah ya yi wa Annabawa (Alaihimus salam) rarauka da yawa, amma sai bayan da suka yi tuntube da abin da suka yi sannan Allah ya yi musu raraukar. Amma shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) ta bangarensa, rigakafin ya ji a ransa cewa ya yi laifi Allah ya yi masa. Manzon Allah shi ne mafi kiyaye dokokin Allah da soyayyarsa saboda Allah ya ce “ba domin mun tabbatar da kai ba ka kusa ka karkata kadan zuwa gare su”. Wannan yana nuna Allah ne da kansa ya jibinci lamarin tabbatar da kiyaye Manzon Allah (SAW) daga barin aikata abin da za a yi masa rarauka a kai. A cikin rashin tsoratar da shi sai Allah ya kubutar da shi. Misalin yadda za a fahimci haka shi ne, wani dan kasuwa ne ya koya wa wani mutum kasuwanci, bayan dan wani lokaci sun zo suna hira sai wannan dan kasuwan ya ce wa mutumin “ba domin na koyar da kai kasuwancin nan ba; da ka zubar da jarin da na baka”. Ma’anar wannan maganar tana nufin salwantar da jarin nan abin tsoro ne kuma hakan ba ta auku ba bisa dalilin koyar da wannan mutumin kasuwancin da yake yi.

To Allah ya kiyaye Manzon Allah (SAW) ga barin karkata zuwa ga mutanen nan kasancewar shi da kansa (SWT) ya tabbatar da shi ta yadda ba zai yi hakan ba. A cikin bashi tsoro (na barin tarku aula) sai Allah ya girmama shi tare da darajanta shi.

Yana daga irin wannan magana fadin Allah cewa “Hakika mun sani abin da kafiran nan suke fada maka yana bata maka rai, sai dai ba su danganta ka da karya (ko ba sa karyata ka, a wata kira’ar) sai dai azzaluman nan (kafirai) suna jayayya ne da ayayoyin Allah”. Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) ya ce sanadin saukar wannan ayar shi ne: Abu Jahli ne ya ce wa Annabi (SAW) “Muhammadu; mu fa ba ma karyata ka, mun san kai maigaskiya ne, abin da ka zo da shi ne ba mu yarda da shi ba muke karyatawa.” An ruwaito cewa a yayin da mutanen Annabi (SAW) suka karyata shi sai Annabi ya yi bakin ciki, sai Jibrilu (AS) ya zo masa ya ce “me ya ke bata maka rai (ya Rasulallah)?”, sai Annabi (SAW) ya ce “mutanena ne suka karyata ni”, sai Jibrilu ya ce masa “mutanenka sun san kai mai gaskiya ne, ba da kai suke ba; da ayar Allah suke”, daga nan sai Allah ya saukar da wannan ayar.

A cikin ayar akwai macira mai saukin riko cikin baiwa Manzon Allah hakuri da shafar zuciyarsa cikin lallashi cewa Allah ya tabbatar Manzon Allah maigaskiya ne, haka nan ma a wurin kafiran domin da kansu sun furta cewa shi (SAW) maigaskiya ne tare da kudurce hakan har ya zamo suna kiran sa da sunan Aminu (Amintacce) tun kafin Annabta. Allah ya dauke wa Manzon Allah (SAW) damuwar zuciyarsa ta hanyar tabbatar da cewa hatta su kansu kafiran sun san shi (SAW) maigaskiya ne. Kuma sai Allah ya sanya zargin (karyar) ga kafiran ta hanyar ambatar su da sunan masu jayayya da ayoyinsa kuma azzalumai.

‎A mako mai zuwa za mu cigaba daga inda muka tsaya cikin yardar Allah (SWT). Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.

Tare Da Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani)08051529900,

tes kawai

RAHOTO: An Yi Wa ‘Yar Sarkin Dogarai Yankan Rago A Bauchi


RAHOTO: An Yi Wa ‘Yar Sarkin Dogarai Yankan Rago A Bauchi

|

Saboda da rashin imani da tausayi, wasu wadanda ya zuwa yanzu ba a kai ga gano su ba; sun yi wa wata yarinya ‘yar shekaru bakwai a duniya yankan rago.

Rahotanni sun nunar da cewa gabanin yi mata yankan ragon sun kuma kwakwale mata idanunta biyu a Karamar Hukumar Dass da ke Jihar Bauchi inda suka yasar da ita a wani filin  makaranta da ke bayan fadar garin.

Binciken LEADERSHIP Hausa ya gano cewa yarinyar ‘yar Sarkin Dogaran Sarkin Dass ce. Sannan lamarin ya auku ne a ranar Asabar 15 ga Afrilun 2017.

Mahaifan yarinyar ‘yar shekara bakwai sun nuna alhininsu kan kisan inda suka bayyana cewar wasu ne suka zo suka dauke ta a gidansu daga bisani sai gawarta suka samu. Sun bukaci mahukunta da su tashi tsaye domin gano makasan da kuma hukunta su.

Da LEADERSHIP Hausa ta tuntubi shalkwatar ‘yan sandan Jihar Bauchi, kakakinta Sifeta Haruna Muhammad ya tabbatar  da aukuwar lamarin, inda ya shaida cewar ya zuwa yanzu suna  ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin tare da bayyana cewa da zarar sun kammala  za su sanar wa jama’a abin da binciken nasu ya gano.

Cutar Sikila: An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Tilasta Gwajin Jini Kafin Aure


Wani wanda aka haifa da cutar nan ta amosanin jinni, wcce aka fi sani da Sikila (Sicle cell), Muhammad Kafi Liman Yana, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Shira ta jihar Bauchi ya yi kira da babbar murya ga gwamnatici a matakan kasa, jiha da ma Kananan Hukumomi da su tabbatar da sanya doka ga jama’a na yin gwajin jini don gano yanayin jinin ma’aurata gabanin aure. Inda ya bayyana cewa ta hakan ne kawai za a shawo kan matsalolar.

A wata zantawa da ya yi da manema labarai a Bauchi, Malam Muhammad ya bayyana cewa, “rashin yin wannan gwajin shi ne ya sa mu ma muka kamu da wannan cutar tun fil-azal, tuni masana suka gano cutar, idan da za a rinka yin gwaji kafin yin aure, to ba za a kamu da ita ba; idan aka tabbatar jinainan na miji da macen bai yi daidai ba; to wanda za a haifa zai kamu da cutar, in kuma ya yi daidai, to shi ke nan za su iya yin aurensu,” misali a ce kowannensu yana da AA, ko kuma daya na da AA, wani kuma na da AS. Amma idan dukkansu suna da AS-AS ne, to akwai yiwuwar samun Sikila a ’ya’yansu,” in ji shi.

Don haka sai ya ce, “a bisa haka nake kira ga gwamnatin jihar Bauchi da ta tarayya da su tabbatar da sanya doka mai karfi da za ta tilasta wannan gwajin domin kawo karshen haihuwar yara masu wannan cutar a cikin al’umma. Domin wallahi mu masu wannan cutar muna matukar shan wahala, tun ina dan wata uku da haihuwa ake shan wahala da ni, yau shekarata 28 ke nan ana fama da ni. Yanzu haka ma da kake ganina, an yi min karin jini ne ya sa ka ga ina wannan tafiye-tafiyen da har ka ganni na zo don na yi wannan kiran.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, “babu damar in yi tafiyar da ta wuce kilomita daya, ko da mashin na hau, ko wani abin hawa, sai na ji kirjina kamar ana daka. Yanzu haka iyayena sun yi nasu har sun gaji, masu taimaka min da jini don na rayu sun ce sun gaji, da me wannan ya yi kama?”

Malam Muhammad ya ce, “a bisa wannan ne nake tausaya wa wadanda ake haihuwa, kuma cutar tana nan tana ci gaba da kashe kananan yara. Abin mamaki kuma kasashen waje da kungiyoyi masu kare hakkin yara sun gagara farkawa don shawo kan wannan cutar. A cikin mako daya sai ka kashe kudin da ya kai Naira Dubu Hamsin, ba wai lallai don an je asibiti ka farfado sai a ce za ka yi wata daya ba ka sake kwanciya ba, gobe ma za a iya dawowa da kai. Wannan ma fa don ni da nake iya wannan maganar ne nake fadin haka, ina ga yara kananan da ba ma su iya Magana, balle su bayyana abubuwan da ke damunsu.”

Ya kuma nuna matukar takaicinsa kan yadda hukumomi suka fi muhimmantar da cutar HIB, inda ya ce bai kamata kungiyoyi da gwamnatoci su fi ba da kulawa ga wannan cutar fiye da ta sikila ba; a cewarsa, yana da muhimmaci a kula da dukkanin cutar, musamman bisa la’akari da yanayin cutar masu na sikila, wanda ya fi kama yara kanana.

Ya kuma ci gaba da cewa yanayin cutar a cikinsu, “babu minti da zata wuce ba tare da na ji wata masifa da za ta sameni ba; wani lokaci zan ji gabata tana ciwo, wani lokacin kuma dan yatsana ke ciwo, na sha magani ya ki yi, amma abin mamaki da zarar an sha magani zai warke ko da ba a sha magani ba. Sannan idan tsautsayi ya sameka ko da wani tsinke zai cakeka, shi ke nan wajen zai yi ta yin ruwa, domn cutar tana lalata kwayar halitta ne, yakan jawo ma kashinmu ya zama babu karfi, abu kalilan sai ka ga mutum ya karye, ko ka ga fatarmu tana wani yelo, ko wani kala. Za ka ganmu wani iri, kai babu inda ba ya mana ciwo. Za ka ganmu kanmu ya yi manya, jikin kuma sirara, ko ka ga wani lokaci mu samu katon tumbi,” A cewar Muhammad Kafi-Liman.

Ya kuma bayyana cewa, har zuwa wannan lokacin ba a iya tabbatar da maganin da ke warkar da wannan cutar ba, “Bargo kashin ne kawai yake tabbatar mana da yana rage wannan cutar. Dashen bargon nan kuwa, yaro ma kawai in za a yi masa yakan lakume Naira Milyan 7. A don haka akwai bukatar a sanya doka don magance wannan matsalar,” In ji shi.

Matashin mai shekara 28 ya kuma bayyana cewa cutar na da matukar hatsari a cikin al’umma, a bisa haka ya zama wajibi ga mahukunta su tashi tsaye domin shawo kan cutar da kuma neman hanyoyin raguwarta a tsakanin al’umma. Inda ya hakikance cewa gwajin jini kafin aure shi ne mataki na farko da ya kamata a fara bi don shawo kan cutar. “Wallahi cutar nan tana da matukar hatsari a cikin a’umma. Yana da kyau mahukunta su tashi tsaye,” ya ce.

A karshe ya yi kira ga al’ummar da su tabbatar da sun yi wannan gwajin jini kafin su yi aure, saboda ita wannan cuta idan ta kama yaro, to ba ma shi ba, hatta iyayensa ma na cikin wahala. Kuma ya ce idan aka yi wannan gwaji aka ga akwai yiwuwar a samu masu wannan cuta a cikin iyali, to a hakura da wannan auren.

 

Bahubali 2: Fim ɗin da aka jima ba a yi kamarsa ba


Image caption

An jima ba a kashe wa fim din India kudi kamar Bahubali 2 ba

A ranar Juma’a ce aka fitar da wani shahararren fim ɗin Bollywood a kasar Indiya mai suna Bahubali kashi na biyu.

Fim ɗin Bahubali na 2 tun kafin fitarsa, ya ja hankalin mutane ciki har da wadanda ba su damu da kallon fina-finan Indiya ba.

Tun a ranar Alhamis, aka fara nuna wannan fim a Amurka.

Shi ne irinsa na farko da aka kashe makudan kuɗaɗe wajen shirya shi, saboda haka ne a kusan ko’ina duniya ake maganarsa.

A Indiya kadai, za a nuna shi a Silimu sama da 6,500 cikin manyan yaruka daban-daban na kasar, babu wani fim da ya taɓa samun irin wannan tagomashi a tarihin Bollywood.

Fim ɗin, ci gaba ne daga Bahubali kashi na ɗaya, wanda ya fita a shekarar 2015, kuma ya samu karɓuwa sosai a duniyar fina-finai.

Sharhi, Aisha Shariff Baffa

Babban dalilin da ya sa Bahubali na biyu ya samu karɓuwa a wajen mutane shi ne yadda ya yi tsokaci cikin sha’anin masarauta.

Ya fito da irin kutungwila da maƙarƙashiyar da ke da alaƙa da neman mulki a wajen wasu. Bayan kashe wani sarki a fim ɗin na Bahubali, sai kuma ake yunƙurin kashe ɗansa.

Abin da mutane ke son gani a kashi na biyu shi ne, dalilin da ya sa babban na hannu daman sarkin, ya ci amanar sarki ta hanyar kisan gilla.

A Nijeriya, masu sha’awar fina-finan Indiya ba a bar su a baya ba, inda suka shiga sahun masu alla-alla su ga fitowar Bahubali na biyu da ke faɗin duniya don kashe kwarkwatar idanunsu a wannan fim.

BABBAN LABARI: Badakalar Naira Bilyan Hudu A Masarautar Kano: Ko Za A Tsige Sarki?


 • Muna Binciken Lamarin —Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Jihar Kano
 • Ba Mu Yi Almundahana Da Dukiyar Al’umma Ba —Masarauta
 • Ya Kamata A Yi Masa Afwa —Saraki Da El-rufai

Dambawar binciken Masarautar Kano karkashin jagrorancin Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II, na ci gaba da yamutsa hazo tsakanin mutane masu bambanci ra’ayi a Nijeriya, inda wasu ke ganin matakin da Gwamnatin Kano ta dauka daidai ne, yayin da wasu ke da ra’ayin akasin haka.

Takaddamar ta dauki zafi tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar, wacce aka dauki lokaci mai tsawo cikinta ba tare da ta bayyana a sarari jama’a sun san da ita ba. Matsala ce wacce wasu masu fashin baki suke alakanta ta da siyasa, yayin da wasu na jikin gwamnatin Kano suke barranta zancen da wata makarkashiya ko tuggun siyasa.

Bayan rasuwar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne Allah ya damka amanar Kanawa a hannun Malam Muhammadu Sunusi II, wanda jika ne a wurin Marigayi Sarki Muhammadu Sanusi. Wanda tun bayan darewarsa kan karagar mulkin Kano aka fara jin sabon yunkurin sake salon tafiyar da fadar Kano, ciki har da sake salon zaman fada, wanda ake karbar korafin al’umma kai-tsaye, bayar da dama ga jama’a domin sauraron zaman majalisar ta sarki, da kuma rabawa mabukata sadakar abinci a duk wayewar gari. Sai da ta kai yin haka ya fara haifar da takun saka tsakanin Masarautar Kano da Gwamnatin Kano, har sai da sarkin ya nuna cewa yana yin wannan sadaka ne daga aljihunsa.

Tun bayan hawan Sarki Muhammadu Sanusi II, ya kasance mai yawan tofa albarkacin bakinsa akan lamurran da suka shafi rayuwar al’umma, ba kawai rayuwar al’ummar jihar Kano ba, har da na sauran al’ummar Nijeriya. Duk da Sarkin ya fi yin fashin baki akan lamurran rayuwar yau da gobe na Kanawa, musamman kan zamantakewa da neman sauyi a halayyarsu.

Daga cikin batutuwan da Sarki Muhammadu Sanusi ya tofa albarkacin bakinsa akwai batun taka burki ga dokar aure da wasu dattawa suka gabatar a garin Dambatta. Haka kuma ya taba janyo hankalin gwamnatin APC akan irin halin wahalar da al’umma ke ciki. Sannan daga baya-bayan nan ya gabatar da wani kuduri na son daidaita aure a Kano, wanda hakan na da alaka da yawaitar sakin aure, da kuma banzantar da yara da wasu iyayen ke yi a tituna da sunan bara, ko talla ba tare da sun tura su zuwa makaranta ba.

Wadannan maganganu da Sarki Sanusi ke yi, sai ya zama ba ya yiwa wasu dadi, yayin da wasu ke ganin ba kimar masarautar Kano ba ne a ce a kowanne kankanin lamari sai sarki ya tofa albarkacin bakinsa.

Wasu rahotannin na nuni da cewa babban abin da ya kara tayar da kurar a wannan karon shi ne kalubalantar gwamnatin jihar Kano da sarkin yayi akan jirgin kasa da take shirin samarwa a jihar, ta hanyar ciyo bashi daga kasar Chana. Sarkin ya ce, wannan jirgi ba zai amfani rayuwar talaka ba ko kadan, sai dai ma barin jiha da za a yi da tulin bashi. Sannan kuma Sarkin, duk a wurin taron zuba hannun jari a garin Kaduna, ya kalubalanci gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari dangane da kalaman da yayi na cewa zunubbai ne suka janyo barkewar Sankarau a jihar ta Zamfara.

Tun bayan wadannan kalamai da sarkin yayi a garin Kaduna, sai lamurran suka dauki dumi tare da sauya salo. Marubuta suka rabu zuwa gida biyu, bangaren masu goyon bayan sarki Sanusi da bangaren masu sukarsa. Kowanne bangare na kawo hujjojin da suka sa ba zai saki ra’ayinsa ba.

Rubutun da wata jaridar yanar gizo ‘Daily Nigerian’ ta wallafa, wanda a ciki ne marubucin ya kawo jadawalin yadda masarautar Kano take fatali da kudaden da ta gada a asusun jihar, da kuma adadin kudin da aka barwa jihar kafin hawan sarki Sanusi, da kuma yadda ya yi da kudaden, ciki har da kudaden da yake kashewa a yanar gizo.

Bayan wallafa wannan rubutu an ci gaba da samun takaddama a tsakankanin marubuta da masu fashin baki. Har dai ta kai wasu rahotanni sun bulla wadanda ke nuni da cewa wasu gwamnonin arewa biyar, cikinsu har da Gwamna Ganduje sun hadu a birnin Guanzhou da ke Chana domin daukar mataki mai kwari akan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Duk kuwa da majiyarmu ta tabbatar da cewa gwamnonin jihohi tara ne suka halarci kasar ta Chana domin taron cibiyar masu zuba hannun jari.

Sai dai a can kasar Chanan, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana, da yawan gwamnonin sun aminta da a tsige sarki Muhammadu Sanusi, inda gwamnoni biyu suka bukaci da kar a tafi kai-tsaye ga tsige shi, a fara bin matakin bincikar asusun masarautar da yanayin yadda aka tafiyar da kudaden ciki, kafin a kai ga matakin tsigewa.

Haka nan kuma gwamnonin sun ce, matukar gwamnatin jihar Kano ta zuba ido ba tare da daukan kwakkwaran mataki akan sarkin ba, haka zai yi ta sakin baki ya na sukarsu da ajandodinsu. Gwamnonin da suka halarci wannan taron akwai gwamnan Zamfara, gwamnan Kano, gwamnan Neja, gwamnan Nasarawa, da kuma gwamnan Borno.

A karshen makon da ya gabata ne kuma wata sabuwa ta bayyana, inda hukumar sauraron koke da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bude babin bincikar asusun masarautar jihar Kano, bisa zargin masarautar da ake yi da tarwatsa biliyoyin kudaden da ta gada a cikin dan kankanin lokaci.

Daga cikin aikin binciken, an aika da sammaci ga ma’aji da sakataren masarautar ta Kano, domin su halarta a gaban hukumar don yin karin haske kan yadda aka kashe naira biliyan 4, kamar yadda wata majiya daga cibiyar ta bayyanawa manema labarai.

Jaridar LEADERSHIP HAUSA ta bankado yiwuwar gwamnatin jihar Kano na ta dakatar da Sarki Muhammadu Sanusi II, bisa uzurin samun damar gudanar da bincike yadda ya dace dangane da zargin tarwatsa kudin masarauta. Wannan kuma ba ya rasa nasaba da irin wutar da wasu jiga-jigan siyasa a ciki da wajen Kano suka kunnowa gwamna Ganduje kan ya tsige Sarkin.

Wata majiya mai tushe daga gidan gwamnatin jihar Kano ta tabbatar wa da wakilinmu cewa, “Akwai shawarar da kwararru a fannin shari’a suka bayar na cewa a dakatar da Sarki Sanusi da wasu jiga-jigan masarautar ta yadda za a gudanar da bincike ba tare da wata tangarda ba.”.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi walin Kano, wanda kuma shi ne majibincin lura da kudaden masarautar, ya ce, “Da gaske ne an fara binciken masarautar. Hukumar ta rubuto mana da takarda ta na bukatar Sakatare da ma’ajin masarautar su bayyana a gabanta. Bayan wannan ba mu san wani abu sai dai jita-jitar da ake ta yawo da ita.”

Tuni dai hukumar sauraron korafi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta nemi izinin gwamnan jihar, akan za ta binciki wannan lamari, wanda a ta bakinsu ke da hadarin gaske a barshi ba tare da bincike ba. Wanda ba tare da wata-wata ba gwamnan ya amince da a gudanar da binciken.

A wata sabuwa kuwa, bayan da lamarin ya kara tsananta, Sarki Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa a shirye yake tsaf ga binciken da ake son gudanarwa kan jagorantar masarautar Kano da yayi na tsawon shekaru uku. Sarkin wanda ya bayyana haka ta hannun Walin Kano, Alhaji Mahez Wali. Sarkin ya ce abin da ya gada bai wuce kimanin naira biliyan ɗaya da miliyan 800 ba daga sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, sabanin naira biliyan shida da wasu kafofi ke yaɗawa.

A bayanin da ya yiwa manema labarai a ranar Litinin, ma’ajin masarautar wanda shi ne kuma Walin Kano, Alhaji Bashir Wali, ya ce abin da Sarki Sanusi ya gada daga Sarki Ado Bayero shi ne Naira biliyan 2,875,163,431.17.

Ma’ajin masarautar ya kara da cewar kafin Sarkin Kano Ado Bayero ya rasu “An fitar da naira miliyan 981, 784,503.73 wanda aka biya kwamitin gina gandun sarki Ado Bayero na Darmanawa domin ci gaba da wannan aikin.”

Har ila yau, ma’ajin masarautar ya kuma ce “Saboda haka abin da ya rage a wannan lokaci bai wuce naira biliyan 1,893,378,927.38 ba. Wannan shi ne abin da sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya gada.”

Alhaji Bashir Wali ya ci gaba da cewa bayan gadon kudin akwai ayyukan da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwanso (tsohon gwamnan Kano) ta bayar da izinin gyara wasu gine-gine a cikin gidan sarki bayan wasu wuraren sun rurrushe. Ya ce ba a fara aikin ba sai lokacin da sarki Sanusi ya hau karagar mulki, ya kara da cewar gidan ya sauya siffa.

Alhaji Bashir ya ce gaskiya ne masarautar Kano ta biya Dabogate kudi Naira 152, 627,723 inda ya yi bayanin cewar an bayar da kudin ne saboda gyaran fada da kuma sayen kujeru da sauransu saboda mafi yawancin abubuwan da ke fada na tsohon sarkin da ya shafe shekara 50 yana kan karagar mulki ne. Ya ce motocin da tsohon sarkin ya bari nasa ne na kashin kansa, kuma bayan rasuwarsa aka yi musu kudi inda masarautar Kano ta biya (miliyan 180) domin su zama mallakarta.

Game da zargin kashe naira miliyan 15 kan tafiye-tafiye, masarautar Kanon ta ce ba haka lamarin yake ba. Ma’ajin Kanon ya ce an kashe kudin kan gyaran zauren da ake fadancin dare a lokacin azumi.

Amman kuma masarautar ta amince cewar an kashe naira miliyan 12 kan kudin tikitin tafiyar ‘yan tawagar sarki, inda ta kara da cewar shi sarkin Kano da kudinsa yake sayen tikitin tafiya da kansa. Har wayau masarautar ta musanta sayen motar kasaita kirar ‘Rolls Royce’, da cewa abokan Sarki Sanusin ne suka ba shi kayuta. Sannan dangane da sayen mota mai sulke, fadar ta kara da cewa gwamnatin jihar Kano ce ta ba ta umurnin sayen motocin bayan harin da aka kai wa marigayi Ado Bayero.

Sai dai shugaban hukumar sauraron korafi da yaki da cin hanci ta jihar Kano, Muhyi Magaji, ya musanta zargi da kuma batutuwan danganta binciken masarautar da siyasa. Ya ce ‘babu siyasa a binciken da hukumar ta ke yi kan korafin facaka da kudaden jama’a da ke yiwa Sarki Muhammadu Sanusi II’.

A wani labarin kuma, Shugaban Majalisar Dattawan, Alhaji Abubakar Bukola Saraki, da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i, sun mika kokon baransu ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, akan kar ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Wannan roko, kamar yadda majiyarmu ta nakalto, an mika shi ne ta hannun mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, da wasu jiga-jigai a gwamnatin jihar.

Bukola Saraki da Gwamnan Kaduna sun yi kokarin ganin sun yi magana baka da baka da Gwamnan Kano, amma har zuwa hada wannan rahoto abin ya ci tura.

 

Me ya sa 'yan Nigeria ke azarɓaɓin zuwa Turai ci-rani?


Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

‘Yan ci-rani kan shafe kwanaki suna tafiya a cikin Sahara da teku don tsallakawa zuwa Turai

‘Yan Nijeriya na daga cikin ƙasashen da hukumar kula da masu ƙaura ta ce na kan gaba-gaba cikin mutanen ƙasashen duniya da ke rawar jikin zuwa Turai don ci-rani.

Wakilin BBC Martin Patience ya gano cewa akasarin masu tafiya ci-rani daga Nijeriya na sanya ɗan-ba ne a jihar Edo.

Kelvin Emeson ɗan Nijeriya ne da aka izo ƙeyarsa daga Libya bayan jirginsu ya nutse a cikin teku, inda ruwa ya ci ‘yar’uwarsa Augustina.

Ya ce jazaman ne na tari aradu da ka don cim ma burina na shiga Turai.

A cewarsa Augustina ma’aikaciyar jinya ce da ta yi aiki a wani ƙaramin asibiti don haka kuɗin da take ɗauka bai taka kara ya karya ba.

Mahaifiyarsu Charity wadda ta ce ba ta san lokacin da ‘ya’yanta suka yanke shawarar yin wannan tafiya mai hatsari ba.

Mace mai ƙaramin ƙarfi don haka su Kelvin ke fafutukar neman hanyar samun kuɗin shiga don tallafa wa kansu da mahaifiyarsu.

A bana kadai, ‘yan ci-rani masu yunƙurin zuwa ƙasashen Turai sama da dubu 40 ne suka tsallaka tekun Baharrum – kuma da yawa cikinsu ‘yan Nijeriya ne.

Alkaluman da hukumar kula da ƙaura ta duniya ta fitar sun ce baya ga ‘yan ƙasar Syria da Afghanistan, ‘yan Nijeriya a yanzu sun dauki wani kaso mai yawa da ke ƙoƙarin yin bulaguro zuwa Turai.

Da yawa daga cikinsu sukan je Turai ne don neman aiki da rayuwa mai inganci – duk da yake, kasarsu ba ta fuskantar wani rikici.

Wani mai fataucin masu zuwa Turai a Edo, Friday Egwadoro ya ce ƙarancin karatu ne ya sanya shi shiga wannan harka.

Ya ce karon ƙarshe da ya yi fataucin wasu zuwa Libya ya ci karo da wasu ɗalibai da suka kammala digiri su uku a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani Turai.

Ko Jihar Adamawa Na Bukatar Bindow?


Tare da AL-AMIN CIROMA (08033225331) [TES Kawai] imel: ciroma14@yahoo.com

Jim kadan bayan da rukunin kamfanin LEADERSHIP ya fito da sunayen fitattun shugabanni da ‘yan siyasa da kuma al’ummar gari da za a karrama a bikin da ya saba shiryawa shekara-shekara, da dama tambayoyi suka fara fitowa, musamman a dandalin sada zumunta na ‘Soshiyal-Midiya’ dangane da hanyoyin da dauka wajen zakulo wadannan gwarazan.

Babban abin misali shi ne, a yayin irin wadannan mahawarorin ne aka rika tambayar ko gwamnan na Adamawa ya dace da shiga cikin sahun wadanda ya kamata su karbi kambin girmamawa daga kamfanin na LEADERSHIP? Wasu kuma a gefe suka rika bayyana ra’ayoyinsu cewa yana da kyau a kalli Jihar Adamawa kafin da zuwan Mai Girma Sanata Umaru Jibrilla Bindow a matsayin gwamnanta. Shin ko jihar tana bukatar irinsa, ko kuma al’ummar na Adamawa za su fara tunanin cefanen wani sabon gwamna a lokacin da aka fara kada gangar siyasa ta shekarar 2019?

Kafin mu ida sanin dukkaninn wadannan, bari mu shimfida Jihar Adamawa a faifai, mu yi mata kallon ta-natsu. Shin jihar ta dace ko kuwa da sauranta? Hakikanin gaskiya dai jihar Adamawa na daya daga cikin jihohi mafi koma-baya a kasar nan ta fuskoki da dama kama daga bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma ta bangaren kasuwanci da sana’o’i. Haka kuma jihar ba ta rasa arziki da dimbin albarkatun kasa da za ta iya amfani da su don cimma bukatu har ma ta tsayu bisa kafafunta ba. Amma a tsawon tarihi, Adamawa ta rasa gwamnoni ko shugabanni masu kishinta, wadanda suka sa ajandar muradun ciyar da ita gaba.

An kirkiro ta ne a daga tsohuwar Jihar Gongola a ranar 27 ga Augustar 1991, karkashin mulkin soja na Tsohon Shugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Tarihi ya tabbatar cewa wasu daga cikin almajiran Shehu Usman Danfodio kamar Modibbo Adama da Lamido Kabi ne suka samar da wasu daga cikin garuruwa masu dimbin tarihi a cikin jihar.

Adamawa wacce ke Arewa masu Gabashin Nijeriya tana da yalwar kasa a matsayin daya daga cikin mafi girman jihohi a kasar nan. Jihar tana da fadin kasa na kimamin zagayen kilomita 36,917, inda ta yi iyaka da Jihar Borno a rukunin Gabas maso Yamma, Gombe ta rukunin Yamma, sannan da ta yi iyaka da Jihar Taraba da shiyyar Kudu maso Yamma. Haka kuma ta sami damar yin iyaka da kasar Kamaru ta shiyyar Gabas.

Shimfidadden sharhin tarihin har ila yau, ya tabbatar da cewa sarakuna dai-dai har goma sha-biyu ne suka mulki masarautar Yola, wadanda suka hada da sarkinta na farko, wanda kuma aka sa wa jihar sunansa, Modibbo Adama ben Hassan daga shekarar 1809 zuwa 1848. Bayansa aka nada dansa, Lawalu ben Adama daga 1848 zuwa 1872. Daga Lawalu sai Lamido Sanda ben Adama, wanda ya yi mulki daga 1872 zuwa 1890. Nasabar sarautar ba ta tsaya nan ba, Lamido Zubayru ben Adama shi ma ya karbi ragamar sarauta daga 1890 zuwa 1901.

Idan aka fadada bincike za a tabbatar cewa Modibbo Ahmadu ben Adama ya mulki kasar nan daga 1901 zuwa 1909. Bayan sa Iya ben Sanda wanda ya yi sarauta daga 1909 zuwa 1910. A yayin da Lamido Muhammadu Abba ya hau gadon sarauta ya yi mulki na tsawon shekaru 14 kacala daga 1910 zuwa. Da Lamido Abba ya gushe, Muhammadu Bello ben Ahmadu ben Hamidu ben Adamu ya hau mulki daga 1924 zuwa 1928, sannan dan’uwansa Mustafa ben Muhammadu Abba ya hau mulki daga shekarar 1928 zuwa 1946. Sai kuma Lamido Ahmadu ben Muhammadu Bello ya hau mulki daga shekarar 1946 zuwa 1953. Bayan da ya yi wafati ne Lamido Aliyu Musdafa ya karagar mulki a matsayin daga daga cikin sarakunan da suka fi dadewa bisa gadon mulki a Nijeriya. Lamido Aliyu ya yi mulki daga shekarar  1953 zuwa 2010. Sannan bayansa, aka nada dansa Lamido Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, wanda yake kan karagar mulki ya zuwa yau din nan.

Wadannan muhimman sarakunan ne suka kafa tarihi a masarautar Adamawa, wadda ita ce babbar masarauta a cikin yankin. Har ila yau, jihar ta samar da muhimman mutanen da tarihin kasar nan ba zai cika ba, tilas sai an ambace su. Kadan daga ciki su ne Atiku Abubakar, Alhaji Bamanga Tukur, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, Farfesa Jibril Aminu, Janar Buba Marwa, Farfesa Iya Abubaka, Alhaji Hassan Adamu, Sanata Binta Masi Garba, Mallam Nuhu Ribadu da sauransu.

Na yi wannan shimfidar ne domin na ji dadin buga misalin halin da jihar ta tsinci kanta a ciki tun daga kafuwarta a shekarar 1991 zuwa yau.

Ta bangaren siyasa kuwa, Adamawa ta kasance daya daga cikin jihohin da siyasarsu ta yi kamarin da har aka rika tafka yakin sunkuru da salon fito-na-fito a bainar jama’a. Gwamnan farko da ya mulki jihar daga ranar 27 ga Agustar 1991 shi ne Abubakar Saleh Michika, wanda ya dare mulkin daga rusasshiyar jam’iyyar ‘NRC’ na lokacin, ya sauka a ranar 17 ga Nuwambar 1993.

Bayan saukarsa ne aka nada Gregory Agboneni, karkashin mulkin sojoji daga 1993 zuwa 1994, inda Mustapha Isma’il ya hau zuwa zuwa 1996, sannan Joe Kalu-Igboama, shi ma ya yi mulki daga 1996 zuwa August 1998 daga bisani Ahmadu G. Hussaini ya karbi mulkin daga 1998 zuwa 1999 dukkansu a karkashin tsarin mulkin soji.

Da aka maido da tsarin mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 ne aka zabi Boni Haruna a matsayin gwamna na tsawon shekaru takwas, a karkashin mulkin PDP. Da ya sauka a 2007 ne aka zabi Murtala Nyako daga 2007 zuwa 2014 a karkashin inuwar tutar PDP, bayan da aka tafka matsaloli da daman gaske a mulkin nasa, wanda ya haddasa tsigewarsa daga kujerar mulkin a 2014, inda aka nbada Alhaji Ahmadu Umaru Fintirin a ranar 15 ga Yulin 2014 zuwa 1 ga Oktobar 2014. Daga nan ne aka kara maido da mataimakin Nyako, Mista Bala James Ngilari, wanda aka tsige su tare da maigidansa (Nyako) bisa karagar mulki daga ranar 1 ga Oktoba 2014 zuwa 29 ga Mayun 2015, a karkashin inuwar PDP.

Bayan da aka fafata a zabukan 2015 ne Sanata Muhammad Umaru Jibrilla Bindow ya lashe zabe karkashin tutar jam’iyyar APC. Shekaru 16 da aka maido da mulkin farar-hula sun bayyana irin bajintar da Gwamna Bindow ya zo da ita a cikin shekara daya rak. An tabbatar cewa babu wani gwamna da ya kama kafar Sardaunan Mubi a fannin raya karkara da birane.

Maimakon al’adar da aka saba da ita ta ‘Daga kwabri sai gwiwan’ da mafi akasarin ‘yan siyasar Nijeriya ke yi a lokacin da suka rungumi madafun iko, ko suka sami wani mukami, shi kuwa Bindow ya fi mayar da hankali wajen daukar kwararrun masana fannoni domin tafiya da su, ba tare da la’akari da bangaranci, addini ko kabila ba. An shaida cewa mafi yawan mukarrabansa mutane ne da ya zakulo su bisa cancanta da kwarewa. Wannan ta sa shekararsa guda daya kacal a bisa kujerar mulki, ta haifar da gagarumar nasarar da shekaru 25 da biyar din da aka yanka ragon rada wa jihar suna ba su samar ba!

Babban abin da ya fi daukar hankalin al’umma shi ne yadda gwamnan ya rungumi hanyoyin sadarwar zamani domin ganawa da al’ummar jihar, ya rika jin kokensu na yau da kullum, kana kuma ya gudanar da ayyukansa tare da kutsawa lungu da sako na jihar, ya na aiwatar da ayyuka daban-daban don raya jihar, gami da zaburar da matasa marasa ayyukan yi, ta hanyar sanya su bisa gwadaben alheri.

Daya daga cikin muhimman ayyukan da mafi yawan gwamnonin baya suke kyama shi ne farfado da harkar kiwon lafiya, wanda suka shafe shekaru da dama a mace. Amma a wannan karon, Gwamna Bisa, tare da taimakon shirinsa na musamman don ci gaban al’umma, wanda a Turance ake kira, ‘Bindow for Social Change,’ ya shimfida kyawawan turakun sake farfaddo da harkar kiwon lafiya a fadin jihar baki daya. Wannan shirin yana karkashin kulawar Kwamishinar Lafiya, Dakta Fatima Abubakar Atiku.

Al’ummar Adamawa sun yi na’am da samun namiji kuma bajimin gwamnan da ya kuduri aniyar samar da kyawawan hanyoyi, musamman a cikin fadar jihar wato Yola. Manazarta sun tabbatar cewa da wuya a yanzu mutum ya bambance birnin na Yola, wanda nan ne mazaunar masarautar Adamawa da kuma Jimeta, hedikwatar gwamnatin jihar sabili da kyawawan hanyoyi da aka shimfida a ko’ina.

Gwamna Bindow shi kadai ne a zangon farko na cikar kwanaki 100 bisa mulkin jihar ya assasa asasin ginin gidaje 300 da kamfanin KD Properties & Estate Ltd. ta samar, domin saukaka wa ma’aikata da kuma ba su damar mallakar gidajensu na kansu.

Baicin wannan, zai yi wahalar gaske a lissafa irin ayyuka nagari da Bindow ya yi a Jihar Adamawa, kama daga shimfida hanyoyi, fitattun ababen more rayuwa da sauransu. Sai dai mu tattara, mu ce: Darasin da ya kamata ‘yan siyasar Nijeriya su dauka a nan shi ne; yin watsi da bangaranci da addini da son kai, sannan a rika zakulo da kwararru don ba su damar su taka rawar musamman wajen zaben wadanda za su gudanar da ayyukan raya kasa. Su sani cewa ‘yan Nijeriya na kallonsu, duk wanda bai yi da kyau ba, sai kuma dawowa neman takara da yakin neman zabe. A nan ne talakawa za su rarrabe tsakuwa daga cikin aya!

Majalisa ta kusa tantance Ministocin da Buhari ya tura


wp-1493356188928.jpg

– Makon gobe Majalisa za ta tantance sababbin Ministoci

– Haka kuma Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da shugaba Buhari ya aika ba

– Jagoran Majalisar Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da wannan

Kuna da labari daga NAIJ.com cewa Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar da cewa suna kokarin ganin an kammala aikin da ya rage na kasafin kudi zuwa mako mai zuwa.

Majalisar tayi alkawarin hakan zuwa karshen watan Afrilu a baya.

Har yanzu dai shiru ka ke ji babu labari.

Marigayi James Ocholi ya mutu a ofis

Majalisar Dattawa ta kuma tabbatar da cewa a makon gobe za a tantance sababbin Ministocin da shugaban kasa ya tura masu. Wata guda kenan da shugaba Buhari ya aika sunayen Farfesa Ikani Ocheni da Sulaiman Hassan.

Amina Mohammed ta bar kujerar ta

Ahmad Lawan ya bayyana haka ne bayan ya fito daga fadar shugaban kasa Buhari inda ya gana da ‘Yan jarida a fadar Aso Villa. Sanatan yace dole a samu hadin kai tsakanin Sanatoci da shugaban kasa.

Sama Da Matasa Dubu 10 Za Su Amfana Da Shirin ‘N-Power’ A Adamawa —Osinbanjo


Sama Da Matasa Dubu 10 Za Su Amfana Da Shirin ‘N-Power’ A Adamawa —Osinbanjo

|

Yanzu haka Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar da cewa matasa sama da dubu goma (10, 000) za su amfana da shirin tallafawa matasa da ta bullo da shi ‘N-Power’ a Adamawa.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbanjo ya bayyana haka a ziyarar aikin da ya kawo jihar, domin bude aikin da kuma wasu hanyoyin da gwamnatin jihar ta gina, ya ce lura da matsalolin da rikicin boko haram ya haifar a yankin, gwamnatin tarayya ta yi hobbasar ganin matasa sun amfana da shirin na N-Power a yankin.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayyar za ta tabbatar ta sake gina garuruwan da ‘yan kungiyar ta boko haram suka lalata, kana ya shawarci ‘Yan Nijeriya da su ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya, domin kuwa ta dauko hanyar samar da kyakkyawar canji ga kasar.

Tun da farko da yake gabatar da nashi jawabin, Gwamnan Jihar Umaru Bindow Jibrilla ya shaida wa mahalarta taron cewa gwamnatinsa ta samar da kyakkyawan sauyi ta bangaren gyara hanyoyi da ma gina wasu sabbin hanyoyin a jihar.

Da yake magana game da kudaden Paris Club kuwa, Gwamna Jibrilla Bindow ya ce gwamnatinsa ta amshi kimanin kashi 70 a cikin 100, ya ce kuma gwamnati ta kashe kashi 60 bisa dari na kudin wajan biyan albashi da fansho da garatuti.

A ziyarar ta mataimakin shugaban kasa a jihar dai, mai martaba Lamido Adamawa Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa, ya karrama mataimakin shugaban kasar da mukamin Jagaban Adamawa.

An kuma sanya wa wasu manyan hanyoyi guda biyu a jihar sunayen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbanjo a matsayin sunayen wasu manyan hanyoyi biyu a jihar.

Tsammani nawa Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose na son biya domin matasan Ekiti su rajista don katin zabe


– Sun je hukumar ne don karbin kati, bayan haka su karbi sakamakon

– Gwamnatin Ekiti a ranar Laraba ya ayyana ranar Jumma’a da Alhamis hutu

– Daruruwan matasa suka cika wajen, kuma suna sauri don samun PVC

Daruruwan matasa a Jihar Ekiti, a ranar Alhamis sun kutsa cikin ofisoshin hukumar INEC na jihar domin rajista a matsayin da hukumar ta ayyana rajista a kasar.

Mutane sun fito da yawa yin rajista amma yana dangane da cewa, gwamnan Ayodele Fayose ya yi wa’adin zuwa sãka wa kõwane matasa, tsakanin shekaru 18 da 21, da suka yi sabuwar rajista N2,000.

Jami’an tsaro a ƙofar ofishin hukumar ba su same ta da sauki kamar yadda daruruwan matasa suka cika wajen, kuma suna sauri don samun PVC.

Ko da maimaitawan rokon da gudanarwa sakataren hukumar a Ekiti, Dr.Muslim Moleke, cewa za a ci gaba aiwatar da rajista zuwa kwanaki ba iya kwantar da matasan, wanda sun kusan rushe ƙofar ta hukumar.

Gwamnatin Ekiti a ranar Laraba ya ayyana ranar Jumma’a da Alhamis hutu don taimaka ma’aikata wajen samun rajista

NAIJ.com ya samu cewa, wasu daga cikin matasan da suka yi magana da masu labari a ofishin hukumar INEC a karamar hukumar Ado sun bayyana cewa, sun je hukumar ne don karbin kati, bayan haka su karbi sakamakon.

Gwamnatin Ekiti a ranar Laraba ya ayyana ranar Jumma’a da Alhamis hutu don taimaka ma’aikata wajen samun rajista.

Babban sakataren labarai na gwamnan, Mista Idowu Adelusi, ya shaida wa manema labarai cewa gwamnan ya dai yi wa’adi da wani sakamako na N2,000 kowane wata har a gama gudanar a jihar a watan Yuni.

Uwargidan Najeriya tayi wani gagarumin kokari


wp-1493356547770.jpg

– Uwargidan Najeriya tayi wani gagarumin kokari ga mata

– Aisha Buhari ta saye kayan noma ga mata

– Matar shugaban kasar dai tana kokarin wajen taimakon al’umma

Matar shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari tayi gagarumar kokari inda ta taimakawa mata da kayan noma.

Hajiya Aisha Buhari ta sayawa mata a fadin kasar kayan aikin kifi da na shinkafa.

Aisha Buhari ta saba taimakawa mata da kananan yara a Najeriya

Matar shugaban kasa tana ba da kyauta

NAIJ.com ta samu labarin cewa matar shugaban kasar Aisha Buhari tayi wannan kokari ne domin taimakawa masu shirin noma. Yanzu haka dai za a ajiye kayan a hannun matan Gwamnonin Jihohin kasar. Matar shugaban kasar dai ta sayi kayan casar shinkafa har 25 da kuma da kuma na busar da kifi da za a rabawa Jihohi da dama.

Mun samun wannan labari ne daga Daily Trust ta bakin Suleiman Haruna wanda shi ke magana da bakin Uwargidan Najeriya. Haruna ya bayyana cewa matar shugaban kasar ta saye kayan ne domin agazawa mata.

Kuma da alamu dai idan ba ayi sa’a ba bana babu kasafin kudi a Najeriya kamar yadda NAIJ.com ke lura da abubuwa. Don kuwa ga shi har yau ana shirin shiga watan 5 Majalisa ba ta tabbatar da kasafin da aka tura ma ta ba.

TATTAUNAWA: Dan Adam Na Iya Daukar Cutuka Sama Da 3,800 A Fatarsa — Dakta Aliyu


Dakta Usman Tijjani Aliyu shi ne shugaban asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wase (CMD) da ke Unguwar Nasarawa G.R.A Kano. Yana daya daga cikin fitattu da suka sami kwarewa a kan sanin fatar Dan’adam Da Cutukan da ka iya kama fatar dan’adam da kuma abin da ka iya inganta fata ko akasin haka (Damatology Consultant Doctor). A tattaunawarsa da wakilinmu, Mustapha Ibrahim Tela, ya yi bayani filla-filla game da cutukan da suke addabar al’umma, musamman masu alaka da fata.

Da farko za mu so jin takaitaccen tarihinka?

To sunana Dakta Usman Tijjani Aliyu, kuma ni Likitan fata ne. Na samu shaidar kwarewa a kan fatar jikan bil’adama, wanda ake kira (Damatologist Consultant). A kan fata kuma ni ne shugaban kula da asibitin kwararru na Abdullah Muhamad Wase da ke Unguwar Nasarawa G.R.A a Kano. Kuma a nan Asibitin Mahaifina yake, sannan kuma a nan Asibitin aka haife ni a shekara 1974 a cikin watan daya.

Na fara makarantar Firamare ta St. Louis a shekarar 1979 zuwa 1984, sai kuma makarantar FGC Kano, na shiga jami’ar Bayero ta Kano na kuma kammala  karatu na a Jami’ar Maiduguri a 1991 zuwa 2001 inda na karanta kimiyyar nakaltar magunguna wato (medicine).

Bayan Kammala karatuna na jami’a na zo nan AKTH don karatu aikace daga 2003 zuwa 2004 daga nan kuma na tafi hidimar kasa a jahar Kwara wato (NYSC). Bayan na dawo kuma, sai na samu aiki da hukumar lafiya ta Kano inda suka tura ni Asibitin Murtala a matsayin babban Jami’in lafiya na yi shekara guda, daga nan kuma sai na yi jarabawar MRC wato (Memebr of Royal College of Physician) inda na shekara guda a wani Asibiti da ke wata Jami’a a Landan da ke kasar Ingila, inda na yi aiki a matsayin babban Jami’a a sashen kula da mafitsara na wannan asibitin daga 2005 zuwa 2006, sannan na dawo gida asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano na yi karatun kwarewa na shekara bakwai (7), wanda ake kira da (Karatun Likita na Kwarewa).

Na yi wannan karatu ne akan fata inda na kammala karatun a shekarar 2014. To dama kuma Gwamnati ce ta turani karo karatun a AKTH din saboda haka bayan kammala karatun sai na koma asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda a ka bani shugaban sashen kula da masu matsalar fata na asibitin Murtala Muhammad ta ake kira (Damatology Department) har tsawon shekara biyu.

To kuma daga nan ne sai ita gwamnatin Kano da dauko ni ta kawo wannan asibitin na Muhammad Abdullahi Wase a matsayin shugaban Asibitin CMD kenan.

 

Kafin mu shiga maganar fata kai tsaye wacce ka kware a kai, me ka ke nufi da a wannan asibitin a ka haife ka?

Abinda na ke nufi shi ne, mahaifina a wannan asibitin ya ke da zama. Amma ba ma’aikacin lafiya ba ne, mahaifina dan kasuwa ne, kakana ne ma’aikacin lafiya wato (Nurse Kenan).

 

Idan na fahimta gadar aikin ka yi kenan?

A a, ina yi ne sakamakon sha’awarsa da nake yi kuma nake da kwazo, wanda hakan ne yasa nake iya kokarina don in ga asibitin ya ci gaba. Idan yadda nake so ne, to wannan asibitin ya zama wanda ya fi kowanne a Kano, ko in ce Nijeriya koma duniya baki daya.

 

Wane muhimmanci fata ke da shi a jikin dan’adam?

Fata wata gaba ce a jikin mutum kamar sauran gabobi, misali akwai gabar koda, akwai gabar zuciya, akwai gabar kwakwalwa da dai sauran sassan jikin Dan’adam da a ke kira gaba, kuma kowacce gaba tana da aikin da ta ke yi a jikin mutum. Misali dauki zuciya, babban aikin zuciya shi ne harba ko raba jini a jikin mutum, haka kwakwalwa na da nata aikin kamar karbar bayanai sarrafa su da dai sauransu. Haka dai kowacce gaba akwai aikinta don jikin mutum ya samu tsari da tafi da al’amuran yau da kullum.

To ita ma fata gaba ce kamar yadda na fada a baya cewa ta na da nata aikin a jikin mutum. Babban aikinta shi ne ita ce mai ba jikin mutum kariya daga cutuaka da ka iya shiga jikin mutum in ka ga wani abu na kwayoyin cuta ya shi ga jikin mutum, to sai in an yankata amma in ba yankata a kai ba, to ba wata cuta da za ta iya shiga jikin mutum.

Wani bangare na aikin fata shi ne, ita ke ba mutum sifa wacce za a gane shi ta launin fatarsa. Misali, ta hanyar fata ne zan iya cewa, ga wani Bature can, da taimakon fata ne zan iya cewa ga wani bakin mutum can, kuma ta fata ne zaka ga a wannan lokaci na zafi ta canza ta hanyar da take rike ruwa da jiki ya ke bukata, a lokacin zafi shi ne yasa idan ta hade a lokacin zafi sai ka ga gumi yana tsattsafowa daga jikin mutum, sai ace fata ta matso wannan ruwan da ake cewa gumi, kuma a lokacin sanyi sai ta saki, ba a cika yin gumi ba a lokacin sanyi. A wannan lokacin zafi rike ruwa ta ke yi lokacin sanyi ta saki.

 

Ko za ka iya bayyana mana rabe-raben fata?

Rabe-raben fata uku ne, a kwai fatar nau’in farko, wato bakar fata, sai fata nau’i na biyu irin ta Larabawa da wasu mutanen Asiya da irinta mutanen Cana, sai kuma nau’i na uku ita ce fatar Turawa mutanen Ingila da na Amurka da sauransu wata a Turance muna cewa black skin, colour skin da kuma white skin.

 

Bayanai da muka samu a binciken mu na jarida na cewa, fata hawa-hawa ce, wata akan wata, me ake ake nufi da likitance?

Eh, ba shakka wannan bayani haka yake, ammu a likitance ne abun ya ke haka, amma mutumin da ba likita ba, ba zai san haka ba, domin mu likitoci mu muka rarraba abin haka domin mutane su gane bayanin. Ba za a gane wannan ba sai an yi amfani da na’urar likita za ayi gane haka, domin fata dai hawa hudu ce zuwa biyar kuma kowacce da sunanta, kuma ta hanyar aikin kowacce za a iya gane cewa fata hawa hudu ce zuwa biyar. Ba za a iya gane hakan ba sai an yi zurfi a cikin ilmin fata sannan za a iya fahimtar hakan. Kuma duk wadannan hawa hudu zuwa biyar, kowacce da irin aikinta, hakan ne ma ya sa suka bambanta. Daga cikin mafitar kwayar halitta kuma, kowacce da irin nata kwayar halittar, akwai fata mai matsewa da fitar da gumi a cikinsu.

 

Idan mun dauki yanayin shekara musamman a nan Afirka, akwai sanyi akwai zafi, wanne ne fatarmu ta fi so?

To gaskiya ba wani yanayi kwaya daya da za a ce fata tafi so sai dai kawai wani abu mai kama da wannan, misali ka ga kamar fatar Bature, za iya cewa ba ta son zafin rana domin a wannan lokacin in abun ya tsananta sai ta kone ta yi ba kyan gani, haka tasa dole za ka ga Bature yana amfani da mai na musamman domin kada fatarsa ta kone ta yi wani iri, shi kuwa bakin mutum ba shi da wannan matsalar.

A kwai yanayin da ya fi wahalar da fata kamar dai ita fatar Bature kenan. Amma mu bakaken fata abin da yake faruwa lokacin zafi, fatar na yin haske, lokacin sanyi kuma sai ta yi duhu, wannan shi ne ya sa ba za ka iya cewa ga yanayin da fata ta fi so ba. Tunda ba magana take yi ba. Amma dai fatarmu tafi ta Bature karfi da lafiya shi yasa take jure kowanne yanayi.

 

Wadanne cutuka ne suka fi barazana ga lafiyar fata?

To gaskiya wannan muhimmiyar tambaya ce kuma amsar ta mai fadi ce, sai dai kawai a takaita domin yanzu din nan da muke magana da kai an gano cewa akwai wasu cutukan da ka iya samun fata  sama da 3800 a duniya to kuma wadannan cutuka sun bazu daga wani wuri zuwa wani wurin. Misali, wasu cutukan a Afirka ake samunsu wasu kuma a kasashe irinsu Amurka, Asiya, haka kuma wasu daga cikin irin wadannan cutuka an fi ganinsu a wajen yara, wasu a wajen mata, wasu wajen masu shekaru da yawa wato tsofaffi, wasu kuma wurin matasa, wasun wadannan cutuka na fata suna faruwa sakamakon kamuwa da wasu cutukan su ne ke sanadinsu, to kaga wannan ba zai yi wu a iya iya lissafasu ba sai dai kawai ka ji yanda suke kasancewa.

Idan muka dau tautau da sauransu shi ne abinda muke kira da mele, su ko jama’a sukan dau cuta kamar hudu zuwa takwas su kirata da suna daya misali yadda za ka gane mele, shi ne an fi ganinsa a wajen yara kanana kuma shi za ka ga kumatu ya canza ya dashe yayi ja, shi kuma yawanci wannan an fi gadonsa daga iyaye, kuma yawanci tana taba sassan ido ko kunne da sauransu. Kuma shi ne har fata na tsagewa da kuma mu likitoci mukan bawa iyaye shawara su rika shafa wa yaro Basilin don kada ta rika tsagewa. Kuma mafiya yawanci in suka girma ana rabuwa da wannan cuta ta mele da sauransu wadanda yawanci yara ne suke kamuwa da ita, wasu ma da ita ake haifarsu.

‘Yan Arewa Masu Ci-rani A Kudu Sun Fara Tattara Komatsansu


‘Yan Arewa Masu Ci-rani A Kudu Sun Fara Tattara Komatsansu

|

A yanzu haka daruruwan ‘yan ci- rani wadanda suke ’yan asalin jahohin arewa da suke kudancin kasar nan sun fara tattara nasu-ya-nasu suna koma arewa da nufin tarar damina domin fara shirye-shirye na aikin gona a wannan shekara da muke ciki.

A cikinsu akwai wadanda suke yin ci-raninsu a Jihar Edo tuni sun bi sahun abokanansu na sauran jahohin kudun suna tattare a wasu tashoshin motoci na garin Benin domin samun tafiyar arewa da nufin ba za a bar su a baya ba domin aikin gona.

Duk da kasancewa bayanai suna nunar da cewa ba a dukkanin yankin arewan ba ne daminar ta fadi ba a wasu sassan na jihohin ba a fara alamar ruwan sama ba amma duk da hakan sun gwammace suna gida daminar ta same su a bakin gonakinsu.

A cikin wadannan ‘yan ci-ranin LEADERSHIP Hausa ta yi kicibis da wasu daga cikinsu a wata tashar motoci masu zuwa arewan a cikin Birnin Benin kuma sun shaida mata dalin da ya sa suke kokari tafiya gida saboda sun ji an ce musu an fara ruwan sama don haka za su tafi domin fara aikin gona kamar yadda wani magidanci mai suna Umar Ali yayin da yake kokari ya saka kayansa a wata motar tireila ya bayyana.

“Na ji labari a wurinmu damina ta sauka, samun wannan labarin ne ya sa hankalina ya tashi na yanke shawara zan koma gida domin in fara aiki tare da ‘yan uwana”, in ji shi .

A yayin da wadannan ‘yan ci-ranin wasu daga ciki ke kokarin tafiya gida; sai ga wasu kuma sun baro arewan zuwa kudu da nufin za su fara ci-raninsu a wannan lokacin kamar yadda Malam Haruna ya fada wa wakilinmu Leadership a zantawar da suka yi.

Ya ce “Ni fa a yanzu ne zan fara ci-rani domin a yanzu haka babu alamar damina a yankinmu don haka da iyalina na zo kuma zan ci gaba da zaman ci-rani a nan kudu har sai na ji an fara ruwan sama na damina ko da zan tafi gida”, in ji shi.

RA’AYI: Turkiyya: Raba-Gardama Ko Alakakai?


RA’AYI: Turkiyya: Raba-Gardama Ko Alakakai?

|

Bayan da nake karantawa a kafafen yada labaranku wadanda suke nuni da irin halin lahaulan da al’ummar Turkiyya ke fuskanta abin dubawa ne kwarai, kan haka ne nake neman edita ya ba ni damar fadin nawa albakarcin bakin a wannan jarida ta ku mai albarka.

Kafin na ra’ayin nawa, a makon da ya gabata, na karanta makalar wani bawan Allah da ya ce, jim kadan bayan rahoton zaben raba-gardama da aka gudanar a kasar Turkiyya, wata kungiya mai zaman kanta, wadda ke da alhakin kula da harkar tsaro da hadin kai wato ‘The Organization for Security and Co-operation’ (OSCE), wadda ke kasar Turai ta bayyana cewa zaben wanda aka gudanar a ranar Lahadi bai sami inganci yadda ya kamata ba, kan yadda aka yi watsi da dukkanin tsare-tsaren tabbatar da adalci a zaben.

Duk da na dan gamsu da abubuwan da ya bayyana, amma kuma inda ya ce sakamakon wata takardar manema labarai da kungiyar ta OSCE ta fitar, a karkashin ofishi na musamman na kwalejin horar da harkokin dimokuradiyya mai suna ‘Democratic Institutions and Human Rights (ODIHR).’ Sakamakon takardar ya nuna cewa tun da fari ma zaben bai doru bisa hanyar gaskiya ba, kuma ba a yi wa bangarorin biyu adalci kan yadda aka gudanar da zaben ba.

“A hakikanin gaskiya zaben na raba gardama da aka gudanar ranar 16 ga Afrilun 2017 bai sami ingancin aiki ba, kuma bai cika sharuddan zama abin tinkaho ga sauran kasashe ba, musamman na Turai. Abin tunawa da a ranar yin wannan refrendum ake ta so a yi.”

Rahotannin sun yi kunnen doki da kusan mafi yawan rahotanni kan sakamakon zaben na raba gardama. Hakan ma ta sa wadanda aka baiwa alhakin sa-idanu kan zaben, sun bayyana rashin gamsuwarsu dangane da yadda komai ya gudana. A hankalce kenan, yanzu Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai ci gaba da mulki har sai shekarar 2029, wanda zai sa ya kasance daya daga cikin manyan shugabannin duniya da za su dade a mulki.

Jami’an na kasar waje, gami da wasu hukumomi, sun sa idanu wajen ganin zaben ya gudana lami-lafiya, sun yi tir da dukkanin abubuwan da ke faruwa a kasar, wanda a mahangarsu, za su iya zunguro tsuliyar dodo da kansu! A nan ya kamata masu karatu su fahimci.

A ‘yan kwanakin nan ne, idan an yi la’akari da al’amuran da ke gudana a Turkiyya a daular saboda haka a yau, a matsayin Turkiya na makwaciyar Syria dole ne ta iya yi wajen daurewa ga matsalolin da yakin makwabciyarta Siriya suka haifo.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar, wanda ya auku a ranar 15 ga Yulin 2016, al’ummar Turkiyya suna ta gamuwa da matsaloli daban-daban. Sai dai akwai alamun da biyu a ke dukan biri da rani a cikin kasar ta Turkiyya, wato tun daga fushin damina! Manyan tambayoyin da al’ummar duniya suka kasa fahimta ya zuwa yau shi ne, mene ne dalilin da ya sanya ake yakar bangare daya kawai? Me ya sa hukumomin kasar ta Turkiyya suka dora karar-tsana a kan fitaccen Malamin kasar, Fethullah Gulen? Wasu daga cikin rahotannin na cikin gida sun tabbatar da cewa rikicin tsakanin Shugaba Erdogan da Sheikh Gulen ba ya rasa nasaba da siyasa. A cewar rahotannin, Gulen yana daga cikin fitattun mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ba wa Shugaba Erdogan goyon bayan samun shiga gidan sarautar kasar, amma daga bisani, wasu ‘yan ba-ni-na-iya suka shiga tsakani, wanda hakan ta tilasta wa Sheikh Fethullah barin kasar tasa ta gado, ya koma cikin kasar Amurka, inda a yanzu yake zaman gudun hijira.

Fethullah dai, kamar yadda rahotanni daga kafafen yada labarai na duniya suke nuni fitaccen malami ne da ya shafi shekaru da dama yana yin kira ga al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da tafarkin rayuwar fiyayyen halittu Annabi Muhammad (SAW). Muhimmin sakonnin yake aikawa a ko’ina a duniya shi ne, Musulmi shi ne kadai tsayayyen mutumin da zai iya tabbatar da zaman lafiya a doron kasa, ta hanyar ayyuka nagari, yin riko da sunnonin Manzo (SAW). A mafi yawan rubuce-rubucensa, Sheikh Gulen ya fi mayar da hankali kan yadda ake bata sunan addinin Musulunci musamman a yanzu da duniya ke kokarin danganta wasu gungiyoyin ta’addanci da Islam. A mafi yawan ra’ayoyin malamin, yana koyar da tsantsan zama a matsayin masu neman ilmi da aiki da shi.

Duk da Turkawan tuni sun san halin da ake ciki, amma dai har yanzu tsugunne ba ta kare ba, domin kuwa ra’ayoyin kasashen waje na ci gaba da nuna irin matsalolin da zaben ke ciki.

Sheikh Ja'afar: 'Ku fayyace gaskiya 'yan sanda'


Hakkin mallakar hoto
NIGERIAN SENATE

Image caption

Batun dai ya taso ne bayan shekara goma da kashe Sheikh Ja’afar Adam a Kano

Sanata Danjuma Goje ya buƙaci rundunar ‘yan sandan ƙasar, ta fito ta bayyana gaskiya kan mutanen da suka kashe malamin addinin musulunci Sheikh Ja’afar Muhd Adam.

Shugaban kwamitin kasafin kuɗi a majalisar dattijan Nijeriya, sanata Danjuma Goje ya ce ya yi wannan kira ne saboda yadda ake ƙoƙarin goga masa kashin kaji.

Ya ce “amma na haƙiƙance ba ni da wani alaƙa da takardar da ta shafi wai yadda Shekarau ya tsara halaka marigayi Sheikh Ja’afar…”

A cewarsa “‘Yan sanda, kamata ya yi su fi kowa shinin wa ya kashe Sheikh Ja’afar. Wa ya tsara.”

Sanata Goje na mayar da martani ne a kan bayanin da rundunar ‘yan sandan ta yi game da kuɗi da takardun da ta gano yayin samamen da ta kai gidansa.

‘Yan sanda sun ce a cikin takardun akwai wani fayel mai ɗauke da rubutu a kan kashe Sheikh Ja’afar Adam a Kano, har ma sun ambaci sunan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tuni dai wannan bayani ya janyo gagarumin ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta a tsakanin ‘yan Nijeriya.

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci yayin sallar asubah a Kano.

Danjuma Goje dai ya ce bayanin ‘yan sanda wani yunƙuri ne kawai na shafa masa kashin kaji “don a cuce ni.”

Ya ce yana wannan magana ce don ya lura da yadda ake son ɓata masa suna. “A manna mini abin da ba gaskiya ne a jikina ba.”

Ya zuwa yanzu dai ba a ji martanin da tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya mayar game da batun ba.

WASANNI: Messi Ya Zura Kwallo Ta 500


WASANNI: Messi Ya Zura Kwallo Ta 500

|

Lionel Messi ya samu nasarar ci wa kungiyarsa ta FC Barcelona kwallo ta 500, a tsawon lokacin da ya shafe yana fafatawa kungiyar tasa wasanni.

Kwallon ta 500 din da Messi ya ci ta bai wa Barcelona damar samun nasarar kan Real Madrid da kwallye 3-2 a karawar da suka yi a jiya Lahadi.

Kwallaye biyun da Messi ya zura a ragar Madrid ya kawo karshen shekaru uku da dan wasan ya shafe ba tare da ya samu nasarar jefa kwallo a ragar Madrid ba, a duk lokacin da kungiyoyin biyu zasu kara.

A sauran wasannin da aka kara a gasar Laliga ta Spain kuwa, Real Sociedad ta samu nasara kan Deportibo La Cruna da 1-0, sai Celta Bigo da tayi rashin nasara a hannun Real Betis da 1-0 yayinda Las Palmas da Alabes suka tashi 1-1 a wasan da suka fafata.

A tsayuwar Teburin gasar Laligar kuwa, Barcelona ke kan gaba da maki 75, Real Madrid na biye mata itama da maki biyar wadda kuma take da kwantan wasa sai kuma kungiyar Atletico Madrid a matsayi na da maki 68.

Kungiyoyi uku na karshe kuwa sun hada da Sporting Gijion ta 18 da maki 23, Granada ta 19 da maki 20 sai kuma Osasuna da ta dauki teburin a ka a matsayi an 20 da maki 18.

Al'ummar Kano na fama da ƙamfar ruwan sha


Hakkin mallakar hoto
TOMMY TRENCHARD / IFRC

Image caption

Al’ummar birnin Kano na kokawa da matsalar karamcin ruwan sha da ta addabesu shekara da shekaru

Al’ummar birnin Kano sun auka cikin matsalar ƙarancin ruwan sha, inda unguwanni da dama suka koma amfani da ruwan rijiya da na famfon tuƙa-tuƙa.

A lokuta da dama waɗannan kafofi ba su da ingantaccin tsafta don haka akwai kasadar yaɗuwar cutukan da ake bazuwa ta hanyar ruwa.

Wani magidanci Malam Hamisu a unguwar Agadasawa ya ce suna matsalar ruwan sha sosai duk da yake akwai kawunan famfo.

Ya ce “sai mu shekara ruwa(n famfo) bai zo mana unguwar nan ba. Ya ce muna sayen ruwa ne daga masu kurar ruwa kuma suna sayar da jarka ɗaya kimanin Naira 30.”

A cewarsa, ɗawainiyar ta yi yawa. “Ina da mata ɗaya da yaro shida.”

Shi ma wani Rabi’u ya ce matsalar ƙarancin ruwan ta yi tsanani don kuwa sukan niƙi-gari zuwa wasu unguwanni don taro ‘yan ga-ruwa.

Kasuwar ‘yan ga-ruwa ta buɗe

Wani mai gidan sayar da ruwa mai suna Buhari a yankin Ƙofar Nassarawa ya ce suna matuƙar ciniki, ya ce a rana yakan sayar da ruwa na kimanin naira dubu uku zuwa sama.

Shi ma wani ɗan ga-ruwa, Malam Abdu Ƙyaure ya ce yana kai ruwa unguwannin da suka haɗar da Sabuwar Ƙofa da Sharaɗa da ƙofar Nassarawa da kuma Sokoto road.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, Alhaji Sule Riruwai ya ce na’urorin tura ruwa da ake da su zuwa birnin Kano na buƙatar gyara.

Ya ce a cikin na’ura takwas da ake ita a Kano, guda uku ne kacal ke aiki wurjanjan. Ko da yake, nan da mako uku za su kammala gyare-gyare.

Kwamishinan ya kuma zargi masu aikin kwasar yashi a koguna da karkatar da akalar ruwa saboda aikace-aikacensu.

KASASHEN WAJE: Sojojin Afghanistan 140 Suka Salwanta A Hannun Taliban


KASASHEN WAJE: Sojojin Afghanistan 140 Suka Salwanta A Hannun Taliban

|

Mayakan Taliban sun kashe sojojin Afghanistan kimanin 140 a wasu jerin hare-hare da suka kaddamar masu a sansaninsu da ke yankin Arewacin kasar a ranar Juma’a da gabata.

Wani Kwamandan sojin Amurka, Janar John Nicholson ya bayyana cewa, Taliban ta kai hare-haren ne kan sojojin da ke dawowa daga sallar juma’a da kuma wadanda ke kalaci a wani kanti cin abinci a sansanin.

Sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar kashe 10 daga cikin mayakan a arangamar da suka shafe sa’o’i a shalkwatar sojojin da ke birnin Mazar-i-Sharif.

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce, mayakan sun kai harin ne sanye da kakin soji don bad-da-kama. Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya ce, harin wani ramako ne don huce takaicin kisan da aka yi wa jiga-jigan kungiyar da dama a yankin Aarewacin Afghanistan.

RA’AYINMU: Ranar Yaki Da Cutar Zazzabin Cizon Sauro Ta Duniya


Kowace ranar 25 ga watan Afrilu, Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin gudanar da gangamin yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya. Sai dai wasu shugabanni a Nijeriya sun danganta karuwar matsalar ga halayyar ‘yan kasa rashin tsaftace muhallansu.

A wani bincike da kasar Amurka ta gudanar, kididdiga ta nuna cewar akalla mutane milyan 80 ne kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, yayin da kusan mutane dubu 300 ke rasa rayukan ta dalilinta a kowace shekara, ba a duniya baki daya ba, wannan jadawali na iya Nijeriya ne kacal.

Zazzabin cizon sauro wata kwayar cuta ce wadda ke gurguntar da rayuwar mutane, wadda ke yaduwa ta wurin macen sauro. Da farko an yi tsammani cewa cutar tazo ne tawurin iska maras kyau.

Kimanin kashi 40 na adadin mutane a duniya, yawancinsu wadanda ke zaune a kasashe matalauta, su na cikin hadarin kamuwa da ita. An sami kauda cutar a kasashen da suka ci gaba a farkon karni na 20. Amma zazzabin cizon sauro na da hadari a yawancin kasashen Afrika inda ya kashe fiye da mutane milyan 300 a duniya, amma adadin wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar ya ragu zuwa mutuwar milyan daya a shekara.

Kusan kowacce shekara, mata masu ciki kimanin dubu 10, suna kamuwa da wannan cutar a Nijeriya, musamman a lokacin daukar cikinsu na haihuwar farko. Kariyar wannan cutar ya hada da amfani da gidan sauro mai magani.

Ya kamata kowacce mace tana kwana cikin gidan sauro ta kuma rika shan magani (Sulfadadine/pyrimethamine), kwaya uku sau biyu a lokacin da ta dauki ciki musamman a makonni 16 na farkon cikin, da kuma sau uku cikinda suke dauke cutar sida.

Tun a shekarar 2015, aka samar da maganin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na farko ya cika muhimman ka’idojin da aka shimfida kafin a amince a fara amfani da shi a kasashen Afrika.

Daga wannan lokaci zuwa yau, ta wata fuskar za a iya cewa maganin rigakafin cutar ya taka rawa kwarai wajen rage yiwuwar kamuwa da zazzabin cizon sauro wanda yake da tsananin tasiri musamman ga kananan yara ‘yan kasa da shekaru hudu.

A wani taro da Hukumomin Lafiya suka gudanar a Nijeriya, an bayyana cewar an samu gagarumin ci gaba ta fuskar yakar wannan cutar. Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Abdul’Aziz Yari Abubakar, ya ce gwamnatocin kasar ana su bangaren na daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai ya ce wajibi ne al’umma sai sun bada gudunmuwa.

A rahoton Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinikin Duniya, wato WHO, daga shekarar 2001 zuwa yanzu, an samu nasarar hana kamuwa da cutar har sau milyan 663 a yankin nahiyar Afirka kudu da hamadar Sahara, inda a nan ne ake samun kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar.

Ga dukkan alamu Gwamnatin Nijeriya na iya bakin kokarinta wajen ganin an yi bankwana da wannan cuta daga kasar kwata-kwata, kamar dai yadda wasu kasashen tuni suka manta da barazanar kamuwa da ita.

Kasashe da yawa sun bi nasu matakan da kuma hanyoyin da suke gani za su magnace cutar zazzabin cizon sauro, musamman wajen bawa shashen ma’aikatar lafiya cikkakiyar kulawar da ta kamata. Kowace kasa tana kallon irin illar da ke tattare da kamuwa da cutar, shi ya sa suke mayar da hankali don bullo da tsarin yi ma ta dibar Karen mahaukaciya.

Abubuwan da suka fi mayar da hankali sun hada da; wayar da kan al’umma kan tsaftace muhalli, kula da lafiya a matakin farko, ziyartar asibiti da zarar an ji alamun zazzabi, amfani da ingantattun magunguna wadanda da suke da amincewar kwararrun likitoci.

Ma’aikatar Lafiya ta Nijeriya na da rawar takawa wajen magance cutar zazzabin cizon sauro a kasar baki daya, musamman da yake ana samun dauki daga Hukumar lafiya ta Duniya WHO, wadda take bada magunguna kyauta daga cikin kudaden da take samu na gudunmawa wanda manyan masu kudi na duniya ke ba ta. Baya ga wannan, kaso mafi tsoka, WHO tana samunsa ne daga ainahin kudin da manyan kasashen duniya ke bayarwa da sunan tallafi.

A Nijeriya, Uwargidan Gwamnan Jihar kebbi, Hajiya Dakta Zainab Bagudu, na sahun gaba cikin wadanda suka himmatu wajen bada kulawa ta musamman ga masu fama da wannan cuta, inda take amfani da gidauniyarta Medicaid domin bada tata gudunmawar.

A lokacin da ake tsaka da gangamin yaki da cutar a duniya, gidauniyar Medicaid ta ware rana guda domin yin gwaji da bada magunguna kyauta ga wadanda suka kamu da cutar.

Hakika hannu daya ba ya daukar jinka. Saboda haka, Gwamnati kadai ba za ta iya magance wannan cuta ba, dole ana bukatar masu hannu da shuni su bada tasu gudunmawar ta fuskar tallafin kudade ga cibiyoyin da ake da su a Nijeriya, wadanda suke da kwarewa kan magance cutar cizon sauro.

 

Barcelona za ta kai karar shugaban Malaga kan kalaman batanci


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelona da Real Madrid suna da maki daidai a saman teburin La Liga

Barcelona za ta kai karar shugaban kungiyar Malaga Abdullah Al-Thani ga hukumomin wasan Spaniya kan kalaman batanci da tace ya yi mata a Twitter.

Ce-ce-ku-cen ya fara ne lokacin da wani mai goyon bayan Barca ya bukaci Al- Thani a shafin Twitter, kan Malaga ta doke abokan hamayyarsu Real Madrid a wasansu na ranar 21 ga watan Mayu.

Daga nan ne sai shugaban na Malaga ya mayar da amsa inda ya rubuta cikin Larabci ; “Da taimakon Allah za mu doke su a fili, amma dattin kumfar Catalonia (ma’ana Barcelona) ba za ta ji kanshin kofin ba, bayan karyar da ta yi a kan koci Michel,”.

Shi dai kociyan Malaga Michel ya harzuka magoya bayan Barcelona ne inda ya nuna cewa yana son Real Madrid ta dauki La Liga.

A wata sanarwa da Barcelonan ta fitar ta ce ta nuna rashin yardarta da bacin rai a kan kalaman da shugaban Malaga, Abdullah Al-Thani, ya rubuta a Tweeter, wadanda sun saba wa manufar wasan cikin lumana da kuma dokokin wasanni.

Barca ta kara da cewa: “A bisa wannan dalili ne kungiyar za ta gabatar lamarin kwamitin yaki rikici na hukumar wasanni, sanna kuma ta mika batun zuwa ga hukumar kwallon kafa da ta gasar La Liga.”

Zakarun na Spaniya, Barcelona da Real Madrid suna kankankan a maki a La Liga, amma Barcan na gaba saboda nasarar da ta fi samu a kan Real din wadda take da kwantan wasa daya.

A ranar karshe ta La Liga, 21 ga watan Mayu, yayin da Real za ta je gidan ta 14 a tebur Malaga, Barcelona za ta kasance a gidanta da Eibar wadda yanzu take ta takwas.

Kocin Malaga Michel ya taimaka wa Real Madrid ta dauki kofin La Liga sau shida a shekara 14 da ya yi a Bernabeu.

An tashi wasan Man City da Man United ba armashi


Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Marouane Fellaini ya samu jan katinsa na uku a Premier kuma na biyu a Manchester United

Manchester United ta ci gaba da zama a matsayinta na biyar a teburin Premier bayan wasanta da abokiyar hamayyarta Manchester City, wanda suka tashi ba ci a Etihad, amma an kori Fellaini.

United tana da maki 64 a wasa 33 yayin da Manchester City ta hudu a tebur take da maki 65, ita ma a wasa 33.

Saura minti shida a tashi daga wasan alkalin wasa ya kori Marouane Fellaini, wanda bai dade da samun katin gargadi ba saboda keta da ya yi wa Aguero, bayan da ya sake yi wa Sergio Aguero karo.

United wadda take maki biyu a bayan Liverpool ta uku da kwantan wasa daya, ta yi wasa 24 kenan na Premier ba tare da an doke ta ba.

Wasanta biyu daga cikin biyar da suka rage za ta yi su ne a waje, a gidan Arsenal ranar 7 ga watan Mayu da kuma gidan Tottenham ranar 14 ga watan Mayu.

Manchester City wadda za ta gama kakar farko da Pep Guardiola ba tare da kofi ba tana maki daya tsakaninta da Liverpool, amma tana da kwantan wasa daya

RAHOTO: Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da Daukar Masu Mukamin ASP Sai…


RAHOTO: Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da Daukar Masu Mukamin ASP Sai…

|

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sanda, DIG Maigari A. Dikko ya yaba wa rundunar  ‘yan sandan Jihar Zamfara bisa kokarinsu na amaso dabbobi da barayi suka sace guda 2,734 tare da damke gungun masu sace mutane suna garkuwa da su.

DIG ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya kawo ziyar aiki a jihar ta Zamfara.

Ya bayyana cewa wannan ziyarar albishir ce ga ‘yan sada daga Sufeto Janar cewa hukumarsu ta ‘yan sanda na shirin samar wa ko wane dan sanda gida mallakar kansa lokacin da zai a je aiki ya kasance yana da gida nasa. A karkashin shirin ya ce kamfanoni za su samar da gidaje 500 a ko wace jiha.

Ya kara da cewa “Hukumar ‘yan sanda na jan kunne ga wadanda suka turje a kai masu canjin wajen aiki suka ki komawa su sani cewa su ‘yan sandan kasa ne ba na jiha ba dan haka duk inda aka kai mutum dole ya tafi kuma idan mutum ya yi turje lalali zai gamu da hukunci.

“Kuma daga yanzu Hukumar ‘yan sanda ba za ta kara daukar masu mukamin ASP ba sai wanda ya yi karatu a Makarantun horar da ‘yan sanda”. In ji shi.

A nasa jawabin mai masaukin baki, Kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara Shaba Alkali ya bayyana jin dadinsa da ziyar DIG Dikko kuma ya bayyana masa nasarorin da suka samu da kuma kalubanen da su ke fuskanta na aiki.

Fifa ta ci tarar Brazil da Argentina da Mexico kan kyamar 'yan luwadi


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fifa ta ci tarar kasashe da dama a kan amfani da tartsatsin wuta da wakokin kyamar masu neman jinsi daya a filin wasa

Fifa, ta ci tarar hukumomin kwallon kafa na Brazil da Argentina da Mexico a kan samun magoya bayansu da laifin wakokin kyamar masu neman jinsi daya a lokacin wasannin neman zuwa gasar Kofin Duniya na 2018.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta ci tarar Brazil fan 27,248 yayin da ta ci tarar Argentina 15,565, sannan ta ci tarar Mexico fan 7,781.

Fifa ta ce tarar ta wanna laifi ne na rera wakokin tsanar masu neman jinsi daya da kuma sauran abubuwa na rashin da’a da ‘yan kallonsu suka yi.

A sanarwar da ta fitar Fifa din ta ce, sun aikata laifin ne a lokacin wasannin baya-bayan nan na neman tikitin zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2018, amma ba ta fayyace wadanna wasanni ba ne.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Albania Fifa ta ci tararta fan 77,945 bisa laifuka da dama da magoya bayan kungiyar wasan kasar suka yi a lokacin wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya da Italiya ta doke su a gidanta ranar 24 ga watan Maris.

Laifukan sun hada da jefa abubuwan tartsatsin wuta cikin fili, lamarin da ya kai ga tsayar da wasan na wasu mintina.

Ita ma Iran an ci ta tararta fan 39,015, saboda magoya bayanta sun yi amfani da abubuwan tartsatsin wutar a filin wasan da ke makare da ‘yan kallo lokacin wasansu da China.

Su ma kasashen Bosnia da Herzegovina da Poland da kuma Montenegro Fifa ta ci tararsu saboda ‘yan kallonsu sun irin wannan laifi na amfani da abubuwan tartsatsin wuta a filin wasa.

Tsohon dan wasan Gabon Moise Brou Apanga ya mutu a fili


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Moise Brou Apanga ya yi wa Gabon wasa 33 da suka hada da na gasar cin Kofin Afirka karo biyu

Hukumar kwallon kafa ta Gabon ta bayar da sanarwar mutuwar da wasan baya na kasar Moise Brou Apanga sakamakon bugun zuciya.

A sanarwar da hukumar ta bayar ta rasuwar Apanga, mai shekara 35, ta ce ya rasu ne a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta yanzu Canon de Libreville, ranar Alhamis.

Dan wasan bayan haifaffen kasar Ivory Coast ya yi wasa a Turai a kungiyar Brest ta Faransa da kungiyoyin Perugia da Brescia na Italiya, bayan ya fara wasansa na kwararru a Romania.

Ko da yake an haifi Brou Apanga a Ivory Coast amma lokacin da ya fara zuwa kungiyar tasa ta yanzu Canon de Libreville ko FC 105, kociyansu na lokacin Alain Giresse ya shawo kansa ya koma dan kasar Gabon.

Daga nan ne kociyan da Faransa ya fara sa shi a wasan kungiyar kasar ta gabon a shekarar 2007, kuma ya taimaka masa ya tafi kungiyar Brest.

Apanga ya yi wa Gabon wasa a gasar cin Kofin Kasashen Afrika a shekarar 2010 da 2012.

Kyaftin din Gabon Pierre Emerick Aubameyang ya bayyana ta’aziyyarsa ta rashin dan wasan a shafinsa na Twitter, inda ya ce ”mun yi wasa tare, mun kuma kara a wasa a kungiyoyinmu daban-daban, amma abin farin ciki ne kasancewa tare da kai a ko da yaushe, Allah Ya jikanka dan uwana.

Gerrad zai yi kociyan matasan Liverpool


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Steven Gerrard (a hagu) ya koma Anfield a matsayin kociyan matasa a farkon 2017

Tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya ce lokaci ya yi da zai matsa gaba ya yi kocin kungiyarsa, bayan an tabbatar masa cewa zai horad da yi kociyan ‘yan wasan kungiyar ‘yan kasa da shekara 18.

Tsohon kyaftin din na Ingila, wanda ya yi wa Liverpool wasa sau 710 a cikin shekara 17 da ya yi zai maye gurbin Neil Critchley, kociyan ‘yan kasa da shekara 18 din, wanda shi kuma zai kula da kungiyar ‘yan kasa da shekara 23.

Gerrard, mai shekara 36, ya koma Liverpool ne a matsayin kociyan matsa a watan Fabrairu bayan da ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa a shekarar da ta wuce.

A lokacin da yake wasa a Anfield, Gerrard ya ci kwallo 186 kuma ya taimaka wa kungiyar ta dauki manyan kofuna takwas, da suka hada da Kofin Zakarun Turai na 2005, lokacin da kwallon da ya ci a wasan karshe ta ba wa kungiyarsa kwarin guiwa ta farfado ta doke AC Milan.

Bayan ya bar Liverpool a karshen kakar 2014-15 , ya koma LA Galaxy ta Amurka, inda ya ci kwallo biyar a wasa 34 a kaka biyu da ya yi kafin ya yi ritaya.

Haka kuma ya yi wa Ingila wasa 114, inda ya yi 38 a matsayin kyaftin, abin da ya sa ya zama na hudu a wadanda suka buga wa Ingila wasa.

El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin Buhari -Tinubu


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bola Tinubu na cikin wadanda suka mara wa Buhari baya a zaben 2015

Daya daga cikin shugabannin jam’iyya mai mulki a Najeriya kuma tsohon gwamnan Lagos, Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki, da kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ne suka hana shi zama mataimakin Shugaban buhari.

Jaridar Punch ta ambato littafin da babban editan Jaridar This Day, Olusegun Adeniyi, ya rubuta mai suna ‘Against The Run of Play’ yana cewa Tinubu ya ce ‘yan siyasan biyu suka hana shi zama abokin takaran Shugaba Buhari a zaben 2015.

A cewar Tinubu, El-Rufai da Saraki sun yi ta nanata wa Buhari da kuma ‘yan jam’iyyar cewar idan aka hada ‘yan takara Musulmai biyu, jam’iyyar ba za ta kai labari a zaben ba.

Tsohon gwamnan na Legas ya ce sun kaddamar da kamfae din hana shi zama abkoin takaran Buhari ne a boye duk da cewar duk abubuwan da jam’iyyar ke yi ana yin su ne a idon kowa.

Ya ce Nasir El-Rufai ya so Buhari ya dauko Pasto Tunde Bakare wanda ya yi abokin takaran Shugaba Buhari a zaben 2011 a karkashin jam’iyyar CPC.

Tinubu ya ce shi janye daga zama abokin takaran ne domin ya mika sunan farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ya taba ambata wa shugaban a shekara 2011.

Wannan labarin ya kara haske kan irin abubuwan da suka wakana a lokacin da ake neman wanda zai zama abokin takaran Muhammadu Buhari gabanin zaben 2015.

Duk da haka Bukola Saraki ya ambato ‘hana wasu zama abokin takaran Buhari’ a matsayin daya daga cikin laifukan da suka aka gurfanar da shi a gaban kotun da’ar ma’aikata a shekarar 2016.

Kawo yanzu gwamnan Jihar Kadun abai ce komai ba game da labarin.

An yi gasar ɓaunar da ta fi kyau a Pakistan


Hakkin mallakar hoto
WIKIMEDIA/JUGNI

Image caption

Hausawa na yi wa bauna kirari na saniyar sake

Akalla ɓauna 200 aka tara domin gudanar da gasar wacce ta fi kowacce kyau a kasar Pakistan.

Jaridar Dawn newspaper ta kawo rahoton cewa manoma da makiyaya ne suka hallara a birnin Mingora, babban birnin gundumar Swat da ke arewacin Pakistan, a wani taro da aka gudanar na kwana uku domin bunkasa harkar kiwo.

Taron, wanda hukumar raya kasashe ta Amurka USAID ta shirya, kuma hukumar bayar da agaji ta farar hula ta kasar ta sanya tsabar kudi naira 75,000 ga wacce ta zo ta daya.

Laiq Badar ne ya samu nasarar samun kudin, wanda ya nuna farin cikinsa da samun nasarar da baunarsa ta yi inda ya shaida wa jaridar Dawn da cewa, “Ina da bakane goma da nake kiwonsu a wuri daya wadanda su ne hanyar da nake samun abin biyan bukatuna na yau da kullum.

Wani jami’in hukumar kula da dabbobi Muhibullah Khan, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Pakistan APP cewa, kiwon bauna na da fuskoki nau’i-nau’i, kuma babbar manufar wannan taron shi ne, “wayar da kan jama’a da kuma nunawa mutane muhimmancin kiwon wannan kyakkyawar dabba.”

Wannan ne karo na farko da aka taba gabatar da gasar baunar da tafi kowacce kyau a Pakistan.

A yankin Swat kawai ake samun baunar, kuma an ce a yankin ne kawai ake samun sanyi da za a iya kiwonsu a wurin, saboda haka ne masu dabbobin ba sa sayar da su ko yankawa idan lokacin sanyi ya karato.

A cewar jaridar, wadanda suka kware a gasar ta garin Mingora sun ce ba ya ga kyau da dabbobin suke da shi, suna samar da madara da kuma wadataccen nama.